Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

UMMAH KO SALMA


_NA A'ISHA HAMZA_ (MUAYSH GRAPHICS)


11/OCTOBER/2004


Bismillah


Godiya ta tabbata ga Allah (S,W,A) Wanda yabani ikon fara rubuta wannan littafi lafiya ina fatan yanda nafara lafiya Allah yabani ikon gamawa lafiya


Labarin Ummah ko Salma labarine kirkirarre ba rayuwar wani aka kwaikwayo ba koda kuwa tayi kamanceceniya data wani zai iya kasancewa domin duk abinda muka hasashe a rayuwa zai iya yiwuwa wani shi hakan ya faru dashi


Ina fatan masu karatu za'a min uzuri kusan dan Adam ajizi ne dole zai iya kasancewa nayi kuskure a wani wajen a cikin rubutu na ina fatan za'a fahinceni kuma aiman uzuri


Nagode sosai da wanda zamu fara karatu dasu da kuma waɗanda zasu karanta nan gaba kuma ina neman addu'ar ku akoda yaushe


Allah ya jikan iyayen mu da gafara Ameen 😭🙏






Umma umma umma sunan da taketa faman kira kenan tunda ta farka kwance take saman tafkeken gadonta wanda taketa faman juyi ita kaɗai sai kiran sunan ummah take idanuwanta gam suke domin ko buɗe su batayi ba


A firgice ta shigo dakin hannun ta rike da uniform da kuma school bag hada da sandal duka a ƙasa ta zube takalman ta juya ta ajiye jakar saman bedside drawer uniform din kuma ta ajiye su daga gefen gadon


A dabarbarce take furta kalmar kiyi hakuri bansan kin farka ba ina sauri ne nahaɗa miki breakfast nakawo maki da naga sun gama


Sai a lokacin ta fara ƙoƙarin bude lumsassun idanuwanta masu kama da wanda bacci bai ishe shi ba ta ɗora su akan yarinyar da taketa faman kwalawa kira


Kin kyauta shine kawai abinda ta iya furtawa kafin ta yunqura ta mike zaune tana ƙara lumshe idanuwanta hadi da hamma


Kasa kasa ta furta saina tuna maki abinda ya kamata ne tanajan tsoki kamar bata son furta kalma da sauri wadda aka yiwa magana ta haye saman gadon tareda zagayawa bayanta tana daga mata rigar jikinta sama


Saida ta cire mata rigar kafin taqarasa yin cilli da'ita qasa ta mike tsaye saman gadon kamar yadda ta cire mata rigar haka taja dogon wandon nata arsh silk ne yadin wandon daga gani kayan bacci ne masu tsada da ɗaukar ido wajen kyallin yadin


Ƙasa tay mata i dashi ya rage daga ita sai short da bazai wuce gwuiwowinta ba da suka fito santala santala sai havebest


Saida tagama taimaka mata tacire kayan kafin ta sauko ƙasa tareda miƙa mata hannu ta kamo ta itama ta ziro kafafunta kamar wadda batasan taka ƙasa haka ta mike


Sakin hannunta tayi a hankali take tafiya ta nufi toilet domin tayi wanka Saida ta rike handle kafin ta juyo ta dubeta tsaye ƙekam daga ƙasa har sama taqare mata kallo kafin tace karki bari yau nayi let a school saboda shiriritarki


Ikon Allah wai na cikin masai ke cewa na waje ka taka kashi kai tunda ga farko zaka fara gane wanene mashiriricin a cikin su amma ta haɗe rai ala dole kar aja mata let a makaranta oh to muje dai zuwa muga ya zata qare kunsan bani gani na kyalene ah to😆😆😆


Sunkuyar da kanta tayi ƙasa tace inshaa Allah bazakiyi let ba Saida ta shige kafin ta sauke ajiyar zuciya tayi waje kafin ta fito tadawo hannunta rike da faffadan tray wanda yake cike da kayan abinci kala kala iya dai abinda nake iya tantancewa a ciki akwai soyayyar kaza a banƙarenta sai kuma tea cup guda ɗaya yaji kayan hadi sai slice bread a cikin ledarsa sai kuma wainar ƙwai da aka soya a cikin plate sai noodles da wasu hadaddun warmers da bangane sukuma suwaye aka zubo a ciki ba


Dan madaidaicin table ta jawo ta ɗora kayan abincin a sama kafin ta koma gefe ta tsaya ba tareda ta fita waje ba


Fitowa tayi jikinta sanye da ɗan qaramin towel wanda ya bayyana santala Santalan cinyoyinta da wani qarami a hannun ta tana ta faman goge jikinta


Saida ta gama kafin tanufi mirror ta zauna batare da tace komai ba Umma tawuce daga bayanta tajawo hand dryer tajona jikin socket ɗin dakin Saida ta tabbatar ta busar mata da kanta bayan ta gama ta shafe mata shi da mai kafin ta bi illahirin jikinta tana shafa mata man a jikinta


Saida tagama tsaf tana zaune anan aka jawo dan madaidaicin table din dakin da aka jere shi da abinci a baki umma ta shiga bata shi tana ci kamar bata son taunawa tsaf tagama tace ta koshi uniform Umma ta dauko ta fara mika mata inner wears ita kuma ta juya baya Saida ta kammala sakawa tayi gyaran murya


A hankali ta taimaka mata ta saka uniform ɗin wanda ko arzikin scarp babu a cikin su sai riga da mini skirt wanda iya gwuiwa ya tsaya sai doguwar safa fara wadda zata kai inda skirt din ya tsaya daƙyar ta tattara mata gashin kanta da ribbom ta daure shi


Saida tagama shiryawa tsaf Umma ta dauko mata school bag dinta sukayo waje parlour suka fito tsaf yake a gyare sai masu aiki da suke ta shirya breakfast a wani dining table mai mazaunin mutum shida uku na facing uku


Tana gama umma na bayanta har suka fito wajen gidan parking space suka nufa kafin su isa saiga wani babban mutum ya fito daga motar ya buɗe bayan motar


Kafin ta shiga Saida yafara gaisheta Barka da safiya Sweety yauwa baba ta bashi amsa a taqaice Saida ta zauna kafin umma ta mika mata jakar daga ciki har zata juya


Muryar ta ta tsaida ita tana faɗin ina zakije waye zai ɗauka school bag din idan mun isa school din


Ƙasa ta kalla tana wasa da yatsun hannunta baba ne yayi saurin faɗin haba umma ke sai kace wata qaramar yarinya idan ta manta saiki dinga tuna mata yau Alhamis zakije tahfeez Koh


Bata dago ba har ya gama magana kafin yace karki damu sweety ni zan rakaki har aji inshaa Allah


Bata qara cewa komai ba tagyara zamanta kafin ya rufe mata motar ya koma mazaunin driver ya zauna


Saida suka fice daga gidan kafin umma tajuya da sauri takoma cikin gidan kamar yanda suka bar parlour bakowa a ciki haka tadawo ta same shi


Wucewa tayi dakin Sweety ta gyara mata shi tsaf duk da dama ba datti gareshi ba ta wanke toilet da inner wears din data cire bayan ta gama ta kwashe kayan da taci abinci tayi waje dasu ta kulle mata kofar


Sauri sauri take tafito tanufi hanyar fita daga parlour ɗin kamar daga sama taji ya ambaci sunanta ke umma kiran da tasan dole sai ya ɓata mata lokacin zuwa gida yanzu


Matashi ne da bazai wuce 19 years ba daga gani jikinsa yaji hutu fari ne sosai yanada dan saje kaɗan saboda an dan fara girma kuma jiki na shan hutu


Na'am ta amsa ƙasa ƙasa su biyu ne a saman dining ɗin suna cin abinci daga gani basu jin yunwa sai wani cakalkalashi suke kamar an musu dole


Meyasa ke bakijin magana umma dole ke sai ana tuna maki ba nace kidinga gyaramin dakina ba eye


Dayan da kamar baisan tana wajen ba wanda bazai wuce 17 years ba suna kama da Babban daga gani yaya da qanine su biyun yace ai kasan ta baiwar Sweety ce kamar don ita aka halitta ta baka isa ka sanya ta abu tayi maka ba indai Sweety na nan


Tsaki yaja yace to yau ko Daddy bazai iya tseratar dake ba bare wata Sweety maza ki wuce ki gyaramin daki na


Shegiya munafuka ana mata magana tana wani sumsum dakai qaramin ya faɗa yana ƙoƙarin mikewa


Juyawa tayi zuciyar ta babu daɗi kullum addu'a take batason haduwa da mutanen nan a cikin gidan nan yau gashi batayi tsammani ba sai suka haɗe


Karki kuskura Inga kin shiga dakin nan Saida ta sauke ajiyar zuciya kafin tace Alhmdllh a zuciyarta
ta juyo Nawwara ce tsaye hannunta rike da tea cup kayan bacci ne ma a jikinta daga kitchen ta fito taganta zata shiga dakin su Safwan


Budurwa ce amma zata kai irin 24 years dinnan tanada dirin jiki itama farace sosai amma ba kamar mazan ba tanada manyan idanuwa da dan hancinta qarami da yasha nose ring


Ba aikin Sweety kaɗai kike a gidan nan ba me zakije yi dakin su Safwan ko so kike kija mana zagi eyyee


Ah ah Anty Nawwara Saheeb ne yace lallai sai na gyara masa dakin sa taqarasa da in,ina… don tasan dole ne saiya hukuntata indai yasamu dama


Ido ya raina fata daga Saheeb har Safwan qarasowa tayi parlour tana ajiye tea cup ɗin hannunta saman stool


Wai kai Meyasa saheeb bazaka girma ba eyee dole kai saika nema mana magana a gidan nan koh to wallahi kufita daga idona daga kai har Safwan Meyasa bakujin magana ne


Wallahi Anty Nawwara ba ruwana yaya Saheeb ne yimin shiru gulmammen banza ta faɗa tana huci kamar zata kai duka


Ya daure fuska kamar bai taɓa dariya ba yana aikawa umma harara daga gefe yace kiyi hakuri Anty Nawwara bazan sake ba yafi maka dai idan kana neman zaman lafiya a gidan nan ah to tafada tareda juyawa ta dauka tea cup ɗin ta tayi upstairs tana nuna umma da dayan hannunta


Karna ƙara ganin wani ya sanyaki aiki a gidan nan kinyi in ba Sweety ba idan bahaka Ni dakene


Daga kai tayi alamar taji bata ƙara kallon kowa ba ta nufi hanyar fita tanajin sanda Saheeb yayi kwafa yana faɗin zamu haɗu saina nuna maki true colour ɗina bata bi ta kanshi ba ta fice


Shin wacece Umma ? Wacece Sweety? Ya rayuwar gidan take gaba ɗaya? Suwaye su saheeb da aka fifita Sweety akan su har aka fidda mata mai kula da ita wadda ba wanda ya isa ya sanyata aiki sai na Sweety? Wacece Nawwara ?


Yanzu wasan yafara domin wannan ake kira wasa farin girki koda kudinka saida rabonka


Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA


Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number 09131096058 ta whatsapp




________________




Bata wani sha wahalar samun napep ba tahaye layin nasu sai hayaniya yara ke tashi irin wanda basu zuwa makarantar nan domin unguwar daga yanayinta zaka gane cewa ta talakawa ne marasa ƙarfi


Dai-dai kofar gidan su ya sauketa ta sallame shi ta wuce ciki da sallama a bakinta tun daga soron gidan


Ai kuwa da gudu wata yar matashiyar budurwa tayo kanta wadda a shekaru zasu iya zama sa’annin juna


Oyoyo Umma oyoyo da murnar ta itama ta buɗe mata hannuwanta suke rungume juna Saida suka gama murnar ta saketa tana faɗin ni fushi nake dake ma umma


Ki kace zakije dani naga Sweety amma kika gudu kika barni ko riƙe hannunta umma tayi tana faɗin ki gafarce ni Amatuna mu shiga ciki yau zaki sha labari shiyasa nadawo da wuri gida ae


Zumbura baki tayi suka wuce ita lallai an bata mata rai a wani daki suka shiga labulen dakin duk ya yagalgale dakin ba ceiling saidai kwano kasan dakin kuwa duk ya farfashe babu komai cikinsa sai yan tsummokaransu a cikin wasu Ghana must go guda biyu sai yar qaramar katifa da bata wuce mutun ɗaya ya kwanta ba shima ba duka jikinsa ba saboda ta yage


Yar tabarmar dakin duk ta cinye akai suka zauna kowa tana nade kafarta Umma tace Amatu ina Mama da Baba ne ko bakowa gidan ne


Amatullah ta tabe baki tana faɗin kinsan hali yanzu suka gama faɗan kuɗin cefane ya fice yana masifa wai baida su itama ta fice wai zataje makota rance tayi mana girki


Umma tadan ɓata rai kadan don kwata kwata batajin dadin abinda iyayensu sukeyi kullum cikin faɗa da masifa suke sai kuma ta ɗan saki fuska tare da jan numfashi tace Amatu ina Abincin da aka kawo sati ɗaya daya wuce


Amatullah tace haba umma kiyita tsareni da tambaya kema fa kinsan amsar shi ake siyarwa ana cefane tunda baba dai baya bada kuɗin cefanen sai yaga dama


Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta kwance dan kwalin kanta sumar kanta da akayi mata Kalaba da'ita ta safko har saman bayanta duk ta yamutse don ko tsagar baka taɓa gani


Daga gefen dan kwalin ta kwance kuɗi ne a ciki yan dubu dubu har guda sha biyu Amatu ta zaro idanu tana faɗin ina kika samu kuɗi har haka Umma


Murmushi tayi to Nima tsareni zakiyi da tambayoyin naki ne to ki adana su kafin lokacin makaranta yayi yanzu ki tashi ga dubu ɗaya kije shagon saminu ki siyo taliya guda ɗaya ta qara mata dubu daya tace tayi kayan miya da sauran abinda za'a buqata tadawo da canjin


Idan kindawo ki hura wuta ki ɗora nikuma zan shiga cikin kasuwa na danyi mana siyayya abinda ba'a rasa ba da wannan dubu gomar


Da murnarta ta mike ta ziri hijab a tare suka fice suka bar gidan kowa ya kama hanya


Ba dadewa saiga Maman ta shigo lokacin bakowa gidan Amatu take ta faman kira ta duba ko ina bata ganta ba domin ta aiketa ta ɗan siyo masu wani abu su ci


Gajiya tayi tasamu kujera ta zauna tana ci-gaba da masifar tata wannan wace irin masifar ce kirkiri mutum ya ajiye ka kuma bazai dinga ci dakai ba itama yar jakar uban tazo kafin rana tayi ta siyo mana ko garin kwaki ne tunda nasamo bashin gidan Balaraba


Assalamu alaikum sallamar Amatullah ce ta katseta daga surutan da takeyi tana faɗin laa Mama kindawo kenan sakin baki tayi tana kallon hannunta data riƙe ledar taliya da kayan miya da mai hada su maggi komai ta siyo hada ɗan canjinta abinka ga cefanen talaka


Bata amsa sallamar ba ta katse ta da faɗin meya a hannun ki Amatu hannunta ta kalla kamar batasan menene ba sai kuma ta dubi maman tana Murmushi tace zan faɗa maki mama amma yanzu dai bari na hura wuta


Taɓe baki tayi tana faɗin to kedai kika sani Amatu nidai karki zamar min kamar Umma ki lalace kice zaki fara cida iyayenki duk da itama laifin ubanta ne


Karaf a kunnen Umma da take ta sauri ta dawo daga kasuwar tasu wadda batada nisa daga gidan su kuma tana fita napep tagani ta haye don Naira talatin ma yace tabashi yaqarasa da'ita


Ajiyar zuciya ta sauke tana jiyo Amatullah ba faɗin haba mama wai meye haka kinsan fa inda Umma take zuwa amma kuma kiyita cewa tana yawon banza


To inba yawon banza ba wane ɗan arziki kika taɓa ganin ace budurwa tana cida iyayenta…..bata kai karshen zancen ba Umma ta doka sallama


Amatu ce ta amsa tana faɗin yauwa Umma sannu da dawowa yanzu muke zancen ki da mama nake cewa tare muka fita naga kinyi sauri ma


Murmushi ta sakar mata duk da zuciyarta babu daɗi akan abinda tajiyo mama na fadi wallahi kuwa Amatu nayi sauri ko Allah ne ya taimake ni ina fita napep taqarasa dani yanzu ma naga wani zai shigo layin nan nabiyo shi shi yasa kika ga ban dade ba tana mika mata ledar hannunta gari yayi zafi


Mama kuwa ko kallon arziki bata isheta ba sai taɓe baki da takeyi karasawa tayi kusa da'ita tana faɗin mama Barka da safiya nadawo Amatu tace man bakinan shine nafita kasuwa


Lafiya kalau ta amsa mata a dakile bata damu ba don tasaba da halin maman dukda cewa batajin daɗin yanda take mata kwata kwata


Amatu da ta maida hankali wajen hura wuta saida tagama tafara fito da kayan da Umma ta siyo masu tana ta faman sakin murmushi ita kuma umma tana musu jajjagen kayan miya a turmi don suyi sauri su gama saboda rana tafara yi kafin lokacin tahfeez


Mama sai satar kallon hannun Amatu takeyi tana kallon abubuwan da umma tasiyo ɗin a ranta taji daɗi sosai saidai baƙin hali yahana ta nuna farin cikin ta a zahiri


Shinkafa ce dai yar hausa kwano ɗaya sai gero ta siyo rabin kwano saboda sunayin koko da safe sai ta siyo musu macaroni da taliya kowane guda ɗaya sai maggi da aka dan yimata hadin su a leda


Ta siyo musu abincin da zai dan kwanan musu biyu kasancewar basuda yawa a gidan kuma ita ba anan take zaune ba kuma duk randa mama bataga dama ba ko sunyi girki su biyu sukeci itada Amatu bata bawa Baba sai tace tunda yar bai kawo musu ba wallahi shima ba zaici ba


Saida suka kammala girkin kafin kowaccen su tayi wanka suka shirya sana suka zuba abincin suka ci a tare su biyu mama ta zuba nata sauran aka kwashe a wata yar qaramar kula saboda mama tace shi zasuci anjima kowa yasha ruwa sai ana tattali badon ganin akwai ba suyita zari


Kowa tagama shiryawa tsaf cikin uniform dinsu Purple Hijab da farin wando da riga hijab dinsu har qasa don ba sosai zaka iya hango wandonsu ba da scarp shima fari Saida sukayi sallar Azahar domin ɗaya ta wuce kuma biyu suke fara karatu a jere suka fito sukayiwa mama sallama suka wuce makaranta


A kofar gida suka haɗu da binta yar gidan Balaraba tana soya wainar fulawa a kofar gidan su da yake ga gida ga gida suke dasu tana ganinsu tare kuwa taci face tana yan habaice habaicenta


Oho dai munsan komai a yawon ta zubar ma ake nemo kuɗin zuwa makarantar aiba lada tunda kuɗin bana halak bane


Ita dai Umma bata tanka mata ba Amatu ce ta dura mata zagi tana faɗin ke yar gidan matsiyata wanda bakusan mutunci ba ke har kinada bakin da zaki cewa wani yana zuwa yawon ta zubar ciki nawa kika zubar da kuruciyarki


Ai kuwa kamar jira take ta mike zata fara nata bala'in Umma ta fizgi hannun Amatullah dama ta hango wata napep ta shigo layin ta sauke wasu ko ciniki bata tsaya ba suka faɗa


Ai kuwa ta qara zuga Binta ta cigaba da balbalin masifa matsiyata suka wuce ku uban naku da ko abinci baya baku sai kunzo kunci bashi kuma a ki biya sai daƙyar


Napep ɗin su ce ta tashi suka wuce tuni Amatu ta fashe wa Umma da kuka kingani Koh Umma duk laifin mama ne wallahi da take zuwa tana faɗawa makota sirrin gidan mu su bazasu bata mafita ba kuma ƙarshe azo anayi dakai har ayi maka gori


Daƙyar umma ta rarrasheta dama ita ba wuyar tafara kuka ka janye mata hankali da fitar Sweety don tasan yanda yake bala'in son a dinga bata labarin Sweety a haka har suka karaso get ɗin makarantar Umma ta sallama me napep ɗin suka shige ciki




Tofah ana wata ga wata ga gidan su Umma saidai ban fahimta ba Meyasa mahaifin su baya kula da rayuwar su kwata kwata ❓ Meyasa mama take aibanta Ummah ❓Meyasa Amatullah take bala'in son ayi mata labarin Sweety ❓Shin wai meke faruwa ne ❓ku biyoni domin jin waɗannan Amsoshin






Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA


Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number 09131096058 ta whatsapp




________________




Har cikin makarantar Saida Baba driver ya shigar da'ita tukun ya buɗe mata ya ɗauka jakarta


Duk yadda za'a tsara kalamai wajen faɗin tsari da haduwar makaranta baza'a iya fasalta ta ba saboda tsabagen kyau da take dashi


Wannan shine kallo ya koma sama tunda suka shigo makarantar idon dalibai masu zuwa makarantar yadawo kan Sweety hankalin ta kwance don bata su takeyi ba ta karɓa jakar ta daga hannun baba driver yace tabari ya kai mata tace ah ah bata yarda ba ai yabata kawai zata iya dauka


Badon yaso ba ya mika mata jakar amma girmama manyan da takeyi ba ƙaramin burgeshi yakeyi ba komai kankantar ma'aikatan gidan su indai tasan kai Babba ne zata mutuntaka


Kafin ta karasa ajiin su ta baya taji an rungume ta ko batayi magana ba tasan mutum ɗaya ce duk girman makarantar zata iya mata haka


Bata juyo ba tace Anam kinaso kimin squizing da uniform koh murmushi tasaki don jin tagano ta dukda tasan dama hakan ce zata kasance


Sorry Sweetyna ta xagayo ta gabanta sukayi hugging juna kafin suka ruke hannun juna suka shiga class tare


Sit ɗin sweety a gefen na Anam suke zaune gaba ɗaya ajin basu wuce takwas ba a cikinsa daga gani kowa a cikin su yanaji da kansa da kuma dukiyar ubansa saidai ace wani yafi wani


Tunda suka shigo sauran yan class ɗin suka fara tasowa suna zuwa suna

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment