Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mataki a kanta.

Wannan kenan.

***
Hajiya Mama da Mijinta zaune a saman kujera a falo, yayinda Umma da Haulatu ke gefe saman kafet. Ganin irin halaccin da suka yi musu ya sa Umma warware musu zare da abawa na asalin dalilin da yasa ta auri Ɗanmutuwa da kuma zamanta a cikin ƴan  bariki wurin mahaifinta. A ƙarshe ta miƙawa Abban su Bahijja hoton mahaifiyarta wanda ke ɗauke da sunan gari da kuma zuri'ar da ta fito.
Da mamaki tsantsa Abban Bahijja ya dubi sunan, ba don wai ya yi mai sunan keɓantaccen sani ba, a'a, sai don sunan ba ɓoyayye ba ne tun zamanin iyayensu har kuma zuwa yanzu da matasan jikokin gidan suke nasu tashe na kuɗi da ma ilimin boko da arabi. Ya maida duba ga Umma dake sharar hawaye na fargabar abin da za ta je ta tarar a cikin dangin mahaifiyarta.

"Na'ima, kina son cewa mahaifiyarki ɗiya ce ga Tsohon Attajirin nan Alhaji Bello Shu'aibu Malumfashi?"

Hajiya Mama jin sunan ya sa ta kalli Abban da mamaki kafin ta kai hannu ta karɓi hoton, matar kamar an tsaga kara tsakaninta da Umma sai ko ta juya ta ga rubutun. Asma'u Bello Shu'aibu Malumfashi. Katsina. Har da kwanan wata na sadda aka yi hoton.

"Ikon Allah." Shi ne abin da Hajiya Mama ta furta. Umma bayan ta amsa da Abban Bahijja da eh, shima jinjina kai ya yi cike da tsantsar mamaki. Ya sani akwai sauran rina a kaba a ɓangare na rayuwar Umma, bai ce ko ba za su karɓe ta ba ko wani abun makamancinsa ba, sai dai babban zuri'a ne da ya tara yara da jikoki. Yana da tabbacin wannan rayuwar da ta shimfiɗa a waje daga baya ta zo musu, za ta fuskanci wasu abubuwan dole kafin ta samu karɓuwa. A hasashen Abban Bahijja kenan. Ita kuwa Haulatu ta ma kasa gane me take ji, ita ba farin ciki ba ita kuma ba akasinsa ba. Ta dai sani Umman ta bata mamaki yanda ta iya ɓoyemata wannan hoto tun tsawon waɗannan shekarun da take nacin sai ta nemo danginsu.

Haka suka rabu bayan Abban ya sa direba ya miƙa su tasha, ya kuma ba Umma kudi masu ɗan kauri cewa su riƙe. Ba iya nan ya tsaya ba sai da ya bi ta da nasiha akan ta yi hakuri ta jure dukkan wani abu da za ta fuskanta a cikin zuri'ar. Umma ta yi godiya sosai. Haka suka kama hanya bayan sun shiga har gidan makwaciyarsu  Maman Hasiya itama sun mata sallama. Haulatu ko ta kan Hindatu ba ta bi ba don tun abinda ya faru Hindatun ba ta ko neme ta a waya ba bayan biki ta ji ya ake ciki wannan ya sa itama ta watsar da ita.

   Ƙarfe sha ɗaya daidai motarsu ta ɗaga daga tasha suka kama hanyar Katsina.  Abban Bahijja ya tabbatar musu cikin Katsina iyalan ke da zama kaf dinsu, ba wai a Malumfashin ba. Ita kuwa Hajiya Mama lambar wayar wata yar uwarta ta ba su akan su fara sauka a can su huta, ta kuma kira ta yi mata bayani, babu musu ta ce za ta jira su.
A hanya haka ta dinga kira ta ji ko sun shigo. Suna isa kuwa, ta ce su nemi adaidaita sahu, su ba shi waya ta yi mishi kwatance.
  Suka kama hanyar unguwar Dutsin Safe Low cost, ita dai Haulatu tana kallon wurare. Ta sani nesa ba kusa ba za ta haɗa garuruwan biyu ba a fagen abubuwa da dama, sai dai kuma muddin kwanciyar hankalinsu a nan yake, ta shirya shimfiɗa sabuwar rayuwa a Katsina, za ta taya Ummanta zaman haƙurin da ta ji Abban Bahijja na magana akai, akan dai ta ƙara rayuwa da mutum irin Ɗanmutuwa.
  Ta kalli Umman ya fi a ƙirga, ko kusa babu ɗigon fara'a a fuskarta, ta dai bar zubar hawayen sai ko kumburin da idanunta suka yi da kuma ja da fuskar ta yi. Ta yi ɗan kwafa, a ƙasan ranta ta ce.
  'Umma kukanki ya zo ƙarshe in sha Allahu koda ba a karɓe ki a dangin Mamarki ba, babu mu babu ƙara komawa Kano.'

Wannan shi ne alwashin  da Haulatu ta ci. Sai a sannan ne ma ta ji ranta ya yi fari ƙal, har wani murmushi ta yi.

Sun samu tarba mai kyau daga wurin yar ƙanwar babar Hajiya Mama, wacce ake kira Hajiya Rabi'atu. Mace ce babba sai dai ba ta kai Hajiya Mama a shekaru ba, gidanta madaidaici mai kyau da tsari. A falonta akwai tafkeken hotonta ita da miji da yaranta su bakwai har da ƴan biyunta maza masu ƙananan shekaru. Ta ba su lafiyayyen abinci da abin sha suka ci suka ƙoshi sannan suka yi sallar Azahar. Duk yadda Umma ta so ta bar su su ƙarasa gidan da zasu je a ranar ƙi ta yi, ta rantse sai sun kwana. Mace ce mai fara'a da son mutane ga hira. Nan ta dinga ba su labari na irin tarin arziƙin gidan Bello S Malumfashi, fadi take.

"Ai Maman Haulatu ba komai ba ne daga arziƙinsa idan an haɗa da na matasan jikokinsa. Sai dai fa naji ance akwai rikici iri-iri a wannan gidan da kuma shegen gasa, kowa burinsa ya fi ɗan uwansa. Amma dai kaf cikinsu naji ance akwai ɗaya da ya fi su a komai, ni ko jikan Hajiya Saratu ne ko wa? Na dai manta. Ke na san fa duka wannan labarin a bakin wata ƙawata da Hajiya Iklima, ita ɗiyarta na auren wani ɗan riƙo a gidan ne."

Haka ta dinga zuba hira wanda Umma duk hankalinta ba ya kai, fargabarta na kan abin da zai je ya zo. Yayinda Haulatu ta baza kunnuwa tana sauraro sai faman washe haƙora ta ke, babu ma kamar Hajiya Rabi da ta dage sai ta yi musu rakiya a goben, acewarta za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an karɓi Umman hannu bibbiyu.

"Uhm." Shi ne kawai abin da ya fito a bakin Umman.

***
  *LATE ALH BELLO S MALUMFASHI RESIDENCE.*
Fitar tsiro
Page 13
*Late Alh Bello S Malumfashi Residence*

Haka aka rubuta a ƙaramin allo wanda ya sha adon baƙi da kuma ruwan zaiba da aka liƙe a daidai tafkeken gate na shiga gidan. Haulatu ta ɗauke kai daga saman allon ta mayar da idanunta kan gidan wanda kusan tun farkon layin har zuwa ƙarshe shi ne ya ci ɓangaren dama. Gida ne mai adon fari da ruwan toka. An ƙawata wajen da shukoki masu kyau inda aka gewaye wurin shukokin da wasu fararen ƙarafina sai kuwa fitilu dake jikin bangon wanda ko ba a faɗi ba idan dare ya yi su na taimakawa wurin daɗa ƙawata su.

  "Madams, ina zuwa?"

Hankalin Haulatu ya koma ga jibgegen ƙaton dake tsaye jikin ƙofar shiga gidan, idanunsa akan Umma, sosai yake ganin kamanninta da mutan gidan, sai dai shigar da ta yi ko ƴan aiki albarka. Hajiya Rabi cikin sauri ta amsa.

"Mun zo wajen Hajiya Babba ne."

Ya ƙara duban Umma kafin ya dubi Haulatu, kai shi abin mamaki yake ba shi, to ko ƴan uwansu ne daga Malumfashi? Ƙarshe dai ya ce su jira yana zuwa. Cikin ɗakinsa na gadi ya koma ya danna kira ɓangaren Hajiya Babba. Koda aka amsa ya yi bayanin an yi baƙi, babu ɓata lokaci aka ba da umarnin su shigo. Ya sani dama idan har ɓangaren Hajiya Babba ne, ba a fiye disga baƙo ba. Matuƙar aka zo ganinta, to fa koda ace jikin girma ya hana ta fitowa wurinka, ba za ka tafi hakanan ba.

Dawowa ya yi ya yi musu iznin su shiga. Nan fa suka shigo farfajiyar gidan da ya kusan tafiyar da numfashin Hajiya Rabi da Haulatu. Ita dai Hajiya Rabi tun da take ba ta taɓa shigowa gidan S Malumfashi ba sai dai ta ji ana koɗa shi a wani wurin, ga Haulatu kuwa, ta sha jinin jikinta don ba ta hangi inda za su sami matsagini a gidannan ba ita da mahaifiyarta. Umma kuwa ƙirjinta ke bugu da sauri-sauri, hatta da jikinta rawa yake yi. Ta daure ta shiga ambaton sunan Mahaliccinta.

"Kun san hanyar kuwa?" Suka ji sautin Maigadin na tambaya. Kamar wasu ƙadangaru haka Hajiya Rabi da Haulatu suka shiga girgiza masa kai.

"Hey! Siii!" Suka dubi wanda yake kira don su gaba daya yanda suka shagala da kallon gidan bai sa sun kula da wanzuwar wata halittar bayan su huɗun ba. Wani ne sanye da irin uniform din dake jikinsa, ga dukkan alamu shi dinma abokin aikinsa ne sai dai shi saurayi ne bai kai shi shekaru ba. 

"Kai su wajen Hajiya Babba."

Ya dube su, baki ya ɗan buɗe ganin Haulatu, da idanunsa suka sauka kan Umma kuwa, sai da ya ɗan fiddo idanu.

"Wai ba ka ji ba?" Cewar babban a ɗan fusace hakan ya sa shi soma tafiya su na binsa a baya.

Haulatu ta ƙirga gidaje masu kala iri guda biyar curr sai kuwa wasu gidajen a gefe guda masu kala daban. Har suka ƙarasa ɓangaren matar da aka ambata da Hajiya Babba ba su ci karo da kowa ba kai ka ce babu kowa sai su ɗin. Saurayin ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa ƙofar, can babu jimawa aka buɗe. Wata ƴar dattijuwa ce.

"Baba Saude, ga baƙin Hajiya nan. Bismillah ku shiga."

Ya faɗi yana mai ba su wuri, Dattijuwar da aka kira da Baba Saude ta dube su, ta ƙurawa Umma idanu tana mai cika da ɗumbin al'ajabi da mamaki. Hanya ta ba su suka shiga ciki, har sannan kallonta take yi.

"Wannan fa?" Ba ta san tayi furucin ba sai da ta ji Saurayin nan ya amshe zancen.

"Kema kin ga kamanninta da Hajjaju ko? Ba ƴar uwarku ce ba daga Malumfashi kuwa?"

Ya yi tambayar cike da son jin ƙwaƙwaf, Baba Saude ta harareshi.

"To shaida, kai dai Bilya ban san sadda za ka shiga taitayinka ba. Wuce ni ka ban wuri."

Daga haka ta rufe ƙofar shi kuwa ya yi dariya ya bar wajen.

Su Umma kuwa da Hajiya Rabi duka su na tsaye suna sauraronsu, ba su yi karambanin ƙarasawa cikin falon ba. Sai dai su na bin ko'ina da kallo, falon daidai gwargwado ya tsaru, har da wajen dinningtable a gefe, sai kuwa wani tafkeken talabijin a jikin bango dake faman aiki kai ka ce za ka yi magana na cikinsa ya amsa. Falon sai ƙamshin turaren wuta yake ga lafiyayyen kafet dake shimfiɗe.

"Bismillah ku shigo ku zauna." Ba musu suka ƙarasa suka nemi wuri ƙasan kafet suka zauna.

Baba Saude ta ƙaraso aka hau gaisuwa ita dai idanunta ya kasa kaucewa akan Umma da Haulatu masu tsantsar kama da Hajiya Babba.

"Bari na yiwa Hajiyar magana." Daga nan ta miƙe ta nufi wani ɗan tsukakken wuri da aka yi bene.

"Wai Allah, Allah ka yi mana arziki duniya da lahira. Hajiya Na'ima Allah yasa kun shigo a sa'a. Ni wallahi wannan fargabar da kike yi ne bana so, ki yi ta addu'a in sha Allahu komai zai tafi daidai. Naga gaba daya tun zuwanmu kin rasa sukuni."

Umma dai ɗan murmushi ta yi wanda ya fi kuka ciwo jin maganganun da Hajiya Rabi ke yi, amma dagaske a tsorace ta ke. Ko wace ce Hajiya Babbar nan? Ita ce mahaifiyarta ko kuma mahaifiyarta ma ta jima da rasuwa ne? Waɗannan tunane-tunanen su ne suka yi ta ƙara jefa ta cikin faɗuwar gaba.

***
Hajiya Babba, tsohuwa mai ran ƙarfe. Yanayi na hutun da take ciki ya taimaka ƙwarai wurin ɓoye tsufanta. Allah ya yiwa zuri'a baiwa ta kyawun jiki. Tana zaune saman darduma hannunta riƙe da carbi bayan ta idar da sallar walha. Sallamar Baba Saude ce ya sa ta dubanta gami da yin gyaran murya na yi mata iznin shigowa. Ta shigo ta nemi gefe ta zauna. Mintuna uku kafin Hajiya Babba ta shafa addu'a ta dube ta.

"Saude, akwai abin da ake buƙata?"

Cike da girmamawa Baba Saude ta amsa.

"Ko ɗaya Hajiya, baƙi kika yi."

Hajiya Babba dake kokarin cire gilashin karatun da ta maƙala a fuskarta, ba tare da ta dube ta ba ta janyo gidan gilashin ta ce.

"Su waye haka da safe?"

"To, nima dai ban gane fuskokin ba. Ba zai wuce wasu cikin yan uwanku na Malumfashi ba don na ga kamanni."

Ta ɗan yi jim kafin ta amsa.

"Ikon Allah, ba damuwa, shigo da su nan."

Baba Saude ta mike bayan ta amsa mata da toh. Ita kanta za ta so sanin su waye a cikin dangin nasu don ba ta taɓa ganin fuskar ba sai a yau. Ta ƙarasa sauka gami da yi musu iznin su biyo ta. Suka mike suka soma taka matattakalar, Umma dai ƙirjinta dukan tara-tara yake. Yau ne karo na farko da za ta sadu da wani a cikin zuri'ar mahaifiyarta, ko wani irin tarba za ta samu? Allah masani.

Sallamar Hajiya Rabi ce ta sa Hajiya Babba kallon hanya.

"Wa'alaikumussal..."

Sauran sallamar ya maƙale a bisa fatar bakinta sadda ta ci karo da photocopy ɗinta sadda take Hajiya Asma'unta. Umma ma kallonta take yi jikinta babu inda ba ya rawa, idan har wannan matar ba ta kasance Uwa a gareta ba, shakka babu jininta ce.

"Asma'u Bello?" Umma ta samu bakinta da furucin cike da rawar murya. Hajiya Babba ta haɗiyi wani miyau maƙwat ya wuce jin sunanta ɓaro-ɓaro a bakin wannan baiwar Allah. Ga Haulatu kuwa ta dubi Ummanta ta dubi Tsohuwarnan, hakanan Hajiya Rabi da ta yi sandar tana ganin ikon Allah. Bambancin Na'ima da wannan tsohuwa sai fa shekaru.

Umma kuwa, ambaton sunayen Allah da ta dinga jerawa a zuciyarta shi ya ba ta damar jin ƙarfin gwuiwar soma magana.

"Hajiya Asma'u Bello, wajenta na zo."

Hajiya Babba ta ji kirjinta ya buga, leɓɓanta suka yi nauyi. Kar dai ace allura ce za ta tono garma? Kada dai asirin da ta riga ta binne a bayanta, shi ne bai tashi tonuwa ba sai da shekaru suka miƙa har tafiya ta yi tafiya? Wani gumi ta ji ya tsirfo mata. Kafin ta kai ga ba da amsa ta tsinci muryar Baba Saude na fadin.

"Ai da ita kike magana Baiwar Allah. Wannan ɗin ita ce Hajiya Asma'u ake kiranta da Hajiya Babba. In ce dai lafiya?"

Jin haka yasa Umma ƙara kallon Hajiya Babba da gaba daya ta ruɗe. Ta rasa me za ta yi, murna ko baƙin ciki. Ɓangaren Haulatu kuwa, murmushi kawai take yi mai bayyana haƙora. Ita sosai ta ke jin wani dadi tana ƙara bin gidan da kallo sannan ta maida hankali ga tsohuwar da ta kasance kaka a wajenta.

"Wace ce ke? A ina kika san ni?" Tambayar da Hajiya Babba ta watsamata kenan.

"Ku zauna mana kuna tsaye."
Cewar Baba Saude don ganin abin na yi ne. Bayan sun nemi wuri sun zauna ta baza kunnuwa don jin abin da zai fito daga bakin Umma. Sai dai madadin Umma ta yi magana, kawai sai ta sa hannu ta fiddo hoto ta miƙamata tare da wani abin hannu na azurfa mai kyau da ba ta taɓa karambanin fiddo shi ba ko a baya, ta yi mishi ajiya mai nisan da ko hoton ba ta adana haka ba domin shi din sunan Asma'un ne da Maikalangu a haɗe wuri guda.

Hajiya Babba hannu na rawa ta karɓi hoton gami da abin hannun.

"Saude ina gilashina?" Ta furta da rawar baki.

Baba Saude ta cika da mamaki, da sauri ta dauki gilashin ta miƙamata, Hajiya Babba ta zura ta karanta rubutun dake jikin azurfar kafin ta kai duba ga hoton har da juya bayansa ta ga kwanan wata da kuma na gari da aka rubuta a jiki. Shikenan, ta faru ta ƙare wai an yiwa mai dami ɗaya sata! Yau ranar wanka ce da ba a ɓoyon cibi.

'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Hajiya Babba ta furta a zuciyarta. Ta ƙara ɗaga idanu ta dubi Umma wacce ta yi mata ƙuri da idanu ga hawaye kwance saman fuskarta.
Fitar tsiro
Page 14
"Kina so ki cemin ke ƴar gidan Saleh ce?" Hajiya Babba ta fisgo tambayar daƙyar daga kwakwalwa zuwa harshenta. Murmushi mai ciwo Umma ta yi.

"Ni ɗiyar Saleh da Asma'u ce. Akwai abin da kike tantama ne? Ko ki na so ki cemin kin manta sadda ki ka yi watsi da ni a bariki ba ki ƙara waiwayata ba?"

"Bariki?" Faɗin Hajiya Rabi da Baba Saude a lokaci guda cike da wani irin mugun kaɗuwa. Ita Hajiya Rabi ai ba komai Hajiya Mama ta baje mata a faifai ba. Ga Baba Saude kuwa, kallon Hajiya Babba kawai ta ke yi, burinta ta ji gaskiyar zance daga bakinta.

Gumi kawai Hajiya Babba ke yi, ranta ya ɓaci. Wato Saleh sai da ya karya alƙawarin da ya ɗaukarmata? Sun yi da shi duk runtsi ba zai taɓa barin ɗiyarsu ta san asalinta ba balle ta kawo kanta wataran ko kuma ya kawo ta, sun ƙulla wannan yarjejeniya shekaru masu yawa a baya wanda sanadin hakan ne ta yi mishi kyauta da wasu kuɗaɗe masu yawa da daraja irin na zamaninsu.

"Me kika zo nema a wurina yanzu? Wace buƙatar ce ta kawo ki?"

Haushi da bakin ciki suka mamaye zuciyar Umma, ta ma rasa me za ta ce.  Ita kuwa Haulatu wani irin kallo na mamaki take yiws Hajiya Babba. Ga ta nan dai a kallo ɗaya ta amsa sunanta da dattijuwar mace mai cikar kamala. Kalamanta sun bambanta da suffarta.

"Granny! Granny!!"

Maganar ta yi daidai da ƙofar da aka buɗe na ɗaya daga cikin kofofi hudu dake a falon. Gaba daya suka dube ta,  yarinya ce da shekarunta za su kai biyar a duniya. Tawul fari ƙal ɗaure a ƙirjinta sai kuwa gashinta mai cika da baƙi wanda ya sha tufka da ribbon. Yanayin yadda ruwa ke zuba daga jikinta za ka fahimci wanka aka yi mata. Tana zuwa ta faɗa jikin Hajiya Babba tana fadin.

"Granny, ki cewa Mami kar ta shafamin mai. Bana so."

Ya yi daidai da fitowar wacce ta kira da Mamin daga ɗaki hannunta riƙe da  kaya da kuma man shafawa na yara.

"Ke Baby ki..."

Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta sakamakon mutanen da ta gani zaune a falon, su dinma kallonta suka yi. Za ta yi shekaru ashirin a duniya, doguwa ce kuma baƙa mai ɗan jiki. Ta gaishe su mamaki dauke saman fuskarta na ganin wata mai ɗiban kama da ƴan gidansu. Wuri ta samu ta zauna kuwa. Hajiya Babba ta ture yarinyar.

"Maimuna, ja hannunta ku wuce ɗaki ina da baƙi."

"Baƙi kika ce fa Hajjaju? Ai ce mata za ki yi ɗiyarki ce da kika bar wa duniya ita ta dawo."

Muryar Haulatu ta zo musu a bazata, zuwa lokacin ta gama kai wa wuya dama, ta kula Hajiyar za ta kawo musu rainin hankali da wayo.  Hajiya Babba duban Haulatu ta yi amma ta kasa magana. Ita kuwa Maimuna sai ta yi turus cike da tsantsar kaɗuwa.

"Assalamu alaikum." Aka faɗi da murya kakkaura. Hajiya Babba ba ta san sadda ta miƙe tsaye ba. Wannan shi ne abin da take jiyewa tsoro, babban burinta ta san yadda za ta yi da su Umma kafin wani ɗan uwan nata ya shigo. Baba Saude da Maimunatu suka gaishe shi.

Dattijon mutum. Dogo mai cikar farin ƙasumba. Kallo ɗaya za ka fahimci girman da ya kama shi sosai. Dakta Suleiman B.S Malumfashi kenan.

Ɗa na huɗu a wurin Marigayi Alhaji Bello. Su biyar ya haifa. Hajiya Asma'u ita ɗaya ce mace a cikinsu. Su uku kawai suka rage a yaransa. Shigowar da ya yi ta musamman ce, magana ya zo su yi da Hajiya Babba akan jikarta Maimuna da ta yo yaji kuma Hajiyar ta ɗauremata gindin zama.

Umma ta dube shi, shi ma Dakta ita ya zubawa idanu yana amsa gaisuwar su Baba Saude.

"Yaya, sannu da zuwa." Fadin Hajiya Babba da rawar baki. Idanunta nan da nan suka kawo ruwa tsabar tashin hankali. Yau dai abin da ta binne shekaru masu yawa zai tonu.

"Yauwa. Asma'u, wace ce wannan din?"

Ya yi tambayar yana ƙara gyara zaman gilashinsa. Tuni Haulatu ta yi caraf ta ce.

"Ni jikarta ce, wannan kuma (ta dafa kafaɗar Umma) ɗiyarta ce ta cikinta da ta haifa ta bar ta a hannun mahaifinta Saleh Mai Kalangu ba tare da ta ƙara waiwayon rayuwarta ba."

"Saleh Mai Kalangu?" Dakta ya maimaita sunan, shiru ya ɗan yi yana nazarin inda ya  taɓa sanin wannan suna kafin ya yi salati a fili yana duban Hajiya Babba wacce tun shigowarsa ta miƙe tsaye kawai sai ta fashe da kuka.

"Asma'u, kodai ban ji da kyau ba. Ɗiyarku ke da Saleh Mai Kalangu? Wannan zancen gaske ne ko kuwa dai wasa ne aka zo a ynda hankulanmu?"

Ta kasa magana sai kukan, ranta na suya da zafi tana ji kamar ta kama Haulatu ta jibga tsabar yanda ta yi mata tonon silili a idanun mutumin da take yiwa kallon Uba kuma ɗan uwa mafi kusa da ita. Mutumin da ba ta taɓa ɓoyemasa komai ba kasancewarsu saƙo da saƙo kuma jininsu ya haɗu sosai fiye da sauran yayyunta maza. Yau dai ga babban sirrin da ba ta taɓa gigin sanar da shi ba. Bayan ita da wasu bayin Allah biyu da ta rayu da su a can wani gari, sai ko uban gayyar Saleh Mai Kalangu, babu wanda ya san da batun cikin Na'ima balle a san da wanzuwarta a doron ƙasa a dai nan garinsu Katsina.

Shiru ma magana ce inji Hausawa, tabbas shirun da Hajiya Babba ya tabbatarwa Dakta zarginsa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un." Ya maimaita a karo na biyu. Wayarsa ya fiddo ya danna kira, yayansu babba da ya rage ya kira ya ce masa ga su nan zuwa da baƙi, magana ce mai muhimmanci.

Yana katsewa ya dubi Hajiya Babba, gaba daya idanunsa sun kaɗa.

"Ku muje can ɓangaren Alhaji a yi magana. Wannan ba ni zan yi hukunci ba."

Ya ƙarashe da jin ɗaci a maƙoshi. Daga haka ya sa kai ya fice daga falon bayan ya ba Maimuna umarnin ta yiwa su Umma jagora sashin Alhaji.

***
Babban falo ne mai dauke da ababen mora rayuwa daidai gwargwado. Tsaruwarsa ya shafe na sashin Hajiya Babba. Wani tsoho ne zaune saman dardumarsa ta ibada. A gefensa wasu matasa ne biyu wadanda duka ba su wuce shekara ashirin da takwas ko tara ba. Hira suke yi kafin wayar da Dakta ya yiwa Alhajin ta katse su. Ko bayan kammala wayar shiru suka yi baki daya domin da yawan lokuta Alhajin yana amsa waya ne ta hanyar sanya ta a handsfree. Wannan ya ba samarin damar jin abin da ya ce. Ɗaya a cikinsu wanda ya fi ɗan uwannasa jiki da kuma hasken fata ya miƙe.

"Bari na ƙarasa ofis kafin wancan Baturen ya kore ni."

Jin haka ɗayan ya yi dariya gami da faɗin.

"Kai Haidar, ka iya bakinka fa, ko ka mance a gaban amininsa ka ke? Wannan ɗan tsohon ko tusa aka yi sai ya fesa mishi."

Alhaji ya kai mishi duka da sandarsa dake ajiye a gefe. Aka yi dariya baki daya. Ya amsa.

"Ja'iri, kun fi kowa sanin ai Sadaukina daidai yake da ku. A hankali zai saita ku kowannenku ya shiga taitayinsa tunda na kula ku kam ba ku da aiki sai kashe-kashen kuɗi. Kai kuma mai kiransa da Bature kamar a kunnensa."

Wanda aka kira da Haidar ya kama kunne.

"Tuba nake tsoho mai ran ƙarfe, Ango kuma miji gurin Hajja Bilkisu mai gadon zinare. Allah ya ja da ranka, idan ka mutu kuma Allah ya haɗaka da ita a aljanna."

"Amin, amma mutuwa kam ba yau ko gobe ba da yardar Allah. Ɓacemin kafin ka kashemin jiki."

Matasan suka tuntsire da dariya karo na ba adadi. Kafin su kai ga tashi sai ga sallamar Dakta, wannan ya sa duka suka ɗan nutsu. Dakta da Hajiya Babba suna daga cikin kakannin da sam ba su sakin fuska yadda ya dace ga jika. Babu ma kamar Hajiya Babba wacce ake masifar shakka idan ta tubure ta hau faɗa da bala'i akan duk abin da aka yi bai yi daidai da ra'ayinta ba. Ita ce ƙaramarsu amma su na ji da ita sosai don suna yawan cewa ita ɗin amana ce ta iyayensu, kuma sun musu Allah ya isa idan har sanadinsu ta shiga wani yanayin. Wannan ya sa ba a

Please Login or Register in order to submit comment