Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ki?"

Sai na ji sanyi a raina,tunda ba laifin jiya da daddare bane,ni har na manta ma mun had'u da Kawu Ummaru,dama na san bakinsa ba zai yi shiru ba,na tausasa murya na fara magana

"Don Allah Ummi ki yi hak'uri, ban yi da wata manufa ba,ni na je neman aikin ne saboda na rage muku wani nauyin akan auren nan,amma tunda ba ko so ba,na bari in sha Allah".

Ummi ta ce" haba Zinatu! Waye ya fad'a miki ba za a yi miki komai ba? Kuma ko za ki nema da kanki tun da ba ki yi ba sai yanzu da aski ya zo gaban goshi? To ki kiyayeni Zinatu,abun naki ya isheni haka!".

Tuni hawaye su ka zubo min,na dinga ba ta hak'uri, har sai da na ga alamar ta hak'ura sannan na ce mata zan tafi, ba ta bari na tafi ba sai da ta bani abin kari na ci na k'oshi.


Mai hali dai ba ya fasa halinsa,ina fitowa daga gidan su Ummi kai tsaye laundry d'in Salim na wuce,yau ma da na je ban sha wuyar ganin wannan ma'aikacin da ya bani bayanan Salim ba,mu ka gaisa na rok'e shi ya kwatanta min wurin gyaran jikin Baby k'anwar Salim

Tiryan-tiryan ya kwatanta min,na yi masa godiya na kama hanya.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*&þFIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION&þ*


Page 9



K'arfe goma sha d'aya a shagon Baby ta yi min,na shiga wurin da sallama,ba wani girma ne da shi sosai ba,akwai ma'aikata su na ta aikin su,da tsirarun mutane da ake yiwa gyaran jiki,na ja kujera na kame ina raba idon ta inda zan ga k'anwar Salim d'in,duk da dai ban tab'a ganinta ba, amma na san idan na ganta zan ganeta,tunda jini ba ya b'uya

"Hajiya me za a yi miki? Gyara,ko kwalliya?". Wata ma'aikaciya ta tambayeni

Na d'an ji dam! Don kuwa dubu d'aya da d'ari biyu ne a jakata,don duka kud'ina su na cikin jakata da na manta ta a d'akin Salim,don haka ban shirya wani gyaran jiki ba

"Amm...Baby ba ta shigo ba?" Na tambaye ta,don ni dai burina na ga yarinyar

Ta ce"ai ba ta zuwa da wuri,da yake ita kwalliya kawai take yi,kin ga kwalliyar an fi yin ta da yamma,sai k'arfe uku take zuwa.Mu mu na yin kitso,k'unshi,wankin kai,da kuma gyaran jiki".

Na sauke numfashi na ce"ga shi kuma kwalliyar na ke so,unguwa zan je kuma sauri na ke yi,don Allah ko za ki kirata ta yi min?"

Ta ce"to bari na gwada,Allah yasa ta na free"

Ta d'auki waya ta kirata,ta yi mata bayani,sai ta kalleni bayan ta gama wayar ta ce"lallai kin yi sa'a,ta ce ga ta nan zuwa".

Na ji sanyi a raina,na yi mata godiya ina gyara zama

Babu jimawa ta zo wurin,aikuwa kallo d'aya na mata na yarda k'anwar shi ce,su na kama sosai,sai dai ita ba fara bace,kuma da alama za ta yi kirki,don sai gaisawa suke da y'an wurin cikin wasa da dariya.

Na gaisheta,duk da dai ba na jin za ta girmeni,ta maido min da gaisuwar ta na murmushi ta ce"ke ce za a yi wa kwalliya?"

Na ce"e ni ce".

Tace"ok,bismillah".

Na matso inda take zaune akan kafet,ta na shirya kayan kwalliyar,ta kalleni ta ce"to,ta nawa za a yi miki?"

Gabana ya fad'i,na dai dake na ce"ta d'ari biyar".

Ba ta yi magana ba ta hau yi min,ni dai ina ta kallon ta, sai can cikin son janta da fira na ce"uhm! Ni fa zan yi kwalliyar ne kawai! Amma ba ni da wayar da zan d'an yi hoto idan an gama"

Ta yi murmushi ta ce"ba ki da waya,da girmanki?"

Na ce"ina da waya,jiya ne na manta ta a d'akin saurayi na,kuma bai kawo min ba".

Sai na ga ta d'an yi damm,sannan ta ce"aikuwa da ya kawo miki".

Ta gama yi min kwalliyar,ta kalleni ta na murmushi ta ce"wow! Gaskiya kin yi kyau,ki na da kyau sosai".

Na yi murmushi na ce"kai Baby! Duk kyauna ai dai ban kai ku ba,ke da kayan ki".

Na yi zaton ma za ta tambayeni inda na san yayanta sai na ga kawai ta yi y'ar dariya,ta d'auki wayarta ta ce na tsaya ta min hoto

Na yi murmushi me kyau,ta d'aukeni,sannan na rok'eta mu yi tare,mu ka yi,mun yi kyau kuwa

Ta na shirin barin wurin na ce"don Allah zan rok'e ki wata alfarma"

Ta ce"ok,ina jinki".

Na ce"lambata zan baki,idan na karb'o wayata daga wurin Salim sai ki tura min hoton".

"Salim?" Ta fad'a da mamaki

Na yi murmushi na ce"e sunan saurayin nawa ne haka".

Sai ta yi murmushi ta ce"nice! Ni ma sunan Bros d'ina ne,kuma ina son shi sosai.Kar ki damu,ki saka min lambar,in sha Allah zan tura miki"

Ta k'arashe maganar ta na mik'o min wayarta,na saka mata lambar na fad'a mata sunana,na yi mata sallama,sannan na je wurin wadda ake bawa kud'in na bata na fito daga wurin da farinciki.

Shabiyu da mintuna na koma gida,na tambayi Mama ko Baba ya shigo da na fita? Ta maka min harara ta ce"ban sani ba! Ko tsoron shi ki ka fara yi yau d'in? Na ga dai ba yau kika saba taka umarninsa ba, shi ma ai da gangan ya ke yi,bai yi miki mari a k'afa ba kuma ya saka ran za ki zauna a gida? Aikin banza..."

Ni dai ban tanka ta ba na shige d'aki,na barta ta na ta yi.Y'an tsirarun kayana na had'a na wanke,na yi kwalimar d'akina,haka dai na yi ta k'irk'irar aiki duk dan kar na gaji da zaman na yi sha'awar fita,don ba a son raina na taka dokar Baba ba,dole ce kawai.



Fess! Ya fito cikin shirin sa na k'ananun kaya,jar riga da bak'in wando,sai k'amshi ya ke zubawa. "Sannun ku Mami,ke da autarki ne ku ke fira?". Ya fad'a ya na murmushi.

Mami ta kalle shi ta ce"Salim ba ka ci komai ba fa,tun safe".

Ya ce"e,yanzu zan je na ci".

Ya kalli Baby da take zaune ta na danne-danne a waya ya ce"my Baby,zan fita".

"A dawo lafiya" Ta fad'a ba tare da ta kalli inda ya ke ba.

Sai ya dafe kai,ya zauna kusa da ita ya ce"na fasa fitar ma,ta ya zan iya fita ki na fushi da ni y'ar'uwa?"

Ta juya kai gefe ta ce"ni fa babu ruwana da kai Yaya Salim,ka je kawai".

Ya ji babu d'adi sosai,ga Mami da take yi masa kallon tuhuma,don ba ta k'aunar duk wani abu da zai b'ata ran autar ta.Khadija(Baby) ita ce auta a gidan,akwai yayyun Salim guda biyu mata,wanda duk sun yi aure da y'ay'ansu,Baby da larurar ciwon zuciya aka haifeta,shi yasa duk gidan kowa ya ke tausayin ta,ake k'ok'arin faranta mata,ko kad'an ba a bari ranta ya b'aci don kar ciwon ta ya tashi,duk cikin gidan sun fi shak'uwa da Salim,kamar ya fi kowa son faranta mata rai,za ta iya cewa bai tab'a saka ta damuwa ba sai bayan had'uwar shi da Junaina.

"Don Allah ki zo ki rakani,zan yi miki wani abun mamaki,kuma na san zai faranta miki sosai".

Sai ta yi murmushi ta ce"ka tabbata?"

Ya na kamo hannunta ya ce"e mana".

Ta tashi ta shiga d'aki ta d'akko mayafinta su ka fita.Ta d'an b'ata rai ganin sun nufi restaurant ta ce"anan za a nuna min wani abun mamaki?"

Ya ce"yunwa na ke ji,mu fara cin abinci tukunna".

Ta yi shiru har su ka k'arasa,sai da ya ja Manager gefe ya fad'a masa kar a turo kowace yarinya sannan ya dawo wurin Baby su ka shiga d'akinsa.

Ta bi d'akin da kallo ta na d'age gira,don ta yi zaton za ta ga hoton Junaina,caraf idanunta su ka fad'a kan jakar mata y'ar k'arama,ta yi saurin k'arasawa ta d'auki jakar

Salim ya ce"ke yanzu daga ganin abu sai ki tab'a ba ki san me shi ba?" Cikin dauriya kawai ya yi maganar,don ya yi mamakin ganin jakar,kuma ya gane tabbas ta Zinatu ce.

Baby ba ta kula shi ba,ta bud'e jakar kud'i ne a ciki sai turare da waya,ta d'akko wayar ta danna aikuwa hoton Salim ya bayyana a fuskar wayar,sai ta juyo ta yi masa kallon tuhuma ta ce"Yaya,wannan jakar waye?"

Ya ji wani takaici,da haushin Zinatu ya rufe shi,ya ma rasa ta yanda zai yi mata bayani,ganin har ta fara hawaye ya ce"zauna don Allah,wallahi jakar me aiki ce,ina jin mantuwa ta yi a d'akina".

Baby ta yi tsaye da jaka a hannu ta na kallon shi,lokaci d'aya tunanin kalaman sa su ka dawo kanta da ya ke cewa'A'a Baby,da gaske na rabu da Junaina,farincikin ki shi ne nawa.Wata ce yanzu ba ita bace'

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ta furta cikin sanyin murya,ta tsaya kallon shi na d'an lokaci,sai kawai ta saka wayar a jakar ta rataya,ta nufi k'ofar fita.Ya yi saurin bin bayanta ya rik'ota ya ce "Baby! Wai ki na nufin ba ki yarda da ni ba? Wallahi da gaske ba ni da alak'a da me jakar nan".

"Amma me ya kawo hotonka a fuskar wayarta? Duka ma me zai kawo ta d'akinka bare har ta yi mantuwa? Haba Yaya,me ya sa za ka fara haka?"

Ta kai k'arshen maganar da sanyi sosai,kamar za ta yi kuka.

Ya dawo da ita,ya zaunar akan kujera ya ce"ki yarda da ni Baby,da gaske ba ni da alak'a da me jakar nan,ni fa ban ma santa ba,kuma ban san yanda aka yi aka samu jakar a d'akina ba, ina tunanin wani tarkon ne dai ake shirin yi min".

Ta yi saurin katse shi da fad'in"don a had'ani da kai? Ko kuma don a had'a ka da matan da ka ke kawowa?"

Ya ji kalmar kawo matan har cikin ransa,ba dan ya na gudun ciwon ta ya tashi ba,da yau sai ya wanka mata mari,ya cije baki ya ce"haba Baby! Ke fa k'anwata ce ba yayata ba,ya zan dinga yi miki bayani ki na neman jifana da wata manufar mara kyau? Oya tashi na maida ki gida".

Ya yi maganar ya na mik'a mata hannu,alamar ta ba shi jakar.Ta maida jakar baya ta ce"ba zan bayar ba,wallahi Yaya sai na ga me jakar nan ido da ido,sai na ji alak'ar ku da har take zuwar maka d'aki,ta yi zaman da za ta yi mantuwar jaka..."

Cak! Ta tsaya,ta yi shiru baki bud'e ba tare da ta k'arasa maganar ba,tunanin kalaman Zinatu na d'azu su ka shiga dawo mata,ta ce ta manta jakarta da wayarta a ciki,a d'akin saurayin ta,kuma sunan saurayin Salim,tabbas Salim d'inta ne buduruwarsa ce

Ta zauna hannunta har karkarwa ya ke,ta dubo lambar da Zinatu ta bata,ta danna kira.K'irjinta ya bada dum! Ganin ga shi a zahiri hasashen ta ya tabbata,don kuwa bugu d'aya wayar dake hannunta ta soma ringing.

Sai ta nuna masa wayar ta ce"Ashe ita ce? To ita ta fad'a min gaskiya, d'azu ta fad'a min ta manta wayarta a d'akin saurayin ta,ashe kai ne Yaya? Yaushe ka fara soyayya da wata bayan Junaina?"

Ya zauna shi ma ya na mamakin ta inda ta samu lambar Zinatu ya ce"ba ni wayar nan Baby".

"Na ce fa ba zan bayar ba,ni zan maida mata da kaina,kawai ka kaini gidansu". Ta yi maganar ta na hawaye

Hankalin sa ya d'an fara tashi,don ba ya son ciwon ta ya tashi,ya sassauta murya ya ce"sister ki tsaya ki fahimceni..."

"Wallahi Yaya ba zan fahimce ka ba,ta ya zan fahimce ka alhalin idona ya nuna min komai? Ba alak'ar gaskiya ku ke yi ba,shi ya sa tun farkon had'uwar ku ba ka bani labari ba ko?"

Ya yi shiru ya na kallon ta.Ta d'ora da fad'in"zan yi maka wata alfarma guda d'aya,ba zan sanarwa da kowa ba,amma fa idan ka min alk'awarin za ka kaini gidansu".

Ya ce"subhanallah! Ba ki yarda ba kenan? Wallahi ban san gidan su Zinatu ba,hasashen ki ba gaskiya bane".

Ta ce"ba abun mamaki bane,na yarda ba ka san gidansu ba,tunda ba ka da niyyar aurenta,shikenan Bros na fahimce ka,amma ni zan nemo gidansu zuwa gobe,zan je za mu yi magana da ita"

Daga haka ta fice daga d'akin cikin sauri ta na rik'e da jakar
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*&þFIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION&þ*


Page 10



A cikin kwana biyun da suka wuce na yarda da lallai Salim ba iya burgeni ya ke ba,har da so mai tsanani ma kuwa,don kuwa tunaninsa ya hanani sakat,komai na ke yi ya na raina,hotonsa ba ya b'ace min daga idon zuciyata,burina kawai na ganshi,ko na ji muryarsa, amma na yi alk'awarin ba zan koma kamfanin su ba,don gaskiya ina jin tsoron mu sake had'uwa da kawu Ummaru,kuma ba wai kawun na ke tsoro ba,b'acin ran Ummi ne kawai ba na so,kuma ba na son komawa gidan cin abincin nan a samu matsala,shi ya sa ma na hak'ura,na zubawa sarautar Allah ido,don na san dai idan Salim ya koma d'akinsa dole zai ga jakata,kuma idan da imani ai ko bai nemeni ba zai sa wani ya kawo min.


K'arfe goma na safe Habib ya zo gidanmu,bayan mun gaisa ya ke tambaya ta ina wayata,wai ya na ta kira ba na d'agawa,ya shiga damuwa ya yi zaton ko akwai matsala.Na tab'e baki kawai na ce masa "hutun amsa kira na tafi"

Habib ya yi murmushi ya ce"kirana ko?"

Na turo baki na ce"zancen ya isheni haka fa,ko dama shi ya kawo ka?"

