Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na fara saki ai sai arcewa nayi sai d'akin kwana na kusan mai gida na wannan babu abinda zai tsinanamin koda tazo, ina nan kwance sai wutar d'akin ta mutu kuma ta koma ta kuna kanta haka akayi ta wasa da hankali rufe ido na yake, ina bud'ewa sai ga Fouraiha gaba na fitsarin da na fara dazun na idasa sakin shi, bansan lokacin da na fara *(A'UZU BIKALIMATULLAH TAMATIN MI SHARI MA QALAKA, INAHU SULEYMANA WA INAHU BISMILLAHI RAHMANI RAHIM)* nayi ta maimaitawa kusan so goma sha, candai naji tsoron ya ragu a zuciya ta kuma banajin alamu wani abu kusa dani na bude idona ban ganta ba na kuna fitilar wayar ta na haska ko ina ban ganta ba na sauke gauron lufashi can san sili(ruhin ) d'akin naji jini na d'asa d'ass d'ass ina haska fitilar sai na ga an rubuta da babban harufa *NA DAWO GAREKU* ina gama karantawa sai naji ihu Naïma a waje, ina jin tsoro amma haka na bud'e k'ofar na fita don ceton ta sai akayi daidai itama ta fito tana dariya.


"Yar uwa lafiya mi ya sameki?"


"Ha ha ha zafi nakeji, yunwa nakeji, aban abinci" cewar Naïma.



Kafin nayi wani tinani sai ga Naïma ta fara fida Kayan jikin ta, kawai tunanin da yazomin ta haukace, shikenan saura ni na fara hawaye.



Ashe a lokacin da Fouraiha ta kawomin ziyara b'angaren Naïma kuma a cikin mafarki taje mata, wai Naïma tana ta gudu don tsira da ranta, tana kuka tana ba wasu mutane hankuri ta kawo daidai wata 'yar k'aramar buka cikin ta akwai haske kawai sai tace bari ta shiga ciki ko ta samu tsira, tana jiga taji arba da d'iyan ta kwance sun sak'a Fouraiha tsaka tana shafar kansu da wuka tana murmushin mugunta.

Naïma ta durk'usa gaban ta tana bata hankuri akan tayi mata rai komai zatayi mata amma ta kyaile yaran ta karta cutar dasu, Fouraiha tayi dariya tace "ke wai akashe ni ko Kika je wajen boka Zagor to ai kinga Zagor kin ya mutu babu abinda wani mahaluki zai iya yimin kaf duniyar nan bale bokan ki"

"Allah badan akasheki bane yi hankuri na tu...."

Kafin ta gama magana Fouraiha ta d'aga wuk'ar nan tana neman cak'awa d'aya daga cikin d'iyan Naïma a mak'ogoro, sai Naïma ta fasa wani irin ihuuuuu ai ta ta farka daga wannan mumunan mafarki, tana zufa tana haki kamar wace tayi tseren gudu, ai kuwa sai ta tuna mafarki da gudu ta tashi don duba yaranta aiko ta isko Fouraiha kwance tsakanin yaran ta shiga bata hankuri akan duk binda takeso zatayi amma ta bar d'iyanta dan Allah, Fouraiha ta fashe da dariya tace "ke baki isa ki sakani abinda ban yi niya ba, nice saurauniya ni zan baki umarni"


Naïma batayi tunanin komai ba tace ta yarda duk abinda takeso shi zata yi itadai yaran ta aiko Fouraiha tace "tsuguna bagana kiyi sujada kice nice sarauniya kuma duk abinda nasaki Zaki aikata koda d'aukar rai ne?"


Naïma tace "na yarda" bata tsaya tayi tunanin abinda zaije ya dawo, sai Fouraiha ta matso kusanta ta bata sumba a goshi sai ga wani jan abu ya fito a idon ta ta shiga na Naïma ,koda ya gama shiga sai Fouraiha ta b'ace aiko Naïma ta haukace.



Abinda ya faru Kenan da Naïma alokacin da nima inacan ana ban tsoro, nayi nasara saka mata riga amman tsawon ta iya gwiwa ne, kuma ina kokarin tsaida ta amman ina ta haukace cikin wannan dare ta fita nikuma da naga na kasa kawai sai na dawo ga yaran ta na kaisu gidanadan kula dasu, a wannan daren nace nima bazan sake kwana a gidan ba, nayi tatare tatare na safiya nayi ina jiran mota, dan har na fara fito da Kayan a waje ina juyowa mukayi kicib'us da Naïma tare da wani mutum k'ark'arfa.


Cikin murna nace " 'yar uwa kece?"


"Nice wallahi, wannan mitumen ya taimake ni"

Na jiya ga mutumen ina masa godiya.

Yace "mu godewa Allah dan shine ya cece ta, yace shi mutum ne wanda Allah ya hadashi da rahonnai sune ke sanar dashi ga wani mutum aje a taimake shi, to haka ta kasance da Naïma yana cikin barci suka ce ya fito akwai wata mata ya taimake ta, ya fitowa ta isko ta kwance tana kuka sai kawai ya shiga da ita cikin gida da yake babban malami ne ya tado almajiran shi suka fara mata karatu aikuma sai ga wani kumfa yana fita a idon ta da kununwan ta, koda ya gama fita sai ta dawo hayacin ta take sanar damu abinda ya le faruwa duk wahalar da kuke sha, shine nace bari nazo na taimake ku......


Sunan malam Abanda.



Tun daga wannan ranar kuma abubuwa suka chanza .........







*Tofah ya kukaji da wannan page?ya zata k'aya tsakanin malam Abanda da Fouraiha tareda mutanan gidan nan?ku biyoni daki daki har karshe domin jin k'arshen wannan labari*












_INA GODIYAR DA ADOU'O'IN KU MASU BINA PRVT NA GODE ALLAH YA BAR KAUNA_












*PRINCESSE RAHIMA CE*👸🏻✍🏼
24/07/2020 à 12:58 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
👸🏻 _PRINCESSE_👸🏻





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*




_ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah ya bar kauna_









🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



8️⃣5️⃣↪️9️⃣0️⃣








Tin daga wannan ranar abubuwa sun chanza a gidan mu danko malam Abanda ya kawo salama.


Abanda yace "insha Allah zan cece ku daga wannan bak'ar azaluma"


Na durk'usa gaban malam ina rok'on ya taimaka yayi mana adou'a ko maji sauki abun.
Malam yace "tashi tsaye 'ya ta ai idai adou'a ce tare zamuyi idan nayi a banza ne amman idan tare mukayi zakuji k'arfin gwiwa koda bana nan kuyi wa kanku"


Nace "hakane malam mun gode sosai"

Yace "kuyi wa Allah godiya dan shine ya turo ni taimake ku"


"To ga mai gida na a d'aki ko zaka bashi wani taimako?"


"Muje na ganshi"

Muna shiga d'aki hummm kar kiso kuga tin a ranar da mai gida na ya fad'in bai sake motsi ba amma suna ido hud'u da malam sai gashi ya fara motsawa yana neman mafaka dan ya tsorata ansha fama anyi yaki kafin aljanu su bar jikin sa Alhamdulillah sauki kam ya samu.


Bayan an gama da mai gida na aka dawo kaina, sannan aka koma kan Naïma hata tsoho David shima an masa rukiya kar kuso kuga ashe dukan mu muna tare da bak'ak'en yaran aljanu a jikin mu, to malam dai ya fida mana su Alhamdulillah munji sauki sai kuma malam yace ya kamata mu kwan dare muna adou'a domin k'orar wannan aljana data adabemu yace zai gayato mana da almajiran shi domin tayamu adou'oi cikin dare.
Haka akayi wajajen sha biyu malam Abanda da sauran d'aliban shi aka taru a cikin gidan mu domin gabar da gagarumin karatu alk'urani mai girma mun fara kennan munkai d'aya da rabi na dare mukaji ihun Fouraiha daga cikin d'akin ta sai kuma gata ta fito idanun ta jawur kamar garwashin wuta tana haki kamar tayi tseren gudu.


"Ku suwaye da za kuzo har gida na kuna k'ona ni?"


"Ni malamin ne da Allah ya turoni nazo na ceci wannan bayin Allah daga zalinci irin naki"



Nan muka k'ara kaimi wajen adou'a, saiga Fouraiha tana safa da marwa tayi nan ta dawo tayi nan,sai kuma ta fad'i k'asa, kamar ta suma, muna cikin karatu mukaga wata bak'ar riga ta bayana a jikin ta saiko gata ta mik'e idanun sun k'ara ja tace "yanzu zaku mutu".


Ta rufe idonta ta d'aga hanun ta sama sai ga wuta a hanun ta ta watsoma mutanen da ke karatu ai duk suka watse hata almajiran nan malam Abanda k'ad'ai ne bai ko motsa ba.
"K'aryaki azaluma baki isa kiyi komai da mu ba".


Fouraiha kwance kasa tana kuka tana rok'on gafara "kayimin rai dan Allah, kana k'onani bazan sake ba lale na zalumci mutanen nan amma ina nema gafara"


*To mi kika aikata masu?"


"Na salwantar da rayukansu"


"Ta yaya kennan"


"Cikin rame na rufe a tsakiyar gidan nan"

Malam ya umarci akawo pelu (abin yasar k'asa)don ta gina rame ta fido abinda tace, da gudu soja (Mazan fama) yaje ya d'auko harda biyowa da wata sharb'eb'eyar wuka a k'ugunsa.

Muna kalo ta fito da wannan k'atuwar tukunyar ta kwanaki da kwayakwai da ke ciki, malam ya zuwa ruwa magani a sama tukunyar sai gashi ta fashe sai kuma ta b'ace batt, malam Abanda ya zuzuba ruwa magani a lugu da sak'o na gidan sai gashi hayaki na tashi, can kuma komai ya lafa sai ga Fouraiha tana kuka tana neman ceto akan mu taimake ta ta tuba baza ta k'ara ba.



Soja (mazan fama) yace "wai tuban mazuru ke ai mutuwa ce daidai ke"


Malam yace "aa kar iuyi saurin yanke hukunci tin tace ta bari ku yafe mata"

Soja ya fito da wuk'a yace "a barshi shine zaiyi ajalin tabata cancanci yafiyar mu ba,irin wannan azaluma basu cancanci aryuwa a doran k'asa ba"



Abanda yace "aa yaro na ai ko Allah ana mashi laifi ya yafe mana ku yafe mata tinda tayi nadama"


Nidai ina tsaye ina kalon ikon rabbi, wata zuciya tana cemin kar in yarda wata kuma tace ai ta tuba komai ya wuce.



Nandai malam ya ci gaba da adou'a ya kama kanta. Fouraiha tace "nayi kuskure babba ku yafemin, nima badaga gareni bane bokaye suka reneni, banason cutar da mutane amman sai inji bana jin dad'in sai nayi cuta ko na samu kwanciyar hankali kuyi hankuri"


Itama ansha fama tayi kukan namin daji kala kala takoma tare kala kala kafin ta dawo daidai, tayi wata irin k'ara sai ta fad'i somamiya.

Malam yace "ku kamata ki kaita d'aki"
Amma mu duka mun kasa matsi, sai shi da kanshi ya kaita d'akin ta muna biye dashi, can sai gata ta farka, tana kuka tana neman yafiyar mu, nidai nace "na yafe mata Allah ya kiyaye gaba"
Naïma tace itama haka, soja ne dai yace zai yafe amman sai yaga abinda hali yayi.


Nandai malam Abanda yayi mana nasiha akan hankuri da juna sanna ya tafi zuwa goshin asuba.




Rayuwar mu ta koma normal komia na tafiya yanda muke son shi mukan fito muyi firar mu kamar farko kulum muna tare da junan mu Wasa da dariya farin ciki ya ziyarci zukatan mu, komai ya zama tarihi........




*TO ALHAMDULILLAH NAN NA KAWO KARSHEN BABI NA FARKO CIKIN WANNAN NOVLS K'IN NA MAK'OTAN ALJANA, SUNAN WANI FILMS WASA FARIN GIRKI*


_Mi zai faru a cikin babi na biyu? Fouraiha tayi ruban gaske ne koko tuban mazuru tayi? Ya MAKOMAR mutanan wannan gida take? Mizai faru da shi mijin Laila ? Itama Naïma yaya makomar ta zata kasance? Yaran Laila da Naïma mi Fouraiha zata aikata masu? Domin jin amsoshin wad'annan tambayoyin ku ci gaba da bibiya ta_









_Wai Allah na gaji mu had'u a gobe insha Allah a next page_









*PRINCESSE RAHIMA CE*👸🏻✍🏼
24/07/2020 à 12:59 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
👸🏻 _PRINCESSE_👸🏻





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*




_ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah ya bar kauna_









🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



9️⃣0️⃣↪️9️⃣5️⃣






Na yafe ma Fouraiha, amman wani b'angaren na zuciya yana min gargad'i akan indai kiyaye, kawai sai in kori wannan tunani inci gaba da harakoki na, na maida hankali na wajen yin adou'o'i safe da yama, saidai kashe nayi sake na bar kula da yara na bana sa suyi adou'o'i kaina kawai na sani.


Matsalar ta fara ne daga kan yaro na Abdallah, yaron akwai kwaizo a makaranta gashi shuru shuru ne bai cika son hayaniya ba, yana aji uku a collège (gaba da primary), abin ya fara wata rana ya dawo daga école (school) na dafa abinci irin wanda ya keso nace "ga abincin ka nan" yace "maman na k'oshi, na rigada na ci abinci".


Mamaki na fido ido "kulum saidai kacemin ka k'oshi ka rigada kaci abinci, to a ina kaci abinci?"


Wannan tamabayar baya tab'a amsawa akan ina yaci abinci, na hasala ina fad'a baban shi yace "karki matsawa yaro yace ya k'oshi ki barshi kawai"

"Kulum fah ya k'oshi ?"

"Ki barshi nace"


Haka na hankura badan raina yaso ba, kuma abinda yasa na maida hankali kan 'yan sana'o'in cikin gida ina kama 'yan kud'i shiyasa bana samun lokacin zama da yara na, bansan abinda suke aikatawa ba.


Abinda ya k'ara tunzirani sai ranar da Abdallah yazomin gida an basu sakamakon jarabawa bai samu maki ba, yaron da bai tab'a zuwa na uku ba kulum daga farko sai na biyu ai ranar kamar zan tada gidan da fad'a, zaunar dashi nayi nace "mike damun ka ne? To daga yau babu kai babu kalo, kayan wasa na rufe kai ko k'ofar gida na ganka kasan saura. Baiyi magana ba yana kuka dan ban saba mashi fad'a ba, raina yayi matuk'ar b'acewa nace "tashi ga abincin ka can kaci kaje ka kwanta" yace "maman na k'oshi".

Na tsani naji wannan na k'oshi, saida zuciya ta dakata da aiki na wucin gadi,nayi mutuwar tsaye ina kalon shi "mi kace?" "Maman na k'oshi" ai ban sake magana ba saida baban shi yace yaje ya kwanta. Na rasa mike damun d'ana na kasa gane kanshi.

Nayi alkawali sai na gano abinda ke faruwa, washe gari ina k'ofar gida ya dawo daga école ya gaida ni ya shigo harabar gidan na bishi cikin sand'a kar yagan ni, saida ya duba yaga babu mai ganin shi ya shige gidan Fouraiha, mintuna biyar sai gashi ya fito yana tand'ar baki ya shafe baki ya mata sai anjima tana d'aga mashi hannu ta rufe k'ofar ta, ai banyi wata wata ba ba isko shi yana fida kaya nace "ba na hana ka cin abinci waje ba? Ohh yanzu na gane wacan matar ita ke baka abinci kake zuwa kana cemin baka cin abinci a k'oshe kake? To daga yau daga ranar mai kamar yau ba' son sake ganin k'afar ka a gidan ta"


Ina fad'in wannan maganar karshe naga fuskar Abdallah ta chanza cikin wata irin murya daban sanshi da ita ba yace " Zaki iya raba ni da mahaifiya ta?ke asuwa? Sabida mi?hummmm"

Idanu da baki bud'e nake kalon shi kamar wata sakara, ioda ya gama fadar maganar ta rufe k'ofar d'akin su, nima nawa dakin na koma ina kuka ina adou'a Allah ya kawomin agaji.
Zuwa dare mahaifin shi ya shigo nake sanarda shi abinda yake faruwa bud'ar bakin shi "ki fida wannan matar a zuciya ki saki ranki abinda ya faru da ne yanzu ta tuba" sai kawai ya kwanta.
Cikin wannan daren ban runtsa ba gani kwance amma ba barci nake ba, Na tashi ina 'yan adou'oina cikin duhu sai naji wani irin iska ya bud'e k'ofar d'aki na, cikin tsoro na kuna wutar d'akin abinda na gani ya firgita ni ya d'imautani Abdallah tsaye da sharb'eb'eyar wuka a hannu idanun shi sun koma bak'i k'irin babu wannan fari na cikin ido, da wata irin kakausar murya wada tafi ta dazu yace "Laila nazo domin ke" (ma'ana wannan tafiyar taki ce).




Fad'in irin firgici da tsoro da na Shiga b'ata lokaci ne ka tarin mamaki d'ana da na haifa yana kira na da suna na ga wuka a hanun shi yace zuwan nan nawa ne.


Innalillahi wa ina illaihi raji'oun!!!!!!!


"Wai d'ana Abdallah mi kake shirin aikatawa ne?"

"Ni ba d'anki bane nazo ne dan ke"


Yana matsowa kamar wani robot yace "mi yasa zaki hanani abinda mahaifiya ta ke si?sabida wane dalili?"



Wannan halin da nake ganin shi ciki yasa na daskare waje d'aya ina kalon shi saida yazo dab dani ya d'aga wukar domin cakamin ......











(Ya zata k'aya ? Abdallah zai kashe Laila ?ku biyo 'yar mutan *marad'i*)






Mu had'u a next page insha Allah na gode.







_Ina jiran comment 100 ko kuma na dakatar zuwa bayan sallah insha Allah💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻_







*Daga alk'alamin Rahima princesse*👸🏻
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
24/07/2020 à 12:59 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
👸🏻 _PRINCESSE_👸🏻





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*




_ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah ya bar kauna_



*RAHEENAT Allah ya bar kauna ke tadaban ce son so fi sabilillah*❤️❤️






*SAMEERAT ALLAH YA SAUKE KI LAFIYA AKWAI SHOKI A RANAR DUK MUN GAYACE KU MARUBUTA BASAI 'YAN NIGER AA HATA 'YAN NIGERIA DA SAURAN K'ASASHE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻



*AMINATOU BOULKASOUM (AMICHOU)* *HBD INA TAYKI MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWA ALLAH YA K'ARA MAKI SHEKARU MASU ALBARKA DA NISAN KWANA DA D'INBI BASIRA TAURARIN NIGER WRITER'S MUNA ALFAHARI DA KE*
🤩🤩😍😍💃💃💃😘❤️❤️🎈🎈🎈🎈🎈🎈🍮🍮🍮🍮🍮🍭🍭🍬🍬🍸🍹🍹🍷🍷🍾🍾🍪🍪🍩🍩🎂🎂🍰🍰🎂🎂🥧🥧🍦🍦🍨🍨🍧🍧🎉🎉🎉🎊🎊🎊







🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



9️⃣5️⃣↪️1️⃣0️⃣0️⃣





*_______________* Ya d'aga wukar domin cakamin fan gaskiya na sadakass kawai kasheni zaiyi ido na rufe ina jiran tsamani... Bansan ya akayi mai gida na ya farka daga barci ba sai kawai ihuuu shi naji yana cewa "to mi kike a zaune ki tashi mana"

Abdallah da mahaifin shi suna kokowa yana so uafi k'arfi mahaifin nashi.

Abdallah "ku sake ni ni, ku sake ni, ni ban dan ku, bansan ku suwaye ba"


"Mi yasame shi? " inji mahaifin shi.


Banma sapu damar amsa mashi ba, suka ci gaba da kokowa sai can Abdallah ya tsaigaita da kokowar.

Yace wa mahaifin shi "babba ka rikemin hannu ina jin zafi"


Abdallah yana kuka akan an mashi ruk'o kuma zafi yakeji, koda naga hawayen shi na ruga na rungume shi ina kuka, mahaifin shi ya k'asa gane komai abinda ke faruwa.

Nace "bbyna mi kake so?"

Yace "maman yunwa nakeji"


Fad'ar irin farinciki da nake ciki baya misultuwa, duk dai da cikin dare ne amman naji dad'in, na shirya mashi abu mai sauki yaci nace yaje ya kwanta.



*Washe gari*


Ina gayama Naïma duk abinda ya faru, tace;

"Kina tunanin Fouraiha bata daina abinda take ba na surkule?"


"Gaskiyar magana haka ne bani shaku"


"To kam idan haka ne ya kamata muje muga malam Abanda mu sanar dashi tin wuri"


"Ba damuwa insha Allah ko zuwa asabar ne dan kinga yau alhamiss gobe jouma'a sai asabar zamu samun shi*


"To Allah ya kaimu"

Naïma ta kasance irin matan nan wanda suke da saurin yarda, duk girman laifi da ka aikata mata idan ka nemi yafiya zata yafe kuma aci gaba da rayuwa, batada ruk'o sam .
Saidai kashe tayi babban kuskure da ta yarda da Fouraiha dan yanzu sun zama abokan juna, kulum idan Fouraiha ta dawo daga idan take zuwa dan bamusan inane ba tace tana aiki, sai ta biya gidan k'awar ta Naïma su d'an tab'a hira kafin ta wuce.
D'iyan Naïma suna jin dad'in mu'amala da ita dan kulum sai ta biyo masu da wani d'an abu naci (chocolat biscuits....).

Haka ta kasance yauma ta dawo ta biyo suna hira Fouraiha tace "'yar uwa yane mike labari?"

Naïma "gani dai, kefah? Kin samu aiki kenan?"

"Eh na salu, yanzu haka wani shagon saida Kayan masarufi nake kula da abubuwan da ke shiga suna fita"


"Masha Allah abu yayi Allah ya rik'a"



"Amin, gashi na biyo ma Yara da biscuits"


Yaran Naïma sun kasance masu son hayaniya, ga son abasu abu dan ita kanta mahaifiyar su bata hanawa, to yau abun yazo da ban mamaki ga Fouraiha.

Naïma "kar ki damu ai har sun riga da sunci abinci dare"


"Haba? Aiko Moussa yace na biyo mashi dashi da safe da zan fita"

"Kar ki damu barci kawai"


Fouraiha tace" hummm ok "

Wannan abun da Naïma tayi bai bar Fouraiha ba tana ta tunanin akwai abinda ke faruwa ya kamata ta fara kai hari"


Lokacin da ta fito zata gidan ta ta had'u da yaran ki daga ina suke oho.

"Yaran kirki daga ina kuke?"

"Gidan tonton (uncle ) soja muke muna kalon télé (TV/v) tata(anty) kin biyo mana da shi?"


"Eh gashi ma"
Ta mik'a masu biscuits suka fara murna har zasu ruga sai ta tsayar da su.

*Kar ki saki ki nunawa mahaifiyar ku dan tace ki daina cin abu mai zak'i idan dare yayi"

"To antyn mu"

Sukayi saurin ciny'e biscuits kafin su Shiga gida, to tin daga wannan ranar yaran Naïma suka zama wasu irin ta kasa gane kansu, d'abi'u kala kala suka tsoro dashi.


Washe garin ranar ta dawo daga aikin ta tana neman su suna can suna wasa kamar kulum, tana kewayawa bayan gida ta ga Moussa nacin k'asa.

Naïma ta girgiza "Kai mi kake anan?"

"Komai maman"

Saidai kashe Moussa bai tsira ba dan ga k'asa a lab'an shi da hak'oran shi.
"K'asa kake ci? Anya wannan ba wani sabon surkule bane?"

Abunka ga marass hankuri da saurin fushi ta jawoshi yar gida ta cika gidan da ihuuu har soja dake gida b'angaren shi ya fito dan sanin Mike faruwa.

Soja "mike faruwa ? wannan ihuu duk na miye?"

Naïma "abin ya wuce tunani na, kali shi ka gani ko ka gano abinda na gani, bayan gida na tarda shi yana cin k'asa"

Soja ya matso dan ganewa idan shi abinda tace, yaga zahiri da bakinshi nan cike da k'asa.
Soja da shine yaran suka fi kusan ci da shi dan idan zata fita wajen shi take barin su idan yana gida, koma tana gida wajen shi suke zuwa suyi kalo dan sunce tv gidan shi yafi dad'in kalodan k'aton gaske ne, ya ke tambayar shi "wai Moïse da gaske ne kaci k'asa ?"

D'aga mashi kai kawai yayi.
"Sabida mi kake cin k'asa ?"

Kanshi k'asa ya kasa magana, muna cikin wannan dramar sai ga k'anan shi d'an shekara 10 yana d'oyi da sabatu kamar wani mashayin giya.

Ko soja ya matsa kusan shi saida ya toshe hancin shi dan warin giya yake, ga sigari a hannun shi, Naïma na ganin shi tayo mutuwar tsaye.
"Wayo Allah ka kawomin agaji"

Soja abun ya bashi mamaki yaro k'aramin yace "Yahaya miye haka?"


Baima yi magana ba sai zuk'ar sigari yake yana tada hayaki sama irin na 'yan duniya jik'ak'u.

Soja "Yahaya sigari kake sha? Wai ma tukunan shekarun ka nawa?"


Yahaya da wata irin kakausar murya yace "Kai ba uba na bane dan haka kadaina tambaya ta"

Kowa yasan d'iyan Naïma duk irin hayaniyar su saidai tsakanin su yara amman ba suyiwa babban rashin k'unya,to wannan kuma d'abi'un daga ina?

Uwar shi na ganin abinda yayi batayi wata wata ba ta zage ta d'aga hanun ta zabga mashi mari, duk ta hasala "bakada hankali ne? A cikin gidan wa wannan rashin k'unya ?ohh dan mahaifin ku ya mutu ta barni da ku shine zaku ringayin abinda kukaga dama ko?"

Baiwar Allah duk ta rikice tqban tausai wallahi, Yahaya yace "fad'a kike min?kinsan ni waye? Tashi nake dama fah"


Naïma da soja sukayi tsale lokaci d'aya.

Soja "mi kace?"

Yahaya"eh nace tashi nake cikin dare dan haka yanzu an dena min magana kamar da"


Soja "tashi? Kamar ya a wane gidan?"


Yahaya "tashi nake sararin samaniya kamar tsuntsu"

Naima da soja kansu ya k'ara shiga a duhu.

Soja yace "to ya kake yi?

Yahaya "toh yanda tsuntsaye keyi Haka nake yi, sai kawai naga fukafukai sun fito a baya na, sai mama na tazo neman na dan mu fita"


Naïma tace"mi kace? Wace uwa?"

Yahaya "ainahin mahaifiya ta ta gaske"

Ai yana fad'in haka Naïma ta tuna yanda na sanar da ita mukayi da Abdallah har taso k'aryata ni.

Soja yace"gaskiya kina barin yaran nan suna yawan kalo (dan baisan abinda ke faruwa ba) gashi suna ta imagine abubuwa da dama"

Yahaya yace "tonton (uncle) ba imagination bane gaskiyar magana ce, idan kana son kaga zahiri to bari dare yayi"

"Da gaske ?"

"Da gaske ne, ko Moussa ma yana canzawa kamar maciji, ki bari dare yayi ku gani"

Kuma duk abinda ya fad'a gaskiya ne, shiyasa soja yace bari bari ya kwana a gidan dan ya ganewa idan shi, dan ga alama gaskiyar shi ce yake fad'a, sunyi wa yaran fad'a suka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

2 Comments On MAKOTAN ALJANA
avatar
umar-faruq

1 year ago

Reply

Jazakallahu Khair

avatar
nana-2

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ubangiji ya qara basira yaushe zamu samu cigaban pls????yamin Dadi sosaii

Please Login or Register in order to submit comment