Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin A shape dinnan tayi mata kyau sosai sannann tayi rolling kanta da mayafin abayar sai yar chain hand bag dunta akafada har suka iso cikin jirgi, seat dinta atsakiya yake nan ta samu waje ta zauna while gefenta is empty by right sannan left dinta kuma wani bayarabe ne…..Bayan Yan mintuna kadan jirginsu ya daga zuwa abuja domin transit zasu fara yi daga abuja su wuce uae.

Free page….



Chapter 40-41



ABUJA NIGERIA.

Mota ce kirar range rover evoque 2020 black color, ko ina na window din is tinted, baka ganin komai daga waje,aguje ta shararo zuwa cikin airport din Nnamdi Azikiwe International airport abuja, daga gani sauri matukin motar yakeyi, koda akayi parking motor din, an dauka almost 5 minutes kafin abude bayan motar, ahankali ya fito da kafanshi ta dama sanye da sandals black color wanda suka haska farar kafarshi da yatsun dogaye, ahankali ya sauko da dayar kafar tashi sannan ya fito gaba dayanshi, Masha Allah😻wayace maqale akunnen shi, juyowa yayi yana fuskantar driver daya kawoshi, Allahu akbar …Allah yayi halitta, wato wani irin kyakyawan dogon saurayi ne😂wanda akalla bazai wuce shekaru talatin ba aduniya, dogone sosai kuma qaqqarfa, fuskarshi sai wani annuri take da glowing , ya aje sajen gashin baki wanda ya kewaye a fuskarshi baki wuluk ga bakinshi dan cute wanda yayi wani oval shape, hancinshi amike gwanin burgewa,ya rufe idanunshi da alamu ranar daya tsaya ta dan dame sa, ahankali ya bude idanunshi wanda suke wani irin sheqi da sparkling lokaci daya, yanada wani irin kwarjinin da you can’t resist him,lashes din idonshi zarr zarr dasu kamar ya saka eyelashes wanda yafi daukan idon mutane, ahankli ya fara magana cikin kakkausar muryarshi, ‘’get my baggage to the counter, I will be there in a minute..’’ ahanzarce drivern nashi ya fito ya bude booth ya dauka Hadadden Louis Vuitton baggage dinshi

ya wuce cikin airport din, shi kuma handsome din ya jingina ajikin motor waya maqale akunnenshi yana sauraro…a hankali ya soma magana…wato muryarshi har wani echoing yake yi, yana da irin harsh voice dinnan ga kuma dadi sauraro, yanda yake tafiyar da lebenshi kamar robot ahankali yace ‘’Amma I’m done with aman’s issue bazan kara Magana ba yaje yayi duk iskancin dayaga dama kawai dai bazan iya zama Ina kallon abubuwan da akeyi agidan nan ba wanda kwata kwata bai dace ba,’’ yatsine fuska yayi sannan ya daure fuska tamau alamun ranshi kamar abace yake sannan ya cigaba ‘’Amma wallahi bazan kara dawowa ba, tunda haka sukeso na bar masu garin, and besides kinsan zan koma training dina so now you can have peace of mind’’ …Magana akayi daga chan’… yatsine fuska yayi alamun ya qagu ya katse call din , cire phone din yayi daga kunnen shi ya kalla screen din ganin 2mins to his flight yasashi cewa ‘’Amma zanyi missing flight bye’’ katse wayan yayi sannan ya fara tafiya cikin isa da kasaita, jikinshi sai kamshin Emilio de pérfumè yake wanda akalla kudinshi zaikai kusan dala dubu uku, riga da wando ne ajikin shi na Nike, rigar rubber ne ta dameshi dam sosai wadda ta fito da builded body dinshi, wani irin murdadden jiki ne dashi wandon jikinshi same color da rigar shima nike, ta kasa yadan dameshi wanda ya fito da damtsen kafarshi he looks soo so damn cute and attractive ,kanshi kuwa babu komai kuma baibar suma ba sosai sai dan few gashii kadan, lunshe donshi yakeyi har ya karaso airport din kamar bazai karasa ba, tunda ya shigo airport dinnan ma’aikata da mutanen da ke kai kawo suke kallonshi, hannunsa rike da briefcase brand din mont’blanc dayan hannunshi kuma laptop ne da wayansa, anatse yake tafiya kamar bazaiba, saida yazo dab da driver din sannan ya zira hannu acikin aljihunsa ya zaro duka naira note din da suke ajikinshi ya bashi, godiya ya fara masa, anatse ya daga mashi hannu alamun ya tapi sannan ya karasa counter din emirates, anatse ya fara ma budurwar dake tsaye jikin counter din Magana, ‘’ evan any update?

anatse ta fara bashi ansa ‘’ you’re welcome sir and we’re very sorry sir, I just talk to our manager, the problem is we got your booking very late, I’m sorry I don’t know what to do about it,”lips dinshi ya ciza har saida ya danyi jaa sannan yace “get..me your manager now, I mean the overall manager of emirates air now!!!’’…. furgicewa evan tayi, da sauri ta jawo landline sannan ta kira akayi mata connecting to office din babban manager emirates air ganin surutan da suke zai bata masa lokaci kuma baya son atmosphere din wajen ya sashi mikewa yace ‘’tell him to meet me at the first class lounge and the flight should be delayed now!! Sanin ko shi waye yasa ta kira direct aka tsayar da jirgin da zai daga zuwa dubai… saida ya idar da sallar asr ah masjid din lounge din sannan ya zauna yana dan latsa waya……





oh araina nace kudi yana aiki ko shi wannan din waye kuma dan uban waye da har yana da ikon tsaida jirgin da zai daga zuwa dubai…. Fatan dai ba jirgin su amra bane😂😂😂 hahaha muje zuwaaaa…..



Anatse manager keyi mashi bayani ‘’sir we know you’re very important to uae government and it’s our loss to loose such important customer, so please sir understand that it’s not our fault, we received your call 10 minutes to takng off the flight but we promise when the flight is transiting to Saudi we’ll get things sorted we’re very sorry sir’’’ … kallon manager yayi kawai kanshi har wani sara mashi yake bayason amashi delay ko abata mashi plans dinshi, anatse ya miqe ya fara tafiya ko kallon manager baiyi ba saida yazo daida harabar filin jirgin sannan wata motor benz GLA-Class black color har gabanshi ta tsaya bude marfin motor yayi ya shiga, taja har gaban jirgin emirates babba wanda ya kamata ya tashi tun 3pm amma sai gashi anyi delaying dinshi saboda wannan masha hurin mutumin.. anatse ya fito yana taka stairs din benen duk inda ya gitta kamshi ke bazuwa, saida yazo dab da kofar shiga yadan tsaya yana motsa baki da alamu addua yakeyi sannan yasa kai, anatse wani balaraben assistant pilot yazo har inda ya tsaya, anatse ya yi welcoming nashi sannan yace ‘’sir let me assist you to your sit,’’ binshi yayi wanda tun shugowanshi economie din gaba daya yaji wani iri, abinda bai saba ba yau zaiyi wato shiga cikin mutane gashi shiba ma’abocin shiga jama’a ba, bin pilot din kawai yake inda duk ya gitta sai crews sun gaishesa da girmamawa sanin ko waye shi, mutane kuwa suna kallon izza da isa.. ahankali pilot din ya tsaya daidai sit din tsakiyan jirgin by the right empty seat din wajen pilot din ya nuna mashi sannan yace ‘’this will be your seat sir remporarily befr the transit thanks for your understanding, wucewa pilot din yazoyi kenan ‘AMAR’ ya kalleshi yana lumshe idanu kamar mai jin barci yace ‘’no need for any special treatment’’ sannan ya zauna… kwata kwata seat din is not comfortable for him kodan baitaba zama ah economie bane oho, gashi kafadanshi yayima wajen kadan saboda yanada wani irin fadi, gefenshi kuwa yaji mutun amma ko kallon wurin baiyi ba saima qoqarin mikar kafafunshi da yake yi ahankali kamar kwai….. mintuna kadan akayi announcing takeoff,,, amra wanda duk surutun da pilot dinnan wanda turancinshi da wanda yake mayar mashi da magana ba ganewa take ba sbd wani irin melodious accents suke bugawa, itadai ta kifa kanta a tsakanin gwiwoyinta sbd tun iyayensu nada rai idan zasuyi tafi itake tsoron takeoff ba kamar salima ba, ahankali ta runtse ido tana jin wani sihirtaccen kamshin dake shiga cikin hancin ta wanda daga gefenta kamshin yake futowa gashi tanajin ciwon mararta kadan kadan kamarma abin zaizo mata gadan gadan, runtse ido kawai takeyi tana addua har suka daga sararin samaniya…………

Hajiya amra yau za ayi kwanan 🇦🇪😂……….

Free page….



Chapter 42-43



saida ta dauka kusan 1hour before ta fara dawo wa daidai, amma har yanxu tanajin ciwon marar nan, amar kuwa wanda ya lumshe ido babu abinda yake tunawa sai fadan da sukayi da dan uwansa, har yana ikirarin sai ya zama karshensa,runtse ido yayi yana jin zafin irin qiyayyar da aman yake mashi, wani irin huci mai zafi ya furzar, zuciyarci babu abinda take sai tafarfasa, yana cikin tunanin nan ya fara jin shesheqar kuka daga gefenshi, mamaki ma ya gama hanashi tantace mace ke kukan ko namiji, ya dauka almost 10 minutes sannan ya fara jin kukan nata yana kara gaba, wani irin bal balin zafi ya dunga ji aranshi babu abinda kukan nan ke tuna mashi sai Amma, baya qaunar kukan mace ko yayane baya so ko kadan, ahankali ya bude idanunshi wanda sukayi jaa sosai bacin rai karara ya bayyana afuskarshi, kallon gefenshi yayi adurkushe yaga mutun, tun daga tsakiyar kanta wanda ta durkushe har gwiwarta, kallo daya yayi mata ya dauke kanshi, ganin kukan bamai karewa bane kuma babu alamun zatayi shiru yasashi saka airpod ya toshe kunnen shi ya kunna karatun qur’an , anatse yake sauraro har ya fara bin karatun, yana lumshe idonshi….



Jin melodious muryar dazu ya sanya ta tsagaita kukan anan take zuciyarta ta fara sassauta mata daman ciwon ciki ne ke nuqurqusar ta ga tunanin su salima duk shi yasata kukan nan, anatse take sauraron yanda yake karatu har yanxu bata dago baa haka har barci ya dauke ta a wahalce….. shima barcin ne ya dauke shi….sun dauki almost 2 hours suna bacci chan yaji dan nauyi akafadar shi, ahankali ya fara bude idanunshi da suka rine tsabar jin baccin bai ishesa ba, jin hannunshi yayi tsami yasa ya fara yatsine fuska,ahankali ya bude idonshi tarr akan ta, kwance take akan kafadar shi mayafin jikinta ya rufe mata fuskarta lokaci guda ranshi ya baci amai ya fara neman kakaro mashi, hankadeta yayi wanda yasa ta buge da gefen hannun kujerar, ahankali cikin barci tace ouchhh wayyo oum, tashi yayi a zafafe ya wuce bathroom, saida ya wanke fuskarshi sannan yadan samu nutsuwa, babu abinda yake ayyanawa aranchi face tunanin wacce mara hankali ce wannan zata kwanto jikinshi, babu abinda ya tsana irin mata mara aji, kwata kwata bai kawo cewa ba da saninta tayi hakan ba, amra kuwa baiwar allah, dalilin farkawarta ya dawo mata da matsanancin ciwon mara tun tana daurewa har kukanta ya fara fitowa sosai, jin haka yasa crews sukayo kanta, tambayarta suka farayi amma kwata kwata ta kasa Magana saidai nuni da take masu da cikinta, ganin nunfashinta na neman daukewa yasa suka firgice, wata crew ce ta wuce wajen announcement ta fara announcing emergency idan akwai doctor yaxo yayi taimakon gaggawa, allah ya taimaka kuwa an samu wani shahararren likita, dr Benjamin, har gaban amra ya karaso koda ya tabata yaji taba motsi yace akawo mashi ruwa domin ta suma, amar kuwa yana toilet saida yakai almost 10mins kafin ya fito ko kallon inda yarinyar take baiyi ba yadaiga mutane cirko cirko agabanta, kawar dakai yayi ya zauna yana lunshe ido,…saida aka dauko first aid akayi mata allurer bacci tukunna ta samu dan sauqi, oga amar kuwa tunda ya lumshe ido bai ko bude ba, koda akazo raba abinci kamar yanda ya umarta bayason special treatment babu wanda ya kawo masa, da akazo raba na yan economie kuwa ko kallon crew dinda ke tambaya mai za ah bashi baiyi ba…. 1hr later jirgin ya tsaya transit, bayan waenda zasu sauka suka sauka, saida aka gyara mashi inda ya buqata tun farko sannan aka sanar dashi, mac laptop dinshi kawai ya dauka sai wayar shi sannan ya bada umurnin adauko mashi baggage dinshi da brief case dinshi, sannan ya kara gaba ko kallon gefenshi baiyi ba daman duk atakure yake, first class ya wuce inda wajen yake nan kamar daki cikin nutsuwa yake komai nashi, saida ya rufe bangarenshi for privacy sannan ya zauna yana yan latse latse cikin laptop dinshi, tunda ya kafa kai yana danne danne har akayi landing, daman sai yan first class sun sauka tukunna Sai yan business sai yan eceonomie, anatse ya fita cikin isa, har gaban wata lexus bayan ya shiga aka fita dashi daga harabar jirgin. Amra kuwa ana chan ana shakar bacci saida kowa ya sauka ita kadai ta rage yasa wata crew ta tashe ta, ahankali ta bude idanunta, ganin anyi landing yasa ta mike, mamaki ne ya cika ta jin garau tajita babu ciwon cikin saidai dan blood flow data fara ji chan kasan ta, anatse ta fito har cikin airport din, owww wow, saida ta shaki iskar garin taji wani irin sanyi a zuciyarta, addua tayi yanda ta taka kasar garin Allah yasa ta tako da alkairi, anatse take tafiya har ta fito exit lokacin har safiya tayi wajen karfe bakwai da rabi na safe, garin is so peaceful,

Kiran airport taxi tayi sannan ta fada mashi inda zai kai ta wato Elvira apartment deira, anan ya shaida bata free ride ne sbd yau anniversary din sarkin garin na cika shekara arba’in da zama a kujerar sarki sbd haka yau komai free ne indai har na government ne.

Free page….





Chapter 44-45



Tafiya sukayi mai dan tsayi saboda akwai nisa daga airport, suna isowa tayi mashi godiya sannan ta wuce cikin reception, koda ta isa nan ta gabatar da duk wani document da shaidar cewa tayi renting apartment din, nan take aka bata key din dakin ta sanan ma’aikata suka taimaka mata da kaya har saman seventh floor, ahankali take takawa har gaban dakinta nan ta sallami worker din sannan tayi setting pin din kofar ta sannan ta shiga, apartment ne na mutun daya mai shegen kyau kana shugowa dan guest toilet zaka samu idan ka gangara sitting room ne mai dauke da L shape chair sai dan center table wanda aka daura remote akai sannan sai yar smart tv babba mai kyau gefen sitting room din kuwa daga chan sako kitchen ne wanda yake dauke da washing machine, dish washer sai gas cooker da oven microwave, gefe dan dusbin bucket ne sai fridge-freezer saidan view balcony agefe, idan ka fito sitting room kuwa by your left kofar da zai sadaka da daki ne, dakine babba daidai mutun daya da gado sai yar wall wardrobe mai 4doors agefen daga chan sako kuma bathroom ne mai dauke da bath aciki da sink sai wani tafkeken mirror kai komai abin burgewa.



Saida ta zaga ko’ina acikin apartment din sannan ta wuce daki da aje baggage dinta da handbag sai ah lokacin ta tuna situation din da take ciki atake ta fara cire kayan jikinta ta wuce bathroom, wanka tayi sannan ta bude akwatinta ta dauko spair pad ta saka ko riga bata saka ba da dan towel din data gani a-toilet din ta kwanta sai bacci.



Amar…..

Tunda ya shiga cikin hadaddiyar lexus din yayi relaxing bayanshi, wani irin bacci ke fusgarshi amma ya hana kanshi, babu abinda yake buqata sai shower, kallonshi driver din yayi ta jikin mirror sannan yace ‘’sir are we going to your penthouse or your mini apartment’’??,….. shuru ya danyi chan kuma yace ‘’take me to palm Jumeirah my penthouse,’’…..anatse driver din ke driving tafiya half an hour sukayi har ya iso ahankali ya tsaya bakin gate, nan take gate din ya fara budewa da kanshi don yayi recognising plate number din motor din wanda shi kadai yake da plate number din wato (UAEAF) R1 united arab emirate armed forces rank one!!!!!!!!! Ahankali driver ya kutsa hancin motor har gaban compound din wani tapkeken building wanda akalla zaikai hawa biyar, tafiyar daga gate zuwa main building dinma kanshi sai an kwashi yan mintuna, ahankali ya bude kofar ya zuro kafafunshi,, ouu GEN AMAR YUNUS TAURA Kenan, saurayi mai jini ajika😂, wannan ganinsa sai kayi sa’a, man of his words, the only young senior officer of united arab emirate army rank one!!!!



Anatse ya doso kofar main entrance door saida kofar tayi scanning dinshi tass for safety sannan tayi authorising dinshi ahankali ya saka thumps dinshi jikin kofan sannan kofan ta fara announcing welcome.. ahankali yasa kafa ya shiga, ko ina tsaftsaf yake ahankali ya fara kutsa kai ciki, first sitting room, ya Allah wani ririn tapkeken sitting room ne wanda ya dauki 3 set of different chairs kowani saqo, jikin bangon parlorn is transparent duk glass ne, ahankali ya fara magana alexa open the curtains… ahankali labulayen suka fara budewa wanda color dinsu wani irin beautiful black and white da alamu yana qaunar bakaken abubuwa, cos everywhere is black and white harda set of kujerun parlorn, domin set daya ne aciki wanda shikuma greenish color ne mai kyau sosai., ko ina yasha kayan alatu daga tsakiyar bango kuwa wata irin tapkekiyar tv ce, ahankali ya kuma furta, ‘’alexa on the aircon ‘’ alexa kuwa tayi karap ‘’air conditioner is on,’’.. direct lift ya wuce shima transparent ya danna last floor 5th kenann ahankali lift din ya fara sama, yana ciki yana kallon ko wani part na floor din gidan har yazo last floor, kai tsaye ya zura kafarshi ya futa ,,, waii zabgi masha allah, wato parlour kasa shirmene, wani parlor ne asaman,bashida wani shegen girma amma yana dauke da wasu English wooden chairs wanda sukasha white leather cotton ajiki sunyi masifar tsaruwa awajen, sai wurin ya bada wani aesthetic view sannan shima ko ina glass ne around the wall amaimakon wall.. ahankali ya taka ya wuce ya isa daidai wata kofa, baima taba kofar ba tayi sensing tsayuwarsa ta bude, ahankali yasa kai, yana matse fuska alamun gajiya.. wato anan bedroom din akayi ruwan kudi, wani irin tapkeken gado ne king size bed yana dauke da wasu hadadun bedside lamb sannan daga gefe ga wata shegiyar resting chairs da jerin pillow da yawa sai dan side stool shima mai shape din oval, asamanshi an daura wasu hadaddun flowers, direct gadonshi ya wuce anan ya aje briefcase da wayoyinshi a gefen bedside sannan ya wuce wani conner row agefe, wani irin glass door ne awajen suna facing juna, bude daya yayi ya shiga wani daki ne babba mai dauke da wardrobes wajen aje kaya iri iri harda wajen briefcase, uniforms ne, laptop, gym wear, glasses, links takalma, kaii babu abinda bai aje ba, gefen daya wani tabkeken dresser ne wanda yake shake da kayan kamshi kamar mace dama shi ma'abocin kamshi ne, sauke komai yayi ya aje sannan ya fara kokari cire kayansa, fitowa yayi yayi sliding door din gefe, nan ma dai ba a magana, bathroom ne wanda yake wurin wanka har biyu, akwai Jacuzzi bath sannan daga gefenshi other end kuma pressure shower bath sai wajen wc da sink da wani katon mirror wanda qasanshi kamar table ne yana shake da kayan wanka, tube kayansa yayi komai sannan ya aje ah laudry, he’s so clean bashi da qazanta ko kadan, ahankali ya taka gaban Jacuzzi bath ya tara ruwa da pressure sosai within 2 minute ya cika bath din, wurin mirror ya karasa ya kwaso bubble bath me kamshin caramel, sai shower gel mai kamshi strawberry, ahankali ya dunga zuzzubawa har saida ruwan ya dawo pink tukunna ya aje babu abin da ke tashi sai mixture of caramel and strawberry, sauran kayan jikinshi ya karasa cirewa, daman wata inner vest ce wadda ta dameshi dam kamar zai tsagata nan take muscles din suka bayyana cikinshi so flat ga wani six packs dauu har wani irin jijiya yake fitowa daga jikinshi zirr,… ciki kawai ya shiga ya kwanta yana lumshe ido saida ya dauka almost an hour kafin ya fito, daki direct ya wuce bayan ya fara tsane sajen shi da wuyanshi da dan tiny black towel dinshi dayan kuma yana nan akasan waist dinshi, duk, aje towel din yayi sannan ya kwanta after ya kunna ac to the highest level, bacci sosai ya daukeshi mai nauyi ahankali yake sauke nunfashi.



Amra kuwa wani irin masifaffiyar yunwa ce ta tashe ta afurgice ta mike dama bata jurar yunwa ita da salim, toilet ta wuce ta chanza pad sannan ta bude akwatinta ta dauko wata abayar ta saka sannan tayi rolling kanta ta zari wayarta da handbag dinta ta fice.

bayan ta kulle kofarta, direct kasa ta sauka inda ta samu wani worker ta tambayeshi eatery maki kusa nan yayi mata kwatancen wani close by eatery, anatse take tafiya harta isa wajen kwatancen don kuwa babu nisa tana zuwa tayi ordern rice and chicken portion biyu sai juice da ruwa shima guda hudu, tinawa da batayi chanjin kudi ba yasata tambayansu ko suna karbar dollar, Allah ko ya taimake ta suka suna karba, saida ta biya sannan ta dawo gida.



Zama tayi ta fara kwasar girki saida tajita dam tukunna ta kara komawa ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai after isha’I toilet ta koma tayi wanka ta sake maida rigarta sannan ta fito domin zuwa chanja kudinta zuwa nasu wato dirham, sannan kuma zataje tayi registering new sim….



Ta dade sosai don sai wajen eleven ta kammala ta dawo gida, nan ta fara kiciniyar gwada kiransu salima saidai shap ta manta bata saya credit ba, hakanan ta hakura akan zuwa gobe idan ta saka kati saita kirasu.



Amar kuwa shima bai tashi ba sai gab da magrib, sallah kawai yayi sannan ya dannan waya domin kiran me assisting nashi da dawainiyar gidan wato chef Pablo, Pablo shikeyin komai daga kan gyaran gida zuwa abinci, he’s a top one certified chef, saida ya bashi umarni sannan ya kawo mashi har sitting room dinshi na sama, zama yayi yaci yayi nak dukda bamai son cin abinci bane, wani wankan ya sake sanan ya sauka 3rd floor nan ne activity room wajen gyming dinshi, saida yayi few activities na motsa jiki sannan ya koma bedroom ya sake wani wanka sannan ya saka pj’s dinshi silky black riga da wando, tv kawai ya kunna ya fara kallon news ahaka har barci mai dadi ya kwashe sa,… mu kwana lpy sir Amar.





Toh ga oga amar fah😂 senior army officer…. lallai akwai show, don naga mutunne maiwuyar sha’ani sannan bashida yarda, ga uwa uba tsafta, amma kuma nikam meysa bayason anything related to mata ne? don naga abinda yayi ma amra baiyi min ba gaskia………..ku biyoni don jin ya zata kasance a UAE, sannan suwaye ke bukatar katin kasa….. love you all muah…..!!!!!!

Free page….



Chapter46-47



Yau Sunday antashi garin da ‘dan banzan zafi, amra kam baccinta ta dunga yi sbd gajiya, already daman tayi planning Sai Monday zata fara zuwa school domin ta karasa duk wani registration dinta, cikin sauri ta shirya cikin wata doguwar rigar material tayi mata kyau, daga wajen cikinta ta daure da igiyar sai kayan ya fidda shape dinta ya maidata kamar doll baby,



wato amra irin matanda ake kira da hour glass babe ce, donma rashin jin dadi da hutu duk ya danne duk wani sirrin kyan ta, ahankali ta kwashi purse dinta da wayanta sannan ta fito bayan ta kulle kofan ta da pin, ahankali ta sauka daga lft din apartment dinsu sannan ta duba wayanta ko rider dinta ya iso, ba’a fi 2mins ba saigashi ya iso, kutsa kai tayi cikin taxi din,.. within some minute sai gasu sun iso mall dama already acikin app din da tayi requesting ride din ta rubuta inda zai sauketa,…anatse ta bashi kudinsa 30 dirhams sannan ta wuce cikin mall din, ahankali take tafiya tana kallon yanda mutane ke shige da fuce, gudun kartayi kauyenci yasa ta fara bin masu wucewa ciki, saidata zagaye first floor sannan ta hau second floor, ahanakli take fitar da wani sirhintattcen murmushin jin dadi da farin ciki, wajen ya matukar burgeta gashi babu mutane sosai kodan yau Sunday, saidata zagaye ko ina sannan ta fara siyan abubuwan da zata buqata, wajen kayan man shafa ta tsaya dukda batasan wasu ba, da daimakon attendant din wajen tayi mata recommending na skin dinta, ahankali ta dunga zagawa, saida tayi siyayya daidai karfin ta sannan ta shiga wani grocery shop acikin mall din, nan ma few abubuwan buqata ta saya irinsu fresh milk, hydrated water, apples, banana, da vegetables, saidatayi leda wajen uku manya sannan ta fara jin kugin yunwa

7 Comments On AUREN KATIN KASA
avatar
salma-6

1 year ago

Reply

wonderful

avatar
salma-6

1 year ago

Reply

wonderful

avatar
fatima-7-2-5

1 year ago

Reply

I need complete one

avatar
fatima-7-2-5

1 year ago

Reply

I need complete one

avatar
aisha-2-9-6

1 year ago

Reply

I need complete pls

avatar
aisha-2-9-6

1 year ago

Reply

I need complete pls

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aisha-2-9-6

You can only get the complete by purchasing it through the Author

Please Login or Register in order to submit comment