Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sai da Aziza ta faɗi haka kafin Hajja ta saketa,da gudu Aziza tayi hanyar gida dan ta shirya ta dawo ta tare yaƙin.

@@@@

Haka Baffa ya shigo yankinsa ya samu gagarumin yaƙi, amma da shike baya da lokacin tsayawa gida ya wuce kai tsaye ya haɗa maganin furen surfa, sannan yaje ya kirawo Hajja a inda ya ganta sadda ya shigo, amma ita bata gansa ba, yake tambayarta ina Aziza da Azima? Hajja ta ce
"Aziza tace min zata zo gida ba mamaki tana kewaye cikinta ya tsure sabida wannan tashin hankalin,Azima kuma ban ganta ba dan Aziza tace min idan zata dawo zata dubota su sameni a can"
Baffa ya ce
"Boye a can,ni kuma zan boye a nan karki kuskura kiyi magana kinji ko?" Hajja tana shirin tambayar Baffa me yake son yi ya ce
"Jumala karki tambayeni komai! Zaki ganewa idanunki!ke dai kiyi abunda na sakaki! Yaƙi kuma inada yaƙini a kan garkuwa zai tarewa yankin kwana tunda yasa hannu kafin na gama wannan binciken da zanyi, dan haka karki tambayi komai kawai je ki boye,kuma karki kuskure ki fito" Hajja ta amsa da to, maganin da Baffa ya haɗa ya kewaye kofar shigowa gida da shi, sannan ya zuba wani ya koma ya maqale, Azima dake kwance a jikin bishiya haka kawai taji kamar an tsikareta saurin saukowa tayi a saman bishiyar idonta ya kara canza kala nan ta nufa hanyar gida ba tare da tasan dalilin hakan ba wanda take ji kamar an saka mata kuran karfe ne yake janta.

@@@

Aziza ce ta fito daga kewaye idonta jajur alama ce na taci kuka, tana fitowa ta shige bukkarsu, Baffa dake maqale ta zanar kofar waje ya hangi Azima na tahowa tana layi, tana zuwa zata shiga gidan da aka yi wani sama da ita aka bugata da kasa, yayinda taji ko wani fata ta jikinta na mata zafi, ihu ta saka tana rirriƙe jikinta, ta kafarta ta fara rikidewa, wani wawan zare ido Baffa ya yi,yayinda yayi sumar wucin gadi, wannan shi ake kira tashin hankalin da ba a sa masa rana.


Aziza kuwa shiryawa tayi dan taimakawa yankinta ta zo fitowa kenan har ta sa kafa akayi sama da ita ma, ihu ta saka ta fadi kasa wanwar, girgiza kai ta hau yi jin yadda jikinta ya amsa tana shirin rikidewa ta koma macijiya,cikin dimauta take furta "furen surfa na macizai? Wa ya kawo ya zuba a kofar gida? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! a'a a'a a'a!!" bata bari hakan ya faru ba ta shige bukka da gudu, Hajja dake kallonta ta zaro ido waje,to meke faruwa da yarta ga Baffansu yace karta fito? Anya zata iya kuwa ba zata fita ta je ta duba me ya samu Aziza ba? Hakuri dai ta yi amma hankalinta na kan Aziza, Aziza kuwa tana shiga bukka ta hau kwalawa Inno Fandi kira yayinda fatar jikinta ya koma fari sol, daga kugunta abunda yayi ƙasa ta koma macijiya🐍, cikin matsanacin kuka Aziza ke kiran Inno Fandi har ta bayyana, ta ce
"Na shiga ukuna Inno Fandi furen surfa na macizai wa ya zuba?"


Inno fandi ta ce
"Yanzu za a fara Aziza! Ba kowa bane ya haɗa maganin furen surfa illa Magaji, wanda a halin yanzu Azima tana waje tana rikidewa,ke ma haka gaki nan, a yanzu *BAFFANKU YA GANE CEWA AZIMA MACIJIYA CE!* kece kawai bai gani ba, dan haka ki gaya masa gaskiya dan a san yadda za ayi a yi maganin abun"

"To wani irin maganin abun Inno Fandi? Karshe dai nasan kashemu Baffa zaiyi da hannunsa" Inno Fandi ta ce
"Bana da ikon gaya muku komai, idan har na gaya muku zan iya mutuwa, Magaji shine zai gaya muku, yanzu dai me kike da bukata na miki?"

"Ina so naje na tsaida yaƙin da akeyi ne kafin na dawo ayi ta gida, ki taimaka min na fita a gidan nan" Inno fandi ta ce
"An gama" sannan ta dauki Aziza suka b'ace dan zuwa tsaida yaƙi.



A waje kuwa fadin halin da Baffa yake ciki bata lokaci ne bayan ya farfaɗo daga suman da yayi, a hankali yake tunkarar Azima dake birgima tana ihu jikinta na kan rikiɗewa, rasa abun yi Baffa yayi kawai yasa kuka ya duƙa a gaban Azima, ganin haka yasa Azima b'acewa b'att! A wajan Baffa ya yi zaman yan bori.


@@@@

A wajan gari kuwa sadda Inno Fandi ta fice da Aziza nan Aziza ta b'ace tana kwasar mutanen yankin ja'i tana watsar dasu, mutum na tsaye sai dai yaji an dagasa an wurgasa, idan ta tashi kwasa kuwa sai ta kwasa kusan mutane goma da jelarta ta watsar dasu, mutanen yankin tudu jin sun daina yaƙi da mutane sun koma yi da aljanu ya sakasu fara arcewa suna fadin kaff! yankin kwana ba mutane bane, harkazalika yankin ja'i da suka fara jin jiki su da kansu suka tsare, su Garkuwa gani kawai suka kafin kiftawar ido da bismillah duk yawan rundunar da suka zo sun watse, hamdala suka fara yi suna godiya ga Allah, amma tabbas an kashe musu mutane.


A hankali Aziza ta bayyana ta zama mutum tana ganin mutane kwance a cikin jini yara da manya mata da maza, hawaye ta share gami da kama hanyar gida,tana cikin tafiya Inno Fandi ta kira sunanta "AZIIIZAAA!" cak Aziza ta tsaya, sannan Inno Fandi ta ce
"Idan kinje gida ki tambayi Baffanku Magaji Bawa su waye *BANJU DA BAHULA!*" Inno Fandi tana faɗin haka bata kuma cewa komai ba, da gudu Aziza ta yi hanyar gida,ko da ta isa har yanzu Baffa na zube a kofar gida ya kasa tashi, da sauri Aziza ta dagasa tana kiran sunansa "Baffa! Baffa! Baffa!" a tsorace dan tayi zaton Azima ta yi masa wani abun ne dan zata aika, da kyar Aziza ta kama Baffa ta zo shiga gidan ta ga har yanzu da sauran furen surfa a kofar gidan, ga shi babu abunda zata iya yiwa furen surfan, abu daya zata iya yi shine ta nemi taimakon Inno Fandi, tun kafin ta kirata ma ta bayyana ta kwashe sauran na bakin kofar kafin Aziza ta ja Baffa suka shiga gida, suna shigowa Hajja wacce har yanzu tana maqale ta kasa fitowa bisa da cewa Baffan yan biyu bai ce ta fito ba shiyasa ta ci gaba da maqalewa, ganin Aziza ta shigo da Baffa a hannu yasa Hajja fitowa a kiɗime tana fadin "Subhnallahi! Aziza me ya faru da Baffanku?"
Aziza bata tsaya ba wa Hajja amsa ba illa randar kasa da ta nufa ta dibo ruwa mai sanyi ta watsawa Baffa nan ya sauke ajiyar zuciya yana ji kamar numfashinsa zai dauke, ruwan Aziza ta ba shi da kyar ya karba ya sha sannan ya dafe kansa, sannu suke jera masa ba tsayawa, sai zuwa can Hajja ta ce
"Wai ni kam Aziza kamar dazu na ga shigarki bukka,amma tayaya kika fita a gidan ban gani ba? Ko b'acewa kika yi?" Hajja ta tambayi Aziza ne kawai amma ga mamakinta sai ji ta yi Aziza ta ce "e Hajja b'acewa nayi, sabida bazan iya bi ta bakin kofa ba, Baffa ya zuba furen surfa!" zaro ido Hajja tayi bama Hajja ba harta Baffa da bai gama dawowa dai-dai ba ya ɗaga kai yana kallon Aziza wacce ta miƙe tsaye tana ja da baya tana girgiza kai tare da hawaye mai ban tausayi tana fadin
"Gwanda ayita ta kare, yau zaku san wani irin yara ku ka haifa, Hajja Baffa kuyi hakuri hakika baku haifi mutane ba, Baffa na san da hannunka zaka kashemu bayan kasan mu ɗin su waye! Na san ka gama gane Azima nice kawai baka gane ba,bazan iya munafurtanka ba Baffa!" da sauri Hajja ta miƙe tana fadin
"Me kika faɗi ne haka Aziza!"

"KARKI MATSO INDA NAKE!!" Aziza ta fada da karfi, Hajja ta ce
"Sabida me Aziza? Nifa mahaifiyarki ce!" tana fada tana kara tunkaro Aziza dake matsawa baya, rintse ido Aziza ta yi ta buɗe ta haɗe rai cikin daga murya ta ce
" *SABIDA NI MACIJIYA CE! AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE!*" Aziza ta faɗi tare da komawa Macijiya! Wani mahaukacin kara Hajja ta saka tare da yin baya-baya ta faɗi timmm! A kasa, ganin haka yasa Aziza komawa mutum ta yi kan Hajja tana jijjigata tare da ambatar sunanta,amma ina Hajja bata motsi numfashi ya tsaya cak, cikin kuka Aziza ta ce
"Hajja ba dai hadiye zuciya kikayi ba!? Na shiga ukuna Baffa!!" Aziza ta fada tare da juyowa wajan Baffa nan ta ga ashe shima ya suma! Randar ruwan kasar gabadaya Aziza ta dauka ta juye a kan iyayenta, da kyar suka saki ajiyar zuciya, suna dawowa Aziza ta ce
"Baffa waye su *BANJU DA BAHULA!!!?*" wani zabura Baffa ya yi yana kallon Aziza, da sauri ya miƙe tsaye ya ce
"Dole kafin nasan abunda ke yawo a jikinku saina haƙo abunda bana son haƙowa, Aziza na fahimci ke ba kamar Azima ba ce, da ace ke kamar Azima ce yadda muka suma da kin kashemu! Na sha zargin Azima na son kasheni amma naki ba wa shaidan damar da zai saka min waswasi a zuciyata a kan 'yar da na haifa ta cikina! Dan haka zan gaya miki waye Banju da Bahula da abunda ya shiga tsakanina dasu, amma kafin nan zo muje jejin firi"


Saurin riƙe hannun Aziza Hajja tayi idonta jajur ta ce
"Ya isa haka Baffan yan biyu! Ka sha saka rayuwarka a hatsari ga shi yanzu ta shafi yarana!" Hajja ta fashe da wani matsinacin kuka tana zuba guiwowinta a kasa, da sauri Aziza ta kama hannunta, ko kaɗan Hajja bata ji tsoron Aziza ba, cikin kuka ta ce
"Macizai! Macizai! Macizai! Ni Jamila na haifi Macizai! Inaaa ba zai yu ba ni kawai a dawo min da yarana!" Hajja ta kuma sa kuka bai tab'a zuciyar mai sauraro, rungumeta Aziza ta yi cikin tausayawa domin kuwa Hajja abun tausayi ce ita da Baffa, fita Baffa ya yi yaje ya kirawo Arɗo da Yawuro, da Inna Wuro, da kuma tsohon sarkin kwana wato Baffa Mandi, bai boye musu komai ba ya gaya musu komai, hakika hantar cikinsu ya kaɗa fiye da tsammani, Arɗo ya ce
"Lallai kuwa idan har Banju ne ya dawo daukar Fansa! Kisa bai ma yi komai ba kenan! Ashe kuwa idan ba a dakatar da Banju ba idan har shine sunanmu toka" Baffa ya ce
"Bazan bari hakan ta faru ba, yanzu daga nan jejin firi zamuje nida Aziza, zanje na haƙo kayana dan nasan taya zan taimaki yankina da kuma yarana" Baffa Mandi ya ce
"Magaji!? Hakowa fa kace? Aljanu da mayu ayi yaya dasu?" Arɗo yace
"Buhun bala'in Banju gwanda haƙo aljanu da mayun da Magaji ya kulle, dan ba karamin babban shaidani bane Banju! Ko ka manta b'arnan da Banju ya yi kafin Magaji ya kashesa?"

"Taya kuwa zan manta Arɗo? Bayan dukka ahalina Banju ne ya kashesu!"

Baffa wanda ke goge gumi ya ce
"Aziza tana tare dani, dan haka yanzu a gayawa su sarki Chubaɗo halin da ake ciki, sannan a cewa yara da manya kar wanda ya fito ko da kofar gida ne, domin kasan aljanun da aka ɗaure duk wanda ya samu damar guduwa zai fito ne da haushi da b'acin rai na dauresa da akayi na tsawon shekaru, dan haka duk wa inda suka samu zasu bugesu ne, Yawuro, Inna Wuro ku kula da Jumala, Aziza muje" Aziza ta amsa da to Baffa a sanyaye abun tausayi, zasu fita Hajja ta kuma sa kuka tana salati dan ita kadai tasan abunda yake damunta, su Yawuro da Inna Wuro suna dannarta, yayinda Arɗo yace bari yaje wajan Chubaɗo su zanta a kan lamarin.



🐍🐍🐍🐍


B'acewar Azima jejin hayi ta nufa tana kan ihu fatar jikinta na mata zafi sosai,zubewa tayi a kasa tare da furta "KARYANKA! NACE KAYI KARYA MAGAJI! FANSA NE DAI SAI NA DAUKA! AMMA NA RASA MEYASA KAKE GALABA A KAINA TUN TSAWON SHEKARA ASHRIN! YANZU MA SO KAKEYI KA SAKE KASHENI! INA HAKAN BA ZAI YU BA, DOLE NA MAKA MUGUN TABO! TA HANYAR CI GABA DA RAYUWA A GANGAR JIKIN 'YARKA AZIMAAA!!"

Wannan murya na gama fitowa ta b'alli gashin kanta tasa a baki nan taji sauƙin raɗaɗin, sannan ba tare da bata lokaci ko dogon tunani ba Azima ta dauki hanyar barin Al'karyan yankin kwana dan ta shiga cikin gari ta cika burinta na tarwatsa jama'a da hanasu kwanciyar hankali.



🍃🍃🍃🍃


Baffa da Aziza suna isa jejin firi ba bata lokaci Baffa ya fara haƙo abunda ya binne, yana gaff da gama cirowa ya kalli Aziza ya ce
"Kin shirya?" Aziza ta gya ɗa kai gami da cewa "e Baffa a shirya nake"
"Fara" Baffa ya faɗa,yayinda Aziza ta daga hannu sama ta fara haɗa wani baƙin guguwa mai cike da rami dan tare mayu da aljanu ya kasance ko da zasu gudu kaɗan ne, da karfi Baffa ya fizgi wani abu kamar irin akwatin karfe na tun tsawon wasu shekaru, yana fizgowa take wani mahaukacin guɗa ya tashi, wanda ba iyakar jejin firi ba dukkan jeji sai da ya amsa tare da dukkan mutanen yankin kwana babu wanda bai ji wannan gudar ba, Aziza na tsaye sai haɗa zufa takeyi yayinda take riƙe da wannan baƙin guguwar wanda ta riƙe aljanu da mayu, ganin halin da take ciki da sauri Baffa ya buɗe akwatin wanda da ka gani kasan ya daɗe ya dauki guru da layarsa ya maida (Allahu Akbar Baffa an tuno baya) duk wani abu da Baffa ke amfani da shi sai da ya dauka,na ɗaurawa ya ɗaura na sakawa ya saka, na mannawa ya manna, ya fiddo wani tulu mai murfi, yana fiddowa ya sake kama wasu aljanu da mayun ya rufe yayinda wasu suka gudu, Aziza na sakewa ta zube sumammiya, Baffa bai damu da sumar da tayi ba dan na hucin gadi ne, ta ma yi namajin kokari, dan ko shi iyakar abunda zaiyi kenan,kuma dabadin ita ba da yana haƙo abun nan ba tare da an rikesu ba bala'in da zata kunno yankin kwana sai Allah.


Baffa na ciro kayansa ya haɗa wasu taurari guda biyu wanda suke kamar dutse mulmulen laka, sunan Azima da Aziza ya rubuta a kai, nan wani haske ya bayyana, na Azima ya fara gani, nan ya hangi Banju a gangar jikinta, Azima a sume take, wasu hawaye masu zafi ne suka wanke wa Baffa fuska, sannan ya duba taurarin jikin Aziza, nan ya ga Bahula ce ke rayuwa a jikinta, sannan ita an maidata Macijiya ba wani ke rayuwa a jikinta kamar Azima ba, cikin ruɗu da tashin hankali Baffa ya watsawa Aziza wani farin kasa nan take ta sauke ajiyar zuciya ta farka, ya ce
"Aziza muje gida" girgiza kai Aziza ta yi ta ce
"Baffa ba zan je gida ba har sai ka gaya min waye Banju da Bahula" Baffa ya ce
"Yanzu kuwa zan gaya miki Aziza, yau zan baki labari"



🍃🍃🐍🍃🐍



*Tabb cakwakiya! Shin ya zata kaya ne? Idan Baffa ya ba wa Aziza labari taya za a rabasu da wannan bala'in? Ga shi Azima ta bar yankin kwana ta do shi hanyar shiga gari,Dukkan wasu manya tambayoyi yana sauran shafuka da suka rage a gaba, naira darinki ya isheki! Idan kuma kika jira cmplt dari uku.
Karku bari ayi babu ku.*
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

COMMENTS AND SHARE
BY MOMYN AHLAN

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE
avatar
ubaidah

4 months ago

Reply

The novel is very interesting and entertaining

Please Login or Register in order to submit comment