Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi karfin SADAKA, ni fa dagaske nake", Abba ya ce "to ni da wasa nake rufamin asiri yanda hajiya take ganin mutuncina ta ce dani aka hada baki ka jamin bakin jini haka kawai ka rufamin asiri", yai dariya "Matsoraci dai baya tu zama gwani ko shi waye ahto", Abba yace"naji ba komai", sukasha hira sosai har kusan maghriba sannan yai shiri suka mike na fito mukai sallama yadanmin barkwanci mutumin nada kirki sosai yabani wrapper kudi yan dari biyu na dubu goma da har bazan karba ba ya ce "aa ba kyau maida hannun kyauta baya nasa hannu biyu na amsa nai godiya", suka fita shida Abba zasu masallaci daganan zai rakashi airport,
Na koma falonmu na nuna ma Mama kudin ta karba da godiya ta ce bara Abbanmu ya dawo a nuna masa na ko bata don dama ni duk abuna ban saba da kudi ba bansan dadin kudi ba saboda baa bani a hannuna a ce na kashe saidai duk abinda nakeso na ce asaimin to komin tsadarshi zaa saimin saidai kawai naganshi bansan zafinshi ba,
Da dare bayan Abba ya dawo ya shiga bangaren Iya gaisheta don dazu da ya dawo bata nan ta fita sai yanzu ta dawo ya gaisheta ya bata tsarabarta suna dan hira Samarin gidan sun dawo sunji Labarin ya dawo dukansu sai da sukazo suka gaisheshi Yaya Mahmud ya Amir Ya Umar Ya Walid yan Sasan Baba Hadi sai Yan bangaren Baba Kalla Yya Ishaq Yaya Abdul Yaya Zakariyya a bangaren su Yaya Deen ne kawai baizoba wai be dawo ba wayasan ma ko yana can yawon gantalinsa su Yaya Safullahi da Yy Abbas da Uy Ubaid sai Yy Junaid, dukansu su sun zo an hadu ana ta masa sannu da zuwa su Yaya Auwal ma suna dawowa suka wuce bangaren nan hira ta barke har iyayensu suka dawo aka hadu aka zauna aka bude sabon shafin hira da naji shuru Abba bai shigoba nace duk yanda akai yana Sasan Iya na mike nasa hijab na fita Ilai kuwa duk sun Hallara, na shiga na gaishesu dukansu Na zauna kusada Iya.
Baba kalla yace "shugabar marasa kunyar gidan nan wannan wannan yarinyar shedaniyace bata da kiriki sam da kake ganinta nan Abba yai dariya have "Yaya ai kaida yar taka ne yar wajenka ce", yai sauri ya ce"aaaa kowa dana ne a Gidan nan banda wannan marajin maganar me kunnen kashi",
Iya ta ce "Sa'a kunnen kashi ai akwaishi kam,", Baba Kalla ya ce "ai salahu duk kai ka bata dama tayi duk abinda ta ga dama take raina mutane", Iya ta ce "aa shi bazai sata ba kam saidai ma ya hanata saidai ko uwarta", Baba Hadi ya ce "aa fa iya karki yanke hukunci baki sani ba kedai",
Naji raina na neman baci na mike tsalam na tsallake na fita a dakin ina shiga Mama ta ganni raina a Bace take tambayata me ya faru ban boye mata ba na kora mata jawabi bata cemin komai ba ta ce "naje kawai", ban jima da dawowa ba sai gasu duka sun dawo har Abba an gama hirar yazo ya zauna sannan ya kirani nazo na zauna can gefenshi kasan kafet ina addua A raina,
Ya ce "Yanzu Sa'adatu bakiji abinda nake fadamiki ko? Kinajin abinda su Baba suke fada nasan bazasu taba yimiki karya ba kinyi din ne ashe fadan da namiki kikace kinji ash karya kike ko?", Na ce "wallahi Abba nayi na rantse da kur'ani Abba naji maganar ka ni babu abinda nayi", ya ce "oh yayi miki karya kenan?", Na ce "aa Abba kayi hakuri", ya ce "kin manta ni ko? Kin manta halina ko?",. Na ce "aa Abba kayiwa Allah da Annabi kayi hakuri bazan sake ba", ya sake maimaitawa a fusace "kin manta halina ko Sa'adatu?", Na rude ina rokonsa sosai kan yayi hakuri kuka katatan nakeyi kaman wadda akama tsinannnen duka, Yaya Sani ya taso kaman zai mangareni na matsa gefe "bazaki bar barewa mutane wannan shegen bakin naki ba?", Abba ya girgiza kai yanayin kwafa "zamu hadu dake wallahi zaki bayani tashi ki bawa mutane wuri shashasha kawai", a guje na diba nai dakina..
'þ



*PAID BOOK 300 ONLY*
*SEND VIA THIS ACCOUNT=ØGÜ*

*SAFIYYA GARBA MUKHTAR*
*JAIZ BANK*
*0007688753*
*EVIDENCE OF PAYMENT HHERE=ØIÜ 09042684315 siyan na gari maida kudi gida*


*AUREN SADAKA BY SAFIYYA MUKHTAR GARBA*

#Share 'þ
#comment'þ
#EditingL'






*AUREN SADAKA 11&12*





*AS.Episod one.pg11&12*. *E*O*W

*09042684315*=ØÞÜ

=Ø…Ü*FC'- 'D5/B)*

*ALHAMDULILLAH=Ø
Þ SATI NA BIYU KENAN DA FARA AUREN SADAKA LAST WEEK MUNYI 5pgs naji Godiya and comments some many people said wai wannan salon daban ne ba kamar SA˜AR ZARE ba any way haka salon yazo don haka NVM kudai sha karatu kawai*,



Abba ya juyo da dubansa kansu "ni bansan me yake damun kan yarinyar nan ba sai kace wata mai Aljanu",?
Yaya Auwal ya ce "Wallahi Abba babu wasu Aljanu tsabar iskanci ne haka take ta addabi kowa da ka ganta nan Wallahi duk abinda suka fada a kanta gaskiyane tayi basuyi mata kari ba, yanzu Driver nan da ka canza mata in kaga irin rashin mutuncin da take karta masa Wallahi Kai kanka sai ka dau mummunan mataki a kanta wallahi Abba",
Duk sunyi jugum babu mai bakin magana Abba yayi tsaki ya tashi ya ya fita ransa a bace yai Sasansa Yaya Auwal ya ce "Mama kin gani ko? Kinga irinta ko? Kinga irin bala'in da yarinyar nan take so ta janyo mana ko? Kinji maganganun da aka dinga yi dazu a dakin Iya? Baba Hadi yai ta fada wai ke kike zugata itama ya zazzaga",
Mama ta ce "duk naji kuma banaso naji an sake tayarda wannan maganar don Allah zanje na mata magana shima Abban naku haka ku kwantar da hankalinku kar wannan abin ya daga muku hankali kunji yaran kirki", suka amsa da to sannan suka fita a falon sukai Sasansu,
Ina kwance naji knocking kofa na tambaya waye dukda nasan babu mai shigomin daki sai Mama ko kuma nayi bakuwa, ta ce Nice ta turo kofar ta shigo, na mike daga kwancen da nake ta zauna gefen gadon,
Tace "Sa'adah tashi ki zauna daidai zamuyi magana da ke" na gyara zamana dai dai ina fuskantar ta ta ce "Sa'adah abinda kikeyi daidai kenan? Kinfiso ki dinga batawa mahaifinki Rai yayinda shi yake fafutukar faranta miki naki ran da yanda zai yi ya rufa muku asiri?, Hakan daidai kenan Sa'adah? ",
Cikin sheshshekar kuka na ce "Haba Mama ya ake so nayi da raina? Ina ake so nasa raina yanzu kema kin yarda kin gaskata maganarsu? Wallahi Mama ni bansan me nayi ba mutane suka samin karan tsana komai nayi hantara komai nayi ban iya ba gashinan yanzu daga dawowar Abba an hadamin sharri an fada masa shikuma ya yarda da su har yana fishi dani, Mama don Allah ki taimakeni ki tayani bashi hakuri wallahi banida niyyar na bakanta muku ko daya Mamana", na karasa fada ina sheka kukan da jan zuciya,
Duk abu irin na Mama amma yau bata hauni da fada ba saima lallashina da tayi da bani hakuri da ban baki ta ce "kiyi hakuri Sa'adah wallahi abinda suke fada gaskiyane ke kin kasa ganewa ne kin kasa gane matsalarki balle ki tunanin gyarawa yanzu komai mutum yayi a wajenki bai iya ba ga shiga cikin maza shi ne Babbar matsalarki komai naki da maza kin maida maza kamar mata ni bantaba ganin kawarki mace ba inba Mamee ba itama don ta juri zama da halinki ne da tuni ta barki,
To matsalarki kenan Sa'adah shiga cikin Maza tun kina yarinya gwanda ma lokacin ance yarinta amma yanzu fa? Da girmanki da hankalinki kinkai munzalin girma kina yawo cikin maza kinga ai dole ai miki wani zargin wallahi dole a zargeki kinga ko me aka ce kinyi babu musu?",
Na fiddo ido ina kallonta "Allah Mama babu abinda nakeyi Allah Mama ki yarda dani", ta ce "aa aa dakata nifa bance kinyi wani abu ba bance ba nufina ki rage dai abinda kike kinji ya ta gari?", Na ce "to Mama in sha Allahu Mama zan daina kibawa Abba hakuri don Allah", ta ce "to naji zan bashi kiyi addua ki kwanta Allah ya bamu Alkairi ya tashemu Lafiya",
Nace "Amin", ta jamin kofa nai addua da fatan Allah ya kawomin mafita da sauki cikin lamurana ya yayemin kunnen kashin da ake cewa ina dashi don ni banganshi ba da yawo da mazan da nakeyi ni a ganina ba laifi bane wannan tunda frndship ne kawai tsakaninmu nai addua na shafa kamin na maida kai na kwanta.
Washe gari na tashi na shirya nai Shirin Tahfeez,ina zaune a falo ina karyawa Abba ya shigo na sake zubewa kasa na gaisheshi nai masa ya gajiyar hanya ya amsamin babu yabo Babu fallasa na karasa shanye shayin a gurguje na dau kur'anina da Azhkar da na ajiye hannun kujera nai musu sallama na wuce, yaukam har ya taso zai budemin get na dakatar dashi saboda nasan Abba na nan na bude kofa salin Alin na fice a gidan da naje yauma an kusa shiga aji sunata muraji'a yauma banyi haddar ba akazo kaina nace ban iyaba ya bugeni son ransa na karkade na koma wajen zamana bulunbukui kaman ba ni aka gama jida yanzu ba shadaya nayi aka buga bell na fito sai gida wai an harbi kare aka,
Haka rayuwa ta dinga juyawa da dadi babu dadi Abba tun yana fishin dani har ya huce ya sakko muka koma daidai muna shirinmu, fada kam ban fasashi ba indai mutum bai taboni ba don siyansa ma nake shiga cikin maza sai abinda ya ci uban nada don su nake dauka frnds dina da zuwa ball duk ban fasa ba saidai nayi a boye, mun fara jarabawa cikin ikon Allah Ademola tun yana nace min ina yakicewa har na fara sabawa da shi ya zamana komai dashi mukeyi tare zuwa tutorial muna karatu da shi sosai mun saba na saki ®[\~jiki da shi ya fara nunamin manufarsa akaina wato yana sona, tun ina ki da kaucewa amma da naci da komai sai da yasan yadda yayi ya janyo hankalina kansa muka fara soyayya da shi cikin lokaci kankani na fada kuma a haukana da nashi yana so ne muyi Aure, watarana muna zaune ni da shi yake cemin,
"Namesake dagaske fa nake wallahi inaso na Aureki ba iya soyayya nakeso mu tsaya ba inaso mu dore har Abada ni yanzu matsalata Dad dina anya zai bari na Aureki? Zai ma yimin Aure yanzu ina tunanin kamar nazo da abinda bazai yiwu ba amma nifa ruwa da iska bazasu hanani Aurenki ba wallahi",
Nayi murmurshi don ni dariya ba dabi'ata bane iyakacina murmurshi shima in ta kama, na ce "Ade kenan ka gama kawo duk dalilanka na cewa bazai yiwu ba yanzu kuma kazo kace zai yiwu abinkam da mamaki, nima bazan so rashin faruwar hakan ba saboda matsalarmu duk itace dai nima hakane a gida naje nai zancen Aure yanzu ai na taro match bani da players Yayyena ma kadai sun isheni bare aje ga Mama da Abba ai kashina ya bushe saidai wata Sa'ar ba ni ba amma, yanda zamuyi kawai mu bari mugama Exam mu shiga wata tukunna a danyi nisa sai mu gani zuwa nan da 3yers ko?",
Ya ce "good idea kin kawo shawara me kyau haka zaai ina so kafin wannan lokacin ki rikemun amana ta banda kula kowa kinji mylv",? Na ce "in sha Allah kaima ka rikemin Amana karka kula kowa ce mace", ya ce "angama ranki ya dade indai wannan ne bakida matsala inda wani ma ki karo inda wani", na ce "aa babu shikenan na gode zomuje na maidaki gida tunda nazo da mota",
Na waiwaya kallon parking space Habu Driver yana zaune saman mota yana jirana na juyo dubana gareshi "Ade ka barshi kawai kaga wannan munafikin Drivern nawa yana kallonmu kuma ni yake jira kar na bika yahadamin wani bom din a gida", ya ce "shikenan ba matsala bazanso ai miki fada ba muje na rakaki", muna tafiya ya rakoni har wajen mota ya budemin sit din baya na zauna yamin Addua sauka lpy da bye bye ya rufe motar Habu ya ja muka tafi ina daga masa hannu har muka bace , saida muka hau kwalta sannan murmushina ya bace na hade Rai ina duban bayan habu na kalla masa harara kamin naja dogon tsaki na maida hankalina kan Timetable dinmu ina lissafa Exam nawa mukayi saura nawa mu gama. Har muka isa gida hankalina yana kan papern saida muka shiga gida sannan na dago kaina na bude murfin motar na fice nai Sasanmu cikin sassarfa,
Na tarar da Mama tayi bakuwa na gaisheta na wuce dakina, na cire school back na yar hijab socks riga wando dankwali komai saida na cire ya rage dagani sai vest da gajeren wando na fada kan katifata ina sauke ajiyar zuciya,
Sai da na huta sosai sannan na mike na shiga toilet na watsa ruwa da daura Alwala na zo na tayar da sallah, ina idarwa kiran Ademola ya shigo na daga muka gaisa ya ce "kira na yi naji ya kika je gida gimbiya", na danyi murmurshi kaWan "Alhamdulillah nazo Lafiya dear kaifa?", Ya ce "kamar yadda kike, ina Mama kin sameta Lafiya?,"
"Na sameta kalau Alhamdulillah", ya ce, "to Masha Allah ace ina gaisheta", na ce "zata ji", muka Wan taSa hira kaWan kafin mukayi sallama, na mi™a na zura doguwar riga mara nauyi na sa hula na dau wayata na fita falo na tarar Abba ya shigo na fara tsumar jiki kamar mara gaskiya ko dayake itace, na zube na gaisheshi ya amsa sama sama suka cigaba da magana da Mama ya gama ya fita sannan na mi™a ina yiwa Mama sannu da gida ta amsa na bita kitchen muna kwaso kayan abinci muna ajewa a falo muka gama ta shiga dakinta zata watsa ruwa nikuma na zauna na zuba abincin a plate ciki na sa spoon na fara aikawa don nima ba laifi ba bayaba wajen ci shiyasa su yaya Auwal kullum gori ci kamar jaka Mama ta kan ce Lafiya ce, don basuyi ™arya ba ci kam akwaishi shiyasa har tumbi ke gareni tunda ina da yar kiba ba laifi,
Na zauna na share abincina tas ina ci ina chart har na cinye na matsar da plate din na janyo gorar ruwa na kafa kai ban dago ba sai da na shanye tas kamin na ajiye gorar, sai lemo shikuma gas ne Popcola nikam Lemo me gas bai dameni ba sam, nai gyatsa na dan kishingida bakina da tsinken sakace inayi wayata a hannuna ina Chart, naga Wif wuta ta Wauke can aka dawo da ita ashe ´an nefa ne sukayi tsiyar tasu aka tayar da Gen, na mi™e don naje na kwanta da wuri, ina shiga ko naji sallamar su sun dawo dukansu Mama ma lokacin ta fito kenan na ce ba ko zan koma ba na kwanta kan gadona ina jiyosu suna ta harkokinsu na mi™e na zauna don kila nasan sunzo da balangu, ina ko zama Mama ta fara saitomin kira na zo na karbi rabona na zumbur na mi™e na fita Yaya Sani ya harareni "munafuka ™walamammiya dama shi take jira",
Na Wan zumSura baki don maganar ta sosamin rai kuma da inada zuciya da na daina karSar abun hannunsu na ja gefe na rakuSa Yaya Salis ya ce "Lallai kin ri™a har mu kike ma rashin kunyar kenan?abin naki ya tsallake kan ´an waje ya dawo kanmu kenan? To bazata yi miki kyau ba wallahi don Ubanki zakici shegiya baki kamar na sheda", suka ™aremin zagi, Yaya Auwal kam bai samana baki ba waya yakeyi ™asa ™asa nasan da har da shi, Mama ta ce "kunga ku bata abinda zaku bata ta wuce duk abinda akai mata ita taja", ta mi™omin balangun da Ayaba da Lemon Sawo na karSa sum sum na wuce Wakina ina shiga na fara ja musu Allah ya isa na zauna na ci namana kusan yanka shida aka bani ba laifi wannan karan da Wan mutunci, ban sha lemon da Ayabar ba na kuskure bakina na kashe wayata na kashe globe na kunna dum light na kwanta da jawo bargo nai addu'a na shafa na kwanta Asuba ta gari...
'þ


*PAID BOOK 300 ONLY*
*SEND VIA THIS ACCOUNT=ØGÜ*

*SAFIYYA GARBA MUKHTAR*
*JAIZ BANK*
*0007688753*
*EVIDENCE OF PAYMENT HHERE=ØIÜ 09042684315 siyan na gari maida kudi gida*


*AUREN SADAKA BY SAFIYYA MUKHTAR GARBA*

#Share 'þ
#comment'þ
#EditingL'








*AUREN SADAKA 13&14*





*AS.Episod one.pg13&14*. *E*O*W

*09042684315*=ØÞÜ

=Ø…Ü*FC'- 'D5/B)*




*ALHAMDULILLAH=Ø
Þ SATI NA BIYU KENAN DA FARA AUREN SADAKA LAST WEEK MUNYI 5pgs naji Godiya and comments some many people said wai wannan salon daban ne ba kamar SA˜AR ZARE ba any way haka salon yazo don haka NVM kudai sha karatu kawai*,




Kwana biyu na shiga busy saboda jarabawarmu don ko Ball ma bana zuwa in Yaya Deen yayi min tayi nakance bazani ba saboda karatu nakeyi babu ™a™™autawa don jarabawar mu ba bu sau™i da yake privet ce komai tsanani haka zaka dage inkaci falillahil hamd in baka ci ba ka kuka da kanka don bazaka kuka da su ba saboda sun baka enough time da zakayi karatu, don haka bani da sakat wayata ma na kulleta na ajiye komai na na ajiye kafin mu gama jarabawa,
Ade yana taimaka min sosai da extra lesson da tutorial na past question papers muna yi tare da shi sosai kuma yanamin yadda zan gane in naje gida na sake maimaitawa har na iya cikin ikon Allah kuma in nazo sai naga ina ta rubutawa ba laifi nayi ™o™ari, har muka kammala akai hutu kowa ya zauna zaman jiran result,
Rayuwata ta dawo kamar da na dawo warkajamina da walwalata yadda nake da gashi dama anata shirye shiryen Match kuma harda ´an ™ungiyar mu mune ma kan gaba Yaya Deen yake faWamin an kusa yanzu dai anata atisaye nai murna sosai saboda ina free sai islamiyya itakam asha ruwan tsuntsaye nake mata in naga dama naje in banyi niyya ba na tafi gantalina rai na fes,
Yauma farkon sati ne na komawa islamiyyar don haka yau ina ta shirye shiryen tafiya Ball nayiwa Yaya Deen waya kan cewa ya jirani, fitowa ta kenan daga wanka lokacin ™arfe Waya da Rabi na Rana tarar da ba™uwa zaune,
Mami ce na kalleta da mamaki "kekuma daga ina?", Ta ce "daga gidana mana", na ce "shine kuma zuwan bazata ko waya babu?", Ta ce "ke nima ba niyyar zuwa nai ba gidan mu zani shi ne nace bara na biyo na gaisheda Mama", na ce "Oh nagane ba ma wajena kikazo ba ga hanya nan sai ki juya", ta ce "Au Ade yaushe kika zama mara mutunci ban sani ba? Banida labari? Korata ma kikeyi? Ba komai dama ni na kawo kaina ba kuma zaki sake ganina ba", ta mi™e zata Wau jaka na maza na ri™eta na mayar zaune, ina cewa
"Haba tawan ta gaban goshin nawa ke bakisan wasa ba? Da wasa nake miki fa sorry kinji Habibaty zauna daina Satamin ranki", haka muke da ita ina mata abu da wasa saurin zuciya yanzu sai ta ce zatayi fushi nikam ta kasa gane halina haka yake wani lokacin badai tsokana ba, da ™yar na lallaSata ta zauna na kawomata drinks muka Wanyi hira ta ce zata wuce na zata ™arasa gidansu muka fito Mama taita samata Albarka don tana son Mami ganin ita kaWaice ™awata da muke tare da ita, na rakata har haraba mukai sallama ta wuce na dawo ciki.
Na shirya na saka kayana JC kalar skyblue masu kyau da taushi na kamfanin ADIDAS da yake ba sallah zanyi ba ina period na maida dogon hijabi na na makaranta a kai nasa Eye Glass Wina yau na tuna da shi don ba kasafai na fiya sashi ba na Wau school bag da Pcap na fita falo lokacin huWu saura uku da rabi ma ta wuce, inayiwa Mama sallama Abba ya shigo na du™a na gaisheshi ya ce "Makarantar ce da wuri haka? Na ce "Eh", ya ce "to Allah ya kiyaye a kula", na amsa ina Allah Allah na fice kar a sake jsnyomin wani ruwan, cikin ikon Allah kuwa bankai ga buWe ™ofar falon ba ya kwaWamin kira "Sa'a! Sa'a? Zo zo...", Na juyo raina a dagule gabana yana Wan faWuwa nasan wannan kiran ba na lafiya bane, na ™araso gabansa naWan rissina, "Abba gani", ya juyo "yawwa ina..¿ ina...", Bai maganar tasa ba aka kirashi a waya ya Waga yana cemin naje kawai sai na dawo, nai maza na sulale na fice na tarar Yaya Deen yana fitowa da mashin daga Sasansu shima yana sanye da uniform ya fita get na bishi a baya Habu ya taso da sauri,
"Hajiya za'a kaiki makaranta ne?", Na waigo ina kallonshi a ™ufule na ce "a'a masallaci zaka kaini ba makaranta ba, na ce maka masallaci zaka kaini", na faWa a tsawace, ya ce "Allah ya huci zuciyarki ba ni bane Alhaji Ne yace dama a dinga kaiki har islamiyya in zakje dawowar nan tasa ya faWa haka", na ce "to bazanje ba bazani da kaiba, wai kai wawan inane ko ina sai ka birni?", Cemaka akayi ko ina sai naje dakai? Da ya faWa maka haka sai kace a'a to wallahi ko nan da ™ofar gida bazaka bini ba aikin banza kawai mutum saikace maye, ko dayake wayasani abu a duhu", na faWa na wuce fiiiii na barshi a tsaye jin yaya Deen yana dannamin horn na dare kan machine Win muka wuce ko hijab Winma ban tsaya cirewa ba muna zuwa anata shirye shirye na ga wannan karon harda wata mace amma Christian ce da ita a cikin wanda zaai gasar karfe huWu aka fara buga wasa wannan karon ban shiga ba saboda indai ina period bana son guje gujen nan gwanda najini waje Waya iyakacina dai an bani tsaron raga Wasa yayi daWi sosai aka gama muka tashi kowa yai nasa waje muma muka yo gida.
Abba ya kirani yanamin zancen makaranta wai wacce nakeso Northwest ko BUK nace nafison Bayero ya ce "to ba matsala", da har zanyi masa tayin Oxford saikuma naga ba fuska in ba kuma sonake naci tsinanen duka ba don tsaf zai iya ko yasa su Yaya sani su daken dama su ´an jiran ™iris, muka bar zancen a haka dama an fara Registration Jamb yasa Yaya Auwal akan komai shi zaimin muka je dashi akayi Registration aka bani Novel Win da something abubuwa dai sannan muka dawo gida ansa ranar da zamuyi exam Win.
Na dage da karatu saboda banaso ace na faWi cikin ikon Allah kam na samu marking da ake so na samu kuma zasu bani duk course Win da nakeso nazaSa Business Adminstration saboda inaso na zama kamar Abba kasuwanci kuWi ko ta ina.
Shima Ademola tunda yaji bazanje Oxford ba shima ya jingine a cewarsa bazai tafi ya barni ni kaWai ba sai kace da mu biyu muke shima yayi Jamb kuma yasamu marking da akeso a Bayero ya zaSa irin course Wina komai dai namu Waya alhalin ba shine burinsa ba a da amma ya canza ra'ayinsa saboda Ni.
An kammala komai da komai har sun bani admition komai yayi kyau na zama sabuwar Waliba ´ar jami'a Abba ya canza min waya Sumsung mai kyau da Laptop Dell itama me kyau ya ce saboda karatu nai godiya sosai har Mama ta tayani ya ce wannan ba komai bane kaWan kenan daga cikin gatan da zai nunamin shidai burinsa bai wuce na daina halina na rashin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment