Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dage sosai " ya k'are da dariyan Wasa,

Cike da bak'in ciki ta bar gurin Jin abin da yace, Najwa ko godiya ta sake mai suka shiga gida,

Suna shiga bedroom Najwa tayi sauri ta bud'e d'an box d'in Nan Dan ya bata sha'awa, ko da ta bud'e sai taci karo da wani necklace da ring mai tsananin kyau, sai letter a ciki, samun kan ta tayi da warware letter'n dan tayi mamakin ko mene ne ya k'unsa, fara karantawa tayi kamar haka,

*Assalamualaikum*

*Ina fatan zuwa yanzu kin huta gajiya ko, a yau Ina son gaya miki abin da na Jima da birne shi cikin zuciya na, a yau zan gaya miki sirrin zuciya na, mu had'u a wajen parking lot bayan magriba,*


Cikin mamaki ta k'ara karantawa Nan take taji wani farin ciki ya ziyarce ta bata san Mai yasa ba, Yusra ce ta shigo nan Najwa ta mik'e dan shiga kitchen ta d'aura abincin dare , Yusra tace"Sister bari in bud'e inga me muka samu" Nan ta bud'e leddojin guda d'aya sweet, biscuits da su chocolates kala kala ne sai d'ayan doguwar Riga ne set uku sai perfume da flowers,

Yusra tace"sister kayan sunyi kyau ya Imran na ji dake fa" ta kashe Ido d'aya,

Tace" hmm...ki d'auki abin da yayi miki keda Aneesa bari inje in fara had'a dinner"

Godiya Yusra tayi sannan Najwa ta nufa kitchen, tana zuwa ta bud'e fridge ta d'auko nama ta gyara sannan ta d'aura tuwo da miyar kuka, cikin k'ankanin lokaci ta gama ta shirya a dinning table, sannan ta shiga toilet tayi wanka da alwala tana fitowa ta shirya cikin wani blue da touch d'in pink d'in material hijab a kai nan taji Mommy na k'wala Mata kira,da sauri ta fito ,

Tana shiga parlour Mommy tace" ke idan ba tsabar iskanci ba ya za'ayi kiyi tuwo kad'ai bayan kin san Aneesa ba suci?"

Tace" kiyi hak'uri Mommy Dan Allah,me za'a dafa?"

Aneesa tace"kiyi min indomie with eggs kawai Dan yunwa nake ji"ta fad'a cikin shagwab'a,

Yusra tace"Ni dai zanci tuwon Mommy"

Mommy tace"ke ai kamar daddy'n ku kike ni Kai na da bana ci amma sai da na fara ci" (da yake Daddy na son tuwo da daddare)

Najwa sai da tayi indomie'n ta kawo ma Aneesa daga Nan tayi sallan magriba ta fita wurin parking lot,

Tun daga nesa ta hango shi ba k'aramin kyau yayi Mata ba dan riga red and black jean yasa, cikin natsuwa ta Isa gurin, tana zuwa ta gaishe shi Nan yace ta zauna kan wani rubber chair dake gurin,

Kallon ta yayi da kyau sannan yayi murmushi yace" NAJWA"

Yanda ya kira ta sai taji wani yarr a jikinta dan bai saba Kiran ta da irin wannan yanayin ba, "Naam" shine abin da tace,

Yace" na Jima Ina son miki magana sai dai na Bari ne zuwa ki k'ara girma ki fahimci me zan gaya miki, wato Najwa zan gaya miki abin da ke adaban zuciya na, ba komai ke damuna yake sani cikin tunani ba illa son ki, tun ranar da na fara cin karo da wannan kyakyawar fuskar naki Allah ya jarabce ni da k'aunar ki"

Tun lokacin da ya fara magana taji gaban ta na fad'uwa tayi mamaki sosai haka Kuma ta shiga wani irin yanayi da bata sani ba, jin tayi shiru kusan 10 minutes sai ya numfasa yace" zan baki lokaci kiyi tunani a kan magana na, Kuma ina son kiyi min kyakyawar fahimta "

Wasa kawai takeyi da Yatsun hannun ta Dan bata san me za tace ba, ganin haka kawai sai ya kyale ta sukayi sallama ta shiga gida, tun lokacin da yayi maganar nan Najwa ke faman tunani ita dai bata sha'awar yin soyyaya yanzu Dan tun bayan ta rasa massoyin ta MARWAN ta cire batun soyyaya a RAYUWAR ta, sai dai Kuma wani gefe na zuciyan ta na cewa ta amince Dan gaskiya Imran Yana da kirki ga son mutane Kuma Yana kyautata mata mai zai hana ta so shi, Nan take taji wani irin son shi na shiga zuciyar ta ranar da k'yar tayi barci,


Washegari da safe, sauri_sauri tayi ta gama had'a breakfast ta shirya dan tafiya school Dan yanzu haka suna s.s.s 3 sun kusa fara jarabawar fita secondary,wanda haka sun kusa cika shekaru goma Sha takwas, kasancewar driver ke Kai su Nan ta shiga mota tana jiran su Aneesa,

Kusan 10 minutes ba su fito ba kamar Najwa tayi kuka dan sunyi late sosai,can taji muryan Yusra tace" kullum Aneesa sai kinsa munyi late wallahi zan fad'a ma Daddy"

Cikin massifa Aneesa tace"to uwar magana ai sai ki fad'a ni wallahi kin Raina ni Yusra zanyi maganin ki"

Har suka shiga mota suka isa school a mota sai rigima suke ita dai Najwa shiru tayi dan ita bata cika magana ba ga ta da kunya,


Bayan kwana biyu, Najwa ta rubuta ma Imran letter ta ba Yusra ta ba shi Dan ya dame ta yana jiran amsan shi, lokacin da yaga Najwa ta rubuta cewar ta amince ba k'aramin murna yayi ba, ai nan suka fara soyyaya,



Hajiya zulaihat ce tazo gidan yau suna zaune a parlour suna Hira da Mommy nan Mommy ta kira Najwa ta kawo ma Hajiya zulaihat drinks,tana fita Hajiya zulaihat ta kalla Mommy ,

Tace"ke Hajiya Aina'u haka yarinyan nan ta k'ara girma?"

"Hmm ke dai bari kawai wlh Habibi(da yake hk take Kiran Daddy ko a gaban yaran kunji iyyayen zamani) ya cuce Ni" cewar Mommy,

Hajiya zulaihat ta gyara zama tace"ai laifin ki ne ke kikayi sake ni har yaushe zan yarda ya kawo min wata kucaka y'ar talaka ta zauna a gida na cab ai ba zai yuwu ba"

Mommy tace" Nima dan ba yanda zanyi ne ya riga da ya gaya ma mama Kuma kinsan bazata yarda da Ni ba"


Tace"to ai shikenan kuskure dai kin riga da kinyi amma naji dad'in yanda kk mayar da ita y'ar aiki"

Tace" ai dole in mai da ta ke dai kawai na San mai zan dinga Mata"


Tafawa sukayi suna dariya Nan suka cigaba da fira,


A yanzu Kam soyyaya ce mai k'arfi a tsakanin Najwa da Imran duk da haka ta dage tana karatun ta Dan har sun fara jarabawar fita secondary School,


A yau ne sukayi final exam d'in su sai murna sukeyi, fatan su yanzu su samu results d'in su yayi kyau, abin da na lura shine Aneesa na bala'in son Imran shiyasa take kishi da yanda yake kula Najwa sosai, duk da bata san da soyyayan su ba Dan bai fito filli ba,


Yusra ko sa Najwa tayi a gaba da tambayoyi Dan ta lura kamar akwai abin da ke tsakanin ta da Imran, ganin cewan Yusra suna shiri sosai Dan har wasu sirrin su suna gaya ma juna nan Najwa ta gaya Mata komai, ai ko ba k'aramin farin ciki Yusra tayi ba,ta Kuma taya ta murna dan Imran akwai kirki ga kyau ga ilimi dan har yana lecturing a wani University , y'anmata dayawa na son shi amma ko kallon su ba yayi Dan Najwa ita kad'ai ce a zuciyar shi,








*Muje zuwa masu karutu*



*Taku ce*



*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป


๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *15*~*16*




*A yau ne* suke graduation, su Najwa na gani sunyi kwalliya sosai sunyi kyau inda suka sa less na riga da skirt milk and orange colour d'in kin yayi kyau daga gyale da takalma da jaka, komai iri d'aya sai dai Daddy ne yasa akayi musu dan Mommy bata yin Najwa komai sai dai Daddy idan ya sata dole tayi ko jaka da takalma Mommy sawa tayi akayi musu na su na mussaman Kuma Daddy yace sai anyi ma Najwa, ni ko nace Najwa y'ar gatan Daddy, haka suka jera suna tafiya a tare, anyi taro an watse inda aka ba ma Najwa gifts sosai har Imran ya zo gurin sukayi ta d'aukan pictures, sannan shi da kan shi Imran ya Kai su gida,


Da missalin k'arfe 9:10pm, Daddy ne zaune da yaran shi gaba d'aya Ana ta hira har da Imran dan haka Daddy yake ware lokaci na musaman yayi hira da iyyalan shi, can ya lura da ba Najwa a gurin Nan yace Yusra ta je ta kira ta, Mommy ko haushi taji ba kad'an ba,


Tana kitchen tana wanke kwanuka dan ita sai ta gyara ko'ina da daddare ba ta barin guri da datti, Najwa kenan sarkin tsafta mata muyi koyi da ita, nan Yusra ta fad'a mata nan ta bar aikin suka shiga parlour,

Gaishe da Daddy tayi sannan ta nema guri a k'asa kamar yanda sauran suka zauna a k'asa, Daddy yace"to Alhamdulilla Ina ma Allah godiya da yasa ku ka gama secondary School lafiya yanzu sai jiran results, Allah ya sa yayi kyau"


Duk suka ce Ameen, sannan Daddy ya cigaba da cewa" yanzu sai ku fad'a min abin da kuke son karanta?"

Aneesa tace"Daddy ni dai teaching nake son yi"

Yusra kuma tace" ni dai nurse nake son zama"

Daddy yace" to Masha Allah ke Najwa ba kice komai ba"

Tace" Daddy nima nurse d'in nake son zama"

Tsaki Mommy taja cike da takaici tace" yaushe zaki iya zama nurse"

Daddy yayi gyaran murya Mommy ta gane yana nufin tayi shiru ne sannan yace" dukan ku Nima Ina da burin ku zama nurses har ke Aneesa gara kiyi karatu da yan'uwan ki guri d'aya Dan haka ki hak'ura da yin teaching"

Aneesa ranta bai so haka ba sam, Yusra ko murna ta shiga yi har tana cewa"Daddy sai ka d'auke mu aiki a hospital d'in ka"

Dariya yayi yace" idan kun dage kun zama nurses kenan , ku shirya gobe driver zai Kai ku kuyi shopping ku sai abin da kuke so dan jibi za muje katsina kuyi hutu"

Murna suka dinga yi, Imran ko bai so ba ko kad'an Dan zaiyi nesa da massoyyiyar shi, Nan aka tab'a hira daga nan kowa suka nufa bedroom Dan yin barci,

Washegari da safe kamar yanda Daddy yace haka akayi sunyi shopping sosai Dan kowa sai da Daddy ya bata kud'i, a ranar da daddare ya kira su ya basu sabuwar waya Mai shegen kyau a kwali, ba k'aramin murna suka yi ba,Nan suka hau Kiran k'awayen su, Najwa ko Bata da k'awaye sai dai Wanda suke shiri, number'n IMRAN tasa a wayan ta kira shi,

Cikin mamaki ya d'auki wayan ganin bak'on number,

Cikin siririn murya tace" I hope you are not sleeping?"

Cike da mamakin Jin muryan massoyiyar ta shi yace" oh my love ke ce da gaske wayan wace ce wannan?"

Tace" Daddy ne ya siyo mana"

Cikin murna yace" Alhamdulilla Daddy kamar yasan abin da zanyi kenan cux bazan iya nisa da ke ba tare da naji sweet voice d'in ki ba"

Murmushi tayi tace" koh?"

Gyara kwanciya yayi yanda zaiji dad'in firan yace"yes my love ban tab'a son wata y'a mace ba sai ke a kullum addu'a na shine inga ranar da zaki zama Mata ta domin kullum buri na ki zama uwar 'yayya na, I really love you Najwa"

Murmushi tayi cikin farin ciki tace"Nima buri na ka zama miji a gare Ni Ina rok'on Allah ya nuna min ranar da zamu mallaki juna a matsayin ma'aurata"

Cikin farin ciki tace"Ameen my wife to be inshallah"

Nan sukayi ta soyyaya har sai da Imran yaji shiru sannan ya gane Najwa barci tayi murmushi yayi cike da k'aunar ta ya kashe wayan,

Washegari gaba d'ayan su suka d'auki hanyar Katsina state, basu suka Isa ba sai around 3:00pm gidan iyayen Daddy suka sauka, suna zuwa suka ci abinci sukayi salla sannan suka huta, sai washegari suka nufa gidan iyyayen Mommy,

Mama taji dad'in ganin su sosai,


Kwana biyu da zuwan su Katsina Daddy yace Najwa ta shirya harda su Mommy suje k'auyen su, Mommy tace ba inda zataje sai da mama ta sata a gaba taje, Aneesa ko ciwon k'arya ta fara Dan bata son zuwa,

Sun Isa k'auyen su Najwa, dai_dai k'ofar gidan kawu Daddy yayi parking, Mommy ko a wulak'ance ta shiga gidan,

Inna suyan Awara taga mutane sun shigo, tsayawa tayi cikin mamaki ta na kallon su, Najwa ce ta Kara'sa gurin ta tace"Inna baki gane ni bane nice fa Ummi"ta fad'a tana nuna kanta da hannun ta,

Inna kallon budurwan da ta kira kan ta da Ummi tayi tace" Aa ba Ummi ba ce wannan "

Najwa tace"nice Inna zo muje Kika Daddy nasan zaki gane shi" fita suka yi waje inda Daddy yake tsaye, cikin mamaki Inna tayi sallati tace"Alhaji Hafiz Kai ne ashe "

Daddy yace" eh wallahi Ni ne" da yake Daddy lokaci zuwa lokaci idan yazo Katsina Yana kawo musu ziyara,

Nan aka hau gaisuwa, Inna ta shiga dasu ciki suka zauna kan tabarma Wanda da k'yar Mommy ta iya zama a gefe tsabar k'yama da takeji,Nan Inna tasa wani yaro ya kira Kawu dake gona cewa yazo ga su Ummi(Najwa),


Lokacin da Kawu ya iso yayi farin cikin ganin su Nan aka hau gaisuwa, Inna ta jawo Najwa jikin ta tace"oh ni larai ashe Ummi ce na kasa gane ta su Ummi an girma"

Duk dariya akayi Banda Mommy dake gefe da takaici ya ishe ta, Najwa na mamakin yanda taga Inna naji da ita,abin da bata sani ba tun bayan Inna sun dawo birni take mugayen mafarkai gannin Najwa ta warke tana tafiya Normal ya girgiza ta sosai, mafarki Inna take ga Maman Najwa ta na zuwan Mata cikin mumunan shiga tana tsorata ta, tun lokacin take nadamar abin da tayi ma Najwa,shiyasa yanzu take son ta haka ma kawu shi Kuma indai Daddy yazo to sai yayi Mai alkhairi dasu buhun shinkafa, dawa wake har da kud'i,



Su Daddy sukayi musu sallama zasu tafi Amma zasu bar Najwa anan Yusra na Jin haka tace ita ma sai ta zauna, Mommy kamar tayi Mata duka Dan ita ko ruwan gidan tak'i sha,


Najwa da Yusra aka Bari akan zasuyi kwana biyu kawai,



*Taku ce*


*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป


๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *17*~*18*




*DEDICATED TO*

*UMMU BASHEER Fan's*๐ŸŒน

*ALK'AWARI Fans*๐ŸŒน

*RAYUWAR NAJWA Fans*๐ŸŒน

*AISHA ALI GARKUWA Fans*๐ŸŒน

*HAUSA NOVEL Part 2*๐ŸŒน

*MUNEERA HAUSA NOVEL*๐ŸŒน

*KHADIJATUL IMAN Fans*๐ŸŒน



*NOVEL GROUP*๐ŸŒน


*A gaskiya nayi tunanin in rubuta sunayen ku ne da to ganin sunayen suna da yawa idan na tsaya rubutawa to zamu k'arar da shafin ban fara labarin ba shiyasa na had'a dukan ku y'an group d'in Nan da na lisafo su a sama*

*Kai Kai Kai wallahi naji dad'i sosai massoyana domin a jiya kun sani cikin nishad'i nayi farin ciki ba kad'an ba nayi dariya sosai*

*Ummu basheer fans kun bani dariya Dan akwai masu wayau a cikin ku*๐Ÿ˜‚

*Aisha Ali Garkuwa da Muneera hausa novel grp tare da Hausa novel part 2 Ashe haka kuke k'auna na gaskiya naji dad'i yanda kowa take rubuta sunan ta Ina son ku sani ni UMMU BASHEER Ina k'aunar ku ba kad'an ba*๐Ÿ˜

*ALK'AWARI Fans gaskiya kun sani dariya sosai wata cewa take a sa sunan ta a farko kud'in da za'a raba a fara ta kan ta wasu rigima suke wata ko matar.... bari in shiru kar in tona ta nayi dariya ba kad'an ba*๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜

*Rayuwar Najwa fans ku din na daban ne domin naji dad'in yanda ake rububin rubuta suna, naji dad'i sosai*๐Ÿ˜

*Kar ku damu massoya na nayi muku wani tanadi mussaman saboda ku za ku ji shi Nan ba da dadewa ba*

*Ina godiya da yanda kuke son litafai na sosai ni UMMU BASHEER Ina k'aunar ku massoya na Allah ya bar zumunci da k'auna, kar ku damu ana mugun tare irin sosai din Nan*๐Ÿค๐ŸŒน






Bayan sun shigo cikin gida ne Najwa ke tambayar Inna Ina Lantana da Yusufa, Nan Inna ta bata labarin cewa ai Lantana tayi aure har da yaran ta biyu ta auri wani Mai kud'i Yana da mata uku ita ce ta hud'u sosai take Shan wahala a gidan Dan mutumin marowaci ne na k'arshe yaran shi goma Sha biyar tana wahala sosai,

Cikin tausayawa Najwa tace"Allah sarki Lantana anjima za muje mu gaishe ta"

Suna cikin hira sai ga Yusufa ya shigo gidan a guje ko lura dasu Najwa baiyi ba d'aki ya shiga ya fito da wata zabgegiyar ada, Inna na ganin haka ta rik'e hannun shi tana cewa" Kai lafiya mai zakayi da wannan?"

Cikin maganar y'an dabba yace" Su b'aleru da Iroro ne suka shigo yankin mu su nake inje in b'arar da su dan uwatar yiiiii hu hu" ya saki wani ihu irin nasu na y'an dabba,

Inna da sauri tace" ba ka ga Ummin ka bane?"

Sororo yayi Yana kallon ta,Nan ta nuna mai su Najwa da ke zaune cikin tsoro, k'arasawa yayi ta gefen Najwa yana cewa" wallahi ita ce wannan UMMINA ne"

Najwa tace" ya Yusuf ashe zaka gane Ni?"

Yace" yo ba dolle in gane ki ba,kina tunanin zan manta da ke ne Ummi na,Ina ai har abada wallahi"

Yusra ta gaishe shi, sannan suka cigaba da hira cikin nishad'i can cikin wasa Najwa tace" ya Yusuf ka fasa fita ne Naga fita zakayi ai?"

Da sauri yace" haba tuni ma su d'in banza bayan ga ki Ina zanje"

Tace"gaskiya ka daina irin wannan fad'an *YAYA NA* "

Da sauri yace" mai Kika ce k'ara fad'a in ji?"

Dariya tayi tace" Yaya na "

Mik'ewa yayi cikin farin ciki ya fara kirari" Wa yace da kai ba Kai ba sai ni Yusufa na Ummi na ba da kan ka a sare kaje gida kace ya fad'i eyiiii huuuu huuuu" yanayi ne yana Wasa da adan shi,

Duk dariya sosai suka dingayi,ranar Yusuf ya nuna Mata gata dan tsire da yoghurt ya kawu, washegari sukaje gidan Lantana,taji dad'in ganin su sosai gidan ba laifi Yana da d'an kyau ama duk ya lalace da k'azan ta , haka suka yini mata,suka tafi,

Washegari Daddy ya turo driver aka d'auke su Yusuf kamar kar ya rabu da Ummi ya ke ji,

Daddy sun koma Kaduna inda suka bar su Najwa su k'ara hutu, aiko sun ta zagaye gidan Yan'uwa sunje gidan k'anwar su Daddy Mami ake ce Mata, tana da kirki sosai da son mutane shiyasa lokacin Bata shiri dasu Mommy da Umma(Hajiya zulaihat mamansu Imran)

Satin su biyu gidan Mami Daddy yayi waya driver zai zo ya d'auke su Dan results d'in su ya fito, Mami na son Najwa sosai haka tayi musu kyauta sosai suka d'auki hanyar Kaduna,


Sun Isa Kaduna lafiya, ranar Najwa ta Sha aiki Dan Mommy sai da tasa tayi Mata kwaleman bedrooms da parlour,sai dare ta samu kanta ga wani irin barci da takeji gashi tayi missing d'in Imran, haka ta shirya suka had'u a wurin parking lot suka Sha hira da soyyaya,

Daddy ya Samar musu NURSING SCHOOL, Dan yafi son su fara karatu kafin aure idan yaso sai su Kara'sa a d'akin mijin su,

Wata biyu kenan da suka fara zuwa Nursing school, ga wani irin soyyaya dake tsakanin Najwa da IMRAN, Dan yanzu shi yace Mata zai sanar da Daddy Dan Yana son ayi auren su, Najwa dai tana Jin kunya Kuma tana tsoron Mommy da Umman shi Dan basa son ta,


Bayan Daddy ya dawo aiki ya gama duk abin da zaiyi sai Imran ya shigo parlour'n dake upstairs (da yake upstairs din babban parlour ne sai can gefe bedroom d'in Mommy sai Kuma bedroom d'in Daddy ta left hand kuma wani corridor ne)

Shigowa ciki yayi ya gaida Daddy suka d'an yi hira can Kuma sukayi shiru suna kallon news, kusan 30minute Daddy ya lura akwai abin da Imran yake son gaya Mai Dan haka yace"Imran kana son magana da Ni ne?"

Cikin kunya yace"eh Daddy dama.....uhm...in...kawai ba komai"

Daddy murmushin manya yayi yace" don't feel shy just tell me, wace ce kake so?"

Cike da mamaki ya kalla Daddy sai Kuma yaji kunya yace"Wallahi Daddy na Jima Ina son ta Kuma mun Riga da mun dai_dai ta kan mu shine nace Bari inzo in fad'a maka Dan wallahi Daddy son ta nake da aure"

Murmushi Daddy yayi yace"Alhamdulilla haka nake son ji dama Ina son gaya maka ya Kamata ka fito da Mata kayi aure, to yanzu kaga yazo a dai_dai Dan haka wace ce yarinyan Dan mu nema maka auren ta?"

Cikin fad'uwan gaba yayi shiru har sai da Daddy ya maimata sau uku sannan yace" Daddy Dan Allah kar ki hana ni ita "

Cikin mamaki yace" kamar ya ka fad'a min wace ce?"

Da k'yar ya tataro natsuwar shi yace" Najwa nake so Kuma wallahi auren ta nake sonyi Daddy"

Daddy ba k'aramin murna yayi ba yace" Kai Amma naji dad'i sosai Imran Allah yayi maka albarka domin nasan zaka kular min da Najwa sosai ko bayan Rai na,Dan buri na *RAYUWAR NAJWA* tayi shi cikin farin ciki ba tare da damuwa ba"

Imran yaji dad'in maganar Daddy yace" nayi maka *ALK'AWARI* *RAYUWAR NAJWA* zai zama RAYUWAR farin ciki"

Nan sukayi ta hira cikin nishad'i Daddy yace zai ma Abba(mahaifin Imran) magana ,

Washegari Daddy yaje gurin yayan shi Abba, ya gaya mai komai, shima yaji dad'i sosai Nan suka sa ranar da za suje k'auye gurin Kawu Dan neman iri,

Lokacin da Imran ya fad'a Mata yanda sukayi da Daddy tayi farin ciki amma Kuma tana cike da tsoro idan Mommy suka ji,

Bayan kwana biyu Daddy da Abba tare da wasu aminan su sukaje k'auye inda Kawu ya tarbe su cikin mutunci sannan akayi magana Kawu Kuma ya amince inda ba tare da b'ata lokaci ba aka sa ranar aure wata d'aya, Dan ashirye suke Kuma Daddy shi zaiyi ma Najwa komai na kayan gida,

Lokacin da Daddy ya dawo ya sanar da Imran abin da ya faru cewa ansa ranar d'aurin aure,ba k'aramin farin ciki yayi ba Imran burin shi ya kusa cika,bayan Daddy yayi wanka Yana Shirin barci yace ma Mommy zasuyi magana,

Kallon shi tayi tace ya gaya mata, ai ko Nan ya fad'a Mata komai, wani irin zabura tayi tace"Habibi bana son irin wasan Nan fa please ka daina"

Gyara kwanciya yayi yace"ok kinsan akwai auren Wasa ai"

Zaro Ido tayi ta mik'e tsaye tace" kana nufin Imran zai auri Najwa, cab wallahi sai dai a mafarki Dan ba zai tab'a yuwuwa ba sam"

Zama yayi cikin b'acin rai yace"ke wata iri ce ke da zakiyi musu fatan Alkhairi Amma sai kice haka to sai ki hana yuwur haka" ya koma ya kwanta,

Cikin b'acin rai tace"ai ko zan hana wannan ya zama dole ma wallahi Dan hanyar jirgi da ban na mota da ban "

Daddy barci yayi ya k'yale ta tayi har ta gaji ta kwanta,


B'angaren Abba ma hakan ne ya faru Dan lokacin da ya fad'a ma Umma ta razana sosai haka tayi ta bala'i da su zagi tace Kuma zata ga ya za'ayi auren,



Bayan su Daddy sun tafi Kawu ya fad'a ma Inna abin da ya faru ai ko tayi farin ciki, abin da basu sani ba Yusuf ya shigo gidan Kuma ya ji Mai suka ce, Dan haka cikin fushi ya shigo yace" wai mai kuke cewa ne akan Ummi na, to wallahi kunyi kad'an ku aura ma Ummi na wani domin Ummi tawa ce Ni kad'ai" ya fita daga gidan cikin fushi,











*Lalai akwai chakwakiya kuci gaba da bina Dan warware muku wannan chakwakiyar*




*Taku ce*


*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป

๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment