Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*IDAN DAI BAKI BIYA KUDIN KARATUNKI YANZU BA LALLAI BANE IDAN NA GAMA KI SAMU CMPLT A #100NAIRA BA, ZA KI SAMU NE A #300 DAN HAKA YAR UWA WANNAN BONUS DIN KAR TA WUCE KI.*


*REMAIND 1 FREE..*
🅿️==2️⃣1️⃣↪️2️⃣2️⃣




"Garkuwa suna can, ya ƙi tahowa wai sai ya musu bayani, da wuya yanzu idan su Garkuwa su na numfashi" Liman ya karasa maganarsa yana zama sharaf a ƙasa yana fifita da hularsa irin na fulanin nan wanda ake saƙa shi, cirko-cirko suka tsaya, yayinda Mai Unguwa Ori ya ce
"Mu ba mu kashe Innu Maciji da gangan ba,akasari ba bamu ne muka kashesa ba! Me yasa zasu kashe mana garkuwa!?" cikin fusata wanda yake nuni da damuwa da ɗimauta Baffa ya ce
"Laifin su waye!? Na ce laifin su waye!? Ga irin abunda nake gaya muku amma kun kasa fahimta, ai shikenan sai mu jira har ta Allah ta kasance damu! Ga bala'in kisan macizai! Ga bala'in yaƙi dame zamu ji ne kam! Ya Rabbi gamu gareka! Babu yadda banyi daku karku aikawa da yankin ja'i wasika ba, yanzu mai hakan ta haifar!? Da ace kun saurareni duk ba za a kai ga haka ba, amma mu da shike fulani Allah ya yi mu da taurin kai bamu jin shawari, wlh da kun bi abunda zan shinfiɗa da mun magance matsalarmu da ikon Allah sabida ina da imanin za a....."


"Ka rufe mana baki Magaji!!Ya isheka haka!!" Jauro ya katse Baffa, Jauro shine mai magani na yankin kwana
"A kan me zamu bi abunda zaka gindaya!? Kana da halin da zaka taimakemu amma kayi hakan ne? Duk wani yaƙin da zai kunno kai kasa a ranka har da sa hannnunka a ciki! Da ace ka taimaki yankinka har za a yi aike a wani yanki mai suna yankin ja'i ne! Dan haka babu abunda zaka gayawa mutanen yankin nan! Sai ka bar mu mutu! Idan an kashe Garkuwa da yan faɗa biyu sai mu ma mu jira mu ga mai zai yi ajalinmu,Macizai ne ko kuma jama'ar ja'i!"


"Haba Jauro miye haka ne kake yi! Bai kamata ka faɗawa Magaji wannan maganar ba! Kwata-kwata ma yanzu ba lokacin musayar yawu bane!" cewar Arɗo, Jauro ya ce
"A kan me ba zan faɗa masa ba! Karya nayi ne! Na ce karya nayi ne!!?" sarki Chubaɗo ya ce
"A gaskiya ban san me zance a wannan lamari ba, amma zan iya bin maganar Jauro! Magana ta domin Allah wannan yanki ya kafu tun kakanni, wanda ya taimaka ya kara tsayawa ma wannan yanki kai ne Magaji! Tun ban san da cewa zan zo na zama sarkin fulanin kwana ba, ni dai roƙonka zanyi da girman Allah ka taimakemu Magaji! Muji da masifa ma daya ta ishemu ba sai an ɗaɗo mana da na yaƙi ba" Sarki Chubaɗo ya faɗa yana haɗa hannunsa alaman roƙo,Baffa ya jinjina kai tare da faɗin
"Naji! Kuma na yarda! Abunda aka binne shekaru ashirin shine zanje haƙosa yau! Shin zaku iya fama da masifu biyar!? E ko a'a? A da masifa daya ce, sannan ku ka kuma janyo mana wata da hannunku, yanzu kuma kun bada dama aje a kara haƙo wata shin zaku iya tayani tareta? Nayi imani a yanzu yankin kwana babu mai iya tayani yaƙi da aljanu babu shi!"

" *AZIZA!* Baffa ya ji an raɗa masa a kunne, da sauri ya dago yana waige amma bai ga kowa ba, "Aziza kuma?" Baffa ya tambayi kansa a zuciyarsa yana shirin faɗawa kogin tunani ya tsinkayo muryan Arɗo da Baffa Mandi suna fadin
"Gaskiya ba zamu yarda a haƙo ba,ta bakinka Magaji babu wanda zan iya wannan yaƙin kawai a bar maganar mu sake neman taimako ku kuma ka faɗa mana hanyar da zamu bi" Sarki Chubaɗo ya ce
"E hakane magaji, ka gaya mana wace hanya ce zamu bi?"


"Inaaaaa! Sam-sam ba zai yu ace Magaji bane zai bamu mafita sam ban lamunta ba! Ni fa wlh ina zargin Magaji, duk yadda aka yi yaransa ne *MACIZAI!*" Jauro ya faɗa yana huci, saurin dagowa Baffa ya yi yana kallon Jauro, dama ya jima da sanin jauro baya sonsa yana baƙin ciki da shi, ya jima yana masa ƙulli amma kawai bai san yadda zai yi da Baffa bane, shuru Baffa ya yi yana kallon Jauro, yayinda Arɗo ya katse Jauro da fadin
"Wai lafiyarka kuwa Jauro? Ko dai akwai wata a kasa ne tsakaninka da Magaji?"

"Miye haɗi na da shi?" Jauro ya faɗa yana yiwa Baffa kallon ƙasƙanci,
"Kawai dai gaskiya abunda na sani ne,meyasa ya ƙi aurar dasu yara duk sun gandare a yanki babu mai rab'arsu, shekarunsu goma sha biyar oh Allah ni Jauro, yara na tafiya jiki na lankwasa ace mutane ne! Taya hakan zata kasance!? Kullum fuskarsu a rufe sabida babu ido mai kyau, sannan duk taron da za ayi na magani basu zuwa, dan Allah a cikinku nan ku gaya min suwaye suka yarda da yaran Magaji mutane ne?" nan wa inda Jauro ya haɗa baki dasu suka amsa da basu yarda da Azima da Aziza ba, sannan Jauro ya matso kusa da Baffa wanda ya koma tamƙar wanda aka dasa bishiya ya ce
"Zan fara sakawa yaranka ido fiye da yadda na saka musu a baya, idan har na gano cewa su ɗin ba mutane bane na maka alkawari da hannuna zan kashesu a gabanka!!" rass!rass!rasss! Gaban Baffa ya bada yana kallon Jauro, shi kuwa Jauro yana gama faɗi ya juya zai bar wajan ya tsinkayi muryar Baffa na faɗin
"Allah ya baka sa'a,ni nan zan baka takwabin da zaka kashe yarana a gabana!" ko uhum Jauro bai ce ba ya bar wajan, Baffa Mandi ya ce
"Wai miye haka ne kam?" murmushin takaici Baffa ya yi ya ce
"Ba komai! Ni na jawowa kaina ai!" shi ma ya juya zai bar wajan sai gasu Garkuwa a muraran! Da sauri aka tarbesu kowa yana furta kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Da sauri aka sauko dasu daga dokin yayinda Garkuwa ana sauko da shi yana sumewa, ba shiri aka ce a kai sa wajan Jauro ya duba sa.


@@@@@@@

A ranar yankin kwana babu wanda ya rintsa, Aziza kuwa ta yi neman Azima ta rasa hakika Aziza idan tace akwai natsuwa da sauran hankali a tare da ita ta yi karya.


Da washe gari Aziza na idar da sallar asuba ta fice, jejin kwana ta nufa, tana zuwa ta kirawo Inno Fandi, Inno Fandi na zuwa Aziza tasa kuka, girgiza kai Inno Fandi ta yi ta ce
"Aziza ba kuka bane mafita, abu mai mahimmanci shine a yanzu ki maido da natsuwarki, rashin natsuwarki shi ya hanaki ganin Azima, zaki iya ganinta amma sai kin samu natsuwa, sannan zaki iya zuwa dan ki gayawa Baffanku gaskiyar su waye ku, dan ba zaku ci gaba da boyewa ba Azima na kashe mutane,idan ba haka ba a duban da nayi kowa na yankin nan ya kusan mutuwa! Abunda Magaji baya so dole karshe shi zai aikata, wato haƙo baiwarsa da ya binne shekaru ashirin, sannan duk yaƙin da zata kama da wuta kece garkuwar mahaifinki Aziza,ki koma gida Magaji ya ba ki asalin tahirin rayuwarsa na abunda ya faru shekara ashirin amma har sai kin gaya masa gaskiyar su waye ku!" Inno Fandi na gama faɗi ta b'ace, Aziza kuka takeyi kamar ranta zai fita,taya zata fara faɗawa Iyayenta su ba mutane bane Macizai ne? Taya!? Ya Hajja da Baffa zasuji? Idan suka gano cewa duk kisan da akayin nan Azima ta yi su?" kuka sosai ta yi ta godewa Allah fuskarta ya yi jajur idonta ya ƙara komawa fari sol, tashi tayi tana ajiyar zuciya tare da tattaro natsuwarta kamar yadda Inno Fandi ta gaya mata sai ta samu natsuwa kafin ta iya sanin ina Azima in ba haka ba yau ma kisan da zatayi sai Allah ne yasan adadi, a hankali ta rintse ido tana karanto adduar samun natsuwa ta hanyar tasbihi ga Ubangijin talikai, sai da taji zuciyarta ya samu natsuwa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta rintse ido nan ta ganota kwance a jejin hayi, da sauri ta buɗe idon tana me daukar hanyar jejin hayi ba tare da bata lokaci ba gwanda taje suyi na yau.



@@@@

Maga Isar da Sakon yankin kwana ne yake karantawa fada sakon yankin ja'i kamar haka
" _DAMA MUNYI MAMAKI ACE KUNA DA MUTUM A YANKINKU KAMAR MAGAJI BAWA AMMA ACE KUN ZO YANKINMU NEMAN TAIMAKO DA INNU MACIJI! HAKIKA MUMA MUN ZAMA SHASHASHU DA MUKA YARDA DA KUDIRINKU! BAYAN MUN SAN DA CEWA KU ƊIN ABOKAN GABANMU NE NA TUN TULI-TULI! A KODAYAUSHE KU YANKIN KWANA KUNA SO KU DINGA NUNAWA KUN FI SAURAN YANKUNA! TO MUNA SO KU SANI KU KARA SANI, LOKACI YA YI DA ZAMU MAIDA YANKIN KWANA BABBAR MAƘABARTA! DAN KUWA MUNYI SAƘO YANKIN JIMO MUN ZUGASU NA JARMAN MACIZAI DA KU KA KASHE! TUN KAFIN KUYI AIKE YANKIN TUDU MUN RIGAKU DAN BA ZAMU YARDA DA KASHE MANA INNU MACIJI DA KU KA YI BA, MUN GAYAWA YANKIN TUDU KUN KASHE MANA INNU MACIJI SANNAN BA MAMAKI KU MUSU AIKE A BAKU IRO MAGANIN MACIZAI TO MUN TOSHE WANNAN HANYAR DAN MUN TONOWA SARKIN TUDU TSOHON RAUNIN DA YANKINKU SUKAYI MASA TA HANYAR KASHE MASA GUDAN JININSA, DAN HAKA KU FARA SHIRYAWA TARBAN YAƘI NA YANKUNA GUDA UKU, YANKIN JA'I: YANKIN JIMO: YANKIN TUDU: SAKO DAGA YANKIN FULANIN JA'I._"


Maga Isar da sako yana gama karantawa aka hau kallon-kallo, Mai Unguwa Ori ya ce
"Yaƙi da yanki uku a kan yankin daya?"


"Kuma lokaci daya?" cewar Sarki Chubaɗo,Arɗo ya ce
"Mu dai mun san bamu aikata komai ba, mu sa a ranmu wannan wata jarabawa ce daga Allah, kuma yana sane damu, shi zai kawo mana dauki, kar mu ce zamu yi wani shirin yaƙi, mu zubawa sarautar Allah ido" kowa ya amsa da haka ne sannan kowa ya watse cike da alhini.



🐍🐍🐍🐍🐍


Azima na kwance a kan bishiya rabinta mutum rabinta macijiya, jelarta na lilo a ta saman rashen bishiya fuskarta a haɗe har gefe da gefe ya yi jaa! Idonta kuwa ya kara rikiɗewa ya rine ya koma blue sosai harta fari babu, Aziza tana zuwa jejin hayi jelar Azima ta fara hangowa, saurin karasowa ta yi ta ce
"Azimaa!?" jin muryar Aziza yasa Azima sulalowa tare da komawa mutum, a fusace tayo kan Aziza tana isowa gabanta kafin ta yi mata magana Aziza ta yi saurin dafe goshin Azima nan take taji abu ya shige mata kai sai da ta girgiza.


Ganin yadda Azima ta tsaya yasa Aziza faɗin
"Azima lokaci ya yi da zaki saduda! Ki dakata haka" murmushi Azima ta yi tana yiwa Aziza kallon baki da hankali
"Ni kike cewa na saduda? To naji zan saduda, amma bayan na kashe Baffa!" ta faɗa tana cije baki, Aziza ta ce
"Wai ke wace irin dabbace Azima?" murmushi Azima ta kuma yi ta ce
"MACIJIYA! ina kina tambaya ne wace irin dabba ce ni? To ni Macijiya ce kamar ke amma bambancin shine ni muguwa ce ke akasin haka! Har yanzu ban huce da abunda kika min ba, ki bar ganin kinsa jikina ya yi sanyi kin kafar min da dafina! Ba shi zai dakatar dani ba, na iya yau ne kawai, amma gobe zan haɗa da kisan da banyi yau ba!" Aziza ta jinjina kai ta ce
"Kin sha fadamin idan na isa na dakatar dake! Ni kuma na sha fada miki cewa bazan bar hakan ta faru ba, shine zan kara nanata miki, ba zan bar hakan ta faru ba! Dan haka muje gida, kafin Hajja ta titsiyemu da tambaya!" a hankali Azima ta juya tana dafe kirjinta dan abunda Aziza ta tura mata ya shigeta sosai, a hankali suka jera suna tafiya dan Azima na da bukatar ta kwanta dan jikinta da ya mutu, sabida abunda Aziza ta tura mata a hankali yake bin jikinta yana kashe mata shi, dan makarin dafi ta tura mata.



Da haka suka iso kofar gida Aziza ce ta fara shigewa da sallama ta samu Baffa da Hajja suna zaune yana labarta mata wasikar yankin ja'i wanda kaff abunda Baffa ya faɗi a kunnen Azima, a tana rarrafawa da kyar amma wani dadi ne ya mamaye zuciyarta nan ta hau murmushi tare da fadin
"Yankuna uku zasu yaƙe yankin kwana? Wayyooo Dadi!bari na ɗan daga kafa dan ganin yadda za a shafe yankin kwana idan ya so na kashe Magaji Bawa daga baya!" ta faɗa gami da sallama ta shiga gidan, Hajja ta ce
"Azima ina kika je ne? Ni anya jiya na ganki kuwa? Yana ganki haka kamar wacce bata da lafiya?"

"Kin ganni mana Hajja! Ko dai wannan bala'in ne yasa kanku ke da Baffa ya kama da wuta!? Sannan da kika ganni haka ba wata matsala bace babba kaina ke ciwo, da nayi bacci na farka zan dawo dai-dai" Azima ta fada tana kallon Baffa, da ido Baffa yake bin Azima yayinda take yi masa wani irin kallo, Hajja ta ce
"Allah ya kyauta, jeki kwanta" Hajja ta shige bukka, Azima ta juya kenan zata shiga bukka idon Baffa na kanta dan ya kasa kauda ido a kanta, wuyarta taji ya mata ƙaiƙaiyi tasa hannu ta sosa, tana sosawa sai ga sab'ar maciji ya fadi carab a idon Baffa, wani wawan firgita Baffa ya yi,ya tashi jikinsa na rawa ya karasa ya dauki sab'ar yana kalla,saurin girgiza kai ya yi yana fadin
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! Me hakan ke nufi?" jikin Baffa ya yi mugun sanyi dan ya tsorata ba kadan ba, bukkarsa ya shige yana jeka ka dawo dauke da fatar a hannunsa, cikin rawar murya ya ce
"me ya kamata nayi? Dole na haɗa maganin ganowa idanuna, amma kafin na samu furen surfa sai naje jejin gangare, kuma kafin na dawo sai na samu kwana biyu sabida dogon tafiya ne ban ci ta zama ba, In sha Allahu zan tafi gobe" yana gami fadi ya fito ya shiga bukkar Hajja ya gaya mata gobe da safe zai tafi jejin gangare Hajja ta ce
"Me zaka je yi?"
"Akwai maganin da nake son haɗawa ne, kuma furen da ganyen dole sai naje jejin gangare"
"To Baffa yan biyu Allah ya kaimu lafiya" Baffa ya amsa da amin ya fice, bai zarce ko ina ba sai wajan Ardo bai boye masa komai ba kasancewarsa mahaifinsa ya gaya masa komai, sosai hankalin Arɗo ya tashi ya kallesa ya ce
"Magaji bana so ka gaya ma kowa wannan batun ka ji ko? Har sai ka tabbatar" Baffa ya gya ɗa kai cike da damuwa, nan suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin.



🐍🍃🐍🍃🐍🍃


COMMENTS AN SHARE
BY MOMYN AHLAN
[3/21, 12:32 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*YAR UWA ZO BIYA KUDIN KARATUNKI DAN JIN YADDA ZATA KAYA A CIKIN BOOK DIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, BIYA DARINKI KACAL YANZU,IDAN KUMA NA KAMMALA CMPLT DARI UKU ZAKI SAMESA.*


*LAST FREE..*
🅿️==2️⃣3️⃣↪️2️⃣4️⃣



Da washe gari asubanci Baffa ya yi ya bar yankin kwana dan bai ga ta zama ba, ko da Aziza ta farka ita ce kawai ta tambayi ina Baffa yake nan Hajja ke gaya mata ya tafi jejin gangare dan samo wasu ganyen magani, Aziza ta ce
"Allah ya dawo min da Baffana lafiya" Hajja ta amsa da amin.


Ita kuwa Azima tunda ta fara bacci ba ita da farkawa ba sai gefen sallar la'asar, ko da ta farka Aziza na shirin ɗora mata hannu a goshi ta yi saurin rike hannun Aziza ta ce
"Ba bukata Aziza, yau ina cikin farin ciki babu wanda zan kashe amma za a mutu dayawa gobe! A'a ba wai ina nufin ta hannuna ba fa,dan naga kina min wani kallo! Wallahi babu wanda zan kashe! Amma gobe akwai zubda jini a yankin kwana!" tana gama fadi ta tashi ta fito ta samu Hajja a tsakar gida, Hajja ta ce
"Azima wannan baccin naki ya yi yawa, haba dan Allah mutum ya ta faman bacci ba sallah ba salati ko kina fashin sallah ne?"

Yatsine fuska Azima ta yi kafin ta ce
"Ni fa Hajja wannan fashin sallan da kika fadi me ma yake da suna? Al'ada ko? To ni banayi! Kuma ban taba yi ba! Sallah gabadayanta ne bana yi,kuma ma Hajja sadda Aziza ke zuwa islamiyyar Malam Saini ni kin taba gani naje ne? Har Aziza ta yi sauko ni ban taba zuwa Islamiyyar Malam Saini ba,ko kuma kin taba gani da watan ramadan ina azumi? Ki kyaleni da maganar wani abu wai shi sallah!" tana gama fadi ta fice, Aziza na tsaye a bukka tana kallon Azima, bayan Azima ta fita Hajja ta kalli Aziza hankali tashe ta ce
"Aziza meke damun yar uwarki!?" murmushin tausayin Hajja Aziza ta yi ta matso kusa da Hajja ta kama hannunta ta ce
"Kun kusa ku sani Hajja nan ba da jimawa ba, dan bazan iya jure ganin hawayenki na zuba a kanmu ba, zan gaya miki gaskiya da zaran Baffa ya dawo ko da kuwa za a kashemu!"


Hajja ta bude baki za ta yi magana da sauri Aziza ta ce
"Dan Allah Hajja karki ce komai, Azima bata sallah bata salati bata Azumi duk wani aikin ibada bata yi,na gaji da miki karya Hajja, bazan iya jure miki karya ba!" tana gama fadi ta fice da gudu da kuka.


Aka bar Hajja da kakkarwar jiki.

@@@@@


Da yamma sai ga wasika daga yankuna uku izuwa yankin kwana, zasu kawo musu farmaki gobe da safe, hakika wannan sako ya hautsine hankalin jama'ar kwana inda mata da dama har ma da mazan wasu suka fara kuka, sarki Chubaɗo da mai unguwa ori suka ce ga shi Magaji baya nan, kuma babu halin yi masa saƙo har sai ya dawo, saukinta ma Garkuwa ya ɗan samu lafiya, kafin kace me Sarki Chubaɗo ya bada umarnin ayi shela a yankin kwana gabadayanta za a kawo farmakin yaƙi gobe kuma yankuna uku,dan haka kowa ya kasance cikin shiri amma bana tarban yaƙi ba.


@@@@@@


Hajja da Aziza sun kasa zaune sun kasa tsaye sabida tashin hankali sai jeka ka dawo suke yi a tsakar gida amma Azima na zaune hankali kwance tana fizgar dogon gashinta, Aziza ce ta kallenta ta ga babu alamun damuwa a tattare da ita,cikin haushi da tsanar Azima da ya fara ɗarsuwa a zuciyarta ta ce
"Wai ke Azima wace irin dabba ce ke ana maganar kawo farmakin yaƙi amma kina zaune kina tsifar kai?"


"Macijiya!" Azima ta faɗa ba tare da ta ɗago ta kalli Aziza ba, Hajja ta juyo a firgice ta ce
"Ma mai kika ce Azima! ?" tana shirin kara nanatawa Aziza tayi saurin faɗin
"Mahaukaciya kawai!"

"Ga ki kuwa babbar mahaukaciya!" Azima ta faɗa tana dagowa a fusace.


"Dan Allah fadan ya isa haka!" Hajja ta katsesu,
"Kuyi ta addua kawai Allah ya bamu mafita yafi wannan fadar naku" ko uhum basu kuma cewa ba.



🍃🍃🍃🍃


Da washe gari kamar yadda sako ya iskesu haka kuwa ta kasance inda yankin ja'i da yankin jimo da yankin tudu sukayi cincirindo sun zo yaƙar yankin kwana, amma abun mamaki babu wani daga yankin kwana da ya dauki makami, abun ya basu mamaki, Arɗo shine wanda ya fito ya fara magana kasancewarsa Babba, tsohon bafulatani mai dattako
"Mu ba zamuyi yaƙi daku ba, idan har kuna so duk ku sa takwabi ku kashemu! Har ga Allah munyi imani wannan ita ce kaddararmu! Bamu kashe Innu Maciji ba, a ranar da aka kashe Innu muma munyi rashin mutane a yankin nan har mutum sha huɗu, haka ma jarman macizai, sannan sarkin fulanin tudu bamu aikata muku komai ba kawai neman fitina kukeyi,idan kuma yaronka da aka kashe a yankin nan ne laifi ya aikata aka masa hukunci, na rantse da wanda ya busamin numfashi idan har aka samu ɗan wani yankin kwana da laifi makamanciyar wanda ɗanka yazo yankin nan ya aikata wlh mun yarje muku ku fille kansa ku kawo mana kamar yadda mukayi, ba a barin laifi a ɗoran kasa, dan ba a san mai zai kuma aikatawa a gaba ba, mu sabida muna bin al'ada da ibada shiyasa yankinmu ta yi baƙin jini a wajan sauran yankuna, idan har maganar da nayi baku gamsu ba kuna iya shafemu a doron kasa ko kwayi farin ciki" Arɗo na gama fadi jama'ar kwana suka miƙa wuya,ganin haka yasa yankin jimo jikinsu yayi sanyi suka ce ba zasuyi yaƙi da yankin kwana ba,nan take suka juya, yankin tudu da yankin ja'i kuwa sunce suna nan, sai sun shafe yankin kwana.


@@@@

Gudu Baffa ke yi a dokinsa dan haka yake ji a jikinsa mahaifarsa babu lafiya.



A kwana kuwa ganin yadda yankin ja'i suka fara zubar da yara da manya ta hanyar saresu da takwabi yasa garkuwan fulanin kwana cewa Sarki Chubado da Ardo
"Ranka ya dade, hakika ba zamu tsaya a shafemu ba tare da mun sa hannu ba dan bamu aikata laifi ba, burin yankin ja'i shine su ga sun shafe yankin kwana, dan haka kowa ya dibo makamai mu gwabza tunda haka suke so" mai Unguwa Ori ya ce
"Tabbas hakane" nan garkuwa ya bada umarnin a dauka takwabi a fara maidawa yanki biyu martani.


Duk wannan tarzoma da akeyi Azima na saman bishiya tana kallo tana dariya, Aziza ganin kisan da ake yiwa mutanen yankinta ya yi yawa ne ya sa ta fadi a ranta "inaaa! Burin Baffa shine ya ga ya mutu ya bar yankinsa lafiya, dan haka dole ne na dakatar da yaƙin nan ta ko wani hanya in ba haka ba, tabbas yau babu sauro da zai rage a yankin nan" ta kalli Hajja dake tsaye tana kalman shahada dan yawancin mutane sun sadakar da zasu rayu ta ce
"Hajja ina jin fitsari zanje gida na dawo" ta karasa fadi tare da juyawa,saurin kamo hannunta Hajja ta yi ta ce
"Aziza bakki hankali ashe ban sani ba?kina ganin yadda ake zubar da jini tamƙar ana ɗibo ruwa a rafin jimulo ne ake watsawa kice zaki koma gida kiyi fitsari? Idan kika bincika wasu a nan har da kashi sukayi a jikinsu,dan haka Aziza yi fitsarinki kawai a jikinki, gwanda mu tsaya ta nan idan har Allah yasa aka gama da sauran kafin a iso kanmu,idan kuma Allah yasa Baffanku ya dawo a kan lokaci to, dan shiyasa nace miki mu tsaya a nan sabida ga hanyar da zai fito nan" Hajja ta faɗa tana kara riƙe hannun Aziza, girgiza kai Hajja ta yi ta ce
"Hajja to ni kin riƙeni babu fa Azima a nan" da sauri Hajja ta ce
"Na shiga uku! Azimaaaa!?"
"Kwantar da hankalinki Hajja bari na je nayi fitsari sai na dubota mu dawo tare"
"To dan Allah Aziza ki kula,ki min alkawari zaki dawo lafiya?"
"Na miki alkawari Hajjata zan dawo lafiya"

1 Comments On AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE
avatar
ubaidah

1 year ago

Reply

The novel is very interesting and entertaining

Please Login or Register in order to submit comment