Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da 'kawayenta kamar babu wanda ke jiranta,, Nawaf yagaji da jira yafito, yasan matarsa tana bu'katar magani danyabaro jikinta da zazza6i, cikin asibitin yanufa, office ďinta yafara zuwa amma arufe, wanine yake gaya masa aii yau bata aiki tana hutu sai dare, ya ce, "ai tare sukazo,, mutum ya ce, "to inaga tana wajen 'kawayenta zomuje na rakaka 6angarensu, acan kuwa ya sameta tana ganinsa tafara wani kame2n binciken takardu,, ya 'karaso yana faďin ummuhabeeba wai har yanzu?,, ta mi'ke tana faďin abii yanzu na kammalane.
'Kawayena ga abiina na 9ja sunansa Nawaf,, suka mi'ke suna faďin woow!! Nice guy, dama sun sansa a hotuna datake nuna musu, suka gaisheshi ya amsa yana tambayarsu ya aiki.
Bayan sun gaggasa yayo waje, itakuma taimusu sigina da ido itama tafito tana dariya suma sunayi.
Amota ta tarar dashi, harya tada, tashigo tana faďin albishirinka abii, batareda ya kalletaba ya ce, "goro, saida taďan cije le6e ta ce, "matarka tanada ciki wata biyu, da sauri ya tsaida motar yana kallonta, ya ce, "da gsk kikeyi ko wasa?, ta ce, "wlhy da gsk, aii baisan sanda ya rungumeta yana murna ALHAMDULILLAH yaketa faďi, yayinda itakuma ta kwanta luf ajikinsa, da sauri ya tureta yana faďin wa'iyazubillah, ALLAH ka nisantamu daga sharrin shaiđan.
Shiru kawai ummu habiba tayi dan batada amsar bashi, haka suka 'karasa gida batareda ya kula dukkan maganganun datake masaba, yana zuwa ya rungume yasmeen babu ko kunyarsu momcy da hajja, ya ce, "fancy face albishirinki, da sauri ta tureshi dan kunyarsu momcy sai asannan ya kula dasu ya saketa da sauri yana sosa kai, yay 'kasa da kai yana faďin sorry mom & hajja.
Momcy ta ce, "kaidai kasani mara kunyar banza, to Albishirďin mi zakai mata??, ya sosa kai ummuhabeeba faďa musu kawai.
Ummuhabeeba dake tsaye kamar gunki tun ďazu, ta mi'kama momcy result ďin, momcy ta amsa tana dubawa, cikin murmushi ta mi'kawa hajja itama, hajja ta rungume yasmeen tana murna suka shiga mi'ka addu'oin alkairi ga cikin dabai wuce wata biyuba, kowa yana cikin farinciki da murna bare uban ginsamin Nawaf, momcy tabata shayi dakanta ta sha dayake ALLAH yasa cikin bamai saka ami bane, tanashan magunguna ta 6ingire barci abinta.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya da sauri, yasmeen tana samun kulawa wajen mijinta da iyayensa, yana zagayawa da ita ko'ina guraren tarihi da gidajen dangi, sunje har kabarin fiyayyen halitta (ANNABI MUHAMMAD ,,,S A W), Tanajin daďin rayuwar saudia, kusan kullum saitayi waya dasu yaseer da ameena tanajin labarin 9ja, satinsu uku papa yazo, shima yay sati ďaya sannan suka tarkato komatsansu zuwa 9ja, yasmeen tayi wani shegen 'kyau kunsan mai yaron ciki akwai bada kala, har wata 'yar 'kiba tayi, sun dawo 9ja suna kewar mutanen saudia,, su mas'ud ne sukazo tarbarsu.
Tun afilin jirgi ameena take mata tsiya wai kodai ta kamu?, dan taga tayi wani 'kyau na musamman, yasmeen ta harareta kedai kika sani 'yarsa ido,, to shima mas'ud ba'a barsa abayaba wajen tambaya, kusan amsa ďaya Nawaf yabashi data yasmeen, mas'ud ya ce, "mutumina karka faďa ainariga na gane kasandai ni likitane, Nawaf ya ce, "to sannu likita, ya faďa yana ďaga nanah dake hannunsa, ya ce, "Ameena mikike bama babyn mu tayi girma da 'kyau haka cikin wata ďaya??.
Ameena tayi dariya, babu abinda akebata, sai abincinta,, kai amma ďiyata 'yar baiwace, wlhy kuwa habibina yasmeen dake baya kusada ameena ta tafaďa.

Hakadai akacigaba da gungurawa cikin yasmeen yana fitowa, sati biyu masu zuwa kuma zasu cane 'kasar Spain, saidaifa papa kamar yana shirin hana tafiya da yasmeen ya ce, "idan ta haihu tataho daga baya.
Saidai nakula maganar bata shigi Nawaf ba sosai,, dan kamar baima yardaba, toko yaya za'ayi kenan kudai biyoni kawai.
Suma su yaseer da Anwar wannan satin suka ďaga zuwa 'kasar Rasha domin fara karatu a6angaren likitanci.
To abokan juna saimuce ALLAH ya taimaka, yasa adawo asa'a.......................✍🏻










© 2017

💓bilyn Abdul💓
💓Mrs Abdus'salam💓
💓luv u oll my fan's😘💓
[1/12, 9:11 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💓



Page👉🏻59 & 60

......Nawaf zaune a falo saman doguwar kujera, yasmeen tana kwance tayi matashi da cinyarsa, sunata 'yar hirarsu, yashafa cikinta yana faďin babyna saura wata biyar yazo duniya insha ALLAHU, yasmeen tayi dariya kai habibina wai har kafara lissafi.
Musrmushi yayi yana shafa kanta, lallaima fancy face ďina, kinsan kuwa yanda na 'kagara naga babyna aduniya, shiyyasa da papa ya ce, "baxaki biniba na rikice, mutum da matarsa ayita nuna masa fin 'karfi.
Yasmeen tayi dariya aiyanzuma bakada tabbacin xan bika ďin, yaďanja la66anta, ta ri'ke hannunsa tana faďin da zafifa habibina.
Ya murmusa ai dama zafin nakeso kaji, ke yanzu kina fata natafi nabarki ke kaďai?, duk faďin gadonnanfa ke kaďai zaki ringa kwana, ke kaďai kuma zaki ringa zama gidannan.
Kai haba ai kana tafiya 6angaren momcy zan koma kamar wancen karan, harararta yayi waike dan ALLAH da gsk kikeyi?, ya 'kare maganar da haďe fuska.
Yasmeen tayi murmushi tana shafa fuskarsa, A'a nifa wasa nake maka, ina zan iya farinciki babu habibina a gefena, insha ALLAHU 'kafarka 'kafata sai Spain, du'kowa yayi ya sumbaci goshinta, yanzu naji magana 'yammatana, yanda bakomai kike iya ci ďinnan ba natafi na barki ai hankalina zai rabu gida biyu, gashi muna komawa akwai manyan wasanni dazamuyi kinga kuwa ni bazan iya ta6uka komaiba.
A'a habibina kaifa jarumine wanda duniya takeson gani a filin kwallo, kanaso yaronka ko yarinya suzo duniya suji kakoma rago saboda rainon cikinsu??.
Ya saki wani lallausan murmushi, my zarah ke dabance acikin mata, kin iya magana mai taushi da daďi ga mijinki, da sauran maza zasuyi sa'a irin tawa da har abada wani bazaiyi tunanin sake aureba, ina alfahari dake amatsayin mata 'kawa 'yar uwa.
Yasmeen ta tashi zaune tana murmushi ta kama hannuwan Nawaf ta rimtse anata, cikin murya mai cike da kissa, ta ce, "nice nayi sa'a mijina, dan tabbas nafi sauran mata sa'a,, da samun miji kamili mai ilimi da tsoron ALLAH, wanda yake tattalin iyalinsa da sauke dukkan nauyin daya rataya awuyansa, nikaďai nasan sirrikan dake tattare da mijina, wanda baki bazai iya furtawaba saboda kar wasu matan suyi sha'awar ya kasance minijinsu koda amafarkine......, da sauri ya rungumeta yana murmushi, my xarah aikinriga da kin mallakeni nazama ra'kumi da akala, babu wata mace dazata sha gabanki awajena komai 'kyawunta, Nawaf na fateema xarah ne ita kaďai, ina 'kaunarki sosai fancy face, ina ro'kon ALLAH ya kasheni da 'kaunarki, kinriga kin zama wata tsoka mai muhimmanci daga sassan jikina, nidake mun wuce hanta da jini,, suka 'kara matse juna kowannensu yana zubar da hawayen daďi, yasmeen taďago tana kallonsa, ta ce, "habibina nima ina 'kaunarka har bansan yanda zan fassara irin 'kaunar danake makaba, dan sunyima bakina nauyi, Nawaf ya kamo fuskarta ya haďe bakinsa da nata, soyayya mai tsafta da tsada suke nunawa juna, dan ballagaxar mace bata samun irinta😡. Nima fitowa nayi nabasu waje🏃🏻🏃🏻.

Da hakadai suka fara shirin tafiya Spain wanda da 'kyar papa ya yarda atafi da yasmeen amma da sharaďin idan cikinta yakai wata takwas zai dawo da ita gida ta haihu, da sauri ya amince kuwa.
Suka fara shirin tafiya,, ya kaita gidansu ta wuni acan tayi musu sallama, gidansu mas'ud ma yini tayi, ranar juma'a suka ďage cike da kewar mutanen 9ja, suma sun barsu da kewarsu, dan tunda suka tafi gidan kamar anyi mituwa kowa yayi sukuku, har papa daba zama yake sosai dasuba shima sai yaji gidan yay masa wani iri.
Ya ce, "ummulkhairi kinga daga tafiyar yarannan yau har gidan yazama wani iri gashi babu auta, dagamu sai Abdallah sarkin rashinji, momcy tayi dariya wlhy Alhaji har wani zazza6i nakeji fa, Abdallah ma saida yasha magani yana ďaki kwance, shiyyasa akace sabo akewa kuka ba mutuwaba, balle yasmeen yarinyace mai shiga rai sosai.
Papa ya ce, "gsky ne yarinyar tanada ha'kuri gatada girmama nagaba da ita,, wlhy danma ba zaman gida kakeyiba shiyyasa, amma modebbo ya dace da mace tagari mai addini kam.
Papa yay dariya aidama haka ALLAH ya ke, sai yabaka abinda bakaso yazama alkairi arayuwarka, idan na tuna randa na sanarma modebbo auren yarinyarnan tamkar zai kwala min ihu koya hau bori, saiya bani dariya randa nace baxai tafi da ita Spain ba tamkar zai min kukafa, momcy ta tuntsure da dariya, itama ďin yasmeen kalar marasa lafiya tazama, shiyyasa nace kawai kabarsu su tafi, cikin yana shiga wata takwas idanma bai kawotaba ni zanje na ďakkota ne aii.
To ALLAH ya kaimu lokaci, yakuma sauketa lafiya,, ameen momcy tafaďa.

Sumadai ALLAH ya saukesu lafiya, suna zuwa barcin gajiya yasmeen tashiga yi, gashi dama jikinta babu 'karfi, Nawaf kam fita yayi dan yanada abubuwan yi masu yawa.
Tadaďe tana barci, saida ta warware a gajiyar data kwaso sannan ta mi'ke da addu'a abakinta, wanka tashiga tayi a haďaďan bathroom ďin, azuciyarta ta ce, "kaga masuyi dan ALLAH, wannan bathroom haka ai ďakin watane a 9ja, tagama wankanta tafito tayi shiri cikin 'kananun kaya, tana cikin fesa turare Nawaf yashigo rungumeta yayi tabaya suna kallon kansu amadubi, ya ďora hannunsa saman cikinta yana shafawa, my baby kabaro 'kasarka zuwa wata 'kasa wadda ta ri'ke maka dadyn ka ko?, yasmeen tayi dariya, to dadyn nasa yabarta mana, gefen wuyanta ya sumbata yana faďin inhar momy ta amince anjima ma saimu ďauki hanyar 9ja.
Hannu tasa tana shafo fuskarsa sunama juna murmushi ta madubi, ta ce, "A'a ban aminceba muyi zaman mu, Nawaf yatashi tsaye yana dariya to zomuje kici abinci babyna yanajin yunwa.
Falo suka koma dakansa yabata abincin taci sosai kuwa, ta ce, "lallai andace, tashi ďaya kikaci abincin nan batareda kin kusheshiba balle yatsina fuska.
Yasmeen tayi dariya nifa wlhy bammasan ina yatsina fuskaba idan banason abinci, okey bari sai ankawo wanda bai mikiba idan kinayi zan ďauki hotonki, kace terere zakami kenan?, babu wani tarere Nawaf yafaďa yana gyara wajen.
Haka rayuwarsu ta Spain tacigaba da tafiya cikin soyayya da jin daďi, suna bama juna kulawa, cikin yasmeen yanata girma, yakan fita yawo da ita taga gari idan yasamu lokaci, idan zasuje wata 'kasar buga wasa da'kyar suke rabuwa idan kuma tafiyar ta wuce kwana biyu to tare suke tafiya.
Komai yana tafiya musu yanda sukeso, suna waya da 'yan 9ja sosai, dakuma su yaseer, kosu haďu a yanar gizo, yasmeen tayi 'kyau abinta tayi 6ul2 ga cikin yayi mata 'kyau, mijinta yana kula da ita dabata farinciki, dan mace mai ciki tana bu'katar kasancewa cikin farinci.
To yanzu cikin yemeen yashiga wata na takwas, momcy fa tafara damun Nawaf da zuwan yasmeen gida, kwata2 bayaso yasmeen ďin tatafi saboda shi bashida damar zuwa 9ja yanzu amma yazaiyi, dole ya ďauki uzuri na kwana ďaya yakawota 9ja ya juya.
Su momcy sunyi farincikin ganinta, sosai nannama kulawa aka shiga bata ta musamman aďaki momcy take zaune, tunda cikinta yashiga watan haihuwa momcy tadawo kwana ďakin dan kar haihuwa ta risketa batareda an saniba.
Awata safiya litinin yasmeen ta tashi da na'kuda babu 6ata lokaci momcy ta kwasheta zuwa asibiti, kar6arsu akayi cikin gaggawa dan haihuwarce gadan2, Alhmdllh yasmeen ta zullu'ko 'katon ďanta maikama da ubansa namiji, karkuso kuga murna wajen wannan family, Abdallah yafara kiran Nawaf yasanar masa, tsalle yaytayi namurna gashi zasu shuga wasa alokacin, wannan farincikin ne yasashi nuna bajinta awajen wasan, saida ya zura kwallo sau uku, wannan lamari yayima koch nasu daďi ba kaďanba.
Tuni hotunan baby boy sun cika masa waya, kowa sai turo masa yake takafa sada zumunta, yaro ďan gatan dangi, zuwa yamma aka sallamesu dan komai normal, sundawo gida yayinda 'yan uwa da abokan arzi'ki suketa tururuwa wajen ganin ba'kon duniya, tsaf aka shirya yaro cikin kayan sanyi masu 'kyau da laushi, yasmeen ma tashirya tsaf tagyara jikinta, bayan taci ta'koshi ta haye gadon momcy.
Tana kwanciya wayarta tahau 6urari, cikin murmushi ta ďauka, cikin kissa ta ce, "ALLAH yabarni da baban baby,, Nawaf yasaki wani lallausan murmushi kamar yana gabanta, ameen dear fancy face, ina fata dai kina cikin 'koshin lafiya, keda sweet babyna ?, yasmeen tayi murmushi lafiya lao muke habibina, ykk kaima??, ya ce, "nima Alhamdllh, sannu da aiki fancy face nagodema ALLAH kema kuma nagode miki da kika haifomin 'katon ďana zuwa duniya,, yasmeen tayi dariya, kai habibina kaida baka gansaba ya akayi kasan 'katone??, yayi dariya lallai fancy face ai inagama narigaki ganinsa, aituni Abdallah da mas'ud suka sambaďo mini pic nasa, insha ALLAHU duk yanda zanyi sainayi nazo 9ja nextweek, to shikenan habibina ALLAH yakawo mana kai lafiya.
Amin xarah na yanzu ina babyna samin naji numfashinsa mana, hhhh ai yana falo wajensu momcy nikuma ina ďaki kwance,, ya marairaice murya to kije falon mana, ido tazaro lah habibina sokake ace banida kunya babu ruwana wlhy.
Yay dariya to sarkin kunya yizaman ki kar ace bakida kunya, amma kiďau al'kawari da an maidoshi kiyimin vedeo ďinsa ki turomin, karka damu naďau al'kawari, daganan hirarsu suka cigaba dazubawa cikin so da 'kauna, sun daďe suna hira, sannan suka kashe, ana kawo baby ďakin kuwa tacika al'kawari tayi video ta tura masa, tsalle yaytayi yana kallo saikace wani 'karamin yaro, ranar abinda yakwana yi kenan, haka yayta kallo yana maimaitawa.
Haka rayuwar take gudu da sauri, yasmeen tana ta jego, hargashi gobe suna, aranar kuma Nawaf ya iso 9ja, dangi sunyi farincikin ganinsa, shima yayi farincikin ganinisu, yarungume ďansa yana maijin 'kaunarsa jiyake kamar yatsaga jikinsa yasakashi, ranar ahanununsa baby ya wuni, da daddarema saida momcy ta koreshi waida nan zai kwana wajen yasmeen.
Washe gari akayi suna yaro yaci sunan MUHAMMAD ubangiji ALLAH yaraya muhammad amin, bayyana muku yanda sunan yakasance 6ata lokacine amma nabawa kowa dama ya kiyasta azuciyarsa, shagali akayi bana wasaba, hardasu hajja 'yan saudiyya,, lallai munra'kashe mun kwalle ranar💃💃💃💃💃kai harma 6arararrajewa mukayi, lol😜.
Bayan sati ďaya dagama suna Nawaf yakoma, yabar su yasmeen suna jego abinsu.

Sunyi arba'in yayinda yaro yayi 6ul2 abin sha'awa, nisainajima kamar subani😘😜lol, su yasmeen an zagaya dangi ko 'ina, kowa yana sambarka da wannan yaro.

Bayan wata uku.
Nawaf yadawo gida hutun 'karshen shekara, tarairayar yaronsa yake sosai, damma wani lokacin su momcy suna masa fin 'karfi saisu kwaceshi ya wuni awajensu shan nono kawai yakesa akawoshi wajen yasmeen, idan papa yana gida shima saiya kwace saikaga kowa yana zum6ura baki, dan kowa yanason ďauka, amma dole ya ha'kura tunda papa ya amsa, na ce, "kaga ďan dangi yanashan tarairaya,, hakadai rayuwa taci gaba da tafiya MD yana girma da 'kara wayo, dole su Nawaf suka barma su momcy, suka koma nunama juna soyayya da fatan suma ALLAH yabasu wani.

BAYAN WASU SHEKARU.
gidansu Nawaf nayima tsinke, nayi sa'a kuwa suna 9ja, Nawaf anzama manya hakama yasmeen anzama manyan mata, ga 'yan yaransu abin sha'awa, bayan Muh'd sun haifi ummul'khairi mai sunan momcy, suna kiranta ummu, sai sa'eed papa kenan shikuma abbu, idan kaga yaran kamar ka sacesu, ďas2, shi dama muh'd sun barma su momcy komai nashi acan yake.
Anyi bikin Abdallah da halimatu 'kanwar mas'ud, naga harda ma 'katon ciki, na ce, "su Abdallah an huta kenan😜lol.
Suma su Anwar da yaseer sun kammala karatu sundawo, sun zama cikakkun likitoci magada mas'ud kenan, abokan juna daba'a jin kansu, sumadai nakula aure sukeso😜
6angaren su umma ma komai dai2 kaji dattijan arzi'ki, hakama su mas'ud suma yanzu sunada yara huďu abinsu gwanin sha'awa.
muh'd yafito daga ďakin Nawaf yana kuka, Nawaf dake falo yanama ummu homework ya ce, "yaya! lafiya dai??.
Muh'd yafaďa jikin Nawaf yana kuka, yasmeen tafito hannunta ri'ke da bulala tana ďaukeda abbu aďayan hannun, tanufo muh'd, Nawaf ya'kara rungumeshi yana faďin sorry ummy miya faru??.
Ta nuna masa goshin abbu dayayi fushi ta ce, "dan ALLAH kalla kagani habibina jibi yanda ya fasama yarona kai dan mugunta, yasan bazai iya ďaukarsaba miyasa ya ďaukesa??.
Nawaf yajawo abbu dake kuka, yaďorashi saman cinyarsa yana faďin yaya ya akayi haka tafaru,, muh'd ya ce, "dady ALLAH ban ganiba, faďuwa yayi dakansa ALLAH bani bane, yasmeen takai masa duka, da sauri Nawaf ya kare yana faďin kiyi ha'kuri tunda ya ce, "bai ganiba kinsan dai bazai cuceshi da ganganba, ai abbunema yacika nauyi.
ALLAH bakasan muguntar muh'd bane, nibammasan miya kawoshi wajen nanba, bama momcy ta ce, "anguwa zasujeba shine yataho jan magana nan??.
To yi ha'kuri dai bazai sakeba, yasmeen tashige ďaki tana mita.
Shikuma yashiga lallashin abbu haryay barci, shima muh'd yay shiru, ummu ta ce, "dady nima inajin barci,, A'a ummu na kigama homework ďin sannan kinga gobe monday kunada school yaya zoka cigaba da koya mata na kwantar da abbuna kaji.
Muh'd ya ce, "to, kusada ita yakoma ya zauna, Nawaf saida yaga muh'd yana koya mata dai2 sannan ya sumbaci kumatunsu yanufi ďaki dan kwantarda abbu, yasan muh'd akwai 'ko'kari amma sai rashinji, babu abinda yabaro daga halayen Abdallah, shiyyasama yanzu yakoma kamanninsa gaba ďaya.
Nawaf ya kwantar da abbu tsakkiyar gado sannan yanufi yasmeen dake tsaye tana gyara masa kaya a wardrobe, ya rungumeta tabaya yana faďin sorry ummy bazamu sakeba,, yasmeen ta ce, "kuma sake mana jikinku yayi tsami ne aii, dan ALLAH jibi yanda aka samini yaro baccin wahala.
To mudai ayi ha'kuri mukace, tajuyo suna fuskantar juna, kowa yanama ďan uwansa murmushi, Nawaf ya ce, "i luv u my xarah,, itama murmushin tayi ta ce, "luv u too habibina, suka rungume juna tsam suna gayama juna kalamai masu daďi da garđi, kowa yana farincikin kasancewa da ďan uwansa.
Tonima dai ina farincikin kasan cewa daku har abada.

TAMMAT BI HAMDULLAH.

Takucedai BILKISA IBRAHIM.
(Mrs Abdus'salam)

Nagode masoyana aduk inda kuke, nagode da 'ko'karin bibiyata dakukeyi,, ALLAH yabarmu tare, ina 'kaunarku kamar yanda kuke 'kaunata da zumuďin karanta abinda yafito daga kwakwalwata.❤❤❤❤❤❤kucigaba da kasancewa dani a sabbabin books ďina masu zuwa gareku insha ALLAHU nan bada daďewaba..

Kusanar dani kuskure ko gyara daya dace nayi a novels ďina, idan kunyi haka shine zan tabbatar da kuna 'kaunata, domin nima 'yar adamce azija.


Kunnuna min 'kauna mai yawa kuma nagode sosai,, baxan iya lissafokuba saboda yawan dakuke dashi,, amma ina godiya gareku da group admins naku, nagode nagode nagode,, luv u oll❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤💔💔😘😘.

Muhaďu asabon littafina mai zuwa KUKAN KURCIYA........, shima zaizo muku da sabon salo mai 'kayatarwa dakuma faďakarwa,, zaizo gareku nan bada daďewaba insha ALLAHU.


CIGIYA
dan ALLAH ina neman book's ďina guda uku.
RASHIN SANI
auren 'KADDARA ko BI YAYA
'KANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA.
dan ALLAH duk wanda yay dacen katari dasu yatura min ta wannan number 09093044460.
ALLAH yasa adace😂👌🏻

TAKU HAR KULLUM BILKISA IBRAHIM
💓bilyn Abdul💓


©2017

💓luv u, luv u, luv u, luv u, luv u oll💋💋💋🖐🏻😂😂💓
Saikunjini😂😂😂👌🏻

©2016


💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘💞



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment