Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce, "bro's barshi zaizo ya samemune.
Momcy tayi dariya A'a karku huce akan d'ana, tunda bashi ya ce, "ayi sadaka dakuba.
Papa ya ce, "barshi ai shima hardashi.
Abdallah ya zaro idanu, papa nikuma asuwa wai kare da gudun layya, 'yan 27year's basuyiba, bare ni d'an 20years papa kwanan fa nashiga jami'a.
Nawaff ya daka masa tsawa, kai dallah kaima mutane shiru, kabi ka ishi mutane da shegen surutu.
Abdallah ya zunb'uro baki gaba yana gunguni, amma Nawaff bayajinsa, Dan yasan idan yajisa, hummm.
Saida sukaci abinci sanan suka tafi b'an garen Nawaff.
Mas'ud ya ce, "kai malam kahuta wlhy karigaya ka kama matarka ahannu, babu rabon ayi sadaka dakai.
Nawaff ya ce, "agidan ubanwa nasamu matar, ALLAH mas'ud kaifa d'an iskane.
Mas'ud ya tun tsure da dariya, kazauna kallon ruwa wlhy kwad'o yamaka k'afa, kanaji kana gani za'ayi sadaka dakai.
Nawaff yaja tsaki tareda kwanciya saman kujera, ya lumshe idanu.
Duk surutun da mas'ud yakeyi yana jinsa amma yay kunnen uwar shegu dashi................✍🏻





💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's 💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻11

....koda daddare yasmeen k'in zuwa kai amarya tayi, ta langyare akan batada lafiya, ta kashe wayarta kuma dan kar akirata.
Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, Nawaf yagama hutunsa ya tattara ya tafi kasar Spain domin cigaba da biga kwallo.
Har ya taho bai k'ara had'uwa da yaesmeen ba, hasalima yamanta da ita, yacigaba da harkokinsa kamar yanda yasaba.
Itakam yasmeen bata manta dashiba, ko makaranta zata takan fita cikin d'ar2, kullum addu'ar ta kada ALLAH ya had'ata da Nawaff ko da amafarki.
Dahaka dai aka shere wata uku bataji d'uriyarsa ba, ahan kali tafara sakin jikinta.

Yau agajiye tadawo daga school ta shigo falon tana jan k'afa kamar kazarda kwai ya fashewa aciki, yaseer ne kawai afalon yana cin abinci, idanunsa nakan TV ko k'yaftawa bayayi.
Yasmeen tadaki kujerar dayake zaune dan taga alama baisan tashigoba, yajuyo da sauri yana kallonta.
Yasmeen ta harareshi kaidai ALLAH ya shiryaka, shikenan indai kana kallon kwallo sai a rasa hankalinka gaba d'aya.
Yaseer yay dariya, sorry my aunty ALLAH bansan kin shigoba, kinsan yau mutumina yake buga kwallo bana son komai ya katseni wlhy.
Yasmeen ta tab'e baki, waye kuma mutuminka??, ata k'aice ya ce, "modeebbo mana, gaban yasmeen yafad'i ras danjin sunan wanda yazame mata baraxana arayuwarta ta yanzu, ta ce, "waye kuma modeebbo??.
Idonsa na kan tv ya ce, "kalli tv zan nuna miki shi, shine number 10.
Yasmeen taja flet d'in abincin dayakeci gabanta, ta hauci, saidai itama hankalinta yana kan tv d'in, wani uban ihu yaseer yatashi ya kwala tareda fad'in 🗣goooooooooooooo⚽!!!!!!!!!.
Yasmeen tai saurin rufe kunnenta danjin zai fashe saboda k'arar da yaseer ya kwala🙉, cikin kara ta ce, "dalla malam karka fasamini dodon kunne.
Ya zauna yana dariya tareda 👍🏻,yana fad'in sai modeebbo, kana wuta my gay.
Sai asannan idanun yasmeen suka kai kan Nawaff tamik'e da sauri tana fad'in yaseer kana nufin wannan gay d'in, ta nuna Nawaf da aka nuno ya durkusa akasa yad'aga hannunsa samma yawani wage baki da alama shima ihun yakeyi dan murna, wasu 'yan kwallo sukazo suka rungumeshi suna ihu.
Yaseer ya ce, "shine sistona, tauraro kenan mai haskawa a duniyar kwallo, yanzu su duniya take yayi dason gani, hala kin sanshine kika mik'e zumbur.
Yasmeen taja ajiyar zuciya ta ce, "natab'a ganinsa dai, da sauri yaseer ya ce, "dan ALLAH dgsk kikeyi??.
Yasmeen ta tab'e baki, ta ce, "kaji yaro natab'a yimaka k'aryane??, awajen bikin Asma'u natab'a ganinsa, dama d'an kwallone??.
Yaseer yagyara zama Taf sisto idan kinji ana fad'in mai laya kiyayi mai zamani to modeebbo kenan!!, ai duk ranar dana had'u da bawan ALLAH nan to sainayi sadaka.
Yasmeen ta tunysure da dariya, amma kaidai d'an wahalane wlhy, tafad'a tana mik'ewa.
Yaseer ya ce, "kedai tafi dan bazaki tab'a ganewaba.

Nawaff zaune ad'akinsa akasar Spain, yana zaune bisa kujera mai zaman mutum d'aya, hannunsa rik'e da remote, yana neman tasha, wayarsa dake gefensa tayi wringing yakai hannu yad'auka.
Saida yad'an murmusa sannan ya ce, "Hello my gay ykk?
Daga can mas'ud ya ce, "ina lafiya my bro's, naga wasa d'azu yayi k'yau, ammafa kayi k'ok'ari, acinkin minti biyu na farko fa ka jefa mana kwallo a raga, ina alfahari dakai my bro's.
Nawaf yay sassanyan murmushi tamkar yana gaban mas'ud, ya ce, "nagode d'an uwana, kana k'ara mini karfin gwuywa a rayuwa.
Karka damu bro's, dama Anwar ne ya ce, "nakira masa kai, tun d'azu yake nemanka bai samuba, yanaso yayi maka murnar nasarar dakuka samu.
Nawaf ya ce, "ayya my little bro's banishi.
Anwar yakarb'a wayan cikin 'yar muryarsa ya ce, "yaya congratulation!!,
Tnx my boy, ykk??.
Ina lafiya yaya, momcy ma ta kalli wasanka na d'azu.
Woow nice, kace ina gaisheta kajiko??.
To yaya bye🖐🏻.
Okey bye autan momcy.
Mas'ud yakarb'i wayan suka cigaba da tattaunawa, mas'ud ya ce, "to shikenan bari nabarka haka, amma gsky kayi k'ok'ari nanda 2month d'in kazo, indai kanada dama, ko kwana uku kayi ma ya isa.
Okey I will try, my bro's
Okey ALLAH yakaimu lokacin.
Sukayi sallama kowa ya kashe wayar.
Nawaf ya kwantar da kansa ajikin kujerar tareda lumshe idanu..................✍🏻






💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻12

....Zan iya cemuku biki yanata matsowa, dan shirye2 akeyi na garari agidan Alhaji buba, gidansu faisal kenan, shirin biki suke na d'an gata, dukda shi yana America abinsa, amma duk shirin da'akeyi da saninisa.
Yau tunda safe hajiya jumai tasa balarabe yakawo mata yasmeen gida.
Tunda balarabe yazo da sak'on kiran yasmeen ta had'e girar sama da k'asa😉, harga ALLAH bata son zuwa.
Umma ta ce, "wai yasmeen banaji balarabe ya ce, "hajiya na nemankiba??.
Yasmeen ta matso 😢hawayen datake matsewa tun d'azu, ta shagwab'e murya umma dan ALLAH kibarsu nikam babu inda zanje.
Dak'uwa🖐🏻 umma tayimata, kinci gidanku, hajiya ba mamarki bace ba, za kitashi kije kosaina Ci k'aniyarki, ko kin manta nanda wata d'aya kin zama surukarta.
Yasmeen tafashe dakuka, umma yanzu nan har fata kikemini nazama matar d'anta😭??.
Umma tayi murmushi mai ciwo, wanda ya nuna ainahin damuwarta, ta kamo hannun yasmeen tayi, ta zaunar da'ita gefenta tana shere mata hawaye, kinga mamana bar kuka, ba fata nake miki ba, amma yakama ta kisa a zuciyarki hajiya uwace awajenki, kuma bamusan abinda ALLAH ya shiryaba nan gaba, karki manta da irin hidima da d'awainiyar dasuke damu, komi muka zama a Najeria sune sila.
Umma aii badan ALLAH sukayi manaba, sunyine domin d'an iskan d'ansu.
Umma ta harareta banace karna sake jiba wai.
Jiki asanyaye yasmeen ta tashi, to umma na daina.
Bawata kwalliya tayiba kaya kawai ta canja ta k'ara turare ta fito.
Umma ta ce, "adawo lafiya d'iyar kwarai.
Amin kawai yasmeen ta ce, "dan idan tayi magana mai tsawo kuka zai iya zuwa mata, tasan umma ma tana cikin damuwa, tana dannewane kawai saboda ita.
A k'ofar gida suka had'u da yaseer yadawo daga islamiyya, ya ce, "sisto sai ina haka??, ta ce, "anguwa zanje.
Shiyyasa bakije islamiyyaba??, malam Dawud yanata nemanki!!.
Yasmeen ta zaro idanu da gsk kakeyi yaseer??, ALLAH karkiji wasa, dan aunty Amina ta ce, "ya karb'i hadda yau.
Yasmeen ta ce, "naga banu, bari nadawo naje wajen Aminar.
To saikin dawo, yaseer yafad'a yana nufar gida.

Tunda suka tafi take sharar kwalla, balarabe yana kallonta, harga ALLAH yana tausayama yarinyarnan, duk da bata tab'a fad'a masa damuwarta ba, amma ya fahimci bata son maigidansa, inama yanada hanyar taimaka mata wajen rushewar wannan auren K'ADDARA ko BIYAYYAR (book d'ina danafi k'yauna❤ ), amma zai gwada sa'arsa yagani.
Dahaka suka isa gidan, mai gadi ya bud'e musu get, balarabe yasamu guri yay parking.
Da sand'a yasmeen tashiga falon tamkar wata muna fuka, tai turus dan ganin samari guda uku zaune suna kallo, ta gaishesu sannan ta shige bedroom d'in Hajiya jummai dan babu inda bata shiga a gidan.
Tunda ta tafi suka bita da kallo tamkar goyon mayu, saida tashige suka kalli juna, d'aya ya ce, "kai gays badai wannan beautyn ce sakarannan zai auraba.
D'aya ya ce, "mudai tsaya mugani.
Suna nan zaune yasmeen ta fito itada hajiya jummai, suka zauna, sai asannan yasmeen talura da kwallo suke kallo, tashiga baza idanu dan son ganin mugun nan ko yananan.
Cikin sa'a kuwa aka hasko fuskarsa, yana tsaye zai buga kallon jikinsa sanye da jan JC sunyimasa k'yau, a bayan rigar anrubuta Modeebbo, kasa ansak 10, ya take kwallo da k'afarsa, da'alamadai penerrity zai buga, dan naga kowa tsaye yana kallonsa, yasaki wani murmushi maikama dana mugunta, sanna ya harba kwallon⚽, cikin sa'a tashige cikin ragar, gurin ya kaure da ihu, yayinda sauran 'yan kwallon suka d'agashi sama suna ihu, sumadai samarin saida suka furta 🗣gooooooo.
D'aya acikin samarin ya ce, "kai gay d'innan lucky nefa wlhy, kaga yacimana kwallon nan.
Hajiya ta ce, "umm kullum kudai bakuda aiki sai kallon kwallo da wak'a, ni bari na shige ciki, ga yasmeen d'innan.
Yasmeen ga abokan mijinki nan, tare suke karatu a america su sun kammalane shiyyasa, sunzo ku gaisane.
Yasmeen ta ce, "to momy.
Hajiya jimmai ta shige, sai asannan yasmeen tad'an kallesu, saitaga ai ita suke kallo suma tai k'asa da kai tana fad'in sannunku da zuwa.
Suka amsa da yauwa 'yammatanmu ykk?, ya Najeria??.
Cikin jin kunya ta ce, "lfy lao kuma ykk, ya turai??.
Suka amsa da lfy lao, d'aya ya ce, "sunan izziddin, wannan kuma hisham, wannan kuma hashim, mu abokan angonkine kodayake baki tanbayemu ya yakeba??.
Yasmeen tayi murmushi mai ciwo ta ce, "karku damu ai nasan yana lfy, d'ayan data kula yafi kowa surutu iziddin kenan, ya ce, "duk da haka yakamata a tanmbayemu.
Cikin kosawa ta ce, "to ya yake??.
Sukace yana lfy ya ce, "agaidaki dak'au.
Ta ce, "ina amsawa ngd.
Nan dai sukayita zuba mata surutu, harda wanda bata tambayesuba, tanaso tatafi dan tagaji, amma bataso suga kamar ta wulak'antasu.
Saida suka gaji dan kansu, konace saida suka gama kallon kwallon sannan sukai musu sallama suka tafi.
Bayan tafiyarsu yasmeen ta ce, "mom nima bari nawuce magriba tayi.
Hajiya ta ce, "aii nazata anan zaki kwana.
Yasmeen tad'an sosa gefen wuyanta tana fad'in A'a mom, zanje gida nayi karatu dan gobe inada test a school.
Okey to ALLAH ya taimaka d'iyata.
Amin yasmeen tafad'a.
Babudai wata matsala ko??, hajiya ta tambaya?, yasmeen ta d'aga kai alamr babu, to shikenan ina balaraben yazo ya kwashe miki kayannan dasuka kawo miki.
Lah mom to kema d'iba mana.
A'a d'iyata ke suka kawo mawa, dan haka jeki da abinki.
Har wajen mota hajiya jummai tarakata, dan har zuciyarta tana k'aunar yasmeen, tamafi d'annata sonta.

Ana sallar magriba yasmeen tashiga gida, balarabe ya tayata d'aukar kayan suka shiga, sallah tafara k'ok'arinyi dan kar lokacinta ya shige.

Abangaren samarin nan kuwa tunda suka fita suke santin k'yawu irin na yasmeen, ixiddin ya ce, "hisham gafa hanya mai sauk'i ta d'aukar fansa, dan maida murtani ga abokin dambe ba laifi bane.
Hashim ya ce, "gsk yarka iziddin, hisham yakamata ka rama abinda faisal yayi maka, dan wannan itace dama ta k'arshe dazaka iya samu, karka bari ta k'ub'uce maka.
Kuma tabbas idan muka aikata, munyi jihadi, dan na lura yarinyar kamilace, bata dace da d'an iska irin faisal ba.
Hisham ya dafa kafad'un abokan nasa, ya ce, "karku damu abokaina, kudai kusaka idanu kusha kallo, amma tabbas gsky kuka fad'a yasmeen kamilallaiyar mace ce, inhar ta airi faisal d'an giya manemin mata tofa tabbas ta cutu.
Dan haka ku biyoni domin kallon wasan, kud'auka nine zanyi wining, faisal zai samu game over, yafad'a yana wata dariyar mugunta.
Na ce, "tofa ana wata ga wata, to bamusan waye keda nasaraba saimunyi bulayiiiiiiiii........................✍🏻






©2016

💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻13

.....A yaune aka kawo gagarumin lefen yasmeen, gsky su hajiya jummai sun taka rawar gani, dakaga lefen zakasan anyishine domin d'an gata.
Tunda lefen ya iso yasmeen tashige d'aki tana kwasar kuka, dukkan mutan gidan idan ka kallesu zaka gano basa cikin walwala, saidai suna iya bakin k'ok'arinsu wajen yin fara'a koda iya ta hak'orice.
Bayan masu kawo lefe sun tafi umma ta shiga d'akin yasmeen dan tasan tana cikin damuwa, cikin bargo ta tarar da ita kuwa tanata rawar sanyi da'alama bata cikin k'oshin lafiya.
Cikin hanzari umma ta k'arasa gareta ta yaye bargo, wani irin zafi taji ajikin yasmeen ga rawar sanyi.
Ba ab'ata lokaciba wajen kaita asibiti taga likita, da haka aka cigaba da hidimar biki, wanda gidansu faisalne kawai suke farinciki.
A yaune kuma faisal ya diro k'asarsa ta haihu, iya yensa sunyi farinciki da ganinsa, babu abinda ya canja arayuwarsa sai lalacewa daya k'ara yi, saidai zamu iyacewa ya k'ara girma da wayewa mara amfani.
Bayan ya huta da yamma ya aiki balarabe wai yaje ya d'akko masa yasmeen, lamarin yabama balarabe mamaki, ya za'ayi ace budurwa ce zatazo gidan saurayi???, haka dai yaja mota yatafi yana waswasi.
Yaro yasamu ya aika saboda gidan yau akwai mata dayawa, anata hada2r biki.
Yasmeen tafito dan taga wake kiranta, daka ganta zaka gano matsananciyar damuwar dake tare da ita.
Takarasa wajen balarabe suka gaisa, ta ce, "balarabe wayake nemana.
Ya ce, "dama ogane ya ce, "nazo nad'aukeki.
kad'aukeni kuma??, to kakaini ina??.
Wai na kaiki gidansu yanacan yana jiranki.
Wata uwar harara ta sakarma balarabe kamar shine da laifin, ta ce, "kaje kasanar masa na ce, "bazan zoba, tana gama fad'a tashige gida.
Balarabe baiga laifintaba dan hakan datayi shine dai2, ta burgeshi wlhy.
Amma dayaje saiya cema faisal ya je bata gida, wai sunfita da k'awayenta.
Hannu kawai yad'agama balarabe dan gsky yaso yasmeen tazo, wayarsa ya d'auka yakira wata number, ana d'agawa ya ce, "su had'u agidan daya nuna mata d'azu.
Tashi yayi ya shirya ya d'auki makullin mota ya fice, kai tsaye gidanshi yanufa inda za'akai yasmeen, babu k'arya gidan ya had'u, anzuba komai amarya kawai ake jira, anan ya tarar da wata kod'ad'iyar mace wadda bilicin yayma k'awanya. 😔lamarin yayi matuk'ar b'ata mini rai, lallai yasmeen taga takanta, dan nakula faisal bunsurune, inagama yasa ad'akko masa yasmeen d'inne dan ya........hummm shege d'an iska.
Tun afalo suka fara k'auce hanya, bak'in cikine yasani nabaro gidan dan bazan iya ganiba.

Haka biki yacigaba da gudana, yasmeen dai tak'i yarda faisal ya ganta, yabi duk hanyoyin dazai ganta amma ta rufe masa k'ofa, daga k'arshe abin ya b'ata masa rai ya tattarata ya watsar, dan yasan nanda wani d'an lokaci zata kasance agidansa dole, kuma duk wulak'ancin datake masa saiya rama.

NAWAFF
a yaune Nawaff ya sauka Najeria saboda kwallo dazasu bugama Najeria, wanda yakasance na Africa, kuma Najeria itace mai masaukin bak'i.
Mas'ud da Abdallah da Anwar ne sukaje tarbosa, sunyi farin cikin ganinsa, shima yayi farincikin ganinsu.
Mas'ud ya ce bro's kudai ba'a ganinku saida dalili, turai ta kwace mana kai gaba d'aya.
Nawaf yay dariya, su sun isa su kwace ni ahannunku, kawaidai nad'an lokacine, amma ni nakune.
Abdallah ya ce, "yaya watanka 6 fa kenan da barin k'asarnan, yanzuma badan zakuyi wasannan ba dabazamu gankaba fa sai hutun k'arshen shekara.
Nawaf yay murmushi kawai batarda ya ce komaiba.
sunata hirarsu har suka isa gida, momcy ta tarbi Nawaf cikin farinciki, Nawaf ya narke murya cikin shagwab'a ya ce, "momcy nayi missing naku wlhy, ina papa ko yana wajen aiki ne??.
Yana can momcy tafad'a, amma nasan yana hanyar dawowa, yakamata kadaina shagwab'a haka nan modeebbo, kagirma fa.
Su Anwar suka tuntsure da dariya, ya wurga musu harara, sannan yadawo da kallonsa wajen momcy ya ce, "momcy ni ban wani girmaba.
Momcy ta shafa kansa tana dariya, ta ce, "ina mas'ud wai?, Nawaf ya ce, "ya koma asibiti, dan yace yanada aiki sosai.
ALLAH sarki Mas'ud sarkin k'ok'ari kenan. momcy tafad'a.
Nawaf ya mik'e momcyna barinaje nayi wanka jikina duk yayi tsami, to abincin fa?, mom sainayi wanka sannan, yanzu zan dawo, dan nayi missing d'in girkinki.
Momcy tayi dariya to aii yau zakaci kamore.


YASMEEN.
rana bata k'arya inji masu iya magana, yaudai aka d'aura auren faisal da yasmeen, d'aurin auren yatara manyan mutane masu fad'a aji ak'asarnan, saka makon babansa sanannen mutumne, kuma d'an siyasa.
Sai dai abinda yabani mamaki duk d'unbin taron jama'ar nan babu ango awajen.
Ana cikin shafa addu'ar k'atshe saiga faisal tamkar mahaukaci dagashi sai wando iya guywa da riga mara hannu, kutsa kai yake kawai cikin jama'a, har ya isa gabn liman, ya tsaya k'erere👯yana wurga idanunsa dasukayi jajur.
Alhaji buba yamik"e da sauri yana tambayar d'an nasa lafiya???.
Faisal ya yamutse fuska ta reda fad'in abba and'aura aurennan kuwa??.
Alhaji buba ya ce, "emana faisal and'aura yanzu kazama ango.........hannu yad'aga wa mahaifinsa ya ce, "to abba awarwareshi yanzunnan.
😳Alhaji buba yazaro idanu faisal kamarya a warware??, cikin k'araji faisal ya ce, "kamar yanda aka d'aura narantse da sarkin dake busamin numfashi bazan zauna da karuwaba, dan haka sai an warware shi.
Gaba d'aya gurin yayi tsit ana kallon sarautar ubangiji.
🎤abin maganar dake hannun liman faisal ya kwace, yajuya yana kallon mutane, ya ce, "kamar yanda kuka shaida and'aura auren faisal da yasmeen, to haka nakeso ku shaida faisal ya saki yasmeen saki uku!!!!!!!!!!!!!!!!!.
Gaba d'aya wajen akad'au "INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN....................✍🏻


Hummm nikaina dabana son wanga aure, saida na girgiza domin jin furicin faisal!!!.






💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞 LUV U OLL MY FAN's💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻14

.....Cikin b'acin rai Alhaji buba ya wankama faisal mari, faisal yadafe kumatu yana kallon baban nasa, mahaifin yasmeen kuwa fad'uwa yayi, dukda baya son auren abin yay masa matuk'ar ciwo.
Gurin ya rud'e da surutai, kowa yana fad'ar albarkacin bakinsa, zuwa sannan an yayyafama abban yasmeen ruwa ya farfad'o, ya fashe da kuka yana fad'in yanzunan irin cin mutuncin daza ayimin kenan saboda anganni talaka, banida komai bani da kowa.
Wani dattijo naga ya mik'e tareda dafa Abban yasmeen, ya ce, "kanada kowa malam, kuma ka kwantar da hankalinka, indai ka amince zan d'aurama d'ana aure da d'iyarka yanzunnan.
Abba yabi dattijon da kallo, gsky ne dattijon mutumne mai kamala da dattako, yatabbata bazayayi dana sani da tayinsaba.
Liman ya ce, "malam ka amince na tabbata bazaka tab'a dana sanin hakanba, Alhaji sa'eed mutumin kirkine, yakuma bama d'ansa cikkiyar tarbiya.
Abban yasmeen ya ce, "shikenan nabashi!!, ALLAH yasa haka yafi alkairi.
Liman da dattijo suka amsa da amin.
Har mutane sun fara tafiya akayi sanarwa adawo za'a sake d'aura aure, mutane kam sun amsa kira, dandanan gurin yay tsit aka nutsu ana jiran mizaije yadawo.
Nantake dattijo ya ajiye sadaki dubu hamsin, nakasa kunne naji dawa aka d"aura amma hayaniyar mata dake cikin gida yahanani, dole na hak'ura.
Bayan angama d'aurin aure komai ya natsa, zuwa sannan labari yashiga cikin gida, dafarko umma taji bak'inciki, amma da'aka sanar da ita k'arshen al'amarin saitaji farinciki mara musali, nutsuwa da annashuwa suka bayyana saman fuskarta.
Ammafa nakasa gano muku amarya bare nasan halin datake ciki.

GIDANSU NAWAFF.
papa yashiga gidan fuskarsa cikeda fara'a, momcy ta taryeshi, bayan yasha ruwa ta ce, "Alhaji lfy dai naganka cikin farinciki haka??.
Papa yay murmushi har wushiryarsa ta bayyana, ya ce, "ummul'khairi ina cikin farinciki yau, kuma kema idan kikaji nasan zaki tayani farin ciki, kamar yanda nagaya miki zanje d'aurin aure to daga can nake, bud'e kunnanki kisha labari.
Momcy tayi dariya tareda fad'in ina sauraraenka Alhaji.
Papa yagyara zama tareda zayyane mata abinda yafaru, yad'ora da fad'in wlhy mutumin yabani tausayi, dan idan nine akayima haka, to idan na suma bazan far fad'oba.
Dan haka atake agurin nabiya sadaki aka maida d'aurin auren akan MODEEBBO!!!!.
momcy tad'an zaro idanu, Alhaji modeebbofa kace??, papa ya gimtse fuska ya ce, "ashe kin jini!!.
Ta ce, "amma kana ganin baza'a samu matsala a wajen modeebbo ba??, papa ya kwantar da kansa ajikin kujera, ya ce, "aii bana fata na haifi d'an dazai bijirema umarnina, ko mas'ud nace na d'aurama aurennan dole ya amince bare NAWAF.
momcy ta ce, "kayi hak'uri Alhaji bahaka nake nufiba wlhy, ina farin ciki da umarninka, ALLAH kuma yasanya alkairi, wlhy tun kafin naga yarinyar ma tashiga raina, kuma ina k'aunarta tamkar yanda nakeson su modeebbo.
Papa yay murmushi yana tashi zaune, yakama hannun momcy yana murzawa, ngd ummul'khairi, ngd da had'in kan dakika bani, inaso ki taimaka mini wajen fahimtar da modeebbo.
Momcy ta zare hannunta daga nashi tana fad'in Alhaji kar yarannan su shigo su gammu.
Murmushi papa yayi batareda ya ce, "komaiba, waya ya d'auka yana kiran Nawaf!.
Nawaf yana kwance ad'akinsa yanaso yay barci, dan yau zaitafi abuja da yamma, ya mik'a hannunsa yana laluben wayarsa datake wringing, da sauri yamik'e zaune dan ganin papane yake kiransa.
Cikin ladabi ya ce, "papa barka da rana, barka kadai papa yafad'a, ya ce, "kana inane??, cikin ladabi ya ce, "ina d'akina papa!.
To kazo kasameni.
To Nawaf yafad'a tareda mik'ewa yafito domin amsa kiran papa.

Afalon momcy ya tarar dashi, ya rissina ya gaishesu, suka amsa, papa ya ce, "Modeebbo miye matsayina a wajenka?.
Cikin matuk'ar mamaki Nawaf yad'ago yana kallon mahaifan nasa, ya daure ya ce, "papa kai mahaifinane, wanda banida kamarsa aduk fad'in duniya.
Papa ya jin jina kai, tareda cewa masha ALLAH, to modeebbo amatsayina na mahaifinka na zartar da umarni akanka yanzunnan, nan papa ya labratawa Nawaf duk abinda ya faru.
Atsorace Nawaf yake kallon papa yayinda zufa keta ambaliya adukkan sassan jikinsa, ya daure cikin rawar murya ya ce, "papa aurefa kace??.
Papa ya ce, "kwarai aure nace modeebbo, kuma ina fata amatsayina na mahaifinka zaka yimini biyaya, zaka kuma karb'i k'yautar da ubangiji yay maka da hannu biyu, natsuwarka nake buk'ata da farin cikinka, bana son wannan lamarin yatab'a rayuwarka bare kasamu matsala akan abinda

Please Login or Register in order to submit comment