Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *1*~*2*







*Garin* yayi duhu sosai kasancewar hadari ya had'u ga wani irin iska mai k'arfi da akeyi, wata kyakyawar yarinya na hango sai sauri ta keyi sai dai tana tafiya ne tana d'ingisawa, burin ta d'aya shine ta isa gida kafin ruwan sama ya sauko, cikin ikon Allah har ta isa gida ruwan bai sauko ba. tana shiga sai ga *INNA* nan ina ta hau ta da masifa kamar zata cinye ta d'anye, wannan yarinyan sai kuka ta keyi kawai.

Cikin kuka tace" Dan Allah kiyi hak'uri INNA wallahi yau banyi ciniki ba"

Cikin masifa Inna tace" Yau naga y'ar banza kina nufin yau ma kinyi min kwantai da Awara, to wallahi ba zai yiwu ba"

Nan Inna ta d'auko wani k'aton ice tayi kan yarinyan nan da shi, ganin haka yasa yarinyan ta ruga wani d'an d'aki da gudu tana d'ingisawa nan Inna ta bita ta fara dukan ta da wannan icen, Allah sarki yarinyan sai ihu ta keyi. dan kanta Inna ta gaji da dukan ta ta k'yale ta.

Haka yarinyan nan mai suna *UMMI* tayi ta kuka dan duktaji ciwo a jikin ta, a haka har tayi barci.


Washegari da safe da missalin k'arfe shida Ummi na kwance tana barci sai ji tayi an watsa mata ruwa. a firgice ta tashi,Inna ta gani rik'e da bokiti tana cewa" Uban wa zaiyi miki aiki kin kwanta sai barci kike ni tashi kije ki d'ebo ruwa kuma kiyo icce yanzun nan"

Tana karkarwan sanyi ta tashi ta d'auki bokiti ta nufa rafi nan ta d'ebo ruwa sannan tayo icce,bayan nan tace ma Inna" na gama"

Inna dake gaban murhu tana suyan k'osai tace" to d'auki bokitin koko ki tafi talla"

Tsayawa tayi ba tare da ta d'auka ba nan Inna tace" mene ne kin wani tsaya min a kai?"

Cikin rawar baki tace" Dan Allah Inna yunwa nake ji"

Da masifa tace" to maya in ban baki ba cinye ni zakiyi" nan ta bata wani koko na jiya har yayi tsami,

Da sauri Ummi ta karb'a hannun ta na rawa tsabar yunwa nan ta hau sha tana gama shanyewa sai amai dan rabon ta da abinci tun shekaran jiya. tana gamawa ta wanke bakin ta sannan ta d'auki tallan ta fita tana d'ingisawa.

Ba ita ta dawo ba sai wurin sha biyu na rana dan takan jima ba'a siya nata ba. tana shigowa Inna ta hau ta da masifa sannan ta bata alallen gwangwani guda d'aya taci. tana gamawa ta shiga d'akin da take kwana wanda ba komai sai buhun kayan ta dan ko siminti babu a d'akin sai k'asa, nan ta shirya cikin riga da wando da farin hijab na makaranta.

Tana fitowa Inna tace" ke ke tsaya ba inda zaki sai kinyi wanke-wanke wato ke mai son karatu ko to wuce maza ki cire kayan"

Cikin hawaye tace" Inna kiyi hak'uri inje wallahi nayi lati kuma malamin zai min duka"

Wani rangwashi tayi mata a kai mai shegen zafi da sauri Ummi ta aje jakan buhun ta ta fara wanke-wanken.

Wani mutum ne ya fito daga d'akin shi yace" yau naga y'ar banza uban mai ya hana ki aikin tuntuni wai ke a dole mai son makaranta "

Inna tace" Ashe kana jina da ita?"

Yace" Eh ai ni wallahi yaya Auwalu ya cuce ni da ya tafiya bar min wannan abar"

Ita dai Ummi na jin su tayi shiru kawai.

Bayan kwana biyu Ummi na cikin yin tatan kamu sai ga wata yarinya wace ba zata wuce sa'ar Ummi ba. ta watsa mata wasu tsoman kaya tace" ke wanke min kaya na dan biki zani anjima saura kuma kar su fita da kyau haha yarinya zan lakad'a miki na jaki wallahi"

"Uban wa zaiyi miki wanki?" wani saurayi ya fad'a haka yayin da ya shigo gidan.

Turo baki tayi wanda yaji jambaki har ya wuce bakin tace" *YUSUFA* kana takura min fa"

Da gudu ya bita nan ta shige d'akin Inna tana ihu ai da sauri ina ta dakatar da shi ta fito tsakar gida tana cewa" kai wani irin wawa ne har sai yaushe zaka bar goyon bayan yarinyan nan?"

Cikin zuciya yace" ba zan daina ba Inna dan ni banga abin da tayi muku ba da baku son ta"

Inna tace"Eh d'in ba mu son ta ka fita a ido na fa Yusufa karka manta da kai da *LANTANA* uwa d'aya uba d'aya kuke amma sai ka so wancan matsiyaciyar to ka kiyaye ni"

Cikin haushi ya kalla wanda aka kira Lantana yace" ni dai da ita da *UMMINA* na d'auke su k'anne nane ba wani banbanci"

Habawa ai nan ran Inna ya b'aci ta shiga massifa tana zagin Ummi shi dai Yusufa fita yayi a gidan. Ummi ba abin da take sai share hawaye.


****** ******


*Asalin* Ummi, malam Auwalu shine sunan mahaifin ta daga shi sai k'anin shi iyyayen shi suka haifa tun tasowan su sun sama tarbiya mai kyau har zuwa lokacin da suka girma inda su keyin noma kasancewar mahaifin su ba shi da hali sosai. sunan k'anin Auwal Rabi'u.

Lokacin da suka kai munzalin aure, baban su yace su fito da mata nan Rabi'u ya had'u da wata yarinya sunan ta LARAI(Inna) nan akayi auren su sai dai Auwal bai sama wace yake so ba sai bayan shekara biyu lokacin har Larai matar Rabi'u ta haifa d'a namiji mai suna Yusuf, nan ne Auwal ya had'u da wata wace yake so acan wani k'auye. yarinyar kyakyawa sunan ta AISHA tun bayan auren Aisha Auwal yake d'an samun arzik'i da gonar shi dan shi Rabi'u yasa wasa bai damu da aiki ba a wannan lokacin ne mahaifin su ya rasu bayan wata uku mahaifiyar su ita ma ta rasu. a gaskiya sun ga tashin hankali dan mutuwar ya shige su.

Tun bayan auren Auwal da Aisha har yau Allah bai ba su haihuwa ba. sai dai suyi ta addu'a , rana d'aya kwatsam dai Aisha ta sama ciki habawa ai ba k'aramin farin ciki suka yi ba nan ta cigaba da rainon cikin ta.

Lokacin da Larai taji Aisha na da ciki tayi bak'in ciki sosai dan ta tsane ta ba kad'an ba.ga shi a wannan lokacin ne Rabi'u ya had'u da mugayen abokai nan suka sa mai son kud'in yayan shi tunda shi ba shi da shi. aiko haka yazo yana ma yayan na shi hassada dan ko gidan shi bai zuwa da yake gidan su ba d'aya ba, shi ko Auwal bai san meke faruwa ba.

Bayan wata tara Aisha ta haifa yarinyan ta kyakyawa inda akasa mata suna UMMI. tunda aka haifa Ummi yaron Rabi'u yake son ta haka Yusuf zai zo gidan ya zauna dan yana son Ummi sai dai iyyayen shi basa so amma ba yanda za suyi.

A wannan lokacin Larai ta haihu ta sama mace aka sa mata suna Lantana tsakanin ta da Ummi shekara d'aya ne.


Ummi na da shekara bakwai iyyayen ta suka rasu sakamakon gobara da ya kama a gidan ba'asan ta ina wutan ya fito ba cikin dare abin ya faru dayake ranar sun je har k'auyen su Aisha to Ummi tace ita sai ta zauna acan nan suka bar ta dan suna son yarinyan sosai.

Kasancewar yarinya ce Ummi ba ta da wayau nan akayi sadakan bakwai da iyyayen Aisha suka tashi tafiya da ita ai nan Rabi'u yace bai yarda ba shi zai rik'e yarinyan dan'uwan shi ba dan sun so ba suka bar ta sai dan ba yanda za suyi. haka Ummi ta fara rayuwa dasu Larai(Inna) da Rabi'u(Kawu) a hankali ta gano ba iyyayen ta har ta fahimci sun rasu dan wani zuwa da kakan ta tayi ta fad'a mata.

Kawu ya dawo gidan baban Ummi da zama duk ya gaje dukiyan shi dalilin da yasa yace sai anbar mai Ummi kenan.

Haka Ummi ta fara rayuwan k'unci da takura a wurin Inna lokacin tana da shekara goma Inna taje gurin boka tace tana son a kasara ma Ummi rayuwa domin yarinyan Allah yayi ta kyakyawa samari na son ta dan gaskiya tana da kyau kamar ita tayi kan ta wai dan tana k'arama ma kenan ina ga kuma ta girma. nan boka yace ma Inna mai take son ayi ma yarinyan tace kawai so take a nak'asa mata rayuwa domin yarinyan ta lantana bata da kyau kowa Ummi yake so. nan boka yayi asiri ya turama Ummi aljanu suka rik'e k'afan wanda bata tafiya da kyau tana tafiya tana d'ingisawa ne. kowa yayi mamaki yarinya kyakyawa amma tana da nak'asa a k'afa. lokacin da kakan ta taji tazo dan ta d'auke ta sai dai Kawu da Inna sun hana dan sun san magani zatayi mata. haka nan ta hak'ura ta tafi tana kukan tausayin Ummi.


A yanzu shekaran Ummi goma shabiyar kyan ta sai fitowa fili yake duk da kasancewar ta mai kasara a k'afa ba k'aramin son ta Yusuf yake ba shiyasa yake kiran ta da *UMMI NA* wanda Inna na jin haushin sunan. suna gana mata azaba iri-iri dan ba ko da yaushe Yusuf ke gida ba dan son da iyyayen shi suka nuna mai ya b'ata shi dan yana bin masu shaye shayen nan tun bai sha har ya fara sha sai dai baya sata da neman mata sai dai yasha kwaya ya bugu yazo yana musu layi a gida sai ya kwana biyu baya gidan sai dai yana kula da Ummi dan wani lokacin saboda shi ake raga mata. tana zuwa makarantan boko da allo dan shi ya dage sai Kawu ya sata. ita kan ta Ummi tana son yayan nata Yusuf dan tana jin dad'in yanda yake kula da ita...




*TAKU A KODA YAUSHE*

*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป


๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *3*~*4*






Da missalin k'arfe 2:00pm, Ummi ce zaune a wani gefen titi da zai kai ki cikin garin katsina kasancewar Ummi suna cikin wani k'auye ne, shiru tayi tana tunanin irin massifan da zata sha yau gurin Inna Dan batayi ciniki Ba. Kamar zatayi Kuka take hi.



Wani mota mai shegen kyau ne ya wuce ta gaban su,kowa Sai da suka kalla Motan, amma Ummi ta Kasa kallo dan ba shine a gaban ta ba, mik'ewa tayi cikin d'ingisawa ta nufa hanyar gida. Wani mutum ne yayi saurin k'arasawa kusa da ita yace"sannun ki "

Kallon shi tayi da mamaki tace"yauwa"

Yace"lafiya naga kamar kina cikin damuwa ?"

Cikin muryan tausayi tace"banyi ciniki ba ne yau"

Cike da tausayin ta yace"to nawa ne gurasa? "

Tace"na murtala shida ne"

Nan yace ta juye mai duka sannan ya bata d'ari biyar taji tsoro lokacin da taga kud'in, nan yace ta rik'e canjin da farko tak'i Karb'a amma daya dage sai ta kar'ba tayi godiya ta wuce gida cike da murna.


Mutumin ko yana zuwa titi ya raba ma almajirai sadaka. Nan ya shiga had'adiyar motan nan yana cewa "Oga ta wuce"

Wani kyakyawan saurayi da yake gefe yana danna waya murmushi kawai Yaya.



Lokacin da ta isa gida Inna ba k'aramin farin ciki tayi ba da taga kud'i Mai yawa ba ruwan ta da ya akayi aka sama kud'in nan Inna ta zuba mata abinci ranar taci ta k'oshi.



Washegari ta fito zataje rafi dan d'ebo ruwa, dai-dai zata wuce taga wani ruwa a bokiti nan ta wuce tana tunanin ko waya aje ruwan shi haka nan dai ta wuce ta d'eba ruwan tana d'ingishi ta wuce, haka da zata yo icce taga an shirya shi a gefe sai dai bata d'auka ba dan bata san na wace ce ba .

Kussan kullum sai taga wannan ruwan da iccen tun tana tsoro har ta fara juyewa tana tafiya gida haka kuma kullum sai taga wannan mutumin kuma sai ya siya tallan da Takeyi.

Ranar ta fito gurin talla kawai sai ga mutumin nan. Yace mata zai tafi kuma da wuya su sake had'uwa kamar zatayi kuka dan har Sun saba da juna nan tayi mai godiya da irin yanda yake taimakon to, nan yake ce mata ai duk ba shine yake mata wannan taimakon ba Ogan shine har d'ebo ruwa da yin icce duk ogan shine ya sa Shi.

Nan ta k'ara mai godiya sosai , sannan yace zasu gaisa da ogan Shi,



Wani kyakywan ssurayi ne ya fito cikin hadad 'iyar motan nan cikin tafiyan k'asaita ya k'arasa gurin su, tun da take a rayuwar ta bata tab'a ganin kyakyawa irin shi Ba, nan ta gaishe Shi, da k'yar ya amsa sannan ta fara mai godiya juyawa yayi kawai ya bar gurin cike da tausayin yarinyan.

A zuciyar ta ko tunanin take shi kuma wannan haka Allah yayi shi ko magana bayayi .nan ta wuce gida.

Tana shiga gida taga Yayan ta Yusufa da murnan ta,ta isa gurin shi tana gaishe Shi, nan ya amsa yana cewa "Ummi na daga ina kike ne haka? "

Tace"talla naje, ko kasan mene ne?"

Yace"Aa sai kin fad'a Ummi na"

Nan ta gaya mai irin taimakon da wannan mutumin yayi mata, shi ma yaji dad,i nan yace zaiyi ma Inna magana kar ta sake d'ora mata talla dan ba ya so,


Washegari Ummi ce ke ta faman wanki dan tun safe bata zauna ba sai aiki takeyi gashi ko abinci yau bata samu ba, Lantana ce ta fito daga d'aki anci uban jagira da jambaki fuskar nan taji shar powder nan ta kalla Ummi a yatsine tace"ke dan ubanki ba cewa nayi ki goge min takalmi na ba kin tsaya kina wani wanki"


Ummi tace"kiyi hak'uri yanzu zanyi"

Wani irin wawan duka ta kai mata tana cewa" ai na Lura tun ba yau ba kike bak'in ciki da ni tunda na fiki massoya shegiya gurguwa kawai"nan taja tsaki ta wuce .

Ummi wani irin kuka ta fashe da shi jin yanda Lantana ta kira ta da gurguwa.


Inna ce ta fito tana faman massifa ita dai Ummi shiru kawai taxi.




Bayan sati biyu

Yau tallan alale ta fita da shi ta jima kafin ta sama wanda ya siya sauran ko har yamma ba wanda ya k'ara siya nan ta tashi tana tunanin irin massifan da zata she.

Dai-dai zata tsalaka titi sai ga wani mota yazo da gudu zaiyi kanta jefar da Bokitin tayi ta tsaya guri d'aya da k'yar ya taka birkin Motan saura kad'an Ya buge ta.


Kyakyawan saurayi ne black beauty cikin tashin hankali tare da rud'ewa ya karasa gaban ta yace"ina fatan ba abin da ya same ki?"

Cike da tsoro ta kalle shi amma ta kasa magana nan yace ta shiga motan ya Kai ta gida k'in yarda tayi sai wani d'an k'auyen su yace su tafi tare .

Har k'ofar gida ya kawo su sannan yace yana son ya gaida baban ta dan a gaskiya yana ganin ta yaji yana k'aunar to, wannan shine love at first sight, nan mutumin yace zai kira mai Innar ta, haka akayi lokacin da Inna tagan shi da wannan had'adiyar motan ai nan da nan ta rud'e ,

Bayan ya gaishe ta ya bata labarin abin da ya faru sannan ya d'auko kud'i masu yawa ya mik'a mata ai nan ta k'ara rud'ewa tayi godiya sannan tace"d'an samari banji sunan ka Ba? "

A hankali yace"suna na *MARWAN*"


Ta washe jajayen hak'oran ta tace"yo ai wannan sunan y'an birni ne,to madallah angode sosai"

Ta shige cikin gida Ummi ko na tsaye tana kallon ikon Allah nan yace mata"y'an mata ya sunan ki? "

Cikin sanyi tace"Ummi"


Murmushi yayi yace"wow nice name "nan yayi mata sallama ya taxi.



Shiga cikin gida tayi tana murmushi.......







*TAKU A KODA YAUSHE*

*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป


[16/11, 22:23] Hussaini Atk: ๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *5*~*6*


Bayan ta shigo cikin gida ne Inna ta Sata a gaba da tambaya wai wane ne wannan mai motar nan tace ki bata San shi ba amma duk da sai da tayi mata massifa wai to Idan ma son ta yake to ba zai yiwu ba,nan dai Ummi tasha kukan ta tashi dan ba mai bata hak'uri dan kwana biyu yayan ta Yusufa baya nan,


Bayan kwana biyu

Ummi taje rafi d'ebo ruwa tana dawowa taga wata mota Mai shegen kyau, tana shiga zauren gidan ta had'u da wannan saurayin wato Marwan Yana zaune akan tabarma, durk'usawa tayi ta gaishe shi sannan ta shige cikin gida,tana shiga Inna ta mik'e da sauri tace "yi maza kije ga mutumin nan kije ku gaisa"


Fuskar ta d'auke da mamaki ta kalle ta tace"Inna ni Kuma?"

Tace"yau naji y'ar banza wuce ki tafi"


Sumi-sumi ta fita, zama tayi daga gefen k'ofa ta takura kanta guri d'aya,


A hankali yace"Ummi ya kike"

D'agowa tayi da kanta suka had'a ido rass gaban ta ya fad'i da k'yar tace"lafiya Lau"

Nan ya dinga janta da fira tana amsawa da k'yar dan wani irin kunyar shi ta keji idan sun had'a ido kuma gaban ta ya fad'i,

Can ya kalle ta yace" Ummi kin min sata fa"


Mik'ewa tayi da sauri ta dafe k'irji tace" Ni kuma wallahi ban sace ma komai ba Allah sata ba Halina ba ne"

Murmushi yayi shima ya mik'e yace" kwantar da hankalin ki ba wani abu Kika sace min ba illa zuciya na"

Hannu ta d'aura a kai tace" na shiga uku nifa ba mayya ba ne" nan ta fashe Mai da kuka ,


Da sauri yace"No please Baki fahimce Ni bane yanzu kiyi shiru in fahimtar da ke"

Shiru tayi tana kallon shi Nan yace" abin da nake nufi shine tun ranar da na had'u dake Allah ya jarabce Ni da son ki, ina fatan zan samu guri a cikin zuciyar ki?"


Rufe idon ta tayi da gefen d'an yamutsatsen gyalen ta,

Murmushi yayi yace"zan baki lokaci kiyi tunani koh zan dawo bayan kwana biyu"

D'aga kai tayi kawai Nan yayi mata sallama ya fita, tana shiga gida Inna wace take musu lab'e tayi sauri tace" shegiya Mai ya Baki ko......."maganar tane ya katse lokacin da taga yara sun shigo da kaya nik'i-nik'i ai sai ta washe baki tana dariya ,kayan kwalliya da su biscuits da chocolates sai buhun shinkafa,dawa,wake da carton d'in su taliya ne,



Ba k'aramin murna Inna tayi ba a ranar Ummi ko mamaki takeyi wannan wani irin Mai kud'i ne haka, lokacin da Kawu ya dawo shima yayi murna ba abin da Inna ta ba Ummi ajiye ma Lantana ita ko Ummi ko a jikinta bai dame ta ba,


Lokacin da Yusufa ya dawo Nan Ummi ke gaya mai son da Marwan ke mata nan yace to ta yarda ta so shi kila shine zai taimake ta a rayuwa ,haka akayi kuwa lokacin da ya dawo ta amince da shi dan ba k'aramin mamaki tayi ganin ta gurguwa wanda take y'ar k'auye shi kuma gashi d'an birni amma yana son ta to meyasa ita zata k'i shi,


Soyyaya tare da shak'uwa Mai k'arfi ne ya shiga tsakanin Ummi da Marwan yayin da Lantana ke bak'in ciki haka Inna ma bata so ba sai dai Kuma tana samun kud'i ai haka ma kawu,



*Wane ne MARWAN*




Alhaji Musa balarabe shine mahaifi ga Marwan d'an kasuwa ne shi Yana da arzik'i su goma ne a gidan su shine na biyar yayi aure da matar shi Hajiya Hadiza tsawon shekara biyar da aure Allah bai ba su haihuwa ba rana d'aya kwatsam sai ta samu ciki habawa ai murna ba a magana UK suka tafi har sai da ta haihu Nan akasa ma yaro suna MARWAN. Sai bayan wata uku sannan suka dawo Nigeria,

Tun daga wannan lokacin basu sake samun haihuwa ba, A yanzu shekarar Marwan ashirin da hud'u ne kawai yaro matashi kyakyawa sai dai iyyayen shi sun b'ata shi dan komai yake so yana samu basa son b'acin ranshi ko kad'an suna bala'in son shi sun nuna mai gata gaskiya lokacin da ya gama primary school d'in shi UK ya tafi ya fara karatu wanda gaba d'aya bai maida hankali ba, ya had'u da abokai marasa tarbiya sun koya mai shan giya da neman mata har ya dawo Nigeria bai bari ba sai abin da yayi gaba, iyyayen shi basu hi dad'i ba ko kad'an ganin halin d'an nasu,


A wannan lokacin ne MARWAN ya had'u da Ummi dan shi d'an garin Katsina ne, tunda ya ganta ya kamu da wani irin son ta mai tsanani shi kanshi yana mamakin yanda akayi yake son yarinya k'arama,



*Cigaban labari*



Marwan ya sama iyyayen shi ya fad'a musu cewar ya samu matar aure Nan yake basu labarin Ummi sun tausaya mata sosai sai dai Kuma sunje tayi k'arama shekaru shabiyar gaskiya tayi yarinya sosai su kace ya hak'ura da ita ya nema wata, habawa ai Nan yace Sam bai yarda ba shi Ummi yake so, gannin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment