Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*GIDAN MAGAJI YA*
Oumyasmeen

*BOOK 2*

_Allah isa yadda na fara lafiya Allah isa na gama lafiya ina godiya masoyana bazan iya biyan ku ba har abada_


Episode 21-22


Da tasan wannan rana zata zo da ta yanke alakar'ta da ko wanne ɗan iska sai yanzu ta gane gaskiyar maganar da kahu yake faɗa mata kullum ki dena tara ya'yan Allah ya shirya mana ina jiye miki ranar da za su dauko miki abin da baki zata ba su goga miki kashin kaji daga kanta sama tayi ba abin da take iya gani saboda duhu lumshe idanuwanta tayi miƙewa tayi ta zauna amma ina ba damar haka ala dole ta koma ta kwanta
iya tsinuwa Asif ya shata ba iyaka daman ita ta dade da sanin duk wani me aikin force bashi da imani.....ko dan uwanta ne ai ta rabu dashi abin tsorone

*🤔tab*

Gurin dinana kuwa da sauke dakin da aka sa shi cel ne yana da fadi kuma shi da rabi aka sa shi sunyi haka ne ko za su ƙara jin wani abu sosai dinana ke kuka yace

"Rabi kin ga irin kaddarar da kaska ya samu ko...?,

Rabi'u dai wanne irin rabi

da sauri dinana ya ɗago tun da aka shigo da shi be shi yayi magana ba da badaki ɗaya aka sa su ba dariya ce ta kubce mai duk kuwa da halin da yake ciki kan rabi da yaci jal ya koma yadda yake bakin nan ko jambaki babu idonsa yayi ziri ziri me zai yi in banda dariya yace

"wayyo Allah huya ta sauka ki rabi kin ga kuwa yadda kika koma sai hawaye ya zobo mai ya share ya ci gaba da cewa zan so ace wannan abin tare muke gabaki ɗayan mu muyi faɗa muyi wasa Allah sarki kahu ko za mu ƙara ganawa ko rabuwar kenan Allah ka duba mu ka fitar da mu Allah kasani abin da ake tuhumar mu da shi bamu aikata ba Allah wannan wata jarabawa ce da muna da rauni Allah ka bamu ikon cinye ta

kai rabi ya jingina a jikin bango yace

"Amin ko wanne hali magajiya take gwara mu an hada mu tare ita fa Allah ya tsinewa kaska....,

Amin ya Allah daga nan sukai shiru

duk hirar nan da suke Asif na ganin'su a cikin laptop ɗin'sa biron hannun'sa ya ajiye ya jingina da jikin kujerarsa wayarsa ce tayi ringing ganin me kiran ya ƙi da gawa har yanzu mamaki yake Aysha ce zata kashe mai waya saka yayi a meeting ya ajiye ta ya ci gaba da aikinsa...


*Kano.....*

yinin ranar haka kahu yayi shi ba dad'i kallon Sama'ila yayi da yake kuka yace

"kai hakuri wallahi inhar sun yi bincike sun ga basa hannunsu kamar an sako sune su hukumar dss basa kama mutun ba tare da sunyi bincike ba in sun kama shi ma za su ƙara bincike nasan magajiya baza ta aikata haka ba kamar an yi an gama....,

ci gaba yayi da kukansa domin daga ita sai kahu suka rage mai a duniya kahu baya haihuwa sau daya ya haihu a wannan fadan na boko haram a gabansa aka yanka ɗan da ya haifa me shekara goma sha biyar sa'an sama'ila wani zubin yana sane yake biyewa su dinana dan ya kawar da radadin zuciyar sa da damuwarsa kallon uwani yayi yace

"kinga gobe bamu da abincin ci ke zaki fara sai da duk abin da magajiya ke yi kafin ta dawo dan murufawa kan mu a siri......ai kai kasan duk inda take karbo kaya ko....? Muci abinci mu ajiye mata sauran kuɗinta....,

eh na sani Sama'ila ya basa amsa

Ajiyar zuciya uwani ta sauke tace

"To Allah ya kai mu yau da dare sai inyi...dan mu tashi da abin da za muci...,

amin ya Allah sumayya ce ta shigo kallon gabas tayi ta shiƙe da dariya tace


"kahu kaga ikon Allah ko aminai uku an tarkata su Allah ya sa ma su dawo ta faɗa tana jin wani dad'i aranta daman magajiya ta tokare mata a rai komai ita kowa ita ga uban ciniki da take....,

kallon ta kahu yayi cike da mamaki saunawa magajiya ke ciyar da ita ko kamata akai ita ke zuwa bilinta dan adam kenan Allah ka rufa mana a Siri Ka bawa maƙiyan mu kunya wannan kadan daga cikin halin dan adam wani burin'sa yagan ka kullum a cikin huya yace

"Hassada da me rabo take ce baka samin nasara ta cikin sauki kar kiyi mamakin wannan shine silar arzikin ta kar ki mamakin wannan abin shine silar daukakar ta da haka Ubangiji yake komai yana da sanadi.....,


Wani kallo tayi mai tace

"Gyara bakin ka kahu gidan yari naje ba sau daya ba sau biyu ba Ni zan faɗa maka wani gidan yari Allah ya rufa maka asiri kar ta dawo da cikin shege domin wasu a cikin su ba mutanan kirki bane.....,

Bakin ki ya sari danyan kashi Allah ba zai jarabbe mu ta wannan fannin ba insha Allahu tana tare da Allah da mala'ikon'sa wallahi wannan abin kamar a kunnan'ta

wata dariya tayi ta fita fitar ta ba dadewa su saudat suka shigo da dan a shararle sai manjagara kuka sosai suke haka suka hunarwa kahu bayan sallar la'asar suka bar gidan inda uwani tace musu za tayi abinci da waina suka ce sai sun dawo daman baka gane masoyin ka sai kaddara ta hauka

*Allah Ka hadamu da masoyan mu na hakika*

*NNDC quarters*


Kabiru wallahi kashedi nayi maka kaga danka ASIF kai mai magana ya fito da matar aure dan kaf dangin mu ba juya ka tsaya ka zuba ido kai da shashashar matar ka....

ƙasa yayi da kansa yace

"Insha Allahu zan masa magana...,

goro ta ɓantara tace

"karma kai masa na kusan zaɓo dalleliyar budurwa a cikin kannan'sa yarinya sharaf yadda waccen saunar zata ji haushi in aura mai badai ina da malam liman ba rana tsaka wallahi za kuji ana sanarwa danni har lefe na gama haɗawa...,

da sauri ya kalleta gaskiya abin hajiyar tasu azimin ne yace

"godiya muke Allah ya ja daranki....,

banza tayi mai tana ci gaba da cin goron ta can ta dube'sa tace

"zaman me kake kuma bayan mun gama magana....?,

tashi yayi yace Allah hucu zuciyarsa ki na zata da wani abin ya sakai ya fita....,

jidda ce ta shigo tare da inteesar suka zauna suna kallo ya akram ne ya shigo da ayman suna hira sallama sukai hajiya ta amsa bakin'ta a washe tace

"a'a yan samari yau kune a gari...?,

zama sukai ayman yace

"eh wallahi Abuja tayi mana zafi haba aikin Company sai da hutu dan ma ogan namu be sani ba jibi za mu koma....,

Innalillahi haka kuka baro mai dukiya kuka tawo ita waccan shashashar ta maƙale kafa ba iya kular mai da ita za tayi ba....to wallahi kamar akunnan sa danni ba'a munafurci dani wallahi


Akram yace

"Kasan halin hajiya faɗi ce ba a tambaye ta ba me isaka Kai Mata wannan zancen dazu na kirashi na faɗa mai ya fada yana kifta ido...,

Karab a idon jidda sanin baya wasa da su bakamar ya ayman ba tayi shiru da bakin ta halin su daya da ya asif shima ba shi da kirki kai hajiya ta gyada yan masifar basa kusa tashi jidda tayi tace


"Hajiya bacci zanyi...,

wata harara hajiya ta watsa mai tace

"zo ki kwanta akai na yau nake jin wani tsohon kinibibi da ba hucewa kike ki kwanta ba shine zaki wani ce bacci kike ji a'a suma kike yi huce ki tafi gidan ku yau bazaki kwanar min ba kibi ki daddanne ni.....salon ki karya min kashi....,

kuka jidda ta kusan sawa ta killi hajiya ta zata huce dakin hajiya akram ya daka mata tsawa ya nuna mata hanya yace

"zo ki huce me ta ce miki...,

kamo jidda hajiya tayi tace

"to me halin uban gidana ku dai sai addu'a da nake cewa zan baka jidda ashe wata ran kashi zan tarar.....tab da sake....,

haɗa rai Akram yayi yace

"Allah ya rufa a siri nii...hajiya karfa ki fara ai wannan salon raini ne....,

Ubanka kai da rainin dan uwarka nawa ubanka ya auri uwarka nace ko da sauri ayman yace


"haba hajiya da fa yara a gurin nan be dace ba....,

Allah ya rufa a siri ta ja bakin'ta tayi shiru dakin shiru yayi a fakaice akram ke ƙarewa jidda kallo yarinyar bata da makusa inba Dan rainon hajiya bace sai addu'a kafin ya tafi chaina zai lallaɓa hajiya a tsaida magana ci gaba da kallo inteesar tayi ɗagowa tayi suka haɗa ido da ayman murmushi yayu mata yace


"zo kiga wata sabuwar game da na ɗauko...,

ba musu tazo haka jidda suka sa shi a tsakiya suna kallo tsawa akram ya dakawa jidda yace

"Baccin ke nan gaskiyar hajiya da tace na kinibibi ne ke inteesar ku tashi kuje kuyi bacci gobe a kwai makaranta....,

ba musu suka tashi jidda rannan a ɓace kamar za tayi kuka ta kusan fita tace

"Ya Ayman Dan Allah gobe zaka bamu yi....,

Eh zan baku

to wayar fa yau she zaka siya mana

sai babban yaya ya yarda

tab kawai ka fito fili kace baza ka siya ba ko inteesar in ta babban yaya ne mu mutu bamu da waya tana faɗar haka ta fita Akram

na'am hajiya

Akram

amsawa ya ƙarayi ta ƙara kiran sunan sa tace

"Saunawa na kiraka...,

Uku hajiya ya bata amsa tace

"Wallahi kafita a sabgar jikokina in ba haka ba zan ɓatar maka...,

To yace ya ci gaba da danna wayarsa haka ma ayman halin hajiya sai hakuri ba wanda ta kyale......


*Abuja osokoro*


Cikin sauri yake haɗa komai da zai buƙata a gida ya saka a cikin brief case ɗin'sa ya zuge wayar'sa ce ta kawo haske dubawa yayi yaga wanda ya bawa receip ɗin nan ne yayi bincike ya ɗauka cikin girmamawa yake cemai

I researched it and sent you a photo of the two people who touched him, and the numbers on his body are now not working ...
ya ci gaba da cewa

but no matter which number there is information about its location


dad'i yaji ganin binciken bazai dau ki tsahon lokaci ba yace

"I'll go home and check...,

see you later ya kashe wayar'sa zura ta yayi a cikin aljihu ya dauki kyes dinsa ya fito har yanzu surayya na office din sai ya tafi zata tafi sai dai in jimawa zai yi yace ta tafi zaune take ita da wata da sauri nihila ta kama kanta tace

"Barka da fitowa......,

Kamar kullum ciki ciki ya amsa mu su ya fita daga tashi surayya tayi tace

"kinga ko ai daman na faɗa miki wannan mutumin in ba malamai muka bi ba wallahi bazai san kina yi ba.....,


dafa kanta tayi tace


"bazan ƙarar da kuɗina a banza ba kina tunanin irin mutanan nan wani abu nacin su wallahi ba a shiga dawa dan karya surayya zai fito ne be shirya ba mudai canza wata shawarar anya kuwa nima ba aikin nan zan sa daddy ya samamin ba wai ke surayya ya akai rana tsaka kika sami wannan damar.....?,

dariya ta shiƙe da shi ta buɗe da jakarta dala ta fito da ita tayi ƙasa da murya tace

"Ni yarinyar matemakin Asif ce nima da ban gane ba sai da na gane nayi mai magana ina so da kyar na samu wai baya son aiki da mace kinji fa karamin dan iska.....ai a duniyar nan kawata inhar zaki bada wannan to wallahi ba inda ba zaki ba abin da ya saka ma naga baki da mu da irin wa'yannan abun ba kin tashi cikin gata nifa yar malam shehu gwara in yagi abin da na yaga kafin ungulu ta koma gidan ta na tsamiya.....,

ajiyar zuciya nihila ta sauke tace

"bawai ban damu bane a'a wannan ita ce daraja ta kimata....,

tsaki surayya ta ja tace

"yanzu fa technology ya yawaita likitoci kwararru sun bayyana tuni za su mai da ke yadda kike a da wallahi ke karya mutum yace anyi....,

dariya nihila tayi tace


"Ginin Allah daban ba ɗaya dana baturai ba....,

zauna kiga zama ni kuwa makarantar ma na dena zuwa wallahi takardar bogi akai min na zo gurin nan ke nifa naga kin tsaya kallon ruwa wallahi Allah tuni zanyi wub da shi sai dai kiji ana buɗa in zama kishiyar Aysha in goga kafada da ita hura hancin da take min nima in hura mata matsayin mu ɗaya da ita


hmmm kin ɗauki duniya da zafi tana kokarin daukar jakarta raya ta yawa tayi tace

"Ni zan tafi sai mun haɗu gobe....,

okay see you later

handle din kofar ta murɗa ta fita kai tsaye wajan da ta ajiye motar ta ta nufa gaban tane ya waɗi ganin uban security ashe Asif be tafi ba kasa shiga motar ta tayi ta zuba mai ido Allah ya ɗora mata son sa taka fatan Allah ya mallaka mata shi mota wani daga cikin security ɗin ya buɗe mai ya shiga sauran ma suka shiga a guje ko wacce mota ta fita cikin tsari kai dole mutumin nan yaji kansa a sama

duk wannan mutanan an tanade sune saboda da shi ba dole girman kansa ya ƙaru ba ajiyar zuciya tayi ta shiga cikin motar ta a hankali take tafiya tana dan sake sake a zuciyar ta har taje gida ko dai-dai ta parking bata tsaya yi ba ta fito key ta miƙawa me bawa shukoki ruwa ta bashi amsa yayi ya gane me take nufi

kai tsaye shiga floor tayi ba kowa a floor gidan yayi shiru daman yau hajiyar ta aikin kwana take hanifa na gun nanny bene ta hau ta buɗe dakin'ta cin karo tayi da zee tana kokarin fita fusgota tayi tace

"na kama ki daman ke kike min yan kana nan sace sace.... bani abin da kika ɗauka....?,

jikin zee na rawa tace

"Wallahi ai kafin ta karasa ta wanke ta da mari tace "ki bani nace miki bawai tsayawa dogon zance ba...., dan Allah ki yi hakuri

Tanka ɗata tayi ta rufe kofar ajiye jakarta tayi akan gado cikin ɗaga murya tace

"Zaki bani ko sai nayi miki abin da zaki nadama na har abada....,

jikin zee na rawa ta ƙara matsai abin da ta ɗauka a bra ɗin'ta a fusace nihila ta fisgota ta yaga mata riga sai ga sakar gold a cikin bra salati nihila ta saki tace

"daman ke kika daukar min waya ta to dole yau ki koma kauye wallahi .....,

ɗur ƙusawa tayi tana kuka tana bata hakuri amma nihila ko a jikin'ta sai ma hutar da take ruruwa a zuciyar'ta daukan sarƙarta tayi cikin kuka zee tace

"Wallahi Allah ba sata nayi ba photo zanyi da ita in dawo miki da ita....,

Rufe min baki dole yau ki bar gidan nan ƙara gigicewa zee tayi dan bata shirya cin kariyar miya ba da baƙin tuwo dakyar nihila ta haƙura ta fita daga dakin......

*Gidan Asif........*

Daidaita parking driver da ya kawo shi yayi ya buɗe mai kofa mamaki ne ya kama shi ganin motar Aysha daman kiran da take mai kenan dauke kansa yayi tare da ƙara karantar wayan nan sabbin masu gadi da aka kawo mai yayi wani kasaitatcan murmushi wanda shi ƙadai yasan ma'anar sa........

*ku yi following ɗina domin samin ci gaba da zarar na ɗora*


GIDAN MAGAJIYA

EPISODE 23-24 book 2


Kofar da zata sada shi da main floor ya shiga baƙin sa dauke da sallama tana zaune yar aikin ta na tsiyaya mata ruwa jin sallamar Asif da sauri ta ajiye ta ƙara risinawa tace

"Barka da dawowa....,

ɗauke kai yayi cikin takaici yace

"yauwa sai mutum ya kasa kunnu tukun na zai ji abin da yace tashi tayi ta bar gurin sai a lokacin Aysha tace

"yauwa gobe ina so in je gyaran gashi wallahi kai na baya min dad'i zaman asibitin da nayi ya ishe ni...,

Ba tare da yayi magana ba ya huce ta yana mamakin halin aysha abin da ta saka gaba shine ci aikin ta buƙatun na rayuwar'ta ba ruwanta da damuwar'sa ita dai damuwar ta kuɗi ta wata yar karamar kofa ya bi ya shiga part ɗin'sa ajiye briefcase ɗin'sa yayi akan kujera ya zauna ji yayi an turo kofa tace

"Sweet magana fa nake maka banji kace komai ba....?,

juyowa yayi ya kalle'ta ya zuba mata idanuwan'sa wani irin kallo yake mata me hautsina ya'yan hanji dakewa tayi dan wallahi dole ta kwashi kuɗin da zata gina kanta ko bayan ba ransa tun da tasan wannan shegiyar tsohuwar dole tayi mai aure a tasa zuciyar kuwa mamakin.....halinta yake

ya aureta ko primary bata yiba ba duk kan wani mataki da ta taka shine sanadi mahaifiyar ta daga makka aka koro su ita sadakar yalla ce sai yanzu yake ganin illar kin bin maganar iyayen'sa kyau ya ruɗesa sai bayan sunyi aure yake ganin abubuwa kala kala tashi yayi da sauri ta sha gabansa tace


"Asif in ma aure zakai ba sai ka sha wahalar hulakanta Ni ba ka fito fili kace min za kayi amma ka tsaya kana yi min hulakancin kala kala daman na sani wannan tsohuwar baza ta barni in zauna gidan miji na lafiya ba....,

mari ya zabga mata idonsa yayi ja cikin ɗacin rai yake cewa wanda yasan darajar tsoho shike girmama shi A'isha ban yi mamakin halinki ba nasan rashin ingantacciyar tarbiyya ke ɗawainiya da ke da rashin ilimin addini halinki ne bazai bari ki zauna lafiya a gidana ba ina ja miki kunne wallahi wallahi wallahi duk lokacin da kika ƙara faɗar wata ɓakar magana da ta shafi hajiya ranar zaki sha mamaki....


dafa kumatun ta tayi cikin ɗaga murya tace

"Asif ai naga ma shan mamakin ka wallahi dan hakasan bani da gata shine kake hulakan'ta ni bani na zaɓawa kai na rayuwa ba Ubangiji ya zaɓa minhar ni zaka duba kace iyayena basu yi min tarbiyya ba amma in ka manta bari in tuna maka bani na ganka nace ina so ba a rashin tarbiyar ka ganni cikin tsumma kace kana sona .....,


baya son cece kuce dan haka ya bata guri cikin daga murya tace

"wallahi ka ban mamaki tun yanzu kafara fito min da ainiyin kalar ka in Ka gaji dani ka fito fili kace ka gaji ina da arzikin da zan iya ci da kai na in ci da mahaifiyata a yanzu na tsaya da kafafuwana Kar ka manta niɗin wace zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shawo sai yayi.....,

cije lips ɗin'sa yayi ya hau sama zuciyarsa tamkar ta fasa kirjinsa ta fito zama yayi a bakin gado ya fara cire safar'sa sannan ya cire agogon'sa a takaice dai daga shi sai boxer ya zauna ya dafa kansa ya zura hannunsa cikin sumar kan'sa yana al'ajabi ko a mafarki aka ce mai Aysha zata aikata haka zai musa wayar sa ce tayi ringing sai a Lokacin ya tuna da yabar ta cikin aljihun wandon'sa janyo shi yayi ya ciro'ta muzabfar ne ke kira ɗaugawa yayi ya saita nutsuwar'sa domin baya son ya fahimci halin da yake cikin yace

"wa'alaikassalam munatanan Germany.....,
dariya muzamfar yayi yace

"Barka da wannan lokaci mutanan Arewa....,

Kwanciya Asif yayi yace

"bakai karya ba wannan shine a salina...,
dariya muzamfar yayi yace

"ba shiri ka baro chaina da fatan dai an ga wa'yanda sukai wannan abun....?,

ajiyar zuciya ya sauke yace

"Har yanzu bincike nake....,

To Allah ya saka a gano ga yarka ta takura sai taji Muryar uncle sai dai uncle din'nata be fiye tunawa da ita ba ya bugo yaji lafiyar ta ba kullum busy work ya faɗa yana dariyar tsokana.....

wallahi muzamfar ka kiyaye ni bani ita salon kasa ta dena ganin girmana kasan yanayin aikin mu da naka ba ɗaya ba kai dan kasuwane nifa

zaɓin ka kabi ya faɗa yana miƙawa mufida wayar amsa tayi cikin maganar yara tace

"uncle good night....,

beautiful princess ya karatu

dariya tayi ta kalli daddy ta tace

"kullum sai nayi kuka bana son school....,

zaro ido Asif yayi kamar tana gabansa yace

"Maza tuba kinyi babban saƙo bakya so ki zama doctor.....?,

uncle ina so mana

to maza ki dinga karatu in bakya yi na dena kulaki uncle yayi fushi da ke

kukan shagwaɓa ta saka mai tace "Please uncle kai hakuri na dena.....,

duk kan wata damuwar'sa ne matar yayi ya rasa ashe daman ya'ya rahama ne lumshe idanunsa yayi a yanzu ya ji sha'awar daman tare yake da yaran'sa sun zagaye shi suna shirme yana biye musu har muzabfar ya ƙarbi wayar be sani ba sai da ya kira sunan sa maxaiwa yayi yace

"me i saka ka karɓa muna hira....?,

cikin takaicin halin dan uwan nasa yana cikin damuwa ba zai iya faɗamai ba suyi maganar matsalar yace

"Miƙo min tayi tace ka kashe wayar baka magana....,
shiru Asif yayi muzabfar ya ci gaba da cewa Wallahi tu da na kiraka naji Muryar ka nasan ba gajiya bace Asif Kai wa kanka adalci mana inna rantsai ko kaffara bazan ba wannan damuwar da kake ciki Aysha ce sanadin shigar ka ka ƙara aure ba duka mata suka taru suka zama ɗaya ba mata nawa ne suke binka suna so ita ta samu tana wasarere da damarta uwa uba rashin haihuwa amma kullum kana jibgawa kanka aiki dan ya rage maka damuwa alhalin ba shine mafita ba ina jiye maka ranar da za awa gari A'isha ta saka maka ciwon zuciya kuma wallahi guduwa zatayi ta barka dan batayi kama da macan da za ta dauki responsible ɗin ka ba tun huri kafin kane mowa Kan ka mafita


Ajiyar zuciya ya sauke yace

"Ina jin ka ubana ci gaba....,

cikin dariya muxabfar yake cewa"ai na gama ƙi faɗi.....,

Kashe wayar'sa yayi ganin muzabfar zai cika mai kunne shiga toilet yayi yayi wanka tare da ɗauro alwala da yake an fara kiran sallar magariba cikin sauri ya xura jallabiya be san lokaci yayi haka ba

Please Login or Register in order to submit comment