Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusada wayoyinsa, yana wajen motsa jiki dayake fita akowace safiyar duniya, inhar yana 9ja.
Sai wajen 'karfe 8:00am yashigo gidan jikinsa sanye da farin JC, gajeren wando da 'karamar riga mara hannu, 'kabarsa sanye da takalmin 'yan kwallo, dad'an gudunsa yashigo gidan, yasaka robar ruwan dake hannunsa cikin bola, key yasa yabud'e d'akinsa ya shige.
Saida yasha ruwa sosai sannan yazauna yana zufa ya fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ya kwantar da kansa saman kujera ya lumshe idanu, yakai minti5 ahaka daga bisani ya cire takalman 'kafarsa ya ajiye.
Bedroom d'insa yashiga, yacire kayan ya jefa cikin wani dogon kwando, ya bud'e wata 'yar durowa dake kusada bayi (bathroom) tawul ne aciki kala2, yad'akko kalar yellow ya d'aura daga 'kugu zuwa guywa.
Wanka yashiga, ammafa ya dad'e, dan nikam harna fara gajiya ma da jira, ya kai tsawon minti50 sannan yafito, d'aure da tawul d'insa, hannunsa ri'ke da 'karami fari yana goge sumarsa.
Zama yayi yashiga tsara ado, na ce, "kai gay d'inana d'an kwalisa ne gsky.
Kwalliyarma yakai tsawon lokaci yana tsarata saikace mace lol, daga 'karshe yafito sanye cikin 'kananun kaya ya d'ora tafkekiyar rigar sanyi jaa mai 'kyalli saboda yanayin sanyin garin, sai zabga 'kamshi yakeyi.
Zama yayi yay break, sanan ya jawo phones d'insa, ya kira wad'anda suka kirashi baya nan, haryazo kan number d'in yaseer, kira yashiga yi amma ba'a d'agaba, yasake kira, harta kusa katsewa aka d'aga.
Mai makon yaji muryar yaseer sai yajita yasmeen, cikin muryarta mai za'ki ta ce, "mai wayar baya nan!.
Nawaf ya ce, "ina yaje??.
Ita bata gane Nawaf bane, ta ce, "yaje school, amma idan yadawo za'a sanar masa.
Daya kula bata ganeshiba saiyayi niyyar zolayarta, ya ce, "toke wacece?.
Saida taja numfashi sanan ta ce, "yayarsace.
Saida yad'an ta6e baki sanan ya ce, "hummm kodai 'kanwarsa, dan dagajin muryarki "k, yarinya 'karamace.
Cikin 'kufula yasmeen ta ce, "kai malam sai anjima, kabi duk ishii mutane da surutu, d'if ta kashe wayar.
Dariya sosai Nawaf yayi, ya ce, "kai yarinyarnan 'yar bala'ice wlhy, dawata muryarta kamar ta gyare.
Yashiga kwaywayon muryarta yana dariya, tamkar mai kallon film ko wa'ka.

--------------''''''---------------------
Da yamma abba ya kira papa awaya yay masa bayanin komai, game da abinda yafaru da safe, maganar ta bama papa mamaki saikace a wasan kwaikwayo, kasaki mace kadawo kana hauka wai kana sonta.
Papa ya ce, "karya damu zuwa gobe zaizo suyi magana, yasmeen ta tare kawai agindasa, ta 'karasa karatun a d'akinta.
Papa yaji dad'in hakan, yakuma yi farin ciki, koda yagayama umma itama murna taitayi dan wanan shine kawai maganin son zuciya irin na alhaji buba da d'ansu.
Yasmeen kuwa batayi murna da hakanba, dan itafa har yanzu zuciyarta bata wani saisaita mata zama da Nawaf ba, tana masa kallon mugune mara mutunci, darashin girmama d'an adam.
To yasmeen koma dai miye?, lokacine zai nuna wannan.

Da yamma ta saci jiki tashige gidansu Ameena, umma tana d'aki bata saniba, tazata yasmeen d'in tana d'akine, tunda tasaba yini a d'aki, bare yau ana sanyi a garin.
Yasmeen kam tana can sunata hirarsu itada ameena da bello yayan Ameena.
Saida taga ana kiran wayarta sannan ta mi'ke zaram, number yaseer tagani, tad'aga da sauri tana fad'in bro's yaya dai??.
Ya ce, "kina ina?, anata nemanki.
Yasmeen ta gwalalo idanu waje tana fad'in naga ta kaina ganinan zuwa.
Ameena ta ce, "kije kisha fad'an umma, dan satar fita kikayi, kuma akwai zunubi
Hararta yasmeen tayi tafice da sauri batareda tabama Ameena amasaba.
A 'kofar gida tayi turus, dan ganin Nawaf jingine a jikin mota, kansa a 'kasa yana danna waya, yana sanye cikin shadda milk, d'inkin iya guywarsa, yayi 'kyau sosai sai 'kamshin tutare yakeyi, yaseer yana gefensa tsaye.
Jiki a sanyaye ta 'karasa wajensu.
Yaseer ya ce, "sisto wai dama kina nan gidan tund'azu??.
Kai kawai ta d'aga batare da tayi magana ba, ta ce, "miyasa kuka tsaya nan??.
Yaya ne ya ce, "mu tsaya muga inda zaki fito.
Yasmeen ta kai dubanta ga Nawaf wanda tunda tazo ko d'ago kai baiyi ya kalletaba, yanata danna wayarsa kamarma baisan dawata yasmeen a wajenba.
Saida tad'an turo baki sanan ta ce, "to kumuje mana, Nawaf ko motsi baiyiba dan haka yasmeen tayi gaba abinta.
A falo ta iske umma, umma ta hauta da fad'a, itadai yasmeen fad'i take umma kiyi ja'kuri ALLAH gidan ne naji shiru shiyyasa na fita.
Tsaki umma taja ta ce, "aii yayi miki 'kyau tun d'azu mijinki yazo yake jiranki, kinacan inda ba a aikekiba.
Shiru yasmeen tayi dan tasan batada gsky.
D'an abinda umma tahad'a yasmeen ta d'auka tanufi falon abba, azaune ta tadda Nawaf yana kallo, ita a zatontama har yanzu bai shigoba.
Ta dire tiren a gabansa sanan ta koma nesa dashi ta zauna.
Suduka kowa ya share kowa, dan Nawaf har yanzu ko kallonta baiyiba, itama saita shareshi taci gaba da harkarta.
Sunkai tsawon minti30 ahaka, yasmeen ta daure ta ce, "nikan gsky inada abinyi dan haka zan 'kara gaba.
Harara ya watsa mata batareda yayi maganaba, ya d'auki remote ya 'kara 'karan tv dan bayaso umma taji hayaniyarsu, tsam ya mi'ke yanufo inda take zaune.
Atu naninta zama zaiyi, dan haka tashiga matsawa tana 'kan'kame jiki.
Tsaki Nawaf yayi ya'karasa gabanta, gashinta ya dam'ko ya matse da 'karfi, gaba d'aya jijiyoyin kan yasmeen suka fito, tasaki wani walallen kuka tana 'ko'karin ri'ke hannunsa, gashi ya toshe mata baki da hankacif.
Ya zare mata fararen ida nunsa masu girma, ya ce, "wayace kifita??
Yasmeen babu damar yin rashin kunya, saidai hawaye dake fita daga idanunta, ya saki gashin yana fad'in gobe idan kin tashi ki kuma fita bada izininaba, kiga abinda zan miki, baki ta murgud'a masa ta ce, "mugu ALLAH saiya saka mini.
Hannu yakai zai kama hannunta ta kauce da sauri, yaja gefe danya kamata saita fad'a jikinsa, mai makon ya ri'keta saiya kama d'an yatsanta, tako daddage ta galla masa cizo a d'ayan hannunsa.
Da sauri ya saki hannunta yana yarfe nasa hannun, abinka da fari gurin har yayi jajur, ga shatin ha'koranta awajen rad'a2.
Nawaf ya rintse ido yana murza wajen, dariya sosai yasmeen takeyi, ta ce, "kaji idan da dad'i kaima.
Ya bud'e ido yana cije le6ensa na 'kasa, har yanzu wajen zafi yake yi masa, ya ce, "ni kika ciza ko??.
Baki ta murgud'a😏 masa, gobema idan ka 'kara gwada mini mugunta saina yimaka wanda yafi wanan, mugu kawai.
Wani murmuahi Nawaf yasaki mai kamada ya'ke😜ya ce, "banza kuriya🐅, wlhy idan na kamaki zaki gane kuranki.
😜gwalo yasmeen tayi masa ta ce, "saidai mu gane kurenmu wlhy.
Kwafa yayi ya ce, "yarodai baisan wutaba saiya taka.
Nunata yayi👉🏻👩🏻yana fad'in kuma wlhy kifad'ama wannan jahilin daya sakeki aka 'ka'kaba mini, daga yau nasake jin yazo gidanna saina sa an 6atar dashi, dagashi har jahilin ubansa, idan kunne yaji jiki ya tsira.
Kemad'in bance karki 'ki fitaba, saidai idan kika cigaba da karya dokata zaki cigaba da shan ba'kar wahala ne, danni ba sa'anki bane.
Yana kaiwa nan ya fice dama har anfara kiraye2 sallar magriba.
Dariya tasaka harda tafa hannaye, ta ce, aii dai kasha cizo azzalumi kawai, aii wlhy na daina 'kyaleka kana sakar min kwanjinka a banza, idan kafi karfina aibakafi karfin cizoba, zakayita shan cizone harsai hannunka yakoma da zanen ha'korana ko ina.

_______________________
D'aki tanufa tayi sallar magriba, tana nan zaune tana karatun alkur'ani har akayi sallar isha'i.
Bata fitoba dan tasan umma tana ciki da ita, saida tabari yaseer yadawo sanan tafito, ganin baya falo yasa tanufi d'akinsa.
Saman gado ta tarar dashi ya bud'e waya 'katuwa akwalinta yanata kallo yana murna, NAWAF ne ya sayamasa.
Yasmeen ta murtike fuska, cikin masifa ta ce, "yaseer yaushe kazama munafiki, kai har ka fifita bare akan ni 'yar uwarka??.
Ubanwaye yasaka gayama wancan mugun faisal yazo gidanan da safe??.
Yaseer ya had'e fuska, kai kaji sisto d'innan koda ban fad'aba ma aii abba ya fad'ama abbansa, kuma nasan zai gaya masa, zaki wanizo kina zagina, yafad'a yana turo baki gaba.
Tsawa yasmeen ta daka masa dallah malam rufe min baki, munafiki kawai, wanda bai iya ri'ke sirrin gudansuba, saboda an kawo maka waya kazauna kasaki baki kana zuba gulma da tsigudidi.
Wlhy daga yau nakuma jin maka manciyar wanan maganar saina daka ka agidanna, idan kaji 'karya ka 'kara, sakarai kawai, tayi waje.
Yaseer yabita da kallo yana murgud'a baki, an fad'a d'in, kumani ba magulmaci bane.
Kinason mutum kina wani kauce2, ai tuni na harbo jirginki😜ooooh, yafad'a yana dariya.

Nawaf kam cikin haushi yaje gida, koda yayi sallar magriba da isha'i bai nemi mas'ud ba, dan yanada aikin yamma shiyyasa basuje tareba.
D'aki yadawo yay kwanciyarsa, kad'a2 saiya kalli inda yasmeen ta cijeshi, wajen yayi jajur.
Yasaki murmushin mugunta, wlhy yarinya sakinyi dana sanin cizonan dakikamin, mara kunyar banza kawai, yay kwafa yana gyara kwanciya.
Ahaka mas'ud yazo ya sameshi, ya zauna yana fad'in angon yasmeen kabarota lfy??.
Banza Nawaf yay masa.
Mas'ud yay murmuahi oh baza'a amsa miniba angon yasmeen??.
Cikin masifa Nawaf ya ce, "kasan ALLAH mas'ud ka daina had'ani da wanan yarinyar inkuwa ba hakaba zamu sami matsalane.
To miye dan munsami maysalar alhaji???, wata ran basai mu shiryaba.
Nawaf yatashi zaune yana fad'in wlhy mas'ud saina koyama yarinyar nan hankali kwanannan.
Hummm mitayi maka dazaka koya mata hankali.
Hannunsa ya nuna masa ya ce, "kalla ka gani waini yarinyarnan ta ciza.
Mas'ud yatuntsire da dariya, kai saikace wata kura??.
Ai tafi kura Nawaf yafad'a yana gyara zama, nan yabama mas'ud labarin abinda ya had'asu.
Mas'ud ya ce, "Ah wanan laifinkane alhaji, aiba haka ake hukunta mutumba idan yayi laifi.
Tsaki Nawaf yaja ya ce, "wanan kuma matsalar kace.........................✍🏻







©2016




💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆







NA BILKISA IBRAHIM💞




page👉🏻23 & 24

......WASHE GARI...su papa sukazo shida 'kaninsa dayazo daga katsina, dakuma Abban mas'ud, bayan angama gaishe2 suka shiga tattauna abinda yakawosu.
An 'kar'kare magana za'ayi shagalin biki nanda sati hud'u masu zuwa, (1monch )sananan su Nawaf sun gama wasan kofin africa kenan, kafin yakoma Spain sai asha shagalin biki kawai.
💃💃💃💃kai zamu shabiki, kowaya yashirya masu karatu😜.
Bayan an 'kar'kare magana yasmeen tashigo ta gaidasu, 'kanin papa ya yaba kam da tarbiyyar yasmeen , yanada tabbacin Nawaf yayi dace!!!!!!!.

-------------------------------------
Yau dai gaba d'aya family d'in suna falon papa, Nawaf yana kwance a kujera mai zaman mutum biyu, Anwar yana saitin kansa ri'ke da littafin larabci, Nawaf yana koya masa, Abdallah kam hankalinsa yana kan tv dan shi dama d'an a hutane.
Papa da momcy suna gefe zaune papa yana nazarin wasu manya2 littatafai shida momcy, da alama bincike yakeyi akan wata shari'ar, momcy tana tayashi, tunda itama mai ilimince👍🏻.
Nawaf ya ce, "Abdallah tashi kakawo mini ☕lifton.
Abdallah yad'an turo baki gaba, yaya dan ALLAH bari ad'an wuce nan.
Harararsa Nawaf yayi, ya ce, "to uncle Abdallah bari najiraka, da sauri Abdallah yatashi dan yasan gatse yay masa, yana kuskurewa saiyasha mari abanza, dan Nawaf akwai saurin hawa kamar filawa😜lol.
Momcy ta ce, "ya ALLAH kashirya mini Abdallah.
Sukace amin.
Papa ya ce, "aii Abdallah shike bama kowa ciwon kai agidannan.
Abdallah yashigo d'auke da butar shayi mai 'kalli da 'karamin kofi da cokali, agaban Nawaf ya dire batare da yayai maganaba.
Girgiza kai kawai Nawaf yayi yad'auka yazuba yana sha, ya ce, "yaro nafika zafin kai.
Papa ya ce, "yau modebbo yaushane zaka koma abuja??.
Papa gobe idan ALLAH ya kaimu da yamma.
Okey ALLAH yakaimu, aii momcy tamaka bayani akan tarewar matarka ko??, Nawaf yad'an rage fara'a, eh tagayamin, amma papa dan ALLAH abari saina koma Spain idan mun gama (KAKAR WASANNI), nadawo tunda muna samun hutu awanan lokacin saita tare!!.
Kagafa ko inda za'a ajiyeta babu, amma zuwa sanan an kammala ginina!!.
Agidan Nawaf yake gini tacan baya, saboda papa yanada burin zama da iyalin guru ďaya yasa yasayi filin dake haďe da nasa yazagayeshi kowa ya girma cikin 'ya'yan saiya gina 6angarensa.
Toshi Nawaf yaďan fara ginin ya watsar, gashi koma aure yaro yanzu.
Girgiza kai papa yayi, ban yardaba Modebbo, kafin katafi za'ta tare, 6angarenka za'a gyara muku yanzu saiku fara zama anan, anjima ka cire dukkan abinda kakeso daga 6angarenka kadawo dasu ďakin kusada nawa, dan za'a gyara 6angarenka asake komai naciki insha ALLAH.
idan kazo wanan hutun saika tafi da matarka kawai, munriga mun gama yanke magana, yanzu hakama 'yan katsina sunsan komai, kuma yau dasafe nakira 'yan saudia na sanar musu, nextweek ma (MAHER da ZAID) zasuzo, 'kannanen momcy ne.
Shiru Nawaf yayi dan zucuyarsa sai tafarfasa take, yanzu sai kawai abokansa suzo suga wanan 'yar yarinyar ya aura, gata mara kunya, kuma 6angarensa bedroom ďayane, kenan papa yana nufin a bedroom ďaya zasu zauna kenan???......
Momcy ta katse masa tunani da fad'in yakamata ka sanar da abokanka, tunda yazu zamanine mai sau'ki komai zaka iya yi ta hanyar SOCIAL MEDIA.
Nawaf ya ce, "to momcy zanyi 'ko'kari nida mas'ud, amma sainake ganin abun kamar babu shiri??.
Miye rashin shiri anan modebbo, acikin wata d'aya mu zamu shirya komai, shiyyasa na ce, "su maher suzo!.
Su Alhaji buba ba muta nen kirki bane, zasu iya aikata duk abinda tu naninsu yabasu.
Momcy ta ce, "gsky ne Alhaji.
Su Anwar suka shiga tsallen murna, za'ayi biki agidansu, shi dama Anwar bai ta6a ganin anyi taro agindansuba tunda shine auta, gara Abdallah yaga taron sunan Anwar d'in.

_________________________
Ita madai yasmeen wanan labarin ya iso mata, saidai suna hanya d'aya da ango itama batayi murnaba, saima kuka data zauna tanayi, umma ta ce, "hawayen gareki dayawa yarinya, ke komai akayi sai kuka saikace hanyar ruwa, haka zakije gidan mijin dayayi miki abu ki hau kuka??, AĹLAH yabaki sa'a.
Abba shidai lallashinta yakeyi, yayinda yaseer keta kwasar dariya danshi farinciki fal cikinsa.
Da yamma Nawaf da mas'ud sukazo, fuskar ango da amarya babu walwala, bayan ta gaishesu mas'ud kawai ya amsa mata, ya ce, "Amarya ina 'kyauta ta??.
Yasmeen tayi d'an murmushi, ta ce, "bari nakira maka ita, tana son tashi tana tsoron Nawaf ita kuma bazata tambayeshiba wlhy, kamar daga sama sai sukaji sallamar Ameena, yasmeen ta ce, " 'yar halak.
Ameena ta zauna tana faďin to miya faru??.
Tunda tashigo mas'ud ya yaba, kuma insha ALLAH yasamu matar aure kenan, Ameena ta gaishesu, amamakin yasmeen saitaga Nawaf ya amsa harda murmushi, ya ce, "Ameena zaki auri tuzurin abokina kuwa???.
Harararsa mas'ud yayi ya ce, "kai malam waye tuzurun???.
Cikin dariya Nawaf ya ce, "kai mana, aii itama tasan kai tuzurune 27years babu aure fa.
Mas'ud ya ce, "ashe kaima tuzurinne??, yasmeen kinji tuzuru kika aura!!.
Haka sukayita tsokanar juna, kuma anan aka kulla 'kya'ky'kyawar ala'ka tsakanin amina da mas'ud.
Ficewa sukayi suka bar Nawaf da yasmeen a falon, suma suka tafi domin yin tasu hirar.
Nawaf ya mirtike fuska, ya ce, "k kice su papa su tsaida maganar bikinnan dasuke shirin yi!!.
Yasmeen ta yaysine fuska, "kai miya hanaka ka fad'a musu naga kaine Namiji.
Harara Nawaf ya sakar mata, sai akace miki ni mara kunya ne irinki!!!.
Baki yasmeen ta ta6e tace ashe....
Yay saurin cewa ashe mi???.
😏ta murguďa baki tana faďin sainaji zafin ma'kara.
twoow tsaki Nawaf yayi yana fad'in yarinya ki ajiye rashin kunyarki a gefe dan wlhy yanzu wahala zakisha bata wasaba.
Yau ba shirmenki ya kawoniba dan inada abinyi, gobe zan koma abuja, duk abinda kike bu'kata ki sanarma mas'ud.
Hummm kaidai kasha cizo malam, yasmeen tafaďa a zuciyarta.
Saida ya'kara mirtike fuska sanan ya ce, "ki koma makarantarki idan kina ra'ayi.
Cikin murna yasmeen ta ce, "dgsk??, harararta yayi ya ce, "k bana son shirme kinji.
Baki ta murguďa😏 masa, ya ce, "dawa kike???, ta ri'ke 'kugu👯da wanda ya tsargu mana.
Nawaf yay murmushi danshi dariya ma tabashi, yakula ta rainashi da yawa, amma zai koya mata hankali kwanan nan, ya ce, "habawa yarinya wataran ko ance kiyi mini rashin kunya bazakiyi ba wlhy.
Kud'i ya ajiye mata 'yan dubu2 ďauri biyu, ya mi'ke, karki ďauka dan bananan ko dannance ki koma makaranta ki ďauka kinsamu hanyar yawo, nasaka masu kulamin da shigarki da fitarki, idan naji wani abu sa6anin dokar dana kafa, tofa kiyi kuka da kanki, yana gama faďa ya fice.
Harara yasmeen tarakashi da ita tana faďin sai an karya dokar taka, tunda ba dokar ALLAH ba ce, "mutun ya rin'ka abu saikace wani ubana.
Tashiga kwaykwayon maganarsa yanda yakeyi aģadarence.

__________ABUJA________
Bayan kammala (colfine second round) da akayi, Najeria ta tashi da maki 7.
To ayau kuma zasu buga da Egypt, (colfine cotter pineal) wasan daf da 'karshe ke nan.
Wasa yayima 9ja daďi, dan antashi 1-0,
9ja 1 & Egypt 0
Karkuga murna wajen 'yan 9ja.

2days later.
(Seme pineal) wasan kusada 'karshe, 9ja da South Afirica, wanan kuma ankai ruwa rana, dan sai ana saura minti2 atashi, cosee!, wani ďan wasan 9ja yay wani fasin da Nawaf yasamu damar antayawa 9ja kwallon cikin ragar south Africa, guri yaruďe da ihu Najeria sai murna mukeyi.
Dukkanin wasanan yasmeen ta kalla, dukda bawani burgeta yakeyiba, amma takanji tana sha'awar kalla, da antashi zakaga yaseer yakirashi yana masa murna, takan ta6e baki ta ce, "ma yaseer uban 'yan shishshigi kawai, ďan san asani.
Oho dai yaseer yafaďa, kema san asani ďin yasa kike kallon kwallon yanzu tunda da ba'ka kallo da.
Duka ta kaimasa ya kauce, cikin shagwa6a ta ce, "umma kinga yaseer ko yana tsokanata.
Umma ta ce, "kunfi kusa, kubar sakani ashirmenku kunji.
Yaseer yatashi yafice yana mata gwallo😜.
Kwafa tayi ta ce, "zaka dawo ka sameni yaro.

Yaune za'a buga wasan 'karshe, yaukam stadium d'in abuja babu masaya tsinke, dan yau harda shugaban 'kasar NAJERIA shima yazo.
Bayan gama addu'a da abinda yadace,Najeria da Algeria suka fara buga wasa, kowa iya 'ko'karinsa yake a wasanan, dan haka har aka tashi hutun rabin lokaci babu wanda ya zira kwallo.
Bayan andawoma gwagwar maya aka cigaba dayi, amma ina komai bai canjaba, tun ana saran wani zai ci har aka fitar da rai, lokaci yacika aka'ara, shima ya shuďe babu wanda yaci, dole saidai ayi (peneritty).

*Algeria ⚽tafara zirama 9ja
*Najeria ⚽ sai 9ja itama ta zira
*Algeria ⚽
*Najeria ⚽
*Algeria ⚽
*Najeria ⚽
*Algeria ❌9ja tazubar
*Najeria ⚽
*Algeria ⚽
*Najeria ⚽Nawaf ya zira mana ta 'karshe.
Dukkan filin da sassan gidajen kwallo dake Najeria suka d'au ihu na murn, bakin kowa abuďe, shugaban 'kasa yayi murna sosai.

Duk da kwallo bata burge yasmeen to yau tayi murna sosai, sai murmushi takeyi dan daďi.
Na ce, "humm yasmeen kodai???????.
Bayan shugaban 'kasa ya karramasu kowa yanufi inda yafi wayo, (club club nasu kenan)
Shidai Nawaf kano yataho..................✍🏻




©2016



💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞



Page👉🏻25 & 26

....To shima dai mas'ud a6angarensa komai ya dai2ta, har ankawo kuďi dan anaso ayi bikin tareda na Nawaf, yasmeen tayi farinciki sosai da faruwar haka, bare ameena amarya, ai tafi kowa farinci, dan tana son mas'ud sosai.
Yau kuma aka kawo lefensu su duka akwatuna bakwai2, komai iri ďaya, wanan aikin papa ne, dan shida momcy suka haďo lefen.
Wannan shi ake Kiran lefen 'yan gata, mutanen anguwa da dangi duk sun yaba.
Filin jirgin na kano cike yake da matasa domin tarbar NAWAF!!.
🛬jirgi yafara shawagi neman muhallin sauka, bayan tsayawarsa fasinjoji suka fara fitowa, Nawaf shine na 6, ahankali yake sakkowa kamar bayaso, jikinsa sanye da 'kananun kaya, ya ďora 'katuwar rigar sanyi fara, ya saki hular a baya, sai tashin 'kamshi yakeyi, yagoyo jar jakka abayansa wadda aka rubuta (Adidas)na ce, "kai gay ďinnan handsome ne gsky.
Da gudu anwar yaje ya rungumesa, shima cikin farinciki ya rungume shi, yana faďin i missing u autan momcy.
Missing u too yayana.
Gaba ďaya 'yan uwa da abokan arzi'ki suka taso gareshi, 'yan jarida kuwa sai 'kutsa kai sukeyi domin samo bayanai.
Da'kyar suka barshi yashiga mota mas'ud yaja suka nufi gida, anata ďaga masa hannu shima yana ďagawa.
Abdallah ya ce, "yaya dabamu samu mun gudoba dasai yamma zamu baro filin jirginnan.
Nawaf ya ce, "gsky ne brother shiyyasa naso na sauka da daddare.
Mas'ud yay dariya ai koda daddaren ne sai mutane sun jiraka tunda anuna a labarai zaka sauka kano yau, aii ko randa kazo daga Spain mutane basu taru hakaba??.
Abdallah ya ce, "to ba sunga ya cimusu kwalloba yau, suka tuntsure da dariya su duka.
Anwar ya ce, "nifa wani tsareni yayi saina bashi number yaya, na ce, "masa banida waya kuma ban ri'ke number ba.
Mas'ud ya ce, "hummm autan momcy sarkin wayo.
A babban tsakar gidan sukai Parking, Nawaf yasha mamaki dan ganin dangi cike da gida, 'yan katsina da saudia, duk sunzo, dangi sai rungumeshi ake ana murna, musamman 'yan saudia dansu dama al'adarsuce.
Family falo suka nifa inda sauran dangi suke harda kakarsu Nawaf ta wajen uwa tanan darai hajja humaira kenan.
Hajja humaira ta ringume Nawaf tana farin cikin ganinsa, ta ce Masha ALLAH mai gida ka 'kara 'kyau da girma, kodai an canja mini kaine??, Nawaf yay dariya A'a hajjana ba a canja miki niba ninedai maigidanki na 'karfen!!!.
Gaba ďaya akasaka dariya, ta ce, "kamanta damu ko Nawaf!!?, da sauri ya 'kara rungume hajja ya ce, "ni na isa na manta daku, uwargida sarautar mata, hajja nayi missing ďinki sosai.
Hajja ta ce, "ďan nema kai dai bazaki hausarba bare larabcin?, turawa sun 6ata mana ka!!.
Nawaf yay murmushi yabi dukkan iyaye da kakannin yana gaishesu, har 'yan katsina.
Ya ce, "ni banga sauran sisters ďina ba??, kobasu zoba??.
Tab wazai 'kizuwa bikin ka (Abi)yaya kenan, kowa yazo, sauran suna gidan amaryarka, muma yanzu za'a kaimu, wai a al'adar hausawa yaune ('kunshi)to zamuje mu ganine!!.
Nawaf yay

Please Login or Register in order to submit comment