Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zama wata kamar bok'anya ko matsafiya to sai a nemo irin su a had'a ta dasu suyi mana maganin ta"
Miji na "bari naje akwai wani mai duba da na sani nazo dashi muga abinda zaiyi"
Naïma "kuje ku kawo duk wanda kuke so mman nidai bazan k'ara kwana a gidan nan ba tafiya ta kawai zanyi na huta da anoba"

Laila "tafiya zaki yi haka, bayan kudin haya d'à kika biya na watan nin? Kuma bai kamata ki sare haka ba wannan yakin ya kamata muyi shi tare"
Naïmai "bana wasa da rayuwar yara na, da tawa rayuwar kawai a sabar tani"
Laila tace "naji kedai ki jira mai gida ya zo dan Allah"
"Kinsan fa ni harakar masu duba kaje adubo maka bala'i,bani cikin shi"
"Kin cika taurin kai wallahi"
"Naji kuje ou dawo ina jira"
Mai gida yaje tahowa da mai duba, ita kuma taje kai yara asibiti, ni kuma na shiga gyairan gida.



Mai gida na ya isko layi koda aka zo kanshi yana shiga mai kai ga isa wajen malamin duba ba yaji yana cewa "kai kuma lafiyar ka, na ganka matace amma kuma ya akayi kake tafiya (ma'ana kana raye)?"
"Ni kuma matace?ban gane mi kake nufi ba?"

"Eh na ganka ka mutu to miya fito da kai alhalin kana gawa?"
"Nifa ba matace bane ya kai malam"

"To muje ka kaini wajen kwancin ka na gani"

"To muje"
"Jira na shirya, dan bansan abinda zan taras ba"
Malam ya shiga ya shirya ya fito, harda wata jarka ta ruwa, sun kawo k'ofar gida, suka tsaya malam yace "anan kake kwana?"
"Yace anan muke muna da yawa" yace "to ai nan mak'abar ta ne kuke kwance ciki, kuma duk an tsunbance shi, dole sai an kori wanan abun da aka kewaye ku dashi"
"Mun shiga uku Haka ta mayar damu kennan?"
Malamin duba "kazo min da duk mutanen da ke zaune a gidan nan yanzu" mai gidan na yace muzo ga malamin nan yazo, duk mun fito muna tsaye gaban shi, yana rike da wata k'araurawa szi fitar da hayaki take, yace mu tsugun na gaban shi babu gardama muka tsugunne, "yanzu zan kare ki daga mungu abun da aka maku" ya fara wasu sabatu koda ya gama yace "yanzu babu abinda zai tinkare ku ya cutar da ku, duk na kore shi" ya fito da wani farin gari da ruwan a jarka duk ya had'e su guri daya, ya Shiga cikin gidan duk wani lungu da sak'o na gidan saida ya zuba, sai kuma wajen gidan, d'aya gama yace "yanzu babu abinda zai same ku ku amshi wannan ruwa idan zaku wanka ku zuba k'ad'an cikin ruwan wanka, sannan cikin d'akunan ku ma ku ku zuzuba a ko wane lungu kafin ku kwanta, duk abinda ke cutar da ku bazai samu damar k'ara cutar daku ba,bale ya tunkare ku"


(Shin mun ware da wannan anoba ta Fouraiha koko yanzu muka fara wasan?)




Wajajen 23h (sha d'ayan dare) duk gidan sit kaje ji dan babu mai son yayi wani motsi, masu cika dare an dena anji tsoro, Fouraiha na hango tana sauya halita zata fara sana'ar tata n'a bamu tsoro, mu duka harda yara na d'aki na muka koma duk mun kudun dune, can sai muka ji wata irin muyar tana kuka tana neman agaji ataima keta, can kuma sai shuru, mai gida yace "bari na lek'a na gani wake ihu?"
"Wallahi babu inda zaka"
"Ki bari na dibo wake kuka"
"Babu mai motsawa daga nan Allah"
Can kuma mukaji shiru kamar anyi ruwa an d'auke. Sanun sanun tsoro ya fara tasiri a zuciyoyin mu ai sai muka ji iska n'a k'ad'awa ta fenêtre (windo) ga wata inuwar mutum tsaye yana kalon mu ta tagar d'akin, can kuma ta inuwar ta gusa tana ta yawo tana buga k'ofar ta kasa shigowa ga sayu tafiya anaji, can kuma abin ya koma saman ruhin d'akin wannan karon ba tafiyar mutum d'aya bace mutane diyawa ne can sai wani cikin su ya fad'o ji kake "timm"
Can sai kuma tafiya ta tsaya sai aka koma k'ofar d'akin ana bubuga wa da k'arfi, mai gida na yace bari yace ya duba kafin nayi wani yunk'urin har ya fita a d'akin, daga dakin nace kar ya bud'e ya tambaya tukun nan, "wane ne" shuru babu amsa sai kawai ya juyo yana zama kennan kuma aka koma buga k'ofar wannan k'aron kamar za'a b'ale k'ofar, nace "kar ka koma ita ce fah" "kwantar da hankalin babu inda zani" kusan minti goma sai muka ji shuru, sai kuma ihu Lya'atou k'anwar Soja tana neman agaji "dan Allah ki bud'e min k'ofar zan mutu" mai gida yace "kina ji fah tana neman agaji haka zaki barta azaluma ta kashe ta" "ba ita bace n'a sani k'ar kaje"kafin nayi magana tuni har ya kai k'ofar d'akin, ya d'ebi ruwan da malamin ya bamu, koda ya bud'e k'ofar ya isko ta kwance shame shame, nidai ina daga fenêtre (windo) ina kalon Lya kwanace a galabai ce, sai kuma muakji bud'ewar k'ofa koda muka juya gidan soja ne tare da k'anwar shi tsaye ai sai oga ya zabura kafin yayi wani yunk'urin wannan k'anwar Soja da ke kwance ta banza ta b'ace, nayi ihu kiran shi ya shigo koda yayi taku biyu sai ga wannan mutumin mai hula na jiya ya baiyana gaban shi ya d'aga hanun ya kwad'a mashi mashi har uku, sai ga mai gida na kwance, gaskiya bazan iya barin shi cikin wannan halin ba haka na jashi cikin d'aki yana wani iri da idanun shi kamar mai ciwan farfad'iya fa kunfa a bakin shi, ni kuma shekarun mu dashi bayada wannan ciwo, kuka nake kamar raina zai fita.


Lya'atou k'anwar Soja duk wannan abun gaban ta ya faru safiya nayi tace ina wallahi bazata k'ara kwana a gidan nan ba ta tatara kayan ta, ta shiga don yin wanka sai gashi babu ruwa a cikin gidan sai da ta fito makewaya waje can ta samu ruwa,sai kawai tace mari tayi wanka da ta koma kuma abun yawa zaiyi, dayake batroom d'in babu nisa da inda nake shara sai kawai naji tayi ihu da gudu na jiga ban d'akin n'a isketa kwance ga jini yana bin k'ahuwan ta, kiran magajinta nayi da ke bakin k'ofar gida koda yazo har na sa mata riga yake tambaya "miya sameta" "nima ban sani ba, amman mu kaita asibiti" a guje ya d'auki mota muka kaita asibiti dan jinin ba na wasa yake zubar mata ba, bayan fitar mu wani k'aton maciji ya fito daga makewaya ya shiga d'akin Fouraiha, Kai amman wannan azaluma gashi ta mayar min da mai gida masaki ko magana baya yi, yanzu kuma ga k'anwar Soja kwance ba rai hanun Allah, kawai nansan sai ta ida kashe mu ta huta, dan harda abinda malam ya bamu bamu tsira to wai mi zamu yi domin tsira da kaidin ta abin yafi k'arfin tunanin mu.....









*To fah fans ya kuke ganin wannan abun zai kasance? Ku basu shadara, bamu fara komai ba yanzu wasan zaiyi dad'in*









_Kun jini shuru banji dad'in jiki na bane amma yanzu Alhamdulillah_







*Domin shawara ko gyara ku tintub'eni a wannan lambar +22792494512 n'a gode*😇





👸🏻 *PRINCESSE CE*👸🏻 ✍🏼✍🏼
24/07/2020 à 12:56 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
👸🏻 _PRINCESSE_👸🏻





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*




_ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah ya bar kauna_







*(Masu bina prvt kuyi hankuri wallahi ciwan kai nake fama da shi mai tsanani kar mutum yace yamin text ban maida mashi ba)*





*Masoya na ina alfahari da ku, so tsakanin da Allah*










🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



7️⃣0️⃣ ↪️7️⃣5️⃣





Mun kai Lya'atou asibiti an bata taimakon gagawa, abin mamaki kuma yanzu da wannan abun ke faruwa damu mun k'ara had'a kanmu, domin ance sarki yawa yahi sarkin k'arfin.




Laila tace "mi ya kamata muyi? dan abin yayi waya gaskiya"



Soja "sai na harbi wannan matar a Kai ta mutu kowa ya huta wannan azaba"



Nace "kana tunanin akwai abinda zai sauya, duba fah ka gani harda malamin duba da abinda ya bamu amma bai yi ba"


Naïma tace "ai daman saida na gaya maku gashi nan, kawai zuwa za muyi mi nemi wani k'asurgumin boka yayi mana maganin ta dan irin wannan mutanan sai bokaye"




Nace mata "gaskiya harakokin bokaye bana cikin su kin sani"


"Allah k'awata wannan daban yake daga ya shigo gidan nan namu komai zai tchanza"



"Hummm ba dani ba yi hankuri, wai ma ba kince garin ku zaki koma ba ya akayi baki tafi ba?"


"Nima na k'asa gane miye matsalar bayan nakai yara asibiti nace bari na je wajen aiki na na sanarda oga yara na basu lafiya kuma ina son hutu na tafi gida,amman ina zuwa mai gadi ya hanani shiga nayi nayo dashi wai ko bai ganeni ba yace kawai na jira sak'on mai gida, yanzu na tafi banki suma suka hanani shiga, duk hanyoyin dazan bi domin samu kud'i nabi amman sai inga kamar mutane gudu na suke"


"To miye kuma wannan abun da ke faruwa?"


"Kedai fad'i na kasa gane komiye, kawai ki bari mu Kira m boka"


"Ina nariga da na fad'a ban cikin wannan badakala"


Soja "ke kuma Laila ki bari ta kawo shi ya gwada sa'ar shi, kin mance mijin na kwance kamar gawa ta mayar maki dashi masaki"


Wannan maganar tamin wai masaki, dole nayi hankuri naje yazo.


"Mijin ki ya kawo d'an duba an gwada bai yiba kennan abari itama ta kawo nata mu gani" inji Soja.

Naïma tace"Allah k'awata ana ji da wannan bokan a garin nan dan manyan masu kud'i wajen shi suke zuwa"


"Naji sai kin kawo shi"


Ta tafi domin zuwa da bokan ta.



Kusan awa uku sai gata ta dawo tare dashi, wani mutum ne d'an kimanin shekaru arba'in, jikin shi duk fatu ne da layu, sai wani d'oyi yake.

Naïma "sanun ku ga boka Zagor nan"

Muna kalon shi don bamusan mi zamuce dashi ba.

Naïma "Zagor ga yarinya da nake gayama ka nan"


Ya fito da wasu abubuwa yayi d'an sirkulen shi, ya fito da reza k'aramar aska ya yanyanka mata goshi da cinya, soja har ya zaburo zaiyi magana na hana shi muka zuwa na mujiya muna kalon abinda zai faru.
Sai gashi ta fara motsi, daman duk mun damu tin zuwan mu bata motsa ba kuma likitoci sunki sanar damu abinda ya sameta, Zagor yace "kar ku damu" ya fito da wani ganye ya tauna abakin shi ya sa a yankan da yayiwa Lya sai gashi motsin ya k'aru, Zagor yace" ku duba" ya mana nuni da k'ahuwan ta jini ne ke zuba gudaje gudaje "yace zata Farka da zaran wannan gubar da ke jikin ta gama zubewa" muka had'a baki wajen cewa "guba kuma?" Zagor yace "wannan yarinya da kuke gani wani bak'in maciji ne ya sareta shine ya zuba mata dahi".


Muka saké had'a baki wajen cewa"bakin maciji?"

"Yarinyar tana da ciki wata biyu, to macijin ya shanye d'an sanan ya zuba mata guba a jikin ta dan tana gaf da mutiwa badan na iso ba"
Soja duk ya rud'e yama rasa abinda zaice.

Zagor "a ina kuka tsunto ta?kamar da ta fad'i?"

Na bashi amsa "a k'ofar bati (botrrom) kwance cikin jini"

"Ku kaini wajen da kuka d'auko ta" cewa Zagor.

"To kanwa ta kuma?
"Zata farka kafin mu dawo"
Muka bar ta ga hannu wata noss don kulata.


Mun isa gida myka nuna mashi daidai douche (batrrom) yace yana son d'an y'an nama, da gudu soja na fita bzkin hanya, sannan yace kuma abashi man ja, ya had'a man ja da wani garin maganin ta tchakud'e sannan ya yi wani k'aton kewaye tsakar gidan sai yace "komi zai faru kar ki matso kusa zaku ga abinda yaso kashe maku k'anwa".

Ya d'oki naman nan ya motsa cikin wannan abun da ya had'a da man ja, sai ta jefa shi cikin salanga, sannan ya fara tab'i yana wani tare wandan bamu san mi yake cewa ba. "Iyee iyee fito fito, iyee iyee fito kazo".
Muna tsaye har muna tinanin ko mi yake aikatawa a bakin k'ofar bandaki sai gashi abinda muke fanin film gashi gaban mu zahiri k'aton maciji bakikirin dashi dogon ba na wasa ba. Sannu sanun yana tab'i yana surutun shi har macijin ya gama fitowa daga makewaya yana janshi har ya zo dashi cikin wannan kewayen da yayi da man ja, koda yaga ya gama shigewa si ya dakata da surutu aiko maciji yana jin shuru sai yayi koshiya yana jiran a tab'a shi ya saki dafi duk ya nannand'e kanshi.


Zagor ya mana alama da mu fito daga mab'uyar mu, yace " kunga abinda ya nemi kashe k'anwar ku nan, ya b'oye ne a cikin makewaya duk mace mai cikin idan ta shiga to zai tsotse cikin sanan yayi ta lasar ta cikin lasar da yake ne guba ke shiga a jikin mace sanun a hankali har sai ankaita asibiti acan zata mutuwa". Sannan ya juya wajen maciji yana cewa "keleni da kyau ba abinda zaka iya min, daman irin ku muke nema masu cutar da mutane". Muka saki baki muna kalon ikon Good, sai kuma yace "to ai ba annan matsalar take ba, wannan maciji na wani ne a cikin anguwar nan ko cikin gidan nan, a kusa da mai shi yake".

Da gudu soja ya nemi wani k'aton ice yazo ya fara bugawa macijin nan saida Zagor ya haba shi yake cewa "zaka iya kashe wanni ka bari" soja yace "koma waye ya mutu mu huta kawai" Zagor yace "ba wannan ne ya kawoni ba,kunce kunason ku samu lafiya barci to zaku samu, saidai idan kun samu kud'i kuzo amaku babban aiki dan gaskiya sai an maku wanka fita daga matatu zuwa masu rai" ya bud'e wani buhun shi sannan ta fara tab'i orin n'a dazu da wannan sabatu sai ya macijin nan ya shige cikin buhun nan, Zagor ya d'auke abunshi, koda mukayi ban kwana ya kama hanyar k'ofar gida sai ta b'ace b'att muka nemeshi muka rasa.



Sai ga wayar soja ana kiranshi daga asibiti yazo k'anwar shi ta farka har tana neman abinci, ai ba shiri na girka abu mai sauki ya kai mata, zuwa kusan magriba aka salame su sun iso k'ofar gida sukayi kicib'us da Fouraiha kanta an d'aure da bandeji, hanun ta a kare, bata iya takawa saida ice, ai soja mi zaiyi inba dariya ba yana mata shakiyanci, ashe Annan bugun da yayi wa macijin nan ne, suka rabu tana musu wani mugun kalo tana kyaici.



Mukai sati d'aya d'aya lafiya kalau muke kwana babu wata matsala, saidai ba haka take wajen Zagor.......






*Wash Allah na gaji, ku biyoni domin jin Mike faruwa da boka zagor ya zata k'aya ne*





_kar ku gaji ina bara adou'oinku har yanzu ciwan kai nake fama dashi ga aikin office abubuwa sunmin over wallahi_






*+22792494512 m'y number*











*PRINCESSE*👸🏻
✍🏼✍🏼✍🏼
24/07/2020 à 12:56 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
👸🏻 _PRINCESSE_👸🏻





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*




_ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah ya bar kauna_









🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



7️⃣5️⃣↪️8️⃣0️⃣



Kwana lafiya kalau muke yi a gida, babu damuwa komai yanzu, sai ga tsoho David yazo ya na bani baki akan yana tare dani dan shima baisan miya faru dashi ba, har na dafa abinci yaci yana ta santi, ga mai gida na kwance har yanzu munyi jike jike mun kira mai duba shima yayi sirkulen shi amma ba'a daceba.




A b'angaren Zagor kuma bayan yaje gida da macijin nan ya hura wuta ya d'ora katuwar tukunya ya zazage wannan macijin a ciki ya rufe, wutar naci balbal, "ko waye sai yazo inji dalilin ki na k'untatawa mutane bada izini na ba, idan bakizo ba kuma ki mutu" maciji a cikin tukunyar yanata mutsu mutsu amma ya kasa fita,wuta na fasa shi, shi kuma Zagor zaune yana jiran mai macijin.




Ai kuwa sai ga wata irin guguwa ta taso ta turnike d'akin shi, sai ga Fouraiha ta bayana gaban shi.

"Kashe wutar nan idan kana son rayuwar ka" inji Fouraiha.


"Sai kin tsugun na"

"Ni kake cewa na tsuguna ? Kasan dawa kake magana ko? Kai wane ne?"


Zagor "ni ne babban boka duk wani aljani dani yake tink'aho nike sawa suyi ko kar suyi,duk Wanda ya cutar da bi'adama bada izini na ba hukunci zan mashi tsatsaura"


"Kana ina lokacin da akamin hukunci akamin azaba,baka isa kahanani rayuwa ba na d'auki rayuka na gidaje zama da 99 yanzu wannan gidan ne na k'arshe da za'a a barni inyi rayuwa ta ba takura" Fouraiha tayi tab'i ta buga k'asa sai gashi k'asa ta bud'e har ta isa wajen tukunya da wannan macijin ke ciki, sai ga tukunyar ta birkice.


Ai Zagor na ganin haka kawai sai ya fito da shima nashi salon yana jifanta da abubu a lokacin ita kuma tana tunkaro shi cikin fushi "sai na kashe ka a yaunzu".


Zagor taga ba SARL sai Allah anfi k'arfin shi sai ya sadakass ya koma bata hankuri akan shima aiki ne aka sashi Naïma ta kira shi, Fouraiha tace "koma waye ya saka yau sai ka mutu" ta kamo wuyan shi ta murd'e atake ya mutu.

(Zagor sauka lafiya)


Fouraiha na ganin cikin fushi mai tsanani "Naïma ke kikasa akamin haka ko to ganin nan tafe sai na salwantar da rayuwar ki a yau".



(To fah Naïma ta k'are maki, ina tausaya maki haduwar ku)





Tin bayan tafiyar Zagor muka samu salama muke rayuwa cikin walwala, har na fara tunanin naje mu had'u da Zagor ko zai samomin maganin ciwan miji na.

Laila "ohh kwana biyu har mun murmuje mun fara k'iba"

Naïma ai na gaya maki wannan bokan aikin shi kamar yanka wuk'a ne gashi zuwa d'aya kinga mun warke"

"Gaskiya na yarda, wai ya labari Lya da saukin jikin ta ?"


Soja "taji sauki sosai, ta ware zuwa k'auye dan cewa tayi bata iya saké zama a gida d'aya da Fouraiha ba, koda kuma batanan ne".


Naïma taxe "ohh kennan ware wa tayi , to ai ya kamata idan abu yana damun ka ka fida tsoro ka tukarin qbun ayita ta k'are ko kai ko shi, dan bata gama gudu ba tinsa idan tasan Fouraiha wasu tasan su?"

Laila "maganar ki haka take"


Bamuga Fouraiha kwana biyu ba har muna mata shak'iyanci yana cewa ko tayi ritaya (retraite) ne ko ana can ana jinyar jiki, muka sa dariya.



(Eh lale gari naku har kun samu damar hira da dariya)




Wani dare muna cin abinci da Naïma dan yanzu gidana take cin abinci dan har yanzu wajen aikin ta sunk'i gaban su maida ta.

Nace "wai ko zaki kaini inga bokan nan naki Zagor domin magance matsalar mai gida na don na gaji da ganin shi haka ?"


"To 'yar uwa ???na zata kince baki cikin irin wannan abubuwan na bokaye?"



"Ke manta daga baya mayi magana yanzu dai yaushe zamu?"

"Gobe ki shirya sai muje"



Bansan mi ya kaini ba ammna inaji kawai na aminta dashi dan Zaman lafiya da ya kawo mana a gida na yarda da shi.




Washe gari mun kama hanyar gidan Zagor, n'a d'auka cikin k'asurgumin daji yake a'a shi a cikin gari yake cikin mutane.
Mun isa k'ofar gidan mun kwankwansa amma shuru Mika sake shiru.

Nace "ko ta fita ne?"

Naïma tace "gaskiya idan ya fita yana barin rakar da a waje ya gayi lokacin dawowar shi dan mutum ya samu damar dawowa a lokaci.
Muna cikin shawara ya zamuyi sai ga wata yarinya ta fito daga gidan da ke kusan nashi, t'ai gaishemu take cewa "Zagor kuke nema?"


Laila cikin zumud'i taan fara take cawa "eh ko kinsan idan yaje?"


"Zagor ya mutu"


Cikin mamaki muka kali juna nida naima, "yarinya da wannan mai gidan muke magana hatsabibi bokan"


"Eh shi nake magana, ya mutu kudan sati d'aya ma har anyi bisa"


Bamusan mi ke faruwa a cikin kannun mu saidai can nace mata "ko mi ya faru dashi ?


"To musan dai yana cikin gidan shi, kwana biyu mukaji d'oyi yayi yawa har muka kai bamu iya shed'awa sai muka kira 'yan kwana kwana, koda suka b'ale k'ofar suka shiga suka isko gawar shi tayi d'oyi har ta fara tsutsa ga k'udaje ke biya gawar"



Baki muka saki mun a kalon ta, Naïma tace "k'awata yama akayi wai wannan bokan ya mutu? Ke sheda ce akan aikin shi"



Laila "kam to bai tunanin wai ko ita ce silar mutuwar shi?"


Naïma "gaskiya ban sani ba"


Haka muka yita jaje muna bitar abun muka dawo gida ba tareda biyan buk'ata ba, ni ina kukan wanda zan dogara dashi yamin maganin matsala ta kuma gashi ya mutu.





Wajen 12 dare (00h) na kwantar da yara d'akin su, ni kuma ina falo ina kalo bayan na gama na kashe komai naje zan shiga d'akin in kwanta, sai naji kukan musa(mage) ita sanina kaf gidan nan ke hata mok'ota na kusa basuda ida, kuma duk ta cika gidan da kukan ta, sannan tana yagar min k'ofar d'aki, sai nace kawai bari na fita na kora ta, n'a bud'e k'ofa sai ga mage k'ofar d'aki na tana kalo na ina kalon ta, yayi mata "ishhhh" na yi mata amma kar idon ta akaina, na buga k'afa ko taji tsoro amman ido cikin ido muke kalon juna, na juya domin d'auko tsintsiya na kore ta sai ga wata irin wacan mage a saman kujera tana "Miaou! Miaou!"
Ina juyo wa kuma sai ga mage biyu d'un sakani tsakiya ai sai tsoro ya shigeni, ina juyowa sai wacan mage ta k'ofar d'aki naga ta ruga a guje tayi cikin ciyayi tsak'ar gidan ita kuma d'ayar cikin kitchen ta ruga ta b'uya harda jan k'ofar ta rufe,ni kuma na bita dan korata.........







*Sai mun hadu a next page*








_Masu comment ina godiya, kun jini shuru aiki ne sai a slow_














*PRINCESSE CE*👸🏻
24/07/2020 à 12:57 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
👸🏻 _PRINCESSE_👸🏻





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*




_ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah ya bar kauna_









🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



8️⃣0️⃣↪️8️⃣5️⃣





Na nemi magen nan sama da k'asa amma na rasa, na kashe komai na juya na fita kennan na rufe k'ofa, sai naji plat nacin abinci a fashe kamar dai ranar farko komai na kitchen yana motsi, ina bude k'ofar na duk'a dan in kwanshe fashashen plat sai na hangi wani plat ya fito daga wirin shi yana tafiyar har ya iso daidai inda nake ya fad'i ya fashe, ai sai ga tukane koshiyai kamai na kitchen yana motsi ai ba shiri na gudu na rufe k'ofar daga baya, ina rufe k'ofar sai kuma komai ya tsaya chak ina daga bakin k'ofar naji wata irin murya an fadhe da wata mahaukaciyar dariya, na rufe idona sai tsoro ke k'ara shiga ta can kuma na hangi télévision (talabiji) ta kuna kanta alhalin nasan nidai na kashe komai hata wayoyin jona wutar na fitar dasu, nayi k'arfin halin duk da ina jin tsoro haka na tafi na kashe na kai k'ofar d'aki naji kuma ta kunan kanta na sake dawowa domin kashewa ina aza hanuna kuma sai komai ya d'auke kamar ba yanzu take kune ba, ina zufa ga tsoro na juya sai kuma naji wata irin mahaukaciyar dariya na juyo naga Fouraiha cikin majigi (télévision) tana kalona ina kalon ta sai kuma naga ta mik'o hannu ta k'ara miko hannu sai gata ta fito a gaba na daga cikin télé tsoro har fitsari

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

2 Comments On MAKOTAN ALJANA
avatar
umar-faruq

1 year ago

Reply

Jazakallahu Khair

avatar
nana-2

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ubangiji ya qara basira yaushe zamu samu cigaban pls????yamin Dadi sosaii

Please Login or Register in order to submit comment