Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai girmanka haka zata maka wanka ta canja maka kaya ta kula dakai tabaka abinci a baki ya Allah ka jikan iyayen mu da rahama 😭 wanda suke raye Allah ya qara musu lafiya da nisan kwana Ameen 🙏


Sai a lokacin nutsuwa tazowa Umma ta tashi tayi sallar Maghreb tayi isha'i ta dade kan sallaya tana addu'a akan Allah yabawa Amatullah lafiya abokiyar firarta yar uwa ɗaya tilo da take da'ita sana tayiwa iyayenta addu'ar Allah ya haɗa kansu su daina wannan rigingimun kafin tayiwa Sweety addu'a domin bayan waɗannan mutanen kuma sai Sweety da iyayenta take bala'in ƙaunar su saboda sun mata abinda bazata manta dasu ba daga ƙarshe tasaka duk Musulmin Allah




________________




Wata irin Dariya ya kwashe da'ita wadda alamun ta na marassa imani ne don ko a dariya akwai ta hankali akwai wadda da kaji ta kai kasan ta Mugayen mutane da babu Allah a ransu ne


Ai dole gyada tayi mai in takiya tasha matsa ni ba ƙaramin shaidani bane ba kuɗi nasaka agaba kuma sune rayuwa ta jikake hahahahaha an ƙara babbakewa da wata dariyar


Wayace manne a kunnen sa hakan zai tabbatar maka da cewa a waya yake magana da wani mutumin


On the other hand yace
Ni shaida ne kai shadani ne Mugu bakada tausayi ko kaɗan kuma bai kamata kayi tausayin ba a wannan harkar


Hakane mutumina ya faɗa kamar mai rada can kuma suka ƙara fashewa da wata dariyar


Ni kaina saida na tsorata da dariyar nan tasu don gani nake dani suke😂 amma sai naga aini banyi a bin dariya ba ko 🤸😂


Gafa wasu shaidanun sun shigo mana cikin labari😲ikon Allah 🤔 su kuma ko suwaye ❓ me suke ma dariya ❓waye kuma Mugu da yake kiran kansa da shaidani ❓dawa yake waya kuma ❓


Muje zuwa abin bana wasa bane ba 🏃 don baza'a barni a baya ba


Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA


Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number 09131096058 ta whatsapp


________________




Babu irin kiran da batayi wa layin Sweety ba amma ba'a ɗauka hakan yasa hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba daga karshe ta yanke shawarar kiran Nawwara don taji me yake faruwa don dama kwanakin nan hankalin ta ba'a kwance yake ba


Saida tayi ringing har ta katse ba'a ɗauka ba tana ƙara kira tana shiga aka daga kafin tace komai daga ɗayan ɓangaren tace


Ammi kin kira ina wanka ne wallahi Inayini lafiya qalau Nawwara ya kuke


Alhmdllh ta amsa tana ƙoƙarin zama kan gadon ta


Dama na kira ne naji ko lafiya yau kusan sati ina kiran Sweety a waya bata ɗauka ko kuma ayi rejecting call ɗin wani lokacin kuma wayan switch off Shine na nace bari na kiraki naji ko lafiya


Ah lafiya lau Ammi inajin ko tace min wai tayada wayan ne amma xanje namata magana sai naji


Murmushi Ammi tayi tace ton amma Nawwara taya Sweety zata yada wayarta bayan kinsan nace maki ina kira ana yankewa kuma idan ta yarda ita ai wayar Sweety kinsan bata satuwa ga wani Koh


Murya na kyarma ta furta eh….haka….ne….Ammi zanje dai na duba naji ko lafiya kafin takarasa taji duff alamar an kashe wayar


Tashin hankali ta faɗa tana kallon wayarta da kiran ya yanke yanzu fa matar nan zaka iya ganinta a ƙasar nan gobe ta faɗa tana mikewa safa da marwa tafara yi domin tasan idan tazo ta iske Sweety a halin da take ciki akwai damuwa


Saida tagama yanke shawara a zuciyarta kafin da sauri ta ɗauki wayarta ta dannawa wata number kira bugu ɗaya aka daga nan sukayi magana wadda ni kaina banji me akace ba saida suka kammala naga tana Murmushi alamun jin daɗin samun nasara


Tunda ta farka yau take faman neman wayarta duk inda take tunanin ta tagama bincike bata ganta ba hakan yasa ta fito parlour da tunda abinnan yafaru bata ƙara fitowa ba saidai Nawwara ta kai mata abincin a dakinta


Su uku ne a kan dining da alamu launc sukeyi bata bi ta kansu ba kawai tasamu waje kan 2 seater ta zauna tana binsu da kallo ba ƙaramin burgeta sukeyi ba kasancewar su kullum cikin farin ciki ba Kamar ita ba


Tayi nisa cikin tunaninta taji an kulle mata ido ta baya murmushi tasaki wanda har saida sautinshi ya fita kafin tace Anam


Sakin idonta tayi ta dawo ta gabanta ta rungume ta I'm really missed you alot Sweety kinbani wahala iñata kiran layin ki but sometimes switched off something number busy I don't know why ta faɗa tana aika mata da harara


Sorry Anam yanzu gani ai zuwan bazata haka ta faɗa tana mikewa akan su shiga ciki


Nawwara ce ta katse su da faɗin Anam ba gaisuwa da ɗan gudunta ta nufeta tana faɗin sorry Anty Nawwara wallahi nayi missing Sweety ne shiyasa ban san kuna dining ba


Buɗe mata hannuwa tayi ta faɗa kan kirjinta sukayi hugging juna tightly kafin tace mu bakiyi missing namu ba shiyasa ai ko ganin mu bakiyi ba takai ƙarshe tana sakin ta


Wallahi bahaka bane Anty Nawwara kuma nayi kewarku sosai daganan suka gaisa dasu Saheeb suka haye sama


Sun dade suna dan taɓa fira kasancewar ma saidai Anam keta zubarta tana bata labarin school bayan data daina zuwa har wajen sati


Saida ta tambaye ta duk yan ajin nasu tace suna lafiya sai wajen Maghreb Anam tace zata tafi Sweety ta rakata har bakin mota


Har ta buɗe zata shiga mota taji an ambaci sunanta Nawwara ce ta fito hannunta riƙe da Bag guda biyu ɗaya mai tambarin (HAJIYA UWANI PERFUME AND SCENT) turaruka ne cike da ledar tun daga kan Humra baka da fara ga kuma kolocca da turaren wuta tace duk ta kaima Mamynta ƙaramar kuma an rubuta (MUAYSH RESIN) Sarka ce da yan kunne masu kyau da karko a ciki sai yar ƙaramar jotter na rubutu an saka Anam daga bangon jotter ɗin


Sosai tayi mata godiya ta karɓa suka wuce Sweety taji daɗin kyautar da Nawwara tayiwa Anam sosai Saida ta koma ciki ta kwanta laptop dinta tajawo ta ci-gaba da kallon wani drama daga karshe dai nan bacci yayi awon gaba da'ita ba sallah babu salati


Karshe saidai Nawwara tazo ta kashe mata laptop ɗin da hasken ɗakin ta kunna mata bedside lamp




________________


Ba ƙaramin kwanciyar hankali tasamu ba ganin cigaban da aka samu na samun sauƙin Amatullah


Ba ƙaramin ƙoƙari Umma tayi mata ba kafin aka samu tadawo dai-dai kullum ne da Asuba idan sukayi sallah zata hanata komawa sai sunyi karatun Alqur'ani da sun tashi da safe kafin suci komai ita zata debo ruwa tayi mata addu'a tabata tasha


Idan zasu kwanta saita sanyata tayi addu'a kafin itama takara yimata ta tottofeta da sati ya zagayo ta nema wani malamin su ta faɗa masa akan ciwon Amatullah kar aga bata zuwa tahfeez nan shima yabada nashi taimakon na addu'a da yayi yakawo mata har gida sosai tayi masa godiya


Tunda abun nan yafaru washe gari Baba ya kawo musu abinci iri iri ba ƙaramin mamaki sukayi ba koda mama ta tambaye shi akan ina yasamu kuɗi


Sai ya balbaleta da masifa akan tanaso wai taji inda ya samu kuɗin ne sai a maida kuɗin ko bazata ciba sai taji inda ya samu ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba


Daganan bata ƙara mishi maganar ba kuma kullum saiya kawo musu kayan miya saidai fa ba zancen zaman mutunci shida mama yanda ake dai ba wani canji


Yau ta shirya tsaf akan zata koma aikinta tunda Amatullah taji sauƙi tun safe ta tashi suka kammala aiyukansu itada Amatu


Bata ɗauki komai ba saboda tanada wasu kayan acan gidan a tsakar gida ta samesu zaune sunacin abinci


Ah ah Ummana yanzu za'a tafi ne kuma naga ke bakici abincin ba


Eh Baba na shirya ma ai idan naje can zanci inshaa Allah ta faɗa tana zura takalman ta yan soso data siya basu dade ba


Amatullah ce ta fito daga banɗaki tana yarfe hannu alamun alwala tayi saboda lokacin Azahar yayi ai har kin shirya Umma zaki tafi


Eh na shirya Amatu zan tafi amma jibi zanzo naganki


Murmushi tayi don taji daɗin maganar Umma da tace zatazo ta ganta don ita ba'a son ranta Umma take zuwa aikin nan ba don basuda wata mafitar ne shiyasa


Sallama tayi musu sukayi mata Allah ya kiyaye Baba sai sanya mata albarka yakeyi hakan ya ƙara kular da Mama ko amsa mata batayi ba da take faɗin mama natafi


Haushi ya sanya ta mike ta shige daki tana matsar ƙwalla don tagaji da irin abinda malam yakeyi na nuna bambanci a tsakanin Amatu da Umma abin yana ci mata tuwo a ƙwarya shiyasa har tafara tsanar Umma


Biyota yayi don ya fuskanci yafara kaita ƙarshe batayi tunanin zai biyotan ba hakan yasa tayi mamakin ganinsa a bayanta


Me kike ma kuka rabi nafara ganin take takenki fa rabi bai ida ba ta katse shi da faɗin bakada abinda zaka ceman malam nagaji nagaji abinnan ya tsaya iya haka wallahi idan bahaka ba kowa zaiyi danasani


Saidai ke kiyi dana sani rabi wallahi don ni kinsan bana danasani a rayuwa ta


Bata damu da zancen nasu ba saboda inda sabo sun saba tunda suka tashi suke ganin irin fitinar da iyayen nasu sukeyi hakan yasa basa damuwa idan sunji sunayi dukda abin yana bala'in damun su


Saida ta zura kafarta dakin taji kalmar da ta tsadar da'ita batasan akan me suke maganar ba saidai ta fahimci akwai wani boyayyen al'amari akan maganar da kunnenta ya tsikayo mata bakomai bane face taji suna faɗin


Wallahi malam hakuri na ya ƙare kawai zan tona Asiri kowa yasan matsayin sa nagaji ta faɗa cikin tsawa


Har ya buɗe baki zai maida mata da ƙarfi can kuma sai yace ki tona rabi kinsan sauran ai don Allah kitona kinji ya faɗa yana zare idanuwansa wanda suka kaɗa sukayi jajir dasu saboda tsabar ɓacin rai


Duk da cewa ƙasa ƙasa yayi maganar hakan bai hanata ji ba jin takun tafiyar za'a fito yasa ta shige dakinsu da sauri kasancewar ga kofa ga kofa dakunan nasu suke


Dafe kirjinta tayi cikin tashin hankali take faɗin me za'a tona me Baba da mama suke boyewa ne har take zata tona tagaji


Innalillahi wa'inna'ilaihirajiun take ta faman fadi a zuciyarta don tafara tunanin akwai wani abu wanda suke boyewa ya'yan nasu


Tofah me ake boyewa ❓🤔 Nima dai ina so nasan wannan sirrin ❓ ɓangaren su Nawwara kuma me yake shirin faruwa ❓ meyasa Nawwara take tsoron zuwan Ammi 9ja❓ shin tana wace ƙasar ma ❓kuma wacece ita Ammyn ❓


To nan fa akeyinta dole muyita bi muji me zai faru gaba




Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA


Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number 09131096058 ta whatsapp




________________




Kofar gidan mai napep ya sauketa ta shiga ciki a parlour ta tarar da Nawwara ta mike kan 3 seater a kwance tana daddanna wayarta


Da alama tana cikin nishadi daga yanayin fuskarta tana typing chat take


Sallama tayi dagowa Nawwara tayi tana dubanta kafin ta tashi zaune tana faɗin ah ah Umma sai yau ake ganinki Sweety ta fadamin sister kine ba lafiya kwana biyu ya jikin nata


Da Murmushi akan fuskarta tace Alhamdulillah taji sauƙi sosai shiyasa nadawo ma


Ohk Allah ya qara mata lafiya ta faɗa tana komawa kwanciyar ta wucewa ciki umma tayi ta nufi upstairs dakin Sweety don taje taga ko akwai abinda take buƙata


Da sallama umma ta shiga dakin nata ta tarar da'ita tana kallo a laptop dinta jimm tadanyi kafin ta maimaita sallamar don ta lura Sweety batasan ta shigo ba


Dan dagowa tayi alamar taji mutum a ɗakin karaf suka haɗa ido da sauri umma tayi ƙasa da kanta don tunani take ko tayiwa Sweety laifi ne saboda ta dade bata leko gidan ba


Murmushi ta sakar mata sai taji hankalin ta ya kwanta alamar bata fushi da'ita kenan Sweety ya gida ina fatan kina lafiya


Lafiya kalau Umma ya jikin sister ɗinki ina fatan ta samu lafiya ta faɗa tana saukowa daga gadon ta alamar wani abun zatayi


Wajen kayanta ta nufa ta buɗe tana fito da wasu Abaya guda uku sai material ɗinkin doguwar riga biyu


Umma ta amsa mata da Alhamdulillah taji sauƙi sosai ta warke kafin tace ya naki jikin Sweety baba driver ya faɗamin kema bakiji daɗi ba to Allah ya qara sauƙi


Maimakon ta amsa mata sai ta daure fuska alamar batason zancen shiyasa itama Umma takama bakinta


Mika mata kayan tayi tana faɗin ga Abaya nan ki ɗauka biyu ki kaiwa Sister ki Meye sunanta kikace ma


Amatullah sunanta umma tafada tana mika hannunta domin ta karɓa kayan ba ƙaramin daɗi taji ba don dama kayansu sai a hankali duk yawanci wani lokacin wajen Sweety take samun masu kyau dukda tana samun kuɗi a gidan a wajen Abbyn Sweety saboda siyan abincin gidan su yasa bata tsinanawa kanta komai


Materials din kuma ki ɗauka ɗaya ki bata ɗaya godiya tayi mata sosai sana ta bata ATM dinta tace gashi tagode sosai duk da bata kashe kuɗi sosai ba saboda dasukaje Asibitin ma ba'a karbe su ba


Bata bukaci komai ba tace da'ita sai zuwa anjima ta kawo mata coffee kuma tanaso su fita da yamma


Dakin da ya kasance anan take rayuwa idan tazo gidan tawuce kai tsaye ta ajiye kayanda Sweety tabata saida taje kitchen ta zubo abinci kafin ta koma dakin


Bayan tagama cin abinci ta koshi ta shiga toilet ta dauro alwala saboda anfara kiran sallah la,asar


Bayan ta idar tafara jero addu'o'in ta kamar yanda ta sabayi Saida ta gama kafin ta haye saman gadon ta ɗan madaidaici da yake ciki dakin ta kwanta


Kwance take tana tunanin duniya da kuma yanda rayuwar ta take kasancewa tun tana ƙaramar ta


Wasu siraran hawaye ne suka dinga silalowa daga idanunta masu zafi a zuciya a cikin ranta tana ayyana irin wahalhalun da tasha


Meyasa iyayena basu farin ciki meyasa suke faɗa kullum rayuwata kullum cikin zullumin yaushe zasu gane bamajin daɗin halin da suke ciki


Meyasa Mama ta tsaneni kamar ba,ita ta haifeni ba bata taɓa jana a jiki ba bare taji matsaloli na ni nake kula da kaina na kula da kanwata Amatullah ni nake ciyar da iyayena kuma a haka ban tsira ba daga wajen mahaifiya ta


Kullum cikin zullumin yau idan narasa wannan aikin da nakeyi a ƙarƙashin mutanen nan ina rayuwata data kanwata da kuma mahaifiyata zasu shiga


Babbar damuwar anan itace mahaifiyata bata taɓa nuna ni a wajen danginta ba mahaifina kuma dukan mu ne baya kaimu wajen danginsa bai taɓa cewa yanada wasu yan uwa ba na nesa kona kusa bare mu sansu


why ❓😭


Why ❓😭


Ni Umma ne nayiwa iyayena ❓❓




Amsar tana anan 👉👉👉👉👉


Mai rabo ne kaɗai zai ji ta👂👂


To muje zuwa dai


Ƙarfe biyar ta tashi ta nufi kitchen ta haɗa ma Sweety coffee tawuce dakinta bayan tayi knocking tabata damar shiga


Waje tasamu ta zauna kusa da'ita a hankali take bata tana kurba kamar wata ƙaramar yarinya Saida ta shanye tass kafin ta taimaka mata ta cire kayanta ta shiga toilet bayan ta fito ita ta taimaka mata ta shirya tsaf kafin suka fito hannun umma rike da yar ƙaramar jakar Sweety


Baba driver ne ya fita dasu don shine amintaccen mahaifin Sweety tareda wasu motoci guda biyu masu take musu baya
wani shop sukaje wanda wayoyi ne kaɗai ake siyarwa a cikinsa


Tare suka shiga da Umma waya ta siya iPhone16 Sai ta siya yar ƙarama Kamfanin Nokia guda biyu saita siya wata wayar Samsung S9 duka suka wuce wajen cashier


Da mamaki sai yace musu ai anbiya kawai duk yanda Sweety tayi akan a karba ATM a cire kuɗin shi kuma wanda ya biya a bashi kayan shi


Yace musu suyi hakuri don an riga da anbiya kuɗin ba yanda suka iya haka suka taho suka tafi


Saida suka je wani park tasha ice-cream tayi saye sayen chocolates ta taho dasu gida ta siyawa umma itama ta bata masu yawa


Ba ƙaramin daɗin fitar da sukayi Umma taji ba saboda tadan yawata gari kuma ga abubuwa masu daɗi da Sweety ta siya mata duk da ba yau suka saba fita irin haka ba har tayi mata siyayya burinta kawai shine ranar da zataje gida ta tafi ma da Amatullah kayan makulashen da Sweety ta sai mata saboda tasan ta da kwadayi


Basu dawo gida ba sai wajen tara na dare daganan suje nan yawo kawai Sweety ta sanya su cikin garin Katsina


Sun gaji sosai suka shigo cikin gidan a parlour suka tarar da mutanen gidan hada ƙarin wasu ma mutanen ma


Zaune take saman 2 seater itada Safwan ya kwanto saman kafadar ta yanata faman zuba mata shagwaba


A ƙalla matar zata kai kamar 40 years a duniya daga ganin zubinta zaka gane akwai hutu a jikinta da kuma izza da jin kai duk ta haɗa sanye take cikin leshi blue mai haɗe da fari daurin dan kwalin nan an coge shi fara ce sosai kana kallonta zakaga kamar su da Nawwara duk da ba sosai ba


Sai wani Babban mutum da suke zaune saman 3 seater shida Nawwara kallo ɗaya zaka masa kagane cewa Mahaifin Saheeb ne saboda bala'in kamar da sukeyi dashi


Sallamar Umma ce ta katse su daga firar da sukeyi gaba ɗaya suka dago suna duban su


Da gudu Sweety ta faɗa kan babban mutumin nan tana fadin Daddy gaba ɗaya ta danne shi can kuma saita fashe musu da kuka


Nikuma mai rubutu nace toh fa ya daga murna sai kuka ko dai duk farin ciki ne bansani ba 😆


Gaba ɗayan su murmushi suke saki a parlour alamun sun fahimci Sweety kukan shagwaba ne bawani abu ba banda mutum ɗaya data haɗe gabas da yamma kamar an mata mutuwa


Sorry Sweetyna Daddyn kine ko kiyi hakuri ya faɗa yana dagota daga kansa yana ƙoƙarin kama kunnensa alamun a yafe masa


Hawaye ya shiga share mata yana faɗin haba yar Daddyn ta kar su Safwan su rainaki mana suce Babba dake kina kuka


Daddy I miss you 🥺 so much ta faɗa tana gyara zamanta a kusa dashi tuni Nawwara ta matsa tabasu waje ta koma 1seater


Daddy kun dade sosai baku dawo ba gashi Ammy ma bata dawo ba cikin shagwaba take magana alamun an ɓata mata rai


Kiyi hakuri Sweety Ammi ma takusa dawowa soon kinji munyi magana da'ita ai tace tana kiran layinki ba'a samu kuma nima na kira ban sameki ba ina wayanki ne ya faɗa yana kallonta yanda ta nutsu taba sauraren shi


Kalaman Daddy ba ƙaramin sanyaya ran Sweety suke ba shine mutum na biyu a duniya da yake nuna mata kauna


Saida ta ƙarasa goge sauran hawayenta kafin tace Daddy kwana biyu bansan inda nasaka wayana ba shine ma yau naje na siya wata gatanan ta faɗa tana nuna hannun Umma da take rike da uwayen ledoji a hannu na siyayyar tasu


Sai lokacin Umma tasamu damar gaisheda mutanen parlour ɗin Daddy ya amsa mata fuskarsa ɗauke da Murmushi kafin ya shiga saka mata albarka ba ƙaramin daɗi taji ba


Mikewa tayi ta nufi upstairs tana faɗin Safwan kiramin Saheeb ku sameni a daki Inason magana daku tana tafiya cikin kasaita


Daddy baiji daɗin abinda Hajiya maimunatu takeyi ba saboda nuna ko in kula akan Sweety da duk wanda ta raina masa arziki to ita ba ruwanta dashi duk da cewa yasan wannan halayen nata amma duk idan tayi bayajin daɗi


Ita dai Umma dakin Sweety tawuce taje ta ajiye mata sakonta tasauko tawuce nata dakin da nata ledar domin ta gabatar da sallolin ta wanda batajin daɗin hadawar da xatayi magrib da isha'i


Ko abinci bata nema ba bayan ta idar da sallah tayi addu'o'in ta sai kawai tayi kwanciyar ta don ba ƙaramin gajiya tayi ba ko minti biyar ba'ayi ba bacci yayi awon gaba da'ita


Sweety yau hankali kwance an dage sai zuba ma Daddy shagwaba akeyi har wajen 11 suna zaune a tare hada Nawwara da take tayasu sosai yau tasamu farin cikin da ta dade bata samu ba


Saida zasuyi sallama yace gobe da safe zai fito mata da tsarabar ta duka gidan ma zai basu nasu saboda dama Sweety suna fita ba dadewa suma suka shigo gidan




________________




Ta kasa bacci gaba ɗaya gidan baya mata daɗi gashi babu Umma bare tadanji sauƙi a ranta ma


Duk idan tayi juyi kalmomin iyayen natane suke tsaya mata a rai sai jinsu take kamar lokacin ake faɗa mata su


Sai dakyar tasamu wani barawon bacci yayi awon gaba da'ita


Cikin baccin ta ta farajin surutai ƙasa ƙasa dolenta ta tashi saboda sun fara damunta a kunne


Buɗe ido tayi Saida tayi addu'a kafin ta tashi zaune kamar wasa takejin surutai amma kuma ga duhun dare alamun ba garine ya waye ba bare tace ko har safiya tayi ko kiraye kirayen sallah bataji ba bare kuma tace ko Asuba ce tayi


A hankali ta mike cikin sanda da lalube tanemo hanyar fita daga dakin da taimakon hasken daya dan leko ta bayan labulen dakin


Saida taxo daidai kofar takara saurarawa don ta tabbatar da muryar da takeji da gaske ne ko ba'ita bace ba


Ga mamakinta dai shine da kansa yake waya can ƙasa ƙasa yana faɗin ban dade da shigowa gidan ba wallahi ai matan nan so take ta jazaman bala'i wallahi batasan waye mutumin nan ba lallai ita saita tona mana Asiri kuma bayan ta hanyar yarinyar nan muke samun abubuwan da muke so a wajen sa batasan zata iya zaja mana mu rasa ranmu gaba ɗaya ma


Yar dariya yayi alamun wanda suke wayar ne ya fadi wani abun kafin ya cigaba da cewa Allah ya shiryaki nidai ba ruwana


Ji yayi ajikinsa kaman ana kallon sa hakan yasa yadan fara waige waige aikuwa da sauri cikin sanda takoma ta kwanta kan katifar dakin nasu ta juya baya


Har ɗakin saida taji motsin an shigo ranta yabata cewa ko yazo ya duba yaga ko idonta biyu ne


Daidai kofar ya tsaya yana faɗin karki damu Saida safe zan kiraki idan nafita don inaji kamar ana kallo na amma koma waye zai iya yin ta ransa


Tashin hankalin da ba'a sanya mashi rana😳 ido ya raina fata su Amatu don gani take kamar ya ganta tafara tunanin anya mahaifin nata ne ko kuwa dai wani ne duk da tanajin muryarsa kuma ta ganshi data leka


Ba ƙaramin rudani ta shiga ba to dawa baba yake waya a cikin daren nan❓ akan me yake magana❓ kuma da alamu ma dai da mace yake wayar kenan❓ tunda yace Allah ya shiryeta to wacece ❓


Tofah 🤔
Amatullah taku tazama yar leken Asiri 😂 mezai faru idan baba yagane tana masa leken Asiri kenan




Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA


Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment