Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma yanaso,daga bisani alhaji rilwanu ya mashi alkawarin idan har da gaske yake zai tambayi itama yarinyar idan taji ta gani tanaso zai daura masu aure sbd ya yaba da halin alhaji Mustapha dukda bai tsaya yayi wani dogon bincike akansa ba. Bayan rabuwarsu alhaji rilwanu ya nemi ganin yarsa labiba domin ya tambayeta idan har itama tana ciki ay kuwa ta nuna tana so, murna kamar ta kashe alhaji Mustapha lokacin da yaji labiba tayi naám dashi kuma zata aure shi anan ya buqaci alhaji rilwanu ya daura masu aure shida labibarsa sannan idan ya koma gida bayan sati biyu idan ya kammala inda zai ajeta sai ya dawo ya dauka amaryarsa. Aykuwa bayan kiran sallar dhuhur aka daura auren labiba da alhaji Mustapha.

Free page….



Chapter 5-6

Alhaji Mustapha kuwa zumudi baisashi ya fada ma hajiya kareema ba saida akayi wata bayan y a gama yan shirye shiryen shi inda ya gyara gefen part din amaryarsa, dama asama part uku ne, na tsakiya nasa ne sai kuma na gefen left side na hajiya kareema saikuma side din inda su abdulwahab ke sauka in suka dawo Nigeria part dinshi ya gyara tsaf sbd amaryar sa don Har kujeru saida ya chanza, Bayan wata cur Alhaji Mustapha ya shirya tsaf domin dauko amaryar sa labiba daga Niger, aranar da zai tafi ya shiga part din kareema anan ne ya sameta tana waya da abokanan kasuwancinta saida ya samu waje ya zauna tukunna ya fara Magana ‘’ki aje wayan nan kareema zamuyi Magana mai muhimmaci,’’ aje wayar tayi sannan tace ‘’ina jinka oga’’ murmusawa yayi sannan yace daman Magana ce zanyi akan aure na, jin haka yasa kareema miqewa tsaye, idonta wiki wiki ta fara Magana, ‘’wani irin maganar aure alhaji haba wasa kake ko? don Allah yanxu da girman ka tsofe tsofe dakai maganar aure kake yi, me kake nufi Kenan” ..kallonta yayi sannan yace ‘’ ay ba maganar aure nake maki ba ay nayi auren ne nake so na fada maki ‘’gabanta ne ya bada daram, ay kuwa tana dagowa me zatayi banda ihu, masifa ihu zagi babu wanda bata gunduma mawa alhaji Mustapha ba daga karshe da yaga abin nata ya zama hauka kuma tanaso ta bata mashi lokaci anan take ya baza malun malun dinshi ya kara gaba, anan yabar kareema da ihu da masifa karshe dai ta koma daki tana bambami.



Alhaji Mustapha kuwa saida ya isa har gidan alhaji rilwanu suka gaisa yaga amaryarshi tukunna ya wuce masaukinsa, kwanan sa biyu ah niger ya shirya dawowa shida amaryar sa, su labiba kuwa ansha kuka sosai sbd rabuwa da yan uwanta, anan mahaifinta rilwanu ya danqa mata sadakinta sisin gwal guda ashirin da alhaji Mustapha ya biya, daganan suka wuce airport tana maqale da mijinta, bayan isarsu kuwa gida direct ya wuce da amaryarsa koda suka isa ranar ya taradda kareema batanan tayi tapiya zuwa turkey domin saro wasu kayayyaki bata san wainar da ake toyawa ba saida suka kwashi sati uku suna soyewa tukunna kareema ta dawo kodata dawo ta tarar da labiba sai taga ay idan har tace zatayi kishi da ita raini ne ma, amma dai da mugunta da kirsa dai saita kuntata mata. Aykuwa anan haka labiba ta samu cikin danta na farko Abdul -kareem inda tana haihuwarsa allah ya amshi abinsa, labiba tayi kuka sosai sbd ta saka rai sosai da cikin nan daga baya kuma allah ya kara bata wani cikin inda ta haifi yarta ta farko kyakyawa Halima suna kiranta da halim, halim nada shekara biyar allah ya kara bata haihuwar da namiji inda aka sa mashi Khalil shima yanada shekara uku ta haifi wani dan nata inda ta saka mashi suna khamis auta.

Hajiya labiba irin matan nan ne masu kyau fara ce ga gashi ga kyau saidai itama fa ba a barta abaya ba wajen makirci, batada matsala da dan kowa amma idan ka shiga gonarta tofa zaka sha wahala sbd ita harda yan tsubbace tsubbace takeyi, tunda tazo gidan ashirye tazo saidai kuma ganin hajiya kareema bata shiga sabgarta ba saita aje makaman yaqi amma duk sanda kareema ta takaleta tofa bata barinta sannan kuma basa shiri kwata kwata da yayan salima musammam abdul wahab da Khadija, bata qaunarsu ko kadan suma kuwa basa sonta basa son yayanta,ayanxu yayanta uku halim 17yrs wadda take ss2, Khalil 10yrs jss2, khamis 7yrs nursery 3). Halim irin yarannan ne sangartattu, tanada son gayu sannan abu qalilan yake bata mata rai amma inka iya zama da ita zakaji dadi, shikuwa Khalil irin yarannan suma da Magana bata damesu ba sai khamis dan cutie sarkin dariya da wasa.

Wannan sune ahalin gidan alhaji Mustapha badaru gambo, to bari muji su wanene amra da kannenta salim da salima, ya akayi sukazo gidan,waye mahaifinsu, sannan su asalin yan ina ne sannan menene taqamaiman matsayinsu acikin gidan.

Free page….





Chapter 7-8



Alhaji Badaru gambo, alhaji badaru haifanfan dan garin katsina ne, anan ya taso agaban iyayenshi da kaninshi alhaji sammani, alhaji badaru mutun ne mai mutunci mai hakuri da sanin yakamata kuma mai son yan uwanshi, su kadai ne awajen mahaifinsu, anan katsina ya hadu da larai wadda ta kasan mace mai hakuri da juriya, shekarar su goma da alhaji badaru allah bai basu haihuwa ba, alhaji badaru bai damu ba sbd haihuwa daga Allah ce, suna zaman lafiya shida matarshi bashida wata damuwa inda alhaji sammani kuwa kanin badaru ya koma kano domin yin kasuwanci anan katsina yabar dan uwanshi badaru, badaru shike kula da mahaifinshi sbd tun bayan haihuwar sammani mahaifiyarsa ta rasu allah ya karbi abarshi, akwana atashi babu wuya shekara wajen goma sha biyar larai babu ciki babu goyo at this point abin ya dan fara damun badaru dukda baya nuna mata cewa ya damu, ana haka har sammani yayi aure ya aure amaryarsa talatuwa inda ashekarar da sukayi aure ta haifi danta santalele inda yaci sunansa Mustapha, Mustapha nada shekara uku allah yayi mashi rasuwa,sammani yaji mutuwar danshi sosai harda yayan shi Mustapha sbd yaso yaron nan kamar dan cikinshi dukda sbd Mustapha sammani ya dawo katsina tare da matarshi talatu ana haka kuwa kanwar talatu wadda take mabiyar ta tazo katsina domin zama tare da yar uwarta anan ne asalin true color din talatu ya fito ganin kasuwancin badaru har yaso yafi na minjinta sammani, gashi bashida da balle jika, ganin haka saita fara kwadaituwa ta gidan badaru asannu cikin ruwan sanyi ta fara zuga sammani akan ya tilastawa dan uwanshi ya kara aure wataqila rashin haihuwarshi daga matarshi ne ba daga shi ba, aikuwa sammani ya samu dan uwanshi da maganar, shidai badaru har yanxu baida wani raayin aure sbd haka ya nuna bai amince ba, ganin badaru bashida niyar kara aure yasa talatu shiga malamai don ganin qanwarta ta samu shiga cikin gidan badaru gashi har lokacin arzikin da badaru yake yi har yaci uwar na sammani nesa ba kusa ba, anan ne Allah yayi ma mahaifinsu rasuwa, bayan rasuwar mahaifinsu badaru ya shiga damuwa sosai ba kadan ba, baya cikin walwala ko kadan daga nan ne kuma ya fara bullo da sabbin halaye na wulakanci, haka dai larai ta daure ta hadiya suna zaman dukda babu dadi, ana haka badaru ya bullo da zancen kara aure, anan ya shaidawa sammani cewa shifa yaji ya gani yana son qanwar matarshi binta, sammani kuwa yaji dadi sosai da kanshi ya nemawa dan uwansa auren kanwar matarshi kuma aka bashi aurenta. Bayan wata biyu aka daura auren badaru da binta kanwar talatuwa, ansha budiri kuwa, duk wannan abun akan idon larai amma bata taba tankawa ba shima kuwa baice mata komai ba, acikin dan zamansu larai ta fuskanci cewa makirci talatu da kanwarta suke shirya wa wadda kanwar talatu har taci uwar talatu ah iya mugunta da wulaqanci ana haka saiga ciki ya bullowa binta, murna farinciki babu wanda badaru baiyiba har Allah ya sauke binta ta haifi santalelen danta inda badaru yayi alkawarin maida sunan marigayi dan gidan sammani Mustapha, anyi suna an kashe kudi sosai ah katsina.,

Yaro ya taso cikin soyayyar ubansa da kawun sa sannan kuma ya taso da mugunta irin ta uwarsa don akan idonsa uwar ke shiryawa larai mugunta iri iri, haka ya taso dai tun baisan me ake nufi da kyamatar mutun ba har ya fara kyamatar larai wato kishiyar mahaifiyarsa, bayan shekarun Mustapha goma aduniya kwanci tashi yau da gobe sai Allah, Allah ya azurta larai da ciki, tayi murna ta godema allah ba kadan ba, daga nan ne ta fara neman tsari daga mugunji da mugun gani tana addua akan allah ya tsareta da abinda ke cikinta da mijinta, har larai takai wata takwas wata rana ta tashi domin kuwa ranar girkinta ne bayan ta gama shirya abinci ta zuba nasu itada badaru ta koma ta aje nata adaki sannan ta fita domin karban ruwan adduar naquda bayan fitarta kuwa saiga Mustapha ya shugo dakin innarsa rai abace dama itake zugashi akan cewa idan har yana kallo larai ta haihu to shikenan gatan da ake mashi yakare, aikuwa ranar ya dawo gida saboda babansa badaru wanda yayi mashi fada akan abokanan banza da yake tara wa,dakin innarsa ya fada nan ya taddata tana shirin fita hannunta rike da wani qulli da alamu batasan ya shugo cikin dakin ba, ganin ya shugo rai abace nan ta shiga tambayar sa me akayi mashi nan take ya zayyane mata komai dagana ta dora mashi da cewa ‘’ay matsiyaciyar matarshin chan ce ta zuga sa sbd haka yau zamu dauka fansa, kaga wannan kullin kaje uwar dakanta nasan yanxu malam ya wuce sallar magariba kaje ka zuba cikin kwanan abincinta dazarar taci nan take zata mutu kowa ya huta, ay kuwa yana karba ya wuce dakin yana zuwa ya tarar da kwanon larai anan ya zazzage duka maganin sannan ya juya miyar kukan datayi, ya fice daga dakin yana dariya,fitarsa keda wuya saiga malam ya dawo daga masallaci yana shiga daki baiga larai ba daman ta fada mashi zata je gidan malam liman domin karbo ruwan adduar naquda.

Free page….



Chapter 9-10



badaru na shiga dakin kuwa ya tarar da flask din data aje abinci dama da yunwarsa ya dawo, zama yayi ya zubama kanshi sannan yayi bismillah yaci ya koshi yayi dam daga bisani yayi sallar isha í sannan ya kishingida yayi kwanciyarsa, koda larai ta dawo ganin mijin nata yana barci yasa bata tashe sa ba, sallah itama tayi sannan tayi kwanciyarta already daman dataje gidan malam liman taci alala da matar liman tayi wadda ta bata sha’awa dama matar lima inno kawarta ce kut da kut, gab da asuba ta farka ganin badaru dai baccin shi yake hankali kwance yasa itama ta koma barcin ta, binta kuwa ganin malam bai fito ba kuma bataji sakamakon abinda take jira ba kawai saita wuce bangaren larai, tana zuwa kuwa ta fara doka masu sallama, larai ce kawai ke iya amsawa sannan ta fito ta sameta, ganin lafiya kalau larai ta fito yasa hankalin binta tashi sosai, gyara nutsuwar ta tayi sannan tace ‘’kicema badaru inason ganinshi’’ wucewa ciki larai tayi sannan ta fara tashin badaru, ganin ko matsi bayayi yasa hankalinta ya tashi, daga karshe dai ta dunga kwala mashi kira ganin baya nunfashi yasa larai kwala ihu nan take ta fadi assume, jin ihun larai yasa binta shugowa da hanzari koda ta shugo taga badaru babu rai saita fara ihu anan take kuwa gidan ya cika da mutane anan aka gane cewa badaru ya mutu cikin barcinshi itakuwa larai doguwar suma tayi bayan an taimaka mata ta farfado nan hankalinta ya tashi ganin badaru ya tafi ya barta tapiya ta har abada, tayi kuka tayi kuka ta godema Allah daga karshe ganin za ah kai badaru makwanci sa yasa larai nagudar dole anan matar liman inno ta taimaka ta kaita wani dakin kaya extra agida, anan aka kira wata nurse makwapciyarsu tazo domin taimakon gaggawa, matar bata ida zuwaba kuwa larai ta haifi santalelen danta kyakyawan gaske gashi black beauty.

Bayan kwana bakwai yaro yaci sunan mahaifinshi marigayi wanda ya rasu aranar da aka haifeshi wato Badaru…binta kuwa ashe tana dauke da sabon ciki wanda sai bayan mutuwar malam ya baiyyana, binta tayi rainon cikinta har wata tara sannan ta haife danta inda yaci sunan sa Aliyu haidar koda sammani yaso yasama yaron suna sai binta ta nuna tanason ta sawa danta suna da kanta aikuwa ya barta da abinta.

Badaru ya taso cikin koshin lapiya da son dan uwanshi Mustapha wanda shima haka Mustapha ya nuna mashi qauna sosai sun taso tare inda badaru keda shekara goma shi kuma Mustapha yanada shekara ashirin dama shekaru goma ne tsakanin su in badan an fada maka ba bazaka taba sani cewa ba uwa daya ce ta haifesu ba, suna kaunar junan su sosai inda aliyu haidar kuwa yakeda shekaru tara aduniya don kuwa badaru ya girmeshi da shekara daya, yanda Mustapha keson badaru kwata kwata baya yima aliyu wannan soyayar, dama gashi shi aliyu bashida hayaniya kuma bai damu da sha’aninsu ba, lokacin da badaru ya kammala secondary school dinshi alokacin shikuma Mustapha ya aje bokon ya shiga kasuwanci inda allah ya buda mashi lokaci guda ya zama tambatsentsen dan kasuwa mai shegen kudi ganin haka yasa badaru ya bishi zuwa kano anan ne ya samu admission ah BUK inda ya fara karanta architecture,Mustapha kuwa anan kano ya hadu da kareema awajen wani taron yan kasuwa tazo tare da baban ta nan kuwa taji itama Mustapha ya zauna mata bayan yan watanni akayi aurensu. badaru yaro ne mai basira da son mutane cikin kankanin lokaci BUK tasan da zaman badaru inda yana kammala karatunshi yayi bautar kasa anan ne wani company suka daukeshi aiki ya zama babban mutun sbd irin kwazon da yake dashi wajen iya zane, har competition akayi na architects cikin ikon Allah shine ya zama gwarzo afadin Nigeria anan ne duniya tasan da badaru daukaka tazo mashi har Allah ya daga shi ya fara tafiye tafiye,alokaci yana da shekaru ashirin da biyar aduniya anan ne yayi tafiya izuwa morocco domin yin wani project anan ne allah ya hadashi da shuwaira, shuwaira marainiyace batada iyaye sun rasu amma tana tare da kanin mahaifinta da matarshi waenda Allah bai taba basu haihuwa ba, shuwaira haifaffiyar yar morocco ce irin black beauties din morocco’s tana aiki ah wani private hospital, amatsayi nurse, ranar da suka fara haduwa da badaru kuwa ranar yaje overall body check up domin office din da zaiyi aiki dasu ah morocco ba a fara aiki dasu saika kawo health history dinka, aranar kuwa ta kasance duty din shuwaira, bayan ta shigo patient scanning room kanta akasa tana karanta information dinshi, muryarta ce ta dawo dashi daga danne dannen wayan da yake yi, wani irin melodious voice yaji akunnan shi ‘’ hey mr badaru how are you today? I will be the nurse to check you up today’’, da sauri ya dago kanshi domin jin me daddaden muryar nan, ya shagala da kallonta saidatayi gyaran murya bayan itama ta gama kallonshi sannan tace ‘’sorry i’m i in a wrong room?’’ cikin inda inda da kuma shauqin ganinta yasa badaru cewa ‘’no noo you’re in the right room, right close to my heart, ganin yanda badaru ya lalace da kallonta yasa tayi dariya tace ‘’kallon ya isa haka karkasa na kasa aikina mana’’ aikuwa kunya ta lullube badaru baisan lokacin dayace mata ‘’mss na kasa daina kallon ki don allah ki bani magani ko zan iya cire idanuna akanki, ganin badaru na neman zaucewa yasata cewa “lallai kana da enough time yau dinnan don inaga kwana zamuyi ahaka you’re not ready for the full body scanning, ganin zata fice yasashi rike hannunta,

Chapter 11-12



ganin zata fice yasashi rike hannunta, juyowa tayi zatayi Magana ya katse ta da cewa ‘’I’m sorry my lady let’s begin with the scan,ganin how cool and gentle badaru keyi mata magana sai taji ya burgeta, preparing dinshi tayi bayan ya chanza outfit dinshi zuwa na asibiti anatse ta taimaka mashi ya shiga cikin body scanning machine din, saida ta tabbatar ta duba lafiyarshi tukunna tayi mashi sallama, zata wuce Kenan yace ‘’ right now at this moment I want to be the only man in your life that will love and take care of u’’ ita abima har mamaki yake bata shiko wannan daga haduwa da ita bai santa ba bata sanshi ba kallonshi kawai tayi sai tayi murmushi ta fita. Koda badaru ya koma gida hankalinshi sam baya jikinshi tunanin shuwaira kawai yake yi ta tafi da imanin shi yanda take magana da yanda take al’amuranta gaba daya ya tafi dashi, haka dai ya lallaba kullum saiyaje asibitin nan, da farko shuwaira bata amince mashi ba daga baya kuma ta fara tausaya mashi harta fara sonshi. Ganin irin soyayyar dake girma tsakanin shuwaira da badaru yasa iyayenta wanda suke riketa suka zauna da badaru domin yayi masu bayanin asalinshi,koda yayi masu bayanin asalinsa Sai uncle ya aminta dashi kuma yayi alqawarin aura mashi shuwaira tunda itama ta nuna tanaso, dukda anty dinta matar uncle bata soba,bayan Yan watanni uncle ya aura ma badaru shuwaira amma da sharadin bazai koma gida ba zai zauna da ita ah Morocco, nan take badaru ya amince da sharadin su. antyn ta bataso hakan ba sbd tana tsoron gujewa matsala don lokacin da akayi auren babu wanda yazo daga bangaren badaru. Badaru kuwa babu wanda ya fadamawa cewa yayi aure saida suka shafe shekara kunsan biyar alokacin ko batan wata shuwaira bata samu ba suna zaman lpy sosai da ita da badaru dukda maganar danginsa yana damunta sosai, tunda sukayi aure saidai ya shirya ya je Nigeria yayi yan kwanakinsa ya dawo. Lokacin da badaru ya sanar da Mustapha auren da yayi a morocco ba karamin zafi Mustapha yaji ba ayanda ya dauki dan uwan nasa har yayi aure amma bai fada ma kowa ba aciki kuwa harda mahaifiyarshi larai wadda suke zaune anan katsina da ita da binta sai kaninsu badaru aliyu haidar.

Bayan komawar badaru da wata daya yaji duk zaman morocco ya chanza masa yaji baya qaunar zama ah garin haka yasa ya samu shuwaira da batun komawa Nigeria, duk da shuwaira tana shaáwar ganin dangin badaru amma hakan bai sata jin babu dadi ba zatabar uncle dinta, bayan yan kwanaki badaru ya lallabata suka shirya sukayima su uncle sallama sannan suka taho Nigeria. Dirar su Kenan ah aminu kano international airport kano badaru ya dauki waya don ya kira dan uwansa, nan ya sanar dashi sun iso, minti kadan saiga Mustapha, Mustapha yaji dadi ganin badaru da iyalinshi, direct gidan Mustapha suka wuce inda anan suka huta sannan sukaci abinci aka kaisu dakin da zasu zauna, shuwaira dai taji dadin tarbar da akayi masu amma duk bata cikin natsuwar ta domin tunda suka iso ta fara jin fargaba hankalinta duk ba ajikin ta yake ba amma dai haka ta daure bata nuna ba, bayan yan kwanaki suka shirya harda iyalan Mustapha wato haj kareema da yayanta uku, wahab, Ibrahim da Muhammad.

Koda suka isa katsina ba karamin mamaki Mustapha yayi ba ganin yanda larai batayi ma badaru fadaba akan auren da yayi, abunda baisani ba ashe ya riga da ya fadi ma mahaifiyarshi komai agame da batun aurenshi kuma tasaka mashi albarka sannan ta umarceshi da ya dungo boye duk wani abun alkairinsa da zai faru dashi, bai dauki zancen baba larai da komai ba shiyasa bai nuna damuwa ba kuma shiyasa bai fadama kowa ba ciki kuwa harda dan uwansa Mustapha.

Free page….



Chapter 13-14



Cigaban labari…….

Sallan asuba da aketa kirane ya farkar da amra wadda ke kwance a kasa miqewa tayi sannan ta tattare kayan shimfidar datayi ta ninke komai sannan ta wuce toilet koda ta fito kwance ta tarar da salima sai salim agefenta, ahankali ta tako ta fara tashin salim…,’’salim salim tashi lokacin sallah yayi”.,..tashi yayi ya zauna sannan ya fuskance ta, yace ‘’ adda amra kin tashi ashe good morning bari na tashi salima’’ dakatar dashi amra tayi sannan tace ‘’ kyaleta zan tashe ta, ka wuce toilet kayi alwala saikazo muyi sallah ko”,

mikewa yayi sannan ya bude kofar toilet, saidata jirashi ya fito tukunna ta shimfida masu sallaya sannan suka tada kabbara, koda suka idar addua sosai sukayi dashi da ita, kallon salima yayi wadda ke baje tana barci sannan yace adda maisa salima bazatayi salla bane ita,? Kallonshi amra tayi sannan tace ‘’salim I will explain to you why salima is not praying but please not now saika girma for now idan nayi maka bayani bazaka gane me nake nufi ba but idan har kaga nida salima bamuyi sallah ba we have our own reason kuma addini yasan da haka kaji ko’’ nodding kanshi yayi sannan yace adda let be get back to sleep,’’ tashi yayi ya kwanta gefen salima itakuwa amra tattare kayan sallan tayi sannan ta wuce wardrop din su ta aje, doguwar rigace ta barci har kasa ajikinta sai hula, fitowa tayi direct daga dakinsu fitilun ko’ina a kashe yake ahankali ta karasa wajen switch din wutan ta fara kunnawa saidata tabbatar ta kunna wanda zata buqata domin gyare gyaren da zatayi sannan ta wuce cikin kitchen, kodata shiga kitchen din yana nan yanda ta bari fess fess,karasawa har cikin kichen din tayi sannan ta wuce store ta fara dibo abinda zata buqata wajen yin breakfast, saidata fara fere irish da doya sannan ta dora shi akan gas, fita tayi backyard ganin gari har ya fara haske yasa ta kwaso tsintsiya da mopper, sannan ta wuce cikin parlor, duk girman parlor nan haka ta share shi tsaf duk da babu wani datti saidata tabbatar ta gama sannan ta fara mopping din ko’ina.



Anaste ta kammala aikin ta sannan ta koma kitchen anan ta fara yan soye soye abubuwa data dafa sannan ta hada masu custard saboda tasan kananu yaran zasu buqata, sannan ta dafa ruwan tea. Wajen karfe 9 daidai suka fara sakko daya bayan daya, Khadija ce ta shugo kitchen jikinta sanye da kayan bacci riga da wanda kanta da ribbom kalar kayan jikinta ta daure yar jelar gashin nata, siririya ce batada haske sannan hancin ta yana nan anane kamar gutsirarren dankali😂, kodata shigo ko kallon amra batayi ba ta wuce wajen tabkeken fridge dinsu ganin haka yasa amra cewa good morning khadi, ko kallonta batayi ba ta bude fridge din ganin bataga abinda take nema ba yasata cewa, “ina avocado smoothie din danace ki dunga hada min duk safiya kina ajewa”??, kallonta amra tayi sannan tace, ‘’avocado dinne yakare shiyasa ban hada ba’’ ..tsaki kawai khady tayi sannan ta dauki bottle water ta wuce dining, ita kuwa amra qannenta ta zubama akula sannan ta aje agefe, mugs din shan tea ta kwasa sannan ta wuce dashi dining room, duk kowa ya hallara amma banda iyayensu mata, daga kan khady, Muhammad, amina, ishaq, jabir,jalal sai khamis da Khalil, halim ce kawai babu acikinsu sai kuma manyan yayyi wahab da Ibrahim wanda basa kasar ma kwata kwata.

Ka’idar gidance duk yaran kowa sai ya sauko anyi breakfast dashi gudun samun misunderstanding kuwa iyayensu basa saukowa saidai ko wacce ta dafa a kitchen din part dinta asama.

kowannan su yana zaune haka amra tazo daya bayan daya tayi serving dinsu, ishaq ne kawai ya bude baki yace mata ‘’thank you sis amra,’’ murmushi kawai tayi mashi sannan ta juya zata koma kitchen, tana gab da shiga kuwa tajiyo muryar halma tana sakkowa daga stair tana sanye da pink riga iya gwiwa,kallon amra tayi sannan tace ‘’ zaki tafi baki bani nawa breakfast dinba kosai na kira mummy?“juyowa amra tayi sannan ta fara zuba mata, ishaq kuwa tsaki kawai yayi, amina kam ko kallon inda take batayi ba,dukda itace akusa da halma .



Saidata sallamesu sannan ta wuce kitchen abunta aranta tana mamakin isa da suke nunawa, kamar basune suke wasa tare ba lokacin da iyayen su na raye lallai baka sanin mai sonka saika rasa gatanka aduniya, murmushi kawai amra tayi sannan ta wuce dakinsu,

Tana shiga ta tarar da su salim har sunyi wanka sun chanza kaya ita suke jira, aikuwa tana shugowa salim jikinshi har rawa yake wajen karban kulan data shugo dashi, waje ta samu ta zauna salima nayi mata sannu da aiki. Kallonta

7 Comments On AUREN KATIN KASA
avatar
salma-6

1 year ago

Reply

wonderful

avatar
salma-6

1 year ago

Reply

wonderful

avatar
fatima-7-2-5

1 year ago

Reply

I need complete one

avatar
fatima-7-2-5

1 year ago

Reply

I need complete one

avatar
aisha-2-9-6

1 year ago

Reply

I need complete pls

avatar
aisha-2-9-6

1 year ago

Reply

I need complete pls

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aisha-2-9-6

You can only get the complete by purchasing it through the Author

Please Login or Register in order to submit comment