Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda ya dage hankalin su ya tashi sai suka hak'ura, Nan baban shi suka tafi k'auyen su Ummi domin neman sure,



Kawu lokacin da suka gabatar Mai da kansu yaji dad'i domin yace idan ta auri Mai kud'i ya tabbata shima yayi kud'i Dan haka Nan ya amince, aka sa ranar aure wata uku ,

Da Inna taji sai da sukayi fad'a da Kawu Dan tace bata yarda ba dan bata son Ummi tayi aure balle Kuma ta auri Mai kud'i bayan ita ga nata yarinyan batayi aure ba, sunyi fad'a sosai dole ta hak'ura Dan ba yanda zatayi,


A cikin watanin Nan Marwan ya canza halin shi dan Yana son Ummi bai son b'acin ranta kar suyi aure bai canza ba shiyasa ya daina ,iyyayen shi ba k'aramin murna sukayi ba lallai Ummi alkhairi ce a gare shi,



Cikin ikon Allah bikin su Ummi saura sati biyu yanzu, Yusufa ya rasa Mai ke damun shi dan baya son rabuwa da Ummin shi amma ba yanda zaiyi sai hak'uri, Lantana ko kamar zata mutu dan haushi da bak'in ciki,



A wannan lokacin ne Umman Marwan tace yakamata ya kawo mata surukarta Ummi kafin ayi bikin Dan su gaisa, to bayan yaje k'auyen ne yake sanar da ita nan Kawu ya amince suje,


Biki saura sati d'aya a lokacin , Ummi ranar duk ta rssa Mai ke damunta gaban ta sai fad'i yakeyi, yinin ranar ta kasa cin komai Dan dangin mahaifiyar ta sunzo yanzu ta rage wahala Dan tuni ta daina talla tunda Marwan Yana ba Inna duk sati kud'i yace baya son tallan,


K'arfe 11:30pm Marwan yazo k'auyen nan yace Ummi ta shirya, ba tare da b'ata lokaci ba k'anwar mahaifiyar ta tashirya ta cikin shada doguwar Riga sai d'an hijab d'an dai-dai,

Lokacin da ta fito haka Marwan yayi ta d'aukan ta pictures Dan ba k'aramin kyau tayi ba duk da cewa tana d'ingishi, Nan suka d'auki hanya sai cikin garin Katsina,


Dai-dai sun shigo cikin garin wani babban mota ya shigo ta gaban su, cikin rud'ewa da tashin hankali Marwan yayi k'okarin kauce ma motar sai dai ina hakan bai yuwu ba sai da motan yabi ta kansu,












*Taku a Koda yaushe*


*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป
[17/11, 19:16] Hussaini Atk: ๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *7*~*8*



*Dedicated to Rahmat Muhammad Rufa'i Nalele*




*Ina rok'on Allah ya k'ara Miki basira tare da k'warin ido,Allah ya Kare ki daga sharin makiyya da mahassada Ameen sosai nake yin ki tawan ina godiya sosai, Allah ya bar kauna tare da zumunci I love u wujiga wujiga*๐Ÿ˜






*Lokacin* da wannan babban motan ta bi ta kansu motan ya kufce ma Marwan nan motan ya bugi wata bishiya, cikin hanzari gurin ya cika da mutane aka fara k'okarin bud'e motan ,


Wani mota ne yayi parking a gefe, babban mutum ne ya fito daga ciki da sauri ya k'srasa gurin inda aka ciro Marwan da Ummi wanda sukayi gaja gaja da jini cikin hanzari mutumin Nan yace asa su cikin motan shi sannan wasu suka bishi ,

Wani Hospital suka shiga batare da b'ata lokaci ba aka nufi Emergency da su cikin gagawa aka hau bincikar lafiyan su, wannan mutumin ya nuna ma doctor's d'in Card d'in shi ashe cikaken likita ne, bayan awa 1 aka fito da su inda aka kai Ummi d'akin hutawa, gani nayi sun fito da Marwan wanda daga k'afar shi har fuskar shi a rufe yake, Inna lillahi wa'ina illaihir raji'un nace, wani doctor ne ya karb'a wayan da aka gani a motan Marwan nan ya bincika sunna yaga ansa Abba na kawai ya kira number'n yace suzo hospital ga yaron su,


Cikin tashin hankali su Abba suka zo hospital d'in ganin Marwan ya d'aga musu hankali, Nan doctor ya sanar dasu cewan Marwan ya rasu sakamakon firgicin da ya shiga kuma kanshi ya bugu sosai dan tun kafin a kawo shi ya rasu,! Jin abin da doctor yace kawai sai Maman shi ta yanke jiki ta suma, cikin rud'ewa Abba ya kinkime ta aka yayafa mata ruwa kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita, Abba ne yayi jarumta ya Isa gurin gawan Marwan lokacin da ya bud'e shi sai da ya kusa fad'i Dan ya shiga cikin firgicin mai tsanani, cikin kuka mama ke tambayar ina Ummi take,


Nan aka kaisu d'akin da take, cikin tausayawa suka kalle ta, wani ikon Allah kujewa kawai tayi a hannun ta, daga suka d'auki gawan Marwan suka nufa gida domin ayi Mai sututa a kai shi gidan shi na gaskiya, (Allahu Akbar dukan Mai rai sai ya d'andani mutuwa Allah kayi Mana cikawa da imani,Ameen)




Bayan awa uku, Ummi ce ta motsa a hankali ta fara bud'e idon ta tana kallon d'akin da take ,idon ta ne ya sauka akan wani mutumi wanda yake zaune a kujera a gefe, da sauri ta mik'e zaune cikin firgicin zata sauka gadon, da sauri mutumin nan ya rik'e ta Yana cewa" yi hak'uri kar kiji ciwo ki zauna"


Kallon shi tayi cikin hawaye tace" ina Marwan ina ne Nan gurin?"

A hankali yace" kina hospital ne kuma ni doctor ne"


K'ara maimaita mai tayi cewan ina Marwan, Nan ya fara kwantar mata da hankali tare da nasiha Mai ratsa jiki sannan ya gaya Mata wanda aka kawo su tare wato Marwan ya rasu, wani irin kuka ta fashe da shi, barin ta yayi tayi kuka sosai duk da bai san wane ne nata ba amma ya tausaya mata,


Ta d'auki lokaci tana kuka sannan tayi shiru ta na ajiyar zuciya, sannan tace tana son ganin Marwan d'in, hak'uri ya bata dan yana tunanin har an kai shi gidan shi na gaskiya, Nan yace yana son Jin labarin *RAYUWAR TA* ? cikin kuka ta fara ba shi labarin ta domin lokaci d'aya taji ta yarda da mutumin,


Lokacin da ta gama bashi labarin RAYUWAR TA ya tausaya mata nan ya k'ara mata nasiha jikinta sai yayi sanyi , lokaci d'aya yaji yarinyar ta shiga ranshi kamar yarinyan da ya haifa, nan ya fita d'akin da su Abba da Kawu sunzo sosai suka gaisa ashe da mutumin da Abba sun San juna Nan dai Mutumin ya tafi cike da son ya taimaka ma yarinyan, su Abba suka shigo d'akin sukayi mata nasiha sannan aka sallame ta suka nufa gidan Abba,


Bayan kwana bakwai, a gaskiya Ummi ba k'aramin shak'uwa tayi da Marwan ba Dan sosai take kewar shi amma sai dai tayi ta mai addu'a, a wannan lokacin ne wannan mutumin ya dawo ya samu Abba da maganar son taimakon yarinyan, Abba yaji dad'i Sosai dan shima Yana tausayin yarinyan, Nan suka nufa k'auyen su Ummi dan neman izinin Kawu ya ba ma wannan mutumin mai sunna Alhaji Hafiz Idris, rik'on Ummi,



Bayan sun Isa k'auyen be suka had'u sukayi magana da Kawu cewan Alhaji Hafiz yana son ya rik'e Ummi kamar yarinyan shi, lokacin da Kawu yaji ai ba k'aramin dad'i yaji ba dan ya gaji da ganin Ummi da yana murna da zatayi aure to ga shi mijin ya rasu yana tunanin ya zaiyi da ita, da sauri ya amince musu, su kansu sunyi mamaki da ya yarda da sauri haka, Nan ya fito yana sanar da Inna habawa ai ina wuta ta saka Ummi Dan bak'in ciki, haka ta fara ma kawu masiffa wai bata yarda ba yace Aiko bata isa ba ya riga da ya bada Ummi, haka tayi ta massifan ta ko kula ta baiyi ba yace Ummi ta shirya kayan ta nan ya fad'a mata komai, duk da bata hi dad'i n yanda za'a bayar da ita ba ko dan iyyayen ta sun rasu ne shikenan ita bata da gata, ga Mai son ta ya rasu ya barta Nan tayi ta kuka sannan ta shirya y'an kayan ta Wanda duk Marwan yayi Mata ne,


Lokacin da ta fito zasu tafi Alhaji Hafiz yayi mamakin ganin Ummi na d'ingishi Nan ya kalla Kawu yake tambayar shi Nan ya bashi labarin cewa Rana d'aya kwatsam suka ga tana d'ingishi, girgiza kai kawai yayi cike da tausayin yarinyan,



Nan suka shiga mota suka d'auki hanyan Katsina,





*Allah sarki Ummi*๐Ÿ˜ญ



*Taku a Koda yaushe*

*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป


๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *9*~*10*









*Lokacin* da suka Isa cikin garin Katsina direct wani gida Mai shegen kyau suka nufa, bayan yayi parking ne suka shiga wani parlour, wata tshohuwa ce hakimce akan kujera, Kara'sawa Alhaji Hafiz yayi Yana cewa" barka da hutawa mama"

"Yauwa kun iso barkan ku" ta fad'i hakan tana mik'ewa tsaye,


Da sauri Ummi ta gaishe ta amsawa mama tayi tana tana Jan ta jikinta jikin kulawa tace" saki jikin ki ki d'auke Ni kamar kakan ki"

Nan ta kira Mai aiki ta kawo drink's da abinci, sannan tace ma Alhaji Hafiz "ya sunnan jikan tawa?"


Yace"sunnan ta *NAJWA*"


Da sauri Ummi ta kalle shi tana mamakin sunnan da ya kira ta da shi, amma sunnan akwai dad'i,

Mama tace"Masha Allah sunnan Mai dad'i yanzu zaku wuce Kaduna kenan?"

Yace" Inshallah "

Nan tace" to agaida iyyalin"

Yace"za suji"


Bayan sun gama ne suka d'auki hanyar Kaduna, anan ne yake fad'a ma Ummi cewan ya canza mata sunna zuwa *Najwa* , da missalin k'arfe 8:00pm suka shiga garin Kaduna, wani unguwa suka shiga gidaje ne masu kyau ne a unguwar da gani unguwar masu kud'i ne sosai, a k'ofar wani gida taga sun tsaya inda maigadi ya bud'e tangamemen gate d'in shiga motar yayi sannan yayi parking, kasancewar dare ne street light ya haskaka gidan, Wasu kyakyawawan y'anmata ne suka fito ta wani k'ofa cikin shigan doguwar Riga wow sunyi kyau, Kara'sawa sukayi gurin motan suna mai barka da dawowa ,

Fitowa yayi daga motan Yana cewa" Aneesa da Yusra ga y'ar'uwa na muku" ya nuna NAJWA (Ummi) dake fitowa


Aneesa ce ta kalle ta cikin k'yama tace" Daddy yar'uwa kuma?"

Yace" eh ku mu shiga cikin gida zan gaya muku ko wace ce"

Da sauri Yusra ta rik'e hannun Najwa suka shiga ciki, wata Mata ce kyakyawa ta fito daga kitchen tana cewa" oyoyo Habibi ya....." maganar ta ne ya katse lokacin da taga Najwa,

Cikin mamaki da k'yama tace" Ina kuma ka samo wannan almajiran?"

Girgiza kai yayi yace" ba almajira bace bari in huta zan Miki bayani, ke Aneesa ku shiga da ita bedroom d'in ku ta huta Yusra ki bata kaya ta canza" Nan ya hau upstairs,

Yusra ce taja ta zuwa bedroom d'in su, wow nice domin bedroom d'in ya had'u komai na ciki red and pink ne kowa ce da side d'in gadon ta da wardrobe, sakin baki kawai Najwa tayi Dan bata tab'a ganin gida mai kyau irin wannan ba a gefe ta ajiye jakan ta Nan Aneesa tayi ball da shi cikin massifa tace" ke wace ce to ni wlh ba a bed na Zaki kwana ba k'azamiya kawai mttwwss" tayi tsaki,

Yusra tace" haba Aneesa Mai yasa zakice haka?"

Cikin fushi tace" shut up ke ta kwana a bed d'in ki mana" Nan ta fita waje,

Yusra ta kalli Najwa tace" kar ki damu please muje kiyi wanka ki huta" ita dai ba tace komai ba Nan Yusra ta kai ta toilet anan fa aka sha k'auyenci dan sai da Yusra ta koya mata komai a hakan ma da k'yar ta iya wanka, Yusra ce ta bata wani night gown tasa sannan suka kwana a bed d'aya,


Bayan Daddy(Alhaji Hafiz) ya gama Shirin say nan ya kalla matar shi Wanda ta k'osa yayi mata bayanin wace ce yarinyan nan,

Ba tare da b'ata lokaci ba yayi mata bayanin Najwa daga lokacin da ya kaisu hospital har zuwa yanzu sannan yace" Ina son in rik'e Najwa kamar su Aneesa Ina son ta samu ilimi da gata tare da tarbiyya domin *RAYUWAR NAJWA* abin tausayi ne ina son ki rik'e Najwa kamar y'ar da Kika haifa"

Mik'ewa tayi cikin zafi tace" wallahi bazan yarda ba ya za'ayi ka d'auko min wata y'ar k'auye kace wai zamu rik'e ta idan taimakon ta za kayi ka basu kud'i mana"

Shima mik'ewa yayi yace" na rigada na yanke hukunci Kuma munyi magana da su Mama" d'aukan wayan shi yayi ya kira mama ya mik'a mata,

Karb'a tayi nan Mama tayi mata fad'a tace kuma dole Najwa ta zauna a gidan, ciki asanyaye ta mik'a mai wayan ya riga da ya gama da ita tunda ya had'a ta da mahaifiyar ta, wucewa bedroom d'in ta tayi cikin fushi,


Washegari da safe, bayan sun tashi ne Yusra tace ma Najwa tayi wanka ta shirya Nan ta bata wani riga da skirt na atamfa brown colour wow kamar ba ita ba nan suka fito dining table danyin break fast,

Cikin girmamawa ta gaishe da Mommy da k'yar ta amsa mata, suna cikin break fast sai ga wani kyakyawan saurayi fari mai d'auke da saje a fuskar shi bazan iya fasalta muku shi ba amma guy d'in k'arshe ne a kyau, k'araso yayi gurin dining ya gaishe da su Daddy sannan su Aneesa suka gaishe shi, nan Daddy yace yana son sanar da su wace ce Najwa, ya basu labarin ta sannan yace su rik'e ta kamar yar'uwan su, amsa Mai sukayi, bayan sun gama break fast ne suka dawo parlour Nan saurayin Mai sunna *IMRAN* ya dinga fira da k'anen nashi Dan shi mutum ne Mai fara'a da was da dariya,



*Wane ne Alhaji Hafiz?*



Alhaji Hafiz Idris mutum ne Mai arzik'i Yana da kirki da son jama'a ga kyauta da tausayin talakawa, su uku iyyayen shi suka haifa babban su shine Alhaji Abdullah sai shi Alhaji Hafiz sai k'anwar su Hauwa'u , Alhaji Hafiz yayi karatu inda ya zama babban doctor Alhaji Abdullah Engineer ne, Duk atare sukayi aure, Alhaji Hafiz ya had'u da Aina'u (Mommy) Nan suka fara soyyaya daga nan sukayi aure iyyayen Aina'u baban ta d'an Nigeria ne Maman ta kuma y'ar Indian ce sana'a yakai baban k'asar India har suka had'u da k'yar iyyayen suka yarda ya aure ta har ya kawo ta Nigeria, Aina'u tana da yayye maza ne ita kad'ai ce mace, bayan auren ta da Hafiz sai da ta shekara biyu Bata haihu ba yayin da matar Abdullah ta haifa yaro namiji mai sunna *IMRAN* Aina'u na son yaron sosai Dan akwai ta da son yara Kuma matan Abdullah ta sake samun ciki sunnan matar Hajiya zulaihat, Nan suka ba ma Aina'u yaron ta cigaba da rainon shi , rana d'aya kwatsam sai ta samu ciki bayan wata Tara ta haifa yaron ta Mai Kama da baban shi ranar sunna yaro yaci sunnan *ASEEM* , Kai Mommy na bala'in son ASEEM tana ji da shi Bata k'ara samun ciki ba sai bayan Aseem nada shekara takwas sannan ta haifa Aneesa bayan shekara d'aya ta haifa Yusra, tsakanin su shekara d'aya ne,

Mommy mace ce Mai son kud'i tare da k'yamatar talaka gashi wayayiya ce tana zuwa aiki Dan tana da Company'n had'a jaka da takalma, duk cikin yaran ta tana son Aseem Bata son abin da zai b'ata Mai rai ko kad'an,

ASEEM saurayi ne kyakyawan gaske fari ne Yana da fafad'an k'irji Kuma Yana da tsawo dai dai shi Kai Aseem giant ne, yayi primary and secondary School daga Nan ya tafi U.S.A karatun soja Dan Yana son zama soja, muskili ne na k'arshe amma idan ya had'u da Mommy shagwab'a yake Mata Dan shima fa Yana k'aunar mahaifiyar shi,

Aneesa tana da wulak'anci Bata son talaka kamar mahaifiyar haka take, yayin da Yusra take da son mutane kamar mahaifin ta,





*. Wannan kenan*






*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป


๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *11*~*12*



*Dedicated to UMMU BASHEER Fan's*



*Sosai nake k'aunar ku massoya na Allah ya bar mu tare Ina muku fatan alkhairi a rayuwar ku a duk inda kuke*






*Bayan* kwana biyu Mommy ta kira Najwa ta kafa mata dokan ita zata dinga duk aikin gidan har girki, da yake Mommy na da wata tshohuwa mai mata girki Kuma ta iya sosai nan Najwa ta fara koya a gurin ta haka aikin gida baya mata wuya Dan ta horu a k'auye, tsakanin ta da Yusra ko suna shiri sosai amma kullum Aneesa cikin hantaran ta take da gaya Mata bak'aken maganganu ita dai Najwa shiru kawai ta keyi,


A wannan lokacin ne Daddy ya kai Najwa babban hospital d'in shi aka fara bincikar lafiyan k'afan Najwa, likitoci sunyi k'okari wurin ganin sun gano abin da ya sama k'afar sai dai babu abin da suka gani, kawai sai ya tafi da ita Katsina gurin iyyayen Mommy dan akwai wani kakan Mommy malami ne sosai na addini, ba tare da b'ata lokaci ba kakan ya gano cewa asiri ne akayi Mata a k'afar nan ya bada wasu magunguna, ta d'auki tsawon sati biyu a gurin kakan Yana mata magani,


Bayan sati uku a wannan lokacin ne Daddy yazo Katsina inda yaga Najwa ta warke sosai dan tana tafiya Normal yanzu bata d'ingishi (nace Alhamdulilla) Daddy yayi farin ciki sosai haka Najwa taji dad'i sosai, nan suka koma Kaduna,

Bayan sun dawo gida Mommy tayi mamaki da taga Najwa na tafiya Normal duk da Daddy ya fad'a mata zai Kai Najwa ayi mata magani, Aneesa ma haushi taji wai akan Mai Daddy zai nema mata magani, Yusra da Imran ba k'aramin farin ciki sukayi ba ,


Ganin Najwa ta k'ware a girki da gyaran gida Dan bata da Wasa, shine Mommy ta sallama tshohuwar Nan Mai aiki wai Najwa zata dinga komai, Yusra kan taya ta wani lokacin duk da Mommy na hana ta, Aneesa ko ba abin da ta iya Dan bata son aiki ko kad'an,


Daddy yasa Najwa a school d'in su Aneesa dayake shekarun su d'aya haka aji d'aya suke duk da Aneesa ta girme su aji d'aya suke Dan bata da k'okari ko kad'an, haka Islamiyan su d'aya inda Najwa ta dage ta Mai da hankalin ta gurin karatu, Allah yayi ma Najwa basira brain d'in ta na caji sosai wani lokacin ita ke koya ma Yusra karatu ita ko Aneesa girman kai tak'i yarda, yanzu haka sun shiga s.s.s 1, yayin da suke cikin shekara na Sha shida, Aneesa kuma na sha bakwai,



IMRAN tun lokacin da ya had'u da Najwa Allah ya jarabce shi da son ta, sai dai bai fad'a mata ba amma yana nuna Mata alamun so kuma Yana kyautata mata, ita ma tana ba shi girma Kuma tana Jin kunyar shi,

Bayan wani lokaci ne su Inna da Lantana suka zo ganin inda Najwa take, kuzo kuga k'auyenci sai zuba shi suke , ba k'aramin razana Inna tayi ba da taga Najwa na tafiya dai-dai, Mommy bata wani kula su ba har suka tafi, Yusuf ko yayi farin cikin ganin Ummin shi cikin daula ba wahala a tare da ita Nan ya tafi cike da kewar ta yanzu jira yake ta gama makaranta suyi RAYUWAR farin ciki, (ni Ummu basheer nace mai kake nufi?) , Lokacin da su Inna suka koma k'auye haka Lantana tasa Inna a gaba da kuka wai ita wallahi bazan ta yarda ba ya za'ayi ace Najwa ta warke Kuma tana gidan masu kud'i ita sam Bata yarda ba, haka dai Inna tayi ta bata hak'uri,

Can ta kalla Inna tace" gaskiya ni ki nemo min mai kud'i in aura dan bazan aura talaka ba"

Inna cikin lalashi tace" yo ai ya zama dole in naimo miki dan kiji dad'in RAYUWAR ki"

Cikin murna ta rungume Inna tana farin cikin ita ma zata auri Mai kud'i,



Najwa ce a kitchen tana wanke_wanke mistakenly glass cup d'in da take wankewa ya fad'i k'asa ya fashe, Mommy ce ta shigo ganin ta'asar da Najwa tayi mata Nan ta rufe ta da fad'a cewa take" Ke kina hauka ne da kika fasa min glass cup ko uban ki ne ya siya idiot kawai" taja tsaki,

Najwa ta durk'usa tana bata hak'uri, nan tace ta gyara gurin ta fita. cikin kuka Najwa ta gyara gurin dan ita abu kad'an ke sata kuka. bayan ta gama ne ta dawo parlour ta zauna tana karatun wani litafin azkar ,

Aneesa ce ta shigo ita da k'anwar Imran sunnan ta *MUNAYYA* , Munayya k'awar Aneesa ce sosai dan halin su d'aya,

Aneesa ce ta yamutsa fuska tace" ke bance ki wanke min undies na ki goge min ba?"

Da sauri ta mik'e tace" kiyi hak'uri yanzu zanyi"

Munayya tace" wait kafin kiyi ki dafa min indomie kuma yayi dad'i "ta k'arasa maganar cikin rashin kunya,

Aneesa tace"ai dole yayi dad'i"

Nan Najwa ta shiga kitchen ,




*THREE YEAR'S LATER*




*Muje zuwa*


*Taku ce*

*UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป


๐ŸŒน *RAYUWAR NAJWA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



*NA*
*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *13*~*14*





*DEDICATED TO PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*



*Wannan shafin naku ne, Ina son ku Ina yinku Ina tare da ku Ina muku fatan alkhairi,*๐ŸŒน

*Allah ya k'ara basira da zak'in hannu tare da k'warin ido, Allah ya Kare ku daga sharin makiyya da mahassada, Ameen*๐ŸŒน


*Love u all p.m.l writers*๐ŸŒน






*AFTER THREE YEAR'S*

๐ŸŒน

*BAYAN SHEKARA UKU*




*Wurin* ya cika mak'il da mutane a wani filli na cikin makaranta islamiyya, d'alibai ne cikin maroon hijab na gani da alama saukan AL QUR'AN akeyi, gurin da aka tanada domin d'alibai da sukayi saukan Qur'ani wani malami ne ya kira sunnan wata daliba ta fito ta karanta suratul AL-IMRAN bayan ta gama ne aka kira wata,

Cike da natsuwa take tafiya har ta k'arasa gurin karatun, sanye take da doguwar hijab maroon k'afar da hannun ta black socks ne, fuskar ta na kallon k'asa ta Isa gurin, a hankali cikin zak'in murya ta fara karanta suratul BAK'ARA, bayan ta gama ne gurin ya d'auki tafi sosai, d'ago kanta da zatayi sai naga NAJWA ce Masha Allah nace dan kyawun ta ya fito sosai kyakyawan gaske ce ita idanun ta farare ne tas kamar madara lip's d'in ta pink ne kamar ta shafa lipstick duk da tasa hijab amma tana da shape mai kyau,

Wasu y'anmata guda biyu na gani sun k'araso gurin ta, suma d'in kyakyawa ne Aneesa da Yusra kenan, Yusra ce ke karb'an gift's d'in da ke hannun Najwa tana cewa"Sister Allah ya k'ara Miki basira"

Cikin zak'in muryan ta tace" Ameen Sister tare da ke"

Aneesa ce taja wani dogun tsaki ta juya ta bar gurin, driver ne yazo ya d'auke su zuwa gida,

Motan na parking wani kyakyawan saurayi ya iso gurin yana cewa" Ayi min afuwan please ban sama zuwa ba" IMRAN kenan,

Yusra tace"ai ko ya Imran ba muji dad'i ba babu Wanda yazo"

Da sauri Aneesa tace" ya Imran kar ka damu ai"

Najwa ko shiru tayi nan Imran ya mik'a ma Najwa wani d'an k'aramin box Mai kyau anyi wrapping d'in shi da foil paper karb'a tayi tare da godiya sannan ya ba Yusra wasu leddoji ta rik'e mata,

Cikin fushi Aneesa tace" ya Imran Ina nawa?"

Yace" ku ai ba kuyi sauka ba Dan haka ku

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment