Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuni ta mike ta riƙo ta. Cikin rawar murya take faɗin.

"Ke, me ya fito dake? Me ya tashe ki? Sakar masa, na ce ki sakar masa mu je ciki!"

Magana ta ke yi amma ina! Haulatu ko gezau, har lokacin jikinta babu inda baya rawa, hawayen kuwa zubowa suke yi kawai saman fuskarta. Kallon Uban take ido cikin ido, jira take ya ce tak! Ta maida masa mai zafi.

Umma kuwa hankalinta ya yi masifar tashi, ba za ta so abin da Haulatun ke yawan faɗi ya tabbata ba a yau. Shakka babu za ta yi kaico na gazawa da ba ɗiyarta ingantacciyar tarbiyya, kawai sai ta shiga jerawa Allahu kirari a ƙasan ranta. Ta zuba idanu tana kallonsu duka har lokacin ba ta saki Haulatu ba.


***
Nan na kawo ƙarshen na free, ga duk wacce ta shirya biya na a lahira, ta fitarmin da labarina.
***
"Sakar min." Ɗan mutuwa ya furta bayan ya tattaro jarumtarsa. Sai a sannan ta samu zarafin magana, tana yi tana jijjiga hannunta haɗi da nasa dake riƙe da belt ɗin.

"Idan na ƙi fa? Cigaba da dukan uwata za ka yi a kan idanuna? Daga inda ka tsaya nan za ka ɗora? Kai Iro! Bar ganin wai ina maka shiru ina kyaleka  ka na kai hannu jikin Mahaifiyata ka yi tsammanin ko tsoronka ne ya sa, ka yi kaɗan! Nace ka yi kaɗan na tsorace ka! Waye kai? Me ka taɓa yi mana a rayuwa? Shi babanta da ka raina har ka ke zagarmata shi, ka fi shi ne?! Ai gwara shi na tabbata bai kafa wannan mummunan tarihin da ka ke kafawa a yanzu ba kuma ko ba komai ta hanyar aure ya haifar maka ita. To ina maka rantsuwa! Daga yau, yanzu, duk sadda ka ƙara gigin kai hannu jikin Umma ka rubuta ka ajiye sai na yi shari'a da kai! Sai na fallasa dukkan sirrinka! Kai ni ba ka cika namiji ba idan a wannan daren ba ka tsinke igiyar aurenka da Umma ba! Har ka na mata barazana da za ka yi aure? Aurenka ɗin wofi! Ai ba ka daga cikin salihan mazan da aurensu zai girgiza zuƙatan mata! Da Umma ta cigaba da rayuwa da kai wallahi ni Haulatu na gwammace ta rayu da mahaukaci!"

"Haulatu! Rufemin baki! Mahaifinki kike jifa da waɗannan baƙaƙen kalaman?"

Ta runtse idanu ta ture hannun Umma daga kafaɗunta bayan ta saki belt ɗin, murya a ɗage yanda maƙwafta na kusa duk za su iya ji ta ce.

"Ni ki daina kiransa mahaifina! Mai irin halinsa bai haife ni ba! Wallahi gwara na kira mahaukaci Ubana da dai na ba Ɗan Mutuwa wannan matsayin! A kansa kina ji kina gani ana kiranmu ƴan bariki, ana yi min kallon karuwa mai ƙwacen miji! Ana yi maki kallon marar asali mai fakewa da siyar da abinci tana aikata masha'a! A dalilin wannan (ta nuna shi da yatsa), na rasa dukkan wani gata! Ki faɗamin nauyina ɗaya da ya taɓa ɗauka tun faɗowa ta duniya?! Umma ki faɗamin ko Ibrahim ya taɓa taimaka ma ki da kuɗin siyan magani idan cuta ta kwantar da ni? Ba zan taɓa kiran wanda ya yi yunƙurin ya kashe ni tun ina cikin ciki da sunan Uba kuma mahaifina ba! Gwara min kare a..."

Wani wawan mari Umma ta kai mata, maimakon hakan ya kashe bakinta sai ma ta riƙo hannayen Uwar ta ɗora saman wuyanta, da muryarta da ta dusashe tsabar kuka da ɗaga murya ta ce "Ki kashe ni! Don Allah Umma yau ki kashe ni. Na rantse na yafemaki har a gaban Mahaliccinmu. Amma don Allah ki kashe ni, na gaji da rayuwar nan Umma. Na gaji da kallon bariki da ake yimin. Wayyo Allahna!"

Sai kawai ta durƙushe sakamakon wani abu da ta ji kamar ya tokare ƙirjinta, numfashinta na kai kawo, tun tana jin muryar Umma na faman kiran sunanta da ƙarfi har gani da jin nata suka yi ɗif.

Umma ta tarairayo ta zuwa jikinta tana mai jijjiga ta gami da salati.

Shi kuwa Gogan kamar wanda aka daskarar a wurin, shi dai Ibrahim Ɗan Mutuwa ake zazzagawa rashin mutunci ya kasa kataɓus? Dama akwai wannan ranar a tafe? Babban tashin hankalinsa dare ne, kuma yana da tabbacin makwaftansu sun ji komai. Ai kuwa bai kai ga gama tunaninsa ba ya ji ana bubbuga ƙofar gidan da ƙarfi. Ya san kururuwar da Na'ima ke faman yi na neman agaji ya yi sanadiyyar hakan. Da sauri ya shige ɗakinsa ya rufe, takaici da baƙin ciki suka lulluɓe shi. Wai har akwai ɗiyar da za ta kalli tsabar idanunsa ta zage shi tas ya kasa ɗaukar mataki? Ƴar ma ta cikinsa? Ya furzar da iska ta hanci da baka kafin ya yi kwafa na tunanin matakin da zai ɗauka kan Haulatun.  Ya kasa kunne jin da ya yi Na'ima ta buɗe ƙofar gidan.

Makwaftansu maza su biyu sai kuwa matasan samari su ma duk ƴan unguwa sai ko mata da ba ta iya tantance ko su waye ba. Wannan ne karon farko a tsawon shekarun da ta yi a unguwar da ta ga fuskar wasu a gidanta masu suffar kamala.

"Na'ima, lafiya kuwa? Meke faruwa da Haulatun?"

Faɗin wata mata kakkaura tana ɗaga tocilar da ke hannunta da zummar hasko inda Haulatun ke kwance. Umma ta ji kuka ya ƙwace mata, cikin tashin hankali ta mata nuni da ɗiyarta.

"Don Allah da soyayyarku da Ma'aiki (s.a.w) ku taimakamin kada na rasa ƴa ta."

Ganin haka yasa suka danna kai ciki, nan da nan mata aka haɗa ƙarfi aka ɗaga Haulatu, wasu kuwa cikin tawagar da gulma ce ta kawo su, gidan suke haskawa su na ƙaremasa kallo. Hatta da belt ɗin Ɗan Mutuwa dake yashe a ƙas sai da suka gani. Nan da nan aka fice da Haulatu, Umma dakyar ta samu nutsuwar ɗauko hijabin wanda garin sauri ma na Haulatun ne ta zura sai takalmi ƙafa daban-daban ta mara musu baya.

Ƙa'idar lokaci na masu ɗan sahun tuni ya wuce hakan ta sanya cikin gaggawa wani magidanci da gidansa ke kallon na su Haulatun ya fiddo motarsa aka hau. Daga Umman sai mata biyu sai ko mai motar da wani a gefensa.

Nan fa wadanda suka yi saura a wurin suka hau maida zance, wasu na fadin ko dai cikin shege ta yi, wasu kuwa kira suke watakila ma shaye-shayenta ta yi har ta sha ya fi ƙarfin garkuwar jikinta. Maƙwaftan da suka fi kusa da su ne suka hau ba da labarin abubuwan da suka tsinci Haulatun tana faɗi. Wasu da yawa sun ji tausayi ya tsirga musu, hakan har ya zama sanadiyyar wanke Haulatu da Umman a zuƙatansu, yayinda ƙalilan ke ganin ai dama tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka kuma kowa ya siya rariya ya san za ta zubda ruwa, da ace mahaifiyarta ba ta biyewa kwaɗayi da burika ba tun farko har ya kai ta ga auren mutum irin Ibrahim Ɗan Mutuwa ba, da yanzun wani labarin ake ba wannan ba. Haka dai suka yi ta tufka da warwara kafin daga bisani kowa ya watse.

***
Alhamdulillah, cikin ikon Allah bayan likitoci sun yi iyaka ƙoƙarinsu aka samu Haulatu ta farfaɗo. Bisa shawarar likitan, ya ce a daure a daina bari tana shiga damuwa mai ƙarfi irin wannan da ya janyo ta yi doguwar suma, irin wannan yanayin zai iya jawomata hawan jini da kuma ciwon ƙirji. Ƙarshe ya yi mata allurar samun bacci don ko da ta farka maganar ɗaya ce ta ke maimaita "Wayyo Umma, duniyar ta ishe ni. Ku bar ni na mutu."

A dole don samun nutsuwarta ya yi mata, ya kuma roƙi duk a fita a ƙyale ta da mutum ɗaya mai jinyar.

Duka aka fito har Umman da ta yo musu rakiya. Tana ta zubamusu godiya ga hawayenta ya ƙi tsayawa, duk su ne suka ɗauki nauyin asibitin, daga mai siyan magani sai mai biyan kuɗin gado.

"Haba kar ki damu, kawai ayi fatan samun sauƙinta. A kuma kiyaye abin da likita ya ce. Allah ya sawaƙe ya ba ta lafiya."

Cewar motar da ake kira Alhaji Shu'aibu Mijinyawa. Ɗayan kuwa Malam Bukar ake kiransa sai mai ɗan jikin Hasiya, ita ce matarsa da kuma bazawarar ƙanwarsa Murjanatu. Haka ta yi ta zuba musu godiya daga ƙarshe suka ce ta koma wurin Haulatu kar a bar ta ita daya. Da wannan ta juya su kuma suka tafi.

A motar ma sai jimami da tausayi suke yi, nan mazan suka yi ta tattaunawa ta yanda aka yiwa gidan gaba ɗaya mummunan shaida. Sun kuma fahimci sosai Uwa da yarinyar na buƙatar taimako, ga dukkan alamu ba su jin dadin zama da uban. Haka dai har suka isa gida lokacin ma asubahi ta gabato.

***
Umma har ta yi sallar asuba ba ta iya ta rintsa ba, idanunta a bushe sai ciwon kai, ciwon jiki kuwa dama ta saba da shi. Hannunta duk ya yi ja saboda duka. Ga shatin belt kwance. Yanzu tunaninta bai wuce makomar rayuwar ɗiyarta ba. Shakka babu ta tsorata da Haulatun da ta gani a jiya da daddare, tana kuma da tabbacin tarbiyyar yarinyar na dab da samun matsala muddin za ta cigaba da ganin waɗannan munanan ɗabi'u na mahaifinta. Ta san zai wahala ya fasa dukkan abin da ya yi niyya, wannan na daga dalilin da yasa tun a baya mutane ke kiransa da Ɗan Mutuwa. Shi fa ko za'a mutu baruwansa, inda ya sa gaba sai ya ga ƙarshensu abun kafin ya haƙura. Anya lokaci bai yi ba da za ta fice a rayuwarsa su gina tasu rayuwar a wuri na daban?

'Ba kya tsoron a cewa ɗiyarki ƴar mace? Kuma ina za ku je?'

Wadannan tambayoyin a koyaushe idan za ta yi tunanin rabuwa da Ibrahim, su na cikin dalilin da dole take haƙura ta fasa. Ta zurfafa cikin tunani a gefe guda kuma bakinta na motsi tana tasbihi sai jin motsin Haulatu ta yi, cikin sauri ta miƙe ta nufi gadon. Haulatun ta dubi ɗakin da ta ke kafin ta maida duba ga Umma wacce ta riƙe mata hannu. Ɗan murmushin da bai kai zuci ba ta sakarmata, itama Umman ta maida mata martani.

"Alhamdulillah, kin farka? Sannu, bari na kira likita."

Da idanu kawai take bin Umma har ta fice daga ɗakin, can suka dawo tare har da wata Nos. Ya tambaye ta ko akwai inda ke mata ciwo, ta girgiza kai, ya gama gwaje-gwajensa kafin ya kalli Umma.

"Masha Allah, komai na ta lafiya lau yake. Anjima zan sa a sallame ku. Yanzu tana buƙatar ta ɗan ƙara hutawa amma a samu ta sa wani abu a cikinta sai ta sha magani."

Umma ta amsa da toh, ita duk sai yanzu ma ta tuna da wai ana cin abinci, yanzu haka za ta bar ta ita ɗaya ta koma gida ko ya ya?

Cikin taimako na Allah, ba ta kai ga gama tantance abin yi ba, suka ji ana buga ƙofar ɗakin, bayan Likitan ya bada iznin a shigo, sai ga matar Alhaji Shu'aibu, Hajiya Mabruka tare da Mama Hasiya (kamar yanda yan unguwa ke kiranta), sai ko wata budurwa da ba ta fi sa'ar Haulatun ba riƙe da kwandon abinci. A bayansu kuwa wani ɗan matashi ne wanda zai girme wa Haulatun da kaɗan hannunsa riƙe da filas na shayi.

Suka gaisa da Likita sannan ya fice tare da Nos. Cike da girmamawa Umma ta gaishe su fuskarnan a sake. Zuciyarta kuwa tamkar an mata albishir da gidan aljanna, wai yau ita ce tare da makwaftanta haka a lokacin da ta ke cikin tsananin buƙatar wani a kusa? Nan aka zauna, ita dai Haulatu kallonsu kawai take. Ta kai duba ga budurwar mai suna Bahijja wacce ba baƙuwa ce a wurinta ba don islamiyyarsu guda kuma ajinsu ma haka, sai dai kawai babu mai shiga shirginta, asalima ƴan cikin su Bahijja sun fi kowa tsanarta kai ka ce wata sabuwar tuba ce a cikinsu. A bakinsu ta soma jin ana mata ƙazafin ƙwacen saurayi ko miji. Ta kauda kai daga gareta zuciyarta na zafi, lumshe idanu ta yi yayinda take sauraron Umma na yi musu bayanin da likita ya yi. Babu wanda ta kula cikinsu sai amsa sannun da ake yi mata ta hanyar gyaɗa kai. Mama Hasiya ce ta taimaka mata ta miƙe bayan fitar saurayin siyo brush da toothpaste, ta shiga bandaki ta yi tsarki da alwala. Can ya dawo ya miƙawa Bahijja sannan ya fita, ita kuwa ta kwankwasa ƙofar bandakin, Haulatu ta leƙo ta karɓa fuskarnan babu ɗigon walwala asalima kallon fuskar Bahijjar ba ta ƙaunar yi. Ai har da ita cikin masu yi mata mugun ƙazafi. Bahijja kuwa duk jikinta ya yi sanyi musamman a hanya da Mama Hasiya ta ba su labarin duk abin da ya afku a daren har sadda suka ji kururuwar Umma. Wani irin tausayin Haulatun take ji yana tsirga mata.

Sai da ta yi sallah, aka zuba mata ruwan shayi ta soma sha kafin su yi musu sallama su tafi domin duk yanda Mama Hasiya ta so Umma ta koma gida ta kimtsa ta dawo ta nuna ita sam ba za ta iya motsawa ba. Sun sha godiya sosai, Hajiya Mabruka har kudi ta ba su saƙo daga maigidanta.

Wuraren biyar na yammacin ranar aka ba su sallama, ɗan sahu suka shiga zuwa gida. A hanya Haulatu sai tunani, Umma abin har ya soma ba ta tsoro don tun da ta farfaɗo ta ƙi yin wata maganar arziki ga kowa. Daga um sai um um sai kuwa murmushi mai kama da yaƙe sai gyaɗa kai.

***
Ina labarin Ɗan Mutuwa?
Tun bayan fitarsu ya ke ta muzurai shi ɗaya a ɗaki. Ya san dai ko mutuwa yarinyar tayi, Na'ima ba za ta ɗagamasa ƙafa ba. Koda dai ya kula itama ta samu bakin yi mishi musu yanzu idan ya yi magana. Fitowa ya yi a ɗakin bayan ya kwashi abin da zai buƙata don ya rantse idan ya bar gidan ba zai dawo ba sai bayan kwana biyu. Ƙunshin nama da gurasar ya shigo da shi a daren ko kallonsa bai ba, sai da ya ji unguwar ta yi shiru shaidar kowa ya shige gida ya fito ya miƙi hanya. Bai zarce ko'ina ba sai gida Hajiya Adama Loma.
 
Gida ne da ba ya rabo da mutane safe da dare, babu ma kamar da daddaren. Yana ɗaya daga cikin manyan gidaje a unguwar, babu ruwan wani da wani musamman da ya kasance wurin yawanci baƙi ne, wasu ƴan Lebanon ne, sai ko ƴan China da Hausawanmu waɗanda boko ya ratsa.  Kowa harkar gabansa yake yi babu takura.
Itama Hajiya Adama ta mallaki gidan ne da maƙudan kuɗaɗen da ta ci gadonsu daga tsohon mijinta da ya kasancewa Balarabe ɗan Libya, bayan rasuwarsa ne ta ci gadon gidan, ta kuma zama Hajiyar kanta don jifa-jifa gidan ba ya rabo da gyare-gyare wadanda yawanci duka manyan Alhazawan da take cuɗanya da su ke yi mata kyautuka na bajinta. Ga uwa uba tana buga kasuwancinta na siyar da duk wani abin ado na jiki da ma na amfani na mata. Katafaren shago ta mallaka a wuraren Unguwar da ta ke wato Nassarawa GRA. Kadarorin da ta tara shi ya zama rufin asiri na asalin sana'ar da ta ke yi a ɓoye.
  Ibrahim Ɗanmutuwa yana cikin mutanen da ba'a yi musu shamaki da shiga ko'ina a gidan na Hajiyar, sun yiwa junansu farin sani tun ma duniya na kwance. Kusan shekarunsu ɗaya a bariki, asalima shi ya kasance kamar wani abokin shawararta tun a baya. Uwa uba da shawararsa aka kashe mijinta ta sigar da ba kowa zai fahimta ba. Sosai ta ba shi nasa kason a baya sai dai kuma kuɗaɗe a hannun Ɗanmutuwa sam ba su zama. Haka ya dinga kashewa ƙadangarun bariki ba tare da ya amfanawa kansa ko matarsa da komai ba.
   Haka ya nausa ciki har babban falon Hajiya Adama bayan Maigadi ya buɗe masa ƙofa. Ƴanmata ne da ba su fi shekaru sha biyar zuwa sama ashirin ba, su huɗu kwance ba su san ma inda kansu yake ba, kallon da ya yiwa kwalaben da ke wurin ya fahimci mankas suka yi. Kai tsaye ɗakin da yake yawan sauka idan ya zo nan kawai ya zarce sai dai ya ji a rufe gam! Koda ya ɗan kara kunne ya ji ana jan munshari ya ja guntun tsaki. Dole falon ya koma ya ajiye jakarsa gami da fiddo sigari ya kunna ya soma zuƙa, kansa gaba ɗaya tururi yake, shi fa har a sannan mamakin wannan ɗanyen aikin da ƴar cikinsa ta yi mishi yake. Wato don uwarta don ta samu ya bar ta tana shaƙar iskar duniya bai hallakata ba tun tana jaririya shi ne har ta ke da ƙarfin cin zarafinsa. Ya yi ƙwafa, haka ya tashi da kara uku na sigari kafin ya kora da ruwan codein ya sheme a saman three-seater na gidan babu ko damuwa akan sallah. (Wa'iyazubillah).

***
Tana zaune a bakin ƙofar ɗakinsu ta yi shiru, daga ita sai vest da zani kan babu ko dankwali, gashinta baƙiƙirin marar tsawo sai cika tufke da ribbon, gefe guda ta ƙurawa idanu tana sauraron shirin da ake yi a gidan rediyo dake magana akan tarbiyya. Wanda Malamin ke nuni da muhimmancin tarbiyya da kuma haƙƙin yara akan iyayensu. Shirin ya sa ta shiga fidda ruwan hawaye, ƙarshe kuma ta ɓige da kuka sosai. Cikin wannan yanayin ta ji ana ɗan bugun ƙofar gidan. Ta sani Umma ba ta jima da fita zuwa sana'arta ba hakan ya ɗan ba ta mamaki. Ta kashe rediyon sannan ta goge fuskarta. Miƙewa ta yi har ta kama hanyar ƙofar sai kuma ta dawo da baya ta ja hijabin Umma dake saman igiya ta zura.

"Ana zuwa." Ta furta cikin shaƙaƙƙiyar murya. Wacce ta gani kwarai ta yi mamaki, Bahijja. Za ta iya cewa tun soma wayonta ita kam ba ta taɓa ganin ƙeyar mutum ɗaya a  ƴan gidansu ya shigo ba. Tare suke da ƙanwarta Nasiba, ta yi fuskokinsu farin sani tunda islamiyya guda suke.
  "Ko mu juya?" Faɗin Bahijja cikin zolaya tana ɗan murmushi. Itama sai ta tsinci kanta da maida mata martanin murmushin kafin ta shige ciki ta yi mata iznin ta shigo. Bahijja na gaba riƙe da kwando sai Nasiba biye da ita ɗauke da wata baƙar leda mai ɗan girma, tsayawa ta yi tana bin tsakar gidan da kallo. Ba wani babba ba ne, ɗakuna biyu ne sai kuwa wani gefe da ta ke zaton nan ne kicin sai ƙofar banɗaki daga ɗan lungu. Haka ta yi ta nazarinta har Haulatu ta shimfiɗa musu tabarma.

"Wai dama tabarma ki ka shiga ɗaukowa? Wallahi sauri ma muke zamu je islamiyya ne, dama Mama ce ta aiko mu, tana maki sannu. Ga wannan kuma ta ce a kawo."

"Lallai, wato kin fi ƙarfin ki zauna a tabarmar gidanmu ko? Ai shikenan. Ki ce mata da sauki, an gode."

Riƙe baki Bahijja ta yi.

"Kai Haulatu, ni ba haka nake nufi ba don Allah kar ki fassara ni. Ai ke kin sani na shiga ajin ƴan hadda. Kiyi hakuri, ai yanzu muka soma aminci, na tabbata sai kin gaji da gani na a gidanku."

Haulatu ta ɗan taɓe baki.

"Ni dai mai ƙwacen samari?"

Maganar ba ta yiwa Bahijja dadi ba, cikin sanyi ta amsa.

"Kiyi hakuri, ki yafe min duk abin da na furta mai muni gareki a baya. Rashin sani ne da kuma jita-jitar mutane. Amma ina tabbatar maki yanzu na fahimceki."

Murmushi kawai Haulatun ta yi, ai ita ta sani babu wani mai fahimtar ta bayan uwar da ta haife ta. Kawai dai ta bi ta da to, haka suka rabu ta taka musu har bakin ƙofa tana ƙara jaddada saƙon godiya ga Mamarsu.

Abinci ne lafiyayye, shinkafa dafaduka a wata cooler ɗin kuwa farfesun kaza ne. Sai leda mai ɗauke da sabulai na wanka da kuma wanki sai kuwa omo. Kai har da auduga na mata leda biyar da mayuka har kala biyu na shafawa. Shiru ta yi tana kallon kayan, karon farko da irin wannan abin arziƙin ya haɗa su da makwaftansu. Haka ta mayar da komai cikin ledar, ta ajiye su a gefe. Ba ta tare da yunwa don haka  ko sha'awar abincin ba ta yi ba. Ta gaji da zaman tunani ta ja guntun tsaki ta miƙe, gaba ɗaya zaman gidan ba dadi yake yi mata ba ta ji inama ta bi Umma zuwa kasuwa, ƙarshe kawai sai ta ƙara zura hijabin da ta cire ta fito ƙofar gidan ta ɗan tsaya. Yana ɗaya daga cikin abin da Umman ba ta sonta da shi sai dai tana ji hakan kaɗai ta fi buƙata a yanayin da zuciyarta ke ciki. Hankalinta ya kai ga su Maada waɗanda suka ɗan kalli inda take. Ta kauda kai gami da ƙara tamke fuska. Ta rantse wataran sai ta sa ƴan sanda sun kawomusu cafka muddin ba za su daina zama a ƙofar gidansu ba. Ta tsinkayi muryar wani cikinsu mai suna Kwarkwar ya buga wani ihu na ƙwararrun ƴan daba kafin ya ce.

"Kai! Ni fa barewar can tana kashe ni billahillazi! Oga Maada! Ya kamata idan Ciyaman ba zai iya farautarta ba mu, ya bari mu shiga da ƙwarinmu."

Maada ya ja tsaki yana fesar da hayaƙin sigarin da ya zuƙa.

"Kai don tsohuwarka ina tambayarka inda Ɗan Aljan ya shiga kana yimin maganar banza da wofi. Ai inda amana ruwa ba zai dafa kifi ba, duk runtsi kar wanda ya ƙara kai idanunsa ga irin gidan Boss."

Kwarkwar da sauran mutane ukun da ke zaune tare da shi, suka harɗe hannuwansu suna kirarin kowa ya bi. Can kuma Kwarkwar ya ce.

"Nifa Oga ban dan inda Ɗan Aljan ya yi ba, na fi tunanin ya haɗu da Kashi (ƴan sanda) sun sa mishi lalle (sun kama shi).  Kasan fa shi Boss ya aika gidan Cuna ya kai tayoyi! To ka san halinsa, ya fiye Nakura (tsoro), ƙila ya yi saranda." Ya ƙarashe yana mai ƙamewa kamar wanda ke gaban soja.

"Aikuwa da matsala. Amma ina zuwa bari na sallami waccan ƙaguwar." Faɗin Maada, Haulatu ta saci kallonsa ta gefen idanu, can kuma ta kai duba ga inda ya nufa, wata budurwa ta gani daga can kan kwana ta rufe fuskarta da niƙab. Waige-waige ya yi kafin ta ga ya sa hannu cikin aljihu ya fiddo wani abu da ba ta iya tantance ko mene ne ba, ita kuwa ta karɓa da sauri ta cusa a jaka ta fiddo kudi ta miƙamasa daga haka ta bar layin da sauri. Shi kuwa ya dawo ya zauna suka bi shi da sowa. Iya Haulatu mamaki ma abin ya ba ta, ba su ko tsoron ta tona asirinsu?
 
  'Tsoron me za su ji tunda dai halinsu guda da mijin Ummanki?' Wani sashi na zuciyarta ya ba ta amsa.
  Hirarsu ta ƙara ɗaukar hankalinta, magana suke yi akan budurwar. Maada ke labartamusu cewa ai yau taro ne da su na birthday hakan ya sa zasu gwangwaje.

Ganin tun tana fahimtar kan hirar har ta bari ga wani jiri da ta ke ji sakamakon jimawar da ta yi a tsaye yasa dole ta juya ta shige gida gami da zura sakata.

Yinin ranar sam bai yiwa Haulatu dadi ba, har Umma ta dawo ba ta da wani walwala. Sosai Umma ta yaba da karamcin Maman Bahijja. Sai da aka yi Magriba suka ci suka ƙoshi, tana da lura da Haulatun. Anan take sanar da ita kiran da Hindatu ta dinga yi a wayar Umman tana nemanta. Yamutsa fuska kawai Haulatu ta yi, ita fa mamakin Hindatu take har lokacin, ta kuma ci alwashin sai ta nunamata rashin jin dadinta a fili.

Umma na so ta tambayi ɗiyar ko Mahaifinta ya shigo gidan, sai dai ba ta kaunar ta tayarmata da abin da ya wuce. Yau kwana biyu da faruwar al'amarin kuma tun sannan ba su ƙara ganinsa ba a gidan. Ga diyar, hakan ya fi nono fari har addu'a ta ke yi a ranta akan Allah ya sa mota ce ta kaɗa shi ya mutu. Ga Uwar kuwa, duk ta damu. Zuciyarta na mata ba dadi, ko ba komai uban ƴarta ne.
  A ranar ma har suka kwanta bacci babu labarinsa, tun Haulatu na jin Umma na juyi da sintirin fita

Please Login or Register in order to submit comment