Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗayar kitso sai kuwa yaro da ke shimfiɗe saman tabarmar, suka amsa mata fuska a sake.

"Wai ke kam Haulatu nidai ban san dalilinki na son buga gidan nan kafin ki shigo ba." Faɗin matar da ke yin kitson. Tana dariya ta ɗan dubi kewayen su Hindatun ganin a buɗe ya ba ta tabbacin tana nan kafin ta ƙarasa ga matar tana mai ba ta amsa.

"Ni haka na fi so ai Baraka, da wannan kaɗai ku ke gane ni ce na zo. Nasan dai duk duniya bayan ni babu mai muku wannan sallamar. Amaryar gidan taku har ta soma fita ne?" Ta ƙarashe tana duban ƙofar ɗakin da ke gefen na Baraka.

"Inye, ka ga masu gida, wato har rabin jikin taki ta labarta maki."

Daidai nan Hindatu ta ɗan leko daga jikin ƙyauren da ya yi musu katanga da sauran mutan gidan daga ita sai ɗaura ƙirji, kallo ɗaya za ka fahimci daga wanka ta fito. Caraf ta karɓe zancen.

"Me za'a fasa to? Mutuwar ko kuwa hisabin? Ai ni kin tunamin ma ban labarta mata cewar tare da ni aka ci kazar Amarcin ba."

Suka yi dariya. Ita dai wacce ake yiwa kitso kallonsu kawai take, tana dai jin labarin Haulatun a bakin su Baraka kasancewarta makwafciyarsu amma ba su taɓa haɗuwa ba sai a yau. Yarinyar da ba ta wuce sa'ar ƙanwarta  ba, kyakkyawa ta bugawa a jarida kuwa sai dai tana tuna ance iyayenta ƴan bariki ne sai ta ji ta ba ta tausayi ta shiga yi mata addu'ar neman tsari daga shiga halaka.

Har Haulatun suka miƙe da zummar tafiya ɓangaren su Hindatu bayan sun gama caftarsu da Baraka, ba ta iya ta kauda kai daga kallonta ba har sai da ƙilu ta ja bau. Haulatu na ganin yanda ta ƙure ta da idanu ta yi dariyar mamaki ta ce.

"Ke kam baiwar Allah wannan kallon fa? Ko dai na maki kama da budurwar mijinki ne?"

Ta ƙarashe har lokacin fuskarta ba ta sauya daga yanayin baya ba, itama Hindatu na taya ta darawa ta ce. "Ke dallah, Lubabatu ce fa, na taɓa baki labarinta na ce ta haifi ƴan biyu har ma ɗaya ya koma? Wacce na ce maki ƙaninta ya na sona?" Hindatu ta ƙarasa maganar da murya mai kama da raɗa.

Baraka ta saba da wannan gwaɓa magana irin ta Haulatu wanda har ka ɗauki zafi ita ko a kwalar rigarta don ba ta gane ta yi kuskure ba, Lubabatu kuwa sosai kalaman sun daki zuciyarta, ranta ya ɓaci. Kafin ta kai ga tankawa sun ɓace daga idanunta sun shige ciki.

"Haulatu kenan, sarkin iya magana." Cewar Baraka.

"Wannan yarinyar na yarda ba ta da mafaɗi, wai Baraka ba ki ji dakyau baƙar maganar da ta yaɓamin ba?"

Ɗan murmushi Baraka ta yi tana mai sakar mata gashi ganin ta ƙi ba ta damar yin tufka mai kyau.

"Kaɗan kenan in dai Haulatu ce, kwanaki can da ta zo daga na ce mata Haulatu wannan kwalliyar fa sai ina? Buɗar bakinta cemin ta yi ai gidanmu za ta je neman sadaka tunda Iro bai ba ta na karin kumallo ba ai gwara ta je wurin Idi. Hum, ke tun daga ranar na ɗauke mata wuta, kuma abin da zai ba ki mamaki fa wallahi wai ita wasa ne ta yimin, har da za ta tafi sai da ta shigo wurina mu yi sallama. Ni dai daga baya ta yi zuwa kusan biyu amma babu alamar ta san ina wani abu wai fushi, sai da ta tambaye ni don kanta ko ta yimin laifi ne, na nunamata kurenta, ke yarinyarnan har da su ƙwalla wai ita wallahi wasa ne ta yimin. Na nunamata iyaye ba abin wasa ba ne ta daina. Ta ce ai wai ganin Idin sunan kakana ne. Nace ko kakan kakana ne kuwa. Toh ban ce ba ta ƙara gwaɓamin ba amma dai na iyayen gaskiya ba ta kuma maimaitamin ba. Shi dai Baban nata Iro da ba ta ganinsa da gashi ko kaɗan kamar yanda na taɓa faɗamaki, shi dai ba ta fasa ba."

Lubabatu ta girgiza kai gami da sakin huci.

"Amma dai kam ta kiyaye harshenta idan kuwa ba haka ba nan gaba zai haifar mata da tarin nadama nan gaba. Ai tunda ta fito daga irin wancan gidan, fiye da hakan ma za ta iya aikatawa. Kai, Allah dai ya kyauta, ya shirye ta kuma. Ga dai kyau iyakar kyau masha Allah, amma ina gujemata faɗawa halaka nan gaba. Don idan har za ta cigaba da zama da wannan yarinya da uwarta, toh abin fa sai du'ai. Mutanen da idanunsa kw buɗe da son naira."

Baraka cikin raɗa-rada ta ce. "Kinga matar nan ki rufamin asiri, dama ya lafiyar giwa balle an jefe shi da kashi? Allah dai ya mallaka wa mazajenmu gidajen kansu mu yar da ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda kamar ya yiwa su Habiba gyaɗar dogo suka tashi."

Lubabatu ta amsa da amin suka yi dariya. Nan kuma aka dasa gulmar Hindatu da Mahaifiyarta da irin zaman haƙurin da ake yi a gidan dalilinsu.

***
Hindatu kuwa, su na shiga ɗaki suka kwashe da dariya.
   "Wallahi ke kam Haulatu ba ki da kirki, ni na tabbata Lubabatu ta ji zafin maganarki. Ke ko kadan ba kya saita bakinki ko?"

"Au, daga wasa sai ta ji haushi? Toh ni kuwa ina nasan ma mijin nata da har abin zai mata ciwo?"

Murmushi kawai Hindatu ta yi bayan ta shiga mulka a jikinta. Haulatu ta fisge robar.

"Ni dallah ki faɗamin, me na fadi mai zafi da kike tunanin ban kyauta ba? Bari na je na ji daga bakinta."

Da sauri Hindatu ta dakatar da ita ta hanyar riƙo gyalenta.

"Ke wasa nake maki fa, ba komai. Ai ke da zuciya daya kika yi mata wasan. Yau fa baƙo zan yi."

Haulatu ta koma ta zauna.

"Waye zai zo? Tj ko Nazifi?"

Tana wani murmushi da fari da idanu ta ce.

"Ba ɗaya, wani sabon kamu na yi. Sati biyu kenan da Momi ta ba shi lambar wayata sadda ta je siyayya a shagonsa. Shi ne fa zai shigo yau."

Cikin rashin fahimtar zancen ta ce "Ban gane ma Malama, yimin dalla-dalla. Shi ne duk jimawarnan ba ki labartamin ba komai ba?"

Dariya Hindatu ta yi.

"Toh ai jira nake na kama dahir. Ke Momy ce ta je kasuwar kwari sarin kaya shi ne fa hira ta yi hira har ake maganar mata yanzu ba su iya kula da gidajensu ba. Mutumin ya nuna ra'ayin shi fa yanzu aure ma yake son ƙarawa, aikuwa Momi ta ce masa tana da ɗiya sai dai ita karatu ta ke son na yi, ya nuna shi ba shi da matsala da karatuna, idan har nayi masa zai bar ni naga ko ƙarshen biro da takarda ne. Toh nidai wallahi daga waya naji ya burge ni don ba laifi ya iya tsara kalamai ga lallaɓa mace da tarairaya kamar kwai. Nikam muna zana SSCE zan shiga daga ciki."

Baki galala Haulatu ke kallonta har sai da ta kai aya kafin ta magantu.

"Kina cikin hayyacinki kuwa? Mutumin da ko ganinsa ido da ido ba ki yi ba? Ba ki san halayyarsa ba amma daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi? Wai ke ce dai me ikrarin sai mun shiga jami'a an dama da mu kuma mun ci karenmu ba babbaka?"

Farr da idanu ta ƙara yi tana duban Haulatu sai kuma ta yi dariya.

"Ke Haulatu, cemin ya yi fa gidana daban, kuma duk abin da nake so zan yi? Ke har mota ya yimin alƙawari. Kuma kike maganar bamu ga juna ba wa ya fadamaki, ya turomin hotunansa ta whatsapp nima kuma Momi ta bani kuɗi na je an min kwalliya na yi hotuna tun wancan satin fa na turamasa. Ba kin ga hotunan da nayi ba kwanaki a wayata har na ce maki biki aka yi a makwaftanmu? Toh ƙarya nake yi, adalilinsa na ɗauka."

Haulatu jikinta ya ɗan yi sanyi, ba ta yi zaton a cikin amintarsu akwai wani abu da suke ɓoyonsa ga juna ba.

"Yanzu har akwai wani abu daman da za ki iya ɓoyemin? To idan kin faɗamin mene nawa ciki?"

Hindatu ta ɗan yi shiru, Momi ce ta zuga ta akan kul ta sake ta labartawa Haulatun. Tunda dama can ba son amintarsu take yi ba, ganinta Haulatu ta fi ta kyau ta ko'ina, ga fatarta luwai-luwai kamar mai cin kaza. Uwa uba ba ta shafe-shafe farinta daga Allah ne. Momi ta ce tsaf za ta iya yi mata ƙwacen saurayi, uwa uba kuma ta iya barikanci irin na gidan da ta fito. Ta kuma tuna akwai saurayinta da suka taɓa rabuwa akan Haulatun, tun ganin da ya yiwa Haulatun ya sauyamata, a karshe ya fito mata a mutum ya nuna Haulatu yake so. Aikuwa suka hadu su biyun suka ci mutuncinsa da ya jawo sanadiyyar daƙile alaƙar baki ɗaya. Ita ba ta san ma ƙaiƙayin bakin da ya kai ta yin zancen a yanzu ba.

"Kiyi hakuri tawan, hirar ce ba ta zo kansa ba. Kin san idan mun haɗu zantukan namu ba sa ƙarewa."

Murmushi mai ciwo Haulatun ta yi, tana ji a ranta akwai wani abun bayan wannan. To ko dai itama Hindatun tana mata kallon ƴar barikin ne irin wanda saura sa'anninta na makaranta suke kallonta? An sha kawo mata zancen wai ita ɗin usulin iyayenta bariki, don haka za ta iya ƙwacewa mutum saurayi ko miji wannan na ɗaya daga cikin dalilan da yasa kowa na unguwar ƙara nisanta kansa da ita. Ba ta mance ba akwai wata Amarya da aka taɓa kawowa unguwarsu, har sun fara sabawa kawai sai gaba daya ta sauyamata, a ƙarshe ma ta fito mata a mutum ta nuna ita fa mijinta ya hana ta sjiga sabgarta. Kafin ta kai ga ficewa a gidan sai ga mijin ya dawo, daga yanda kuma ya tarbe ta cikin sakin fuska ta fahimci ƙarya ne. Sai daga baya ta ke jin wai Amaryar ce aka gargaɗe ta da shiga shirginta.
Haulatu na kai wa nan a tunaninta ta ji kwalla sun ciko mata, ta yi gaggawar kauda su. Sai kuma ta miƙe tana gyara zaman mayafi sannan ta ɗauki ƴar jakarta.

"Wai don Allah mene haka? Kina nufin ki ce ba za ki tsaya ku gaisa ba? Daga zuwanki har za ki tafi? Ke ko dai haushi kika ji?"

Ƴar dariyar da ba ta kai zuci ba ta saki kafin tana mai janye yatsun hannunta cikin na Hindatun da ke ƙoƙarin dakatar da ita.

"Haushi a na me? Ko ɗaya, kawai dai dama Umma ta ce kar na sake ta riga ni dawowa gida. Kuma kinga yamma ta yi, gwara na lallaɓa."

Sakin ajiyar zuciya Hindatun ta yi, ita kam koda ba haka bane, za ta so tafiyar Haulatun gudun kar Momi ta dawo daga amsomata rubutun da ta tafi su yi kiciɓus, don a yau Momin ba za ta so ganinta ba musamman tunda babban baƙo zasu yi.

"Shikenan, amma don Allah kiyi hakuri. Kinsan ba ma ɓoyewa juna komai ko? Na rantse to mancewa nayi."

Ƙaramin dariya ta ƙara saki karo na biyu. Ta ya ya mutum zai mance da hirar wanda ya fi so da kauna? Kawai dai ta karɓi zancen yanda ya ta faɗi don a zauna lafiya.

"Dallah can sai ka ce ni na haifeki kina wani faman damun kanki da rantsuwa. Kar fa ki damu na fahimceki. Bari na wuce nidai, sai Monday idan mun haɗu a makaranta. Ki gaida Momi."

"Aa, bari na taka maki." Fadin Hindatun da sauri tana mai janyo hijabinta ta zura. Ita kuwa Haulatu tuni ta fito.

A tsakar gidan su Baraka kuwa, tuni Lubabatu ta miƙe tsaye tana gyara goyon ɗanta da ta yi, sun kammala kitson. Ta yi musu sallama ba tare da ta biyewa Baraka da ke tambayar ko lafiya daga zuwa sai tafiya ba ta fice, Hindatu na biye da ita. A daidai ƙofar ta jawo mayafinta. Suka dubi juna, Haulatu cikin kokarin danne ɓacin ran ta ɗan harareta. "Wai ke Malama lafiya kike ta ja min gyale? Bana ce maki magana ta wuce ba?"

Cikin karyar da murya Hindatu ta ce "Kin tabbata har a ranki Haulatu? Na fa san ba ki da riƙo."

"To kin san ba ni da riƙon mene ne abin damuwa? Ni don Allah koma ciki ki shirya kar ki je ya yi maki zuwan bazata ya ganki hakanan ba kwalliya sai ɗaura ƙirji da hijabi. Big Mama, inji ƴan aji."

Suka yi dariya.

"Ƴan duniya ba. Shikenan to ki gaida Umman."

Ta amsa da toh sannan ta yi gaba, Hindatu ta ɗan bi ta da kallo. Taɓ, wato da gaskiyar Mominta da ta ce Haulatu tsaf za ta sace zuƙatan maza fa dama, ga ta dai bilhaƙƙi ta ke tafiyarta amma sai mutum ya rantse da biyu take girgiza jikinta. Ta ji wani abu ya tsaya mata a rai mai kama da haushi da burin inama ita ce mai kyawun halittar. Sai kuma ta yi saurin kauda zancen gudun kar shaiɗan ya jefamata wani abun daban mai akma da hassada da kishi. Ta ji gwara ma da Haulatun ta bar gidan da wuri.
*FITAR TSIRO*

*©️Rufaida Umar*

Paid book: 500
Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB
Phone number: 09034973645

LAST FREE PAGE.

Da daddare misalin ƙarfe tara tana kwance saman ƴar katifarta ta yi shiru gami da zubawa rufin kwano idanu. Dagaske Hindatu itama tsoronta take ji? Ashe ita ce kawai ke zaune da ita da zuciya guda? Kodai ta yarda da abin da mutane suke yi mata ƙazafi a kai ne?

Ta juya tana fuskantar tagar ɗakin, idanunta fes akan  farin watan da ya hasko su. To idan ma hakan ne, ai bai kamata ta ga laifinta ba, komai da ke faruwa a rayuwarta silar tsatson da za ta fito ciki ne. Nan da nan hawaye suka wanke mata fuska. Ba zato ta ji hannun Ummanta a kan ƙafafunta.
  "Haulatu, tashi zaune mu yi magana."

Ta share hawayen gudun kar Umman ta gani sai dai tuni ta makara, zama ta yi jikinta duk a mace ta ƙurawa ledar ɗakin idanu wanda duk ya cinye ana ganin ƙasar dake a ƙasa.

"Tun da yamma da na shigo gidan nan na fuskanci akwai abin da ke damunki amma ƙoƙarin nunamin kike babu komai. Kina da wacce ta fi ni ne?"

Ta girgiza kai, kukan da ta ke dannewa a ƙirjinta kawai ta saki gami da faɗawa jikin Umma. Ba ta hana ta ba, sai da ta yi mai isarta ta yi shiru kafin Umma ta ɗago kanta. Cikin murya ta rauni irin na Uwa ta ce.

"Faɗamin meke faruwa?"

Ta labarta mata yanda Hindatu ta yi mata ɓoyon sabon saurayinta har tsawon sati biyu, da kuma nunawa Umma abu ne da ba su yiwa juna. Ita komai da ya dangance ta Hindatun ta sani. Ta ƙara da faɗin.

"Umma na soma zargin ko dai itama tana guduna ne saboda ƙazafin da jama'ar unguwa ke yimin wai nima yar bariki ce zan musu ƙwacen miji ko saurayi idan naga fuska. Ko dai shi ne dalilin da Mominta ba ta taɓa nuna tana kaunar alaƙarmu da ita ba? Umma zuciyata na zafi idan na tuna wai iyayena ba ku da asali. Dagaske ne a bariki ku ka haɗu kamar yanda ake faɗa? Don Allah ki taimaka yau ki fidda ni a duhu."

"Haulatu, kenan dama duk zaman da nayi da ke na baki tarihin aurenmu da mahaifinki bai gamsar da ke kin yarda cewa ni ɗin ba ni da wani aibu ba? Ban fadamaki ban san inda mahaifiyata take ba? Duk bayanan da nayi maki bai gamsar da ke ba?" Umman ta yi maganar cikin nuna dakiya a zahiri, amma can ƙasan ranta ita kaɗai ta san baƙin cikin dake dunƙule a ciki.

Ta ƙara duban mahaifiyarta fuska cike da rauni ta ce.

"Ai ban ce ƙarya kike yi ba Umma, kawai dai so nake na ƙara sanin wani labarin dangane da rayuwarki. Yanzu ace ko sunan dangin mahaifiyarki, babanki bai taɓa sanar da ke ba? Anya zan yarda da wannan?"

Ran Umma ya ɓaci da irin kalaman Haulatun. Magana idan ta furta shi gareta kai ka ce da ƙawarta Hindatu ta ke yinsa.

"Kalmar ƙarya da kika ambata a maganata da ke kuskure ne, kar ki sake ki ƙara gangancin furtawa ga wani ma ba ni ba. Ina jiyemaki yanda kike furta kalamai gatsal ga kowa, don Allah ki yi kokarin koyon magana, duk abin da na hane ki na kuma ci gyaranki a kansa, ki dinga matukar kokari wajen kaucewa maimaici a zancenki na gaba. Kin ji ko?"

Ta gyaɗa kai kawai don ita fa ba ta ga abin zafi ko wani abu da ta furta ba daidai ba cikin maganarta. Ta fi tunanin kodai Umma ba ta son zancen ne ta wayance da cin gyaranta. Sai can kuma ta tsinci muryarta cikin sanyi ta soma magana.

"A rayuwa sai kin kauda kai kin kima koyi toshe kunne. Ba komai ne mutum zai yi ya dameki ba, kar ki sake ki kasance cikin masu zargi, ki kyautatawa ƙawarki zato tunda ba ki taɓa kama ta da laifi makamancin wannan ba. Kuma mene ne ciki idan ta yi maki ɓoyon samarinta? Komai ne ya zama dole ki sani na rayuwarta? Ko kuwa dole ne ta san komai dangane da ke? To me za ki amfana da shi idan kin san labarin saurayinnata? Ki koyi kauda kai a duk abin da ba'a nemi ki sa baki ciki ba."
Umma ta ɗan numfasa sannan ta ɗora zancen ba tare da ta ba Haulatun damar cewa kanzil ba.

"So kike na yi ta maimaita maki baƙin tarihina? Mene ba ki sani ba a kaina yanzu? Kin san mahaifina Kalangu shi ne sana'arsa, mahaifiyata kuwa an ce tun ina ƙarama ta maido ni hannunsa ba ta ƙara waiwayata ba. Kauna tsantsa, babu irin wacce ban gani a hannunsa ba, ya yi iyaka kokarinsa na ganin ya tsaremin mutuncina bai bar ni na faɗa hannun ƴan barikin da ke farautana ba koyaushe. Haka na taso ya sanya ni makaranta boko da arabi, ban yi nisan kirki ba iyakata sakandire ya cire ni ya aurar da ni ga Mahaifinki. Abu uku na sani game da mahaifiyata, na farko sunanta Asma'u, na biyu kuwa, ya cemin daga babban gida ta fito, alokacin za'a yi mata auren dole. Ya kuma ce ƴar Katsina ce. Bayan wannan abu ukun, babu abin da zan iya faɗi game da ita. Shi kuma mahai..."

"Ni bana son sanin komai a kansa. Iyaka wannan ya wadace ni." Ta katse mahaifiyarta cikin sauri da jin zafi a kirjinta, a duniya anya akwai wanda ta tsana sama da shi? Kai ba za ta ce ga shi ba.

Umma murmushi ta yi mai ciwo, sai dai ta kasa cewa komai. Ta tabbatar muddin za ta nunawa Haulatun hoton da ta ke ɓoyo shekara da shekaru wanda Babanta Mai Kalangu ya ba ta sadda yake kwance cikin ciwon ajali, to fa a taurin kai irin nata, za ta iya bazama ta ce za ta Katsina nemo mata asalinta idan ya so komai zai faru ya faru. Tun a baya ta yi niyyar ta nunamata hoton wanda a bayansa hatta da cikakken sunan Asma'un akwai da na mahaifinta wanda ba ɓoyayye ba ne har a yanzun ma koda ace ba ya raye, sai dai yanda ta kula da zafin ƙiyayyar yarinyar akan Uban nata sai ta fasa. Ita kuma a ranta ta riga da ta ƙullaci mahaifiyarta Asma'u da har za ta iya yin watsi da lamarinta har haka, ta tafi ta bar ta a bariki saboda kawai son zuciya irin nata. Ba ta taɓa muradin zuwa inda take ba har a yanzu da take jin zai wahala ace tana nan a raye ciki duniyarnan. Wasu lokutan takan fiddo hoton ta zubamata idanu idan Haulatun ba ta gida, ta yi hawayen ta share sannan ta mayar ma'adani, har ma ta tsinci kanta da sanya ta cikin addu'a. Babu yanda ta iya tunda wannan na daga cikin haƙƙin iyaye akan yaransu. Ba ta fasa yi ba.

Yanda uwar ta zurfafa cikin tunani, hakanan Haulatun ke fidda hawaye tana tunanin baƙaƙen ɗabi'un mutumin da ya kasance uba a gareta. Bugun gidan da ake yi ne kamar za'a ɓalle ƙyauren shi ya fargar da su. Eani guntun tsaki Haulatu ta ja gami da komai katifarta ta runtse idanu tana jin wani raɗaɗi a kirjinta, bugun da yake yiwa gidan ji take inama za ta iya zuwa ta ɗauki mataki a kai, sai dai inaa, ta san hakan ba mai yiwuwa bane. Tana jin fitar Umma daga ɗakin ta ƙara jan zani ta rufe fuskarta.

***
Ya dube ta sama har ƙasa, ta kauce ya shigo ta rufe gidan. Shigewa ya yi bai ce mata komai ba ɗauke da ƙullin baƙar leda a hannunsa ko sannu da zuwan da ta yi bai amsa ba. Ba wannan ne farau ba. Ita dai duk sadda ya shigo ba a buge ba ta sani akwai dalili babba. Har za ta koma ɗaki ya dakatar da ita.

"Ke, ki zo ina son ganinki."

Umma ta ji zafin kalaman sosai, ta tabbatar ɗiyarta sai ta ji. Juyowa ta yi ta amsa.

"Ina zuwa."

"Kina zuwa? Har in ce maki ki zo ki cemin kina zuwa Na'ima? To ban baki iznin shiga ɗakin nan ba, ki zo ki shige yanzu." Ya faɗi cike da jin isa. Dama tun can Ibrahim Ɗan Mutuwa bai iya wani abu wai lallaɓa ta ba, ta ga dai yana yiwa ƴan barikinsa hakan don kafin ta haihu har gidan yake kawo su, idan ta yi magana ta sha jibga.

Zuciyarta zafi take yi sosai, wai ace mutum ba ya tashi tunawa da kai sai idan ya ga dama? Ko kuma ya nemi ƴan barikinsa ya rasa? A cikin rayuwar aurensu babu abin da ta fi gujewa kamar haɗa shimfiɗa da shi. Ba za ta iya zama ya goga mata cutar da za ta nakasta mata rayuwa ba. Ta gwammace sai dai su yi wacce za su yi. Har ga Allah ta san babu kyau juyawa miji baya, amma fa ita kam miji irin na...

Tunaninta bai kai aya ba ta ji an haɗe kanta da ƙyauren ɗakin ji ka ke kau! Ta bugu a goshi. Sam ba ta ji tahowarsa ba hakan yasa abin ya zo mata bagatatan.

"Don ubanki mai kalangu ni nake maki magana kina ji kika mai da ni wani banza? Ai ko sadda na ci zamanina Ubanki ma bai isa na yi magana ya ji ya yimin kunnen uwar shegu ba ballantana kuma ke da kanki!"

Idanunta a runtse cikin jin zafi da raɗaɗin maganganunsa.

"Ka daina zagin ubana, na faɗamaka ba ya min dadi."

Ta furta cikin dakiya, ya kuwa kai mata bugu a baya, hakan bai masa ba sai da ya zaro belt.

"Ni kike gayawa na bar zagin Ubanki? To yau kuwa za ki ci uban naki Na'ima! Kuma ki kwana da shiri don aure zan ƙaro naga uwar uban da zai hana ni! Wato na taimaka Ubanki na rufamasa asiri na karɓi sadakar da ya bani shi ne yau ki ke nunamin ni Ibrahim ban isa na kiraki ɗakina ki zo ba ko?"

Bai jira amsarta ba ya ɗaga belt ya shiga lafta mata, ihun ma ta kasa yi wannan karon yayinda idanun suka bushe ta kasa fidda ruwa hawayen.

Haulatu dake kwance a ɗaki tana jin komai, zuciyarta na wani irin suya, jikinta ya ɗauki rawa saboda tsananin ɓacin rai. Wani irin kaɗawa idanunta suka yi. Tana ji ana laftawa Mahaifiyarta belt akan abin da ba ta ɗauke shi laifi ba, ba ta san lokacin da ta miƙe daga katifarta ba kamar yanda ba ta san ya aka yi sai tsintar kanta ta yi a waje, Umma har ta kai ƙasa tsabar duka, yana yi yana zubamata ruwan ashariya da gori har da kiranta shegiya marar asali. Caraf ya ji an riƙe belt ɗin, ya juya yana duban ɗiyartasa wacce hasken farin wata ya haske masa fuskarta. Ya rasa dalilin da yasa tun sadda ta yi mishi barazanar tona masa asiri yake ɗan jin shakkar yarinyar. Sai dai ai sunansa Ibrahim Ɗan Mutuwa, ba zai taɓa bari abin da ya haifa ya gagareshi ba a cewarsa don haka ya ƙara tamke fuska yana kallonta. Kafin ya samu abin fadi, Umma

Please Login or Register in order to submit comment