Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kofar gidan Mal Fatihu. Samari da sanduna da gorori suna ta hargowa su dai kawai su bar garin. Kauyukan makota kowa zancen Mawadda akeyi ana bata mata suna. Su kuma sun gaji da zama dasu. Su kansu iyalin gidan abubuwa da dama idan suka je siya a yan kantunan dake kauyen sai a hanasu. Rayuwa tayi kunci garesu komai yayi tsanani.

Ana wannan rigimar Mal Isiyaku mahaifin Dahiru ya gansu. Kememe dama sun shatawa Dahiru layi akan zuwa gidan amma yadda yaga samari da yara suna wake wake ana jefa duwatsu a gidan ya tayar masa da hankali. Gidan maigari ya nufa kai tsaye ya sanar dashi. Ranar fadar maigarin hirar da aka dasa kenan.

Washegari Maigari da kansa yaje gidan Mal Fatihu saboda yasan bashi da lafiya. Shimfida akayi masa a karkashin bishiya matasa sukayi dafifi a wurin.

Kaninsa ne ya riko shi ya fito aka zaunar dashi akan tabarmar ya kwashi gaisuwa. Maigarin yasa aka kori matasan sannan ya soma magana.

"Mal Fatihu ina sake jajanta maka wannan hali da kuka sami kanku a ciki Allah Ya kiyaye gaba. Yaran garin nan sun bullo da sabuwar fitina wadda idan ban kawar da ita ba suna iya yin abinda bazai mana dadi ba. Sabili da haka ga mutane a wurin nan suna shaida nasan baka da wurin zuwa idan ka bar Tariwa. A cikin Kano unguwar Tunga ina da gida dan karami ne daki uku da bayangida. Wata shidan farko na amince ka zauna kyauta daga nan idan na shigo garin sai muyi maganar kudin haya. Ka amince?"

Kuka Mal Fatihu yake kamar yaro. Wannan wace irin masifa suka shiga. Ya koma Kano yayi me? A kauyen ma shi talaka ne sosai ina ga ya koma birni. Yanzu saboda kaddara ta fadawa yarsa shikenan sai a taru a koreshi daga mahaifarsa?

Maigari ga katse masa tunani "nasan kana cikin tashin hankali da damuwa amma ina tsoron abinda zaije ya dawo. Ka tafi da iyalinka idan kura ta lafa sai ku dawo. Zan gargadi yaran da iyayensu na baka sati guda"

Har Maigari ya tafi Mal Fatihu yana kuka ya ma kasa godiyar gida da aka bashi. Da taimakon kaninsa ya koma ciki ya sanar da iyalinsa. Ranar Malam babansa yazo gidan da kansa yace gara ma su tafin saboda yanzu ma meye marabarsu da basa nan kowa ya fita harkarsu.

Kuka dai baya karewa iyalin gidan. Haka suka hada kaya Mawadda tana jin kamar ta wayi gari taga komai mafarki ne ko kuma ta mutu ta huta.

*Sabon Shafi*
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰9

*Batul Mamman*💖



Kafin ya karasa ciki yayi kokarin saisaita kansa a soro sai dai kallo daya zaka yi masa kasan akwai abinda yake damunsa.

Innarsa ce ta fara tambayarsa ko Dahirun ya fada masa magana wadda batayi masa dadi bane. Murmushin dole ya kirkiro sannan yace

"haba Inna kema kinsan yaron ba dai dattako ba kamar wanda ya tashi cikin tsofaffi irinku"

Jin har lokacin kirjin nasa ba dadi ya zauna sannan ya cigaba da cewa "yaso kwarai ya ga Mawadda nace ya dai yi hakuri ya nemi wata ita ma zamu yi ta bata baki ta karbi kaddararta"

"Hakane, amma gaskiya ban taba tsammanin haka daga gidan Mal Isiyaku ba" cewar Iya.

"Wani masoyin sai kana cikin yanayi kaka-ni-kayi dama kake sanin ainihin me ya aje a zuciyarsa game da kai. Allah Yasa hakan ne mafi alkhairi. Yaya Fatihu sai ka fadawa Yaya a tattaro komatsansu a mayar musu ko"
Ade ta fada kana ji kasan ranta a bace yake.

Shi dai Baba shiru yayi sai can ya tashi ya shige rumfar mahaifinsa ya nemi wuri zai kwanta.

Mawadda na zaune kamar an kafeta sai da ya tashi kuka ya taho mata ta mike tayi dakin Iya cikin sauri. Inda ta tashi Iyan ta kalla sai ga alamu na jini a jikin tabarmar.

Wata guda Iya tayi kai kace haihuwa ko amarya akayi a gidan. Innar Fatihu da Ade suka zabura suna kallonta ta murmusa sannan ta nuna musu wurin da Mawadda ta tashi.
"Allah Maji rokon bawanSa Yaga zuciyata da irin du'a'in da nake yi kada Ya jarabcemu da goya dan gaba da Fatiha. Ga shaida idona ya gani iftila'in Mawadda bai hada da ciki a dalilin fyaden nan ba"

Ade ta ma manta da abu makamancin wannan bata taba tunani ba akan zai iya yiwuwa fa ciki ya shiga. Wani sanyi itama taji ya ratsa zuciyarta tayi hamdala sannan ta bi bayan Mawadda tace mata ta gyara jikinta don ta lura tunani yayi mata yawa bata san dashi ba.

Innar Fatihu ta tashi ta shiga rumfar maigidanta wurinsa. Yana jingine da bango ya dafe kai yana aikin tunani.

"Fatihu fada min gaskiya ya kuka yi da yaron nan."

Jiki a sanyaye ya fada mata ta shiga tafa hannuwa.
"Amma sun bani mamaki sosai. Nasan ko nice da wuya na amince amma irin haka da sosa rai. Nagode Allah yarinyar nan ba da amincewar ta akayi ba da bansan yadda zamuyi da ranmu a garin nan ba"
******

A fusace Baffa yake ta doka sallama Inna ta saki rariyar da take tankade da sauri saboda tsoro.

"Menene?" ta fada tana mikewa sai kuma ta kula da Dahiru tasa fuskar tayi kalar tausayi harda guntun hawaye a idonsa.

"Kai kuma daga ina?"

"Ki jawa yaron nan kunne ina daf da nuna masa bacin rai mai tsanani. Ta yaya za'ayi naje nayiwa Mal Fatihu magana akan yarinyarsa mun gama yankewa a bar zancen aure danki ya rinka zagayawa ta baya. Wato ace gani mugun uba dana ya fini tausayi ko. To baka isa ba, in ba aure kake so nayi maka gobe goben nan ba kuma na soke karatu a Kanon ka shiga taitayinka"

Inna ta harari Dahiru sannan tace "kayi hakuri Baffa. Yanzu dai fada min me ya yi"

Cikin daga murya ya bata labari don ransa a bace yake. Inna kuwa hannu tasa ta tsinke Dahiru da mari. Tsabar mamaki ya hana shi kuka sai kallon iyayensa da yake yi wani iri. Ya kasa gano meye laifinsa don yace bazai guji masoyiyarsa a wannan lokacin da take bukatar karuwar masoya da masu nuna mata kulawa ba.

Muryar Inna ce ta dawo dashi daga tunaninsa "Dahiru kada kayi abinda zamuyi fushi da kai kana jina ko. An fada maka da ka muka yanke shawarar fasa auren naku? Wannan zamani na cututtuka idan ta shafa maka kanjamau waye da asara? Kuma muna nan galau bamu sani ba kila da ciki a jikinta a ganganda ayi aure a yaba maka dan jaraba"

Kwalla yaji ta taru a idonsa har yana zafi kamar yadda ransa ke yake yi. Ji yake kamar yasa ihu yayi musu bayanin da zasu gamsu. To amma iyaye da girmansu da darajar da Allah Ya basu bazai iya ba.

"Inna, Baffa kuyi hakuri don Allah. Auren nan idan anyi dama ina da niyar kaita ayi mata gwaje-gwaje sannan in taimaka mata yadda zata ji saukin bakincikin da yake ranta ne"

Baffa ya mike kamar ya rufe shi da duka "dan zaman naka a Kano ne yasa kake tunanin ka fimu wayo da sanin ya kamata? Idan baka yi hankali ba na fada maka karatun ma sai a hakura ka dawo gabanmu ka zauna...shashashan yaro ana ga yaki kana ga kura"

Inna tabe baki tayi "duk abin nan kila ma shiryowa tayi tazo ta fada kai kuma ka hau ka zauna. Idan karya take yi fa bariki ce ta kare mata shine ta dawo ayi auren ka rufa mata asiri fa"

Hawayensa ne ya sakko ya kalleta a sanyaye yace "Innaaaa!"

Jikinta ne yayi sanyi yayin da Baffa ya dauki bota ya shige bayan gida.

Abinci tayi masa tayi yace ya koshi kawai ya mike
"zan koma a satin nan zamu fara shiga aji"

"Allah Ya bada sa'a Ya shi albarka. Ungo maza ka tashi ka tafi zan taushi mahaifinka kafin ka sake dawowa"

Zaninta ta dan kwance daga gefe ta hado masa dubu biyu da dari bakwai ta bashi. Karba yayi yasa a aljihu tare da godiya duk da fuskarsa babu annuri ko kadan.

Haka ya juya ko ruwa bai sha ba Inna tana ta masa addua har kofar gida. Yana jin ta koma ya dawo soronsu ya tsaya yaci kukansa sannan ya share ido. Yana son iyayensa amma baiji dadin matakin nan da suka dauka ba sai dai zaiyi hakuri ya barwa Allah ikonSa.

*****

Haj Mara yau tayi bacci harda minshari tamkar an gama shari'ar an basu gaskiya. Juyi tayi akan makeken gadonta don jiya daga kotu gida suka wuto abinsu.

Wayarta ta janyo ta kira Alh Sule cikin isa da kasaita tace "da baka sa hannu ka nuna damuwarka akan danka ba me ya ci mu Alhaji? Na kira ne kawai nayi maka albishir da cewa kiris ya rage mu sami nasara mu baiwa marada kunya"

"Ni kike fadawa haka Marakisiyya?"

"Da 'yan hamayya nake wadanda basu damu da halin da 'ya'yansu suke ciki ba. Ko kana cikinsu ne?" Tayi masa tambayar rainin hankali tana 'yar dariya.

Murmushin takaici yayi "bana cikinsu gaskiya domin ni ina nan ina addu'a akan Allah Ya fitar min da dana idan yana da gaskiya idan kuma shi mai laifi ne Ya fitarwa wadanda aka zalunta hakkinsu"

Kafin ta ankare ta bashi amsa ya kashe wayar. Kallonta ta rinka yi rai na kuna tana ayyana yadda zata rama idan ya dawo.

Shima a nasa bangaren yana bakincikin yadda neman kudi yasa shi sakar mata ragamar gidan. Yayi babbar sa'a sauran yaransu mata babu wata mai mugun hali ko ace miji ya kawo kararta. Ita Haj Mara din ma arzikinsa da ta ga yana ta habbaka ne yasa ta kara kwallafa rai akan tilon namijin nasu ta sangarta shi har ya kai matakin da tankwara shi zaiyi matukar wahala.

Mikewa tayi zata shiga wanka BB ya shigo dakin nata ba ko sallama yana muzurai.

"Babawo lafiyarka kuwa?"

"Ras nake Hajjaju mutan Makka da Madina. Wai yane....?"

Kasa cewa komai ma tayi jin yadda yake mata magana. Gashi kamar yasha wani abu. Da kyar ta iya cewa
"Me kake nema ne?"

"Ke muka yi magana kika ce min idan na fadi abinda kika sani yarinyar nan Mawadda kamar kin aura min ita kin gama ne kuma gashi har mun taho ko iyayenta baki nema ba"

"Bansan rashin hankalin naka ya kai nan ba. Ta yaya za'ayi nayi musu magana ba'a gama shari'a ba? Ka bari a kare komai mana ka ga iya gudun ruwana"

Hade rai yayi yana kunkuni "to ni dai kada ayi min solo don ba yarda zanyi ba na fada miki tun wuri."

Daga haka ya fita tayi saurin sakawa kofarta mukulli don tsoro ma ya bata.

*****

Dr Tani ta wuni a asibiti tana gyara duk wani report na Mawadda. Wadancan na gaskiyar ta sa wani masinja ya dauko mata ainihin file din ta bashi kudi sannan ta tura a jakarta. Nan ta zauna ta sake komai da taimakon masinjan ta buga sababbin takardu da suka dace da kwanan watan wadancan. Tana aikin tana tausayawa BB domin ba karamin abu bane ace anyiwa mutum sharrin fyade.

Wayarsu ta dazu da Haj Mara ta dada tayar mata da hankali inda tace mata ko ruwa baya iya sha zabgegen namiji kamarsa wai jiya har kuka yayi mata da suka dawo yana cewa rayuwarsa tazo karshe wace mace ce zata taba aurensa. Cikin lallashi Dr Tani tace ta bashi hakuri ta san duk wannan tashin hankalin nasa akan Qareeba ne kuma alkawari ne tayi masa kamar anyi aure an gama tsakaninsu.

Kwafa tayi a hankali tana jin tsanar su Mawadda. Tunda take ita dai tasan 'yarta ba mummuna bace gata fara amma samari basa wuce zuwa uku idan sun kai zuciya nesa suke zukewa a nemesu a rasa. 'Ya'yan nata duka sunki aurowa saboda yanayinsu. Ita kuma hakan bai taba damunta ba balle ta gane sokoncinsu yake hanasu aure. Murnar samun BB a matsayin suruki yasa komai aka fada mata take hawa ta zauna daram.

Sai da ta gama gyara komai ta tafi gida gabanin magariba.

Dahiru yana zaune a kan benci a kofar gidan ya nisa cikin tunani wani yaro da baifi shekara hudu ba ya taho kan titin gidajen wurin yana buga ball. Dr Tani ta taho ga duhu ya kawo kai saura kadan ta buge shi Dahiru ya tashi a guje ya dauke yaron har yana faduwa.

Kanta ta zuro ta taga tace masa "don tsabar wulakanci me ya hanaka dauke yaron tun da na karyo kwana?"

Batare da ya saki yaron ba yace "Hajiya kiyi hakuri"

Tsaki ta doka ta shige bayan maigadi ya bude mata gate.

Shi kuma Dahiru ya fuskanci yaron.
"Assha ba dai kaji ciwo ba ko, daga ina kake?"

"Nan gidan" ya nuna wani gida da tun zuwansa ya kula aikin gininsa ake yi.

"Shine zaka fito kai kadai kana buga kwallo akan titi. To wuce muje ka shiga ciki kuma idan na sake ganin kafarka a wajen nan sai na yanketa."

Yaro yayi kwalkwal da idanu "da wuka ko reza?"

Dahiru ya dan murmusa. Shi tsorata yaron yayi niyar yi saboda ba karamin ganganci bane fitowar tasa "da almakashi zan yanke nasan yafi zafi. Idan zaka yi wasanka kayi a cikin gida banda titi kaji ko"

"Naji sakeni na tafi to.." yaro ya fada duk ya tsure.

"A'a sai na kaika har ciki nace a zaneka kana fita titi"

Wani mutum da yake jinsu daga gefen gate din gidan da ake aikin sanye da 'yar shara ne ya fito yadda zasu ganshi sosai. Yaron ya ruga wurinsa shi kuma Dahiru yana ganin haka yayi zaton ko maigadin gidan ne.

"Baba don Allah a rinka kulawa da amana. Kaga da bana kusa yau da karshen aikinka yazo idan da tsautsayi"

Mutumin ya gimtse dariyarsa yace "Allah dannan me ya faru?"

Dahiru ya sanar dashi duk da cewa akan idonsa akayi komai. Shima da sauri ya biyo bayan jikan nasa sai dai kafin ya iso ya tsallaka titin.

"Zan kiyaye in sha Allahu. A nan kake ne?"

"Eh ina aiki a gidan can ne."

"Mu kuma aikin gini mukeyi a nan an kusa gamawa"

Addu'ar gamawa lafiya Dahiru yayi har ya juya zai tafi mutumin ya dakatar dashi suka je masallaci tare. Bayan sunyi sallah Dahiru yace zai shiga ya karbi abincinsa ya wuce gida. Mutumin yace to yana jiransa.

Ko da ya fito baiga yaron ba sai yayi zaton ko yana wurin ainihin masu gidan tunda ga dankareriyar mota an paka ta a wajen gate din. Da ya ga mutumin bai tafi ba sai yayi masa tayi abinci shi kuma yace ya koshi.

'Yar hira suka taba anan Dahiru yake ce masa gobe zai fara shiga aji daukar darasi
"Mu mun saba karatunmu a kauye nan sai fargabar gobe nake yi zan hadu da 'yan gayun birni"

Mutumin nan yayi ta dariya. Dahiru kansa mamakin yadda ya sake dashi yake yi da yaga Isha na neman yi yace masa zai wuce gida ya sake goge rigarsa don kada 'yan birni su raina shi.

"Dannan kace 'yan mata zaka nema ba karatu ba"

Shiru Dahiru yayi yana tunanin Mawadda "ina da matar da zan aura a kauyenmu, karatu kawai zanyi na koma wurinta"

Yanayin maganarsa kadai ya nuna akwai babbar damuwa a tattare da shi. Mutumin ya sami kansa da tausayin Dahiru sosai. Gashi matashi don yace masa shekarunsa ashirin da biyar amma ba girman kai ga son cigaba yazo yana aiki domin yayi karatu. Kati ya ciro a aljihunsa ya mikawa Dahiru.

"Ga wannan inji Kakan Khalil yaron da ka taimakawa yace na baka ka neme shi"

"Kakansa ne mai gidan nan kenan"

"Eh"

Godiya yayi masa sosai da korafin baici abincinsa ba sannan ya tashi yayi gaba. Mutum ya bishi da kallo, da farko kudi yayi niyar bashi amma 'yar hirarsu tasa ya shiga ransa.

*****

A daddafe iyalin Mal Fatihu suka karasa kwanakin da kotu ta diba kafin a cigaba da zama. Tsagwama da bakaken maganganu kullum yi ake. Hatta 'ya'yansa masu aure su Bilki basu tsira ba. Makota suyi musu dangin mazajensu suyi. Abu ya taru ya cakude musu.

A wannan lokacin Mawadda ji tayi inama bata taba rayuwar duniya ba. Ko kuma da BB ya keta mata haddi dama harda ranta ya hada. Bakar rana guda daya ta zame musu bala'i ita da duk wani makusanci nata. Hatta Dahiru wasu sun fara yawo da zancen kila shine yake nemanta suke neman dorawa dan iyayen gidanta.

Abubuwa sai gasu nan babu dadi ko kadan. Kannenta ma yanzu ko kofar gida basa so a aikesu.

Da sassafe suka shirya suka tafi Kano saboda Baba yace baya jindadin yadda yake rara gefe yana takurawa mutane akan wurin kwana.

Shabiyu za'a fara sauraren tasu karar amma ko da suka isa wurin goma da rabi kotu ta cika da 'yan kallo da 'yan jarida.

Haj Mara a gidan aminyarta ta kwana shi Dr Auwal maigidan bai san wainar da ake tonawa ba. Matarsa dai ta fada masa zata je kotu shaida akan wata yarinya yace sai ta dawo.

Da hillata Haj Mara tasa BB ya amince yazo gidan. Qareeba duniya kamar an bata sweet-kamfo jinta take tafi kowa sai wani yauki akeyi.

Shi kuma BB komai yana yi ne kawai saboda biyan bukatarsa na samun Mawadda. Sun gama shiri zasu tafi kotu yana jingine da mota Qareeba tana tsaye a gefensa suna jiran fitowar iyayensu sai ga Dahiru zai wuce.

Sauri yake yi ya gama aikinsa Danlami ya tsegumta masa yau za'a sake zaman shari'ar su Mawadda da karfe shabiyu. Da yake mutum ne mai shige-shige kuma yana yawan zuwa Kano yawo yasan court road din ya kwatanta masa. A ka'idar karatunsa ma yana da aji yau hudu zuwa shida amma bai damu ba ko zai rasa indai zai ganta.

Qareeba ta kalle shi ya kwaso shara zai wuce tace "kai Ahirin meye haka baka ganin Man dina bazaka gaishe shi ba"

Dahiru yayi banza kamar baiji ba ta kuwa daga murya "Dashiru mai ahirin baka ji na ne? Tsaya nan dalla can ko na fadawa Mummyna"

BB ya dan daga ido ya kalleta sai yake baki take da suka hada ido "Man kaga wannan shine Dashiru din da nake fada maka yace ahirin....hehehe..." tayi dariya ita a dole 'yan mata zata burge masoyi.

Dahiru ganin zasu bata masa lokaci yace "barka dai Man"

Qareeba ta cika da haushi "me yasa kake min haka ne, ni kadai nake kiransa Man meye naka na fada. Kada kace min a kauyancinka baka san akwai sunaye da ake warewa na kiran wanda ake so ba"

BB duk ta ishe shi da hayaniya ya rasa me ya zaunar dasu Hajiyarsa a ciki. Ji yayi ta sake cewa

"Man kasan 'irinsu Ahirin basu san komai na love ba har tausayi suke bani ga auren wuri. Kai Dashiru me kake kiran budurwarka ta kauye"

Har ransa tausayi ma take bashi saboda yana ganim yadda saurayin nata yake ta wani yatsina shi a dole ya hadu. Yasan idan baiyi yadda take so ba karshenta Mummynta ta hana shi fita idan ya nemi uzuri kafin lokacin laccarsa don har timetable dinsa tasa ya kawo mata.

Dan buga kafa ta soma na shagwaba tana kyabe baki "Man please mana kace ya fada maka muji muyi dariya"

BB ya tsani wannan suna na Man kamar ya bugeta ya dai maida hankalinsa ga Dahiru.

Shi kuma ganin haka yace "Qulqulatul qurabati nake kiranta. Zan iya tafiya ko"

Haba Qareeba dariya har da kaiwa kasa. Muryarta kuwa har bakin gate maigadi sai da ya jiyota. Dr. Tani suna doso wurin taji takaici ya rufeta har da kunyar idon Haj Mara. Ita kuwa nunawa tayi ba komai tunda bukatarta zata biya a kashe case ta tura danta wata kasar ta yakice Dr. Tani. Dan zamanta a gidan duk sun gundureta ita da 'ya'yan. Wai jiya gotai gotai dasu suka rinka fada lomar wa tafi girma ana cin abinci.

Dr Tani ta jefi Dahiru da kallon banza don tasan shi kadai ke kara kunna Qareeba tayi ta rashin hankali.

"Kai me kake a nan kamar mara aikin yi? Ka wuce yau nasan sai la'asar zaka shiga aji ga wanki can mun hada ka wankesu tas a goge zan bar sallahu a tada inji. Asabar ba sai kazo ba"

Uzurinsa ya gabatar mata yana da wurin zuwa ta haushi da fada harda cewa idan ba so yake ya bar aikin ba ya rufe mata baki. Duk bakincikinta dariyar da yasa Qareeba a gaban BB da babarsa.

Ba don yaso ba haka ya tafi yana jira su fita shima ya saci jiki ya fice.
*****

Lauyoyi sun gabatar da kawunansu sannan Alkali ya bukaci a cigaba. Wani matashi aka gabatar wanda yace shi abokin Na'ibi mai kiyos ne kuma shine ya ga Mawadda a dakinsa har ya sanar da Haj Mara.

Barista Shafa'atu tayi dariya "kuma kana ganinsu baka yi tunanin yin yekuwa jama'a suzo ka sami shaida ba ko ka kira wani da yasan Na'ibin sai uwardakin Mawadda ce kawai ta fado maka a rai?"

In-ina ya dan soma "saboda nasan zata dauki mataki ta hana ne"

"Ashe akwai alaka tsakaninka da Haj Marakisiyya kenan"

"Eh to....a'a babu kawai dai nasan a gidan Mawadda take kuma zata bata min aboki tunda da ba halinsa bane"

"Da gaskiyarka kuma. To zamu so ka kwatanta mana hanyar da ake bi daga gidan Hajiya Marakisiyya zuwa dakin Na'ibi" tayi maganar tana kallon Haj Mara wadda taji cikinta ya kulle.

Saurayin ya soma raba ido domin shi gaskiya ko Na'ibin bai taba gani ba hasali ma ba dan unguwar bane.

"Ni bansan gidan Hajiyar ba amma nasan dakin nasa"

"Kace kuma kasanta har kasan zata dauki mataki idan ka sanar da ita halin da mai aikinta take ciki"

"Objection my lord" cewar Barista Dalhatu. "Barista tana neman juya zancen shaidarmu. Babban abin nema shine ya gansu kuma yaje ya sanar da uwardakinta"

Alkali ya karbi korafinsa yace ta kiyaye. Jin haka tace zata gabatar da shaidarta wato Dr Tani.

Wata yar musabaha Dr Tani da Haj Mara suka yi sannan ta tashi taje ta tsaya. Iyayen Mawadda dukkansu da Mawadda suka zuba mata idanu.

"Dr Tani ko zaki iya fada mana meye aikinki da shekarunki a wannan sana'a"

Sunanta ta sake nanata musu da bayanin kanta a matsayin likita da ta kwashi shekaru ashirin da uku tana aiki. Gashi har asibiti gareta wanda gwamnati ta bawa lasisin aiki.

Barista Shafa'atu tace "My lord munji wace ce Dr Tani saboda ina so kotu tayi duba da nazari mai kyau game da shaidun da zata kawo"

Alkali Dawud ya gyada kai ita kuma taci gaba.

"Doctor muna bukatar kiyi mana bayani game da halin da kika sami Mawadda ranar da tazo asibitinku"

"Tazo asibitin ne da lalura ta rashin iya rike fitsari sosai sannan tace anyi mata fyade ne shine dalilin wannan lalura"

Magana take babu wani alamu na damuwa kai tsaye kamar wadda tazo wurin a bisa tilastawa. Yanayinta kadai ya dagawa Barista Shafa'atu hankali sai dai ta cigaba da tambayarta.

"Idan na fahimceki kenan kina nufin fyade yakan iya janyo sakin jijiyoyin jikin mace har ta kasa rike fitsari hakane?"

"Gaskiya kamar yadda kowa ya sani yoyon fitsari ana samunsa ne ta dalilin haihuwa, tsufa ko infection wato idan kwayoyin cuta suka shiga mafitsara. Ni a tsahon lokacin da na dauka ina aiki ban taba jin ance fyade ya zama sanadin yoyon fitsari ba"

Barista Shafa'atu tun a lokacin ta gane inda Dr Tani ta dosa jikinta yayi matukar yin sanyi. Ta daure tace "amma ba yoyo take yi sosai ba tunda kadan kadan yake fita wannan ba alama bace dake nuni da cewa abinda ya janyo shi bai kai haihuwa ba?"

"Ga takardu na gwajin da muka yi mata mun tabbatar ba infection bane yake damunta. Sauran bayani kuma mun dogara ne da abinda ta fada da bakinta. Shawarata a nan shine idan da hali a sake bincikenta ko ta taba haihuwa ko yunkurin zubar da cikin da yayi kwari..."

Wani kukan kura Ade tayi ta taso daga inda take ta nufi Dr Tani take tsaye tana kuka sosai "Dafta amanarmu zaki ci? Nawa suka biyaki zaki yiwa 'yata kazafi irin wannan"

Durkushewa tayi a wurin tana kuka Alkali yace 'yan sanda suyi waje da ita ko ya hukunta ta saboda dakatar da shari'a batare da izini ba. Suna kokarin kamata Iya da Innar Fatihu suka taso suma suka rikota kowa cikinsu na kuka suka fitar da ita waje. Mawadda kamar ta hadiye zuciya ba kuka sai ajiyar zuciya.

Barista Shafa'atu tace ta gama tambayoyinta domin tun da fari yarda da itan yasa ta dada nanatawa kotu cewa likita ce da ya kamata a kama maganarta saboda dadewarta a aiki da kwazo.

Barista Dalhatu ya taso yazo gabanta kana ganinsa yana cike da nishadi.
"Dr Tani da kika duba Mawadda baki ga wata alama ba kenan dake nuni da cewa anyi

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

10 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment