Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number 09131096058 ta whatsapp




________________




Wajen 9 am ta farka da wata irin mahaukaciyar yunwa don inda tayi sallar Asuba ma nan take kwance akan darduma dakyar ta mike ta nufi kitchen domin sama ma cikinta abinda zataji don tasan yanzu Sweety bata isa tashi ba tunda ta yaye makaranta hutu tabawa kanta gashi suna gab da zama jarabawar ƙarshe


Mutun biyu ta tarar a kitchen ɗin Baraka da safiya suna aiki suna fira jefi jefi sallamar tace ta katsesu nan suka shiga gaisawa


Hajiya Umma manya sai a kwana nawa ba'a saka ki ana mujiya ba Baraka ta faɗa cikin zolaya tana kama haɓa


Murmushi tayi wallahi bahaka bane ba Baraka sanda zan shigo ne dai Bama haɗuwa kuma kwana biyu ma banzo ba saboda kanwata da tayi rashin lafiya


Allah sarki to ya jikinta suka faɗa a tareda Baraka da safiya ta amsa musu da Alhamdulillah ta warware ma


Saida Umma tagama haɗa tea ta ɗauka slice bread har zata fita kuma ta tsaya tana faɗin wai ina Halima ne nasanta sarkin aiki ce ta faɗa da zolaya


Baraka Sarkin gulma har an kame ana tafa hannu haba umma kar kice min bakisan abinda uwar dakin taki ta aikata mata ba


Da dan mamaki umma tace me yafaru ne taɓe baki Baraka tayi ah ah baza'a ji mutuwar sarki a bakina ba ta juya ta nufi fridge tana fitoda kaji don Hajiya maimunatu tace tayi mata farfesun kaji tunda safe ta kira layin kitchen ɗin ta faɗa musu don ta riga kowa tashi da yake acici ce matar


Safiya tace ai tunda kinfara Baraka da kin karasa bata labarin ai nima dama a bakinki naji kuma ni yanzu zan iya yin kuskure ma wajen bata labarin gara ke da akayi kina kusa taqara zancen tana ɗaukar kwai tana fasawa a bowl zata soya doya


Umma baya tsaya ta kansu ba don taga abin nasu ba mai dorewa bane basuda niyyar faɗa mata yasa ta fito takama hanyar dakinta


Saida ta fara shan tea din kamar an mintsine ta kuma saita mike tanufi upstairs ɗakin Sweety don taga ko ta farka


Karo sukaci tanata uban sauri hakan yasa har wayarta ta fadi ƙasa bata tsaya ta wanda ya bangaje taba ta duka ta dauka wayarta ta cigaba da tafiya


Anam cak ta tsaya jin ambaton sunanta da Sweety tayi can kuma sai ta ci-gaba da tafiya don gudun kada ta gane ta


Mamaki ne ƙarara akan fuskar Umma me yakawo Anam gidan nan tunda safe to kuma taga daga hanyar dakin Nawwara ma ta fito can kuma sai tace kila Sweety ta kirata tunda safe ko wani wajen zasuje ne oho


Da wannan tunanin tayi gaba abinda tana waiwayen yanda Anam data sauka daga stairs ɗin ta nata bala'in sauri zata fita daga parlour ɗin gidan


Dakin Sweety ta kwankwasa taji shuru sau uku tana knocking kafin ta tura a hankali ta buɗe kasancewar Sweety bata rufe daki kuma batason a rufe mata Duk da hakan ya samo asali daga Abbynta da yahana ta saboda gudun kar wani abu ya sameta kafin abu de ta cutu a cewar sa


Kwance take tayi dai-ɗaya alamun baccin yana mata armashi cikin magagin bacci tace waye ya shgomin daki


Umma ce ta faɗa tana ƙoƙarin juyawa ta fice don karta tashe ta ai na tashi ta faɗa tana mikewa zaune juyowa umma tayi tana faɗin kiyi hakuri Sweety na tasheki


Karki damu ai dama inaso na tashi tun ɗazu cikin subul kalam umma tace naga Anam tazo kila kota sameki kina bacci ne shine taje dakin Anty Nawwara


Ware idanunta tayi gaba ɗaya akan umma dake magana har Saida Umma tasha jinin jikinta tana haɗa kalma da kalma kafin takai karshen zancen


Daga kanta tayi tana duban Agogon dakin nasu ko 10 batayi ba amma Umma tace mata wai Anam tazo


Dan numfasawa tayi kafin tace Anam kika gani dai Umma eh tabata amsa a takaice okey kawai tace ta mike ta nufi toilet kafin tadawo umma tafita kitchen taje ta hado mata breakfast


Tana fitowa daure da short towel dinta tace Umma yau a dining zanyi breakfast Umma batayi mamakin hakan ba don tasan Daddy yana nan tana nufin tare zasu karya


Saida ta taimaka mata ta shirya kafin ta dawo nata dakin har tea ɗin yayi sanyi hakan yasa takoma kitchen ta zuba wani abun don tasamu taci


Tadan jima a tsaye har tagaji da knocking zata juya taji an buɗe dakin daga ƙasa zuwa sama take kallonta dakyar Sweety ta tattara dukkan nutsuwarta kafin ta iya furta good morning Mommy


Sanye take cikin sleeping dress rigarta tadan wuce gwuiwa irin burgujejiyar nan ta manya tanata faman haɗe rai Morning lafiya naganki anan ta faɗa tana watsa mata harara


Lafiya kalau Mommy nazo wajen Daddy ne bai farka ba ta faɗa tana niyyar rufe kofar


Juyawa tayi duk jikinta ba kwari har wata yar kwalla ta taho mata sai taji an dagata sama ko bata dubaba tasan aikin waye batasan sanda ta tun tsire da dariya ba tana faɗin Daddy


Sauketa yayi yana fadin Sweety najiki da nauyi cikin shagwaba tace Daddy na girma da yanxu tana wani juyi alamun ta kalleta da kyau mana sosai tabashi dariya


Tsokin da aka jane yaja hankalin su gareta kafin ku ƙara motsi kuma fa banko kofar ta rufeta


Lokacin da Sweety ta juya ashe Daddy yana jiyo su itada Hajiya maimunatu hakan yasa ya biyo bayanta dama yagama shirinsa kenan ya tasheta akan taje tayi wanka tazo su karya shine da taji ana knocking tace yabari ta duba taga waye da taga Sweety shine tayi mata wannan abin duk yana jinsu tana juyawa shine shikuma ya fito hakan ne ya bata ran Hajiya maimuna taja kofar tare da jan tsoki




Parlour suka sauko anan suka samu Saheeb da Safwan a dining suna karyawa Safiya ce take serving dinsu


Waje suka samu kowa ya zauna Saheeb yace Daddy good morning shima Safwan abinda yayi kenan


Morning too my boys ya kuka tashi ya faɗa yana ɗaukar tea cup a hannunsa Lafiya Alhmdllh suka faɗa kafin kowa ya ci-gaba da cin abincin sa


Daddy sweety bata cin abinci a tare damu idan bakanan Safwan ya faɗa yana cusa bread a bakinsa yana aika mata da harara itama martanin hararar ta aika masa


Taya zataci abinci tare damu bayan an fifita a gidan kular da ake mata daban ce ai dole zata raina mu bazata iya cin abinci damu ba saheeb yaƙare zancen nasa yana haɗe rai


Ya isa haka ba'a magana idan anacin abinci Daddy ya faɗa batare da nuna ɓacin ransa ba akan abunda yaran suke faɗa saboda bayason zancen nasu yayi tsawo don yasan hada mahaifiyar su da take zugasu


Saida suka kammala aka dawo parlour aka zauna nan Daddy yace a kira masa ɗaya daga cikin masu aikin gidan Baraka ce tazo Saida ta gaishe shi kafin ya haɗa ta da saheeb akan cewa suje su dauko masa akwatinan da yazo dasu


Guda uku ne kowane sai uban nauyi Baraka ta dauko biyu saheeb ya dauko guda ɗaya


Suka sauko a gabansa suka ajiye su Saheeb nata fama sauke ajiyar zuciya wai nauyi Sweety na kusa da Daddy ta ƙagu taga an buɗe akwatinan taga tsarabar ta


Nawwara ce ta sauko cikin takunta a hankali tasa blue black din a baya tayafa mayafin ta a saman kanta wanda tayi masa manyan kalaba da gashin attach ya sauko har bayanta mai 2 color Black and brown


Morning daddy ta faɗa tana zama saman 1 seater tareda ajiye jakar hannun ta a ƙasa morning my dear ina zakije da sassafen nan naganki da jaka ya faɗa yana saukowa ƙasa


Sweety ce ta dubeta tana faɗin Anty Nawwara good morning bata yarda sun haɗa ido ba ta amsa ƙasa ƙasa wanda ya sanya Sweety mamakin abinda tayi don ita bata mata haka


Nan Daddy ya shiga buɗe akwati na nafarko yace mallakin Nawwara ne ita kaɗai daɗi kamar tayi me ta dauka tafara buɗewa na biyun kuma na Sweety ne amma yace musu ita da Nawwara su duba wani abun abawa yan aikin gidan a cikin akwatinan su na ukun kuma shine yafi girma akace saheeb da Safwan


Kowa ya shiga farin ciki kayane sosai a cikin akwatinan nasu na alfarma wanda duk kayan cikin babu na hausawa tun daga kan English wears na matan da Abayas hada sari da Pakistan duka dai tarkacen kayan sawa


Saida kowa ya kammala farin cikin nashi kafin Nawwara tace wa Saheeb ya kai mata daki xataje unguwa wai zasu haɗu da wasu kawayenta da sukazo Katsina daga Abuja


Daddy baiyi musu ba ya barta don yasanta da tarin kawaye bare su ɗin daman a Abujan suke da zama


Anty Nawwara adawo lafiya Sweety tafada tana mikewa don ta kira Umma takai mata kayanta daki ita kuma tafice batareda ta amsa mata ba


Kwance take bayan tayi wanka tasa ɗaya daga cikin kayanda Sweety tabata sunyi bala'in yi mata kyau don Umma kyakkyawa ce ajin karshe saidai talauci ya ɓoye asalin suffarta don ma tana samun kula a gidan su Sweety


Knocking ɗin ɗakin ne ya fargar da'ita daga tunanin duniyar data shiga waye ta faɗa tana gyara zaman ta muryar Sweety ta jiyo hakan yasa tayi saurin mikewa taje ta buɗe kofar


A tare suka taho bayan ta sanar da'ita abinda xatayi mata


Saida Umma takai mata daki har zata fito saiga Sweety ta biyo ta kaɗan ya rage su bangaji juna Umma zata fito ita kuma zata shiga


Sweety tace yauwa Umma dama akwai sakon da nake so nabaki tun jiya da muka dawo to kuma bansamu dama ba


Shiru Umma tayi tana sauraronta ita kuma Sweety ta shige ciki bedside drawer ta buɗe ta dauko ledar jiya da suka dawo da'ita


Gefen gado ta zauna tana faɗin kizo ki zauna kusa dani Umma yanayin yadda tayi maganar yaso yadan rudar da Umma sai kawai dai tayi kaman yanda tace amma hankalin ta duk ba'a kwance ba


Wayoyin ciki tafara fiddowa saida taga ma ta ɗauki ƙaramar wayar guda biyu ta mikawa Umma tace amshi Umma amsa tayi tana jiran taji me zatace sai taqara mika mata Samsung ɗin tace ta karba taqara karba


Sweety tace Umma wannan ƙaramar wayar guda ɗaya ki kai ma kanwarki ɗaya ki riƙe babbar kuma takice na siya miki gashi kuma bani na biya kuɗin bama takarasa fade tana dauko Babbar kafin ta ci-gaba da cewa karki godemin umma na ɗauke ki ne kamar yar uwata sana wannan wayar dana baki na baki ita ne saboda akwai abinda ya kamata ace muna magana direct ta waya idan ka ina buƙata


Sana na fuskanci cewar gidan ku baki samun damar samun su idan kikazo nan shiyasa kike damuwa sosai akan zuwa koda yaushe ki gansu amma idan kika basu wayar zaku dinga jin juna koda yaushe


Hawayen da take ƙoƙarin shanyewa ne suka ki tsayawa suka fara sintiri saman fuskarta duk duniya mutum biyu ne suke fuskantar halin da take ciki daga Amatullah sai Sweety jinsu take na daban a duniya kullum burin Sweety ta faranta ran umma ita kuma burin umma ta faranta ma Amatullah saboda itace take mata kalamai masu daɗi idan tana cikin damuwa


Batasan Sa'adda ta zube kan ƙafafuwan ta ba tana raira kuka mai tsuma zuciya Sweety Nagode sosai yanda kika faranta min kike kaunata da yan uwana kema Allah ya faranta miki Sweety


Murmushi tayi tanajin daɗin kalaman umma har cikin zuciyarta tana bala'in son yarinyar tun tana ƙaramar ta da aka kawo mata ita don ta kula da wasu abubuwan nata Duk da kasancewar su ɗin basu wuce sa,annin juna amma a haka umma take kula da Sweety kamar wata ƙaramar yarinya Umma tana yiwa Sweety hidimar da iyayenta ma suka gaza tsayawa suyi mata


Umma ki tashi don Allah ki daina godemin inajinki keda kanwarki kamar yan uwana ne wallahi shiyasa kin min abinda Bazan biyaki ba kuma kisani umma a gabanki wanine ya biya kuɗin nan bani ba bansan ma waye ba


Umma ta share hawayenta tana faɗin Alkhairi da kikayi niyyar yimin ne kema Ubangiji ya hadaki da wanda zai yimiki amma wannan kyautar nidai inajinta har a raina daga gareki kawai take ba daga wani ba don niyyar taki ce kuma ko bai biya ba zaki biya ne


Daga karshe Sweety tace wannan week ɗin zankoma school saboda zamuyi final exam ne kuma nasan da mungama Abby America zai kaini karatu kusa dashi saboda haka nasan kema idan natafi zamuyi kewar juna kuma kinga wannan wayar zata taimaka mana sosai wajen rage kadaici ta faɗa tana nuna hannun umma inda ta rike wayar


Sosai Umma ta gode ma Sweety kafin takoma dakinta bayan Sweety ta kira an kawo musu layika har ɗakin umma taje ta kai mata layikan ta sanya mata sana ta saka ma kowace waya number juna


Umma tace mata ita bata iya waya ba nan Sweety tafara koya mata a dakin umma ɗin basu ne suka tashi ba saida aka kira sallah umma tace suje suyi sallah Sweety dai bata tashi ba tace taje tayi zata jirata


Anan Sweety ta zauna har Umma ta idar da sallah tayi addu'o'in ta yayiwa Sweety addu'a sosai bayan ta gama suka cigaba daga inda suka tsaya


Umma da yake irin yaran nan ne masu ɗauka da wuri wasu abubuwan da kanta take shiga sai taga tayi dai-dai


Sweety tace umma yunwa nakeji da sauri umma ta mike taje kitchen ta haɗa mata abinci hole


Saheeb ne ya shigo kitchen ɗin umma na ƙoƙarin fita wani dan iskan kallo ya bita dashi har ta fice ga mamakin sa sai yaga tayi hanyar dakinta mai makon tayi hanyar parlour tahau upstairs


Binta yayi harta shige kafin yadawo yayi abinda xaiyi ya koma parlour yana ƙwafa


Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA


Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number 09131096058 ta whatsapp






________________
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment