Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

malam, musamman Daya ga dukkan dalibansa sun taru suna kallon su,hakan yasa yafara ball da duk wani abu dake tsakar gidan yashiga sababi.Nan fa gida ya kacame,inda Yana Fadi matansa na Fadi,abinda Bai taba faruwa ba a tarihin aurensu,hakan yasa wasu daga cikin yaran suka ruga suka kirawo wasu daga cikin abokan malam dake zaune kofar gida.
Sam ba Wanda ya lura da sulalewar maryam,tsawon lokaci ana fama da malam da matansa suyi shuru amma Abu ya faskara,shi yanaso su fahimci gaskiyarsa su yadda baida wata alaka da laraba,su Kuma sunki amincewa.Zuwaira ce ta mike tana fad'in,ai wallahi tunda kaki sakinmu to daga Kai har amaryar taka inta shigo zaku gane kurenk......" Maganar ta makale ganinta ta shigo famkam-famkam,aikuwa da matsiyacin gudu Zuwaira ta shige dakinta ta banko kofa,yayin da salame tace"ke kuma lafiya Kika wani shige d'aki ko ya tsorata ki ne da idanu,to Ni yanzu Sam kallonsa baya firgita ni,Dan Haka Bari na karasa abinda Baki fada ba,idona idon laraba wallahi sai dai buzun t........" Itama ta kasa k'arasawa ganin an budawa laraba hanya ta nufo ta.
Wata irin k'ara ta saki tana fadin"na shiga uku malam,badai aikawa kayi aka kirawota ba,muna Nan muna tsara yadda za'ai muyiwa dakin da zata zauna saukar kur'ani ,shine ka aika a kirawota salon ka wahalar da amarya,sannunki da zuwa amaryar mu,yanzu nake cewa idonki idona saina gode Miki bisa dawainiya da malam" ta karasa maganar tana me karkade tabarma Dan laraba ta zauna.Aikuwa hankam-hankam ta shiga washe baki,ta juya ta nufi gurin Zama,Dan dama Maryam ce taje tace Mata Wai tazo malam nason ganinta zai musu nasiha,shine fa ta debo jiki ta taho,Dan Koda ta fadawa uwar cewa tayi taje kawai,inma ba matsala tayi zamanta sai su biyota da kayanta a daura aure da la'asar,ita duk Bata fahimci ma abinda matan malam din ke fada ba,shiyasa take fara'a, musamman data gansu duk Ahlin gidan a had'e hakan ya k'ara tabbatar Mata da gabatar musu da ita zaiyi,"kaiiii gaskiya malam d'an soyayya ne" ta furta a zuciyarta........



_Idan naga comment dayawa zaku Kara birgeni,sannan ga Wanda ke cikin group Dina,bazan gaji da shara ba,domin duk wadda Naga ta karanta babu comment ko tana zaman labe to zata jita a waje,sannan duk group din da kukaga na daina musu posting,to basa comment ne,Dan haka kada aga laifina Kuna Raina masoya._



*Alakamin khady* ✍
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€ πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*NΓ€*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )



*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


2⃣6⃣-3⃣0⃣


🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣
Gaskiya na Dade Banga comment din Daya dinga bani dariya ba,kamar jiya da yau,Ashe Haka laraban malam keda masoya,to muje zuwa danjin yadda zata Kaya.

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
________________________________

Ji malam yakeyi kamar yayi hauka yau,Dan inya juya suka hada ido da laraba saita sakar mishi wani makahon fari,Wanda ke Kara sashi yaji wani yarrr,idan Kuma yakai duba ga inda take zaune yaga yadda ta mamaye fiye da Rabin tabarmar Saiya ji gabansa ya fad'i,Dan Haka ya kasa cewa komai,illah laraba daketa zuba mishi murmushin soyayyaπŸ™Š.

Suna a Haka Zuwaira ta Dan bude K'ofa ta leko,Dan taji batajiyo ihun kowa ba,hakan yasa tace Bari ta fito taga meke faruwa.Ganin Maryam dare dare bisa cinyar laraba daga fitowarta ta kasa hakuri tace" na shiga uku,ke laraba nono kike Shirin Bata kome? Wannan shi ake Kira tayani kallon lalle a duwawu,inba Haka ba,ai gara kice a kaiki gidan marayu in nonon ne yayi Miki nauyi kike son ragewa,saikije ki rabar wa marasa iyaye sadaka,amma ba kizo ki dauki tsohuwar yaye ba kice Zaki shayar da ita".

Tunda ta Fara maganar laraba ta tsareta da ido,sannan ta Fara yinkurin sauke Maryam ta shiga kiciniyar mik'ewa.D'an autan malam ne yace" wallahi baba Zuwaira ki gudu,in laraba ta kamaki alkur'an dukan tsiya zatai miki,Kuma babu me iya kwatarki daga baba har babarmu gara ki gudu kafin ta mike".

"Ba inda zani,ita harta Isa tazo har gidan mijina tace zata dakeni wallahi da saina b'ara Mata Kai gida biyu "ta fad'a tana rarumo k'atuwar tabaryar da suke surfe da ita.

Itako Laraba,Sam hargagin Zuwaira Bai tsoratata ba,Dan Haka ta mike ta nufeta yayin da Zuwaira ta tattale ta d'aga tabaryar tana fad'in" kina k'arasowa Ina sauke Miki ita".Ganin da gasken zuwan zatayi yasa malam daka musu tsawa duka,tare da umartar kowacce ta dawo ta zauna.Cike da salo laraba ta juyo ta Fara bada wani taku Wanda take ganin zai jawo hankalin malam ji kake taffff,taffff,taffff.Malam baisan lokacin da yayi baya ba ya dafe bango Yana Kiran astagafirullah,saboda ganin manyan Kaya,yayinda ya dinga kallon matansa kamar wasu 'yan daudu,Dan gani yayi kamar halittun matan k'auyen aka hadowa laraba duka gaba da baya.

Malam labaran ne ya shiga fad'in" subahanallahi,malam yi a hankali kada ka Fadi,yakarasa maganar Yana me kallon bayan laraba,a zuciyarsa Yana ayyana sai an Dora bokin ruwa ko kwarya ta zauna das a bayan laraba saboda tudun mazaune,"Masha Allah" ya furta a fili.

Shikuwa malam nuhu Yama kasa motsi,illa ido Daya zubawa kowa a gurin,sai daga baya ya k'arasa ga malam din shima Yana tambayar lfy?,Yara kuwa duk suna Nan sun Sami t.v suna kallo.Ganin da salame tayi Zuwaira nata sababi shiyassa itama ta shiga nata sababin suka hadu gaba Daya.


Da dai akaga za'a Bata lokaci Nan malam yace kowacce tasami guri ta zauna zaiyi magana.Dan tsabar biyayya irinna laraba dukawa tayi,ai abinka da ba'a sababa take Taji kamar ta tsugunna Kan k'aya,Dan yadda kafafunta sukayi mata,batasan lokacin data sulale ba tana haki.

Bayan kowa ya nutsu dan har abokan malam suna Nan sannan yayi gyaran murya kafin yakai duba sa ga Maryam yace ta zo,.Kowa yayi tunanin bazata iya zuwa ba,amma kawai sai gani akayi taje gabansa ta tsugunna.

Kallo yaci gaba da binta dashi kafin yace"Maryam"

"Iyi" ta amsa

"Hmmmm" yace ya girgiza Kai yace "kina kaunar Allah da annabinsa?"

"Kaiiii sosai ma,Allah yasa Annabi ya ceceni" ta furta tana washe baki.

"Ai kuwa bazaki taba samun ceton ma'aiki ba muddin baki Fadi gaskiyar abinda yake faruwa ba,Dan koma menene,to kece silar komai bakar munafuka"

Hade fuska tayi jin ya kirata da munafuka,aikuwa saita kalli gefe tana gunguni.
Nunata yayi da yatsa Yana fadin"wannan, wannan da gani uwarki tana zunduma ashar ta haifoki,Dan duk yaron da aka Haifa da Bismillah,bazaiyi abinda kikayi ba,Ni ba'ama taba kawomin makurar kangararru ba sai ke,Dan Haka ko ki fadamin gaskiya ko in tattara ki in maida ki gurin ubanki,tunda ba Dole sai a kanki Zan Sami lada ba".

Jin yace zai maidata gida in Bata Fadi gaskiya ba,yasata Fadi a zuciyata"aikuwa wallahi bazan Fadi giskiya ba,tunda in ban fada ba za'a kaini gida,inje inci uban ummita Dan na rantse saina daketa".kawai sai gani sukayi ta mike ta rike k'ugu tace "yehhhh!

Wani takalmi dake kusa da malam ya rarumo zai jefamata malam nuhu yayi saurin karbewa ya shiga bawa malam hakuri,ita Kuma akace ta zauna.

Bayan ta zauna malam ya Kara had'e Rai yace" Zaki fad'a kowa yaji gaskiyar zance kokuwa?"

Gyara Zama tayi, tai Zaman rak'uma sannan tace Zan fad'a yanzu kowa yaji,idan Kuma nayi karya a tambayi Anty laraba".Duka matan malam da harara suka bi laraba,sannan sukace "yauwa 'yar albarka yarinyar kirki Mai gadon fadan gaskiya,maza fad'i a gaban kowa yaji abin kunyar da malam yayi,Dan mun San bazaki yi Masa karya ba"

K'ara muskutawa tayi sannan tace" dama um rannan ne da malam ya kirani yace Wai babana yace baida kudin dazai aikomin,amma shi ba matsala in Ina bukatar wani Abu in tambayeshi,sai nace Masa to Zan dinga tambayar ku in baya Nan,shine yace Wai ah'ah kada na tambayeku bazaku bani ba ko na tambayeku Dan son kudi Ne daku,shine na tashi Zan tafi yakirawo ni yace Wai idan nasan wata 'yar bazawara k'atuwa a garinmu inyi Masa kwatance zaije,Dan ya gaji da ganinku a bushe,shine fa nace Masa Ni duk wadanda na Sani a garinmu sirara ne,shine yace na tafi.To bayan kwana biyu sai ya kirani yace Ina zani nace Masa gun laraba inci danmalele,shine yace dama Yana nemana zai aikeni gurinta,Wai idan naje ince yace Yana sonta,shine na fada Mata daga Nan ta amince take kawo Masa abinci kullum ko Anty laraba?"

Ta nuya akalar tambayar ga laraba,wadda sanyin Dadi yasa Banda murmushi ba abinda take zubawa,Wanda inba ka k'ura ido ba bazaka fahimci ma bakin nata bude yake ba,Wai Kuma har tana murmushi.Jin tambayar da Maryam tayi Mata danta k'ara burge malam,Dan gani takeyi duk ya shirya hakan ne cikin salon soyayya,Dan Haka ta lankwashe harshe da kashe murya tace"gaskiya ne,shiyasa ma nake sa masa onga a dukkan abincin da nake yimasa,danya cemin Yana son onga".

Wannan karon kam malam ashar din gaske ya lailayo ya mike su malam nuhu suka rik'eshi Nan ko ya shiga fizge-fizge Yana son kwacewa,Dan shima ji yakeyi kamar ya kashe Maryam koya huta,Dan Haka ya shiga fadin"ku sakeni ala gafarta,ku barni in kakkarya yarinyar Nan inkira iyayenta Suzo su dauki gawar ta,Anya ma kuwa wannan yarinyar mutum ce,inko mutum ce da ganinta ba yarinya bace wallahi rikakkiyar wada ce kirar da can,Dan mu yaranmu na Nan Basu Isa su wassafa wadannan zantukan data fad'a ba".Yana kokarin Kara fizgewa sukaji hayaniyar mata duk kowa ya juya ga kallon bangaren da suka ji,suna jiran masu shigowa.

Wata kyamu shasshiyar tsohuwace ta daddage ta rangada guda tana sannan tace"Alhamdillah yau nagodewa Allah Daya nunamin wannan ranar,jikata zata amarce,Dama nayi alkawari Ni zanyi Mata gara,Dan tunda laraba ta Fara girma nake tarin kayan gararta,Dan so nake duk mijin Daya aureta yasan ya auri 'yar gata,yanzu uwatata ta aikemin laraba tayi miji Kuma mijinma na gwadawa sa'a wato malam Shu'aibu Mai abin mamaki,Dan Haka muka tattaro duk kayanta gasu Nan mun kawo,inya so tayi zamanta har zuwa ranar da za'a daura aure,kaga kafin ranar ma tasaba da matan ka an k'ulla zumunci,in Kuma yanzu kake bukatar a daura mu ashirye muke" ta karasa tana Kara rangada uwar gud'a,wadda tasa duka matan malam hasala suka juya suka kalli malam,Sai dai me? Leme suka ga malam Dan tun maganar tsohuwa ta farko ya sulale ya Suma,nanko laraba ta tare kayanta,yanzu Haka ma kansa Yana cinyar ta tana yarfa hannu da matso kwalla.........




🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣


*Gareku team laraba*
*Team Maryam*
*Team matan malam*

_A kafta_

*KU bani comment kuga posting,KU hanani kuga d'an Karen dankarewa* πŸ˜‚

_mura nakeyi,irin Mai gigita mutum din Nan shiyasa na kasa katabus_ 😩

*Alakamin khady* ✍
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€ πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*NΓ€*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )



*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


3⃣1⃣-3⃣5⃣



_wallahi jiya da yau na Kuma Shan dariya,Naga alamar akwai masu halartar bikin malam da laraba_ 🀣🀣🀣

Masha Allah Ina yinku fans Dina fiye da yadda ma kuke yina😘

*************************

"Yau na shiga uku Ni salame,me Zan gani haka? Dama idan kaje zance akan katifar gargajiya ake d'oraka,wayyo ni Allah dauki Raina na huta da ganin wannan abin kunyar,ga 'ya'ya ga jikoki amma malam nashe-nashe akan cinyar mace Ku tayani gani jama'ar musulmi".ta karasa maganar tana d'ora hannu aka tare da razga sabon kuka.Itama zuwairar nata jidalin ta Fara da Kuka,Nan ko jama'a suka Sami abin kallo hatta 'yan kawo gara.

Kukan laraba ne ya k'ara jawo hankalin kaka tace"mun shiga uku,daga maganar aure sai takaba,aikuwa Koda malam ya mutu laraba takaba tahau kanki Dan sai kinyi Masa kin Sami wannan ladan".Jin an ambaci malam zai mutu yasa laraba canyarewa da kuka,Wanda yayi sanadiyar farfadowar malam,Dan ji yayi kamar an busa Masa usur a kunne.Wata kyakykyawar mik'a yayi,danshi ya d'auka duk abinda ya faru mafarki ne,jin kansa a lallausan filo yasa ya dad'a bankarewa Yana addu'ar tashi daga bacci,tare da wage Baki Yana hamma yasa hannu ya rufe Baki Yana shirin mikewa idonsa ya sauka Kan Zuwaira dake huci.Ganin hakan ne yasa yafara karewa kowa kallo Dan tabbatar daba mafarki yakeba.k'okarin ja baya yakeyi yaji ya dunguri abu da sauri ya juya aikuwa sai ji yayi laraba tace, "Alhamdillah gishirin zuciyata Allah ya karbi addu'a ta Dana dinga yi cikin zuciyata,wallahi malam daka mutu yau Nima mutuwar zanyi" ta k'arasa maganar tana marmari da ido alamun kuka.

Maryam dake gefe tayi caraf tace"in Allah ya yarda ma bazaku mutu ba saikun haifi Yara 'yan lukutaye inta taba musu kumatu ana Mana hoto a irin wayar babana".Wata irin fyaud'a malam yakaiwa Maryam Yana daga zaune,aikuwa ta goce ya maki kasa,a zuciye ya shiga fad'in"wallahi Maryam idan Kika shiga hannuna sainayi gunduwa-gunduwa dake"

Tana dariyar shakiyanci tace"kaga ko sai ayi miyar biki Dani,ransa ne ya Kuma hasala ya k'ara yunkurawa Yana fad'in" wannan wadar yarinyar kisan gilla shi yafi dacewa dake a halin yanzu".

"Haba masoyi"yaji laraba tace, kalmar data sashi makalewa jikin bango,itako tana matsowa tace"Ni bana son kayiwa Maryam komai,dan 'yar arziki ce,Ina sonta,in munyi aure ma gurina zata dawo da Zama ko darling?"ai Duka muatanen gurin kowa baisan sanda ya rungume Dan uwansa ba Jin kalmar da laraba ta Kira malam da ita.Shiko malam tsayuwar da tayi akansa ne Saiya ke ganin kamar giwa ce tayi Masa rumfa,Dan son ta kauce ya shiga furta"kwarai kuwa ai gurinki zata zauna" Jin dadin kalaman malam yasa laraba muskutawa ta zauna a gefen sa batasan da hannun malam a gurin ba,Dan inda ta yanka zata zauna ta dauka bazata kusanta kwarai dashi ba,ai kuwa ji kake kurusssss🀣hannun malam yayi k'ara yayin da malam ya kwalla wata siririyar k'ara,itako Laraba Fadi take,"oh Kunga na zauna akan Kara ban lura dashi ba",ta fada tana muskutawa gefe Dan Jaye Karan,aikuwa tayi ido biyu da hannun malam Wanda malam din ya zuwa yanzu kwallar azaba ce kawai ke shatata,su kuwa mutane tunda hannun malam yace b'asss kowa ya zaro ido yakuma rasa bakin magana.

Cikin kidimewa laraba ta yunkura ta tashi danta matso gun malam sai ji tayi yace"kina k'arasowa Ina tsine Miki albarka" ya k'arasa maganar Yana yiwa malam nuhu alama dasu zo su d'aga Masa hannun sa.Cak laraba ta tsaya takasa motsi,yayin da Kaka tace" kul 'yar Nan,danki samu albarka muka kawoki gidan nan,Dan Haka duk abinda yace kada kiyi to ki bari,Dan bama fatan kiyi zawarci,Dan Haka zauna Nan idan Nan yake son ganinki" aikuwa sai laraba ta koma ta zauna,yayin da duk ahlin gidan malam dama makotan gidan na sauran bangarori suka shigo,Dan Jin gudar da kakar laraba tayi,yasa sukazo Dan ganin meke faruwa,nan suka iske wannan lamari Suma suka tsaya kallon t.v ,Dan haka kowa ya Kama k'unshe tashi dariyar,Dan hatta matan malam Saida suka Dara wannan karon,duk da takaicin dake cin zuciyarsu.

Inda Allah ya taimaka Malam labaran ya iya ire-iren wadan Nan gyaran shiya duba hannun malam ya tabbatar karaya ce,Nan yace Bari yaje ya kawo kayan gyara.sam malam ma yarasa me zai yi, yau dayasan inda zaiga 'yan Boko Haram ,ba abinda zai hana Bai damka musu Maryam sunyi gaba da ita ba,inyaso yacewa ubanta ta gudu,Yana wannan tunanin ya juya ya kalli barayin da laraba take,yaga yadda ta kwabe fuska kamar taci sabulu,sai Wani kyafkyafta ido takeyi,Dan tunda taji Wai tajiwa malam d'inta ciwo duk hankalin ta ya tashi.dan Haka ta kwab'e fuska tana matsar kwalla.

Koda akazo ana gyaran,Saida aka Kori yara,Dan malam sosai ya zage Yana ihu,Haka itama laraba kukan takeyi iya yinta,su kuwa matan malam Allah ya k'ara kawai sukeyi,itako Maryam tana daga gefe Banda dariya ba abinda take yiwa malam,inya d'an bud'e ido ya ganta,Saiya yunk'ura da niyyar maketa sai rik'eshi,da Haka har aka Gama gyaran,yayin da dangin laraba sukayi jugum-jugum Wanda hakan ke k'ara sa jinin malam hawa,amma Kuma idan yakai duba ga tarin buhunnan da aka shigo dasu,Saiya ji Kuma labari na neman sauyawa.Haka dai aka zauna shiru.


Ganin la'asar tayi Kuma lokacin sallah yayi yasa masu yi suka yunk'ura da niyyar yi,amma matan malam duk suka tattare butocinsu da Kuma kayan ruwansu,suka ce babu Mai tab'a musu.Hakan yasa sauran matan gidan sukace Suzo bangaren su su yi ,amma Kaka tace ai sunfi k'arfin wulak'anci,yanzu zasu Nuna su ba matsiyata bane. A cikin wasu daga cikin wadanda suka rakota tace wata taje ta karbo musu butoci a gidansu Laraba,aikuwa ba'a wani jima ba sai jin tsayuwar mota sukayi a k'ofar gidan,Dan Haka cikin aka shiga kwada sallama Nan Kaka na Shirin yin magana saiga wadda ta tafi kawo butoci ta shiga fadin"a shema Kaka sauri mukayi Dan Ina zuwa na tarar da innar laraban ma ta dawo daga kasuwa wajen siyen kayan gado ana debo kayan tarkacen Kuma a cikin gida,zuwana ba jimawa suka kammala shine muka taho gaba d'aya,a Nuna Mana d'akin saboda maza zasu shigo da kayan katako..........."


🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣


*Team laraba gareku*

*Wai Ina team malam ne,Ku fito a kafta*πŸ˜‚



*Alkalamin khady* ✍
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€ πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*NΓ€*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )



*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


3⃣6⃣-4⃣0⃣



_Idan laraba ke Saku dariya,ni comment d'inku ke Sani dariyar wallahi,gaskiya ba abinda zance muku fans sai godiya, Allah yak'ara k'auna, Duk masu comment wlh Ina gani Kuma Ina godiya kwarai,masumin addu'a ma duk nagode_😘


*************************

Dan tsabar mamaki ma shi malam daina Jin zugi da rad'ad'in ciwon hannunsa ya daina ji.Ita kuwa kakar laraba ta kafa ta tsare tana Nuna inda za'a ajiye kayan, dai-dai k'ofar dakin data zab'awa laraba.Kusan duk kayan tare da laraba aka dinga kiciniyar shigo da su dan zumud'i.Saida aka shigo da kayan kaf,kafin Kaka ta kalli d'ayan saurayin tace" yauwa laminu,Dan Allah in kun fita ka biya gindin gawo shagon haruna me siminti,kace Masa yazo Nan gidan malam ja'afar ana nemansa".

Da "toh" ya amsa Mata yasa Kai ya fice,sannan tasa wasu yaran cikin wadanda suka kawo kayan Suma tace su d'ebo musu ruwa a rijiyar gidan.Haka ko akayi nana da Nan suka cika musu robar sabuwa fil, aka shiga alwala Nan suka shimfid'a k'atuwar tabarma a k'ofar d'akin da suka za'bar ma laraba.Duk kowa da kallo ya bisu,yayin da matam malam suka koma gefe suna gunguni,Dan suna tsoron suce wani abu laraba tabi takansu,Dan sun lura tun d'azu ita kad'ai sai had'a zufa takeyi,da alama jira takeyi ace kule ta casss.

Duk inda suka waiga neman Maryam ba Wanda ya ganta ko yasan inda ta nufa.

***********************

Itako Maryam daga Nan ba inda ta nufa sai gidan su laraba,dayake Babar laraba ta ganeta saita hau washe baki tana tambayar ta ko me akeyi a gidan? Aikuwa Maryam ta karkace duk ta zayyano Mata duk abinda matan malam sukayi harda cewa tai Wai sunce laraba kuncen yunwa ce,gashinan ya Nuna a jikinta Bata samun wadataccen abinci,yanzu Haka ma sunce you bazasu bawa malam tuwon dare ba.

Aikuwa a fusace mahaifiyar laraba tasa aka Nemo Mata Yara,Nan tasasu suka shiga kamo Mata zakaru da kaji,Wanda kusan rabinsu duk na laraba ne da ake Bata,Kuma dayake kiwon ya karbeta sai sukaita yawa ba'a ci bakuma Wanda ya Isa ya taba Mata,wasu su mutu ana gani Amma baza'a yanka ba.

Saida aka kusa kame Rabin kajin,tabawa yaran kudi tace sukai bakin kasuwa gurin Idi Mai gyaran kaji ya yanka ya gyaro.

Yaran Basu wani jima ba suka dawo dauke da gyararrun kajin,Dan yanada Yaran da suke taimaka masa.maryam cewa tayi zataje ta dawo saita kaiwa malam d'in.

************************

Shikuwa malam bayan idar da sallar la'asar Dan wani zazzabi ne ya rufeshi Dan ciwon hannun nashi,ga takaicin abinda ke faruwa ga Kuma matansa da suka rufe idonsu sukaita zazzaga Masa rashin mutuncin da tunda sukayi aure Basu taba Masa ko kwatan kwacin sa ba,gashi yanzu Haka Wai bwasu kawu Nan laraba suna nan suna jiransa Wai maihaifiyar laraba ta aika musu akan shi malam din Yana son ganawa dasu,shi yasa abun ya hadu yayi Masa yawa.

Malam nuhu dake gefensa ya kalleshi Yana nazarin malam d'in,da tun d'azu yaketa faman tunani yace" ala gafarta malam,Wai meye gaskiyar wannan maganar ne, Dan ni abin ya dauremin Kai,domin Naga kamar akwai alamun gaskiya a maganar yarinyar Nan,Dan Inka duba yarinya ce k'arama da batayi giraman da za'ace ta iya had'a irin wannan abun ba,Dan Haka ka fad'a Mana gaskiya musan abinyi mu sallami wadan can dangin turun tun kafin abin nasu ya motsa Dan kasan dai asali"

"Wannan Haka yake" cewar malam labaran,gara ayi duk abinda ya kamata,dan banza bata kai zomo kasuwa"

Jinjina Kai malam yayi wato ma kowa ya yarda kenan ko? Lallai baya raba d'ayan biyu yarinyar Nan Maryam tana da nasaba da jinsin arnan farko,wadanda Basu San ma da Allah ba,Basu tuna mutuwa bare su San da hisabi,Kuma duk yadda akayi daga k'aramar hukumar munafukai yarinyar Nan ta fito,dama ana cewa kano ta dabo tumbin giwa, Koda me kazo an fika,tabbas ya yadda,Dan gashi yau yaga yarinya ma k'arama ta fishi gulma da sharri da had'in husuma.Tabbas yanzu ya lura bashida wata mafita illa kawai ya amincewa auren laraba ,badan komai ba sai Dan shima ya rama karyashin datai,Dan shi ba mutunci ma wallahi a cinya zai karyata,ita kuwa maryam Kiran ubanta zaiyi yazo ya d'auki abarsa,Kai bama ita ba dukkan yaran dake gurinsa kowa yazo ya zo ya d'auki 'yarshi inya so ma yaran su koma fashi da makami ba abinda ya shafe shi,Dan an maida shi matattaran 'yan iska da yarinya ta Fara kangarewa sai a d'auko a kawo Masa,to shima ya kile yanzu ba wadda zai k'ara dauka,Maryam duk ta jamusu.

Baiko bi takan su malam nuhu ba ya fita yana me cije baki,Dan ciwon da hannunsa yayi masa,a zuciyarsa kuwa,Yana kissima yadda zai Kama kashin laraba yai Masa karayar wulak'anci.

A Haka ya fito ya samu kawun nan laraba su biyu.nana yace musu ai shi ya tura a kirawosu Dan Yana son a d'aura auren sa da laraba yau d'in nan.dukansu hamdala suka shigayi,daga bisani yace Yana zuwa.bai wani jimaba a d'akinaa na zaure ya fito da kud'i a hannunsa ya damkawa malam nuhu yace ya k'irga.Koda yagama k'irgawa yace" dubu ashirin ne cif"

Gyada Kai malam yayi kafin yace" wannan sadakin laraba kenan Ina son kaimin walicci"

Batare da gaddamar komai ba ko ya amsa da na'am.

Nan suka dunguma zuwa masallaci,aka Kira liman da Dan sauran jama'a Nan take aka daura auren malam ja'afar da laraba,aka sadaki naira dubu ashairin lakadan ba ajalan ba.


🀣🀣🀣🀣🀣🀣


Tab zamusha biki alkur'an



*Alkalamin khady* ✍
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€ πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*NΓ€*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )



*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


4⃣1⃣-4⃣5⃣


_fans Ni da ku,ba'asan Wanda dariyar zata jigata ba,ku Kuna dariyar laraba,Ni Ina dariyar comment d'inku,gaskiya ba abinda zace,kun bani nishadi dai-dai iyawarku Allah yabar k'auna ya k'ara zumunci amin_



**************************

Tuni labari ya iso cikin gidan an daura auren laraba da malam.Aikuwa Nan k'aramin bala'i ya tashi,domin kuwa su salame rashin mutunci kawai da ruwan bala'i sukeyi.Ita kuwa Kaka Koda haruna me siminti yazo,ce Masa tayi dama fenti suke so ayi musu,ba Bata lokaci ya fad'a Mata kudin,Babu ko neman ragi ta Lalo su a lalitar ta ta damka Masa da cewar yayi sauri fa.yana fita kuwa yaje shagon say Nuna kwarewa irin tasa da Kuma son janyowa kansa kasuwa,harda had'o me kala biyu Kuma na musamman da a ganinsa zai haskaka d'akin,wato yellow da Kuma dark blueπŸ˜‚,Haka ya tattaro yaransa suka d'unguma gidan malam aka hau haramar fente d'akin laraba batare da b'ata lokaci ba.


Duk masifar da matan malam keyi ko a jikin laraba,domin farin ciki kawai ya cike Mata kowanne gurbi na jikinta,babu wata kusfa da bacin rai zai samu zarafin shiga,Dan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment