Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


**** **** ****

HEARTBREAK
Kwanaki uku kenan da yin wayarsa da ‘yar uwarsa Murjanatu. Kwatanta halin da Abdulrasheed yake ciki a kwanaki ukunnan bazai yuwu ba, he is frustrated and heartbroken, kasancewar babu kowa a tare dashi shikadai ne a gidansa sai mai yi masa hidimar share-share da goge-goge da girkin abinci, daga shi sai zuciya da kwakwalwarsa suke aiki a kwanaki ukunnan, don haka suka taru suke ta kitsa masa duk abinda suka ga dama akan mata da al’amarinsu. Mai kyau da maras kyau. Shaidan ma yana taka rawarsa wajen gaya masa mata duka mazinata ne ya fita harkarsu. Babu wata soyayyar gaskiya in existence. Hakan yasa tunaninsa mafi rinjaye duk ya gurbace akan diya mace.
Abdulrasheed ya kullaci mata da soyayyarsu kowace iri ce, ta aure kota watsewa duk ya barranta kansa daga ciki, daga yau ya nesanta kansa da kowacce iri. Ya tsani taimako, duk da in tunanin hakan yazo masa yana cewa (astagfirullah). Ya zo ya tsani yarda da duk wata mace. Shaidan ya cigaba da ribatar sa yana gaya masa ai duk mata irin Hasinah ne marasa godiya, maciya amanar kauna, kuma marasa tsarki na jiki dana zuciya.
Saboda shi mahaifiyarsa ta dade tana cusa masa wani irin tsoron zina, tun sanda ya fara balaga, ta taso dashi da upbringing mai kyau cikin hikima da lallami take cusa masa kin zina, sau tari tana yawan gaya masa cewa ko mata nawa yake so kuma ko ‘ya’yan wa yake so a sarauta da arziki, haka kona talakawa ne yakeso zasu aura masa indai akwai nagarta da kykkyawar nasaba.
Amma ya taimaki kansa da su kada ya kusanci zina a rayuwarsa, sabida ita zina bashi ce wato dattinta naso yake yi a cikin zurri’a, da wannan belief din ya girma a ransa, duk da Haseenah taso ta wargaza wannan tufkar da Nenne ta dade tana yi a zuwanta Japan.
Amma yau Hasinah tasa abin ya shafi har mu’amalarshi da kowa, don gani yake duk ‘yan uwansa na wajen Uba ma irin Tokumbo ne wato mazinata ne (subhanallah), marasa la’akari da girman ‘yan uwantaka da abokantaka da yarda da aminci in dai akan mace ne, idan babu tsoron Allah ai ana barin halas don kunya.
Watakila shiyasa iyayensu maza (musamman Dan Iyan of Ilorin, Babansu Tokumbo) ya damu sai yayi aure cikin ‘ya’yansa mata kuma yafii kowa damuwa a takura masa yayi auren cikin gida, ashe ya san ‘ya’yan nasa watsatstsu ne marasa tarbiya.
Hakika Tokumbo yaci amanar tarbiyyar gidansu. Ya saka a ransa ba shi ba aure a duniya balle cikin zuri’arsu, kai duka matan duniya daga yau ya yafe su koda diamond aka kerasu, zai rufe ido ya kauda kai daga kansu in dai tawali’unsa wajen zaben macen aure (did not yield a positive result), wato indai kaskantacciyar hanyar da yabi wajen zaben macen aure bata sa ya samu abinda yake tsammanin samu na macen da zata so shi ta girmama shi, ta kaunace shi domin Allah ba.
Ya yardarwa kansa a can baya ‘ya’yan marayun sune zasu fi zama nagari saboda rashin gatansu zasu iyawa maraicinsu, fiyeda ‘ya’yan masu arziki dana sarauta, wadanda yake ganin baza’a samu masu tarbiyyar da yake so a cikinsu ba, da irin yadda yakeso matarshi ta kasance ta so shi tsakani da Allah, sune yafi tunanin a cikinsu babu nagari, to ashe matan daga kowanne tushe suka fito ba kwarya bane balle ya kwankwasa cikinsu ya zabi ta kwarai. Babu wadda zaka ci wa alwashi akan soyayya, haka babu macen da zaka iya baiwa amanar zuciyarka da soyayyarka a wannan zamanin ba tareda ta ci don abin duniya ba, a karshe zata kekketa zuciyarka tabi ta kai ta tattake ba tareda tayi la’akari da tarin alkhairorinka gareta ba.
Da daddare Prince Abdulrasheed yana zaune a karamin falon gidansa da na’ura mai kwakwalwa a gabansa da sunan aikin project dinsa zai cigaba, wanda ya dade da jinginarwa saboda harkokinsa na Polo. Yau bacin zuciya da rashin abinda zai debe masa kewa yasa ya dauko project dinsa yana son karasawa ko ya samu ya bar kasar Japan bakidaya, ko ya samu ya huta da binbinin da Haseenah ke masa kullum na neman sulhu. Amma abin takaici ya kasa tabuka komai daga aikin da yake son yi. Har zuwa lokacin zuciyarsa bata koma daidai ba, amma dai ta rage tafarfasar da take yi.
Gidan Prince Abdulrasheed na Japan wanda ya kasance karamin ‘Penthouse Apartment’ ne cikin birnin Tokyo, Kakansa Emir ne ya kama masa hayar gidan shikadai don kawai ya zauna yayi karatu babu takura, baya son duka abunda zai takura takwaransa kuma jikansa na farko da yake kira “Kehinde” wato Hussaini, don haka ne ya gwammace ya kama masa wannan tsadadden gidan ya zauna a cikinsa shikadai yayi karatunsa cikin nutsuwa, maimakon ya zauna cikin gidajen dalibai yana manejin rayuwa irin wanda galiban kowanne dalibi da yazo kasar ke yi.
Shi da kansa ya san ko cikin zuri’arsu ta Sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni shi dan gata ne, yafi kowa gata da samun kulawa da soyayyar Sarki. Prince yayi amanna da cewa, Sarki Abdulrasheed na masa son da baya yiwa kowa cikin ‘ya’ya da jikokinsa, cikin zuri’ar Sarki Abdulrasheed kaf dinsu shine na gaban goshin Kakan nasu. Hatta Taiwo da aka haifesu tare saidai ta biyo bayansa a gun Emir duk da taci sunan mata mafi soyuwa a gareshi Olori Murjanatu. Kai Sarki baima cika shiri da Taiwo ba don yakan ce halinta irin na Babanta ne bata son shiga cikin dangi.
A kokarinsa na neman abinda zai kwashe masa damuwar da yake ciki, sai ya sake kunna na’u’rar ya budo aikin ‘final project’ dinsa na kammala digiri na biyu, wanda shi ya rage masa, in ya gama ya mika aka bashi certificate zai bar kasar Japan.
Wayarsa a kasha take tun jiya bayan sun gama magana da Taiwo, ya kasheta gabadaya ne don tsira daga azababben kiran Hasinah, wanda take jefo masa shi a jejjere babu kakkautawa sanda ya bar wayar a kunne, haka na Tokumbo ma yake shigo masa duk bayan minti, wani zubin kiran nasu har turereniya suke yi da juna, amma ko kusa ya kasa dagawa dayansu, don ya san maganar guda daya ce (hakuri zasu bashi) wanda bashi da amfani gareshi a halin yanzu, me zasu ce masa bayan wannan? Ya riga ya gama (making mind) dinsa kan cewa babu shi babu soyayyar mace bayan mahaifiyarsa! Babu shi babu soyayya da kowacce mace kuma. Don haka tunda har zuwa lokacin zuciyarsa bata saki ba sai ya kasa tabuka aikin komai na (project) din nasa, wanda daga shi ya hada masters dinsa a (Petro Chemical Engineering).
Har ila yau, Abdulrasheed yayi wani kuskure domin kasa furta addu’ar yayewar bakin ciki, kamar yadda Nenne ta dade tana nuna masa cewa a duk hali makamancin wannan ya dimanci addu’ar yayewar kunci da damuwa da Annabi SAW ya koyar, amma a yanzu bayan bakin ciki har da shaidan ke jagorantar ragamar fushin zuciyarsa, yana controlling emotion dinsa da grievance dinsa, yana gaya masa saboda abinda Hasinah tayi masa to daga yanzu bashi babu kallon wata diya mace, koda da jan yaqutu (emerald) aka kerata, daga nan har gaban abada.
Daidai lokacin, kararrawar kofa (door bell) ta sanar dashi yanada bako a bakin kofa.
Kamar bazai tashi ba, don kafafunsa kansu sun yi masa nauyi, sabida dadewarsa a zaune, kamar yadda zuciyarsa ma tayi nauyi mai yawa a cikin kirjinsa, ya dade gaban allon kwamfuta (doing nothing). Baya tsammanin zuwan kowa a dai-dai wannan lokacin don a saninsa bashi da appointment da kowa, amma ko mai yasa?
Sai ya ji ya kasa kyale kiran kararrawar, don mai dannawa ya ki tsagaitawa da dannawa, ya tashi ya taka a hankali cikin basarakiyar tafiyarsa, yana tafe cikin nutsuwa kamar bai son taka kasa, wadda tafiyarsa ce wannan ta halitta.
Abdulrasheed ya bude kofar falon fuskarsa ba yabo ba fallasa. Ga mamakin sa sai ya ga ‘yar uwarsa rabin ransa da bait aba kawo zuwanta a yanzu ba.
Doguwa kakkaura Murjanatu-Taiwo ce a tsaye, cikin bakar abayat, ta nade kanta da dankwalin a bayar ta saka face-mask, wanda ya rufe fiyeda rabin fuskarta, Taiwo na rungume da diyarsa (Kiki) Ruqayyat.
Kiki ta sha ado da ribbons mai kalar pink da yellow kamar ka sace ka tafi da yarinyar don kyau.
Taiwo a Tokyo, unexpected, don kawai hankalinta ya gaza kwanciya da halin da yake ciki.
Hakika kamar yadda tayi tunani yana bukatar wani nasa kamar ta a gefensa, a dai wannan lokacin, wanda zai tunasar da shi ALLAH! Da karbar kaddara.
Ko Nenne da Dade basu san da tahowar Taiwo Japan yau ba. Daga ita sai Toufeeq wato mijinta suka shirya maganar tahowar tata da gaggawa don ta lallashi Abdulrasheed don ta san shi bai iya daukan frustration da sauki ba musamman in yana ganin ka masa unfair treatment da bai cancanta ba.
Hannu yasa kawai ya karbi Kiki daga kafadunta ya sumbaceta bayan ya bude kofar, ya dan yiwa Taiwo (side hug), amma ya kasa boye feeling din dake kasan zuciyarsa na hakika ya ji dadin ganin su a wannan lokacin akan basarakiyar fuskarsa.
Taiwo ta kama hannunsa ta rike cikin nata, a haka suka karasa tsakiyar madaidaicin hadadden falon nasa, tana mamakin fadawar da Kehinde yayi, cikin ranta tana korafin duk neatness din dan uwan nata da kullum zaka ga komai na gidansa tsaf-tsaf yana kyalli, yau falonsa kaca-kaca, gabadaya ya canza daga dan gayun Kehinde din data sani cikin kwanaki biyar kacal. Ta tabbata da kyar idan a duka kwanakin nan ya ci abinci kuma yayi wanka yadda ya saba, balle akai ga zancen gyaran fuskar da bai bari da kasumba.
Ta yarda soyayya masifa ce (ga wanda bai yi sa’arta ba) sannan cin amana daga wanda kake so, ka kuma yarda dashi da zuciya daya, ka wahaltawa rayuwarsa a lokacin da yake tsananin bukatar taimako kamar Haseenah da Adetokumbo yafi komai lahanta zuciyar dan adam wato (butulci).
Balle Abdulrasheed da zata rantse bai taba cin amanar kowa a rayuwarsa ba, mai kirkine mai alkhairi ne shi, zuciyarsa mai kyau ce kuma mai tsafta ce akan kowa da komai, komai zai yi ma mutum yana yi ne saboda Allah ba don ya rama masa ba.
Taiwo ko kafin ta ko huta kicin ta shiga ta samar masa abinda zaya ci mai zafi da nauyi wato Amalar bawon doya miyar Ewedu data ji naman turkey da smoked fish zuku-zuku. Saida ta tabbatar ta masa favourite food dinsa ya ci sosai ya sha tea na nescafe mai zafi, sannan ya kishingida akan sofa da Kiki a gabansa yana wasa da ita.
Ko a kwayar idonsa ta lura yunwa tayi masa lahani a kwana biyar ba kadan ba, kasancewarsa mutum mai yawan cin abinci, kullum Nenne na cewa “his best friend is food”. Idan akwai abinda yafi karyawa namiji zuciya toh Hasinah ta karya maza, ta karya zuciyarsa raga-raga.
A daren shi da Taiwo sun zauna sun kara tattaunawa kan al’amarin da ya faru dashi da Hasinah, kuma Taiwo bata barshi da mummunan tunanin da ya riga ya tsirga ya samu muhalli a zuciyarsa ba na cewa duk mata haka suke, tayi ta bashi baki da kwantar masa da hankali da bashi kyawawan misalai iri daban – daban na halin lalacewar da al’umma ke ciki a wannan zamanin, tace don haka wannan bazai zamo wani abin mamaki daga halayyar dan adam ba.
Taiwo ta kara da cewa “ka yarda ba kuma duka mata muka taru muka zama daya ba a halayya da dabi’a, ta kara da nuna masa cewa Hasinah ba itace karshen rayuwarsa ba, sannan ba itace autar mata ba, wasu matan ma nagari ko haihuwarsu ba’a yi ba, tace kada hakan yasa ya fidda kyakkyawan fata akan mata tagari. A cewar Taiwo, “mata nigari yanzu aka fara haifarsu”.
Shirmen Kiki ma ya taimaka kwarai wajen cheering dinsa up. Ya fara murmushi, murmushinnan nasa mai matukar kyau da aji, da Kiki ta hau jan kasumbar daya bari a fuska wadda bata saba gani a tareda shi ba, ya dan fara sakin ransa da mantawa da damuwar Hasinah Ambursa don ita tafi bashi mamaki fiye da Adetokumbo wanda dama su maza ai kunyarsu ragagga ce akan macen da zuciyarsu ta kwadaita musu.
Shikuwa Tokumbo Akanni a ranar bai kara kwana a Tokyo/Japan ba, yana jin karshen shigarsa kasar Japan din kenan gabadaya, har dai in Abdulrasheed yana cikinta, duk da a can ne harkokin kasuwancinsa suka fi yawa.
Taiwo da Kiki, basu baro Tokyo ba saida suka kwashe sati tare da Prince Abdulrasheed (Kehinde), har sai da ta tabbatar Prince din ya manta da damuwar da Hasinah ta haddasa masa, ya koma harkokinsa da rubutun project dinsa amma ko sunanta yace kada ta kara ambata masa.
A zahiri Prince Abdulrasheed ya saki ransa sosai yadda Taiwo keso, har ya koma harkokinsa na baya ya soma duba schedules na tournaments, yayi kokarin da ya kammala project dinsa kaf tun kafin barin su Taiwo gidansa. Musamman da komai Taiwo ke masa cikin gidan na kula da abincinsa da tsaftar gidansa da lallashinsa shi kawai aiki yake wuni yi akan kwamfuta.
Amma abinda Taiwo bata sani ba shine mummunar illar da incidence din yayi a zuciya da tunaninsa, ya riga ya gurbata psyche na tunanin sa akan mata da soyayyar dukkan diya mace in general.
Ranar da suka kwana bakwai tare dashi Taiwo da ‘yarta suka juyo gida Lagos cike da kewarsa. Da alkawarin sai sun zo bikin kammala karatunsa nan da ‘yan watanni masu zuwa.
***** ***** ****
WACECE NENNE SAPPA?
Nenne (na nufin ‘Uwa’ kenan), da harshen fulatancin Arewacin Najeriya na sassan Gombe, Adamawa da Taraba, wanda Hajiya Sappa ta fito daga cikinsu, kuma da shi yaranta ke kiranta, Nenne Sappa, irin iyayen mun nan ne na zamanin da, masu halin zuhudu (gudun duniya), taqawa, da tsananin yawan ibadah wadanda duk halaye ne na NANI OUMMANA.
Mahaifiyar ta Nani Ummana ta kasance mace mai yawan kaskantar da kai, da gudun rudin duniya, wadannan sai suka zamo halaye ne wadanda dasu ta raini Sappa, duk wani halin tawali’u wato humbleness (a down to earth personality) Nenne Sappa ta hada shi cikin kyawawan halayenta.
Nenne Sappa ta kasance kyakkyawar dattijiya, fara ce kal, jazur da ita mai yalwar sumar kai, gira data idanu, mahaifiyarta Nani bafullatanar garin Gombe ce don haka kusan zamu ce kamanninta Sappa ta debo, wadda yawan shekaru baisa kyawunta ya gushe ba sabida hutun da take ciki kuma jikinta mai boye shekaru ne, yanayin jikinta ya nuna cewa an zuba kyau da farin jinin manyan sarakuna a zamanin kuruciya.
Kai kace Sappa ita ta zabarwa kanta duk wata kankanuwar halittar dake jikinta don kyawun fasali, har zuwa yanzu data baiwa sittin da biyar baya, Nenne Sappa, na nan da extra added beauty dinta (zallar kyawunta).
Kenan a takaice sai mu ce Nenne, (Hajiya Sappa) ta samo personality dinta na (Down to Earthiness) ne daga mahaifiyarta Nani Oummana, wadda ta kasance uwargida a cikin duka matan Maimartaba Uban Kasar Gombe, Sarkin Gombe na goma, wanda duk da kasancewarsa basarake to gawurtaccen Shaihun malami ne shima. Nenne itace ‘ya ta biyu cikin ‘ya’yan da ya haifa masu tarin yawa da matansa na aure hudu.
Cikinsu duka yafison Oummana da suke kira Nani wadda ta kasance mahaifiya ga Haj. Sappa. Bayan rasuwar Sarkin Gombe wato mahaifinsu Nenne a dakinsu ne aka gaji sarautar.
A halin yanzu Yayanta da suka fito ciki daya ne akan karagar mulkin Gombe wato Maimartaba Sarki AbdulYassar Jalloh Umar (CFR).
Tsohuwa Oummana ta cigaba da zama ne a dakinta bayan rasuwar sarkin Gombe Ahmadu Jalloh Umar, yayinda sauran matan da yake da sauran kuruciyarsu duk suka fita suka sake aurarraki. Don haka ta zama uwa ga ‘ya’yan sarkin Gombe bakidaya wadanda ta haifa da wadanda bata haifa ba wato diyan kishiyoyinta duk ta hada ta rike ta mayar nata don yanzu babu iyayensu mata a gidan.
Sarki AbdulYassar babban dan Nani Oummana shi Hajiya Sappa ke bi haihuwa, sai autan Nani Abdulmajid wanda ke kasar Morocco da iyalinsa, sukenan ‘ya’yan da Nani ta haifawa uban kasa, sauran ‘ya’yansa maza da mata guda goma sha biyu duk na kishiyoyinta ne amma bazaka taba iya banbance wadanne ne wanda Nani Oummana ta haifa da wadanda take rikewa marigayin mijinta ba, saboda adalci da halin dattaku irin na mutanen da.
Da irin wadannan kyawawan halaye Nani Oummana ta raini diyarta Sappa mace daya (Nenne Sappa) cikin maza har itama ta girma suka aurar da ta ga zuri’ar Akanni’s tun mahaifinta yana raye, har itama a yanzu gashi ta tara nata bataliyar iyalin.
A yadda Hajiya Nenne take gudanar da rayuwarta wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yanta hudu dake gabanta, sak halin mahaifiyarta Nani Oummana, ba bazaka taba cewa ita din ‘yar Sarki kuma jikar Sarki, sannan matar babban dan Sarki, uwa ga jikan Sarki na farko bace.
Sabida yadda take nuna musu gudun duniya da mantawa da madaukakiyar nasabarsu, ita dai burinta shine su bi Allah, su kasance masu tausayawa mara karfi, su kiyaye sallah akan lokaci, su nisanci zinah kowacce iri kowanne nau’I ce, wannan itace tarbiyyar Nenne kullum ga yaranta hudu, duk wani burinta a yanzu shine ya zamo cewa halinta suke kwaikwayo, halin kankan da kai da tawali’u, shi takeso Taiwo da Kehinde da kannensu twins mata guda biyu wato Firdausi da Fatima su siffantu dashi.
Amma me? Cikin ‘ya’yan nan nata guda hudu kowa halinsa daban da nata, babu mai irin halinta na kaskantar da kai. Suna gudanar da rayuwarsu ne bisa tsari na ‘ya’yan manyan sarakuna da irin tarbiyyar gidansu na Akanni’s wato yadda suka taso suka tarar a masarautarsu ta Ilorin. Kakansu Sarki Abdulrasheed da kansa ya taba cewa Nenne ta haifo masa jikoki masu halaye daban-daban da yake tinkaho da dabi’unsu na sarauta. Abdulrasheed baya rayuwa irin wadda take so, baya zama a kasarshi, rayuwa ce yake yi daidai data ‘ya’yan gata kamarsa, domin Kakansa ya tsaya masa.
Taiwo kuma miji ya tsaya mata don ba karamin dukiya Toufeeq ya mallaka a turai ba.
Sannan Fatima da Firdausi Yayansu Abdulrasheed da suke kira Hamma wato (Prince) ya dade da tsayawa rayuwarsu matuka, tun shigarsu jami’a yake dawainiya dasu, bai yarda Dade (mahaifinsu) ya kashe komai akan karatunsu da bukatunsu ko dawainiyarsu tayau da kullum ba, shine komai nasu, baya so su kannen sa su nemi wani abu komai tsadarshi su rasa tunda shi ba iyali ya ajiye ba, so kusan zamu iya cewa komai na Prince na ‘yan uwansa ne baida wani buri bayan walwalarsu da wadatuwarsu.
Princess Fatima da Princess Firdausi nada albashi mai tsoka duk wata kai tsaye daga account dinsa zuwa nasu. Haka Kiki da Hakeem ‘ya’yan Taiwo.
Hajiya Sappa kullum tsaye take a kansu da addu’a, shine kadai saukinta. Musamman shi da yayi nisa da ita, kullum ko a waya bata fasa tunasar da shi bin Allah, kaunar musulunci da kiyaye sallah, ko yana dauka ko baya dauka ita dai Nenne bata fasawa kuma bata fasa yi masa addu’a ta musaman a duk inda yake cikin duniya Allah ya kare mata shi daga rudin zamani dana kuruciya, kasancewarsa namiji daya tal a cikin mata uku da Allah ya bata.
A yadda Hajiya Sappa take rayuwa cikin yawan ibadah kullum, da kula da bautar aure da mijinta uban ‘ya’yanta, kai sai kayi tsammanin ita din wata waliyya ce. Shigarta kullum cikin hijabai (jilbabs) kala-kala kamar bata da alaqa da kowacce sarauta.
Duk shekara Hajj da umarah basa wuce Nenne Sappah, bata azumin Ramadhan a gidanta dake Lagos sai a birnin Makkah da Madinah duk shekara, wani abun burgewa da Nenne in zata je Hajji bata bin International saidai Pilgrims duk cikin halinta na (down to earthiness) da kaskantar da kai, wanda take bi duk shekara daga hukumar alhazai ta jihar Lagos zuwa Saudiyyah.
Shekarun Nenne Sappa a halin yanzu sun kai kusan sittin da biyar a duniya. Yayin da mahaifiyarta Nani tayi tsufa mai inganci saboda ibadah, har yanzu cikin koshin lafiya Nani Oummana take rayuwa a Gombe da jinta da

Please Login or Register in order to submit comment