Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kike?"

Malamin ya yi mata magana a tsawance, ta ɗan bishi da kallo tana ƙunƙuni, a duniya idan da wanda ta tsana cikinsu har da Malam Bukari, yana cikin wadanda ba su fiye ba ta ƙofar kawomusu wargi ba. Ta kauda kai ta yi ciki, sai da ta gama kallon mazauna saman bencinan da ba su fi biyar ba a ajin, ta watsa musu harara kafin ta yi ƙwafa ta zauna gefen Haulatu saman darduma. Malam Bukari na juya baya ciki bada umarnin a yi sauri a bada amsoshin tambayoyin da ya rubuta a allo a ƴar takarda, ta kalli Haulatu cike da ɓacin rai da murya ƙasa-ƙasa ta ce.

"Wai ke meyasa idan kin zo ba kya tashi shegu daga benci ki kama mana wuri? Kinsan dai na tsani zama a ƙasa ko?"

Haulatu ta wurga mata harara.

"Toh sannu Uwani, tunda kin zo ai sai ki tashe su. Kinsan tun lokacin da nake jiranki ne?"

Hindatu jin haka ta ɗan fiddo idanu kaɗan.

"Haba? Ki ce da labari."

"Akwai labari amma fa ba wani mai dadi ba. Bari dai wannan ya fice naga idanunsa a kan mu."

Wannan bai sa Hindatu damuwa ba, kallonsa ta yi kadan sannan ta ja guntun tsaki bayan ta kauda kai tana mai karɓar takardar da Haulatu ta fillo mata a cikin littafi.

"Ke dallah rabu da shi, ni faɗamin kawai, duk na matsu na ji me Mijin Umma ya aikata don nasan dai tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi."

Ita dai Haulatu sai ta yi dariya kawai ganin idanun Malamin dai na kansu, a dole Hindatu ta bar zancen sai bayan ya fita ne ta tashi wasu akan tebur suka koma, ganin haka Haulatu ta basu aron dardumarta su zauna a ƙasa. Ba yadda suka iya face su karɓa sanin da suka yi idan ma sun ƙi wannan zaluncin da Hindatun da ta yi musu babu wanda zai iya taka mata burki. Koda kuwa an yi magana, toh fa abin da zai biyo baya bai wuce ta tare su a hanya ta ci zalinsu son rai ba.

"Ina jinki." Cewar Hindatu.

Hakan ya ba Haulatu damar fayyace mata batun Ciyaman Nazifi. Wani uban ashariya da Hindatu ta yi murya a ɗage, sai da ƴan ajin duka suka dube su. Ta banka musu harara.

"Uban me ku ke kallo?" Sai kuwa suka kauda kai, wasu kuwa suka ja tsaki.

"Amma mijin Umman nan ya cika azzalumin ƙarshe, wallahi kar ki sake ya tauyemaki haƙƙinnan. Ke me kike jira da ba za ki bi shawarata ku bar masa gidan ba?"

Cikin rashin kulawa da kiran Baban da azzalumi da aka yi, Haulatu ta taɓe baki gami da jan guntun tsaki.

"Wannan matar ce za ta yarda mu bar gidan? Ai ko asiri ya yi mata sai haka. Amma wallahi kin ji dai na rantse, ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zan bari ya cimma wannan halakakken burinnasa a kaina ba. Zan nuna masa nima na iya rashin kirkin."

"Ato, idan ba haka ba ko mu zo mu sha biki."

Faɗin Hindatu cike da tsokana tana dariyar shaƙiyanci, duka ta kai mata a baya, aikuwa ta gantsare. Haka suka cinye lokacin babu wani Malamin da ya shigo ajin da har aka fita hutun rabin lokaci. Dama sun saba, malamai ba su wadaci makarantar ba wannan ta sa ɗalibai da yawa suna zuwa ne kawai ba don suna samun wadataccen ilimi ko fahimtar abinda aka koyar ba yanda ya kamata. Zasu iya zuwa su wuni amma bai fi su sami darussa uku kacal ba. Wannan na ɗaya daga cikin illar da dalibai ke fuskanta a ire-iren makarantun na gwamnati. Hakan kan jawo nakasu da koma baya a harkar iliminsu. Sai ka ga ƴar sakandire babu turanci a bakin, hakanan shi kansa rubutun ba kowanne ya iya yanda ya kamata ba. Sassauƙar kalma sai ta gagari ɗalibi rubutawa.

Haka suka cinye ranar a makaranta da darussan da basu wuce uku ba aka tashe su. A hanya su na tafe su na hira inda Hindatu ke ƙara rura wutar tsanar haɗin auren a zuciyar ƙawarta. Aikuwa haƙanta ya cimma ruwa don Haulatu sai da ta ji ƙarfin gwuiwa fiye da na baya akan shirin yin gudun fanfalaki don tseratar da kai daga wannan mugun nufi na Mijin Umman.

Har suka zo hanyar da ta raba su hirar da suke yi kenan, ƙarshe dole suka bar sauran da zummar gobe Juma'a zasu hadu a gidan su Hindatun.

Kai tsaye Haulatu gida ta nufa, tun daga nesa ta hango su zaune saman benci ƙasan bishiyar darbejiya dake ƙofar gidan nasu. Wani guntun tsaki ta ja, majalisarnan ta su Audu Maada ya tsaya mata a ƙahon zuci, babu wani a unguwar da bai san da zamansu ba. Duk wani hira na dabanci da ma bushe-bushen hayaƙi ya tattara ne a wurinsu. Rigima ba irin wacce ba'a yi ba a unguwar akan majalisar nan amma hakan bai sa ta rushe ba sakamakon ɗaurin gindin da suka samu daga shi Uban gayyar, wato Maigidan, inda ya ce ai ƙofar gidansa ce ba ta wani ba kuma babu wanda ya isa ya hana su zama tunda ba shirginsu suke shiga ba. Magana har wurin ƴan sanda sai dai kasancewar shi ɗin mutum ne mai idanu cikin gwamnati yasa babu inda ƙarar ta je aka yi watsi da ita. Wannan ce ta sa kowa ya zuba musu idanu kawai, iyaye na takatsantsan wurin ja wa yaransu kunne akan shiga sabgar su Audu Maada balle kuma su kai ga shiga gidan.

Ta ƙara jan guntun tsaki gami da ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa. Haka har ta ƙaraso ƙofar gidan, za ta gifta su ta ji sun soma maganar tasu ta rainin wayo inda ta tsinkayi muryar Ɗan Aljan ya yi wani busa da baki sannan ya ce.

"Kai! Kai!! Ni fa wallahi Oga Maada ba don da manya a gabanmu ba, babu abin da zai hana ni farautar wannan babbar tsokar. Billahillazee tana..."

"Kai dallah ware can! Kai daɗina da kai ka cika zalama. Ina kai ina shiga gonar Ciyaman? Ai babu mai ninkaya a wannan kogin idan ba shi ba!"

Suka kwashe da dariyar zancen Duuna, Haulatu ta dube su ta watsamusu harara kamar idanunta za su faɗo sannan ta ƙarasa tura ƙofar bayan ta fidda kwaɗon ta shige, tana jinsu suka ƙara sakin wata dariyar ba ta ko saurare su ba don ya ci ace ta saba da haukansu da ba shi da magani. Maida ƙofar gidan ta yi ta rufe ruf sanin da ta yi ba su da kai, don su ce zasu shigo kai tsaye ba komai ne a wurinsu ba. Wanka ta soma yi ta sanya riga marar nauyi gami da ɗaura zani, ba ta tare da yunwa saboda Hindatu ta siyamusu wainar fulawa sun ci sun yi nak a makaranta, madadin ta yi sallah kawai sai ta shimfiɗe a tsakar gidan inda iska mai sanyi da daɗi ke bugowa, aikuwa nan da nan bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Ba ita ta motsa na sai da ta ji kamar ana faman dukan ƙyauran gidan, a dole ta tashi tana murza idanu gami da ƙarewa garin kallo, ga dukkan alamu dai yamma ta yi ganin yanda rana ta yi sanyi sosai.

"Ina zuwa!" Ta furta cikin muryar bacci, tana jin sadda Garba ɗaya daga cikin almajiran Umma masu yi mata dakon kaya na fadin. "Tana ciki, yanzu tayi magana."

Hakan ya fahimtar da ita Umman ce ta dawo. Koda ta buɗe, ta gan su tsaye ga uban manyan kuloli biyu da tarkacen kasko da sauran kayan girki. Ba wannan ba har da su Ɗan Aljan tsaye da yake bin ta da kallo kamar wani tsohon maye.

Fadi yake "Ai Ranki ya daɗe dama na faɗamaki tana ciki, muna nan ɗazu ta shige. Sai dai ko ta ɗan harba duniyar Mass (Mars)." Ya ƙarashe da dariyar shaƙiyanci, ita kuwa daga yanda Umman ta haɗe rai tana kallonta yasa ta fahimci kuskuren da ta yi na fitowa kai babu ko kallabi sai zanin da ɗaura saman ƴar rigar, duk dai ga ta a birkice alamun mai bacci.

Bayan ta shige ciki, yaran su uku suka bi bayanta da kayan suka sauke, sai da Umman ta sallame su ta ba su abinci da kudi sannan ta dawo kan Haulatu. Rai a ɓace ta ce "Kin yi sallar Azahar da La'asar?"

Ta turo baki kaɗan. "Yanzu fa na tashi daga bacci, shi zan yi."

Cike da takaici Umma ta girgiza kai.

"Ki ji tsoron Allah Haulatu, wannan rayuwar da ki ke yi na rashin sauke haƙƙin Allah a lokacin da ya kamata babban kuskure ne. Kina tunanin matsalolinki za su warware alhalin kina yiwa Allah yanda ki ke so? Wato yau ma ba ki yi ko tunanin zuwa Islamiyyar ba ko? Kin kyauta, ki cigaba, nidai Allah na gani ina iyakar bakin ƙoƙar.."

"Kai Umma, nifa ba cewa nayi ba zan yi ba. Haba don Allah, wannan masifar ma da kike ta yi ai sai ya ƙara cinye lokacin."

Umma ta saki baki kawai tana kallonta har ta cika ruwa a buta ta shige banɗaki tana ƙunƙuni, yanke ta idan tana cikin magana wannan ba sabon abu ne a wurinta ba, amma kalmar tana masifa ya yi mata ciwo ƙwarai. Haulatu sau da dama idan ta yi magana kamar an buɗe masai tsabar rashin sanin abin da ya dace ta fadi. Sam, ba ta iya tauna harshe kafin ta furzar ba, komai ya zo mata hakanan ta ke jinsa daidai a wajenta.

"Allah ya shirya." Abin da ta iya fadi kenan zuciyarta babu dadi sannan ta shiga tattara kayan, tun a kasuwa ta saka yaran sun wanke komai, maida su ta yi kawai kicin ta adana, abincin da ta rage musu da zasu ci, shi ta juye cikin madaidaitan kwanuka sannan ta shige daki don rage kaya ta watsa ruwa. Koda ta fito daga dakin, ta iske ta a tsakar gidan ta tayar da sallah bayan ta zura dogon hijabin Umman dake ajiye saman tabarmar. Ita kuwa bokiti ta ɗauka ta cika ta shige.

Haka Haulatu ta yi sallolinta kafin ta miƙe ta dauko faranti, kai tsaye ta dibi shinkafa da waken ta sanya kabeji da mai a samansu. Tana cikin ci Umman ta fito, cikin sakin fuska Haulatu ta dube ta.

"Lah Umma yau dai kin yi sa'ar mai, babu warin nan irin na rannan."

Ganin yanda ko kallonta ba ta yi ba ta shige ɗaki sai ta sha jinin jikinta.

"Ita kuma wannan ita da wa?" Ta yi tambayar a fili babu mai amsa mata, sai kuma ta ja guntun tsaki tunawa da ta yi mai yiwuwa rashin zuwa islamiyyarta ne ya yi wa Umman ciwo. Hakan yasa ta miƙe duk abincin ma ta ji ya fice a ranta don ita fa ba ta kaunar ta ga ko alamar ɓacin rai a fuskar mahaifiyarta.

"Umma ni ce ko? Ban je makaranta ba, kiyi hakuri na dawo kaina na ciwo. Amma zan je ran Lahadi tunda gobe juma'a." Kasancewar makarantar hutun juma'a da asabar ake yi.

Umman dai ba ta ce uffan ba ta zura doguwar rigarta ta shan iska, ganin dagaske dai ba za ta kulata ba yasa hankalinta tashi. Nan fa ta shiga ban hakuri har da su hawaye, Umma ta dube ta, dagaske ita laifinta ɗaya ta ke hangowa kanta, wato na ƙin zuwa makaranta, a ganinta shi ne dalilin fushinta. Ta ɗan yi shiru tana nazarin wannan wauta na ɗiyarta. Can kuma ta numfasa gami da soma magana.

"Shikenan, amma ki sani kalmar da kika yi amfani da ita na ina masifa, ba daidai ba ne yiwa babba ita. Ba ma wannan kaɗai ba Haulatu, ko kaɗan bai kyautu ace babba na magana ka katse shi ba, wannan yana nuni da rashin ladabi gareshi. Sannan ba sau ɗaya ba, na sha nunamaki illar wannan tsakin da kike yawan yi ga babba balle kuma ni da nake mahaifiya gareki ba daidai ba ne, na lura ya riga ya zamar maki jikin da yanzu da kuma nan gaba zai iya haifar maki da tarin matsaloli, koda ace ba a wurina ba, za ki iya samun matsala da gidan da za ki je nan gaba."

Cikin rashin fahimta Haulatu ta ce.

"Gida kuma? Ni zan je? Wayyo Umma kin amince kenan mu bar masa gidansa?"

Ta ƙarashe a ɗokance tana jin nesa ta matso kusa, burinta zai cika sai dai kuma girgiza kan da Umman ta yi ya sanya ta yi kamar ta ja tsaki sai kuma ta tuma ta saita leɓɓan da ta turo gaba da farko. Sosai ta lura da abin da ta yi niyyar yi, ta sani yarinyar sai a sannu za ta gyara.

"Umma wane gidan zan je na bar ki?"

Ta katse mata tunanin da ta tafi. Ta numfasa.

"Ita mace ai ba ta zama ba ce, dole wataran ki tattara ki je gidan wanda Allah ya ƙaddara shi ne mijinki."

Dariya sosai Haulatu ta sanya.

"Kai Umma kina magana kamar a irin Indiyarnan mai fassarar Hausa. Aure manya. Ai fa, Iro dai zai ga wacce zai kai gidan wancan tsohon ƙwarton mai sa..."

"Haulatu!" Tsawar Umman ya dakatar da ita. A zafafe ta cigaba da magana.

"Meyasa kika da taurin kai da kunnen ƙashi ne? Mahaifinki kike kira da wannan banzan sunan wai Iro? Na fadamaki duk lalacewarsa shi din Uba yake a wurinki! Kar ki kuskura ki kai ni maƙura! Aure kuma ai dole wataran ki yi shi! Kin fi kaunar ki zauna kina rayuwa cikin waɗancan ƴan daban masu shirin farautarki a kowane lokaci? Idan ke har yanzu ba ki san meke maki ciwo ba, ni na sani!"

Umman na kai wa nan ta fice daga ɗakin. Dagaske sosai Haulatun ta sha jinin jikinta, ko mene ne ta aikata, tana da tabbacin wannan faɗan ba iyaka nan ya tsaya ba, akwai wani abin da ke ran Umman da ta kasa fahimtarsa. Kusan ta mance rabon da ta ga bacin ranta irin wannan. Wannan yasa duk ta rasa sukuni. Daƙyar da suɗin goshi ta shawo kanta har ta sake bayan ta mata nasiha akan gyara kalamanta ko don gaba musamman ma na wannan sunan da ta sanyawa mahaifinta daga Ibrahim zuwa Iro.

Haulatu dai ta amsa da toh za ta gyara don komai ya wuce amma har a zuciyarta ba ta jin yana da wani sunan bayan Iro, ko a makaranta ma da Muhammad take amfani matsayin sunan Uba. Umma ba ta hana ta ba tunda dai ana jika, ita ta san sunan mahaifin baban Haulatun ne sai kawai ta rabu da ita.

***
Ya yi shiru yana juya cokali cikin kofin ruwan shayin dake ajiye saman teburinsa a ofis. Numfashi yake ja gami da furzarwa tamkar wanda ya ci gudu. Can kuma ya cire hannun ya ɗan bugi tebur har ruwan shayin na ɓata wasu takardun dake ajiye gefe. Hakan ya ɗan tsoratar da mutane biyun dake zaune a ofishin tare da shi. Babu wanda ya samu damar cewa uffan a cikinsu har sai da uban gayyar ya soma magana don kansa.

"Kai Ɗan Mutuwa! Ba fa zan yarda da wannan soki burutsun naka ba! Ya kake ƙoƙarin haramtamin abincin da Allah bai yimin iyaka da shi ba?! Ka fito kawai a mutum, kai tsaye ka cemin ba za ka iya auramin ɗiyarka ba kawai!"

Mutumin da aka ambata da Ɗan Mutuwa cikin maƙurar ladabi ya soma magana.

"Haba Yallaɓai, na rantse ka fi ƙarfin dukkan wata alfarma. Ni ko Na'imar ka gani kake so ai zan iya sakarta ka aura ballantana kuma abin da yake ƙarƙashin ikona? Kawai dai akwai babbar matsala ne."

Ya ƙarashe murya a ƙasa da tunanin ƙaryar da zai shirgawa Ciyaman ya samu su rabu lafiya.

"Wace irin matsala ce kai kuwa Ɗan Mutuwa da har za ka kasa biyawa Yallaɓai buƙatar da ba ta fi ƙarfinka ba?" Cewar wani kakkauran mutumin dake zaune a kujera suna fuskantar juna. Ɗan Mutuwa ya sauke ajiyar zuciya, ya kula gaba ɗaya hankulansu na gareshi wannan ya sanya shi haɗiyar yawu daƙyar.

"Mata maza ce."

Abin da ya tsinci harshensa da furtawa kenan, babban burinsa wannan ta kawo ƙarshen zancen, ya kasa haɗa idanu da su duka. Kirjinsa na bugawa tamkar zai fito. Kalaman Haulatu ɗiyartasa ke amsa kuwwa a dodon kunnuwansa cewar da ta yi za ta fallasa dukkan sirrinsa. Toh kuwa da fashewar ruɓaɓɓen ƙwan nan baragurbi, wanda warinsa zai shafi mutane da dama, ai ya gwammace ya yi wa maganar auren kisan gilla ko ta wace hanya.
*FITAR TSIRO*

*©️Rufaida Umar*

Paid book: 500
Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB
Phone number: 09034973645

Free page 3



"Ɗan Mutuwa, ni za ka kawowa wasa?"

Cikin dakiya ya girgiza kai gami da ƙara narkar da fuska kamar muminin da ya tuna kwanciyar kabari.

"Wane ni na zo maka da wasa Yallaɓai? Wa ya ƙi ɗakinsa da ƙwan jimina? Ai bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne. Tunku, ya san jibar da yake yiwa kashi, ba irinku ake zuwa gabanku da ƙaramar magana ba."

Jin haka sai kuwa jikin Ciyaman ya yi sanyi, komawa ya yi ya jingina da kujerar gami da ɗan rufe idanu. Tabbas dole ya yiwa abin tufka kafin wankin hula ya kai shi dare. Bai so ace wai Haulatu, mace ta uku cikin wadanda ya so aure amma ba a dace ba. Ga dai tafarkin da bokansa ya ɗora shi a kai, ruwansa ne ya yi gaggawar aure nan da sati lafin guguwar siyasa ta motsa, ruwansa ne ya yi fatali da zancen ya ci karo da sakamako mafi muni a rayuwa. Sharuɗɗa biyu bokannasa ya ba shi, ɗaya shi ne ya nemi matashin namiji su aikata alfasha, ɗayan kuwa shi ne ya nemi budurwa marar kowace nakasa ta kowane ɓangare ya aura, wato sabuwa dal a leda wacce aka yi mata kyakkyawar shaida ta kamun kai. Muddin ya cika waɗannan sharuɗɗan bayan layu da ya sa aka binne a sabon gawa, to babu abin da zai hana shi cimma nasara da yin tamola da abokan hamayyar kujerar takararsa na ɗan majalisar dokoki na Jaha. Budurwar farko ya samu rahoton tana shaye-shaye, ta biyu kuwa tana biye-biyen maza. Idanunta sun bude da son abin duniya hakan yasa take iya komai don ta samu biyan buƙata. Sai ga Haulatu wacce ya samu shaidu sama da hudu a kanta ta bakin majalisar su Maada cewar ba ta tsayuwa da kowa ba ta kula kowa. Asalima haushin ubanta take ji da munanan ɗabi'unsa, itama ashe ya yi kura ce lulluɓe da fatar akuya duk da dai abin ba daga gareta ba ne. 

"Ayi hakuri ranka ya daɗe."

Faɗin Ɗan Mutuwa karo na biyu, Ciyaman ya sauke ajiyar zuciya bayan ya dawo daga kogin tunanin da ya afka.

"Shikenan, kar ka damu. Kuturu da kuɗinsa ai alkaki sai na ƙasan kwano, zan samu daidai da zaɓina. Nasan inda zan nufa kuma."

Suka dube shi su biyun duka, shi dai Ɗan Mutuwa bai fahimci abin a zo a gani ba, shi kuwa ɗayan mai suna Mahadi, kasancewarsa na hannun damar Ciyaman ya gane karatun don haka ya dubi Ɗan Mutuwa.

"Kana iya tafiya."

Ɗan Mutuwa cike da jin haushin irin wannan mulkin mallaka da Mahadi ke nunamasa a gaban Ciyaman ya miƙe yana ɗaure fuska ya kama hanyar fita, Ciyaman ya maido shi baya ta hanyar kiran sunansa hakanan ya dawo kirjinsa na ɗan bugu, duk a zatonsa ƙullinsa ne zai warware. Sai kuma ya ji saɓanin tunaninsa.

"Ka je gobe war haka ka dawo ka karɓi saƙo hannun Mahadi."

Ya dubi Mahadi karo na barkatai, shima Mahadin fuskarnan babu fara'a, shi fa bi yarda da zancen Ɗan Mutuwa game da ɗiyarsa kawai dai yana ji a jikinsa akwai wata a ƙasa. Dama can ba son tarayyar Maigidannasu da Ɗan Mutuwa yake ba. Babu yanda zai yi ne kawai saboda akwai hannun mutumin dumu-dumu acikin ɓoyayyiyar harƙallar da suke yi. Ga wata baiwa da yake da shi na saurin siyar da dukkan kayan da suka shiga hannunsa ya kuma ninka riba har fiye da yanda aka tsammaci zai kawo. Sai dai har gobe ba ya kaunarsa, kuma yana fatan ranar da zai kawo ƙarshen alaƙarsa da Maigidan duk kuwa da sanin cewa abu ne da sai ya zage damtse.

Har ƊanMutuwa ya yi godiya ya fice bai bar watsamasa harara ba.

"Yanzu mene ne abin yi Mahadi? Kai kasan komai dangane da sharudɗan Na Kan Tudu, wa kake ganin ya dace na nemi aurenta wacce aka yarda da salihancinta da kamun kai?"

Ya gyara zama.

"Toh Ranka ya daɗe nifa na gama dukkan lissafina, tunda dai duk inda aka bi ba ya ɓillewa, me zai hana mu koma can gida Rano mu samo daga cikin dangi."

Ciyaman ya ɗan yi shiru kafin ya amsa.

"Nayi wannan tunanin, amma kuma ba ka tunanin asirinmu ya tonu sanadin auren ta gidan?"

"Ba zai tonu ba, ai da ace bamu da Boka Na Kan Tudu, shi ne zamu tsaya wala-wala. Ai ba banza ba, mallake yarinya za'a yi ya kasance sai yanda aka yi da ita. Ni dai a nawa ganin can ɗin ya fi rufin asiri kan ko'ina. Aka ƙulle bakin mutum me ya isa ya faɗi?"

Dariya sosai Ciyaman ya yi, sai a lokacin ya samu nutsuwa sosai. Ya kuma ji daɗin samun mutum irin Mahadi, koyaushe idan ya kasa samun mafita na matsala, sai ya zo masa da mai kyau. Har ya soma hango kansa a ɗakin taro na majalisu na Jaha ana damawa da shi. A nan suka yanke ranar da ta dace su kama hanyar garin.

***
Ɗan Mutuwa ya koma wurin aikinsa na kanikanci inda yake fakewa da guzuma yana harbin karsana. Zuciyarnan fari ƙal saboda ko ba komai ya kashe maganar da ta fi kowacce damunsa a ruhi. Ya iske yaransa na ta faman aiki, tun kan ya ƙarasa wurin ɗaya a cikinsu ya iso inda yake yana yi yana waigen sauran da ke faman harkar gabansu sannan ya juyo da muryar ƙasa -ƙasa ya ce. "Boss, tun ɗazu fa yaron Prince ke jiranka zai karɓi kaya."

Jin haka ai sai wani sabon annashuwa ya ƙara lulluɓe Ɗan Mutuwa. Ba shiri suka ƙarasa, yaransa na gaida shi yana amsawa cike da kulawa, can kuma ya ƙarasa ga wata baƙar mota Honda Accord wacce ta sha baƙaƙen tinted. Ya kalli ɗan tsamurmurin saurayin dake tsaye gefen yaran wurin.

"Afuwan Harɗo, na tsaida ka."

Wanda aka kira Harɗo ya maida waya aljihu yana dan murmushi ganin hankalin kowa a kansu.

"Ai fa, jira ya zama dole tunda Prince ba ya buƙatar kowa ya taɓa motarsa sai kai. Mu ƙarasa don Allah na soma gajiya dama."

Daga haka suka yi dariya suka yi can gefe inda motar take. Suna isa Ɗan Mutuwa ya shiga mazaunin direba shi kuwa Harɗo ya zagaya ta ɗayan gefen, idan ka hango su daga nesa sai ka rantse babu wani abu da ke wanzuwa face makaniki da ya mayar da hankali ga duba mota da kuma mallakin motar.

"Na fa jima anan, Prince sai kirana yake gaba ɗaya ya rasa control."

Ɗan Mutuwa bai ko kalle shi ba ya amsa.

"Na je ganin Maigidana ne. Yanzu dai wanne za ka karɓa?"

"Tayoyi za ka ba shi da turaren wuta."

Ya jinjina kai yana wani murmushi.

"Ya ci sa'a kuwa akwai su." Daga nan ya zura hannu cikin takalminsa sawu ciki, ya fiddo wata ƙaramar leda mai ɗauke da Codein (ƙwaya) ya miƙa masa ba tare da hankalin wani ya kai kansu ba. Ya zura hannu cikin rigarsa ta ƙasa inda yake adana tabar wiwi cikin wata ƙaramar jaka da yake ɗaure ta a ƙugu, idan ba jikinsa ka goga ba, ba za ka taɓa sanin da zamanta ba, ya fiddo na adadin da suka nema ya damƙawa saurayin.

Sosai Harɗo ya ji dadi. Nan take ya fiddo waya ya turamasa damin kuɗaɗe cikin asusunsa na banki da tuni ya jima da adana shi cikin wayarsa.
Sai bayan sun fito daga motar ne, Hardo ya fiddo takardun kuɗi har dubu uku ya ba shi a hannu yanda idanun kowa zai gane mishi.
Da haka suka yi sallama Ɗan Mutuwa ya koma gurin aikin nasu yana ta washe haƙora don ya sani yau kam akwai shagali.

***
*FITAR TSIRO*

*©️Rufaida Umar*

Paid book: 500
Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB
Phone number: 09034973645

Free page 4

Ta daki ƙyauren gidan sau uku da ƙarfi kafin ta shiga da sallama, mata biyu ne zaune a tsakar gidan jikin ƙofar ɗaki inda ɗaya ke yiwa

Please Login or Register in order to submit comment