Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

toilete tai nan ma taji shiru, budewa tai a kasada ta leqa wayam, komawa tai ta sanar da iya komai, kallo iya ta bita da shi can tace ta tashi taje, " Allah ya shiryi yaronnan, barikin tashi ta motsa ya tafi ba sallama," Eamaan na fita kai tsaye bangaren Hajiya babba ta shiga da yake kusa dana Iya ta ganta a zaune tana karyawa, da bread da kwai, ta hada Tea mai kauri tana korawa, sai baza hanci hake, kan ba dankwali as usual, ga shi ba gashi ba, kitson ya hade , amma fuskar tasha kwalliya, an dambara jagira, an saka jan baki a saman idon,sannan a bakin ma ta saka jambaki, jagirar an ja ta doguwa sosai, gashi an lafta mai a saman ta, ita a dole tai kyau, tana ganin Eaamaan ta daure fuska, gaida ta tai, ta amsa a shaqe, ta miqe ta fita,tana jiyo sanda taja tsaki ta hai zagin ta ko juyawa ba tai ba ta fada bangaren Hajiya Qarama, tana shiga Sabeerah ta saka uniform, ta ganta ta tafi da gudu ta dale ta, sama ta daga ta tana mata wasa, Ilham ta tako da yanga itama taje kusa da Eamaan, ta dan duqa ta gaida ta, amsawa tai cike da jin dadi, Sabeerah ma ta gaida ta," Ina Mum?" " Tana daki, tana dakko mana hijabs din mu," "k" zama tai ta jira sai gata ta fito, fuskar ta ba yabo ba fallasa, gaisawa sukai tace masu su biyo ta basu wani abu su tafi da shi makaranta murna sikai," U ar the best Aunty Eamaan," " ba komai sai kun shigo, ina jiran ku," ta fita,dan murmushi Hajiya Qarama tai, dan tana jin dadin yanda take kula da yaran ta, bayan ta koma ne ta ga har ya shirya,ita yake jira, a gaggauce ta kona kitchen ta dakko abinda ta bada umarni masu aiki si hada mata, ta kawo mai ya karya ta hada mai wanda zai tafi da shi, tana hadawa tana tsokanar shi, sallamar su Ilham ce ta katse su, sweets da suka siyo jiya da chocolate, ta debo ta basu,sukai mata godiya suka tafi, Alhaji shi ma yana jin dadin yanda take son yaran shi ba kadan ba,a ranshi yana ayyana gaskiya Eamaan ta daban ce.





Kusan wata biyu kenan ba labarin Sahabee, ba waya ba saqo, hankalin Iya yai matuqar tashi, a qallah yana waya in ya tafi, amma wannan karon shiru, samun Alhaji tai da maganar ya kwantar mata da hankali, ya nuna mata zai bincika yaji ko lfy, a ranshi ko yana ayyana " dan dan bariki yai nesa da gida haka ai ba abin mamaki bane".
Iya tai matuqar zurfi a tinanin ta,tajiyo qamshin girki,tabbas ta san Eamaan ce ta shigo,miqewa tai ta nufi kitchen din, Eamaan na ganin ta ta durqusa, ta fara gaida ta, bata amsa ba ta fara magana," ke me kikai wa dana? Me kika mai ya bar gidannan ba waya ba saqo? Tinda yake ko ya tafi kullum sai ya min waya amma wanan karon ba ko pilasha,(Flashing) kuma dan tsabar munafirci da kk zo bakije kin gaida ni ba sai yanzu ne zaki wani zube kina gaida ni?" " iya ki hakuri,naje na gaida ki naji shiru, da alama kinyi nisa cikin abinda kk tinawa,bana son katse maki ne yasa na taho aikina, Iya ban mashi komai ba, ko ganin shi ban ba ma lokacin da zai tafi, inshaa Allah iya zai dawo ne ki daina sa tinani da yawa a ranki, saboda lfyr ki," ta dan ji dadin maganar ta ta qarshe, saboda a qalla ta samu wanda ya tina mata ba ta da isasshiyar lafiyar sa tinani aranta,a hankali ta ja jiki ta bar kitchen din, tana matuqar son Sahabee fiye da kan ta, dan ko wanne laifi zai aikata a wajen ta bai komai ba, dakin shi ta shiga direct, ta hai dudduba kayan shi, ba abinda take gani sai kayan shaye2, da wata leda doguwa, mai kamar madara ce a ciki ko me oho, gida2, ledar mai qyalli,(condom) ajewa tai ta ci gaba da dudduba dakin, a gefen gado ta zauna tana ta tinani, kan wani lokaci kan ta ya fara ciwo, a wajen ta kwanta bacci ya dauke ta.

Eamaan na gama girki, taje dakin Iya ta duba koina har toilete bata gan ta ba? Dakin Sahabee taje, ta duba tagan ta kwance, tana bacci, ta cika dakin da munshari, zata ja qofar kenan Iyan ta farka, kiran ta tai, ta kama ta suka bar dakin suka koma nata, magungunan ta tai umarnin Eamaan ta dakko mata, fita tai ta debo mata da abincin da ta dafa, jellop din taliya data ji kayan ciki, da kayan lambu, sai tashin qamshi take, ga Tea data hada mata dan ta kula ko karyawa batai ba, sannan ta dakko mata ruwan roba, shigowa tai ta ja qaramin Table dake dakin, ta dora mata sannan ta binciko mata magungunan,abinci ta nada sosai, dan abincin Eamaan ko baka jin yunwa ka fara ci zakaji kamar kar ka daina ci, balle da 'yar Gusau din dama, tas ta share plate din, ta kora shayin , sannan ta sha maganin, a hankali ta fara jin nutsiwa na zuwa mata, ruwan wanka Eamaan ta hada mata sannan ta mata sallama ta fice, Hajiya Qarama ke girki ranar,Alhaji na bangaren ta,da dare Eamaan ta dafa ruwan Tea kawai sai ta soya kwai da ta saka ma timatir mai yawa da albasa, ta soya ruwa2, bayan ta saka kayan qamshi da dan maggi, ta zauna ta ci, sannan ta sha tea, wanka tai tai brush,ta saka kayan bacci, riga ce qarama iya cinyar ta, sai wandon digar shima iya cinyar ta, budaddune daga qasa, sai ta sama rigar ta dan kama kadan, ta saka hula kalar kayan, ba qaramin kyau tai ba, tai addua ta shafe jikin ta da shi, sannan ta bi lafiyar gado, kwanciyar ta kenan Alhaji ya shigo mata sallama, saida ya jagwalgwala ta sannan ya fita, yana fada mata yanda yai missing din ta, ya matsu jibi tayi ya dawo gare ta, and he wish a nan zai kwana yanda tai kyau da ya mata abubuwan da ba zata manta da su ba, bla bla blaπŸ™„ y tafi, cike da shauqin son kasancewa da ita, yana fita ta koma ta kwanta,zuciyar ta cikw da tinani kala2, ita tata jarabawar kenan," Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin," Alhaji Bismilla yai ya topa a qofar, sannan ya ja mata, ya shige bangaren Hajiya Qarama, tana zaune ba kwalliya kamar yanda ta saba,ba wankan dare, ba qamshi,ba komai, kuna wai a haka jiran miji take, mijin da ya je sallama da sauran matan shi,ya isko Hajiya Babba ta caba adonnan nata na kwalli da jan jambaki, an sha lace an sha dauri, duk d haka ta burge shi,a qalla bata wari, kuna tai kwalliyar ne domin shi,Eamaan kam ba a magana, tsaki yaja ya kwanta, can kuma kamar wanda aka mintsina ya miqe ya saka kayan shi ya dau key ya bar gidan, fitar da yai xikin daren ba wanda ya sani, me gadi ya zaga, dan haka gaba daya kan ya fito ya manta da zuwa ya jaddada rufe gate din, Fitar Alhaji da kamar mintuna sha takwas, Sahabee mai machin ya aje, a qofar gidan, ya sallame shi,ya tura qofar dan yaga a dan bude take kadan, yana shiga har ya nufi hanyar bangaren su wata zuciyar ta kada shi, ya nufi bangaren Eamaan, dan ba qaramib kewar ta yai ba a wannan watannin, ko neman matan na shi yake, yana kwance da mace zai ta ayyana Eamaan ce, amma inaa, baya wani samun gamsuwa, haka zai ta abu daya cikin haushi ya tashi, ya bar mace kwance da takaici, yayi iya qoqarin shi na cire ta a rai, amma ya kasa, musamman in ya tina deadly look din ta, da marukan da ya sha,sai yaga kaiiii wannan ba matar nema bace tafi qarfin shi, amma a haka ya leqa, kwance ya ganta, ta kifa cikin ta, ta dage qafa,tana kada su, da ice cream a hannu tana sha, sannan da wani littafi na su na school of nursing tana dubawa,ya dade yana kallon ta ya kula yau Alhaji ba a bangaren ta yake ba kenan,wani dariyar mugunta ya sake, ya tattaka a hankali, ya murda hannun qofar, a bude ya ji ta,murmushin shine ya qaru, ya sa kai ciki, ya rufe,kashe fitilar yayi, ya hau laluben hanya, yana kaiwa bakin qofar shiga duhu daga cikin dakin, alamar ta kashe fitila, ta bangaren Eamaan kuwa, tinda taji kashe fitilar parlor ta san ba lafiya, sannan ta ji taku a hankali, tinanin ta ya bata akan barayi ne suka shigo, wayar ta ta laluba ta kira Alhaji, tana ta ringing bai daga ba, ajewa tai ta miqe, ta dakko tiraren ta, ta labe bayan qofa, bayan ta kashe wutar, hasken waje ke ratso labulayen yana shigowa,zuciyar ta kamar zata fito dan tsoro, hankalin ta yai matuqar tashi, qirjin ta sai dagawa yake, a hankali ya murda qofar ya...............













*Dadahhhhhhh what do u think is gonna happen guys?*😱
πŸ’…πŸΌ BIYAYYAH πŸ’…πŸΌ





BY HAERMREBRAERH





*Hey guys, i am sorry zaku dinga jina shiru daga yau zuwa wasu kwanaki inshaa Allah, saboda zan yi busy sosai, amma in kuma Allah ya sa na samu dama zaku ga post dina,ina fatan za kui hakuri d hakan, and for those of u that ar saying " yanzu ba a mana rubutu sau biyu," ko " Yanzu pages din ba yawa," da dai sauran su, i am sorry, ayyuka ne ke min yawa, believe me ni kaina nafi son ina yi da yawa na gama. THANK U SO VERY MUCH FOR THE LOVE, ME LOVE U XOXO❀*






Page 8:






Qafa ta saka mai, ya kife a qasa ya yunqura zai tashi ta fesa mai turaren a gefen fuska, dan tsoratarwa, sannan ta sa bayan hannun ta ta buga masa a baya,daga gwangwanin turaren tai ta kwada masa a kafada, yana son yai ihu dan azaba amma baya son asirin shi ya tonu, fitila ta kunna, yana duqe a gaban ta,ya hade hannayen shi daya cikin daya,yana zubda hawaye,yana bata hakuri, mamakin ganin wai Sahabee ne ya gama cika mata ciki,daga hannun ta tai tana son magana, ta cije leben ta, ta kai ta dawo, a gaban shi,ta tattare gashin ta ta daye,kawai sai ta samu kan ta da falla mai mari, sannan ta kai mai naushi, kwantawa yai yana bata hakuri akan tai mai rai, tsautsayi ne ya kawo shi," zan rufa maka asiri, dan nima wannan abun kunya ne ace maganar nan ta fita,ko dan rashin lfyr Iya bazan so maganar nan ta fita ba,sannan ba zan so bata zumuntar dake tsakanin ka da dan uwan ka ba, amma ka sani, duk sanda ganganci ya sa ka qara kallona ka bari muka hada ido da kai a cikin gidannan ma, Hmmmmm,"tai wata dariyar da ta matuqar tsorata shi, yau shi da yake bariki a qasar masu kwale, shi ake wa haka, uban bariki, yau ta juye da shi, yau ya gane ashe barikin ma suna ta tara,mace sai ta so duk wani iskanci ke wakana, ashe dama mata suke ba maza qofa ko da da murmushi ne, balle magana , lallai yau ya gane, ashe ba kowacce mace bace yar iska, kuka yake sosai, gefen idon shi yai jawur inda turaren ya dan shiga, umartar shi tai daya fice maya daga waje, da gudu gudu ya miqe zai fice ta daka mai tsawa," wannann jakar taka da takalmin ka daya uban wa zai daukar maka," " bbbaaaabaaa kowwaaa, niiii zannnn dauuuke," wurga mai tai ya debe komai ta danna qofar ta rufe da makulli, kuka ta zauna a wajen tana yi, sosai zuciyar ta tai mata kunci ba kadan ba, wannan shine babban misalin in kai za a maka, ta ga ficewar motar Alhaji, wannan dalilin ne yasa ta je ta dakko Ice cream ta sha ko ranta zai sanyi, ta dau karatun ta ta fara ko zai dauke mata damuw, kawai taji shigowar shi, ta tabbata Alhajin na su sai gobe a ganshi, ya tafi wajen matan banzan shi, kuka take sosai, zuciyar ta kamar ta fito waje, wannan wace irin rayuwa ce," Yah Allah ka qaramin hakuri da juriya, Allah ka sani daga bayin ka masu godiya," ta miqe ta share hawayen ta, ta hada zufa,kamar wadda tai dambe, ko dake dan uwan damben ne ai, wanka ta dada shiga, tai wanka tai alwala ta zo ta saka doguwar riga, ta saka tiraruka ta dau hijab ta fara nawafil, yi tai tayi, saida taji ta gaza tsaiwa, sannan ta zauna ta fara karanta 'Qur'ani, tana idarwa, tai addu'o'i, ta shafa, tasha kuka wajen addu'ar sosai, ta kwantar da kan ta jikin gadon bacci ne yai gaba da ita.


Yana fita ya hau waige2,baiga kowa ba, saida yaje dab shiga bangaren su, sai mai gadi ya fito ya gan shi, Hajiya Qarama ta leqa tace waye nan, muryar shi na rawa yace," Ni ne Sahabee," sake kabulen tai tare da sake tsaki ta koma,me gadi ne ya dalle shi da fitila, yana ganin shine ya sauke ya fada dakin shi, dan ya san rashin mutuncin shi, karya karta mai da safe,inaaa Sahabee ba wannan a gaban shi, tinani sun cika kan shi, sannan ga wani mugun tsoron Eamaan da ya ke ji na qara shigar shi, budewa yai ya shige, direct dakin shi yaje, ya aje jakar shi, ya fada toilete, wanka yai ya fito, ya wanke kayan da ta fesa tiraren a jiki, dan gaba daya qamshi yake,a toilete din ya shanya su ya fito daure da towel,kallon kanshi yai a mirrow, yaga irin kyaun qirar da yake da ita, yammata na mutuwa akan ya kwanta da su, duk da bai da cimar kyaun fuska,amma a jiki ba ya da makusa sai ma burgewa, amma wannan da ta auri tsohon wai take mai wannan cin kashin, murmushi yai ya tabbatar wa kan shi yau abincin wani gubar wani, ba kowacce mace bace ashe zata zauna ta ci amanar mijin ta da wani ba,ba kowacce mace bace ballagaza mara kamun kai, ashe akwai matan kirki,masu jiran sakamakon su na alkairi a wajen Allah, yau ya tabbatar da cewa komai rashin samun yanda mafe take so a wajen mijin ta akwai na kwarai da suke jiran ladan su na hakuri a wajen Allah, rigar shi ya dauka ya saka,ya haye gado, ya kasa bacci sam, a kowanne second qara ganin girman Eamaan, yake, sannan wani kwarjinin ta na cika qirjin shi, Hajiya Babba ya tina, da ta ke mai waya, kuma take manne mai ya neme ta, rintse ido yai ya toshe kunnen shi,nadama yake jin tana son shigar shi yana toshewa, dan baya son ya saduda yanzu, gani yake kamar akwai dauran nasara ko ta bangaren Hajiya Babba zaina ci gaba da rage zafi, tinda in yana nan ba ya zuwa wani waje sosai, saboda Iya tafi son shi a gida.

Asubar fari Eamaan ta farka, ta sako alwala tai sallah, tai karatu, tai azkar, sannan ta tashi ta shirya ta fito zuwa wajen Iya,a hanyar ta ta zuwa taga motar Alhaji na shigowa, tsaywa tao ta dan kalle shi, fuskar ta ba kyaun gani tsabar bacin rai, sannann tai gaba, gaba daya ta zare mai laka, da kyar ya qarasa shigowa, ya fita yai bangaren Hajiya Qarama, tai kicin2 itama,ko kula ta bai ba ya wuce daki, yai wankan tsarki, yai wankan sabulu, ya fito, ya shirya ya nufi bangaren Iya, a kitchen ta gama markada waken da tasa tin jiya mai aikin ta sirfa mata ta wanke ta aje, sannan da asuba ta shigo daga bangaren masu aikin da asuba ta jiqa mata, albasa da attaruhu ta saka ta markada, sannan ta juye a wani bowl, ta saka zallan gishiri, sai dan farin maggi kadan, saboda in ta saka maggi dunqule yana watsewa, baya hade jiki ya tashi,bugawa tai sosai, ta fara soyawa, sannan tai kunun gyadan da ta saka mai nono mai kauri bayan ta gama mara tsami, asalin kindirmo, yai fari, ga shinkafar ta dahu, ta zuba su a flask, ta saka plate daya, cup daya, dan bata son ta saka biyu a san ta san dawowar Sahabee, tana jiyo Alhaji na gaida Iya, suna hira, bata son ganin shi sam, tana matiqar jin qyanqyamin shi, amma haka ta dauka ta ta shiga da sallama, Iya na ganin ta yawun ta ya tsinke, amma dan mugun rai ta bata rai, Sahabee ne ya bude qofa zai fito, yai maza ya koma, sai qarar danna qofar suka ji, kowa kallon wajen yai, dan ganin waye, amma bamda Eamaan,dan ta san waye, ajewa tai ta gaida Iya, wadda take ba Alhaji Umarnin ya leqa yaga waye, meke motsi a wajen, dagawa Eamaan hannu tai, ta na zaro ido tana kallon wajen, Eamaan da taga hankalin su yai wajen, tai murmushi ta fice,bangaren sauran matan taje ta gaida su kamar yanda ta saba, ta wuce nata wajen.
Alhaji na leqawa ya ga Sahabee, sai wurga ido yake, a zaton shi, zuwa tai fadan me ya faru, kasa cewa komai yai da Alhaji ya nuna farin cikin ganin shi," yaushe ka dawo?" Yaqe yai yana sosa qeya, " jiya da daddare na dawo, na isko kowa yai bacci, kawai sai ban tada kowa ba nima na kwanta, ina kwana?" Gaisawa sukai, sannan suka qarasa Iya na ganin shi, ta ida tashi zaune, murna kamar bata yai aka ganshi, sosai taji dadin dawowar shi, waya ta dauka tace bari na kira Eamaan ta zo ta hada maka abin karyawa, wata sufa yai ya damqe wayar yana in ina ," Baaaattttaaaa kawaiii, zan ci ko me aka maki, ni daga yanzu ma ana hada mana abinci, kome aka maki zan ci kawai,ba sai kin wahal da ita ba,"goshin shi zufa ta tsattsafo kamar wanda yai gudu,mamaki ne fal cikin su,bama ya Alhaji, alamar tambaya ya digawa qanin nashi, tabbas akwai wani abu a qasa, yana kula da hakan ya fara qoqarin kare kan shi," naga duk kunyi shiru, kawai ina son gaya makunje, i have changed,na daina duk wani rashin da'a ko BIYAYYAH, ko na dinga qasqantar da na qasa dani," murna ce ta cika su da jin hakan, abinci Iya tai ta dura mai, shiko sai kwashewa yake.
Tana isa ta rufe bangaren ta ta fara gyara gidan, ta goge, sannan ta hadawa kanta oat ta sha, a kitchen din,bayan ta gama ne tana ta wasa da spoon din a cikin qaramin bowl din, take tinanin, mijin ta ya je neman mata, ya ci nasara, dan da alamar shi ya dace, ita kuma qanin shi ya je neman ta, tasan Allah ya kare ta ne kawai dan Allah ya sani kullum sai ta nemi tsari daga zina, da illolin ta, musamman a wannan zamanin da zinar tai katutu a zuqatan mutane, kwallar ta ta mayar, tare da godewa Allah daya kubutar da ita,ta wanke bowl din ta aje, ta fito,daki ta shiga tai wanka, ta kwanta,bacci mai dadi ya dauke ta, Alhaji yazo yaita bugu yaji shiru, sannan ba ta saba rufewa ba, kada kan shi yai,ya koma bangaren Hajiya qarama, wadda har a lokacin batai wanka ba, daki ya nufa shima ya rufe ya kwanta, wayar shi ya duba yaga missed calls din Eamaan a jiyan, nan da nan yaji tashin hankali, dan ya tabbata hakan ne ya sata fush, wataqila shi yasa ta rufe qofa,ya qudurta kome zai faru zai shawo kanta, kuma zai qoqarin daina bin mata.


Wanj matsanancin ciwon baya ne yake damun Alhaji kwana biyu, wanda ya sa sai sunje asibiti anga me ya jawo hakan?.........







*nima zan so sanin me ya jawo hakan*😱



*wane na yasshigo mana gida ba ko sallama*😱😱

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment