Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Haka ko kallonsu batayi ba.Ganin Kuma anata fenti ya k'ara hasala su,Nan fa salame ta aika a kirawo yaranta idi da mamuda a can gidan biredi su zo su lakadawa su laraba dukan tsiya.


*************************

A can gidansu Laraba kuwa,duk an aikawa yayyenta dake gidan aure,Jin kanwarsu ta auru duk suka dungumo zuwa gidan,batare da b'ata lokaci ba😳tab ashe laraba ba ita kadai bace hankatamar ba,sai dai duk ta fisu girma,Dan abun kamar bin bi akayi shi,wata tafi wata,to ita laraba sai nata yafi nakowa.

Cikin matan kawunansu laraba wasu masu hankalin ciki suka zo da kyar da lallabawa suka tafi da laraba gida,akan anjima zasu zasu kawota kamar yadda al'ada ta tanada.Da kyar laraba ta bisu Saida Kaka ta lallaba ta tukun.

Bawani mashahurin gyara sukai Mata ba,amma dai a kauye Kam ta gyaru.

Shikuwa malam tunda aka d'aura aure aka nemeshi aka rasa,abinda Basu Sani ba kuwa malam wata hanya ya yanka ya Miki daji,Saida ya tabbatar yayi nisa da gari Kuma ba Mai ganinsa ya labe jikin wata bishiya kawai ya rushe da kuka.Sai da yayi me isarsa yaji har kanshi yafara ciwo tukun yayi shuru ya shiga tunanin hanyar dazai bi ya azabtar da Maryam kafin ubanta ya zo ya d'auke ta,haka kawai taja Masa,'yan kudaden Daya ajiye dan noman bana dazaiyi gashi tasa ya fito dasu,Shidai yasan aure sunna ne,shiyasa ma ya auri har Mata biyu,Kuma harga Allah su kadai sun isheshi,su kadai yaga zai iya ciyarwa da 'ya'yan da Allan ya bashi,amma gashi tsabar rashin mutunci irin na yarinyar Nan,tasa shi auren dole,in ba iskanci ba,ai da alama babanta Mata d'aya gareshi,meyasa Batace ya auri laraba ba sai shi,gashi dama yanada labarin bala'in cin abinci irin na gidansu Laraba da sukayi gado gun babansu,Wanda Koda ya tashi mutuwa sai a akori kura aka dauke shi ga tsayi ga kiba.shi yanzu babbar damuwarsa ba dama ya saki laraba,dan ana Masa kallon mutunci,Yana wa wasu wa'azi akan zamanta kewar aure aikuwa shi yanzu baya Bari asamu wata baraka daga gareshi ba. Tunawa yayi da uwar garar da aka kawo wa laraba,sai Kuma yaji kaso mafi yawa na damuwarsa ya ragu ,kawai bari zaiyi su kusa Gama cinye garar Saiya Fara gallaza Mata azaba da kafarta ma zata gudu.da tunanin wannan mafitar ya goge hawayensa ya nufo cikin garin,inda Yana zuwa ya iske jama'a cike suna jiransa danyi Masa Allah ya Sanya alkhairi, kasancewar sa babban mutum da kowa ke ganin kimarsa.


*********************************

Kusan a gidan malam akayi shagali,Dan kusan Nan gidan dangin laraba suka tare,Wanda hakan yasa suka Dora babbar tukunya,aka shiga shagalin girki.hatta da awakin laraba haka aka kwanto su da kajinta,tace duk gidan malam ta nufa da abinta.

Sai wajen karfe 9pm ma sannan aka samu zarafin Kai amarya,inda sai kaje kudaje haka jama'a suka dunguma gidan malam,yayin da idi da mamuda suke tsaye tsakar gidan suna jiran 'yan kawo amarya Suzo Dan su basu San fa laraba babansu ya auro ba.

Famkam-famkam babbar yayar laraba ta shigo da sallamar ta, dai-dai idi na Shirin Kai duka,aikuwa caraf ta rike hannun Nasa,kamar ta samu gugguru ji kake rumus ta matseshi,Wanda yasa idi sakin ihun azaba.Zuwaira dake tsaye taga meke faruwa,da gaggawa ta shiga kad'a 'ya'yanta d'aki ta rufo har window duk da kuwa zafin da akeyi Bata bar musu ko kofar Shan iska ba.Ganin abinda ya faru ga idi yasa mamuda kallon salame yace,"Inna Wai dama zuri'ar gidan D'an lami k'ato baba ya d'auko?"

Saida ta hadiye yawun takaici sannan tace"ai wadan Nan gara ma d'an lamin dasu,dubi fa yadda ta b'allamin hannun d'a kamar tasami karas,Dan Haka Kai dawo daga baya- baya tunda shi kaddara ta haushi ya had'u da mota k'irar bodi garin karambanin shi".

Ganin yayar laraba tsaye tana huci yasa salame tahowa kamar marainiya tace"sannu Anty,ai Bai zaci Ku bane na dauka yaran da suketa lekowa ne Dan kartar kayan Amarya sunga sabon Abu,ashe kece cikin rashin Sani yakai Miki mazga" Ta fad'a tana karkarwa kamar wadda ruwa ya daka.

"Itako yayar laraba cikin babbar muryarta tace"Ai na d'auka Hari ya kawo Mana dan anwa uwarsa kishiya zai kawo Mana wargi in Nuna Masa ko ni wacece".

Cikin sauri salame tace" Haba shiya Isa,yaron da tun kafin zuwan wannan ranar shi kullum maganarsa d'aya umma laraba,har fad'i yakeyi yaushe wai za'a kawo musu ita Nan gidan shine fa nace Masa yau d'in nan,kin ganshi dayake ba girma saina jiki Wai yazo taryar Amarya,shine fa ya tsaya anan Yana korar yara ke Kuma kikayi Masa wannan cikin rashin Sani".

"Hummm,ya kyauta" kawai tace,kafin ta sa Kai ta shige ta barsu anan,aikuwa kamar jira akeyi ta wuce Nan fa jama'ar kawo.amarya suka shigo duuuuu,wata cikin yayyen larabar itama batare data lura ba tabi takan idi dake kwance,garin zuwa gurinshi aka had'a da salame,Haka aka dinga bibbige su ana shigewa ciki,inda wasu ma takansu suke shigewa,tsabar azaba ma sun kasa ihun,yayin da mamuda tuni ya silala d'akin matarsa yayi luff.


Cikin tsananin azaba salame ta tashi da kyar tana Kiran "idi tashi maza dokunan sun Gama wucewa".Da kyar ya bude idonshi ya kalleta kafin yace,"Inna har an Gama wasan sallar?"Kai dai tashi kawai Idi lallaba inkaika bangaren suwaiba ta gasama jikin ka".

Haka suka rarrafa suka mike har zuwa bangaren matar idi itama Tasha dariya Jin sambatun da mijinta keyi.

*********

A Haka aka jera kayan laraba,ko fentin Bai bushe ba,dakin kuwa yadau haramar warin fenti,Amma ko'a jikinta ,burinta a tafi a barta da malam d'inta,daga gefen dakinta kuwa aka kafa turken awakin ta kusan goma Sha biyu aka jeresu,kajima da akurkinsu aka taho,inda aka jera musu suma nasu gidajen har masu danyen goyo🤣.


Maryam kuwa tana rike da fantekar kaji,taci taci har takai Mata Karo ,Dan Haka ta tafi dakinsu duk ta bawa 'yammatan da sukayi jugum-jugum suna ganin abinda ke faruwa.Kowacce Saida ta karba da aka Bata,sauran Maryam ta d'auka ta rike ta doshi dakin laraba dashi,inda laraba na hangota tajawo ta ta zauna kusa da ita,a takaice dai laraba ba wasu kawaye Maryam ce kawai,Dan auren kunsan na gaggawa ne.Kusan Zan iya cewa laraba ita ta Kori kusan mutanen da suka kawota,Haka dai kusan kowa ya watse aka barta da sauran yayyenta, fad'a suka yi mata akan ta rage wannan rawar Kan Kar malam ya rainata da sauran yaran gidan,Haka dai aka Gama Suma suka Kama gabansu,ko kallaon inda matan malam suke basuyi ba bare su Kai amarya kamar yadda akeyi bisa al'ada.An bar Amarya dai ita da Maryam inda suna fita tace Maryam ta Bata fantekar kajin Nan ta ajiyewa malam inya shigo saita bashi.Koda maryam ta Mika Mata fantekar kaji taga saura kad'an saiko ta shiga tambayar ta cikin masifa wayaci Naman da akayi Dan malam? ,Kai tsaye Maryam tace "ni ce",aikuwa a fusace Laraba ta yunkura tana fad'in,"kin San muhimmancin malam a gurina kuwa Zaki tab'a abinshi,to wallahi sai kin San kin ci Naman Nan"

Murguda Baki maryam tayi sannan tace"Allah in Kika dakeni wallahi saina sa malam ya sakeki"

Jagwab laraba ta koma ta zauna cikin marairai ce murya tace" waya ce Miki dukan ki zanyi,dama zaunar dake zanyi akan cinyata fa,amma tunda bakya so shikenan na Bari ,yi hakuri,inma Bata isheki ba cinye na bar Miki duka ma".

Mika Mata k'aramar fantekar maryam tayi,sannan tace, "ah ah ungo ajiye Masa Ni na k'oshi tana kaiwa Nan ta juya tana fad'in " Anty laraba amaryar baba malam Saida safe"

Wannan karon laraba Bata dakatar da ita ba,Dan dama so takeyi ta tafi ko malam d'inta ya shigo.amma harta gaji da jira ta bingire da bacci.

**********

Shi kuwa malam yak'i zuwa dakin laraba ne Dan ciwon hannunsa,yafi son idan ya warke komai ma ayishi ta Kare,Dan wallahi Saiya karyata ya rantse,Hakan yasa har matansa ba Wanda yake shiga d'akin ta,duk yadau fushi dasu
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀

*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*NÀ*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )



*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


4⃣6⃣-5⃣0⃣

_Hak'ik'a ke d'in ta musamman ce,kamar yadda kike ta musamman a wajena, comment d'inki ya k'ayatar dani sosai nakuma ji Dad'i,tare da addu'ar Allah ya barmu tare.Wannan shafin sadaukarwa ne gareki Hafsat garkuwa besty na kiyi yadda kike so dashi kinji tawan_ 😘


*************************


Abu kamar Wasa,sai ga malam ya shafe tsawon kwanaki Bai ko lek'o cikin gidan ba,sai dai kawai ya aiko musu da abinda zasu d'an yi cefane,dayake ma kun San cefanen k'auye sauk'i gareshi.Dayake garar laraba duk kayan hatsi ne shiyasa ba wani kayan ta'bawa,hakan yasa dole matan gidan in sun dafa su bawa laraba nata,duk da salame dai na bayarwa ne kawai Dan gudun abinda zaije ya dawo.Itakam Zuwaira Dan tattalin lafiyarta ne,haka Kuma duk 'yan mata d'aliban malam suna zuwa gaisheta kullum,harda masu biyo Maryam a d'an tab'a hira,Dan Maryam kamar itace angon ma,laraba ba yadda batayi da ita akan ta zo su dinga kwana ba,amma tace bazata kwana ba,ita Maryam a cewarta indai ta kwana gado d'aya da laraba to kwananta ya k'are, Dan tasan juyi d'aya laraba zatayi sunanta ya Zama marigayiya Maryam.To a fannin 'ya'yan malam dai mamuda ma biyayya yakeyi shida matarsa da yaransa,hakama Idi,to itakam Zuwaira kadaran kadahan,dan harga Allah akwai tanadin datayiwa laraba,Dan saita zaneta ciki da bai d'inta,shiyasa bata nuna wani abu sosai.Itama salame hakan ne a ranta,dan haka haka tayi likimo itama.

*******

Abu kamar Wasa,Saida malam ya shafe tsawon kwanaki bai ko leqo gidan ba,abin yayi matuk'ar damun laraba,inda tasami Maryam a tace taje tabawa malam hak'uri,aikuwa k'iri da muzu maryam sai tace bazata ba sai laraba tayi Mata d'anta malele,Haka zata zage tayi Mata ,inta fita saita dawo tace malam yace tayi hak'uri bak'i yayi ne,Haka kullum laraba ke siyawa malam kayan dad'i tace Maryam takai Masa,aikuwa Maryam tasamu abinda take so,tuni ta dinga cinye abubuwan tana zuwa ta tsarawa laraba kalamai, tace malam ne yace ta fad'a Mata,a haka har Saida 'yan guzirin kud'in da laraba tayo ya k'are,aikuwa ta aika Maryam gidan su.Da farko abar Laraba hanawa tayi,da Maryam ta dawo ta sanarwa laraba abinda Innarta tace,sai laraba tace taje tace Mata in bata bata ba zata dawo gidan wallahi tayi zamanta.Hakan da uwar taji jiki na b'ari ta dauko kud'i tabawa maryam tace takai Mata,gobe ma in sun k'are ta aiko,aikuwa Maryam tasami abin nema,kusan kullum saita je gidan su laraba tace a bata kud'i inji laraba ko ta dawo gida,ita Kuma uwar a 'yar ribar sana'ar da takeyi zata dauka ta bayar tana mita a zuciyarta.Maryam na fita zata tafi bakin kasuwa,itace cin ganda, ragadada, d'an bagalaje,cofe da acama,Kai duk dai kayan kwalama,gashi ta dinga wa laraba wayo tace ta dinga wa malam farfesun kaji kullum zai k'ara sont.Aikuwa ba b'ata lokaci laraba ta shiga kashin kajinta tana dirjewa malam Maryam na kwamushewa a cikinta.


*******************************


*K'URUN KUS*

Yau malam an warke sumul,Kuma yau tun safe Daya tashi yake k'ullawa da kwancewa ta hanyar dazai bi ya karya cinyar laraba,shin wane salo zaiyi Mata ya karyata a shammace,dan so yakeyi taji zafin daya zarce shi Wanda yasha.kasancewar baida lfy tsawon lokacin ba Wanda ya fita karatu,dama jira yakeyi Saiya warke rass ya rama karayar sa,sannan ya Kira uban kowacce ya zo ya d'auki 'yarshi.Ita Kuma Maryam Saiya tabbatar Daya Gama azabtar da ita ta yadda iyayenta ma said sun mance kamannin yadda suka haifeta,sai dai in sun dauko hotonta su tuna,sannan zaice Suzo su dauketa,ko yaje tasha yabada sakonta kawai a kaita gida.Kai Bari ma yakira su tun yanzu,dan a yau yake son ya kaddamar wa da Laraba ita Kuma Maryam gobe da safe,Dan Haka ya shiga lalaubar wayar d'ansa malam Garba,bayan ya d'aga ya sanar dashi ya sanar da mahaifin Maryam gobe Yana son ganinsa da gaggawa,Nan malam Garba ya amsa Masa da toh sannan suka gaisa,danshi baida labarin auren da mahaifin Nasa yayi.

*****************************

Wanka sosai malam yasha,kafin ya baza turarensa irin nasu d'an d'uri mai kamshi.Kan Nan yasha aski ga Kuma gyaran fuska daya Sha,abin gwanin sha'awa.Dan ya kuntatawa matan nasa,bisa yadda suka ki yadda dashi a baya,suka dinga zuba Masa rashin mutunci,Dan Haka ya daura damarar ramawa shima.
Kusan duk Wanda ke cikin gidan yau Kam ya San malam na cikin nishadi, inda ya tattara 'yan jikokinsa,ya raba musu alawa ya Kuma Basu sabulai yace su kaiwa iyayensu Mata,cikin Wanda ake kawo Masa yake ajiyewa.


Sai da ya gama lekawa gaba Daya dakin matan nasa,Wanda dukansu Babu wadda yasami kyakykyawar tarba,in Banda ba'kak'en maganganu,shi dai murmushi kawai yayi ya fice Yana musu sallamar Saida safe.

****

Tun shigowar malam Maryam tayi sauri taje ta sanar da laraba, kasancewar kowacce bandakinta a bayan d'akin ta yake, yasa laraba saurin tafiya tayi wanka,cikin sa'a kuwa harta Gama shiryawa ta bad'e jikinta da turarenta kala biyu,Habiba da balila ,aikuwa saita hau tashin kamshi ga kamshin da dakinta keyi irin na amare😜.

Tunda ya doso dakin ya had'e ranshi,dan so yakeyi ya aro rashin tausayi da rashin imani ko iya na yaune kawai ya gwada su Kan Laraba.Ita kuwa Laraba tana zaune gefen gadonta,yayin da taci adonta cikin shaddarta aikin wuta kalar lemon green light,sannan Tasha bakin mayafinta,abinka da bakin mutum,saita fito tayi dass da ita wallahi, musamman da bakin Nan yasha jambaki kalar anti daba,ga Kuma jagirarata data Sha da jar jagira abin dai zasshawa,kwaliyyarta kirar zamani.


K'asa-k'asa ta amsa Masa sallamar,kun dai gane, irin kunyar Nan ta amaren asali,shikuwa malam kallon gefen ido yakeyi Mata,Yana son ya gano ta fuskar dazai fi samun nasara wajen aiwatar da kudirinsa.Ganin yanayin zaman datayi yasashi murmushi a zuciyarsa,aikuwa ya tattaro duk karfinsa ya had'o tun daga kuruciya zuwa samartaka da tsufa, ya daddage ya tuma tsalle ji kake timmm! Ya tima a cinyar laraba,amma Kuma sai me,ji yayi tana fad'in"subahanallahi malam lafiya? Ince dai ba tuntunbe kayi ba".Ji yayi duk lakar jikinsa tayi sanyi, sakamakon duba da yakai ga hannun laraba yaganshi kwance bisa hannunta kamar ta dauke jariri,ashe lokacin Daya tuma d'in Nan a hannunta ya fad'a🤣.

Wani zunzurutun takaici ne ya ziyarce shi,cike da jarumtar daukar fansa kuwa ya mik'e,ya k'ara buga uban tsalle wannan karon iya karfinsa,nan ma aka Kuma na d'azu sai ji yayi ta cafeshi tana yunkurin kwantar dashi gefen gado kamar wani danta takuma cewa"malam kwanta ka huta,Dan ba mamaki fa jirine ke d'ibarka,Kar kaje ka fadi kaji ciwo sannu kaji bari in kawo maka ruwa kasha"Dai-dai ta Gama kwantar dashi ta mike da kyar ta dauki kofin silba sabo fil ta nufi waje Dan kawo Masa ruwan.

