Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bata tsoro, amma ya mata kallon 'yar lyf, ganin shigar ta, ( kunji jahili da bai saba ganin matan yayun shi na irin wannan shigar ba, ita ta yi dan mijin ta shi kuma ya daka akan ita 'yar duniya ce) tsawar ta ta qarshe ta bashi tsoro,kuma ya tabbata wannan fuskar ta ba alamar wasa, fita yai salalo2, ya koma bangaren Iya,yana shiga ya zauna dabar,yana dogon nazari, wannan 'yar yarinyar ce ta daka mai tsawa kuma ya bi me tace? Lallai sai ya koya mata hankali, sai ya nuna mata bariki fa sune babannin ta a qasan gada a lagos, kwafa yai ya janyo jug din da ta hada mai juice, ya tsiyaya ya sha wani gardi ne ya buge mai kunne,ya daga glass cup din yana kallo, duk abinda yake Iya na kallon shi, murmushi tai tace," Labartan abinda ya faru daga fitar ka zuwa yanzu," kwafa ya sake sannan.ya zayyana mata komai bai rage ba, ya qara da," har ni zata kora da kakkausar murya na bar mata waje, ta suturce jikin ta? Ni wanne kalar jiki je ban gani ba,kuma ban taba ba,daga na turawa har larabawa zuwa baqaqen fata namu na nan, zata fadan jikin ta," " dole ta fada maka jikin ta mana danneman lalatacce( ita take lalata shi kenan tin da ga sunan da ta fada mai lalatacce)kai da ko kunyar fadin kai mazinaci ne ba kayi, a gabana kk fadan wacce mace ce baka taba ba ko, dau abinci kaci soko kawai,".
Bayan fitar shi ne ta tashi ta sako doguwar riga akan kayan,ta yafa dankwalin rigar, ta dakko wayar ta ta dubalokaci taga lokacin yin Chatting din ta ne,ta hau yin Chatting da A'isha qawar ta,

"Babe y kk"


" Gud and u?"


"Hmmmm gani nan nekawai"


" mekefaruwa?😱"


"Allah wani wawa ne kawai in zauney fadon,ba sallamadag ni sai qananan kaya, dadikkan alamu yanz da nake replaying fuskar shi ga raina nasan qanin Alhaji ne da ake fada,kumada gani ba qarmin dan isabane, ni ya zan da shi ne dan Allah?"😭😭



Sa kace tana ganin ta hakata zubo hawaye,



"Just chill bae in ya maki iskanci kici qaniyar shi ke da shi, kar ki sakar mai fuska ko dawasa, kar ki taba kai qarar shi,ki handling komai da kn ki, kai qarar dangi miji ma miji na ja maki baqin jini, in kuka ci uban juna ya buga ya jiki a tsaye to shi da kan shi zai tonawa kan shi asiri kin gane me nake nufi kuwa?"


" Eh na gane, nakuma gode, dan da na fara tinanin sanar da Alhjin makuwa,"



"Kar ki fara ku ci uban juna kawai, kar kina sakar mai fuska ko ki bashi damar zuwa bangaren ki ma kwata2 tinda kin gane halin shi,"

" to na gode sai anjima lokacin ibada ya shigo kin san gwanda komai kana yi kana tsarawa,"


(ba dan chatting aka halicce mu ba dan bautar Allah aka halicce mu, ya kamata 'yar uwa ki ribaci lokacin ki, kar ya lalace a banza, ya zamana kina da lokacin yin komai, ko da a online kk kullum kuma ko wanne lokaci, to ya zamana aikin da zaki samu lada wajen Allah kije yi, balle akwai Application na Qur'ani a waya zaki iya kunnawa ko ki bude ki karanta, in baki karanta shi kina tasbihi, in baki tasbihi kina fafakarwa akan aikin Allah, banda zaman banza sisters)



Miqewa tai tai alwala, tai sallar magrib, ta zauna nan tai azkar, aka kira isha'i ta dora sannan ta ninke kayan sallar ta, wanka ta sake na dare, sannan ta saka kayan bacci, ta haye gado in da sabo ta saba dadewar Alhaji a waje, cikin ranta ba qaramin qyamar shi take ba saboda sai yaje wasu sun gama jagwalgwala shi ya dawo ya sauke masu dattin zina a jiki, hawaye ne suka zubo mata," Yah Allah ka sani ban kasance daga cikin mazinata ba, Allah ka shiryar da mijina, ka yaye mishi neman matan waje qazamai," ba qaramin jin kunyar addu'ar da ya riske ta tana yi da qarfi ba yaji, a hankali ya koma baya,dan a zaton shi ta yi bacci a wannan lokacin, zama yai a kujerar parlorn ya dafe kai, for the first time daya taba jin nadamar wata aba zina, dan bai daike ta a komai ba, a hankali ta miqe yai sallama ya shiga, saurin goge idon ta tai tai kamar bacci take,baiga laifin ta ba, tana ma qoqari a shekarun ta, direct bandaki ya shiga,dan a halin janaba ya shigo gidan, yana wanka yana saqe2, bayan ya gama ne yai brush ya fito, kaya ya saka ya dan shafa mai da turaruka sannan ya hai gadon, janyo ta yai yanda ya saba akan sui bacci ta juya fuskar ta jikin shi, idon ta rufe, ta ciki fal hawaye, data bude zasu ziba, kallon ta yake da so da qauna, tare da girmamawa, dan ba wanda ya taba jin ya mai addu'a haka,ko da mahaifiyar shi ce, kullum sai dai ta zage shi, " I knew u ar awake, i am sorry for everything, inshaa Allah zan dena ne, ba lokaci daya na zama mazinaci ba, amma da yardar Allah ina sa ran dainawa lokaci daya, but i need ur help,"cikin kukan da take riqewa tace," and i promise to help u in any way i could, ni dai fatana ka dinga qoqarin bari, kan ka bar zina sai ka bar sabab din ta, daina halattar wajen da ake yin ta, daina kula abokan zinar, da abokan da suke saka ka aikata ta,sannan sai ka kiyaye jinka da ganin ka,ina fatan zaka qoqarta wa wadannan abubuwan," daga mata kai yai kamar yaro, tallafe fuskar shi tai ta mai kiss a lips din shi, tare da murmusawa , hawayen ta ya share mata, sannan ya mannata da qirjin shi, a haka sukai bacci.



Cikin shiri mai kyau suka fita shi da ita zuwa bangaren Iya, dan yace da kan shi zai kaita gida yau, ya dawo da ita, ta matuqar jin dadin hakan, suna shiga, ya baje daga shi sai gajeren wando ba komai, duk jikin shi a waje,ko a takalmin shi, sai katse2n waya yake, da sauri Alhaji ya maida Eaamaan baya, ya ce," kai tashi kaje ka saka kaya, meye haka, zaka zauna tsirara," miqewa yai ya na sosa qeya yai daki,Iya ce ta dingiso ta fito, yau ciwon qafar ta ya motsa, Alhaji ne ya matsa Eamaan ta bayyana bayan shi,"Toooo 'yar jakar Audu, ina kuma zaku da sanyin safiyar nan, qarfe sha daya?," " Iya barka da safiya," "baka amsan tambaya ta ba, nace ina zaku," "Iya zan kai ta gida ne, jiya naji bata je ba,""Ohhhh bayan tijarar da kikai wa Sahabee jiya, shine kenan yau kk tasa shi gaba sai ya kai ki gida ki?" Da sauri Alhaji ya daga kai daga duqon da yake yace," me kikai wa Sahabeen jiya?" Idon ta fal hawaye ta kasa magana, dan dai ta san ita tsakanin ta da wannan zalben ba komai sai alkairi, dan qarewa ma ita ta gyara mai dakin da zai kwanta, ta mai girki, amma shi ya shigo ya nuna mata rashin tatbiyyar shi, ,"ina zata iya fada maka, yaje ta koro min shi,"kallon ta Alhaji yai yagane tabbas akwai wani al'amarin da ya faru da zai sa ta koro shin,shiru yai daga baya yace," zamu hadu dake ne," rai a bace, Iya da Sahabee da ya fito sake da jallabiyya sukai murmushi, a zaton su wani rashin mutuncin zai mata, ( kar ki zaci wai kyautatawar ki zai sa dangin miji su soki,sam ba lallai bane,haka kawai wani zai tsane ka,baka ci mai komai ba balle ka sha mai,) gaida Iya tai tana daddaukewa ta amsa, Sahabee ne ya gaida Yayan shi, sannan itama ya gaida ta yana shan qamshi, Alhaji ya kula da hakan, sannan ya kula da kallon maitar da qanin shi ke wa matar tashi, ," Iya ni zan je na sauke ta, na tafi Office inna dawo na dakko ta, a min addu'a," "to Allah ya kare ka ya maka albarka," miqewa sukai ta na gaba yana baya, suna zuwa mota ya bude mata ta shiga a ranta tana mamakin hakan ta zaci zai bata rai yai ta masifa ne, bayan sun fita daga gidan ne sun dau hanya yace," me ya hada ku, bana son ki boyen komai, gaskiya nake son ji," " dama jiya ne da zan je gida na je sanar da Iya, sai ta ce na mai girki na gyara mai daki,ti nayi hakan na gama kenan sai na ga lokaci ya tafi, ba zai yu naje gida ba, ina shigowa kawai sai nai wanka, na shirya cikin qananan kaya, wanan da na irin shi da weekend din can,shine bacci ya dauke, sai naji kamar ana kallona na bude ido na ganshi na kore shi, shine ya tafi ban san kuma ko shi waye ba,kuma koda na sani dole na kore shi saboda mutuncina yafi mun komai," bayan ya saurare ta ne tas, yace,"abinda kikai kinyi daidai,sai dai zan fada maki kome zaki kinayi kina kiyaye wa kar ran Iya yana baci, dan kk bata mata rai sai ta bata maki,ko ina nan ko bana nan,kuma nima bazan so ran mahaifiyata yana baci ba kin ji?" Daga kai tai ta bashi hakuri kuma, bai ce komai ba ya kama hannunnta ya riqe,a haka suka isa, suna zuwa gate ya ja ta yai kissing din ta, kamar ta saka ihu,ga mutane can gefen wani babban gida,ko da dai sun yi nisa amma wani zai iya ganin su ai, yaqe tai ta daga mai hannu, ta dakko jakar ta, ta fice, tana shiga taji kamar ta taka a guje ta gan ta gaban Ammin ta, ta baya taji an dafa ta, tana juyawa taga Ammin ta,ai cike da ihun murna ta dale ta,Hajiya kareema dake gefe ta saki dariyar jin dadin ganin diyar tasu, "kar ki ballan 'yar uwa fa, ku har yanzu yarannan baku girma, Yayar ku ma haka take wannan shirmen in ta zo," sakin Amman ta tai taje ga Hajiya Kareema, "Mama nai missing din ku ne sosai, wata uku faa," ta qarasa cike da shagwaba, takawa sukai sika shige ciki gaba dayan su, ranar Eamaan ji tai kamar kar yamma tayi, sun sa ta a gaba da cima kala2,irin wadda take matiqar so, ga hirar bayan rabuwa ana sha, tambayar ta sukai komai lfy dai ko, ba wata matsala, ta tabbatar masu da komai, lfy, Hajiya kareema ce tace," A'a Eamaan na san halin ki irin na uwaki ga ta nan,da zurfin ciki, kar kije kice zaki zurfin ciki a gida mai iyali irin wannan, in da matsalar da zamu iya baki shawara ki fada mana,"" Allah Mama ba komai, kawai dai rikicin su ne da suka saba tin kan naje kullum sai anyi, in yau ba ai ba gobe za ai,sai dai in yaran na skul,ni da su kuwa muna shiri,har maman su,kawai dai bata nuna min, amma bata min baqin hali,sai Iya da Sahabee, su ma banda matsala da su, iyaka na je gaida ta na koma sashe na, ita kuma Hajiya babba kishi take dani sosai,amma itama iyakar mu gaisuwa,bana shiga harkar kowa," ( in baki iya rufe sirrin gidan ki gaban iyayen ki ba,topa tabbas mata kk rako, domin kuwa fadan matsalar da kk ciki ma iyayen ki, kowacce iri ce, in ba wai ta kai ta kawo,dole manya su sani ba, zai ja ma iyayen ki tsanar mijin ki da dangin shi, daga nan zaman lfy zau maji qaura, mijin ki najin haushin iyayen ki, su suna jin haushin shi da dangin shi, in kuma aka samu kuka shirya, duk yanda zaki su so shi ba zasu so shi ba,sai dai kawai suna sharewa sabi da ke) sun gamsu da bayanan ta, sannan ta nuna masu ita da alhaji kamar zai na goyata kullum dan gata, wannan kuma haka yake, a haka har yamma tai Daddyn ta ya dawo ya mata nasiha, Alhaji yazo ya ci abincin dare anan sannan suka kama hanyar gida.


"Ku banni da su, wato ga 'yan iska an bari a gida, itace da girki ta tafi, mu nemi abinda zamu sa abaka ko?............
💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼



BY HAERMEEBRAERH







Page 6:





Saida ya biya da su supaer market ta sai kayan kwalama sosai, son ranta, shi da kan shi ya qara mata bayan ta gama, sannan suka dawo, a tsaye a qofar shiga wajen Eamaan suka gan ta ta coge, tana kada qafa, Sahabee na ta bata baki akan su koma iska nata kada ta, ga shi da ga alama ba da wuri zasu dawo ba, banza tai da shi, ya juya ya fara tafiya ne suka shigo da mota gidan, gyara tsayuwar ta tai ta cuno baki, Hajiya A'i tana leqen su ta window, taga ya za a qare, itama Hajiya Qarama tana leqawa, bayan ya bude mata motar ne ta fito, ya dakko mata jakar ta da ledojin, suka jero suka taho, haushi gaba daya ya kama kowannen su, amma banda Sahabee da yake da wani tinani na daban a qasan ran shi, " sannu riqaqqu, sai yanzu kuka ga damar dawowa? Na zaci a titi zaku kwana ai, KE ! Wuce muje ki tuqan tuwon alkama, miyar kubewa," ta sa kai tai gaba,su Hajiya babba na jin haka farin ciki ya kama su dan sun dan yau Eamaan sai ta ci uban aiki kan ta kwanta,yana son yai magana ma ko ya bata hakuri amma Eamaan ta kada mai kai, cike da murmushin da ya nuna mai she is totally ok with it, kada mata kai yai alamar ta bari yaje ya bada hakuri," A'a sweet ka bari kawai yanzu zan dawo ai, abinda ba zai wuce awa daya ba, kaga kan na dawo kaima na saka aiki, ka saka min ice cream dina da chocolate dina ga fridge, kuma kar a sha min sweet ta wuce biyu, inna dawo zan qirga," kamo ta yai cike da so da qaunar halayen ta, da kuma tsantsan girmamawa a tsakanin su, yai mata kiss sannan ya raka ta har side din Iya, sannan ya juya, a wannan lokacin kam Sahabee ya cika yai fam, ganin yanda Alhaji yai ma Eamaan kiss, " shegen kaya sai kwasar dadi yake ni ina nan na qare a qadangarun bariki, ni da zan samu kamar wannan ai ba zan irin taka ba, daga ranar na bar bariki," yai kwafa ya kada kai tare da murmushin da ban gane na meye ba, ya kada hannu ya shige shima, kitchen ta tafi direct,ta fara hada2r hada tuwon,ba jimawa ta dora ruwa ya tafasa, garin niqagge ne wanda yake zuwa a tankade, ta diba tai rude, a ruden ta zuba kanwa kadan,ta rufe, tukunya mai kyau ta dora ta kunna daya bangaren na gas din, ta zuba manja, ta yanka albasa, ya soyu, dama ta daka daddawa da kayan miya, tare da wake, a tsakanin lokacin da ruwan tuwo ke dahuwa, ta, hada su tai ta zuba, suka dan fara soyuwa, sannan ta dakko naman da ta wanke ta zuba,ruwa kadan ta dakko dakakkiyar albasa da kayan qamshi ta zuba, sannan ta saka dangin maggi kala2, sai da ya tafasa kamar na minti 5 sannan ta qara ruwa, ta rufe, nan da nan gidan ya dau qamshi, Sahabee ne ya shigo, yana tafiya a ranqwafe yanda ya saba,yai hanyar sink zai dau cup dan gaba daya qirjin ta ba qaramin tsone mai ido suke ba, yau ya dau aniyar taba su ko ta halin qaqa ne, daidai zata juyo kenan, kawai gaba daya qirjin ta ya daki nashi, sai da ya kusa suma, wani irin abu yaji ya ratsa dikkan jikin shi, da farko dai ta dauka, bai sani bane, amma sai taga ya aje cup din yana matso ta, ya kai hanu zai taba ta kenan, bai ankara ba yaji ta dauke shi da wasu gigitattun maruka guda uku, fuskar ta kamar ba ta ta ba,ya matuqar kidima? Ga zafin marin da ta mai ga mamakin qanqantar ta da yake gani, sannan ga tsoron yanayin fuskar ta," kai dabban ina ne, dan akuyan wane gari ne kai? To bari kaji, ko a qasar jakai ban taba jin labarin mai son aikata abinda kk da quduri ba, na dauka ba da sanen ka bane ka buge ni, amma yanzu na fuskanci duk inda ka dosa, to bari kaji, ni Eamaan, nafi qarfin dan iska da izinin Allah, kuma in ka kallen da kyau ba ragowar qadanqarun bariki bace, balle ka tsammaci wani abu daga waje na, ka kula," tana kaiwa nan ta koma wajen miyar ta da ta dahu, ta debo kubewa ta zuba busasshiya, dan da danyar zata wanke ta goga,amma ta fasa,ta tuqa tuwo,5mnts kawai yai ta kwashe, fuskar nan ba walwala, haka ta gama ta zuba a flask ta leqa taga Iya ta riga tai bacci, ja mata qofar tai tai gaba, tana fita ta saki wani kuka mai daci, ta kame cinyoyin ta ta duqar da kai, tana ta rera kuka, na halin da take qoqarin shiga da Sahabee, wannan wanne irin dan akuya ne , bai san ni matar wanshi bace ko me? Tin da ta fita yake tsaye a wajen kamar wanda aka dasa, na farko ya qudurta niyyar ko zata mutu sai ya dana jikin ta, sai ya amfana da albarkatun ta, sannan sai ya rama marukan da ta watsa mai, amma wata zuciyar tana tsorata shi da yanayin ta, itan ba kamar sauran mata bace, da suke son ma ya kula su,amma ko ba jima ko ba dade shima sai ya cimma burin shi.


Goge fuskar ta tai, ta leqa pampon da suke bam ruwa, ta wanke fuskar ta, ta goge da mayafin ta, ta tafi side din ta, kwance ta ganshi yai wanka,ya kwanta, ga sweet leda biyu yasha, sai 'yar takarda a jiki da rubutu, an rubuta," biyu na sha as promised, I love u with all my heart Eamaan,"ninkewa tai ta qurawa fuskar shi ido kawai, ba wani emotion a fuskar ta, ba zaka iya tantance me take ciki ba, ta dade a haka ta miqe ta shiga toilete, tai wanka ta fito, ta shafa mai ta fesa turaruka, sannan ta saka kaya tai sallah, ta kwanta, a jikin shi ta kwanta, dan tana buqatar lallashi, ko ba mai bata hakuri a qalla ta jingina da wani, hawaye ne suka zubo mata, ta share tai ta qoqarin shanye kukan ta, amma ta kasa, miqewa tai ta fita kitchen ta bude fridge ta saka kanta ciki tai ta kuka, sai da tai mai isar ta ta dakko ice cream ta fita, a tsaye ta ganshi, ( kar ku manta fa alhaji ya tsani tashin dare,in ya kwanta shifa sai safe,) " me aka maki? Waya taban ke? Zo nan ki fadan," cikin dakewa, dan ta riga ta koka baqin cikin ta, yanzu idon ta qamas, ta qarasa wajen shi, " ni ba abinda aka min, kaina ne yake ciwo, kuma na kwanta na kasa baccin, shine na fito na dau Ice cream dina dana duqa naji bayana yai zafi, shine nake kuka," " Assha sannu Eamaanina,tashi muje na miki tausa, sai kiji dadin wajen, sannu kinji, Allah ya sawaqa, bari na baki maganin ciwon jiki, daga kai tai cike da shagwaba take takawa, daukan ta yai kamar daukan yara in sunyi bacci, ta saqala qafafun ta a gefen jikin shi, ta kwantar da kanta, ta bude robar Ice cream tafara sha,sai da suka je dakin ta zuba mai kadan a baya, gantsarewa yai yai yar qara,ta saka dariya, tace," na warke aje ni qasa, amma kai hakuri kar ka rama, manya Allah ya zuba masu haquri daban dana yara," dariya yake sosai, ganin yarinya qarama na son mai wayo dan kar ya rama, murmushi kawai yai yace " juya to na maki tausar na yafe, aike baki laifi a wajena," juyawa tai ta kwanta ya mata tausa tana shan Ice cream din ta, a haka har bacci ya dauke ta, robar na kan gadon,miqewa yai ya dauke robar, ya aje gefe,ya gyara mata kwanciyar ya kwanta ya rufe su.



Washe gari da safe Sahabee ya shirya ya koma Ibadan, dan baya son kowa yaga shatin yatsun Eamaan a fuskar shi, a tambaye shi, tabbas za a gane shi ne yaje neman ta, Iya ta tashi ta duba, taga tuwon har lokacin da zafi sosai, dan flask din akwai riqe zafi, miyar na tukunya, ba qaramin son ci take ba,amma kar dai ta bar Eamaan ta huta, ta danna waya ta kira Alhaji, ya turo Eamaan ta hada mata abin karyawa," Iya bacci take,jiya bata samu bacci ba sosai, in ta tashi zan turo ta,ko masu aiki su dan maki mana," " Iyeeeaaa ashe kai zaka nuna mata ta raina ni? Da kaga ina cin abincin masu aiki ne ni? Ba sauran matan ka ke min ba, duk da ba wadda ta iya komai cikin su, sai yanzu dana samu wadda zata min mai dadi shine zaka hana, to shikenan ni bari naje,in hawan jinin nawa ya tashi na mutu ka huta ai," " Aaaa aaa Iya nifa ba haka nake nufi ba ga ta nan zuwa," cikin bacci taji ya tada ta a gigice, "Tashi maza je kiwa Iya a bin karyawa," bata nuna komai ba, ta amsa, nan da nan kuma sai yaji ba dadi, yarinya mai biyayya, kamar wannan, amma ya zaiyi, Iya ta ce kullum ita zata na mata abinci, dan ta iya girki, yana tinani har ta gama komai ta shirya zata tafi," Eamaan ki qara hakuri, ba yanda zan na hana hakan faruwa, mahaifi.....,""dan Allah ka bari,is nothing, ni a gidan mu tin dazu da na tashi, hadawa Daddy abinci, har na tafiya Office, yanzu ba ga shi ba inna je ina jifan tsuntsu biyu da dutse daya ba, zan mata,kaima zan maka wanda zaka tafi da shi, duk da kana wani qi, wai kai babba da tafiya da abinci ko, to yunwa ba ruwan ta da girman ka,kuma ai dole macen kirki tai tarayya da mijin ta wajen kyautata wa mahaifan shi in dai tana son ya shiga aljanna, tinda shi na miji iyayen shi kawai zai bi ya samu aljanna, dan haka ka daina ban hakuri daga yau pls in ba haka ba gobe da botle water irin na su Ilham zaka Office da irin lunch box din su" ta qarasa cike da wasa, dariya yai ita kuma ta fita,yana mamakin halaye irin nata, ta iya boye damuwar ta, dan tabbas yasan kukan jiya ma wani abu ne ya same ta,amma ba abinda ta fada ba, kada kai yai ya miqe cike da girmama ta a ranshi.



Tana zuwa iya ta bata umarnin ta dumama mata tuwon ta, sannan ta mata farfesun kifi, da kunun shinkafa, amsawa tai ta shiga ta hada mata tsaf, ta kawomata," Oh ni yarinya kamar inji, ke baki gajiya da aiki ke ? Ko dake in ma kin gaji za dai kiyi dolen ki,sai ki tashi ki tafi,uwar son miji, yarinya dake sai jaraba,wani har yana gayan jiya baki bacci ba, Oh ni yaran yanzu akwai jarabar tsiya," idon ta ya kawo kwalla amma tace," na tafi iya na gode, sai anjima me za a dafa maki anjima?" " Oh ho, ko dambun shinkafa zaki min ma je waya sani, sai anjiman dai in kinzo," miqewa tai ta zata tafi,har ta kusa tafi ne tace ke zo nan, dubamin dakin Saheebee ya taso ya karya, ki tambaye shi me zai ci ki hada mai...........







*hhhhh ya kusa isa garin yarbawa wallah*😆😆
💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼








BY HAERMEEBRAERH








Page 7:








Dab zata kwankwasa dakin ta hade fuska kamar bata taba dariya ba, ta sa hannun dama ta fara kwankwasa qofar, shiru2 tafi minti uku bai bude ba, murda hannun tai a leqa, taga ba kowa, ba kayan shi ma kwata2,yanda ya saba bazasu ba komai, kwankwasa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment