Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301

💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼







BY HAERMERBRAERH






*Assalamu alaikum, Fans, i am here with another intresting, heart touching, and amazing novel just for u to get more knowledge, out of it, ina roqon Allah yanda ya ban dama da ikon kammala sauran cike da nasara,Allah ka qara min damar isar da saqon alkairi ka kare ni daga otherwise, ya rahman idan nayi kuskure ka yafe min, idan nayi daidai ka ban ladan ta*

*HAERMEEN HAERMMAERH NA RIQON DUK MASU KARANTA NOVEL DIN TA DA MA WADAN DA SUKE SHA'AWAR FARAWA DAN ALLAH SU NA TARAWA, KO BA YANZU ZASU KARANTA BA, SABODA MATSALAR WAYAR TA DA KUKA SANI NA QIN TURA ABU MAI YAWA. ME LOVE U XOXO❤*









Page 1:









"Eamaan kin san ba wadda na ke so, in ba ke ba, kema kuma na sani duk samarin da Allah ya azurta ki da su ba wanda kk so kk kulawa sai ni, to mai zai sa ki bari a raba mu, in bake ba zan iya rayuwa ba, ba macen da zata zama a madadin ki," cike da qunar rai, Anwar ke maganar, ," Anwar kai ma ka san maganar iyaye tana sama da ta kowa ko, ba zai yu iyayena su ce ga abinda zan aikata ba ni kuma daboda son zuciya ta na qi, kai ne kullum kk fadan yanda zan qara kyautata tsakanin mu'amala ta dasu, me yasa yanzu kk son canjawa, ina kallon yanda kk ma iyayen ka biyayya,na tabbata da kai ne suka umarce ka da ka rabu da ni zakai hakan, why are u influencing me to disobey my own parents? Ina zaton mun wuce wannan lokacin, kai nake so, duk duniya ta san hakan, kuma ba zan sake so ba, wanan kuma Allah ne shaida akan hakan, fatana kawai Allah yasa yanda nai karatun nan kar su tauye ni wajen yin aiki, domin yana daya daga burina na rayuwa," ta qarasa zancen ta tana hawaye masu zafi a fuska, kallon ta yai,da girmama wa, ya mata fatan alkairi, sannan ya tafi, kuka suke sosai gaba dayan su, a haka ta shiga gidan ta fada gadon ta,madaidaici da yake kusa da gadon yayar ta Hafsat, gaba daya rayuwar gidan su take tinani, anya ba a qwarar su ita da mahaifiyar ta? sun taso suna masu son junan su tin yarinta, ita da Anwar, maqota ne su, iyayen su abokan juna ne, mahaifin Eamaan, cikakken dan boko ne, mai ra'ayin kan shi, ba wanda ya isa ko da shawara a canja mai abinda yaso aikatawa, matan shi biyu,Kareema ita ce babba yaran ta biyu mata,sun aurar da babbar, mai suna Fa'iza,a nan cikin garin kano, ga wani hamshaqin dan siyasa, sai ta biyun, ita kuma tana ci gaba da karatun ta a bangaren Law, Eaman diyar khadija ce,itace matar Alhaji Muhammad Kabeer, ta biyu,mace ce mai biyayyar aure,halayyar su ta sha banban da uwar gidan ta, Kareema bata yarda a na bata umarni ba sam, sai dai in ma za a bata umarnin to fa ya zama ba zai takura ta da yaran ta ba,sabanin Khadeeja,ko me za a ce tayi, indai bai zama haramun ba,ko zai tauye haqqin ta da na diyar ta tilo zata yarda. Hakane ke shirin faruwa yanzun ma, duk dadewar Anwar da Eamaan a soyayyan, gashi Daddyn ta na neman raba su, sakamakon wani ra'ayin shi na son zuciya, domin kuwa wanda yake son bawa Eamaan sa'an shi ne, mai shekaru kusan 57, a duniya, ita kuma ba zata wuce shekara 22 ba, a cikin wannan shekarar ta gama school of nursing ta fita a matsayin midwife, ba qaramin son aikin take ba, tayi wannan karatun ne dan taimakawa mata, bata son taji labarin maza ko arna ke karbar haihuwa a asibiti,ranta na matuqar baci, tin a shekarar da zata gama secondary school suka yanke shawara ita da qawar ta A'ishaa zasui karatu akan hakan, sai gashi Allah ya cika masu burin su, ita A'ishaa har ta fara aiki, a wani asibiti mai zaman kan shi a unguwar da tai aure, kuma da taimakon mijin ta hakan ya samu, Eamaan ta taya ta murna sosai, itama taiwa kan ta fatan samun hakan, amma da dikkan alamu ba zai samu ba, na farko dai mijin da zata aura ba yaro bane, da gani zai ra'ayi irin na mahaifin ta, na biyu kuma, dan siyasa ne shima, tasan ko da wahala ya barta zuwa aiki, ajiyar zuciya tai ta kalli sama " Allah gare ka nake neman zabin alkairi ba son zuciya ta ba, na sani duk abinda ka zaban daidai ne, aslamtu nafsi ilaika ya rahman," hawaye ne masu zafi ke gangara ta gefen idon ta, shigowa akai tai saurin goge su, ta zauna, " me kike yi anan tin dazu banga alamar kin je kin ci abinci ba yau, dazu naga kin je parlorn baqi, Anwar ya zo ne?" Mahaifiyar ta da take kira Amma ce ta ke mata wannan.tambayar," Eh Amma, ya zo, kuma ya tafi, na mai bayanin komai akan auren da Daddy ke son min," ta qarasa cike da kyabe baki irin na mai son yin kuka, hannu mahaifiyar ta ta sa ta jawo ta jikin ta sosai, ta kwantar da ita a qirjin ta,ta na shafa kanta zuwa fuskar ta," Huss huss my baby, kar ki sa ka damuwa a zuciyar ki, ki zo kina samun ciwo kina qaramar ki, damuwa ba taki bace bayan kin san dama ba ke kk halicci kan ki ba,ba kuma ke kk haifi kan ki ba,kina da iyaye, kina da wanda zaki bautawa ya baki lada, dan haka in kk bi iyayen ki sai wanda zaki bautawa wato Allah ya baki lada mara yankewa, ko kina son sabawa iyaye ki shiga fushin Allah?" Girgiza mata kai tai alamar A'a," yauwa yarinyar kirki, ku zama mai Biyayya ga iyayen ki, zaki zama mai riba a rayuwar ki, beside Alhaji Abdullahi Mai Nasara na son ki, ba zai bar duk wani abu ya cutar da ke ba, matan shi je kawai da mahaifiyar shi ,suma kuma in kk zama good gurl ba zasu zama matsaka ba,kinji?" Daga kai tai kawai,amma tasan Amman ta na magana ne dan ta kwantar mata da hankali, sarai ta san gidan Alhaji Abdullahi, ba qaramin gidan da ake kwasar shokin tashin hankali bane, musamman da surukar su, ta tsufa tukuf amma sai rashin M, ga sa ido, Matan shi kuma kishin bala'i ne da su, su biyu, Hajiya A'i itace babba,ba ta da yara, in ta haihu komawa suke, sai Hajita Rabi, itace ta biyu, yaran ta qanana ne guda biyu, dika mata, Ilham, da Sabeerah, akan yaran nan sharrin ta ba qarami bane ga duk wanda ya masu kallon banza, amma in kaso su to fa zaku zauna lfy da ita, wannan dalilin ne yasa ake dambace wa a gidan, dan kuwa Hajiya A'i bata son yaran sam, a cewar ta ma waya sani ko 'yan kwaroro ne, dan dai Hajiya Rabi akwai son zuwa unguwa, duk kullen Alhaji Abdullahi sai ta saci jiki ta fice, in tai sati bata fita ba to tabbas ya tsanan ta tsaro, in ko taje ta dawo sai Iya ta tona, daya gama fadan da zai ya fita zata je bangaren Iya ta zazzage mata kwandon tijara. Miqewa tai ta bi bayan Amman ta domin cin abinci.



" Daddy na amince da zabin ka a gare ni, ina fatan ya zama na alkairi," " Yauwa Mamana,Allah ya albarkace ku, ke da mahaifiyar ki, domin nasan akwai sa hannun ta a yardar ki,kinga wadancan yanneman masu kama da mutane dana roqi alfarmar ai qi sukai, wai za a tauye ta karatun ta waye2, to taje ta auri biro ma qarewar karatu, nan da wata daya za ai komai a gama, game da Anwar kuma kar ki damu, na ma mahaifin shi bayani ya kuma gamsu, shima yaron mun yi magana dashi dazu bayan kun gama, na kwantar mai da hankali, ya fahimce ni, duk da cewar yana cikin damuwa, Allah ya muku albarka ya baku ladan biyaya, murmushin yaqe tai ta amsa da "Ameen Daddyna," miqewa tai ta shige dakin ta ta kwanta, hawaye na korar wani, a hankali tana shassheqar kuka," ke kk sani, wai ke me biyayya, zaki kai kan ki inda zaki wahala,na farko ma dai ba zaki more rayuwar aure ba, dan wannan tsohon bana jin zai ita tabuka maki komai, na biyu kuma matan shi kadai jarabar su ta ishe ki, sannan ga mahaifiyar shi da qanin shi, dan ma dai qanin zuwa yake ya tafi, ke wahalar gidan bata qirguwa ko da girkin su aka bar ki, kin wahala, ni ba zan taba yarda a min wannann aiki ba, a tauye ni, kuma keda cika burin ki na aiki,sai in wa'adin wannan tsohon ne yai yancika kk gama takaba kin yi aikin inda rabon ki," toshe kunnuwan ta tai bayan Yayar tata ta gama zayyana mata abin da ta riga ta sani, kuka take sosai ga soyayyar Anwar da take jin kamar qara mata ake, ina zata sa kanta, ," Ya Allah ka kawon komai da sauqi," " Ameen" shine abinda Hafsat ta fada cike da tausayin qanwar ta ta,da tana da iko da ta hana wannan auren, Yayar su ma auren dan siyasa tai, amma ita ta nace, kuma shima abokin Abban su ne, fatan ta Allah karya qaddara mata irin wannan auren na 'yan siyasa, ita tafi son auren da zata sakata ta wala, ba wani surutai na masu mulki,juyawa tai ta kwanta, tare da dora pillo a kanta, dan ba zata iya hana qanwae ta koka takaicin dake ran ta ba.




A cikin wannan satikan gaba daya duk wanda ya san Eamaan sai ya tausaya mata, tayi rama sosai, dan yarinya ce dumui2 da ita,son kowa,ga ta da haske fata, sai dai ba sosai ba, ga ta da tsahon gashi, mai sulbi, tana da ido masu kyau duk da ba manya bane,amma suna da matuqar fari baqin ma baqiqqirin, ga zara2n gashin ido,da sajen fuska, tana dauke da siririyar hushirya, sai dimple din ta daya a gefen kumatu, duk da ba wani sosai bane amma in tana dariya yakan fito, a gaskiya Eamaan ta hadu sosai, ga ilimi both western education and islamic, dan saukar qur'anin da tai haddane, kusan dik littafin addinin da akai masu ta shanye shi akan ta, Alhaji Abdullahi yana son ta ne saboda kyawun ta, ba qaramin manemin matan tsiya bane, in ya shallake ya fita Abuja, sai sanda ya ga dama ya shigo gari, sarai Daddyn ta ya san hakan, dan tin kafin zancen auren su shi ke ma Alhajin fada akan wannan mummunar dabi'a, zancen auren su ya samu ne ta dalilin alqawari da Alhaji Abdullahi yai na in Daddyn Eamaan ya aura mai ita ko Hafsat ba zai sake neman matan banza ba, jin haka Daddyn ya ce zai aura mai Hafsat, amma ita da Maman ta suka qeqasa qasa suka ce sam ba da su ba, kar Allah ya sa ya daina neman matan, hakura yai ta bangaren su ya nemi alfarma wajen Amma, ita kuma ta tabbatar mai da ba komai, ai Eamaan mallakin shi ne, dan haka bazata taba hana shi iko da ita ba, wannan shine dalilin auren Eamaan da Alhaji Abdullahi........








*Wannan hadi anya zai haifar da da mai ido kuwa?*
💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼






BY HAERMEEBRAERH





page 2:






Eamaan tasha gyara wajen Amman ta, gyara bana wasa ba, duk wanda ya kalle ta sai ya qara, tayi iyayin ta sa tai qiba dan samata abinci take gaba sosai ta tsare ta sai tacinye amma all in vain, ga ta nan ne dai kawai, 'yan uwa da abokan arziqi sun hallara, domin gudanar da shagulgulan bikin da aka tanadar, wasu da suka san ta da Anwar sun matuqar tausaya mata, amma ba mai jajan tawa saboda yanda kullum take da alama sai ta ci kuka, a fuska da ka kalle ta kamar mai shiri fasa ihu, haka take cikin quncin zuci, Hafsat kullum sai ta taushi zuciyar ta amma bata samun wani sauqi, a wajen Hafsat da Amman ta ne kawai take samu tai kuka a jikin su ta samu sauqi. Daga lefen da aka kawo kowa yasan gidan da za a kaita ba na wasa bane, wasu a unguwa cewa suke Daddy ya saida ita ne ga dan siyasa, wasu suce kwadayi ne irin na masu kudin yanzu suna da shi sai sun qara, ba wadatar zuci, masu fahimta ne suka san qaddara ce ta sauka akan ta, kuma sukai mata fatan wanyewa lfy,( ko ina ruwan masu cece kuce din oho). An daura auren Eamaan da Alhaji Abdullahi, taron daurin auren da ya qunshi manyan mutanen qasar mu Nigeria, motoci a layin har rasa wajen tsaiwa ake, Daddy kam bakin shi yaqi rufuwa, dan murna yake da aurar da diyar shi ma dan siyasa a karo na biyu.



Yan kai amarya na gano baki sake suna kallon gidan da aka kai Eamaan kowa sai san barka yake, qawayen Hafsat ne ke mata tsiya, " babe yanzu da kin yarda da tini muna zuwa ganin wannan makeken gidan, muci arziqi mu bar shi inda yake," " hmm baku da hankali, itama fatan Allah ya kubutar da ita daga sharrin dake tattare da wannan gidan nake," a haka kowa ya dinga watsewa ana ma amarya fatan alkairi, bangaren ta ya rage ba kowa sai ita kadai, kafin su tafi saida suka qara gyare mata gidan tass ko ina sai daukan ido yake, komai na gidan pink ne da ratsin fari, gidan ya mata kyau sosai,rufe idon ta tai wasu hawaye suka zubo mata, wannan rana sun dade suna tsara ta ita da Anwar, gashi zata yi ta a wani gidan, gidan da bata taba mafarkin aure a cikin shi ba, " Ya Allah na roqe ka dan kyawawan sunayen ka tsarkaka,Allah ka ciren damuwar komai a raina, ka bani ikon da juriyar yiwa mijina biyayya da mahaifiyar shi, Allah ka bami zaman lfy da abokan zamana, sharrin dake tattare a cikin gidan nan Allah ka kare ni da shi, ka hada ni da alkairin dake cikin gidannan ya raheem," a haka ta fashe da kukan da ya taso mata, na kadaici, ji take duk duniyar ita daya ce, ta rasa kowa nata, Anwar shine kowa nata, tabbas rabuwa da masoyi akwai ciwo akwai azaba, gashi tana dandanar hakan, gani tai har sha daya bai shigo ba ta miqe taje tai wanka, tai brush, ta gyare gashin ta, ta fito, tana fashin sallah, zuwa tai ta tofe qofar shigowar da addu'a ta dawo tai addu'ar bacci ta shafe jikin ta ta ja abun rufa, ta kwanta, bata jima da kwanciya ba ko bacci ya dauke ta mai dadi, mai cike da mafarkai barkatai wanda ba zata iya tantance su ba, cikin baccin taji ana shafa ta, firgigit ta miqe tana tsilla idanu, Alhaji ta gani, cikin qananan kaya, tsufannan ya boye,sai sheqin angonci yake, komawa tai ta ja abun rufan ganin sai kallon ta yake yana hadiye yawu, dugawa tai ta gaida shi ya amsa, kanta a qasa bata qara cewa komai ba, tana jiran taji daga gare shi, ledar dake hannun shi ya miqa mata yace taci kan ta kwanta, dan ya ga alamar bacci take ji, ya dade da shigowa bata ji shi ba, da safe sun yi magana da sauran matan a babban parlorn gidan, wanda yake ta can bangaren mahaifiyar shi ne, daga mai kai tai sannan ta furta saida safe a hankali, takalmi taga ya cire ya dale gadon ya janye abin rufa ajikin ta ya kwanta ya rufu, a hankali shima yace mata saida safe, zare ido tai a hankali ta furta," anan zaka kwana Daddy?" Did she just call me Daddy? Oh my God noo," me kk kira ni?," a hankali ta furta," Daddy," " no pls don't call me Daddy, i am ur husband not ur Daddy, call me with any sweet name like honey, sweetheart, baby and so on," zare ido tai ta kame baki tana mamakin wannan tsoho mai budurwar zuciya, daga mai kai kawai tai, dan bata son komai yai nisa , ledar dake hannun ta ya karba ya jawo ta jikin shi ya zaunar zumbur tai ta miqe,ya maida ta," Amman ki da Daddyn ki basu ce maki banda yima miji musu ko gardama ba?" Daga mai kai tai alamar sun fada,Oya zauna na baki abinci naji qarar da cikin ki ke yi, na masu jin yunwa, ni gidana bana son ana zama da yunwa kin gane?," daga kai tai bakin ta na rawa jikin ta nayi, a baki ya dinga bata kazar tana ci da kyar, a haka ya ciyar da ita ta qoshi ya bata fresh milk, sannan ta miqe taje tai brush ta dawo, shima hannun shi ya wanko ya koma gado ya kwanta, can qarshe taje ta takure, murmushi yai daya ganta haka, ya hai gadon ya jawo ta jikin shi," ba abinda zan miki bacci zamui,dan dana dauke ki naji alamar baki sallah ko?" Daga kai tai da sauri, dariya yai mara sauti, " yaushe zaki gama?" Nuni ta mai da hannu alamar kwana biyar," K ba damuwa Allah ya kaimu, mui bacci kenan yanzu ba,naga kin gaji," nan ma daga mai kai tai, taga kawai ya rufe ido zai bacci ba addu'a miqewa tai ta fara addu'a a tafin hannun ta, tana gamawa ta fara shafawa, binta yai da kallon sha'awa dan gaba daya yanda take shafawar ya tafi da shi, ita kuma sam bada wata niyya yake ba,"nima ko zaki min addu'ar ne," daga mai kai tai, ta fara karantowa , tana gamawa ta hura mai, " A'a ni kenan ba za a shafa min ba?" Kauda kai tai cike da kunya ta koma makwancin da taiwa kan ta ta rufa, murmushi yai ya matsa jikin ta yace," haka zamuna bacci bana son ki nisa dani kinji?," daga kai tai cike da tsoron abunda take ji na tabo ta, sai wurga ido take, ga bacci tana ji ga ta kasa, hawaye ne ke zuba mata, yama jin haka ya sake ta ya juya, dan ya kula ta takura ta da yawa, yana juyawa ta sa pillo tsakanin su, yai murmushi, a haka suka kwanta. Qarfe 3:30am nayi ta farka, tai addu'ar tashi a bacci, kallon shi tai ta ganshi shame2 yana ta kwasar bacci,miqewa tai taje tai alwala ta fara karanta qur'ani da ka saboda mahaddaciya ce ita, ta kai kukan ta wajen Allah, lokacin sallar subh, nayi ta kalle shi duk kiran sallar da ake a masallacin gidan bata ga ya motsa ba sam, sai da aka idar ne ma taga yai wani juyi tare da munshari ya qara jan bargo, tana so ta tada shi tana tsoro, a haka tai shahada, taje ta tada shi,ya juyo fuskar nan kamar wuta, ba walwala2, gata zulum a hijab, " ko dake ke baquwa ce a gidannan amma in ina bacci ba a tada ni daga yau ki sani," juyawa zai ya kwanta yaji tace," Wayyo ban sani ba kai hakuri,inshaa Allahu zan kiyaye, wai da naji maka tsorom fitar lokaci ne, tinda Allah yace azaba ta tabbata ga wadan da basa sallah akan lokaci, naga in kai sallar zaka iya kwanciyar ka ka huta,amma tinda haka ne zan kiyaye daga yau," duk.bayanan ta a kunnen shi, tsaki yaja ya miqe, ya shige toilete, yai brush, yai alwala , ya fito, Sallah ya tada ya burbura ta ya sallame ya haye gado ya koma baccin.shi, mamaki ne fal cikin ta, dama haka masu kudi suke ko dai shi ke hakan?



Kafin ya tashi da safe ta yi wanka gudu2 a dayan dakin, dan bata son ya tadda ta, ta gama ta saka kayan da ta tafi da su, tai kwalliya mai kyau, sannan ta koma, zaune ta tadda shi ya dafe kai, durqusawa tai ta gaida shi, ya amsa cikin dan sakewa, kallo ya bita da shi, ba qaramin sha'awar yarinyar yake ba, a hankali ya miqe ya shiga toilete yana saqa abubuwa da dama akan ta, wanka shima yai ya shirya sannan ya kama hannun ta, suka fita,tana ganin sunyi hanyar waje ta ce," bari na dakko hijab," kallo ya bita da shi," a gidan ma sai kin saka hijab?" " a wai naga kamar sai munbi ta wajen masu aiki ne, kar na hadu da wani daga cikin masu aikin ba mayafi jikina," kada kai yai ya jingine yana jiran ta, saka hijab din ma ba qaramin kyau ya qara mata ba," lallai Eamaan komai naki mai kyau ne," murmushi tai tacen" Na gode," Hajiya A'i dake tsaye jikin window ce ta hango su suna murmushi, zuciyar ta kamar ta fito, saboda kishi, " dubi dan siya mana

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment