Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

_🌹IN BANI🌹_





_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI_



_Wanan littafin nakine Fauzy, you're very Special, I love you so much, Allah ya raya three plates_ .

M. Shakur

1.....

Mata ne makil a babban compound din gidan dayasha simenti duk sun sanya anko iri daya, yara da manya sai hayaniya ake anacin shinkafa, wasu nashan pate, wasu nacin tuwon shinkafa da miyan taushe, wasu nacin fried rice da zobo, daga gefe kuma wasu tsofaffi ne daketa rera waka suna buga kwarya, wasu mata na rawa ana shewa ana manna musu kudi, ana guda kana gani kasan gidan biki ne.

Babban gidane mai fadin gaske wanda saika wuce inda ake bikin sanan kabi wata kofa kaje dayar sasan dasuke kira da sasan kaka.
Kasancewar sasan kaka baida girma sosai babu mutane a tsakar gidan, saidai ko ina fess simentin kasa sai kyalli yake tsabagen neatness din wurin saikuma pampoo dayake diddiga da ruwa dil dil dil da alamu duk wanda yay amfani dashi na karshe bai rufe da kyauba, flat daya ne a sasan kaka dake dauke da wani babban fankacecen falo da akalla zai iya daukan mutane hamsin, falon na dauke da wasu irin hadaddun kujeru maroon color, sai ledan daki mai shegen kyau shima maroon, sai wayansu hadaddun kwaryaye da ake jera ajikin bangon dakin, kana ganin dakin kaga dakin tsohuwa. wani magidanci ne ke zaune yasha fararen shadda inda akamai malum malum sai wata tsohuwa wacce akalla zatakai 79 agefenshi taci atampa daketa gyalli kaman an shafa mai ajikinta, an mata rigan kayan buba da zanin data daura akan rigan, sai kafanta da gabaki dayanshi yasha jan lalli tai lallin da akafi sani da dungulmin tsohuwa, farace tsohuwar, gashin idanunta dana giranta sun koma fari sabida tsufa, sai hancinta daketa uban zufa, dudda tsufanta bai hana kamanninta da magidancin dake zaune kusa da ita bayyana ba alamun mahaifiyarshi ce, cikin muryanta na tsofaffi kuma cikeda masifa tace "Sama'ila, Sama'ila, Sama'ila kaga dai sau uku nakiraka ko, wlh to nagaji, kodai ka tsawatar wanan karan, kona tattara yinawa yinawa nabarma gidanka nakoma chan kauye abina, aikin banza kawai" yanda take masifan yasa mutumin data kira da sama'ila ya sassauta murya yace "kiyakuri Umma na" "bawani zancen na yakuri" ta mishi ihu akah tana nunashi da yatsa tace "iskanci Hamida yay yawa kuma uwarta ke daure mata gindi inba hakaba iskokai ne mutane datake jin tsoron taro iyye? Mayune jama'a? Cha nayi duk yan uwane da abokan arziki suka cika gidan, yau bikin yayarta, yayarta fa Sama'ila amma ace tun safe ba'aga yarinya ba tasaci hanya ta sabe tafice, yo kajimin yar bazan yarin..." shiru tayi sabida sallaman da akayi wata kyaykyawan mace mai jiki doguwa tasa hadadden paper lace doguwan riga pitch da akamai stone work, ta shigo dakin fuskarta ba yabo ba fallasa ta karaso ciki ta gaida tsohuwar. "sannu da hutawa Umma" hararanta tsohuwan tayi batare data amsaba hakan yasa matar ta dubi mutumin dake kallonta tace "gani Alhaji ka aiko akirani" cikin fushi yana girgiza kafa yace "ina Hamida?" shiru tadanyi tana kallonshi kafin ta sauke ajiyan zuciya cike da damuwa tace "Alhaji nima bansan inda take ba" "karya takeyi na rantse maka Sama'ila, matar nan makira ce, itake kara lalata Hamida, wlh, wlh Sama'ila kajini na rantse maka na sake rantsewa in bata nemo Hamida ba saina bar gidan nan nakoma kauye abina dama nafi samin kwanciyan hankali achan" takarashe maganan tana uban huci kaman tana filin yaki, kallonta mutumin yayi cike da takaici yace "haba Umma, to kibari nai magana mana, nace kiyakuri babu inda zaki, kiyakuri kinji" kwafa tayi tawani juya ido tana karkada kafa tace "nayi, yi maganan ka" kallon matar yayi datai shiru tana kallonsu, anatse yace "Halimatu ina Hamida taje?" ahankali tace "wlh Alhaji nima bansani ba, bansan inda tayiba, ina fama da jama'an biki ban masan bata gidan ba saida Ihsan tazo ta fadamin" cikin fushi da tsananin takaici yace "to kije koma ina take ki nemota kindaisan Umma tace da ita za'akai yayarta chan legas gidan mijinta ko, na fadamiki kinemota ta dawo gidan nan right away" dan ajiyan zuciya ta sauke tana kallonshi kafin ta girgiza kai kawai cike da takaici ta juya zata fita daga dakin saikuma ta juyo ta kalleshi da idanunta da sundan chanza kala tace "amma Alhaji kasan matsalan yarinyar nan batun yauba ko, batun yau mukasan matsalan Hamida na Agoraphobia ba, batasan mutane, tanada tsoron shiga taro, tun tana yarinya haka take, yanz..." cikin fushi ya katseta ta hanyar cewa "yanzu yarinya ce? Me amfanin ki amatsayinki na mahaifiyanta? Kinga kisan yanda zakiyi kinemo Hamida kindaiga ran Umma abace yake kina kara bata lokaci ne karfe biyar za'a zo daukan Habiba yanzu karfe uku harda kwata" juyawa tayi ahankali tafita daga dakin, da kyar ta iya saita fuskanta ta amsa gaisuwan da mutanen tsakar gida ke mata amatsayin ta na uwar amarya ta wuce ta shiga bangaren su inda falon ma ke cike da jama'a makil, corridor su tayi tabude wani daki ta shiga mace dayace a zaune a dakin tana hada kayan akwatin amarya data ciro kana ganin matar kaga kamaninta da matar data shigo, maida kofar tayi ta rufe ta shigo ta zauna kan gado dabas da sauri tasa hannu tana goge kwallan daya zubo mata, da sauri matar dake hada kaya a akwati ta saki kayan hanunta tazagayo tazo ta gabanta tace "menene kike kuka Maman Ayush?" share idanunta tayi tanadan nishi alamun kuka nacinta tace "Yaya narasa yanda zanyi da Hamida, kullum, kullum dakika sani saita jamin cin mutunci daga wurin Alhaji da Umma, laifinane Yaya? Nina hallice ta? Munanan dake ai inata trying number ta baya shiga, natura yan uwanta duksunje makota kiramin ita ba'a ganta ba, Yaya ya zanyi? Narasa yanda zanyi na chanza Hamida, narasa wace irin yarinya ce, imagine fa Yaya yau bikin yar uwarta ma ta gudu tabar gidan, ni yanzu a ina zan ganta, yaya zanyi da raina?" takarashe maganan cikin daga murya sosai hawaye na gangarowa daga idanunta, da sauri Yayar tata mai suna Yaya Lami wacce take her only sister a duniya ta rungumeta ta daura kanta acikinta tana shafa bayanta tace "ya isa, ya isa dena kukan, bari na gwada kiranta kozai shiga, is okay."

_Kukkuruku old train station._

Babban train station ne that has been abandoned for years yanzu, ba'a amfani dashi sabida sabon da aka bude, wajen shiru babu mahaluki ko daya sai wani tsoho baba mai gadi dake kwance kan wata yar katifa yakafa babban radio dinshi a kunenshi yaja antenna waje yana sauraran labaran rana.

Zaune take akan dan danddamalin dake kusada railway, tana sanye da bakin hijabi har kasa daya rufe har takalmin kafanta, gefen fuskarta nake hangowa, farace sosai tana sanye da farin eye glasses, gashin idanunta bakin kirin dogaye, lips dinta kananu sunyi pink sosai sun bushe danko mai bata shafa akansu ba, gefenta wani karamin black and white jakane na MK sai wasu duwatsu yan kanana dake gefenta da akalla zasukai guda hamsin, ahankali ta zare hanun damanta dake cikin hanun hijabi data kankame ajikinta ta daura hanun akan duwatsu, farine hanunta sol da dogon yatsun ta sirara inda farcenta ke dauke da jan lalli, ahankali tai picking one stone tana kallon railway ta sauke ajiyan zuciya mai sauti cikin wata irin siriruwan murya nai bala'in dadi tace "Kakan mu!" jefa dutsen tayi akan railway tabi dutsen da kallo harya sauka akasa dutsen ya hargitsa duwatsan wajen ahankali tace "dutsen nan is just like Kakan mu, duk inda take saita hargitsa komi, Kakan mu! Kaman zakaran dawaki ce kukanta ba na alheri bane, Kaka! she's the definition of Iska ba nauyi gare kiba sai kada itace" wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu ahankali tace "wanan ne Baba, duk inda Kakan mu take yana wurin, baya tsalleke abinda tace, in kana neman sa kanka a bala'i a wurin Abba ka batama Kaka rai, hausawa sunce, Allah ya sauwake wahala, tsohuwa ta ga ajalinta ya kusa" wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu tace "Mama! Mamana! My everything" shiru, ahankali tace "Mama kaman rake take, tanada zaki amma batada tau..." shiru tayi sabida ringing din da wayarta yafara dake cikin jaka.
_🌹IN BANI🌹_





2....

Duka jikinta rawa yafara da sauri ta kalli jakan, kasa taba jakan tayi har wayan ya karasa ringing ya katse, yafara ringing akaro nabiyu, sosai hanunta ke rawa da sauri tajawo jakan tabude taciro wayar tata kirar Samsung A50, Anty Lami data gani a screen yasa kirjinta ya buga da sauri ta dau wayar ta kara a kunenta kafin ma tai magana Anty Lami tace "ina kike Hamida? Nace ina kike?" ta daka mata tsawa, sosai hanunta ke rawa, kirjinta na bugawa dan bamatasan mezatace ba, kasa magana tayi but tana iyajin Maman su nacewa "tamiki shiru halan ko? Ban wayan kigani Anty" karban wayan Mama tayi ta kara a kunenta cike da fushi da takaicinta tace "wlh Hamida inba kinaso ki gamu da fushina da kin dade bakiga irinshi ba ki kamo hanya kidawo gidan nan right this second, dan iskanci ana bikin yar uwan ki kin kama hanya kin gudu, kidawo gida yanzun nan kinajina Hamida?" gyada kai tayi bakinta na rawa sosai tace "t...to Mama" katse wayar sukayi hakan yasa tabi wayan da kallo gabaki daya hankalin ta yatashi cewa da akayi tadawo gida, jakar ta jawo ta saka wayan ciki kafin ahankali ta mike tsaye, doguwar mace ce kyaykyawan gaske, fara ce fat kana ganinta kaga Maman su kaman su harya baci da Mama, tana sanye da fararen eyeglass idanunta ba kawalli saidai eyeliner dataja a saman ido dayama idanun wani irin cool kyau, giranta acike da gashi, gashin bakin kirin, sai dogon hancinta da dan karamin bakinta daya bushe, black hijabi ne jikinta wanda hulanshi ya rufe goshinta sosai dan saura kadan ma yarufe giranta amma dudda haka kana hango kwantaccen gashi a forehead dinta, dogon hijabi ne ajikinta dahar kafafunta ya rufe bama ka hango asalin kayan datasaka, da sauri tadau handbag dinta ta rataya tafara tafiya a natse kaman batason taka kasa ahaka ma wai sauri take tafito wajen da sauri Baba mai gadi ya rage karan radio dayake ji ya juyo ya kalleta yace "har zaki tafi Hamida?" gyadamai kai tayi batare data kalleshi ba tana kakkare fuskarta da hijabi kaman wacce tai laifi tana kara sauri, murmushi yayi yace "shikenan sai gobe tunda baza amin magana ba, gobe ma zaki kawomin tuwon ne Hamida?" gyadamai kai tasake yi still batare datamai magana ba tafice daga wurin da saurin ta, murmushi Baba mai gadi yayi yakomar da kanshi ya daura akan filo yana murmushi ahankali yace "Hamida kenan" yasake yin wani murmushin ya kara karan radio shi yacigaba dasauraran shirin da ake.


Da sauri take tafiya akan titi tana kakkare fuskanta da hijabi, keke napep ta tsayar ta shiga ciki da sauri tana kallon gefe daya batare data kalli mai keken ba tace "j...jan bulo zani" "naira dari uku ne kudin ki hajiya" gyadamai mai kai tayi tana kara rufe fuskarta da hijabi tace "to" tada keken yayi suka fara tafiya har zuwa jan bulo sosai gabanta yafadi dan sosai anguwan su yacika da manya manyan motoci, da mutane ga maza ko'ina, jitayi hankalinta yatashi tunanin ta shine yanda zata wuce mutanen ta shiga gidansu, ahankali tace "yayi nan" tsayawa mai keken yayi ta zage jakanta taciro dari ukun ta bashi sanan tafito tana kare fuskarta da hijabin ta saukar da kanta kasa tafara tafiya ahankali batare data bari sun hada ido da kowaba kirjinta kaman zai fashe zuciyata kaman zai fito waje, a kofar gidansu ta tsaya chak ta leka ciki uban mutanen data gani ciki yasa ta koma gefe jikinta na rawa duk ta birkice, wata yarinya ce kyakyawa da bazata wuce 10yrs ba tafito sanye da doguwan rigan ankon dayamata kyau sosai, ware manyan idanunta tayi ta kalli Hamidan dabama ta lura da itaba sai kakkare fuskarta takeyi tana sake mammanewa ajikin gate dinsu kaman wacce tai laifi ake shirin kamawa akaita ciki, cikin daga murya tace "laaaa Anty Hamida yaushe kika dawo? Ina kikaje anata nemanki? Kinga anma kusa kai Anty Ayush" dan janye hijabinta tayi back jin muryan kanwarta ta kalli kanwar tata dake kallonta, da idanunta dasuka cika da hawaye cikin rawan murya tace "I..Ihsan jeki fadama Mama nadawo ni bazan iya shigowa ba mutane sunyi yawa" juyawa Ihsan din tayi ta leka compound din saikuma ta dawo wurinta tace "wlh Anty Hamida babu wasu mutane fa, su kawayen Mama ne dana Kaka, saikuma su maman Rabi makotan mu, zomuje ki shirya kisaka ankon ki" tai maganan tana kamo hanunta, sake komawa baya tayi tana zaro mata idanu kaman zatai kuka da yar karaman cool voice dinta tace "Ihsan stop dan Allah kunyan shiga nake" daidai lokacin wata budurwa da bazata wuce sa'an Hamidan ba tazo zata wuce ta shiga gidan dan daga gidan Pharty su na kawayen amarya take taci gayu sosai cikin ankonsu na yan mata wani pink ashobi doguwan riga an mata dauri hadadde tadan yafa gyale a kafada, kwala mata kira Ihsan tayi. "Anty Zainab" da sauri budurwan ta juyo ganin Hamida tsaye tana kakkare fuska da hijabi tana komawa baya yasa ta rike waist takaraso wajensu cike da mamaki tana kallon Hamidan tace "Kinga daman dawowa Hamida?" da sauri Ihsan tace "Anty Zainab kinga wai bazata shiga cikiba, kumafa Mama na nemanta tun dazu dasafe, Kaka ma ta aikani nemota yafi sau dari uku" kallonta Zainab din tayi ta harareta tace "wuce mutafi" da sauri ta share hawayen dasuka zubo mata da hijabi tace "Anty Zainab mutane" "to uban me zasu miki? Cinyeki zasuyi?" kallon wajen tayi cikin tashin hankali tace "nidai zan tsaya anan kucema Mama nadawo" ganin kara makalewa take a bango kuma tasan halin ta tsaf inba ka tursasata ba wlh bazata shigan ba yasa zainab ta karasa wajen ta finciko hanunta tajata da karfi, fashewa tayi da kuka sosai tana waigen baya tana neman fizge hanunta daga na Zainab din, da sauri Zainab tace "rikemin dayan hanunta Ihsan mu shiga ciki" da sauri Ihsan din ta rike dayan hanun suka jata zasu shiga ciki, fashewa tayi da kuka duka hankalinta yatashi tanason kwace hanunta takasa dan zainab akwai shegen karfi, cikeda tsoron shiga gidan tace "Anty Zainab dan Allah no, please kinji wlh kunyan shiga ciki nake, ai nadawo kusakeni bazan kara fitaba, kunya nakeji" waigawa baya tana neman abinda zata rike dan karsu shiga da ita ciki karaf suka hada ido da Ya Faruk yana zaune kan white Lexus dinshi yaci farin shadda gizna hanunshi rike da waya yana kallonsu, wani mugun kallo ya watsa mata da sauri ta dauke kai tana share hawayen da sun kasa tsayawa suka shiga gidan da ita da karfin tsiya, kara fashewa tai da kuka sabida yanda ake kallonsu ta rufe fuskanta da hijabinta da sauri hankalinta duk atashe, dakin Mama suka bude suka shiga da ita ciki Zainab tace "Mama gatanan tun tuni tana waje taki shigowa shine na jawota" wani irin kallon takaici Mama ke mata gashi ta tsaya tanama mutane kuka aka hakan yasa wani irin zuciya ya debi Mama ta tashi ta zuba mata mari tana huci, ihu tayi ta tsugunna akasa tafashe da kuka sosai, cikin fushi Mama tace "kukan ubanme kike mana iyye?" zata kara kai mata wani dukan Anty Lami ta riketa tace "ke Maman Ayush dena dukanta, addu'a ake ma yara" cikin tsananin fushi tace "wani irin addu'a Yaya? Kullum Hamida saita jamin cin mutunci, meke damunta ne? Yanzu bagata ananba ta wuce mutanen wani abu yasameta? Wlh Yaya kimata magana kotamin shiru kona sassaba mata Allah bazance ta girmaka duka zan kirba mata kaman yar shekara biyu agidan" hanunta Anty Lami ta rike ta zaunar da ita tace "calm down, ya isa haka, kidena bata rai yau babban ranace kina aurar da ya baikamata kina fushi ba" ta juyo ta kalli Zainab dake tsaye itama tana kallon Hamidan data boye fuska cikin hijabi tana kuka tace "ina ashobin nata Zainaba?" "yana dakinmu" tafada ahankali, "yauwa to jeki dauko ki kawomin tai wanka ta shirya taje wajen kakan ku dake nemanta kafin ku tafi" juyawa tayi dan zuwa dauko ashobi, ta kalli Ihsan datai shiru tana kallon Hamidan idanunta sun cika da kwalla itama kaman zatai kukan dan ta tsani taga an taba Hamida tace "jeki taya Zainab dauko kayan" juyawa tayi tafice tarufo musu kofan hakan yasa Anty Lami ta dawo inda take tsugunne tana kuka ta dagota tana murmushi tace "haba Hamidan Maman ta, mai kama da Maman ta" tsakin takaici Mum tayi ta tashi tafice daga dakin, sakinta tayi ahankali tace "oya cire hijabin kije kiyi wanka kizo ki shirya" gyadamata kai tayi ta zare eyeglasses din idanunta ta sauke handbag dinta tasa aciki tana goge idanunta da bayan hannu da hawaye ke zuba ta ijiye jakan ta mike tana kallon gadon ganin ba Mama, ahankali ta zare hijabin ta ijiye akan gadon, kyaykyawan yarinya ce Hamida bana wasaba, gawani irin shape da Allah yamata mai bala'in kyau tana sanye cikin simple riga da skirt na wani poker dot silk material skirt din yabi jikinta yafito da fine curve hip dinta rigan ma yakamata yay mata shegen kyau, kitson shiku ne akanta manya manya dabaza su wuce guda gomaba, gashinta dogon gaske yay tsufa gashi ya kwanta akan goshinta sosai, babu dan kunne a kunenta,looking naturally beautiful, sake goge hawayen daya zubo mata tayi Mama Lami tace "Ya isa kukan haka wuce kije kiyo wankan ki kinji Hamida" gyadamata kai tayi ta wuce tabude bayin dake nan dakin Mama ta shiga bata wani jima sosai ba tafito daure da zani kayanta dasu Zainab suka kawo Anty Lami ta nuna mata akan gadon, daukan kayan tayi bayan tagama tsane jikinta ta shirya cikin kayan doguwan rigan itama aka mata kaman na Zainab bakaramin kyau dinkin yamata ba yafito da shape dinta sosai, zama tayi kan gadon tana wasa da yatsu Anty Lami tace "tashi zakiyi kiyi kwalliya kije kakan ku na kiranki" gyadamata kai tayi tana kokarin danne kukan datakeji taje gaban madubin Mama ta tsaya, tashafa farin hodan data gani awurin, ta shafa man baki, Anty Lami daketa binta da kallo sabida kyan datayi dudda batai gayuba sosai ba amma tai wani irin kyau tace "bayan kin dawo daga wurin kaka kije dakin ku kihada kayan da zakiyi amfani dashi in kinje Lagos din ance kwana uku zakuyi" hawaye ne suka zubo mata da sauri ta share, hararanta Anty Lami tayi tace "ai kyaji dashi lamarin ki ya tabarbare Hamida wuce kibani wuri danni inzan miki nawa wlh saiyafi na wanda maman ki tamiki, kayan takaici kawai mtsww" taja tsaki, ahankali takoma gaban gadon tadau hijabin ta ta zura, baki Anty Lami ta bude tace "kinsa ashobi ki na yan mata saikin saka hijabi kuma? Lallai Hamida nidai wuce kiyi duk yanda zakiyi kekika sani" ta nuna mata hanyar kofa, ahankali tadau jakanta tawuce tafita daga dakin mutanen data sake gani chaa ana hayaniyan biki yasa taja hijabin ta rufe fuskarta tana tafiya ahankali ko ina na jikinta na rawa, kafin takai falo taci karo da mutane sama da goma sha da kyar tasamu ta fice tai hanyar sassan kaka, karo taci da mutun da sauri tai gaba zata wuce batare data dagokai ba taji an wani irin fizgota, a tsorace tadan dago kai hada ido sukayi da Ya Faruk yadaure fuska kaman baitaba dariya a duniya ba, saukar da idanunta tayi kasa bakinta narawa sosai tace "s...sorry Ya Faruk" wani irin matsiyacin kallo yamata hakan yasa jikinta yadau rawa, cikin wani irin kakkausar murya yace "mahaukaciya kawai" yawani irin turata, ahankali ta dagakai ta kalleshi da idanunta dasuka cika da kwalla shima ita yakema wani kallon tsana, cike da dakewa zuciyarta na tsinkewa sosai tace "niba mahaukaciya bace".
_🌹IN BANI 🌹_




_M. Shakur_


3....

Cike da fushi yawani irin daga hannu zai dauketa da mari daidai lokacin Kaka ta leko, da sauri tace "wlh katabamin ita Faruku Allah ya isa, nitama laifi bakaiba, tamin laifi kaitamawa dazaka fara hukunta? Wanan rapkeken hanun naka mai kama dana basamude zaka zuba mata salon ka nakasamin ita mugu mai zuciyar sojoji, cikata" takaraso wajen tana nishi ta janye hanun Faruk din daga jikin hijabin ta ta ingizata ciki tace "wuce ciki kijirani miskilan yarinya" cikin tsananin fushi Faruk ya fizge hanunshi daga na Kaka yace "dalla chan ki sakeni karki sama fararen kayana datti ni" da sauri ta kalli hannayenta tace "Allahu Akbar wlh babu dauda a hannuna fa Faruku, yi hakuri kaji dena fushin" ta kawo bakinta saitin kunenshi kaman zatai gulma tace "nafiso na hukunta ta dakaina ne, inna bari ka hukuntata aisai ka karasata baka ganta daban bane acikin yaran Sama'ila guda bakwai da Allah yabashi, kabarni da ita nasan maganin ta" hararanta yayi yajanye kunenshi yace "dalla ni kidenamin gulma a kunne, kuma wlh bazan siyomiki namijin goron ba" zata kamoshi yawuce yafice abinshi haba takama tana hararan bayanshi tace "chan ka karata, sojan banza sojan hofi yanda kakeda zuciya inna barka kashe wanan ja'iran yarinyan zakayi" tajuya tashiga dakin a zaune ta ganta akasa jikin dogon kujera tana wasa da yatsun ta, wani mugun kallo ta zuba mata tace "daga ina kike? ina uwarki ta turaki

Please Login or Register in order to submit comment