Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[9/17, 5:23 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain we touch the heart of readers_*

P.m.l

*Dan allah duk mai ra'ayin krnt book dinnan ya karanta sbd banaso sai na fara wani ya biyoni private yace inturo mashi daga farko nasha wahala sadda nayi nida yah fauzan shiyasa na yanke shawarar bazan turama kowa ta private ba*πŸ™πŸ™πŸ™

*Nafara book dinnan ne sbd banaso ya kaini har gab da sallah ban gama ba shiyasa na yanke shawarar bari nafara yau*


*BISMILLAHIR RAHMANU RAHEEM*

CHAPTER 1\5


Yarinya ce wadda bata wuce shekara 20 ba,zaune take tana kuka idanunta sunyi jawur sbd kuka,doctor Bilkisu tashigo tanufi inda take tace"haba rahama kukan me kikeyi.
Tunda aka kawo ki kike kuka, kisani kuka bazai magance matsalar da kike ciki ba.

Doctor tace"ina danginki suke"?ba amsa sai sautin kukan da takeyi ke fita, doctor ta amshi babyn daga hannunta ta kwantar da ita.
Tace"rahama ki kwanta ki huta idan na dawo zamuyi mgn,bayan fitar doctor garin yayi jawur da hadari,iska ta ko ina kad'awa yake.


Rahama ta mike ta d'auki babyn a hannuta tafito,iska nata kad'awa kowa ya koma ciki sbd iska.

Rahama ta nufi wata baranda ta aje babyn hannuta tafita da sauri,dr bilkisu ce tafito da alama gida zata,jin kukan baby yasa tai ta juye juye ko zataga daga inda kukan yake fitowa.

Ganin bataga komi ba yasa ta nufi mota zata shiga,d'aga kan da zatayi ta hango babyn nata kuka a baranda.

Da sauri taje ta d'auka ta kwala ma masu gadi kira suka fito,ta tambayesu sunga wadda ta aje baby a nan"?

Sukace Aa wlh basu gani ba.

Ciki takoma tana tambayar nurses wacece tafita yanzu"?d'aya daga cikin nurses d'in tace"ta wance gadan tafita.

Dr tajuya taga gadan da rahama take ake nufi,tace"subhanallah toh ta aje babyn tatafi.

Kowa mamaki ya kamashi,nurses suka ce"indai wannan mai kukan ce zata aikata.

Sbd tunda tazo take kuka har tafita,cikin biyu dole ayi guda,ko cikin shege ko dangi sun juya mata baya.

Dr takira mijinta tace dan allah ya sameta gidan marayu tasamu wani case ne,gidan marayu aka kai babyn.
Mijin doctor yayi helping dinta akayi cike ciken papers.

Suna zaune a inda zasu bada yarinya bayan sun gama yin bayanin yanda suka sameta.

Wata mata da bata wuce shekara 35 ba tayi shiru tana sauraren su.

Bayan sungama bayani matar dake can gefa taji san babyn ya kamata.

Tamike tace"baiwar allah idan bazaki damu ba,ina so zan amshi babyn da kika kawo.

Dr tace"kamar ya

Matar tace toh nidai sunan khadeeja,shekarata 18 da aure amma d'a d'aya allah ya bani.

Ina bala'in san d'iya mace shine na yanke shawarar inzo gidan marayu in adopting baby mace.

Dr jikinta yayi sanyi tace" toh nidai nariga na kawo baby nan,izinin ansarta na wurinsu.

Matar tace sir ina so zan amshi babyn,yace toh dr kinji tanaso.

Kuma ina mai tabbatar maki bakida matsala,sbd mijin abokina ne, shi ya faramin mgn kan yana so ya amshi babyn.

Dr tace"toh nidai ina da mgn,ayi a rubuce cewa duk radda uwar yarinya ta dawo zata koma hannunta.

Matar tace ta yadda,aka d'auki baby aka ba mata.

Bayan rahama takoma gida tayi wanka ta zauna kan gado tana tuno abinda ta aikata a rayuwarta.

*KATSINA STATE UNIVERSTY*(UMYUK)
Yarinya ce wadda bata wuce shekara 18 ba,sanye take da jeans nd t-shirt duk surar jikinta tafito,fuskarta d'auke da murmushi.

Wasu yan mata biyu suka nufota da fara'a.

Inda take sukazo tare da cewa ramcy sai yanzu koh.

Tayi murmushi tare da cewa kai babies irin wannan shining da kuke miyen sirrin"?

Sukayi dariya tare da cewa"ai duk wani wanda zaiyi shining ya biyo bayanki.

Ta cire glass din dake fuskarta tace"kai nifa ba lectures ta kawoni ba.

Nazo na d'auke ku muje yawo,sukace"ramcy test fa za'ayi yanzu.

Tace"to miye basai mu bi malamin da kud'i ba ya bamu marks.

Sukace"yayi babbar yarinya muje kawai.

Fita sukayi daga cikin mkrnt,sai karfe goma suka koma gidan da aka d'aukar ma rahama dake *sardauna estate* ta zauna ciki.

Washe gari suka tafi mkrnt, dukkanin su sanye suke da jeans nd t-shirt.

Class suka nufa,ganin wanda ke ciki yasa suka tsaya cak.

Ummita tace"ramcy shiga class bai ganki ba dan kau d'an sa ido ne.

Rahama tayi tsoki tare da cewa"wannan stupid din wlh ya takura mani.

Minal tace"ai kawai kiyi tafiyarki karki shiga,rahama tace damani bawai san shiga nakeyi ba.

Bari naje hostel in dawo,sukace toh sai kin dawo allah yasa karya ce ina kike,



By:πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:23 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
(For Loveβ™₯ndJusticeπŸŽ“)
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain we touch the heart of readers_*

P.m.l


DECATION TO *Maryerm Mukhtar Fans*

Chapter 6\10

Class din suka shiga ya dakatar dasu,tare da cewa" ummita ina rahama take?" sukace"sir tana gida bata da lafiya.

Yayi murmushi sannan yace"toh kuje.

Suka wuce suka zauna,bayan anfito daga lectures,rahama ta dawo nan cikin mkrnt,tana tsayw jikin mota lectura dinsu yazo wucewa, had'a ido sukayi dashi ya dawo inda take yace"rahama akace bakida lafiya.

Ta dan rusana tace"eh sir na d'anji sauki yanzu nashigo shcool din.

Yace"ki sameni office d'ina yanzu,tace toh sir gani nan zuwa.

Bayan tafiyarshi tayi tsoki tare da fad'in kai wannan mutumin wlh ka cika takura,sai shegen sa ido.

Muryar minal taji tana cewa"keda wa ramcy?"

Tace"wakike tunanin zai matsa ma rayuwata irin Muhamnad auwal,sukayi dariya tare da cewa"ya ganki kenan?"

Tace"ya ganni wlh nifa gsky idan ya cigaba da samin ido toh wata rana rashin kunya zan mashi.

Ummita tace"yanzu ina zamu?"rahama tace kafin muje ko ina zanje wurinshi kirana yake.

Sukace"toh fa sai kin dawo,tafiya tayi tana zuwa bakin office d'inshi tayi knocking yace"yes

Shiga tayi ta zauna ya tsaya yana kallanta,daga bisani yace"rahama wai mike damunki a rayuwa"?

Tace"sir me kagani"? yace rahama haka d'iya tagari akace tayi yawo"?


Cikin ranta tace"toh nan kuma aka kamo uban sa ido,ta d'ago ido tace"sir me kayana sukayi.

Ya girgiza kai yace"rahama bakisan karatu,bakisan sa sitirar kirki,gaba d'aya kin koma kamar ba musulma ba.

Ya sake da cewa"look rahama zan gaya maki dalilina na ganin kin shiryu,rahama ina sanki kuma aurenki nakeso nayi.

Batasan sadda dariya ta kwace mata ba,dariya take sosai,da taga ya d'aure fuska sai ta nutsu.

Yace"dariya na baki"?

Tace"no sir kawai dai naji abin kamar a firm,ya girgiza kai yace"toh na baki nan da sati d'aya kije kiyi tunani,

Mikewa tayi tafita,har kan hanya dariya take idan ta tuno kalmar da muhammad auwal ya gaya mata.

Ta iso wurin mota su ummita na tsaya,ganin tana dariya yasa sukace lfy kike dariya"?tace"kai wlh akwai banzayen mutane a duniya.

Tafad'i masu abinda ke faruwa,suma dariyar sukayi,har suka shiga mota suna dariya.

*Yau takama ranar weekend*
Suna zaune rahama ke cewa"kai yau fa honorable zai shigo gari.

Sukace"kai da gaske"?

Tace"wlh dan har munyi waya dashi,dan haka kunga zanje salon daga can zan wuce wurin gyeran jiki.

Minal tace" kai kice zamusha ruwan nairori,rahama tayi murmshi tare da fad'in yanzu tashi zanyi intafi.

Sukace"owk sai kin dawo,karfe 2:00 dai dai ya sauka,gidanshi dake cikin garin katsina,unguwar g r a.

Daga wurin gyeran jiki rahama ta wuce gidan honorable,yana zaune falo tare da baki,shigowarta ya sallami bakin.

Ta zauna kusa dashi tana fad'in sweety sannu da zuwa,yayi murmushi tare da kai hannushi bisa fuskarta yana fad'in yawwa darling.

Mai aiki ya shigo ya kawo masu lemu,ta zuba tana sha.

Kallanta ya tsaya yana yi daga bisani yace"darling naga kinyi kyau sosai,tace"sweety ba dole nayi kyau ba na kashe dubu hamsin wurin gyeran jiki dan kai kad'ai.

Yace"kai gsky dole na na linka wajen biyan kud'in kwalliyar nan.

Hannu ya kai zai ta'bata tai saurin mikewa,tare da cewa"sweety kasan moto d'ina yana bani matsala.

Kuma banso nayi ma old man d'ina mgn sbd yana kashe kud'i a kaina.

Yace"toh darling sai asake maki wata,rahama tace sweety kwana nawa zakayi"?

Yace one week kawai.

Tayi wani d'an murmushi ta dawo kusa dashi tace"amma fa yau dole muje club.

Ya girgiza kai alamar a'a

Yace"darling kinsam ni d'an siyasa ne,muddin aka ganni tare da mace a club toh zan samu matsala.

Ta turo baki tare da cewa"toh why not bazamu had'a party dinmu ba a nan.

Yace"owk amma party din dagani saike sai kawayenki ummita da minal.

Tayi tsalle tare da cewa"yes na yadda.

Da daddare aka gyera falon aka jera lemu kala kala,aka kunna music.

Rahama ce tashigo ita dasu ummita,sanye suke da jeans nd t-shirt.

Honorable ya fito,rungume juna sukayi shida rahama, suka ida isa cikin falon.

Kid'i nata tashi.

Rahama ta mike ta d'auki kwallbar veer ta zuba a cup tana sha.

Rawa suka fara ita da honorable,ummita da minal da gaba d'aya hankalinsu baya jikinsu sunyi mankas.

Rahama tafara ganin bishi bishi,honorable da yaga kamar bata cikin hankalinta ya sungumeta ya nufu d'aki da ita.

Cikin yana yin maye taji kamar wani nugun abu na shirin faruwa da ita,ta bud'e ido.

Ganinta tayi daga ita sai breziya da panta,ga kuma honorable da yake kokarin cire mata bra.

Tamike cikin yana yin maye tare da cewa"honorable miye haka,pls ka rabu dani bacci nakeji ta fad'a kan gado.

Muryar minal yaji tana cewa"honorable kyale wannan,kazo ni zan baka abinda ka dad'e kanaso ka samu daga wurin rahama baka samu ba.

Yayi murmushi"ya nufeta



By:πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:23 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
(for loveβ™₯nd justiceπŸŽ“)
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain we touch the heart of readers_*

P.m.l


*DEDICATION TO MARYERM MUKKTAR FANS GROUP*


Chapter 11\15


Kallonta yayi daga sama har kasa,sannan yace"minal bake nakeso ba,kawarki ita nake ra'ayi dan haka ki daina kokarin saka kanki tsakanina da ita.

Ya karasa maganar yana tafiya.

*Washe gari*
Basu tashi daga bacci ba sai around 11:00 bayan rahama tayi wanka ta maida kayan da tacire.

Falo tafito honorable na zaune yana waya,tayi wani murmushi tare da zama kan kujera.

Bayan ya gama ya kalleta yace sweety kin tashi lfy"?tayi wani fari da ido tace lfy qlau darling.
Yace"toh me kikeso akawo maki"?tace tea kawai zansha,ya kira mai aiki ya kawo mata tea.

Tana sha yace"sweety wai sai yaushe zaki bani dama ne akan abinda nake nema wurinki"?
Tayi murmushi tace"haba darling nifa macece,duk iskanci na bana tunanin zan iya aikata abinda kakeso.

Sbd zan wulaqantar da kaina.

Ya girgiza kai cikin ranshi yace"hmm indai muna tare sai na samu abinda nakeso.
Fitowar su minal yasa suka tsaya da mgnr da sukeyi,minal tace"ramcy tashi muje kinsan fa dole muje shcool gobe koh.

Rahama tace"eh nikam ba zanje shcool cikin week dinnan ba,sbd kunga honorable na nan,so zaku iya tafiya,anjima zanzo in d'auki kayana bazan dawo ba sai darling ya tafi.
yayi dariya tare da fad'in gsky kina bani mahimmanci sosai.

Tayi murmushi ai dole na kula da kai,kaga kafin ka tafi sai kabani yan kud'in da zan kashe sbd yana yin rayuwa.

Yace"don worry sweety dole nacika maki jakarki da kud'i.(πŸ˜”allah ya shirya mana zuri'a)

Satin shi d'aya da ya tashi tafiya yaba rahama kud'i masu yawa.

Rahama na zaune d'aki tana waya da wani saurayinta,minal tashigo tare da fad'in ke aje wayar kiji.

Ta kashe wayar tare da cewa" meya faru"?

Minal tace"next week za'afara exam,kuma muhammad auwal nata nemanki ya kuma san satinki d'aya baki shiga shcool ba.

Rahama tayi tsoki tare da cewa"stupid man d'innan allah kai tsaye zance bana sanshi.
Dan bazai takura ma rayuwa ta ba,minal tace" toh amma dai da kunya kigaya mashi haka kai tsaye.

Rahama tace"ke kinsan zan iya,rashin kunya ba wadda ban iya ba.


Rahama bata shiga shcool ba sai ana gobe za'a fara exam, sanye take da riga da skirt na atamfa,tayi irin d'inkin nan mai rabin nono waje.

Gaba d'aya surarta ana gani,rahama yarinya ce kyakyawa san kowa kin wanda ya rasa,indai zatayi kwalliya tazo gittawa sai an kalleta.

Suna fitowa daga mota dai dai m auwal ya fito shima, sukayi ido hud'u da rahama.

Ta dukar da kanta kamar bata ganshi ba,yace"nasan kin ganni ba sai kin d'auke kai ba.

Tayi murmushi tace"sir banganka bane ai,yayi murmushi yace ya jikinki"?tace"sir ance maka bana da lfy ne?

Yace A'a amma nasan zakice bakida lfy,sbd two weeks kenan baki shigo shcool ba.

Tace"ayya sir naje kd gida ne,yayi murmushi yace owk,yaushe kika dawo?

Tace"jiya

Ya girgiza kai yace"kai rahama wai meyasa bakisan fad'in gsky ne"?

Tace"sir bana fad'in gsky fa kace,yace"yes

Sbd na ganki 4days ago a sajuma keda wani bansan waye ba.

Ta d'ansha jinin jikinta tace"Oho na tuna eh nice.

Ringing phone dinta tafara,tana dubawa taga honorable ne,taki d'auka.

Yace"kuje idan kin gama abinda zakiyi kizo office ina san ganinki.

Yana tafiya tace"stupid kawai.

Ummita tace"rahama wlh m auwal na sanki sosai,minal tace"kedai bari amma ita sai wani shan kamshi take.

Rahama tace"kai nifa bazan so shi ba,me zanyi dashi ya cika ustazanci,nikuma nafisan big boy.

Sukayi dariya tare da cewa"big girl kuma sai big boya dama.

Karfe 12:00 suka gama abinda zasuyi, rahama tace kubari naje wurin stupid din cen,kujira na dawo.

Sukace"owk

Yana zaune office yana cike papers,tashigo ya kalleta ganin irin yanda kirjinta ya bayyana waje yasa yace"rufe jikinki da gyelan hannuki.

Ta rufe tare da turo baki,ya fara da cewa"toh rahama time din dana baki yayi har ya wuce.

Mekika ce"?tayi shiru sannan tace"sir kasan yanzu dai karatu nike,kuma kaga tsarinka da nawa ba d'aya bane.

Kawai dai ka nemi wata,wani irin das yaji a ranshi,sbd irin san da yake mata.

Ya dafe kai tare da cewa"rahama baki sona"?

Tace"eh gsky

Hannu ya d'aga mata alamar ta tafi,tamike tafita.

Tana zuwa wurin mota ta gayama su minal abinda ya faru,basu so abinda tayi ba,amma suka kyaleta.

M auwal kam gaba d'aya ya rasa ta inda zai shawo kan abin,sbd bayajin zai iya rabuwa da rahama ba.

*Washe gari*
Suka shiga exam ba abinda rahama tasani bare ta rubuta,ana fita exam d'in taje ta biya lectura d'in kud'i dan kar ya kada su.

Bayan tafito daga office din lectura d'in,tana cikin tafiya phone d'inta tafad'i.

Ta duka zata d'auka sukayi ido biyu da m auwal,d'auke kai tayi ta duka ta d'auki phone d'in tayi tafiyarta.

Cikin ranshi yace"ya allah kabani rahama.

Yau exam d'in m auwal zasuyi chemistry,rahama kuma tasan bazata iya sayenshi ba.

Tashiga exam d'in taga ba abinda zata iya yi, bayan sunfito minal tace"ramcy ya zamuyi"?

Tace"bawani mafita illah zamu fad'i exam d'innan kawai.




By:πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:23 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
(for love ndβ™₯ justiceπŸŽ“)
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain we touch the heart of readers_*

P.m.l

Writeen:by Maryerm Mukhtar

*Chapter 21\25*


Tayi murmushi tajuya suka tafi,

*Monday*
Sun shigo mkrnt dan su duba result,komi sunci amma banda chemistry,Rahama tayi murmushi tace"stupid man wato hana mu chemistry yayi.

Minal tace"nikam banga laifinshi ba,Rahama tace"kubari naje na dawo,office din m Auwal taje dai dai zai fito sukaci karo.

Ta d'ago kai ta kalleshi tare da cewa"sir dama wurinka nazo,yayi murmushi yace"owk ina jinki.

Tace"sir naga bani da exam d'in chem ko dan ban yarda ta tayinka bane?"

Yace"A'a Rahama baya daga cikin dalilin, Rahama bakiyi karatun exam ba shiyasa kika fad'i.

Tace"sir koh.

K'arar da phone d'inta tayi ya katse su,dubawa tayi taga honorable ne,nan yake gaya mata yazo gari,tace"owk gatanan zuwa yanzu.

Ta aje wayar, m Auwal yace"Rahama wake kiranki?"

Tace"saurayina, ya girgiza kai tare da cewa" No Rahama kar kije.

Tace"toh sbd me?"yace"Rahama zuciyata na gayamin akwai abinda zai faru dake.

Tayi mashi wani kallan banza sannan tace"aikam wlh sai naje,da da nake zuwa tambayarka nake.

Juyawa tayi tatafi,taje ta d'auki su minal suka tafi,tana aje su minal ta wuce gidan honorable.


Wajen 4:00 Rahama ta isa gidan honorable,yana bisa dining zaune Rahama tashigi.

Ta isa inda yake ta zauna,kallanta yayi tare da bud'e kwalbar veer ya zuba mata.Rahama tayi tatul da giya.


Mikewa tayi cikin maye tace"sweety ni zanje in kwanta,ciki tashiga honorable ya mike ya bita ciki(innalilahi wa'inna ilaiheer raji'un😭😭😭 bawa baya kauce ma kaddarar sa)

Karfe 10:00 na dare Rahama ta farka,ta ganta cikin wani hali, kuka tasaki tare da dafe kai,kuka take mai shiga rai,honorable ya fito daga toilet,kallanshi tayi tare da cewa"abinda kaimin kenan?"

Allah ya isa ban yafe maka ba,in allah ya yadda sai kayi nadamar abinda kamin,mikewa tayi tasa kaya tafita.

Dariya yayi tare da cewa"allah ya isarki ta banza,an gaya maki kud'in da nike baki na banza ne.

Haka Rahama takama hanyar sardauna estate tana kuka,koda ta isa bata gayama su minal komi ba.

Sundai ga tana kuka.

Tun daga ranar Rahama tashiga damuwa,bata da wani walwala sai kuka.

Aka sake hutu kowa ya koma gida.

Mom taga dai Rahama duk ta canza ta tambaye ta lafiya meke damunta?"tace bakomi.

Rahama hutu ya kare takoma mkrnt,yau wata 4 da faruwar abin.

Sunfito daga lecture ne,Rahama taji zuciyarta na tashi, batasan lokacin da amai ya yanke mata ba.

Nan su minal suka bata ruwa ra wanke fuskarta,tana d'agawo sukayi ido biyu da m Auwal.

Ganin yanda Rahama ta reme duk ta lalace yasa ta bashi tausayi.

Tafiya gida sukayi,nan ciwo ya danneta,m Auwal ya lura yana ganin su minal amma banda Rahama yasa ya tambaye su.

Nan sukace"bata da lafiya sati d'aya kenan.

Har kofar gidan yaje yasa aka kirata,da kyar tafito suka gaisa.

Yace"tazo ya kaita asibiti da kyar ta ta yadda.akayi test result ya nuna tana da ciki wata4.

Hankalinshi ya tashi,Rahama taita kukan sai an zidda,yace" baza'a zidda ba.

Ta haihu shi zai aureta ya kuma ya rike abinda ta haifa.

Rahama tashiga tashin hankali yanda zata fuskanci gidansu.

M Auwal yace karta 'boyema danginta,tafad'i.

Takira honorable ta sanar dashi amma yace"karta sake kiranshi.

Amma ina Rahama ta 'boye har taje hutu ta dawo babu wanda ya sani.

Wannan da wowar ne ta haihu,amma ta bar babyn a hospital.

******************
Rahama ta dawo daga tunanin da tatafi,cikin ranta tace ko wane hali yarinyata take ciki.

Hannu ta d'aga tace"ya allah kabata masu kula da ita fiye dani,allah kuma ya yafe min laifina.

*AFTER FIVE YEARS*
Da gudu tashigo falo tana fad'in Mamah Mamah Mamah,bayan mai aikinsu tashige tare da cewa murja ki 'boyeni yah faisal zai kamani.

Murja tace" *Zarah* bakijin mgn ko kad'an wlh,me kuma kika mashi kinsan bayaso kina masa 'barna.

Tace"murja wai dan na keta mashi book d'inshi fa,murja tace"ai nasan dama bakida gsky toh maza ruga d'akin mamah.

Da gudu tatafi,faisal yazo inda murja take yace"murja kinga *zarah* tace"A'a lfy?"

Yace"book d'ina ta keta.

Murja tace"kai faisal kaifa babbane kaida kake ban kwana zatafi mkrnt.

Yace"wlh bata jin mgn amma allah ta kara saina bugete,dan taga mamah na hanani bugunta.

Da daddare suna falo suna kallo, *zarah*kuma tana bisa cinyar mamah tana shan tea.

Faisal yace"mamah wai meyasa aka shagwa'bar da yarinyar nan?"

Mamah tace"nida d'iyata ina ruwanka,ita fa kad'ai gareni mace.

Yace uhmm ai wlh yarinyar nan da gida nan zan zauna saina gyera mata zama.

Mamah tace"wai kai meyasa ka takura mata,kaida kanwarka baku zama wuri guda sai fad'a.

Kafa gama Primary gashi yanzu har zaka tafi secondry,amma ace bakayi hankali ba.

Mikewa yayi ya fita yana turo baki.

Washe gari aka kai faisal airport zai tafi karatu America acan yayi secondry da universty ya krnt engneering.

*After 12 years*
Yarinya ce doguwa fara tas tsaye gaban madubi tana makeup batafi 17 years ba,tagama shirinta tas tafito falo,sanye take da doguwar riga ta atamfa,tasa hijab har kasa.

Tayi wani irin kyau,rike take da gandbag,mamah na zaune falo, zarah tace mamah zantafi shcool.

Mamah ta kalleta tace"kai zarah abaya kikasa amma bakiga kyan da kikayi ba,zarah tayi murmushi tace"mamah kinaso kisani in makara koh.

Mamah tace"toh sai kin dawo driver na waje yana jiranki.


harta juya zata tafi,mamah tace yawwa zarah gobe fa faisal zai dawo.

Zarah tace"mamah kinsan bafa shiri muke dashi ba,ni wlh mamah bana ma murna da zuwanshi.

Mamah tace"zarah miye haka,yayanki ne fa,ace shekara 12 amma kice min bakiso ya dawo,zarah tace"ya hakuri mamah nidai natafi.


By;πŸ‘Œ
MARYERM MUKHTAR
[9/17, 5:23 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
(For loveβ™₯nd justiceπŸŽ“)
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain we touch the heart of readers_*

P.m.l

*DEDICATION TO MARYEEM MUKHTAR FANS GROUP*β™₯

Chapter 16\20


Bayan sun gama exam akayi hutu,rahama takoma gida kd.

*Unguwar governor road kaduna*
Da gudu Rahama tashigo gidan tana fad'in mom mom,sama tahau tashiga d'akin momyn na waya ganin Rahama yasa ta katse wayar,rungume juna sukayi.

Rahama tace"i really miss u mom,mom tace i miss u too my daughter.

Rahama tayi murmushi tace"mom ina dady"?tace" ai babanki baya k'asar bakuyi waya dashi bane?"


Rahama tace"kai mom shine dady ya tafi bai kirani ba,mom tace"kwantar da hankalinki next week zai dawo,Rahama tayi murmushi tace"toh shikenan mom bari naje nayi wanka nagaji sosai.

Rahama ta tafi d'aki tayi wanka tasa kaya marasa nauyi ta kwanta, bata tashi ba sai 4:00 ko sallah batayi tayi wanka tasa riga t-shirt da d'an k'aramin skirt.

Tafito falo ta kunna tv, fitowar mom yasa ta juyo tare da cewa"mom kinfito.

Mom ta kalli Rahama tace"Rahama ina fata kina kula da mutuncin kanki dai,ta d'an sha jinin jikinta sannan tace"eh mom ina kama mutunci kaina sosai.

phone d'inta tayi ringing tana dubawa taga new number ajiki,ta d'auka tare da cewa hello.

jitayi ance pls ina mgn da Rahama ne?" tace"eh.

Yace"toh idan bazaki damu ba nasan kinzo garin kd,ina san ganinki ne.

Ta bud'e baki zatayi mgn ta juya taga mom ita take kallo,tamike ta shige d'aki,tace" a ina kasami number ta?"

Yace"alhaji lawal ne d'an majalisa ne ni,ke kika bani number ki a facebook.

Tayi murmushi tace"owk nagane,yace"toh ina so muhad'u ne.


Rahama tace"ta kaga yanzu na dawo gida ne,ba za'abarni inta yawo cikin gari ba,amma zan baka address d'ina sai kazo.

Yace"toh kimin text d'in address d'in anjima zanzo,tace"owk sai ka jini.

Tayi mashi text d'in.

Bayan isha'i yazo ya kirata yace" gashi yazo,tace ya jira tana zuwa.

Ganin yadda take kuma tasan mom bazata bari tafita haka wurin wani namiji ba.

Ta kofar baya tafita taje.

Yana zaune cikin mota,bud'ewa tayi tashiga,ya kalleta yace wow wato ganinki yafi jin muryarki dad'i.

Tayi murmushi tace"koh

Sun dad'e suna fira,nan ne yake sanar da ita yana so su ringa had'uwa koda ta koma shcool.

Tace"sai dai ya bita kt dan idan tatafi sai anyi hutu take dawowa.

Yace"bata da matsala duk duniyar da taje zai bita.

Bud'e mota tayi zata tafi,ya ciro bandir d'in 500 ya bata,ta amsa tare da yin godiya.

Tunda Rahama tazo kd bataje ko ina ba, mom bata barinta fita,koda alhaji lawal ne yaxo sai dai tafita ba'asani ba.

Ana saura 1week takoma,tana d'aki gaban mirror tana makeup,mom tashigo ta kalli Rahama tare da cewa"yau fa dadynki zai dawo.

Rahama ta buga tsalle tare da cewa wow mom,yau mom akwai fira tsakanina da dady.

Babanta ya dawo tayi murna da ganinshi sosai, yana bala'in san Rahama,duk abinda takeso shi yake

Please Login or Register in order to submit comment