Ya ce"a'a,shikenan an bar shi". Mu ka d'an yi fira,har ya nuna min gidanshi,wanda za mu zauna a ciki,na kalla na ce ya yi kyau,ya tambayeni komai ya yi min,ko da wani gyaran? Na ce ai gidanshi ne,kar ya biyewa ra'ayina,bai jima ba ya tafi,don dama daga wurin aiki ya zo gidan namu.

Ya na tafiya nima na k'ara gaba,wurin Anas na je na ari wayarsa,na saka lambata a ciki na danna kira,ban yi zaton za a d'aga ba,don duk a zatona har yanzu ta na d'akin babu wanda ganta,ga mamaki na sai na ji muryar mace ta d'aga da sallama, na amsa ina nazarin muryar,mu ka yi shiru na y'an sakanni kafin ta ce"waye me magana?"

"Me wayar ce" Na bata amsa

Ta ce"Zinatu ce?"

Na ce"e,sai na ji muryar kamar ta Baby"

Ta ce"e ni ce,wayarki ta na hannuna,ki kwatanta min gidanku zan zo na kawo miki yanzu".

Na d'an yi jim! Ina tunanin ta yanda wayar ta je hannunta,sannan na kwatanta mata tiryan-tiryan,ta yi min godiya ta ce ga ta nan zuwa.

Na bawa Anas wayarsa,sai da na siyi ruwa da lemo sannan na koma gida,na d'an k'ara kimtsa d'akina na kunna turaren tsinke,har tsakar gidan nan share,duk da na ga Mama ta share da safe,Allah ma ya taimakeni ma su siyan waina sun watse,na koma d'akina ina zaman jiranta

Ina kwance ina sak'a da warwara na ji muryarta ta na rangad'a sallama na tashi na tareta da fara'a,Allah ya taimaka Mama ba ta nan,bare ta sa mana ido,bayan ta zauna mu ka gaisa,na ba ta ruwa

Ba ta sha ba ma,ta mik'o min jakata sannan ta nisa ta ce"Zinatu zan tambayeki,ki fad'a min gaskiya don Allah".

Na d'an ji dam! Na ce"to in sha Allah".

Ta ce"menene ya had'aku da Salim har ki ka je d'akinsa ki ka manta jaka?"

Na yi shiru ina tunanin na fad'a mata gaskiya,ko na yi k'aryar da za ta shigar da ni rayuwar Salim.Ban gama yanke shawara ba na ji muryarta "don Allah ke ki fad'a min gaskiya, shi ina kokwanto akan abin da ya fad'a min".

Cikin y'an sakanni dabara ta zo min,na ce" zan fad'a miki gaskiya, amma da sharad'i".

Da d'an mamaki ta ce"sharad'i kuma? Na meye?"

Na gyara zama na ce"ina son ki ba ni labarin soyayyar Salim da Junaina,da kuma abin da ya rabasu,sannan ki samo min lambar ita Junainan,ko kuma adireshin ta".

Baby ta tsaya kallona kamar me nazari,cikin so tabbatar mata na ce"wannan shi ne sharad'in,amma idan ba zai yiwu ba babu dole fa,za ki iya auna k'aryar da Salim ya yi miki".

Ta nisa kafin ta ce"amma ke me yasa ki ke son jin labarin?"

Na ce"ina da babban dalili,ke dai ki sanar min daga baya kya ji dalilin"

Ta ce"to shikenan,amma dai kin san ba zai yiwu na san komai ba,saboda haka iya wanda na sani zan sanar dake".

Na gyad'a kai alamar gamsuwa.Ta fara ba ni labari "Junaina y'ar jihar Katsina ce,a Manumfashi,gidansu su na da yawa,amma ita k'ad'aice mace,ta na da kyau babu laifi,ina tunanin za ta kai shekara ashirin da biyar.Wani yayanta ne abokin Salim,wanda su ka yi makaranta tare a Egypt.Wata rana Salim ya kai masa ziyara Katsina,saboda ya duba shi,sakamakon rashin lafiya da ya ke yi,a ranar ne suka had'u da Junaina,Yaya ya ce ya na ganinta ya ji k'aunar ta,amma ya dake har ya baro garin bai nuna ba,ashe ita ma haka ta kamu da son shi,ta samu lambar shi a wurin yayanta,ta yi ta damunsa da kira da sak'onni har dai ta bayyana masa son shi take,ya amince da ita,ya na mugun son ta sosai,lokaci d'aya duka dangi kowa ya sani saboda yawan zuwa Katsina da yake yi,in dai ka na son ganin Salim a farinciki to ka yi masa firar Junaina.Ganin da gaske suke soyayyar, ya sa Abbanmu ya ce ai kawai gwara ayi auren kowa ya samu nutsuwa,sai dai ana zuwa da zancen aure Junaina ta ce ta amince,amma ba yanzu ba,sai ta yi digiri"

Baby ta sauke numfashi,ta tab'e baki ta ce"saboda babu gaskiya, tun da me take yi ba ta yi digirin ba?"

"Gaskiya kam!" Na fad'a ina gyara zama.

Ta cigaba "kuma ta ce ita a Kano take son yin karatun,Yaya ya fi kowa jin dad'in hakan,saboda ya dinga ganinta akai-akai,admission ma shi ne ya sama mata,kuma ya d'auki nauyin karatun ta da duk wasu buk'atun ta,mahaifinta shi dai godiya ce kawai aikinsa,B U K ta fara zuwa,da farko ta na karatun kamar abin arzik'i,Salim ya na ta hidima da ita,sai daga baya wasu mazan suka fara d'auke mata hankali,mutane da yawa sun so ankarar da Salim,amma ya k'i yarda,saboda tsabar k'aunarta.Haka ake ta tafiya,abun Junaina ya na k'ara gaba,shi kuma ya na k'ara rufe idonsa,har dai ta kai ga ta daina b'oye masa komai, ta na kula samari a gabansa,ya sha zuwa ya tarar da ita da saurayi sai ta ce masa abokinta ne,idan ya ga abun bai yi masa ba zai iya canza shek'a,haka ya yi ta hak'uri ya na daurewa,saboda ba ya so ya rasa ta"

"Kin san wani abun takaici?". Ta dakata,tare da tambaya ta.

Na girgiza kai alamar a'a.Ta d'ora" daga k'arshe dai Junaina sai da ta yarda da samarin shaho,suka d'auke mata hankali,tun ta na yiwa makaranta asha ruwan tsuntsaye har ta daina karatun duka,wani saurayin ta ya kama mata gida a 'Dorayi,yanzu haka ta na can da zama".

"Subhanallah! Zaman kanta take yi kenan?" Na tambaye ta da mamaki.

Ba ta bani amsa ba ta d'ora"lokacin da ya ankara kar ki so ki ga yanda ya shiga tashin hankali,sai da ya kusa shafe wata d'aya a kwance,ya na daga kwancen yana kiran wayarta,amma wallahi ba ta zo ta duba shi ba.Da k'yar mu ka samo kan shi,ya dawo cikin hayyacin sa,amma duk da haka sai ya cigaba da bibiyarta,ita kuma ta na yi masa wulak'anci son ranta,amma wai a hakan ta ce masa shi za ta aura idan zai jirata,kuma kud'i ko nawa ne idan tana bukata shi take tambaya ya tura mata ko ya kai mata".

Na jinjina kai na ce"tabb! Amma wannan ta cika y'ar rainin hankali!".

Baby ta ce"ai duk ba ma wannan bane abin haushin,kin san kuwa y'an'uwanta shi suke zargi da lalata musu y'arsu?"

Na zaro ido cikin mamaki na ce"rainin hankali! Ai sai su zo su gani"

Baby ta ce"su ga me!? Shi fa suka kira,kuma ya tabbatar musu da shi ne ,kawai saboda ya kareta. Ke so fa k'addara ne!"

Na ce "tabbas! Lallai wannan Junaina ta cika mara rabo".

Ta cigaba"to daga baya ta dawo ta ce masa ta daina komai,ya ba ta jari za ta fara sana'a,saboda mahaifinta ya gargad'e ta k'ar ta kuskura ta koma Katsina,jiki na rawa ya d'auki kud'i masu yawa ya bata,ta bud'e wani wurin sai da kayan sawa,na maza da mata,amma duk da haka dai ta k'i yarda da auren su.Ba mu san lokacin da ya fara shaye-shaye ba,ba mu san dalili ba,amma gaskiya duk mun fi danganta abun da halin da Junaina ta saka shi ne ya jefa shi a harkar".

Ta d'ora " kuma ya ce shi zai jira har lokacin da za ta nutsu,ta amince da aurensa,ba zai tab'a yin aure ba,saboda ta ce muddin ya yi aure to ta rabu da shi har abada! A cewar shi dai yanzu ya rabu da ita,amma duk ba mu yarda ba,sai dai daga lokacin da na ga jakarki a d'akinsa na fara zargin wani abun kuma na da ban.Wannan shi ne labarin Junaina,sai ki cika alk'awari ki fad'a min gaskiyar tsakanin ki da Yaya".

Hawayen da ban tantance ko na meye ba suka shiga zubo min,tun ina gogewa har na fashe da kuka sosai.Wata k'aunar Salim da tausayin shi suka yiwa zuciyata dirar mikiya,har na ji idan ba shi na aura ba ni ma har abada ba zan yi auren ba.

Baby ta tsaya ta na kallona da alamun mamaki,sannan ta ce"Allah yasa dai ba zatona bane ya ke shirin tabbata!".

Na yi shiru ina saita kaina,na ce"ko kad'an,Baby kar ki zargeni ko d'an'uwanki,yanda ya fad'a miki d'in na san gaskiya ne...". Na kwashe labarin tun farkon had'uwarmu har izuwa ranar da na bar jakata na fad'a mata.

Ta yi shiru kamar me tunani,sannan ta kalleni ta ce"Zinatu tsakanin ki da Allah da gaske ki ke son Salim?"

Na yi saurin fad'in"wallahi har zuciyata nake k'aunar Salim,tunda na yi masa kallo d'aya,idan so ya na zama k'addara to son Salim shi ne tawa k'addarar". Na fashe da kuka

Cikin sanyin murya ta ce"ayya! Ki bar kukan haka,ba zan yi miki alk'awarin auren Salim ba,amma zan yi iya yi na ganin na had'a alak'ar ku,ke ma sai ki had'a da addu'a, da kuma y'an dabarun ki".


Na ce"na gode sosai y'ar'uwa,amma a ganina me zai hana na shiga jikin Junaina,na karanci halaye da d'abi'unta,ko koyi da ita zai sa Salim ya maye gurbinta da ni?"

Baby ta yi murmushi ta ce"Zinatu gurbin ido ba ido bane,kuma shi so babu ruwan shi da halayya,tunda ita d'in yake so,to fa ko za ki yi birgima a tab'o ki koma kamarta sak,bai zama lallai ya so ki ba".

Na jinjina kai na ce"hakane,amma duk da haka ina son ganin ta dai,ki taimakeni da lambarta don Allah".

Ta ce"wa!? Ni kam me zan yi da lambarta,kin san yanda na tsaneta kuwa? Zan dai kwatanta miki wurin sana'arta idan ki na so".

"Ina so!" Na fad'a da sauri.

Ta kwatanta min,babu nisa ma sosai,a zoo road ne wurin,kuma siffanta min kamannin ta

Na rakata har bakin titi ina ta kwarara mata godiya kamar ba gobe.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_


BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_


*&þFIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION&þ*


Page 11



Ina dawowa daga rakiyar Baby,na zauna na kira lambar Salim,har ta katse bai d'auka ba,sai da na kira sau uku sannan ya d'aga cikin fushi ya ce"ke! Lafiya kike kira na?"

Na d'an ji fad'uwar gaba,amma na dake na ce"lafiya lau,na kira ne kawai na gaishe ka,kuma na ji lafiyarka".

Bai bani amsa ba,kawai ya kashe wayar.Na
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment