Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli fatar jikinta ta ga yana sab'ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama dawowa hayyacinta tuni ta fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce
"Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah"
"To Baffa" Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta jima tana addua sannan ta tashi.


Abu na gaba da zata yi shine daukar zaren saƙar dana taje ta kona shi, to amma abun tambayar a nan shine a ina Azima ta ajiyesa? "zaki iya dubawa ki gani ta tafin hannunki ai an baki karfi a daren jiya a jejin lore" wata zuciyar ta bata amsa da haka, da sauri ta buɗe tafin hannunta na dama tasa hannun hagunta tana shafe tafin hannun daman tare da lumshe ido, nan ta ga ashe ma a cikin kayanta Azima ta ajiye zaren saƙar danar, tasan tabbas Aziza sai ta binciko,kuma duk bincikenta ba zata duba kayanta ba tunda ba zata yi tunanin zata saka a ciki ba, da sauri Aziza ta buɗe ido tana fadin "lallai Azima ke shaiɗaniya ce! A cikin kayana kika ma ajiye?" da sauri ta wargaza kayanta ta dauki zaren wanda Azima ta saƙa shi ya yi tsayi, lullubi ta yi ta boyesa a cikin mayafinta ta fito a hankali dan gari ya yi haske, har ta kai bakin kofa zata fita ta ji Hajja na kwala mata kira da gudu ta fice dan bata son ta rasa wannan damar, jejin kwana taje ta ajiye zaren bayan ta duba babu kowa a wajan, da ido ta kalli zaren yayinda idon nata ya koma jajur kamar garwashin wuta,nan wani jar wuta ya fito daga idonta ya kama zaren,nan zaren ya kama da wuta har yana wani irin ƙara passpasspass! Da sauri Aziza ta ja da baya, nan zaren ya ƙone ƙurmuss! tokar Aziza tasa hannu ta shafe shi ya b'ace nan ta sauke ajiyar zuciya mai karfin gaske tare da fashewa da kuka tana zubewa a kan guiwowinta tasa goshinta a kasa ta yi sujjadar shukur, ta yi tsammanin ta kashe wannan bala'in bata san wanda yake shirin ci ba.



🍃🍃🍃🍃


*AZIMA.*


tun fitarta a gida tana kwance a kan bishiya a macijiya tana jiran isowar Innu maciji, sai bayan da garin Allah ya fara wayewa ta ga wasu yan matasan samari biyu sun zo sun tsaya a jikin bishiyar da take kwance, dayan ya ce
"To ma ban da abun Mai Unguwa taya zamu iya kare Innu Maciji da za a wani turo mu dan mu tarbesa"
"Nima dai abun da na gani kenan" saurin zare ido Azima ta yi ta kallesu da kyau sannan ta yi murmushi
"Ohhho kenan yan fadar mai unguwa ne! Aiko su ya yi, shin na bar ma su bada labari ne? Idan kuma suka tona min asiri fa?" nan ta haɗe rai tare da sulalowa daga bishiyar ta zama mutum, hannu ta miƙa sama sai ga kwaryan nono, murmushi ta yi ta buɗe kwaryan wanda yake cike da nono kindirmo fari sol abun sha'awa ta watsa dafi a ciki sannan ta gyara mayafinta tayi lullubi ta rufe fuskarta ta nufi inda suke, cikin karairaya ta musu sallama, su kuwa sun ga ƴar budurwa har rige-rigen amsawa suke yi,cikin harshen fulatanci suke magana ta ce musu
"Ga fa nono, daga ina ku ke da sassafen nan haka ku ka zo ku ka zaune a tsakanin yanki?".



"Wlh mai unguwa ne ya aiko mu, kin san ai masifar da ake fama da shi a yankin nan na macizai, to yau Innu Maciji zai zo wanda yake yankin ja'i shine mai unguwa ya aiko mu dan mu tarbesa,kin san kwanaki da Jarman macizai ya zo gawarsa kawai muka gani, kai duk wannan macijin da yake kisan nan ko take kisan nan ko humm idan Innu Maciji ya zo zan ce ya bani dama na kashesa da hannuna" cije baki Azima ta yi ta ce "da gaske?"
"Aradun Allah kuwa! Sanda zan sha na dinga roɗewa macijin kai har sai ya koma ga Allah" damƙe hannu Azima ta yi jin yadda ranta ya b'aci zuciyarta na tafasa amma ta daure tare ta k'wak'ulo murmushin mugunta ta ce
"Ai kuwa nima ina da wasu sirrika a kan macizai, kafin na gaya muku ga wannan nonon ku sha" ta fada tana tura musu kwaryan, dayan ya ce
"Allah sarki! Ashe kin san yau da yunwa muka tashi, ga shi kafin mu karya karin kumallo aka turomu yanki" murmushi kawai Azima ta yi ba tare da ta sake magana ba, nan suka buɗe nonon nan suka hau sha, sai da suka shanye tass har suna mata godiya, Azima ta kyalkyale da dariya tare da yaye mayafin fuskarta nan blue eyes dinta ya bayyana, tare da rikiɗewa ta hau komawa macijiya, tsananin tsoro da firgici yasa suka kasa motsi illa junansu da suka rungume gagam!, bayan Azima ta zama macijiya sannan ta koma ta zama mutum ta matso kusa dasu ta duka ta ce
"NI CE AZIMA MACIJIYA! WACCE DUK KASHE-KASHEN DA AKE YI NI NA KE YI! NI! NI! NI CEEEE! SANNAN KU TAKU TA KARE DAN DAGA NAN BABU WANDA ZAI MOTSA A CIKINKU, DAN KUN SHA GUBANA" tana gama faɗi kuwa suka hau aman jini, su na riƙe wuyarsu tsananin azaba, jini na fita ta baki da hanci, suna birgiman fitar rai Azima na ta sheƙa dariya, da haka har suka daina motsi, bayan sun mutu ta kwashesu ta maida su gefe ta ajiye sannan ta ci gaba da tsumayin jiran isowar Innu Maciji, ba jimawa sai ga shi nan kuwa ya yanko a kan dokinsa, daka gansa ka ga basamudan bafulatani mai ji da kansa, wuyarsa rataye da maciji, Azima na ganinsa ta hau murmushi tare da gyara lullubinta ta zo ta tsaya a kan hanya, (ga Azima ga Innu Maciji, ya zata kaya?).




Kamar yadda ta yiwa jarman macizai haka ta yiwa Innu Maciji, shi ma kalar tambayar da jarman macizai ya mata shi ya mata
"Mutum ko aljan?" murmushi ta yi tare da fadin
" *RUWA BIYU!*" sannan ta juyo gami da yaye mayafinta, Innu Maciji na ganin kwayar idonta nan ya sauƙo da sauri tare da zare takwabinsa yana fadin
"Keeeee!" haɗe rai ta yi ta ce
"Ajali ya kiraka!"

Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce
"Kina tunanin zan mutu a hannunki ne?"

"Ashe dai baka cika ba! Tunda har ba zaka iya bambance wacece ni ba, amma ina so ka sani ba zaka shiga yankin nan ba,kamar yadda ba zaka koma yankinku ba" tana gama fadi ta yi kansa tare da komawa macijiya,ganin haka yasa Innu Maciji saurin b'acewa dan ya ga da karfinta ta nufosa, Azima gani ta yi Innu Maciji ya b'ace yasa ta koma mutum tana ta kalle-kalle,ji tayi an tokareta ta baya nan ta fadi kasa ta bugu tukunna Innu Maciji ya bayyana yana dariya yana kallonta ya ce
"Ba mamaki baki da labarin waye Innu Maciji ko? Humm ni ne nan mai fada da aljanu da mayu, sabida shaharata yasa sadda aka raba kambun girmamawa ni ne nan nayi na daya, dan haka sai na baki wahala! Na galabaitar dake sannan na daukeki na kaiki wajan mutanen yankinku na nuna musu ke!" yana gama fadin haka ya zaro wani dogon igiya ya naɗe Azima da shi, ya hau bugunta tare da watsa mata wani ruwan magani wanda da ya watsa mata zata kurma ihu, fatar jikinta ya koma blue sabida karfin dafinta ne ke raguwa, haka Innu ya ci gaba da ganawa Azima azaba wanda izuwa yanzu fadin halin da take ciki b'ata lokaci ne, sai da ya ga bata iya motsin kirki sannan ya kyaleta yana shirin daukarta ya ɗorata a dokinsa yaje ya nunawa jama'ar yankin kwana, har ya dauketa Azima ta buɗe ido a galabai ce, a ranta ta ce
"Yanzu idan aka kaini Baffa da kansa na san zai kasheni! To ina kuma daukar fansata!? Inaaa ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan bar yankin nan ba, ba tare da burina na son maida yankin kwana maƙabarta ba, sannan ba zan bari na mutu ba tare da na shiga cikin gari ba" tana gama fadi ta yanki gashin kanta ta haɗiye ta rintse ido ta mamayi Innu Maciji wanda ya sab'ata a wuya yana shirin ɗorata a kan doki, nan ta zama macijiya tasa jelarta ta shaƙe wuyar Innu Maciji, shaƙa bana wasa ba, sannan tasa hannu ta b'abb'alle guru da layoyin dake jikinsa ta zubar, sannan tasa ihu ta koma macijiya gaba dayarta ta hau sarensa,duk yadda Innu Maciji ya so kwacewa ina hakan bai samu ba, Azima sai da ta ga Innu Macijiya ya zube kasa babu rai a tattare da shi sannan ta sulale gefe ta koma mutum tana sauke ajiyar zuciya idanunta jajur, kallon Innu Maciji take yi na wasu lokuta sannan ta ja samari biyun da ta kashe ta haɗa da innu maciji sannan ta bar wajan.



🍃🍃🍃🍃

Bayan Aziza ta koma gida aikin gabanta ta ci gaba da yi, ko kaɗan bata tambayi ina Azima take ba, nan ta yiwa Hajja shara da girki sannan ta hau ɗibar ruwa, sai da ta cika babbar randar kasarsu sannan Hajja ta ce
"Ayye Aziza ba za ki huta ba?" murmushi ta yi ta ce
"Hajja hutuna shine naga Allah ya rabani dake lafiya" Hajja ta yi murmushi jin dadi tare da sa mata albarka,nan suka zaune hira suka shantake sai zuwa anjima Hajja ta ce
"Wai ni ina Azima ne kam?"
"Wa ya san mata" cewar Aziza,
"Bata rafin jimulo ne?"
"Ni dai wlh Hajja har na gama jido ruwa ban ganta ba, da ace tana can dana ganta"
"Ikon Allah!" Hajja ta fada, Aziza ta ce
"Hajja miye amfanin damuwa a kan Azima ita da ba jaririya ba,duk inda taje zata dawo ai" Hajja ta ce
"Hakane" suka ci gaba da hirarsu, sai zuwa can Aziza ta ce
"Hajja wai ina Baffa? Tun fitarsa sallar asuba fa bai dawo ba ga shi yanzu ana neman lokacin azahar" Hajja ta ce
"Oh! Kinga na mance ban gaya miki ba, ai suna can fadar sarkin fulani, Chubaɗo"

"Wani abun ake yi ne?" Aziza ta tambaya cikin rashin sani tana kallon Hajja, Hajja ta ce
"E lafiyar kenan, kin san ai an yiwa yankin ja'i aiken wasikar taimako, har Innu Maciji ma ya ce zai zo yau, to jiran Baffan naku nake yi idan Innun ya iso zai zo ya gaya mana muje can fadar sarkin fulani"



Wani firgita Aziza ta yi ta miƙe tsaye ta ce
"Hajja yaushe aka yi aike yankin ja'i har Innu Maciji yace zai zo?" ita ma Hajjar miƙewa ta yi ta ce
"Aziza lafiya kuwa?"
Kama hannunta Aziza ta yi ta ce
"Hajja tun yaushe ne Azima bata gida?" Hajja ta ce
"Ban sani ba Aziza, dan ni tun wayewar garin yau ban ga Azima da idona ba, ba shine nake tambayarki ko kin ganta rafi ba"
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Aziza ta faɗa tana jan mayafinta zata fita Hajja na tambayarta ina zata je, har ta kai bakin kofar zanar gidansu bata kai ga fita ba suka yi mugun karo da Baffa wanda ya shigo a fijajan hankalinsa a tafin hannunsa, da sauri Hajja da Aziza suka tare Baffa,ganin yanayin da Baffa yake ciki yasa Aziza fara addua a ranta Allah yasa dai Azima ba Innu Maciji ta kashe ba,idan kuwa ta kashesa tabbas ta b'allowa yankin kwana yaqi.

Da sauri Aziza ta ɗibawa Baffa ruwa ta kawo ta ba wa Hajja, Hajja ta karba ta ba wa Baffa wanda da kyar ya yi kurbi daya wanda ya taho masa da kuka,ganin haka yasa ita ma Aziza ta fashe da kuka, Hajja na ganin Aziza ta fashe da kuka ita ma tasa kuka,nan aka rasa mai rarrashin wani,da kyar cikin kuka Aziza ta kama hannun Baffa tana faɗin
"Dan Allah Baffa ka gaya mana meke faruwa!"

" *AZIZA? JUMALA! AN KASHE INNU MACIJI!! DA MASU TARBAN BAƘIN SHIGOWA YANKIN KWANA SU BIYU!*"

BAFFA na fadin haka Aziza ta sake hannunsa tare da yin zaman yan bori!
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! mai Azima take son zama?" kasa motsin kirki Aziza ta yi illa komawa da ta yi tana bin Baffa da Hajja da suke kuka da ido, sai zuwa can Hajja ta ce
"Ya aka yi da gawar har an binne su ne?" Baffa ya girgiza kai ya ce
"Ba zamu iya hakan ba, ana ganin gawar ba shiri Arɗo da Chubaɗo da Ori suka ce garkuwan fulani da Galadima da Liman da mutum biyar a fada su tafi yankin ja'i da gawan, yanzu Allah ne kadai yasan me zai faru an kashewa yankin ja'i Innu Maciji, taya zasu fara fuskantarmu su fahimce mu? Innalillahi wa inna ilaihirrajun!" nan suka ci gaba da jajinta lamarin inda a karshe Hajja da Baffa zasu fita Hajja ta ce
"Aziza zo muje" murya can kasa wanda take ji da kyar ma take maganar ta ce
"Hajja kuje zan zo"
"To amma kiyi lullubi kafin ki fito anani ko?" Aziza ta gya ɗa kai, kanta a sunkuye, Hajja da Baffa suka fice,dan Aziza tana ji ba zata iya tafiya ba jin kamar kafafunta basu gangar jikinta.


Bayan fitar su Hajja da Baffa kamar da rabin awa sai ga Azima ta shigo babu sallama kamar an wurgota ko kallon Aziza ba ta yi ba, da ido Aziza ta bi Azima tana ji kamar ta haɗa musu guba su sha su mutu ko duniya zata zauna lafiya.


Azima na shiga bukka ta hau dariya kasa-kasa gami da faɗin
"Innu Maciji na kashesa! Yau kuma *MAGAJI BAWA* zaka mutu! Sauran mutanen yankin nan za a kashesu ne idan tarzoma ta tashi, dan nasan yankin ja'i ba zasu hakura ba, ta fada tana murmushi tare da zura hannu dan ta dauko zaren sakar dana da ta saka a kayan Aziza amma ta ji wayam,ido buɗe take warware kayan Aziza amma bata gani ba,kamar mahaukaciya haka Azima ta fito ta zo ta tsaya a kan Aziza
"Ke Aziza Magaji! Nayi ajiya a kayanki amma ban gani ba" dago kai Aziza ta yi ta kalli Azima sannan tasa hannu ta share hawayenta ta miƙe a hankali cikin sanyin murya ta ce
"Me kika ajiye a kayana?"
"Mtswww! Bana son rainin hankali Aziza! Ki bamu abuna!?"
"Wani abunki?"
"Zaren sakar dana da na ajiye a kayanki" Aziza ta jinjina kai ta ce
"Owoohhh zaren dana? Na ƙonasa!!" wani zabura Azima ta yi tasa hannu ta shaqi wuyar Aziza ta ce
"Kin ƙona fa kika ce!? Ke meyasa baki son mu dauki fansa ne kam!? Me yasa ba zaki bari na rama mana abunda aka mana ba! Kin ƙonasa!? Aziza ke mahaukaciyar wace al'karya ce? Na ce ke....." ture hannunta Aziza ta yi daga wuyarta sannan ta kwalfa mata mari ta ce
"Kin kashe Innu Maciji da samarin fada mutum biyu! Akan me!"

Ɗagowa Azima ta yi ta wanke Aziza da mari ita ma, ta kuma shaƙe mata wuya
"Kin min asara! Shin kin san da cewa jejin lore sau daya tak suke ba wa mutum abu? Kuma dole da zaren sakar dana zan iya kashe Baffa me yasa! Aziza na ce me yasa! To wlh kin jawowa kowa, yau kisan da zanyi ban ga mai dakatar dani ba!" tana gama faɗi ta zama macijiya ta sulale ta fice, ganin haka yasa Aziza ita ma ficewa da gudu.



🍃🍃🍃🍃🍃



COMMENT AND SHARE
BY MOMYN AHLAN BAIWAR ALLAH MASOYIYAR ANNABI MUHAMMADU S,A,W,🙌🏻🥰
[3/21, 12:31 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*STILL FREE..*
🅿️==1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣



Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba, riƙe kai Aziza ta yi tare da furta "YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala'i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama'ar mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!" Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta iske wata budurwa kwance bakinta sai jini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota, tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu tana furta "AZIIIMAAAAAAA!!!?" da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue.



Duk inda Aziza take tunanin zata ga Azima amma da ta je sai dai ta iske gawa, hakiƙa fadin yadda hankalin Aziza ya tashi b'ata lokaci ne, ga shi ta rasa yadda zata yi, bata kara shiga ruɗu ba sai da ta yi gamo da gawar mutum takwas wanda Azima ta kashe, daga karshe Aziza ta koma tayi zaman yan bori.

🍃🍃🍃🍃

*YANKIN JA'I.*


a lokacin da garkuwan fulanin yakin kwana suka isa yankin ja'i da gawar Innu Maciji hakika sun ga tashin hankali, sun ga masifa da bala'i a wajan jama'ar yankin ja'i, ko kaɗan sarkin fulanin yankin ja'i wato Jawo da kuma mai unguwa Sodangi da sauran duk wanda yake yankin ja'i basu tsaya sun saurari su Garkuwan fulanin kwana ba, suna isa da gawar fadar sarki Jawo nan yankin ya ɗauka daga tafiyar Innu Maciji yau yankin kwana sun kashesa, nan jama'ar yankin ja'i suka janyo wuƙaƙe da adduna da sanda kokara,suka yi kan su garkuwan fulanin kwana tare da fadin su ma ba za a barsu a raye ba, Galadima da Liman suka ce yadda suka tunzura gwanda kawai su gudu, garkuwan fulanin kwana ya ce bai kamata su gudu ba tare da sun musu bayanin abunda ya faru ba" Galadiman fulanin kwana ya ce
"Baka da hankali ne garkuwa? Ka ga yadda suka haukace suna ihu ka ce mu tsaya musu bayani taya zasu sauraremu? Ka zo kawai mu gudu dan ceton ranmu daga baya idan suka yi sanyi sai mu dawo! Amma kaga yanzu suna abu kamar wa inda mahaukacin zaki ya cije su" Garkuwa ya ce
"A gaskiya ba zamu tafi ba tare da munyi musu bayani ba,tunda duk abunda ya faru mu muka ja wa kanmu! Da ace mun bi shawaran Magaji da ba haka ba"
"Amma dai garkuwa kasan rashin hakuri irin na yankin ja'i da haukarsu ko? Ka zo mu gudu idan ba haka ba zasu iya kashe m...." maganar da Liman bai karasa ba kenan yaji saukar dutse a goshinsa,nan ya riƙe goshin yana faɗin "Ya Rabbi!" kafin su Garkuwa su dago nan suka ji ihu, inda gaba daya ahalin yankin ja'i mata da mazansu kowa ka gani da makami nan suka yo rututu suna shirin kai wa su Garkuwa farmaki,nan suka hau musu ruwan manyan duwatsu kafin su isosu,ganin haka yasa Galadiman fulanin kwana da Limamin fulanin kwana suka kwasa a guje dan tseratar da ransu, sauran mutum biyar na fada mutum uku su ma suka arce da gudu aka bar Garkuwan fulanin kwana da mutum biyu na fada su uku kenan, kafin Garkuwan fulani ya yi kokarin faɗin wani abu tuni, an rufesu da duka da sanda, yayinda ƙanin Innu Maciji yasa adda ya sare daya daga cikin ɗan fada a wuya yana sare san nan ko minti daya bai yi ba yace ga garinku, ganin haka yasa garkuwan fulanin kwana yace shi da dayan ɗan fada su gudu, da kyar suka kwace suka hau dokinsu ba shiri suka sab'i hanya jikinsu jina-jina da jini, dan garkuwa ma kam an saresa a hannu.



Har mutanen yankin ja'i zasu bi su garkuwa, Sarki Jawo ya ce su dawo ai sun b'allowa kansu yaƙin da basu san wanda zai tare musu ba, za ayi wasika a tura musu su shirya tarban yaƙi,kuma suna da yaƙinin zasuyi nasara ta hanyar shafe al'karyan kwana tunda Magaji Bawa ya yi murabus!.



@@@@@@


*YANKIN KWANA.*


haqiqa yau yankin kwana tana cikin ruɗu da ruɗani,yayinda suka jera gawawwaki har na mutum sha ɗaya wanda saren maciji ne a jikinsu.


Yau da safe mutum biyu sun sha dafin maciji sun mutu, Innu maciji saran maciji ya mutu,yanzu kuma ga gawawwakin mutum sha daya, tsananin tashin hankali yasa suka kasa yiwa gawawwakin jana'iza ga magriba ya gabato, ganin haka yasa sarki Chubaɗo bada umarnin a musu sutura a binnesu kar su yi kwanan keso, da kyar suka yi musu jana'iza suka binnesu, bayan sun fito daga maƙabarta sai ga isowarsu Galadiman kwana shi da Liman a fujajan, da sauri mutanen yankin kwana suka tarbesu suna tambayarsu me ya faru? Baffa ya kalli goshin Galadima dake zubar da jini an fasa masa goshi,Baffa ya ce
"Daga ganin goshin Galadima ba sai an tambaya ba! Mun taro yaƙi ko? Ina su Garkuwa!?"



🍃🍃🍃🍃


😔😔😔 1readmore
For ur sake yar gidan Anty Zahra,Slimzy☹️
[3/21, 12:32 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin

1 Comments On AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE
avatar
ubaidah

1 year ago

Reply

The novel is very interesting and entertaining

Please Login or Register in order to submit comment