Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalonshi ga fenΓͺtre (taga) halau ita ce bakin taga ba shi sai salon, ya iske Lya na karatu.

*Grand frère (yaya) lafiya ?"

"Ina lafiya,wata mata can waje cikin doguwar riga bak'a"


"Bari mu gani"

"Kar kisaki ki fita kindaiji abinda na gatamiki"

"Toh"

Can sia ya sake kai duban shi ga taga baiga komai ba, sai ya sauke wani gwauran lunfashi suka ci gaba da hira sama sama.
Can sai suka ji cikin kitchen kwandon kashiyai ya fad'i duk sun zube, "kina jin abin nake ji kuwa?"

Lya ido duk sun cika da hawaye tace "yaya gaji ko sun fara wayo Allah !!!"
Sai ga wutar salon(falo) ta d'auke yayi yayi ta kunu taki kunnuwa, can kuma kitchen abubuwan sai k'aruwa suke, banci koshiyai yanzu ga assiette (tagaran)na cin abin ci ake fasawa, abu yaki k'arewa,can dai ya samu k'arfin gwiwa yaje kitchen koda yakai hanun shi zai tab'a k'ofar sai komai ya tsaya tchak, ya bud'e k'ofar ya shiga babu alamu wani abu ya faru a kitchen d'in, a lokacin ne ya gane eh lale akwai abinda ke faruwa a gidan nan, yakai hanun a kashe wutar kitchen ta kashe kanta ya jante hanun ta kuna kuma m, ai ba shiri ya arta da gudu kafin ya kai kofar kitchen d'in ta rufe kanta yayi yayi taki bud'ewa, daga bayan shi yaji motsin kwano koda ya juya sai tukane da kwanoni da cup suke fad'owa suna fashewa, sai ya fara ihuuuuuuuuu a bashi agaji kamar wani karamin yaro, rufe fuska yayi yana rufewa kamai ya tsaya, ya bude idon shi, k'ofar kitchen ta bude kanta,ya fito yaji kukan mage (chat 🐈) bayan shi koda ya juya wannan matar doguwa mai riga bak'a, da gudu sai dakin barcin shi tareda k'anwar shi.

Lya sai kuka take, yace" ui shuru k'anwa ta zan kare ki babu abinda zai cutar da ke".
Bindiga ya d'auka ya haka ta yana jiran ko ta kwana.

Suna nan lab'e cikin dan lungu yana ta kalon kowane lungu na d'akin yaga ta ina abin zai b'ulo, can idon shi ya kai wani hoton mahaifin su, yaga hawaye na zuba a idon mahaifin nasu amma a cikin hoton dake bangon dakin, yace wa Lya ta diba,koda itama ta juyo taga mahaifin su na kuka harda share hawaye sannan ya d'ago masu hanuπŸ™‹πŸ½β€β™‚οΈ hiii sai kuma yayi dariya ya kashe ido dayaπŸ˜‰, ai da gudu dan sun tsorata ainun har basu son zama a gidan sai suka d'unguma zasu fira amma su kayi su kayi k'ofar taki bud'ewa yasa clΓ© amman ta kiya, can suna nan tsaye suke jin tafiya mutu na tukaro su daga cikin d'aki, duk sun firfito da idanuwa waje😳😳 suna juyowa mi zasu gani ☠️kwarangwal na mutum yana tunkaro su Lya koda taga wanan squelette sai suma tayi, shi kuma yana ta harbin ta amma a banza harbin iska ne nake har saida alburshi (cartouche) ya k'are,koda kwarangwal ta kawo daidai samman kansu, soja an saduda rufe ido yayi yana jiran abinda zai faru dashi.....
Can sai yajin ana buga k'ofar d'akin kamar za'a b'alata, David ne koda ya bud'e "mi ke damun ka ne cikin gida nan bazaku barci na huta ba?"
Soja ya bud'e baki....amman ya kasa magana.

"Bakada harshene komiye kayi magana mana"

Sai ga soja a some yabi sahun k'anwar shi......





(To na gode da adou'oinku naji sauki Alhamdulillah, mu had'u gobe insha Allah a GODIYAR SU CE🌺)






*Domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar+22792494512 na gode*πŸ˜‡πŸ˜‡






*PRINCESSE CE*πŸ‘ΈπŸ»βœπŸΌ
24/07/2020 Γ  12:53 - πŸ‘ΈπŸ»PrincesseπŸ‘ΈπŸ»: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*πŸ‡³πŸ‡ͺ
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



4️⃣0️⃣β†ͺ️4️⃣5️⃣



Bayan duk wannnan abubuwan da suka faru da Soja tare da k'anwar shi Lya'atou, harbin bindiga ya tada mu muka d'unguma sai k'ofar d'akin su, ni da NaΓ―ma muna tsaye kansu, soja ya fara farkawa yale tambayar "mike faruwa ne?"

Nace "kai zaka gaya mana dan a haka muka isko ka kaida Lya"

Soja ya d'aga kai "ohhh daren jiya" ya fara kale kale kamar yana neman wani abu.

NaΓ―ma tace "mi ya faru daren jiya ne?"

Nan dai mutunan ku ya fara ratatowa duk abubuwan da suka faru daren jiya, muna so muyi dariya amma ba halin yi.

NaΓ―ma tace et"abun mamaki yanzu ka yarda da abinda k'anwar kantake gayama ko?"


Soja yace "eh na yarda gaskiya, tana ina ma ban ganta ba?"


Nace mashi "kwantar da hankalin ka tana dakin kwance"

Wannan karon mu duka mun yarda akan wannan gidan akwai abinda ke faru cikin shi bale gashi bamuda nisa da cimetière (mak'abarta).

Muna cikin rautaunawa nace "yzt kamata muje muga mai gidan domin sanar da shi abinda ke faruwa kar wani abu ya faru yace ba'a sanar da shi ba, sabida tin zuwan wannan mak'ociyar bamu samu salama ba amman da can lafiya muke"


Soja yace "wace mak'ociya kennan?"


NaΓ―ma tace "kudai dan irin maganar da zaku ringa fad'i (les murs on des oreilles, dan katanku suna da kunnuwaπŸ‘‚πŸΌ)"

"Badan naga mutuwa ta da idanu na a daren jiya ba wallahi bazan gazgata abinda kike fad'a ba, to mizai hana muje mu same shi domin sanar dashi" cewar soja.


Muka d'unguma zuwa d'akin David mun isko yana shirin fita wajan sana'ar tashi ta sa ido k'ofar gida, yace "Allah yasa kud'in haya ne kuka zomin dashi, kai soja daren jiya kayi Harbin katangu na yanzu kuma mi zaka harba ko ni?"


NaΓ―ma tace "a'a munzo ne mu maku magana"

"Magana akan mi kennan?"


Soja "mu Shiga daga ciki dan bai kamata muyi maganar a waje ba"


Mun shiga daga ciki d'aya bayan d'aya kowannen mu ya fad'in abinda ya faru dashi.


David "to duk naji abubuwan da kuka fad'a yanzu kuna nufin ita Fouraiha Aljana ce?"


Nace "ko alama babu wanda ya furta hakan, saidai akwai alamar tambaya a cikin tin bayan zuwan ta ba abubuwa ke faruwa kennan kawai kuma kuyi tunani da hankalin ku"


David "duk da ban tab'a samun korafi daga gareku ba shekaru un kuna zaune lafiya kuma ina sa ran ya zama k'orafi k'arshe"

NaΓ―ma tace"kuyi duba da idon basira"


David "kuje kawai zuwa dare k'arfe takwass akwai had'uwa annan gida na kuma halarta kowa ya zama wajibi dan asan abin yi"


Kowa yayi na'am da wannan maganar don shi mai ba kowa hakin shi ne indai wajen magana ne to ko fito ka kare kanka. Kowa ya watse ana jira dare yayi, (ni kuma nace da kunsan abinda ke jiran ku a daren da bakuyi zumud'in yazo ba).


Wajajen uku da rabi na marece David na k'ofar gida,aka sauke Fouraiha a mota nan ya tsayar da ita sun gaisa take tambayar shi ko lafiya, yace "idan na gaya miki to kinsan cewa ba lafiya"

"Go ka isko ni gida zuwa hud'u et sai muyi magana"

"To sai nazo"
David yana d'aya daga cikin mutanen da idan suka samu labari to sai sun kaishi dan bai iya bakin shi ba.


Hudu dadai yana k'ofar gidan Fouraiha.
"Toc toc toc...."


Shigo a bude take aka amsa mashi.
Bayan ya shigo daga can cikin kitchen ta ke ce mashi ya nemi wuri ya zauna gata nan, nan nima na k'arewa d'akin kolo daidai gwargwado tanada tsafta ga anyi dΓ©corΓ© (dΓ©coration) d'akin duk ja ne da bakin ya bada kala sosai.

Sai gata ta fito suka k'ara gaisawa ta aje mashi tiren abun gaban shi, abinka ga tuzuru rabin da ya ci abinci irin haka har ya manta, nan kuma ta juya ta kawo mashi lemo da dai kayan tab'awa, tace nansan la da giya Bari na kawo maka tsoho yaji kaya nanfa ya et fara fitar da hakora waje, ta zuba mashi abinci shima itama ta zuba suna ci suna fira sama sama can tace "bari na kuna maka tΓ©lΓ© (telenbijin) lokacin kwalo yayi"

Can saida ya saki jiki dan har ya manta abinda ya kawo shi, sannan tace "tsoho mafanar miye zamuyi?"

"Kin tunamin dan har na manta wallahi, to wad'ancan mak'otan naki ne suke k'orafi wai ana basu tsoro ana hanasu barci tin bayan zuwan ki gidan nan ko kema ana baki tsoron ?"


"Tsoro kuma ni a'a, kamar miye kennan ?"et
Nandai ya bud'e baki ya sanarda ita ce abubuwan da muka sanar dashi.

Tace "to Kai mi kake gani yace ai matsala ce kawai k'arfe takwass a zauna a magan ce matsalar"

Sanye take cikin wata yololuwar riga, ta mik'e tace "Allah ya kaimu dare lafiya, amma nidai babu wata matsala dana ke fama da ita sai ta tsagewar gini d'aki na, ko zaka duba domin samo mai gyara?"


Ya mik'e ya bita zuwa dak'in ta ta nuna mashi yana cikin dubawa koda yake juyowa ya isko ta sitir ta tub'e, ya kasa magana, ta bashi zuwa gado, yana kiciniyar kwatar kanshi tace kaleni ya d'ago ya kaleta sai wani haske ya fito daga idon ta zuwa nashi tace ya bud'e baki ya bud'e wani maciji ya fita daga bakin ta zuwa nashi tace ya had'e, koda ya had'e sai barci, kamar wani karamin yaro..........






(To nima bari na ware kafin David ya farka muka yanda zata kaya)






*(Ina bara adou'oinkuπŸ™πŸΌπŸ€²πŸ»)*


_domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar +22792494512 na godeπŸ˜‡πŸ˜‡_









*PRINCESSE CE*πŸ‘ΈπŸ»βœπŸΌ
24/07/2020 Γ  12:54 - πŸ‘ΈπŸ»PrincesseπŸ‘ΈπŸ»: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER WRITER'S ASSOCIATION*πŸ‡³πŸ‡ͺ
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



4️⃣5️⃣β†ͺ️5️⃣0️⃣





Bayan ya had'iye maciji nan ya b'ingire sai barci.
Fouraiha ta kewaye gadon da David yake kwance da wani farin abu, tayi zaune ta lankwashe k'ahuwan sannan ta zura hanun ta karkashin gadon ta fito da wani gwangwani ja ayi mashi ❌❌ a jikin gwangwani,ta fitar da wata kwalba katuwa daga ciki tare da wani litafi, ta fara karanta wani tare wanda ko ni ban gane abinda take nufi ba, can sai na hagin kurwa shi David ta fito, Fouraiha tace "zo, zo gareni ka zama nawa ni d'aya" sannan ta saka kurwar a cikin wannan kwalbar t rufe ruf ta maida komai mahalin shi sannan ta tashe da David.

"Ina nake nan?"

"Gidan mu ne, mike maka ciwo yanzu?"

"Kaina ke ciwo"

"Zai dena, sannan duk abinda nace shi zakayi babu musu"

"To masoyiya ta"

(Ikon AllahπŸ€”πŸ˜…πŸ˜‚πŸ€£ 🀐)


"To je la shirya ma rΓ©union (taton mu na dare"

"To ma chΓ©rie"

Ya fito daga cikin d'akin ta tuna dazu bai gama cin abincin nan nashi ba, "to ina kuma sauran abincin nan yake?"

"Bakai babu tambaya sai abinda nace zaka yi ok?"

"To masoyiya na gane"

David ya koma kamar karamin yaron duk sai abinda tace yake yi kama rakumi da akala.(na tausaya maka David).




Bayan lokaci yayi duk mun had'u a gidan David cikin falon, "barkan ku da zuwa duk na gaisheku, mun had'u a wannan wuri ne domin magance wata 'yar matsalar da ta adabin wasu daga cikin mu, domin fida zargi a zukatan ku, kamin mukai ga farawa inason na gabatar maku da masoyiya ta, sannan daga yau itace patronne (shugaban ku yanzu ma'ana ita zata ringa kula da gidan nan).


Duk munyi murna ganin shima d'an tsoho ya samu wata.


Wa zamu gani ta fito daga cikin d'akin David wai Fouraiha!!!😳😳😳😳
Ta fito tana rangwad'a tana karkad'a kugu da wasu tsinanin kaya a jikin ta.
Kowa yayi mutuwar zaune babu mai magana.

Fouraiha tace " nasan duk kunyi mamaki da ganinan a nan to daga yau nice mai gidan nan, kuna so ko baku so kuma zan buga sandar iko na babu wanda ya isa ya ja dani, dan haka ku b'ace min da gani banason ganin ku"

NaΓ―ma tace"mi? Kutmelesi"

"Eh kinji sarai abinda nace ina son ganawa da mijin na"


Sumi sumi kowa zuciya ba dad'i muka tashi zamu fita mun kai k'ofa mukaji tana cewa "dani kuke zancan, sai kun yabawa aya zak'in ta dan na lahira sai yafi ku jin dad'i, sai kunyi nadamar zuwan ku duniya"


Munji tsoro kowa ya kama gaban shi domin ko Fouraiha ta nuna mamu ita d'in hatsabibiya ce, rai babu dad'i kowa ya shiga gida, kuma zaman jiran tsamanin abinda zata aikatawa, mun sakankance amman duk yanda muke tunanin ta ta wuce haka, dan yanzu ne za'a fara wasan.





(Gaskiya kunga ta kanku, dan yanzu ne Fouraiha zata d'and'anna maku azaba sai kunkai kuna gudu da k'ahuwan ku, na tausaya maku)



*Tofah fans yanzu ne za'a fara wasan ku ciga da bibiya ta domin jin ya zata k'aya*









*Domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar +22792494512 na gode*πŸ˜‡πŸ˜‡







*PRINCESSE CE πŸ‘ΈπŸ»βœπŸΌπŸ‡³πŸ‡ͺ*
24/07/2020 Γ  12:54 - πŸ‘ΈπŸ»PrincesseπŸ‘ΈπŸ»: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*πŸ‡³πŸ‡ͺ
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼




5️⃣0️⃣β†ͺ️5️⃣5️⃣



Bayan rΓ©union (taro) da mu kayi kowa da abinda yake sak'awa a zuciyar shi.


Nace "kuna dai gani sa idon ku"

NaΓ―ma tace "gaskiya ya kamata muyi mai fida mu"

Soja "gaskiyar magana kennan, kuma ta nuna mana mungun halin ta"


"To yanzu dai kowa yayi hankali a lura sosai"


Bari mu koma wajan masoya.

Fouraiha tace ma David "ka ajemin kud'in haya zanzo na k'arb'a"
"To sai kinzo ai naki ne"
"Kuma ya kamata a k'ara kud'in haya"
"K'ari kuma? Gaskiya tinda na gina wannan gidan suke cikin ba dad'i idan anyi k'ari"
"Abinda nace shi za'ayi"
"To gimbiya "
"Idan sukaji basu iya zama su kama gaban su a sa wasu sabi"
Fouraiha ta maida David karen ta sai yanda tayi dashi.




Fouraiha ce tsaye tsak'ar gidan sanye da doguwar riga ja, tana hak'a rame tana wasu irin sabatu cikin naji tana cewa duk 'yan gida da abinda ke cikin gidan ya zama nawa malaki na sai yanda nayi da su tana dama wata gumba a cikin wata katuwar tukunya sannan naga ta fito da kwai guda shida ta zo k'ofar gida na ta aza wani sannan ta shata layi da wani jan abu tana magana"Laila daga yau sai yanda nayi daku a cikin gidan nan bazaku zama wani abu ba har abada da keda iyalin ki" sannan ta fasa wani kwai sai dukan abubuwan suka b'ace, sannan ta dawo wajen tukunyar nan ta jefa kwai d'aya saida wani jan hayaki ya fito, sannan ta koma k'ofar d'akin NaΓ―ma yanda tayi a nawa haka tayi ta k'ara da cewa yaran ta sai sun zama manyan b'arayi k'arshe su mutu ga hannu police ('yan sanda), sannan ta koma k'ofar d'akin soja da kai da k'anwar ka rayuwar baza tayi kyau ba kai sai ka zama mai biyan matan banza kud'in ka duk acan zasu k'are, ita kuma Lya'atou karuwan ci et zata sa gaba k'arshe kuyi hatsarin mota ku mutu, ta dawo wajen tukunyar nan koda ta zuba wani abu sai ta b'ace batt, lokacin da take k'okarin juyawa can ta hangi kurwar d'aya daga cikin d'iyan NaΓ―ma yana kalon ta, koda ta juyo sai ya gudu zuwa gidan su daman NaΓ―ma tana k'okarin ta tinda abin nan ya faru take rufe gida ko k'aramar huda bata Bari bale wani abu ya samu damar shiga, can na hangi Fouraiha ta rikid'e ta koma kusu πŸ€ "ni zan yarda ka gan sirin na kuma n'a kyaleka ka kwana lafiya?" Tana gama rikid'eAwa tabi ta sama cikin lunguna ta shiga gidan NaΓ―ma.


Tana shiga d'akin yaran NaΓ―ma tayi suna barci harda wanda ya gama gulmar lek'enta ta fara cin faratan su ('yan yatsun su) suka fara ihu da neman agaji cikan kwana NaΓ―ma taji kukan d'iyan ta da gudu ta shigo d'akin koda ta kuna wutar d'akin can gefe ta hangi wata katuwar kusanya tana ci fartayen da ta diba n'a d'iyan ta ga hakoran ta zaro zaro sunfi na mutun, da gudu ta tafi kitchen d'auko tab'arya domin bugawa wannan kunsanya amman lokacin da zata buga mata kawai sai ta rikid'e ta koma mutun katuwa da jar riga har k'asa, ai ko yaran suna ganin haka sai ihuuu can sai ita Fouraiha ta bude bakin ta Wani hayaki ya fito duk sai suka zuba sai barci, har ita NaΓ―ma wannan d'an barci wai tayi mafarkin wai wata tsohuwa ta d'aure ta sannan tazo ta mata kashi a fuska bayan haka wacan matar mai doguwar riga taje neman wuka domin a yanka ita NaΓ―ma ai da gudu Allah ya bata wani karfi ta kubce tana ta gudu sai ga wannan matar da tsohuwa suna biyan ta a bayan ta gaji iyakar gajiya sai ta fad'in tana kuka tana cewa "ku kashe ni bazan iya tsira ba shikenan" sai wacan matar mai wuka a tazo zata caka mata sai wufff ta farka tana zufa sai gasu kwance itada yaran sanan tace "Kai mafarki akwai firgitar wa wallahi"
Ta cicib'i yaran ta suka koma d'akin ta duk ta rungume kayan ta sai ta fad'a tunani tana kalon sili (plafon) sai ga wani jini yana rubutu da kanshi *BA ZAKI TSIRA BA SAI NA KASHE KI, MUTUWA ZAKIYI....* Ai NaΓ―ma da ta ari na kare yanran ma baya ta barsu suna ihu da neman agaji sai gasu a kofar gida na........





*(Wai na gaji wallahi kaina ciwo,domin jin ya da zata kaya ku ci gaba da bina)*



_sai naga comment da yakai 50 ko hiya da haka zan cigaba da typing ko n'a mayar dashi na kud'i tinda baku son comment_





*Shawara a tintub'eni a wannan lambar +22792494512 n'a godeπŸ˜‡πŸ˜‡πŸ˜‡*








*PRINCESSE CE*βœπŸΌπŸ‘ΈπŸ»πŸ‡³πŸ‡ͺ
24/07/2020 Γ  12:55 - πŸ‘ΈπŸ»PrincesseπŸ‘ΈπŸ»: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*πŸ‡³πŸ‡ͺ
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



5️⃣5️⃣β†ͺ️6️⃣0️⃣



Sai ga NaΓ―ma a k'ofar gida na ta bubugamin k'ofa da k'arfi, "Laila dan Allah ki bud'e k'ofar nan wayo Allah mun shiga uku" cikin barci naji ihu NaΓ―ma na tashi zaune tareda mai gida na mu bud'e k'ofar sai gata tsaye duk a firgice a tsorace tana kuka ga majina a hanci, nake tambayar ta ko lafiya yaran kuma Mike faruwa ne wai???
"Kashe mu zata yi yara na ta ilatamin su" ta fashe da matsananci kuka taban tausayi wallahi.
Muka d'unguma da miji na zuwa gidan ta domin dubo mi ya samu yaran nata, abinda na gani yafi k'arfin tinani na, yaran kwance sun kasa tashi kafafuwan su duk jini babu farce ko d'aya wani kuma harda dindinge abin babu kyai gani sai kuka nake tunanin nayi idan nice aka yiwa yara na haka ko yazan yi? Gaskiya wannan matar ta cika maras imani, mu d'auke su mun kaisu gidan mu da taimakon oga na muka musu bandeji kafin safe mu kaisu asibiti, wannan daren ban runtsa ba ina zaune ina jinya su kar wani abu ya same su hata yara na ma, wajajen biyar da asuba na shiga douche (batroom) don inyi wanka da alwala ina wanke fuska ta na daga kaina don kalon madubi ai abinda ya ban tsoro saida nayi fitsari a wando (maganin masu kalon madubi cikin dare kennan😜) wani mutun tsaye ya rufe fuskar shi da wata jar hula ga wuka a hanun shi ya saita wuya, ai da gudu na baro batroom na fito ina haki, "miye kuma?" oga ke tambaya ta wani mutum na gani a kewaye nake sanar da shi, "babu kowa a gidan nan fah kinsani sai mak'ociyar mu da yaran ta, "wallahi ba wasa nake ba",ina karkarwa ina kuka duk na firgice "to muje mu gani" muka d'unguma zuwa makewaya muna shiga kuma ba kowa muka duba bayan k'ofa babu, yace "kin gaji ne wallahi muje ki kwanta zan kula da ke matata" mun juya don fita daga batroom kennan muka ji madubi makewaya ya fashe, kafin mu tantance abinda ke faruwa sai mukaji iska mai karfi ta bud'e tagar batroom d'in, muna cikin wannan hali kuma mugaji k'ofar falon tana "crac crac " kamar anason bud'eta da k'arfin tsiya muka ruho muna zuwa ta bud'e wannan mutumin da nagani a madubi tsaye da wuka a hanun shi ba shiri muka bud'e baki sai ihuuuuuuuuu har mai gida na sai mutum ya b'ace b'at.... Gidan nan muna ganin azaba gaskiyar Fouraiha da tace na lahira sai yafi mu jin dad'i.
Oga na kamar wani zarare, yana sambatu. Allah dai ya kyauta.



Mai gida na yayi fushi matuka don cewa yayi idan yak'i take so a Shiga ro bismillah wannan cin zalin yayi yawa, "Allah ya kaimu safe lafiya sai na nuna mata ..."yayi kyaici .

A b'angare na nayi nayi in nuna mashi illar abinda yake son aikatawa amman yaki saurare na dan ina guje mashi nadama marar anfani, fad'an da yafi k'arfin ka maida shi wasa.




Nayi tagumi ina tunani "Fouraiha, Fouraiha mi muka aikata maki mai muni haka ?mi mukayi da zaki cutar da mu?miyasa ????




Domin jin amso shin wannan tambayoyin kuci gaba da bibiya ta.





Na kusa mayar dashi na kud'i tinda abun haka ne.πŸ˜’







(Wasu sun fara k'orafin akan wai mi yasa basa adou'a to ai sai idan adini ya zauna wa mutum zaman bariki fah,hummm baku iyacin albasa sautu ba,bamu fara komai ba cikin labari yanzu ne zamu fara shi tinda mijin Laila ya fusata)







(An b'atamin rai shiyasa kuka jini shuru sai na huce yanzu ma kad'an nayi sai monday insha Allah,kuma wasu na k'orafin bana maida comment to wallahi sai idan ban lura da shi ba, masu bina prvt sune shaida ina amsa masu idan sukace suna son book daga farko zan tura idan akwai wanda yamin magana ban gani ba to yayi hankuri jiki da jini, aiko ne yamin yawa ga office ga gida ga typing har biyu yazan yi a ringa uziri)







*+22792494512 domin gyara ko shawara na gode*









*PRINCESSE CE*πŸ‘ΈπŸ»
πŸ‡³πŸ‡ͺβœπŸΌβœπŸΌπŸ‡³πŸ‡ͺ
24/07/2020 Γ  12:55 - πŸ‘ΈπŸ»PrincesseπŸ‘ΈπŸ»: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
πŸ‘ΈπŸ» _PRINCESSE_πŸ‘ΈπŸ»





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*




_ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah ya bar kauna_









πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*πŸ‡³πŸ‡ͺ
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



6️⃣5️⃣β†ͺ️7️⃣0️⃣




Bayan wannan abun da ya faru miji na yayi fushi mai tsanani bar yana cewa "wannan k'aramar yarinya ta adabe mu haka ta zama mana anoba, to ba zata sab'u ba wai bindiga a ruwa, gwara ayita ta k'are kowa ya huta"
Laila tace "Allah ya huci zuciyar ka mai gida, amma nidai a tunanin na abi abun a sannu"
Bayan safiya tayi nake tambayar NaΓ―ma "wai mi ya faru daren jiya ne ?"
Kuka take ba na wasa ba dan gaskiya na lalashe nace ta sanar dani abinda ya faru.
Tana gayamin tana kuka, bayan ta gama d'anta shima yake gaya mana abinda ya gani kuma yaji.
Miji na yayi mamaki abinda yaron ya fad'a saΓ― yace "abin fa muna tunanin k'arami ne ashe ya girmi tunanin mu"
Nace "mai gida kayi shuru bana son kana d'aukar abin da zafi haka mu fito mata ta bayan fage kawai, tinda

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

2 Comments On MAKOTAN ALJANA
avatar
umar-faruq

1 year ago

Reply

Jazakallahu Khair

avatar
nana-2

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ubangiji ya qara basira yaushe zamu samu cigaban pls????yamin Dadi sosaii

Please Login or Register in order to submit comment