Tsabar takaicin rashin nasarar sa a Karo na biyu,Bai San lokacin Daya Kama fatar hannunsa ba ya gartsa wa kansa cizo,sannan ya saki ya matso kwallar takaici.Yana a Haka ya hango inuwarta tana shigowa,aikuwa sai ya yanke shawarar bin shawara ta uku,ya mike da sauri ya sakko,sai da ya tsaya Nan ma ya tattale kafafu kamar zaiyi dambe,sannan ya saita hanyar Yana jiran ta taho.Itako kanta tsaye ta nufo kofar Dan shigowa,bama ta lura da malam dake tsaye ba,ita dai kawai taga kamar wulgowar abu, kawai sai ta d'an kauce,aikuwa wata iriyar sufa malam yayi waishi a nufinshi ya sai ta Koda dantsen laraba ne ya karyata a kafada tunda yaga tana da makaran Kare Kai a cinya,shiyasa ya kawo wannan farmakin ita Kuma cikin rashin Sani ta kauce wannan sufar da yayi aikuwa ji kake kummm rakwacam,fuskar malam ta daki simintin tsakar dakin,yayin da jerin kwallayen da langunan da akayiwa laraba suka biyoshi suka danne...........



🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣


*Dariyata nafara yi tun yanzu,Dan nasan comment din dazan gani cikina Saiya kusa k'ulle wa Dan dariya.To masoyana Allah yabarmu tare*


_sai kun Kara hakuri da yanayin typing din sai a slow wlh abubuwa sunyi yawa kudai ku Kara hak'uri_






*Alakamin khady* ✍
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀

*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*NÀ*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )



*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


5⃣1⃣-5⃣2⃣


_Ha'kik'a Naga zallar soyayya ga masoyana,nakuma gode da addu'ar ku, wadanda suka Sami zuwar min gaisuwa ma nagode muku sosai da sosai😘_


*************************

Ya ilahi! Laraba ta furta cikin siririyar muryarta da zata ja hankalin malam da ita.Da saurinta ta karaso tana me kokarin d'ago malam d'in,bayan ta kawar da tarin fantekun da suka rikito Masa,malam tsananin azaba da rad'ad'in dayake ji,sunma hanashi yinkurin yin komai.A haka Yana hi har laraba ta d'ago shi.
Tozali tayi da bakin malam dake yoyon jini,gashi tashin farko bakin ya haye yayi suntum,hakan ba karamin daga hankalin laraba yayi ba.Cikin yanayin damuwa ta shiga fadin"na shiga uku malam tashi muje gurin sule me chemist Kar jininka ya k'are".

Malam dayake jin garama ya mutu ya huta,Dan shikam wannan shekarar ya tabbatar a cikinta jarrabawar sa take, Yana Kuma da tabbacin guda uku ce,ta farko zuwan Maryam gidansa,na biyu auren laraba,na uku kuwa mutuwarsa ce,Dan Haka Yana jinta yai Mata banza ya kyaleta,illah kawai idan yaga zata tabashi Sai ya doke Mata hannu,hakan yasa ta fashe Masa da kuka.

Ganin tana kuka ne yasashi cewa "Baki ma fara kuka ba tukun,Dan wallahi saina cika kudirina akanki".ganin bakin malam Yana rawa Kuma gashi Sam Bata fahimtar abinda take cewa yasata k'ara tsananta kukanta tace"nakuma shiga uku bayan wadda na shiga a baya,malam harshenka ya karye harka koma maganar gawa,wayyo Ni larabayye na mutu in malam ya mutu".

Kallon ta yayi da sauri kafin jikinsa yafara mazari,kaddai laraba Mayya ce ta gano Masa mutuwar sa,shi Ina ma yataba Jin wani zance Wai na gawa,to kodai da gaske ne hasashen shi cewar mutuwa zaiyi,shiyasa har yafara warin gawa,shine Dan rashin hausa laraba tace Masa Wai zancen gawa.Da Gama wannan tunanin Nasa,Bai San lokacin Daya zabura ya makale laraba ba,wadda itama ta rik'e shi suka shiga rusa kuka,kukan da kowa da niyyar da tasa yake yinshi.Sun jima a Haka,inda laraba ta mike da kyar ta lalubo minsileta da tasa aka siyo Mata Dan tana shafawa a jikinta inda ke d'an Mata ciwo take shafawa saboda har yanzu gajiyar biki Bata Gama sakinta ba.Aikuwa jambaki tayiwa malam dashi,bayan tafi tudun leben ta shafeshi dashi,Wanda malam ya saduda yanzu badan Allah ba,Koda ya kalli laraba a kaikaice ya banka Mata harara kafin yace cikin zuciyarsa"Hummm ki gama wahalar ki yarinya,kwanton bauna zanyi Miki inta Miki kisan mimmike har saikin rame,duk wannan jikin naki wallahi saina maidashi kamar sillen kara" ya saki murmushi a zahiri,Wanda ya Kara kwab'e fuskar,laraba da karaf a idonta tace" sannu malam,kadaina Kuka haka,bari gobe da safe sai in dafa ruwa in gasa maka wurin sannu kaji mijina"
Dammm! Kirjinsa ya buga,take yaji zuciyarsa tayi Masa d'aci,banda damuwa dayake ciki,daba abinda zai hana shi yiwa laraba d'an banzan Duka ya tattara ta a baro gobe yakaiwa iyayenta,amma yanzun ma Bari ya warke zai Rama ne.

Laraba da kanta ta tallabi malam ta Dora Kan gado,sannan tajawo Masa bargo ta lullube abinta Dan taga Yana rawar sanyi.Shikuwa malam,sosai yaji dadin gadon, musamman da laushin katifa kirar zamani ta ratsashi,ga lallausan bargo da aka luntsume shi dashi,kawai sai yake Jin wani k'aramin nishadi,duk da kudirin dake ranshi na tarin daukar fansa.Laraba Bata Bari malam ya kwanta ba,Saida ta lalubo ciwo takwas ta bashi yasha, Bata San waya yadda shi ba ranar da aka kawota,da har zata jefa shi shara,sai Kuma ta bari dan gudun Kar a aiko cigiya,to gashi ma yayi Mata rana.

Allah sarki baiwar Allah laraba,Sam kasa runtsawa tayi,tana kwance a katifar kasa,Amma ta zubawa malam Ido tana sharar kwallar tausayinsa.Duk abinda takeyi Yana kallonta sai Kuma yaji tabashi tausayi,Dan Haka ya rage yawan hukuncin da zaiyi mata,a Haka har bacci ya kwashe su.
🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅


Tun asuba laraba tafarka danta d'ora ruwan zafi ta gasawa malam fuska kafin ya tafi masallaci.koda ta fito d'ibar ruwa,saita tarar gaba d'aya matan malam ba wadda randarta ke tsakar gidan,komai sun kwashe yau,hatta duwatsun girkin da sukeyi,bare Kuma azo maganar ice.Ashe dai Maryam tayi Mata dabara,da tace Mata jiya ta kawo a siyo Mata kananzir karta yadda ta dinga girki da ice,zatayi warin hayak'i,tunda ita 'yar gata ce,Kuma anyi Mata auren gata,to gara kawai ta nuna itama wata ce,kawai ta dinga girki a risho ta nunawa su baba salame ita wayayyiya ce.Shine ta bayar aka siyo Mata din ta zuba a rishon Dan dama da lagwani a jiki,Ashe zaiyi Mata amfanin kusa Dan a da ta dauka ba amfanin dazaiyi mata,duba da yadda taga tuwon gidan malam nada yawa,shiyasa,amma yanzu ta fuskanta ko a Dora ruwan zafi zai Mata àmfani.

Randarta ta ruwa ta bude ta debi ruwan ta shige d'aki.Cikin kankanin lokaci ta Gama dafa ruwan,ta tashi malam da kanta ta zuba ruwan a wata roba me Fadi,aikuwa cikin hikima da tattali ta shiga gasa malam,Wanda yake jinsa kamar jariri,saboda Jin sabuwar tarairaiyar dayake Samu,aikuwa sai a zuciyarsa tuni ya yanke shawarar karawa laraba tsawon Zama a gidan bayan yagama morewa.Haka ta gama gasa Masa,Kuma Alhamdillah yaji Dadi sosai,aikuwa a gida ma yayi sallar asuba,Dan Bai samu fita ba, Dan har yanzu kansa na Masa ciwo.Dan Haka Yana idar da sallar ya koma ya dada luntsume wa cikin katifar sa mahadi ka lotsa😜 Tuni kuwa bacci yayi awon gaba dashi.Ita Kam laraba bata samu zarafin komawa ba,illa dauko kayan malam datayi Wanda jini ya bata,da kayanta da suka Baci lokacin data rungumeshi,ta zuba a bokiti,tana jiran gari ya ida wayewa a siyo Mata klin saita wanke su.

🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Su kuwa su salame,kusan sa iya cewa cikinsu babu wadda tayi baccin kirki,kowacce ta so ta leko ta ga meke faruwa a dakin laraba,amma Sanin gidan gida ne mutane,yasa ba wadda ta fito Dan Kar taje a ganta,amma Kuma kowacce window da kofarta a hangame suka kwana.Lokacin da sukaji rakwacam din Nan k'arar zubowar kwanuka,kowacce matsuwa tayi taga meke faruwa amma sai suka dinga jiyo nishin malam,hakan ya Kara daga hankalinsu,a takaice dai ba wadda ta runtsa Dan suna son suga Taya za'a kashe arna(d'orawa Kai wahala).

Da farko sun dauka kwashe ruwan da sukayi da Kuma itace da murhu sunyi nasara.Itako laraba wani dan gidan Zuwaira da taga zai fita da bokiti karami zai siyo Koko,shi ta bawa ya siyo Mata klin din.

Kusan a tare matan malam suka fito tsakar gidan,yayin da kowacce ta shiga sabgar gabanta, amma kuma hankalinsu naga ɓangaren ɗakin Laraba,dan ganin me zai wakana.Itako Laraba bata ko bi takansu ba,tana son zuwa ɗakin dasu Maryam ke kwana,amma Bata s dokar gidan ba,dan duk abin Laraba bata da ɗabi'ar shiga shirgin daba nata ba,amma kuma kai inka shiga nata,tofa nanne ake kuturun bala'i,dan danƙarar ka zatayi kamar uwar data haifeka.

A gaban idonsu yaron yabata klin ɗin ta shiga wanke kayan da shaddar ta da ta malam.Sai da ta gama ta shanya duk suna kallonta kowacce idonta ya sauka aka dabbaren jinin daya kama zanin Laraba yaƙi fita,aikuwa nan da nan zuciyar kowacce tayi baƙiƙirin,tare da cin alwashin cima malam mutunci idan ya fito.

Shikuwa malam bai sami zarafin farkawa ba saida rana ta take,ya miƙe da addu'a a bakinsa,yayin da yaga Laraba kwance tana bacci, ƙara miƙa yayi da hamma,dan wata kafirar yunwa yake ji,ga kuma fuskarsa da gefen bakinsa daya hau,dan ma Laraba ta gasa masa jiya,ya kuma ji daɗin gashin,dan tanayi ne cike da salo,ga kuma wani ƙamshi datake yi wallahi.Hararar ta ya shiga yi,a ƙasan zuciyar sa yace ba ƙamshi ba,saina gama zuƙe ƙamshin zan karairaya ki in ƙara dake gaba,ko ba komai ai na ɗan more.Haka yasa kai ya fito waje,ya nufi ɗakunan matan nasa.a zaune ya samesu,duk da suna zamani irin na kishi,amma hakan bai hana yau wani zumunci ƙulluwa a tsakaninsu ba.

Koda yayi musu sallama ba wadda ta amsa masa dan sun hango shi amma basu kalli fuskarsa ba.Jin sunyi shuru yasa shi magana cikin faɗa"wai bakwa ji ne ina muku sallama kunyi banza dani?"

Batare da sun ɗago ɗinba salame tace"kabari ka haɗiye naman daka ƙunso a bakin naka tukun ,inka kammala cinyewa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment