Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muguntar kuwa nai ready yana ja na rikeshi ram,saida muka daidaita a kan kwalta sannan na sakeshi muka mika,
Muna isa kuwa saura minti sha biyar a tashi haka muka zauna mukaga kadan kafin a tashi muka nufi hanyar gida, nace don Allah ya kaini Gidan Mamee wata yarinyara tare mukayi Nursery and primary da ita tayi secondary nata daban anyimata Aure ita kadaice nake tunanin kawata da muke tare da ita muke dan shiri amma wani lokacin in ta kama mukanyi fadan don ni ban bar kowa ba,
Muka shigo layin nasu na duba kamin na gane kofar gidan, na nuna masa kofar ya cake machine din na dirgo nace ya tsyani ya daga kai ina shiga naji ya tayar da machine din ya tafi a zuciyata nace gantalalle jeka Allah ya so ai zan iya zuwa, wayata na ciro a jaka na kira Mama bugu daya ta daga nace mata "Mama naje gidan Mamee ancemin batada lafiya shine na biya zan gaisheta", ta ce "to karki dade inba haka ba kinsan halin yayyenki insuka tarar bakyanan ke dasu", na ce "to Mama sai na dawo", ta ce "ki gaida Mamee kimata ya jiki", na amsa sannan na kashe wayar na sanya a jaka, na karasa main parlon gidan nai knocking, mai aikinta ta bude min kofa ta ga ga nice taban hanya na shiga ta mayar da kofar ta rufe ta gaisheni kamin tace bara na kira miki ita,
Ta sauko a saman bene ta karaso da saurinta "wazan gani? dan Allah Ade kece dagaske?, Wallahi bakida kirki sam, nai murmurshi kawai ina dubanta ganin duk da wani kumbura ta zama katuwa da kiba nace "ke? Me ya sameki lafiya ko rashinta naga kin wani haye kin kumbura? Kaman wadda tasha Sha ka fashe?", Tai dariya "aa abinda yafi sha ka fashe jin dadi ya maidani haka Aure mai dadi, ke Ade kisa Allah a ranki kinki kiyi Aure sai gantali kika iya da kule kulen maza, nasan har yanzu kina nan da wannan mugun halin naki na shiga tsakiyar maza ko?", Na ce "kinga irin abinda yake hadani dake fa wallahi shiyasa bana son zuwa gidanki ahto zama ki daina ganina",
Ta ce "ai ita gaskiya daci gareta wallahi gaskiya nake fadamiki Ade ba don ina kinki ba duniyace ki bita a hankali in ba haka ba ta koya miki hankalin ah to, Rahma!? Rahma!", Ta kwallawa mai Aikinta kira ta zo ta kawowa bakuwarta ruwa da lemo,
Na mike nai sallah mukai firar yaushe gamo da ita na dan jima kamin na mike mukai sallama tai tamin godiya na fito a kafa na tattaka har gida na shiga naci saa kuwa Yan bala'in basu dawo ba sai Mama kadai a falon a zaune na gaisheta da mata sannu da gida nai wuff na shige nace mata zanyi sallar isha'i nai maza na tube JC na na maida doguwar riga kamin na daura Alwala na tayar da sallah ina idarwa ko shafa'i da wutri banyi ba na fito nazo na zauna saboda inaso muyi hira da Mama da maganar da nakeso nai mata.

Ina idarwa na fito kamin yayanta suzo itama ta fito kenan daga dakinta ta zauna kan kujera na zauna kasa na ce "Mama dama wata Magana nakeson fada miki tace "to Auta ina jinki",
Na ce "Mama zancen makarantar mu ne dama kinga mun kusa fara Waec shine Malamanmu suka ce Oxford University zasu fara bada Admission kowa yaiwa iyayensa magana inda mai so shi ne nace dan Allah Mama ki fadawa Abba kinji"?,
Tunda na fara magana bata katseni ba sai ido data zubo min sai da nagama tas tace "sannunki to kinji? Sannunki ni zaki jawa magana da barbada a gari da bakin jamaa ki turani wajensa? Ki jazamin Bala'i banji ba ban gani ba? To Wallahi kinyi kadan ai kinsan hanyar Wakin nasa maza kije ki fadamasa shegiya, wato abin naki yabar nan da ake fada kasar waje zaa kaiki kiyi yanda kikeso nan ma kaka aka cika barega kinje wajenda uwa babu kwaba uba ko dunguri kina gani ko yayansa Maza bai kai ba saike shafaffiya da mai maza kije yaji kinsan Halin Bala'insa ya balla shegiya ya zubar tashi ban waje shasha mara hankali",
Na mike ina tunzura baki nai daki na na fada kan gadona kuka ya tahomin inajin wani tukuki a raina bansan me yasaba na zama tamkar mujiya a cikin mutane anayimin wani irin kallo na zargi da tuhuma komai nai sai a hantareni komai nai zagi cin mutunci ban iya komai ba babu mai iya min nasiha sai zagina abin yanamin ciwo a raina kuma ni banga ba daidai din da nakeyi ba a ganina komai nayi daidai ne,
Nayi juyi naji wayata tana ringing na duba Mamee ce, na ajiye wayar ina doka tsaki, tana yankewa ta sake kira na daga ina tambayrta Lafiya? Ta ce "wa ya batamin ran Gimbiya duk yanda akai ranki a bace yake me akayi Miki? Na ce "Bakomai", tasan tunda nace ba komai to bazan fada din ba kuwa yasa ta bagarar da zancen ta ce "ya kika zo gida?", Na ce "Lafiya", ta ce "to Allah ya huta gajiya mai gidan yana gaisheki muna godiya", nace "ina amsawa", taimin saida safe mukayi sallama, na kashe wayar na kwanta ko Online ban hau ba jina nake raina a bace nai addua naja bargona ina karanta wasikar jaki har bacci ya saceni.
Washe gari ta kama Ranar Juma'a Babbar rana ta kama da wuri zamu dawo a makarnta sha daya sabanin sauran ranakun da muke dawowa daya da rabi zuwa biyu,, muka fito kamar yanda aka saba duka yan gidan wanda suke zuwa makaranta sun shirya an fito masu zuwa aiki suma sun shirya school bus ta gidan ta fito duk aka shishshiga nikuma driver na ya fito da mota, Yaya Auwal har zai shiga mota ya hangoni ya fito da sauri ya zo ya kamamin kunne ya murde na dafe saida wajen yayi kas ya ce "wallahi wallahi naji wata Magana karama ta tashi kika dawo sai naci Ubanki Allah tom", ya juya kansa "malam habu don Allah duk abinda tayi maka inkun dawo ka fadamin don Allah kaji?", Ya daga kai "To yallabai", ya amsa ba don zai fadaba saboda in ma ya fada bata canza zani ba saidai ya janyo wa kansa wani ruwan da zai lakada masa du™a, yana wucewa na zumbura baki na shige motar naja na kame ina jira mu bar gidan,
Mun kusa isa makarantar na ce "Dakata! Tsaya!Tsaya!, Auziya ce ta subuce a bakinsa saboda yasan hali yasan zaa rina gashi a tsakiyar titi ya kusa rikicewa zai saki kan mota ya matsa gefe yayi Parking, na ce "Ai? Ni shedaniya ka maida ni zakai min wannan auziyar? Shedaniya ka maisheni? Yau koni ko kai wallahi fito fito dan Kutumar Ubanka", na balle murfin mota na fito har ina buga tuntube na zagayo na balle murfin motar gaba nace "fito mana Wallahi yau mai rabani da kai sai Allah da Malaman gari Wallahi ba kai mara mutunci ba? Yau zan nuna maka asalin kalata zakaga karyar tashanci dan kan Uwarka,..
'þ

*PAID BOOK 300 ONLY*
*SEND VIA THIS ACCOUNT=ØGÜ*

*SAFIYYA GARBA MUKHTAR*
*JAIZ BANK*
*0007688753*
*EVIDENCE OF PAYMENT HHERE=ØIÜ 09042684315 siyan na gari maida kudi gida*


*AUREN SADAKA BY SAFIYYA MUKHTAR GARBA*

#Share 'þ
#comment'þ
#EditingL'






*AUREN SADAKA 7&8*





*AS.Episod one.pg7&8*. *E*O*W

*09042684315*=ØÞÜ

=Ø…Ü*FC'- 'D5/B)*

*AFUWA DA JINA SHURU LAYINA YA SAMU MATSALA AN MIN HACKING ACCOUNT DINA NA WHATSAPP DA DAYA NUMBER YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI* *09042684315* *WANDA SUKA TURO MIN KUDI SU TURAMIN SHEDAR BIYA TA SABUWAR LAMBATA NAI ADDING NASU A PAID GROUP NGD.*




Ganin baya da niyyar fitowa yasa na sa hannu na cacumo wuyansa ina kokarin janyo shi ya rike sitiyarin kam "nace bazaka saki ba? Bazaka fito ba? Ashekai dan iskan karya ne munafika, kamin kace kwabo jamaa sunyi dafifi tamkar masu jiran kiris aka cika wasu na kallo yayinda wasu suka matso kusa damu suna bani hakuri, da tambayar ba'asin me ya faru? Ban kulasu ba na zazzageshi tasss nai masa wankin babban bargo na kama gabana na barshi dasu suna tambayarsa ya akai,
A kafa na karasa makarantar ina zuwa ma na makara amma babu yanda zaai dani dole aka barni na wuce, ina hawa step din class dinmu na hangoshi ta gate ya shigo nai kwafa kamin na shige class din ina cin magani donma kar a kawomin Raini na tafi desk dina na zauna,
Sai Eleven aka tashi aka ce muje mu duba an kafe Timetable sannan maganar Admission na Oxford kuma zaai maganar ranar Monday, muka duba 10 June zaa fara nanda sati daya kenan tunda yau 3ga wata,
Daga wajen ganin Timetable nai hanyar fita na fara takawa a kafa har na fita titi naji Horn a bayana na waiga Habu driver ne ya fito ya biyoni yana rokona na "don girman Allah ranki ya dade ki taimakamin ba don ni ba badon Halina ba ki taimaka ki shiga motar nan kizo mu tafi kinga yau Juma'a garin goslow bazaiyuwa kitafi ke kadai ba kar wani abun ya sameki", na ja na tsaya kamin na juya na watsa masa banzan kallo, "in wani abin ya sameni matsalar kace? To ka kama gabanka bazan shiga motar nan ba in sama da kasa zata hade bazan shiga ba", ya ce "bama zata hade ba nidai ki taimakeni kimin rai ki rufawa aikina asiri kizo mu shiga",
Nace "bafa na son Kutumar ubanci yaushe na fara wasa dakai Habu? Wallahi ka fita min a ido in rufe billahillazi",
Na kama gabana ina cigaba da tafiya bai ko fasa bina ba naje daidai junction naga anja machine an cake a gabana na daga kaina ina mamakin wane mai karfin halin ne,
Wani dan Class dinmu ne dukda ba kasafai muke magana dashi ba dukda abokin takarata ne a ajin bangaren karatu mune gifted din ajin queez ko dibet in zaa fita da mu ake zuwa amma bama magana da shi sam Bayerabe ne sunansa Ademola, but ana kiranshi Ade, mutane kukance sunan mu iri daya shiyasa muke da kokari kila,
Ya ce "Namesake ina zuwa haka a kafa ina Driver naki yau?", Jinai kamar zan masa rashin mutuncin tareni da yayi sai kuma na auna na gani inason ya taimakeni don a halin da nake ciki bazan iya zuwa gida ba don ban ma san hanyar ba, nace masa "yau be zoba" ya ce "amma shine kike tafe a kafa kamarki wannan ai bai kamace ki ba, gashi ban fito da motana ba amma ki hau machine sai na karasa dake",
Banda zabin da ya wuce haka dole yasa na hau kan machine din, ina hawa Habu ya karaso na dafe kaina ina jinjina maita irin ta wannan bawan Allah, ya rike kan machine din, "kai kuma daga ina?, Ina zaka kai yar mutane?", Ade ya juyo kaina"wannan mutumin fa? Kinsanshi ne", ta ce "ina fa? Na yanzu muka ganshi dakai ba? Bansanshi ba wayasani ko irin mahaukatan nan ne?,", Ya ce "to matsa mu wuce bamu hanya Allah ya sawake", Habu ya ce "Kaga yaro ka fita daga idona in kulle ka sauke yarinyar mutane kamin na kirama hukuma", na ce "Ade please let's go kar mahaukacin nan ya taramana jamaa anan oya muje", ya ja machine fiiii muka wuce muka barshi nan tsaye,
Habu ya rasa inda zaiyi Kar ya tafi musu da yarinya yaje ya shiga uku yasa a daureshi haka kawai, gashi shi zuciyarsa haka kawai yaji bata aminta da yaron ba ya daga kansa har sun bace ya daina hango kyallinsu to shi yanzu ya koma gidansu yacewa iyayenta me? An saceta ko mene? Ina ba ma zaiyuwa ba, haka ya dinga sintiri da zirga zirga ya rasa ma wane tunanin zaiyi,
Yakusa awa biyu a wajen bai tafi ba kamar mai jira a dawo masa da ita amma, daga karshe yaga bashida wani zabi yasa dole yaja motar yai gida yana sakawa da kwancewar me zaije ya fada musu ya tabbata yau sai ya kwan a hannun yan sanda babu makawa tabbas,
Yana zuwa yai parking a parking space ya wuce direct wajen mai gadi yana tambayarsa yaga Ade ta dawo kuwa? Ya ce masa "Eh ta dawo itada wani namiji ya kawota tun dazun ma, ya akai yau baku dawo tare ba?", Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, "kaidai bari ai nashiga cikin yanayi Allah ne kawai ya fitar dani wallahi".. ya bashi labarin duk abinda ya faru", yai masa dariya "tab wallahi wannan yarinyar tana wahalar da kai in nine akasa wallahi bazan iya daukar wulakancin ta ba sai na tafka mata rashin mutunci na kamata na ci ubanta sannan na kaita wani wajen inda ya ke babu mai ganina nai mata ehh yaneee...naci banza wallahi Ai ka gane", ya karasa fada yana daga gira,
Habu ya ce "ai kai kace nikam rufamin asiri bama zan iya ba wllahi wai babu ruwana kam kai daban ni daban", ya ce "kaji irinta kai dadina dakai wani lokacin kanka a tukunya yake wallhi maza kaje tai ta gasa ka a banza a hofi", Habu ya canza musu hirar suka ci gaba da wata...

Kamar yanda muka saba a gidan duk Juma'a zama take kamar Ranar idi a gidanmu zaa dafa abinci mai yawa a rabawa makota sannan a fita dashi waje maza manya abokansu yaya da su Abba ai ta zuwa a zauna a ci a
Musanya sabbin kaya inda dama ma muje ziyara gidajen yan uwa to hakan ce ta kasance yau a gurguje na shirya don naso na makara na zura hijab dina na dau sallaya na fita har sun cika a mota duka yan gidan babu ragin daka muka dau hanya sai masallaci, muna zuwa ana kammala huduba aka tayar mukai sallah akayi adduoi na neman tsari da zaman lpy da bamu shuwagabanni na gari, sannan muka juyo izuwa gida lokacin an kammala girki duk sasan Iya kakarmu muke haduwa a ci abinci asha ayi hira kowa ya fadi matsalarsa ayi solving shine amfanin zaman da taruwan da akeyi dama don a tattauna,
Da dare Ademola ya kirani wai mu gaisa yamin bangajiya ban kiba tunda gaisuwa ce muka gaisa kamin na masa sallama na kashe wayar don ina bukatar kwanciya da wuri saboda in tashi da wuri zamu Tahfeez.
Washe gari na gaisheda Mama take cemin zamuyi gyaran Gida yau da dare Abbanmu zai dawo nayi murna da farin ciki sosai da jin maganar nan saboda wajen Abba kadai nake samun ragi agidan nan dukda shima A ne badai fada ba amma ni yana sassautamin ba kamar Mama datake min keke da keke ba take nuna fifiko tsakanina da yayyena shikam yana sona shiyasa nake matukar ji da shi ina sonsa nima,
Na ce "to Mama bara mu dawo daga tahfeez sai in tayaki nasan dai kamin na dawo kin fara", ta ce "eh Allah ya kaimu ki dawo din sai mu cigaba, na koma dakina na karasa azhkar na na dan daddana wayata don ka'idata ce wannan indai zan jini a zaune to sai na taba waya ko nahau Online nai chart, ina gamawa na shiga wanka na shirya nasa uniform dinmu kalar dark green riga da wando da dankwali da hijab duk kala daya na dau kur'anina da azhkar sai farin hankie na sa wayata a wardrobe don su Baa zuwa musu da waya makarnta in kaje dashi kwacewa ne kuma kai da ita har abada ka barta kenan, an taba gwadani shiyasa nima na kiyayesu duk abuna bana zuwa da ita saboda inason abata in suka kwace kafin a saimin wata saina yara gashi ni ba kudi ba ballantana ince na siya da kaina shiyasa nake lalllaba abata,
Nagama shirina tsaf na fito na karya a gurguje sabida kar na makara nayiwa Mama sallama na fita bada driver zan fita ba saboda bamu da nisa da makarantar bayan layinmu ne tafiya kaWan zai kaika na fito na wucesu yana zaune shida mai gadi yana ganina Idi mai gadin ya taso da hanzari ya budemin get kusan rabi don na riga na fada masa ni bazan fita ta kofa ba saboda tamin kadan don haka dole a budemin get ya ko bude na fita yamin adawo Lafiya na bawa banza ajiyarsa ya maida kofa ya rufe nasa kaina gaba na shiga na tarar Yaa sayyadinmu yazo amma bai shiga aji ba da sauran mintuna ina shiga na tarar anata bita baji ba gani saboda yau zaa karbi hadda ni namanta da ita ma shaf gashi banyi ba yau kam saidai ya dakeni,
Lokaci yana cika ya shigo aka mike aka gaisheshi ya zauna sannan muma muka zauna aka fara da yan gaba gaba har akazo kaina banma tsaya wahalar da Sharia ba nace masa ban iya ba dama haka ya ke so ya zage ko ya dinga lodata tamkar ya samu ganga sai buguna yake,
Saida ya dakeni don son ransa sannan ya kyaleni kuma tunda na bada hannu daya ban kauce ba don ni dama gaskiya inada juriyar duka ko zaaimin bulala nawa bazan gaji ba saboda ni tun ina yarinya na saba da dukan mazan gudanmu saboda rashin jina wannan ya daka wannan ya rankwasa shiyasa dukan makaranta banajin ko dar don zaayi yan class dinmu har mamaki suke bani in naga suna rawar jiki in zaayi bulala goma, tab yo me akayi akai bulala goma Allah na tuba?
Shiyasa suke cewa don naga ina da karfine don basuyi karya ba karfi kam akwaishi ko doki Albarka don Wallahi lokacin ina primary dama kwayena maza ne in ta hadomu da su haka zamu zage muyi ta dambe harbi da kafa naushi salosalo naiwa yaro jina jina iya kaci akaini to wajen malami aimin duka ko punishment shiyasa na horu da wahala tun ina karama,..
'þ



*PAID BOOK 300 ONLY*
*SEND VIA THIS ACCOUNT=ØGÜ*

*SAFIYYA GARBA MUKHTAR*
*JAIZ BANK*
*0007688753*
*EVIDENCE OF PAYMENT HHERE=ØIÜ 09042684315 siyan na gari maida kudi gida*


*AUREN SADAKA BY SAFIYYA MUKHTAR GARBA*

#Share 'þ
#comment'þ
#EditingL'






*AUREN SADAKA 9&10*




*AS.Episod one.pg9&10*. *E*O*W

*09042684315*=ØÞÜ

=Ø…Ü*FC'- 'D5/B)*

*AFUWA DA JINA SHURU LAYINA YA SAMU MATSALA AN MIN HACKING ACCOUNT DINA NA WHATSAPP DA DAYA NUMBER YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI* *09042684315* *WANDA SUKA TURO MIN KUDI SU TURAMIN SHEDAR BIYA TA SABUWAR LAMBATA NAI ADDING NASU A PAID GROUP NGD.*


Haka muke tataburza da Yaa sayyadinmu yace ai tsabar raini ne wai yana duka na bazanyi kuka ba baisan ni karamar magana sai ta sani kuka yawan duka bai sani ba ma kuma duk abin nasa bai taba sani kukan ba.
Shadaya daidai aka tashi na kamo hanyar gida ina zuwa na tarar Mama na ta aiki itada masu aiki suna tayata gyaran falo da goge inda yayi kura da wankin tiles ita kuma tana kitchen na bita kitchen din na mata sannu da aiki ta amsa tana mikomin katon baf ta kwaba fulawa ta kayan snacks da zaayi dayake akwai kayan aiki na gashi nan da nan mukayi muka gama aka dora abinci me rai da Lafiya Aka zuzzuba a flask ta fito falon taga yanda yayi kyau kaman an sanjoshi tace lallai komai yanason gyara ji yanda wajen yai haske Masha Allah sannuku da aiki suka amsa itama sukai mata sannu aka gama abinci ta zuba musu ta sallamesu sukai godiya suka koma bangaren su na masu aiki, don ita bataso masu aiki kwata kwata ragowar matan gidan ne suka daukosu tace ita bata so gwanda ta dinga yin aikinta da kanta.
Ba mu muka gama ba sai kusan daf da La'asar muna kammalawa ya kirata ya ce sun shigo cikin gari yanzu zasu karaso gida in Allah ya yarda anan ma zasuyi La'asar ta ce to Allah ya kawosu Lafiya ta fadamin nai maza na shirya zasu karaso nai sauri na shiga wanka na dauro Alwalata ta La'asar nazo na shirya na danyi yar kwalliya kaWan a fuskata na bude wardrobe na dauko Abaya don ni kayana kusan duk itace saboda ina sonta saboda ko atamfa ce doguwar riga nakeyi A shape saboda Mama ma ta hanani dinka riga da sket saboda inada kiba sosai indai na dinkasu to sai an matsemin kuma shape dina zai fito saboda ni din ba kaWan bace irin sangaman matan nan ne giant ga tsayi ga kiba Abbana na biyo shima haka yake yasaka bana riga da sket kuma dama can bana sonsu sai dogayen riguna kawai zani ban iya daurashi ba balle nayi sai kananan kaya da JC da afterdress sune kayana,
Na gama shiryawa cikin abayata kirar dubai me favorite color na Wato Dark blue wadda Abba ya siyomin ita wancan dawowar takanas tundaga Dubai tayi min kyau sosai dukda ni bakace amma hutu da jin dadi ya boyeminshi nakoma kaman chocolate don jikina a mulmule yake babu alamar rama bakina mai kyau sabanin yan uwana da suke farare tas sun dauko Mamanmu mutane su ya cewa dama ni na yo farinta da anga kyau yanda nake Masha Allah kyakykyawa wasu kuma suce Bakin halina yasa Allah yayoni baka ciki harda su Yaya Sani na ce "bakomai haka Allah ke son ganina.
Muna idar da sallah kam sai gasu sun dira Yaya Salis ne ya daukosu shida wani abokinsa ne ya sauka anan zai huta ya ci abinci yai sallah zai wuce kd zai bi flight din maghriba, aka bude musu dakin baki daman a share yake suka shiga shikuma ya shigo cikin falonmu da murna sosai muka tareshi Ya rungume Mama ni kuma ya rika hannuna guda biyu nima na rike nashi cikin murna da doki nace "Abbana sannu da zuwa", Yaya Salis dake gefenshi ya ballamin uwar harara na kautar da kaina ina cigaba da masa Magana Abbana nayi kewarka sosai", ya ce "nima nayi kewarki yarinyata ya karatu ya rashin jin magana ince kodai ana ragewa don bana ce andaina ba", Yaya Salis yai caraf "Abba tana nan tanayi sai ma abinda ya ci gaba", nai maza na ce "Allah Abba na rage ba kayi min fada kafin ka tafi ba?", Ya ce "Eh hakane nasan ai zaki rage kina jin maganata Allah ya kara shiryamin ke ya kareki", na amsa cike da jin dadi,
Ya juya kan Mama "Gimbiya Madam yadai", Kallo daya ta mana daga ni har Yaya Salis muka bace ni nai dakina shikuma yai waje, Abba ya ce"Uhm kin korar min yara me zaki bani", tace "kasan halinsu daukan abu yanzu sai su fassara mi", ya ce "Au hakane ranki ya dade ai yanzu tare da bako muke a kai mana abinci amma bara muyi sallah tukun sai ku kawo mana keda yar taki ku gaisa ko?", Ta ce "to kuyi sallar", ya juya ya fita ta kwallamin kira na fito ta ce naje na dauko hijabina, na ce to na juya na dauko dark blue me hannu kalar rigata na saka na sa takalmi plate shima Blue na fito na taddata a kitchen tana hada abinci ta hada lemon kwakwa ta zuba a dispenser ta bani cups na zuba a tray babba ta ce na fara Kai wannan dakin baki nazo mu kama abincin na dauka na ce to, da naje ma sallah suke na aje aka kasa gefe na fito aka jera abincin da miyar da kayan cowslow da plates da cokula muka dauka lokacin sun idar muka gaisa da bako mukai musu sannu da hanya sannan muka fito don barinsu suci abincin,
Abokin Abba yai ta santin abincin ya ce "wannan ce yarinyar wajenka da kake bani labari?", Ya ce "eh itace mara ji ba", ya ce "ah gaskiyane kace mun girma mun kusa samun jika", ya ce "aikam yo shashancinta ba sai barta ta zauna ba?", Yai dariya "Haba dai Aboki kai ka zauna ma balle ita, ni da zaka bani ita ma na Aura zanso wallahi don tanada hankali",
Abba yai dariya "Lallai Alhaji Musa Labarin Sa'adah kake ji bakasan halinta ba, ai kaine SADAKA ma sai na baka ita batareda ko sisinka ba", ya ce "ina wane mutum wannan ai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment