Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hugging Sweety da Anam suna musu Barka da safiya banda mutum ɗaya a cikinsu wadda tunda taxo take danna wayarta hankali kwance ko kallonsu batayi ba


Cikin zafin rai Anam ta mike tana faɗin waike Nasrin me kike takama dashi ne dagowa tayi tana zare lulu eyes dinta akan Anam da take mata magana


What do you want from me ta faɗa tana juya hannunta guda ɗaya idonta akan Anam


Har zata buɗe baki tayi magana suka haɗa ido da Sweety ta lumshe mata ido tana sunkuyar dakai hakan yasa ta fahimta tana nufin tayi shuru ta kyale ta


Ƙwafa tayi ta juyo ta zauna tana ƙara haɗe rai domin ba tun yau Nasrin take musu haka ba amma Sweety ta hana ayi mata magana


Nasrin taja tsoki tana faɗin aikin banza har tayi shuru tunda uwarta ta harareta wani kallo Sweety ta juyo ta watsawa Nasrin mai alama da gargadi ta kiyayi harshenta


Tuni ta kama kanta don ko iya kallon Sweety ma magana ne ba sai ta buɗe baki ba don idan ta buɗe mutum zai gane waye shi


Teacher su ne ya shigo suka shiga gaisawa dashi malamin nasu kwata kwata bayajin Hausa ko kaɗan nan yake faɗa musu an saka date ɗin Exam din su ta gamawa baki ɗaya ba ƙaramin farin ciki sukayi ba saboda kowa dama yanada burin ya gama secondary ya cigaba da wata wasu suna hasashen kasashen da zasu tafi karatu


Saida lokacin break yayi suka fita suka je cafeteria domin cin Abinci wajen zaman mutum huɗu suka zauna Sweety tana facing Anam sai Suraj kusa Da ita shikuma yana facing Khadijah da take kusa da Anam


Kowa abinda yake so aka kawo masa koda suka gama a hanyar su ta komawa aji Nasrin tana tafiya tana wani yanga da gangan ta biyo ta kusa dasu don basu ganta ba ma sai da sukaji an bangaje su Sweety tayi taga taga zata fadi kawai suka jiyo dariyar wasu Juniors a kusa dasu


Juyawar da Anam zatayi ta faska mata mari har saida taga wani kyalli nawucewa ta wajen idonta kafin Sweety taqara mata guda ta gefen tuni yaran nan suka nema hanyar guduwa don sunga kallon da Anam take watsa musu


Ai kuwa basu sha ba don Anam tasa suraj da Khadijah akan su kamo mata su sai taji yaran ubanwaye a school ɗin


Nan Nasrin ta zube tana kuka akan sun mareta bayan ita ta tsokane su da taga kukan bamai fissheta bane ba saita nufi principal's office


Tana zuwa ko sallama babu ta faɗa masa tana rera masa kuka hankali a tashe yake faɗin Nasrin what's wrong with you kin shigo ko sallama babu kuma kinata kuka


Take faɗa yan class din su suka mareta kuma batayi musu komai ba


Su waye suka mareki ya faɗa yana mikewa har sun kai kofar fita yayi gaba tana bayansa tace su Anam ne da Sweety a sukwane ya juyo yana kallonta ya ɓata rai


Haba Nasrin kinyi hauka akan me zaki shiga sabgar su har su mareki ni yanzu bansan ya zanyi dake ba to nidai nasan koda Anam zata mareki hakanan to banda Sweety bcos I know her batada matsala Sweety saidai idan tokanar ta kikayi koh fadi gaskiya dai Nasrin yaqarasa yana juyawa cikin office dinsa tareda jan kujera yana zama


Ɓata fuska tayi bata tsaya sauraren shi ba tayi waje batada wata mafita data wuce ta koma class ta zauna kawai hakan tayi


Tunda ta shigo ido ya dawo kanta fuskarta tayi jaaa saboda kukan da tasha wasu daga cikin su har dariya suke mata suna mata Allah ya ƙara maganin mai neman faɗa kenan


Komawa tayi seat dinta ta zauna ta kwantar da kanta saman desk din gabanta tana cigaba da matsar ƙwalla


Kamar daga sama taji an dafa kafadar ta ta dago da niyar tayi masifa amma kuma saita fasa ganin Sweety a kanta


Murmushi ta saki tareda shafa kuncinta wanda yayi ja saboda marin da tasha sai kuma ta numfasa tace kiyi hakuri Nasrin


Kamar saukar aradu haka taji saukar maganar a kunnenta don mamaki har ƙara buɗe idanuwanta takeyi wai taga ba mafarki takeyi ba Sweety ce take bata hakuri da kanta


Saida ta lumshe idonta kafin ta buɗe takara cewa kiyi hakuri Nasrin laifinki ne kuma ni banyi niyyar marinki ba kin ɓatamin rai ne saboda bana shigar harkanki bansan me na tare maki ba kikejin haushi na amma don Allah kiyi hakuri marin da nayi maki bada son raina hakan ya faru ba


Gaba ɗaya ajin kowa ya nutsu yana sauraren ta dukda bada ƙarfi take Maganar ba amma saboda su a iya shekarun da sukayi da Sweety zasu iya ƙirga sau nawa tayi doguwar magana irin wannan


Ita bata fira da kowa ko Anam da suke shiri saidai ita tabata labari wani tayi Murmushi idan abin ya kai na tayi dariya kuwa saidai kaga jerarrun haƙoranta farare amma bazata wangale baki tayi dariya ba har wani yaji


Akwai shakuwa sosai tsakaninta da yan ajinta dama Nasrin kaɗai ke bata matsala kuma bata taɓa tanka mata ba saboda bata ita takeyi ba yau ma ƙarshe ta kaita saboda batason raini duk abin da mutum zaiyi shi yasani amma kar ya rainata


Daƙyar Nasrin ta kakalo murmushi har zuciyar ta taji daɗin hakurin da Sweety tabata dukda cewa laifin ta ne itace ta tsokaneta amma sai gashi tazo tabata hakuri sai yanzu ta yadda da cewa Sweety batada girman kai, a halitta ne kawai take da zati da kuma kasancewar ta yar Babban mutum wanda duk makarantar babu wanda ya kai ubanta jida kuɗi da mulki da siyasa


Kema kiyi hakuri Sweety nasan laifina ne nice nafara tsokanar ki amma inshaa Allah komai ya wuce


Hannu Sweety tabude mata alamar su rungume juna tunda komai yawuce har sauri take wajen mikewa don ta rungume ta kamar jira suke yan ajin sai ji kake rap,rap,rap suna tabawa domin sun burgesu


Anam fa rai ya ɓaci don ba haka taso ba duk duniya ba abinda ya tsana sama da wani yayi kusanci da Sweety sama da'ita batason taga kowa ya rabeta bataji daɗin shirin da sukayi da Nasrin ba dukda Sweety Saida tace mata suzo subawa Nasrin hakuri tace wlh ita bazata je ba kawai ta kyaleta


Kowa ya kama sabgar shi cikin class har lokacin dawowa break yayi Teacher su ya shigo suka cigaba daga inda suka tsaya


Gaba ɗaya yan matan ajin su duka su biyar ne Daga Sweety da Anam sai Khadijah da Nasrin sai Naomi sai maza Uku Suraj ne kaɗai musulmi a cikin su ɗayan twins ɗin Naomi ne Ruben sai Jacob


Ƙarfe Biyu suka tashi tare da Anam Sweety suke fitowa amma kafin ta ɗauki jakarta ma har Anam ta fice girgiza kai kawai tayi saboda tasan zancen fushi take da'ita saboda ta bawa Nasrin hakuri


Kowa ya fita sai Sweety da takejin jakar tata ma tayi mata nauyi har sauri take wajen faɗin kawo jakar na tayaki Sweety juyowa tayi Nasrince tsaye bayanta


Ah ah kibarshi kefa naki jakan wazai daukan miki
Nakai nawa mota nadawo duba littafi na dana bari saman desk ne sai naga baki fita ba amsa tayi suka fito waje tanata mata surutu


A bakin get suka rabu dama Bana driver tun ɗazu yazo yana jiran fitowar ta su wuce gida ban kwana sukayi akan idon Anam da take ta jiran taga ta inda Sweety zata fito taga shuru shiyasa taki shiga motar gidan su ta tafi ai kuwa ganinsu tare da Nasrin yakara bata mata rai taja tsaki ta shige mota


Kuka ta fashe dashi gaba ɗaya hankalin driver ta ya tashi Anam me yafaru dake kike kuka don Allah idan wani abu akayi maki a school ki faɗamin tun kafin muje gida kinga Daddyn ki zaiyi min faɗa yace sakaci na ne Koh


Dogon tsaki taja tana faɗin dallah ka rabu dani kabarni naji da abinda nakeji haba zaka dameni da surutunka


Shuru yayi bai ƙara cewa komai ba don yasan yanzu Anam zata fara zazzage masa masifarta babu ruwan ta da girman shi bare da take ganinshi saurayi ne don ita tace batason aikin tsoho


Ba yanda batayi da Sweety ba akan a canja mata driver amma taqi tace tabar mata Baba tsohonta tana son driven ɗin sa


Tunda Sweety ta shiga Mota takejin faduwar gaba ji take kamar wani abu zai faru da'ita ko waninta Amma abinka ga mai rashin ilimin addini bata san tayi addu'a ba kawai dai sai ta kunna waqa tasaka speaker ta qureta wai ko zata daina jin abinda takeji


Baba driver baki abin magana yace to Sweety yau kuma casu akeji kenan Murmushi kawai tayi ya hango ta ta mirror dake a gaba motar tasu tana baya


Toh Anam kukan me takeyi ne ❓ kishin kawarta takeyi kenan ko me ❓Wacece Anam ɗin ma ❓ga Nasrin ta shiga rayuwar Sweety ya kuke ganin zata kaya a tsakanin su da Anam uwar kishi ❓ ga Sweety na jin faduwar gaba tunda suka shigo mota me yajawo hakan ❓ ya akayi Sweety batada ilimin addini ne ❓


Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA


Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number 09131096058 ta whatsapp






________________




Ƙarfe shida suka tashi daga tahfeez bakin makaranta ya cika da yan makaranta wasu anata zuwa daukar su wasu kuma suna wucewa gida a kafa irin wanda basuda nisa


Basu nema napep ba saboda babu kuɗi a hannun su dama canji ne ɗazu Umma ta biya musu suka hau gashi Amatullah tace ma Umma zazzaɓi takeji har jikinta yafara kyarma


Ba yanda suka iya haka suka kamo hanya suka taho gida a kafa gashi sunada yar tazara


Gab suka da gida aka fara kiraye kirayen Sallah maghrib jikin Amatu yayi tsauri hakan yasa saidai Umma taga ta rinjaye ta dama ita ta riketa suke tafiya a hankali kicaaa suka tafi ƙasa gaba ɗayan su aiko Umma taji jiki don Saida ta bugu jikin wani dutse don ita Amatullah ashe suma tayi


Tashin hankali wanda ba'a sanya mashi rana inda suke babu mutane sosai hakan yasa takara rudewa ai kuwa duk napep ɗin da tazo wucewa take ƙoƙarin tarewa saboda wannan hanyar ce kaɗai mafitar ta daƙyar tasamu wani ya taimaka mata don ko iya ɗaukar ta bazatayi ba saidai ya kama mata


Ba dadewa suka iso Kofar gidan nasu saboda dama gab suke da gida da gudu Umma ta shiga tana haki tana faɗin mama mama mama Sallah take sallamewa kota ƙarasa sallamar ma oho mata tamike zumbur tayo waje


Ke lafiya kikemin kiran mafarauta dakyar tace Amatullah ce tana nuna hanyar waje ai bata tsaya taji karshen zancen ba tayi waje ko takalma babu


Gida suka shigo da ita Umma ta tambaya me napep ɗin nawa zata bashi don dama batada su arowa zatayi a shagon saminu tabashi sai yace ta barshi kawai Allah yaba yar uwarta lafiya tace Ameen tayi masa godiya sosai ta koma cikin gidan


Mama tasa Amatullah gaba sai kuka takeyi Umma ma dai hawayen ne cike a idanuwanta amma batason mama taga raunin ta kuma a rasa mai rarrashin wani a cikin su haka sukayi jugum jugum babu mai ko sisi koda zuwa chemist ne bare kuma Asibiti


Baba ne ya shigo gidan babu wanda yaji shigowar su sai dai sukaji shi a kansu yana faɗin jugum jugum ɗin ubanme akeyi anan


Amatullah ce batada lafiya baba Umma ta faɗa tana duban shi jimm yayi kafin yace to ai wannan sai dai muce Allah yabata lafiya kawai tunda ba kuka ya kamata a zauna anayi ba


Wallahi malam kaji kunya ni wallahi nafara tantama a kanka wannan wane irin abu ne ka dinga nuna bambanci a tsakanin ƴaƴan ka da ace Umma ce bata da lafiya kana kyarmar jiki ko baka da kuɗi zaka nemo bashi


Murmushin mugunta yayi kafin yace to ai sunada bambanci a gareni ke bakiga alama ba kema ai abin a tuhumeki ne ke Meyasa kike nuna musu bambanci eye ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya irin na yan duniya ba wanda ya lura dashi


Jan majina tayi tana faɗin nidai wlh malam an cuceni kuma bazan yafe maka ba indai yata tarasa ranta sanadiyyar wannan baƙin halin naka


Me kike nufi da an cuceki mutuniyar banza kawai nanfa suka fara kace nace irin wanda suka saba


Babu wanda yaga fitar ta saboda batason tashin hankali tabar gidan kuma tana tunanin hanyar da zata bi domin ta nemawa yar uwarta tilo guda ɗaya magani




Tunda tadawo daga school cikinta ko ruwa bai gifta ba kuka take kawai tarasa meke damunta wanka ta fito ba sallah babu salati ta saka kaya marasa nauyi ta kwanta wayarta tajawo tana dannawa ta shiga TikTok ko tarage damuwa saidai komai zafi yake ƙara mata


Mikewa tayi taje gaban mirror tana kallon kanta why damuwa why Meyasa zakizo wajen duk abinda ya kamata inyi don kifita daga zuciyata kinki tafiya ihuuu tasaki kamar diyar kafirai tafara dukan kanta hannunta ta ɗaga tana kallon su wai ko wani ciwo taji bata sani ba tana ta yan dube dube tana sambatu ihun ta ƙara saki mai raxanarwa


Kamar ihuu nakeji daga sama Koh Saheeb ya faɗa yana kallon Safwan dake ta faman game a laptop dinsa


Banza yayi dashi can kuma sai cewa yayi yana wuce waccan zararriyar yarinyar da idan ta tashi haukanta kamar mai aljanu


Saheeb ya gyara zaman shi yana faɗin wai kai Safwan baka tunanin akwai abinda ke yawan sanyata tana irin wadannan abubuwan


Taɓe baki yayi kafin tace to menene banda gata da yayi mata yawa ai wallahi gata ke damunta yaya Saheeb kasan idan daɗi yayi yawa sai kace Allah kasheni in huta


Wanka ta fito tana shiryawa tun tana toilet take jiyo ihun ta hakan yasa take ta faman sauri don taje taji menene


Gudu gudu sauri sauri ta nufi dakinta da yake duka dakunan su a upstairs suke koda ta shiga cikin jini ta isketa hannunta yanata zubda jini ga mirror data fasa ya tarwatse cikin dakin


Subhanallah Sweety me yake damunki har haka bata dube ta cikin tsawa take faɗin ki fita Anty Nawwara banason ganin kowa a kusa dani gaba ɗaya idanunta sun rufe gam sai cizon labba takeyi har tafara fasa lebenta na ƙasa hawaye sharkaf da suka jike fuskarta kuma basu daina sentry ba


Duk yadda nawwara taso ta shawo kanta abun ya faskara haka ta haƙura ta zubawa sarautar Allah ido


Fitowa tayi ta sauko parlour tana faɗin wai Saheeb ina umma ne bata dawo ba daure fuska yayi don shi har yanzu haushinta yakeji akan abinda yafaru da safe


Eh bata dawo ba ya faɗa yana kare tamke fuska tsaki taja kafin tace kiramin ɗaya daga cikin yan aikin gidan nan


Mikewa yayi ita kuma tasamu waje kusa da Safwan ta zauna tana faɗin wannan wace irin masifa ce yarinya tabi ta ruɗe a kasa gane kanta


Halima ɗaya daga cikin masu hidima da gidan ce tazo tana faɗin ance kina kirana bata kalleta ba tace kije dakin Sweety ki gyara mata kuma karki sake ki tanka mata kawai kiyi abinda nace


To tace ta miki hanya tun a kofar dakin takejin kukan ta ƙasa ƙasa kasancewar tadaina ihun da takeyi


Kwance take saman gadon ta tayi rubda ciki baka iya ganin fuskarta saidai hannuwanta data ware su gefe da gefe tana raira kuka mai tsuma zuciya


Kamar yanda aka bata Umarni bata tanka mata ba ta fara neman fara aikinta kamar daga sama taji tana faɗin Halima kifita daga dakin nan idan bahaka ba natashi tabbas zan illataki


Abinda yaso ya rudar da'ita shine ba'ita kaɗai bace mai aikin gidan to tayaya har Sweety tagane itace ta shigo bayan ta bata baya kuma rubda ciki tayi


Da bataji ba sai ta cigaba da tattare manyan mirror da yake daukuwa zata fita dasu bataji motsinta ba sai dai ganinta tayi a gabanta


Zara zaran eyelashes dinta sun sauko Kasan idonta sakamakon rufeshin da tayi ruwan hawayen daya jikasu ne yasa suka ƙara kwanciya luff


A razane take ƙoƙarin mikewa ai ko kafin tayi wani yunƙuri Sweety ta danne ta kanta ya bugu cikin glass ɗin


Wata azababbiyar ƙara mai razanarwa Halima ta saki wanda yajawo hankalin yan gidan tun daga kan Nawwara Saheeb Safwan har yan aikin gidan ba'a barsu a baya ba yanda kasan ana yar tseral haka suka nufo ɗakin Sweety


Tashin hankali gaba ɗaya ta farfasa mata fuska da mirror ɗin gashi ta damki wuyanta sai wujijjiga ta takeyi tun ihunta na fita har muryar tafara disashewa an rasa mai ƙarfin halin da zai karɓe ta


Abu tun anayi kamar wasa duk wanda ya rabesu komai ƙarfin mutum haka zatayi cilli dashi kamar pillow


Da suka ga abin babu nasara Nawwara tace da Safwan ya kira mata Baba mai gadi Saida yazo daƙyar ya kwaci halima a hannun ta kafin ya ruketa yafara mata karatu tana ihuu har ta lafa


Yan gidan fa sunga tashin hankali yau tunda suke da Sweety bata taɓa irin wannan haukan ba dukda dama idan abin nata ya motsa tanayi tayita ihu tana kuka tana farfasa abubuwa amma yau abin yaci tura


Tunda aka samu ta lafa Nawwara ce ta gyara mata dakin nata don yan aikin gidan a tsorace suke ganin illar da tayiwa Halima ƙarshe Saidai aka wuce da'ita Asibiti


Tunda yayi mata addu'a nan bacci mai nauyi yayi awon gaba da'ita lura da hakan ne yasa Nawwara ta dauko first aid ta gyara mata hannunta inda taji ciwon aka saka bandage akasa plasta bayan an goge shi da hydrogen hada allura tayi mata ta tetanus


Tunda Nawwara tagama gyara komai bata ƙara lekowa ɗakin ba saida aka kira sallah Maghreb kafin ta leko taga ko ta tashi still bata tashi ba taja mata ƙofa takoma dakinta


Ba yanda ta'iya hakan yasa bayan ta gama shan kukanta a soro tayi waje napep ta tara ta gaya mata inda zata kaita uniform ɗin jikinta dai sune har yanzu dasu ta fito saboda halin da take ciki


Dai-dai get ɗin gidan tace ya ajiye ta saboda tasan baza'a barshi ya shiga ba ɗaya daga cikin Sojojin da suke tsaron kofar tacewa yabata kuɗi ta manta jakarta a gida ba musu ya zaro dubu daya yabata tabawa mai napep yana ƙoƙarin bata canji yaga ta shige yana canjinki baiwar Allah tace barshi


Kowa ya lura da halin tashin hankalin da take ciki ba kamar yanda suka saba ganinta ba a natse amma yau a firgice ta shigo musu tunda baba driver ya sallame sallah yaxo bakin get tareda ɗaya daga cikin masu kula da flowers ɗin gidan sunata fira


Bata lura dasu ba ah ah Umma umma baba driver ne yaketa faɗan sunanta batasan ma yanayi ba


Allah sarki Umma yanzu haka a jikinta taji cewa Sweety ba lafiya shiyasa duk tabi ta ruɗe ya faɗa yana kallon idi mai kula da flowers ɗin jinjina kai kawai yayi alamar gamsuwa da maganar baba driver ɗin


Babu kowa a parlour kasancewar basu cika zaman parlour ba idan dare yafara kowa dakinsa yake shigewa


Dakin ta kwankwasa shuru ba'a amsa mata ba tayi knocking har tagaji da tsayuwa don sweety tahana a shigar mata daki ba tareda tabada umarni ba don madai yawancin ko da yaushe suna tare da juna


Handle ɗin ta murda tareda kutsa kai cikin dakin kwance take idonta a buɗe ta kalli sama kallo ɗaya zakayi mata kaga daga dazu zuwa yanzu ta rame


Yanayin tashin hankalin da umma take ciki ne yasa bata fahimce hakan ba


Sweety iñata knocking baki tanka ba kuma naga idonki biyu ta faɗa murya na rawa can ƙasa ƙasa tace mata ai tunda kin shigo ina saurarenki


Tasan halinta idan sarautar ta motsa duk da dama ita ba mai son magana bace shiyasa batayi tunanin komai ba tafara kora mata jawabi


Wallahi dama Amatullah ce ba lafiya gashi Baba baya gari toh mama kuma babu kuɗi a hannun ta munata kiran layin Baba baya shiga don ya turo mana kuɗi toh kuma naga banida wata mafita shine nace bari nazo na faɗa miki


Don Allah kiyiwa Abby magana ko cikin Albashi na ne na watan gaba a bani wani abu


Yanayin yanda take maganar kaɗai zai tabbatar maka bakomai ta faɗa gaskiya ba kawai tanason kare mutuncin iyayen tane


Saida taja dogon numfashi kamar bazata tanka ba can kuma tace kiduba cikin bedside ATM yananan banida cash


Har sauri take karasawa budewa tayi ta zaro shi kafin takara dubanta Sweety nawa zan cira ta faɗa tana dubanta da kyau sai yanzu ta danga alamun damuwa a fuskar Sweetyn gaba ɗaya sai taji bataji daɗi ba


Kije kawai duk abinda ake buƙata a biya mata har ta juya sai tadawo tana wasa da yan yatsunta wanda hakan ya zame mata dabi'a idan tanason yin wata maganar


Da akwai wata matsalar ne ta katse mata zancen zucin da takeyi da sauri ta dago tana faɗin bakomai kawai dai naga yanayin ki kamar bakijin daɗi ne shiyasa nake so na tambaye ki


Dan murmushi tayi wanda bai kai zuciya ba saboda damuwar da take ciki tace karki damu Umma ba abinda ke damuna kije ki kula da Sister ki


Kibari saita warke saiki dawo godiya tayi mata sosai kafin ta juya ta wuce gida sai da zata fito suka gaisa da Baba driver nan yake faɗa mata rashin lafiyar da Sweety tayi


Gaba ɗaya sai taji bataji daɗi ba kuma ta tausaya mata duk da dama ta dade tana mamakin rayuwar yarinyar ba abinda ta nema ta rasa saidai tana kuntata kanta sosai


Kamar taje takara ganinta takeji tayi mata sannu don tasan akwai abinda take da buƙata a yanzu amma itama batada halin yimata saboda jikin Amatullah da take neman agaji da wuri


Saida aka kammala sallar isha'i kafin Allah yabata damar isa gidan nasu Bata iske Baban ba sai Mama da ta idar da sallah taketa faman kuka


Mama naje gidan ne na karbo albashina na watan gaba muje Asibiti a duba Amatullah


Taji daɗi har ranta har takasa boyewa dukda haushin umma da takeji a ranta yanda ta tafi tabarta haka ta sameta har ta mimmike yanzu saboda ruwan da mama tayita zuba mata wai da tunanin zata tashi


Basu wani ɓata lokaci ba suka tafi Asibiti sun dade ana dubata saidai likitoci sukace musu wannan gaskiya sun kasa gane Asalin me yake damunta


Basu gajiya ba suka tafi wata Asibitin nan ma haka akace musu kuma su basa duba mutum dole sai sun san me yake damunshi to ita duk gwaje gwajen da akayi mata sun nuna tanada koshin lafiya


Wani babban doctor ne yabasu shawara akan su nema na Hausa wala,alla adace saboda yana tunanin ko Aljanu ne


Mama tasha kuka kamar idonta zai fita ba yanda suka iya haka suka kwaso kafa suka dawo gida


Umma ce tayi tunanin ko ta gwada yimata addu'a ai kuwa haka tayi ta yayyafa mata a fuska ta rike kanta mama ta taimaka mata tayi mata wasu addu’o’in daga haka sai sukaji tanajan numfashi daƙyar tana wani uban nishi kamar ranta zai fita


Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba Umma bata gajiya ba nan tafara raira mata Qira,a Alqur'ani kan kace me yarinya ta burkice sai kuka sai ihu buge buge nan fa suka yarda da zancen wannan doctor aljanu ne


Daƙyar suka samu tadawo hayyacinta duk budurin da akeyi fa Baba ya ware bayanan baisan ma anyi ba don hakan bai dameshi ba


Bacci ne mai nauyi yayi awon gaba da'ita Saida mama ta canja mata kaya suka kwantar da'ita


Allah sarki rayuwa idan bakada lafiya mahaifiyar ka

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment