Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don ya samu sa’ida ya kuma huta azabar.
Nenne da Princess Fatima, suka taka suka isa gareshi suka tsaya a kansa suka kura masa ido, suna kallon kyakkyawar fuskarsa (with great affection) da alhini cikin idanunsu, daga bisani duk suka aje mayafansu akan kujera don yin alwallah su sauke sallolin da suka riskesu a hanya.
Har suka yi sallah suka idar duk AbdulRasheed yana barci na karfin allura baima san da zuwan nasu ba.
Pareto wanda shi yake kula dashi a asibitin kafin isowar ‘yan gidansu, shi ya kawo musu abinci na alfarma daga ‘restaurant’ din asibitin, daga cikin provisions din da aka yiwa Engnr. AbdulRasheed, duk irin abincin da yake so shi asibitin zai bashi, haka wadanda ke tare dashi don kula dashi.
Sai magriba ya farka, yana bude ido a hankali, ya yi tozali da Nenne a gefensa tana sallah, Nennensa, daidai lokacin data sallame sallahr, wani kyakkyawan murmushi Prince ya saki yana fadin,
“welcome my Nenne, saukar yaushe haka babu zato? What a surprise!”
Sannan ya yunkura ya tashi zaune da kyar, ta mike daga kan dardumar ta gyara masa filo a bayansa yadda zaiji dadin jingina sannan taja kujera daidai kansa ta zauna, shikuma ya gaisheta cikin harshen Yoruba. Ita kuma sai ta mayar masa cikin fulatanci, haka sukeyi daman, in sun yi mata tana ji amma bata mayarwa, don har gobe Nenne jefi-jefi take yin yaren mijinta da ‘ya’yanta, tafi rike nata da kyau. Bata son yadda yaranta suka fi yin na Babansu suke kin yin nata, ba kuma don basu iya ba saidon sun fi girmama nasu.
Nenne ta koma kujerar daidai kanshi ta zauna, ta dubi yadda ya sha daurin bandeji waje-waje, hannu da kafa duk karaya, tayi kwafa cikin damuwa da takaici ta ce.
“Isn’t this enough Hammansu? Ni na tabbata yadda ka dauki hawa Dokinnan da muhimmanci bana jin ko aikinka kana maida hankali haka a kansa.
Balle kuma sallah da ibadar Allah, na tabbatar suna wuceka, alhalin kana bisa sabgar Dawakai, wadanda su kadai zasu tserar da dan adam ranar lahira ba wasan tseren Doki ba”.
Sai kuma Nenne ta dakata kadan sannan ta sassauta murya ta koma yin magana wannan karon cikin lallashi da lumana, ganin yadda Prince ke wani irin yamutsa fuska akan zantukanta, baya so take cewa baya ibadah sai hawa Doki.
A ganinsa yana baiwa kowanne lokacinsa yana kokari kwarai wajen kiyaye sallah a duk inda ya samu kansa. In akayi la’akari da irin schedules dinsa. Yana irin nasa kokarin a ganinsa.
“Magana ta domin Allah, Hammansu, ka maida kan ka kamar wani tsuntsu mai tashi sama kan fiffike, yau baka nan gobe baka can duk don hawa Doki?? Ni menene a cikin hawa doki ne? Ka ki tsugunnawa a wuri guda ka fuskanci rayuwa ta reality. Saboda Allah yaushe rabon ka da zuwa aikin Hajj don sauke farali balle umarah da take sunnah?
A tunanina duk wata daukaka, ko suna da kake nema cikin wannan sana’ar ina ganin zuwa yanzu daka mallaki kofunan Zinare sau ba adadi a sanadinta, in ban yi kuskure ba kofunanka sun kai biyar, ko shidda, ina ganin ai ka gama samun daukakar Polo kuma Hammansu.
Ko tunanin aure da aje iyali baka yi wanda shine wajibinka a rayuwa ta hakika kuma mai ma’ana ga dan adam, ba don komai ba sai don saboda hawa doki ne kadai a ranka, ka manta cewa harka fita shekarun kuruciya da jimawa ka shiga na girma, don ma dai bakayi kama da shekarun ka ba; you are still looking fit and healthy”.
Nenne ta kara kwantar da murya yadda dole dan nata ya tausaya mata, tace “Abdulrasheed ko tausayina baka ji, duk faccalolina sun ajiye jikokin ‘ya’yansu maza ni ko daya babu, ba don Taiwo ta bani ba, jikoki ba da saidai kowa ya riga ni tarawa, har wadanda sukazo a bayana, ga maganganun nan marassa dadi da duniya ke yi akan ka suna dawowa kunnenmu, haka ‘yan uwan ubanka suma suke yimin irin tasu tijarar a kanka, suna ganin ni na hana Ubanka kara aure har tsufansa, haka zai mutu da mace daya kamar rai sai kace auren zobe, kai kuma dana haifa mun daure maka gindi kana yawon tambada da lalata a duniya ka ki cika Sunnah, kana gudun aure wanda yake sunnar Annabi SAW.
Ka ki ko tsayawa kayi tunanin ya kamata ace a wannan matakin na rayuwarka kana da yara lafiyayyu har guda uku ko hudu.
Yau dai tunda Doki ya kusa hallaka ka kana ji kana gani, ina ganin ya kamata ka hakura dashi haka Kehinde! Babu sauran alfanu kuma a cikin hawansa”.
Prince AbdulRasheed ya muskuta ya gyara kwanciyar sa cikin jin azabar zafin ciwo irin na hadewar kashi, yace.
“Nenne bana so ko kadan kike sakawa kanki damuwa akan abinda at least kin riga kin san bazan iya bari da sauki ba.
Polo ya zama wani bangare na jikina Nenne, ina yi ne kawai don jin dadina da biyan bukatar sha’awata ga wasan Polo, amma ba don tara kofuna ba, yana debe min kewa yana hanani tunani yana kuma hana ni damuwa da komai, ba don neman wani abu kuma nake Polo ba ko da can balle yanzu da nake da aikin yi kwakkwara, don haka banaso kina damuwa da ance-ance din mutane wadanda basu da gadonka. Su mutane ai al’adarsu ne damuwa da abinda bai shafesu ba.
Abinda ka kwashe rabin shekarun rayuwarka kana yi yana da wuyar bari a dare daya kuma farat daya Nenne. Kimin addu’a, idan inada rabon barin hawa Doki in bari a hankali.
Nenne nifa zan iya ajiye aikina na refinery dungurungum! In rungumi wasan Polo shikadai.
Idan Doki shine ajalina haka Allah ya kaddara min Nenne”.
Yayi dan shiru yana dan haki, na zafi da zogin ciwon karaya, kafin yace “Nenne tun shigowarki bakiyi duba da halin ciwo da nake ciki ba, sannan ko jajen raunin da SAHEEB yaji baki yimin ba kin hau ni da fadan rashin aure anya Nenne?
Ki godewa Allah da ban zarce ba, na barki da ciwon rashina bana rashin aurena ba.
Kimin addu’ar samun sauki da gaggawa kinji Nenne na, ki daina damun kanki akan abinda banida rabo a cikinsa, ki roka min tsahon rai da lafiya mai amfani mu rayu tare, yafi min rayuwa da wata mace, tunda ba wani abun kunya na ke yi a yawon hawa Dokin nawa ba, sha’awa ce kawai, hobby na ne kawai yin wasan Polo.
Amma ba haka kawai rana daya kice lallai in bar abinda nafi so a rayuwata ba, wai don tsautsayi ya gitta min wand aba yau farau ba, kuma mutane suna maganar banza a kaina da ke, ina ruwana da maganar mutane?
Ko an gaya musu inada business da mutane su yabe ni ko su zage ni?
Aure ra’ayi ne, kuma banida ra’ayin yinsa a yanzu, tunda dai auren nan Sunnah ne ba farillah ba”.
Nanne sai ta zama speechless, ta rasa me zata ce masa kuma, duk ta inda tabi don Kehinde ya gane damuwarta da ciwon ranta akan rashin aurensa bazai gane ba, ta yarda kuma babu abinda zai sa AbdulRasheed barin Polo, idan wannan karairayewar da ta sameshi yanzu, basu saka ya barta hakannan ba.
Ta kuma yarda bashi da niyyar yin aure nan kusa, aure baya ransa kwata-kwata, baya cikin burikansa da fatansa na gaba, burinta na samun jikoki daga jikinsa, bata san ranar da Allah zai dubeta ya cika mata shi ba.
Wayar Murjanatu ce ta katse tunanin Nenne, ta boye dan guntun hawayen da ya tsatstsafo mata. Hankalin sa kacokam ya koma kan waya da Aunty Taiwo dake ta koka jin abinda ya sameshi ta waya tana zata taho itama yana ta zauna ai ya ji sauki, yana lallashinta da taushin murya, yana gaya mata ta san dai ba yau ya fara faduwa a Doki ba, shi nasa ciwon bai daga hankalinsa ba kamar lafiyar SAHEEB dinsa.
**** **** ****
Zaman jinyar Nenne da Fatima tare da AbdulRasheed a asibiti, ya taimaka matuka gaya wajen samun lafiyarsa da wuri, sakamakon addu’o’I na (Ayatushshifa) da Nenne takeyi kullum a ruwa tana bashi yana sha dare da rana, da kuma dorewar lafiya da take roka masa a duk bayan kowacce sallahr farillarta.
Ya fara jin sauki sosai cikin ‘yan kwanaki kalilan, har yana tashi ya zauna yayi sallah daga zaune, bakin Nenne baya hutawa da yi masa nasiha akan bin Allah da tunasar dashi soyayyar Manzonsa, saidai in basu kadaice a dakin jinyar ba.
Har ila yau Nenne bata gushe ba da nasiha sannan bata fasa ba. A kullum bata gajiya wajen nuna masa muhimmancin aure da ajiye iyali ga faein ciki da cigaban rayuwarshi, cikin nasiha da lumana, ta kan ce masa ‘ya’ya sune gatan bawa duk arzikinsa, tunda su zasu dinga yi masa addu’a a bayan ransa. Kuma su tsaya masa a sanda yake bukatar su.
Auren kuma da yakewa kallo na daban Nenne tana kokari wajen nuna masa cewa ibadah ne ba son rai bane.
Koma meye dalilinsa na gudun yinsa bai isa dalili a wurin Ubangiji ba, tunda dai ya bashi lafiya da abinda lafiya zata amfana.
Tace ana yinsa ko ba’a so domin katange kai daga sabon Allah da tsarkake kai daga daudar zinah da katange zuciya daga sha’awar aikata sabo kowanne iri ne.
Wadannan sune ire-iren kalaman Nenne Sappa ga danta Prince Abdulrasheed lokacin jinyarshi. Princess Fatima kuma ita ke bashi abinci a baki da cokali.
Yau daya gama cin abincin rana, Princess Fatima tana gyara masa filon da zai kishingida ta bayansa, a cikin tarin sumar kansa sai ta hango tsillin ‘furfura’ a cikin gashin kansa. Ta kai waje guda 20 a cikin lallausar sumar kansa, ta kuwa ce me zata yi ba sakin shakiyyar dariya ba.
Princess Fatima tasa hannu ta tsigo furfura guda daya daga saman kansa, tana dariya tana kanne ido ta nunawa Nenne, tana fadi cikin yanayi na (banter) harda neman sikewa don dariya,
“someone has finished, ooh my Dear! Getting white hair before even getting a first wife…
Nenne furfura ce fal! A kan Hamma!”. (Ta kara gishiri).
To ma yanzu sabida Allah Nenne, wacece zata yarda ta auri mutum over 40 kansa duk yaci furfura?
Ai saidai kwantan ‘yammata kamarsa dan (mid forties), irin bazawara mai ‘ya’ya biyu haka, ko widow (wadda miji ya mutu ya barta) haka dai, amma ba dai (sweet 16) ba!”.
Nenne an sosa mata inda yake mata kaikai, sai ta gyada kai tace “in ya samu sweet 16 din sai ki hana ruwa gudu! Furfura baiwa ce ‘yar nan, ba itace tsufan namiji ba, wani ma sai ya fara ta yake fara jin mazantaka da karfin samartaka, rashin aure haka kawai babu dalili shine mishkilarsa, domin tamkar izgili ne ga rahamomin da Ubangiji yayi maka Abdulrasheed.
Saidai kuma bansani ba ko abinda mutane suke fadi marar dadi a kanka din, ko gaskiyane Abdulrasheed?”
Yanayin fitar sautin muryar Nenne, a halin yanzu ya nuna helplessness din da take ciki akan situation din, wanda hakan yayi matukar karya zuciyarsa, jikinsa yayi sanyi matuka, amma dai bai yi magana ba.
Princess Fatima, ganin yanayin da suka shiga na damuwa su duka, sai ta dauki ipad dinta ta bar musu dakin, ta koma can reception na asibitin ta samu kujera ta zauna tayi tagumi itama, don taga zancen na Uwa da Danta ne, kuma yau raunin Nenne da bakin cikin ta na shekara da shekaru akan rashin aurensa yafi na kowacce rana bayyana a tare da ita da nauyin shekarunta da suka bayyana kan kyakkyawar fuskarta yau saboda damuwa.
Wai AbdulRasheed ya fara furfura ba aure!!!
Wannan al’amari ya tsorata Hajiya Sappa matukar tsoratawa.
Fitar Princess Fatima keda wuya, sai ga hawaye mai kauri ya tsinke a fuskar Nenne Sappa. Kamar jira take Fatima ta gusa.
Hankalin AbdulRasheed yayi tashin da bai taba yi ba yau, ba yau Nenne ta soma korafi da kuka akan rashin aurensa ba, amma na yau yafi na kullum daga hankalinsa ko mai yasa? Don ya ga bakin cikinta muraran a idanunta.
Abdulrasheed ya shiga rokon Nenne cikin kaskantar da kai, akan ta gaya masa menene exactly damuwarta har haka akan rashin aurensa, take irin wannan zafafan hawayen dalilinsa, masu barazanar tarwatsa rayuwarsa?
“Zubar hawayenki a kaina Nenne masifa ne a gareni kin sani”.
Nenne Sappa saida ta yi sharbe son ranta, tana gogewa da habar hijab dinta. Kafin ta soma Magana cikin rauni da karaya.
“Na soma zama cikin zargi mai girma a kanka nima!
Na soma yarda da zargin da duniya ke maka, na cewa neman maza ‘yan uwanka kake yi (you are gay) shine abinda yasa ka juyawa auren Sunnahr Ma’aiki SAW baya. Haka ne ko ba haka bane Kehinde?”
Nenne ta tsatstsareshi da jikakkun manyan idannunta da suka rine kamar garwashi suke jike shatab da hawaye mai yawa.
Ko kadan babu firgita kan kalamanta a tare da shi, ko don ba yau ya fara jin ana zarginsa da hakan ba? Jin maganar yau daga bakin mahaifiyarsa shine babban abinda yafi tada hankalinsa.
Amma ko kadan babu tashin hankalin maganar akan fuskarsa sai tsantsar damuwa da yanayin da mahaifiyarsa ke ciki.
Abdulrasheed yace (cikin despair).
“Nenne in kowa zai min wannan mummunan zargin ke UWATA (mahaifiya) ya kamata ki kyautata min zato.
Ban taba zaton Nenne ranki zai yi bacin da zakiyi duba da wannan banzan zargin na mutane marar tushe da hujja ba, tunda kin san irin tarbiyyar da kika yi mun da hannunki, ba wani ya tarbiyyantar miki ni ba, kuma kinada tabbaci a kan ingancinta, na cewa ko bayan ranki bazan zubar da ita ba, balle da ranki da lafiyarki in yi wannan mummunan aiki.
Anyway, bazan musa ko daya ba, cikin abubuwan da ake zargina dasu din.
Allah ne kadai ya san zahiri da badinin zuciyar bayinSa, da abinda suke aikatawa na fili dana boye, kuma shaidarsa nake nema bata mutane ba Nenne, tunda ke kanki da kika haifeni kin kasa shaidata….…”.
Yayi shiru, ya koma ya kwanta yana maida numfarfashi da sauri da sauri kamar mai ciwon asthma. A hankali AbdulRasheed ya rufe idanunsa…. Mummunan ‘scene’ din na Hasinah da dan uwansa kuma wanda ya rika a matsayin “amini” duk cikin family dinsu Adetokumbo akan gadonsa na gilma masa. Abinda ya faru kusan shekaru goma sha hudu a baya, amma har yau yake ‘haunting’ dinsa… ‘trauma’ din abun ya kasa barin ransa ya huta, zuciyarsa ta sake da mata.
Cousin dinsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni da fiancée dinsa Hasinah Ambursa turmi da tabarya, kuma a kan gadonsa sannan a dakinsa mallakinsa a gidansa dake kasar Japan.
Wani ‘incidence’ ne da kullum yake komawa ‘GREEN’ a idanunsa… ya kasa barin duhun idanunsa su huta ko hasken wata mace ya ratsa ta cikinsu.
Shikuwa me zaiyi da mata yanzu? Ai ya dade da rufe babinsu daga kan Hasinah Bello Ambursa.
A cewarsa dukkansu are nothing but ‘Gold-Diggers’, wadanda in dai namiji zai basu kudi to ya gama samun mutuncinsu, kowanne kare da kowanne doki ma yazo ya fanshi mutuncinsu da diyaucinsu in dai yana da kudi.
A tasa mummunar fahimtar da ya dade da yiwa mata daga kan Hasinah, wadda ta dade da yin babakere a zuciyarsa ya gama yardarwa kansa duk matan yanzu irin Hasinah ne, masu son holewa ta jiki data aljihu, ya yarda mafi akasarinsu namiji daya ba zai taba isarsu ba, batare da sun zagaya sun ci amanarsa ba ko me zai musu na halacci kuwa, ko me zai basu iya karfinsa don kula da lalurorinsu, kuma koda zai yagi naman jikinsa ya basu bazai hana su hango wanda ya fishi samu ba, they are totally greedy, rashin wadatar zuci ya yiwa zakatan ‘yammatan yanzu katutu, babu soyayya ta saboda Allah a zuciyarsu yanzu.
Shiyasa yake ganin bashida mata a duniya, ba’a haifi macen da zai kara gangancin so ba, bazai kara yarda da mace a duniya da sunan soyayya ba in ka cire soyayyar da yake yiwa Nennensa da ‘yan uwansa mata. Bai ki ba dai a gidan aljannah in yana da rabo.
Me yasa mostly kyawawan mata kamar Hasinah ne kullum suke yin dage, domin hango wani wanda bai kama kafar mijin da Allah ya basu a komai ba? Marasa shararren kyau zaka samu basu cika dage ba.
Me ya rasa da Da namiji ya rasa daya cancanci abinda Hasinah tayi masa? Me Tokumbo zai nuna masa banda cikar aljihu a lokacin?
Idan har aljihun wani namiji dan uwansa ne zai sa Hasinah yi masa haka, to kuwa duk matan duniya ya dade da yi musu jimilla da ‘gold-diggers’, kwadayayyu, hadamammu, ma’abota manta halaccin mai halacci, wadanda burinsu kawai namijin da zai basu kudi suyi bushasha, ba wanda zai so su saboda Allah ba, kuma wanda zai kwatanta irin soyayyar da suke so ta banza da da sunan itace soyayyar da zata bulle dasu, koda kuwa ace babu abinda Allah ya rage ka dashi a rayuwa.
Ya rasa wane irin jin dadi mata ke nema a wurin namiji fiyeda daya. Shi kuma Allah da ya halicceshi yayi shi mai matukar kishin kansa da kishin macen da yake so, watakila shine dalilin da yasa daga kan Hasinah ya daina sha’awar kowacce mace sai Polo dinsa, yanada kishin kansa fiyeda yadda harshe zai iya bayyanawa!
Nenne ta rainesu akan turbar tsoron Ubangiji, tana tare dasu ko bata tare dasu suna tuna Allah, ta rigada ta dorasu akan turbar gujema ketare iyakokinSa.
In aka duba kuma, a rayuwa ba abinda bai yiwa Hasinah ba, a matsayinta na wadda yaso aure da dukkan zuciyarsa ba tareda tunanin banbancin nasabarsa da tata ba, kuma marainiyar da ya fiddo daga gidan marayu, ya maidata daliba mai ‘yancin higher education, ta hanyar sponsoring karatunta daga gidan marayu zuwa Lagos eventually zuwa kasar Japan ba tareda sanin kowa nasa ba bayan Taiwo.
Bayana fara karatunta na jami’a ya zama shine uwarta shine ubanta a Tokyo, shine cinta shine shanta, shine sutturarta da duk wani shopping dinta duk don ya katangeta daga neman wani abu ta rasa a rayuwarta duk da shima a lokacin ya dogara ne da abinda Kakanshi ke turo masa duk wata, da na mahaifinsa, a matsayinsa na dalibin postgraduate, soyayya ta gaskiya ba irin wadda bai yi mata ba, har da ta kauce hanya, domin ta saka shi ya danyi deviating daga tarbiyyar da Nennensa ta bashi, duk don ya faranta ma fiancée dinsa Hasinah ya kuma katangeta daga sha’war wasu mazan ba don yana so ba.
A dalilin ganewa da yayi cewa ta soma wayewa da irin wannan rayuwar da tazo ta tarar ‘yammata da samari kamarta nayi a jami’a, lokacin da ya fahimci ita din mai son wannan rayuwar ce sai ya biye mata, bisa dalilai guda biyu; na farko son da yake mata, na biyu tsoron shi na kada ta kwadaici wani, idan shi din yaki biye mata.
Da wannan Hasinah ta dulmiyar dashi a baya cikin rayuwar soyayyar shan minti, kazamar rayuwar da ’yammata irinta ke yi a turai, rayuwa ta rashin tarbiyya da baya ko son tunawa yayi da Hasinah yanzu.
Duk da haka a kullum yana godewa Allah da bai taba sanin Haseenah diya mace ba (as in having sex) bai taba ba. Sai abinda ba’a rasa ba bisa jagorancinta.
Amma duk da soyayyar shan mintin da ya biye mata suka soma ba don yana jin dadin afkuwar hakan ba, saboda a irin son da yake ma Hasinah yafi so ko meye zai shiga tsakanin su sai ya mallaketa ta hanyar aure, amma ta nuna ita bazata iya jira har zuwa wannan lokacin da Nenne zata amince da maganarta ba, dole ya biye mata suke kananan abubuwan da har ransa baya so. Don kuwa mace duk inda take komai kankantarta shaidaniya ce, balle shaidancin Hasinah mai license ne tunda ‘yar kwararo ce, amma duk da hakan biyemata din domin ya katangeta bai sa ya iya ya rike sha’awarta da hangenta da kwadayinta na abinda shi har lokacin ya kasa yi mata ba, saboda addu’ar Uwa ta dare da rana dake tasiri a kansa, ya kasa rike sha’awar Hasinah daga sauran mazan da basu kaishi komai ba.
Amma a bukatun rayuwarta kam na yau da gobe baya jin ya gaza, sai dai don ta kasance mai son bushasha da sha’awar rayuwar kere sa’a.
By Allah! Yayi duk wata bajinta da namiji kamarsa mai gata da asali da nasaba tsarkakakkiya ta sarauta da ilmi mai zurfi da malanta bazai yi akan matar da ya tsinto a kwararon gidan marayu ba!
Bayan duk wannan wane irin sakamako ya samu a mahaukacin son nan kuma gurbatacce da yayiwa Hasinah???
Prince ya runtse ido da karfi, yana tuna Hasinah a ranar, da kazantaccen yanayin da yazo ya samesu ba zato, mantuwa yayi ya dawo, abin mamaki tareda kaninsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni, the worst part dinma kuma a dakinsa sannan a kan gadonsa.
Saboda kawai Abdulfatahi ya fishi kudi, ya fishi iya shege ya fishi rashin tsoron Allah, uwa uba yanada ra’ayin yin bushashar arzikinsa ga matan banzan duk da zasu bashi jikinsu, don a lokacin shi Abdulfatahi wani babban Automobile Business Mogul ne, kasancewar a tsakanin Japan da Spain yake harkar shigo da motocinsa, to duk sanda ya shigo Tokyo a wajen dan uwansa Prince Abdulrasheed yake sauka, baya sauka a hotel, kuma ta haka ne ya san Hasinah a matsayin fiancée din dan uwansa, har suka saba shi da ita suna tsokanar juna irin dai wasan nan na kanin miji da wadda Yayansa zai aura.
Yaya akayi-yaya akayi suka sarke a bayan idonsa kuma bai taba gane komai a tsakaninsu ba banda sani da yayi tun fila azal Hasinah mai dogon buri ce, mai kwadayi ce, mai son kyale-kyalen mata na fita tsara ce wato (Hasinah is a designer baby) sannan yana ankare da cewa tana son wannan harkar, a hakan kuma yana iya bakin kokarinsa akanta, don ganin bata rasa komai take bukata ba, kusan duk abinda iyayensa ke aiko masa a matsayinsa na dalibi a lokacin akan bukatun Hasinah masu dan Karen tsada yake karar dasu da kwalliyarta na sittiru tsadaddu, da kayan kawa da khyale-khyale ba tareda Nenne ta sani ba. Ko dama ita Nenne from day one, Hasinan bata kwanta mata ba tunda aka ce a gidan marayu aka daukota, tun a lokacin Nenne tace “NASABA” wato tsatso, wani abu ce mai girma da muhimmanci a neman aure to amma Hasinah fa?
Suwa zata bugi kirji ta kira Kakannin jikokinta na wajen uwa na jikin Abdulrasheed Kehinde?
Shikuma har a lokacin lallaba Nenne yake yi akan ta yarda ta karbi Hasinah a matsayin surukarta, ita kadai zuciyarsa keso, ita yake yiwa kauna ta saboda Allah ba zai iya auren kowacce mace in ba itaba.
Shi ya bata surname da Bello Ambursa lokacin da zai shigar da ita makaranta, sunan abokinsa Bello da ya rasu.
Sakamakon da ya samu a duk wannan sadaukarwar da yayiwa Hasinah shine Hasinah ta bige da cin amanarsa, itada dan uwansa mafi kusanci dashi, mafi kazantar cin amana har a gadon barcinsa kuma a gidansa. A cire maganar girman zina wadda lahani ce mai girma ga martabar diya mace.
Abin ya kara dawo masa sabo. Kamar yanzu-yanzu ya faru. Shekaru goma sha hudu kenan da faruwar al’amarin a can baya, amma kullum sabo scene din yake koma masa a idanu da zuciyarsa, in ya tuna ko aka yi masa fadan yin aure ko ya kamata ya zabi matar aure a family dinshi. Nan da nan jikin sa ya hau tsuma, zazzabi mai zafi ya rufe shi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, zuciyarsa kamar ta hudo kirjinsa ta fito sabida yadda take hawa da sauka don bacin rai…..
Ya dade bai shiga bacin rai irin na yau ba sakamakon wannan dogon tunanin da yayi. Ita da kanta Nenne ta lura da halin canjin mood da kalamanta suka jefa dan ta Prince AbdulRasheed, sai taji wani irin babu dadi a zuciyarta da kasan ranta.
Ita ta san Abdulrashid dinta is always bold and smart fiyeda Taiwo, kasancewarta mace tanada saurin nuna rauni (sai karambani da rawar kai da shiga sharo ba shanu), but today he looks pale har fiyeda Taiwo uwar kankanba idan ta raunana.
A ganinsa tunda har uwar

Please Login or Register in order to submit comment