Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata fyade?"

Tunawa tayi da raunukan jikin Mawadda ta dan runtse ido. Ta tabbatar Haj Mara bazata yi mata karya ba amintarsu tun kuruciya. Idan an gama case din ya kamata iyayen Mawadda su tsareta ta fadi gaskiya waye yayi mata fyade.

"Abu daya na gani shine yarinyar ba budurwa bace"

Yaya sai kuka ta rike hannun Mawadda tana matsawa.

"My lord ina fata kotu taji bayani mai gamsarwa daga bakin shaidar da masu kawo kara suka kawo. Ta yiwu da gaske fyade aka yiwa Mawadda amma ba BB bane saboda bayanin da suka yi shi da mahaifiyarsa da rashin wata shaida da zata karyata hakan. Haka zalika duk inda ake tunanin samun Na'ibi mai kiyos abu ya gagara mutane da dama sunce ko garinsu ba'a sani ba. Da wannan nake rokon kotu da ta taimaka ta yiwa Babawo Sule adalci" dan dukar da kai yayi ya koma ya zauna.

Alkali yace ko Barista Shafa'atu tana da karin bayani ta kalli Mawadda ta girgiza kai.

Ya duka yana kallon takardunsa yace ga hukuncin da kotu ta yanke bayan dan jawabi

"Duba da rashin kwararan shaidu daga bangaren masu korafi da kuma bayanan likita wannan kotu mai alfarma ta kori wannan kara, ta wanke Babawo Sule daga zargin da ake yi masa sannan ta ci Mawadda tarar naira dubu ashirin da biyar bisa dalilin bata masa suna. Wanda bai gamsu da wannan hukunci ba yana da damar daukaka kara."

Yana gamawa ya buga gudumarsa ya mike sannan kowa ya tashi ya fita ta baya.

Yaya tayi tayi ta daga Mawadda daga wurin da take zaune ta kasa saboda mutuwar zaune da tayi. Barista ta matso kusa dasu

"Kuyi hakuri zamu iya daukaka kara sai mu karo shaidu. Kunga tun da farko bakuyi min bayanin asibitin Bebeji da ta fara kwanciya ba da tuni munje har can saboda karin shaida "

Mal Fatihu ya tashi yana murmushin da yafi kuka ciwo yace "Barista mungode a haka ma."

Zata sake magana ya je gaban Mawadda ya tayar da ita har lokacin murmushi yake yi mata "Ni nasan wa na haifa kinji ko, idan duniya zata taru ta nuna miki yatsa maganarki kadai zan dauka. Shari'a kuma mu barta haka zuwa lokacin da zamu taru a gaban Sarkin da Ya halicci kowa da komai"

Da haka ya samu ta tashi zuciyarta tana wani irin bugu da sauri da sauri. Suna fitowa waje aka yanyamesu da tambayoyi ga mutane kowa na fadin abinda yazo bakinsa.

Su Iya sun taso da sauri su tarar dasu Baba yana kare Mawadda daga 'yan jarida. Yaja hannunta suyi gaba kawai ya yanke jiki ya fadi ita kuma tayi kansa saboda rashin kwarin jikinta a wannan lokacin da kuma rikon da yayi mata ta kwala ihu "BABA....!!!!"
[08/01 8:32 pm] : *GUMIN HALAK...*💰11

*Batul Mamman*💖



Yau su Mal.Fatihu zasu bar kauyensu, mahaifarsu kuma tushensu. Tuni sun gama hada kayansu da ba wani yawa garesu. Da wuri Yaya ta fita ta tafi sallama da 'yan uwanta wanda a gidanta suka yini a jiya.

Ade dasu Iya suka zo gidan domin tare zasu tafi har Innar Fatihu. Idan sun taimaka musu sun nutsu a gidan su dawo duk da Ade ma tasan zaman kauyen yanzu yafi karfinta. Aiki zata bazama nema ko don samun lafiyar Mawadda dake fama da digar fitsari har yanzu.

Kowa na can ana tarkata kaya Ade na zaune kan kujerar girki Baba yana daga kan tabarma yace mata

"Sa'ade ina fata zaki yafe min tura Mawadda aiki da nayi har hakan ta faru"

"Haba Yaya me ya kawo wannan zancen kuma? Ka barmu muji da bakincikin mutan garin nan na yanzu"

Gyara zama yaso yi hularsa ta fado. Dora masa ita Ade tayi akan hannunsa mai lafiya ya danyi murmushi

"Kinga fa naso shiga layin zaurawanki ashe ba rabo na koma rabin mutum"

Mawadda na fitowa daga daki taji abinda ya fada kunya ta kamata ta koma da sauri. Ade kuwa dariya tasa don ta kara kwantar masa da hankali tace "ko zaka fito ne?"

Shima yayi dariya "rufa min asiri kada Iya ta cinyeni danye."

Iya na jinsu ashe da ga dakin da Mawadda ta koma. Murmushi tayi sannan hawaye ya sauko mata duk kuwa da dakiya irin ta ta.

"Ehem, ehemmmm....gafarar ku dai masu yi da mutane da rana tsaka. Muna jinku daga ciki ana shuka a idon makwarwa"

Ade mikewa tayi da sauri ta bar wurin don kunya shi kuma Baba ya dauki hularsa ya rufe fuska. Iya tayi 'yar dariya ta wucesu.

Sai da suka yi sallar azahar aka fara batun nemo mota daga bakin titi. Nan fa sai koke-koke yawanci daga 'ya'yansu ne ma saboda Baba yace bai yarda su biyosu a yau ba. Baya so suyi abinda suma nasu auren zai gurgunce irin na Jamila. Sun hakura tare da alkawarin zuwa kafin suyi sati. A haka Malam kakansu yazo ya riskesu an soma fita da kaya waje. Baba na ganinsa yaji kwalla ta taho masa.

"Meye hakan Fatihu a gaban 'ya'ya da jikoki" cewar tsohon mai halin dattako cike da dauriya. Ba karamin tashin hankali ya shiga ba sakamakon abubuwan da ke faruwa da iyalin dan nasa amma ya yarda jarabawa ce mai wucewa.

"Malam ka yafe min duk wani abu da na taba yi maka da gangan ko bisa kuskure."

Malam ya dafa masa kafada "Allah Ya baka lafiya Fatihu Yasa wannan tafiya ta zama tamkar budewar wani *sabon shafi* na rayuwarku. Bansan lokacin da zamu sake haduwa ba ni ga tsufa ga lalurar kafa da ido. Kai kuma ga yadda Allah Yayi da kai sannan Maigari yace yafi son ka bawa garin nan iska har abin ya lafa"

Nasiha yayi ta musu akan rike mutumcinsu idan sunje birni kada son abin duniya ya rudesu.
*****

Danlami ya shigo gidansu da sauri ya tari Inna a kofar dakin Baffa yana faman haki.

"Inna tafiyar fa tazo har an samo a kori kura sun fara lodin kayansu"

Juyawa tayi ta sanar da Baffa sai ta ga har ya fito shima. Kwanansa uku yana son zuwa yiwa su Mal Fatihu sallama amma tsananin kunya ya hana. Inna ce tace ya kamata su ajiye komai suje kada ayi rabuwa ba ta arziki ba. Rashin yardarsu da auren yaran suna ganin ko wasu ne da wuya su amince.

Mayafi ta sako Baffa yasa hula suka je gidan. An fito da Baba kenan za'a saka shi a mota. Mukullin sabon gidan nasu Maigari ya bawa kanin Mal Fatihu dreba shine zaiyi musu jagora an nuna masa gidan.

Baffa yana jin nauyi haka ya matsa jikin motar suka gaisa da Baba. Inna ma haka yayi suka gaisa dasu Yaya kowa yana kokarin boye abinda ke ransa. Idan ka cire 'yan uwa na jini su Inna ne kadai suka zo yi musu sallama. Inna ta kawo wani madaidaicin buhu da Danlami ya biyota dashi tace gashi ba yawa. Ledoji uku ne a cikinsa daya shinkafa, daya wake dayan kuma waken soya. Sun rabu su Bilki suna ta kuka a gefe ma Inna sai da tayi nata na tausayin wannan iyali.
******

*KANO TA DABO TUMBIN GIWA*


Sati biyu kenan da dawowarsu Kano. Gidan ba laifi yana da fadi fiye da tsammaninsu. Kuma banda dakuna uku na ciki akwai wani a soro shi aka barwa Marwanu da Saifullahi 'ya'ya biyu maza da Mal Fatihu yake dasu 'yan kasa da shekara shabiyar. Jamila, Mawadda da kanwarsu mai binta Rafi'a an basu daki daya su ma. Dayan kuma na Baba ne yayin da Ade dasu Iya suke cikin na Yaya.

Iya da Inna kwanansu biyar suka koma sai dai Malam ya matsa Iya ta dawo saboda hankalinsa bai kwanta ba. Ga bakunta ga maigida a kwance suna bukatar sa ido na babba. To dayake abubuwa da dama sun faru ko kadan da ta dawo babu wannan rigimar ta matsawa Yaya. Ita kanta tasan Yaya mai kaunar jininta ce shiyasa yanzu take kokarin rike girmanta. Ade kuma ta sami aiki gidan wani tsohon minista a rijiyar zaki da gudu ta karba don tasan banda 'ya'yanta da take biyawa kudin makaranta dole ta nemi kudi saboda Mawadda.

Wata rana suna zaune ana cin dumame Mawadda tace "Yaya wai bazamu fara sana'a bane?"

"Nima tunanin da nake kwana dashi kenan amma na rasa me zamuyi"

Jamila da take gwanar kitso tace anjima idan sun shiga gaisawa da sauran makotan da basu sami damar shigarwa ba zasu sanar dasu ana kitso a gidan.

Da wannan shawarar suka fita. Gidaje uku suka shiga. Dayan da yake da 'yar tazara dasu harda gate mai kyau dashi. Sun shiga sun sami matar tana hada garwashi a bayan gidan da danta ya kaisu. Gefe ga mace ta lullube da bargo fuskarta tayi yelo. Tana aikin suna gaisawa tace suyi hakuri bata shigo ba aikin amaryar nan ne ya tsayar da ita. Hankalin Mawadda kacokan yana gareta tana kallo ta zuba wani turare a kasko wurin ya bade da kamshi ta daga bargon ta tura kaskon sannan ta sake lullube yarinyar.

Mawadda ta kasa hakuri ta tambayeta me take yi haka.

Murmushi tayi "gyaran jiki ne na amare da matan aure ko kina so?"

A kunyace Mawadda tace a'a sai dai fa da kyar ta tashi suka bar gidan. Komai ta ga matar tayi burgeta yake. A kwaba wannan a kwaba wancan ance duk amarya za'a shafawa jikinta yayi kyau. Matar kanta mai suna Zahra ta kula da yadda Mawadda ke kallonta ita kuwa ba gajiyawa kome tayi sai tayi mata bayani.

Suna komawa gida Mawadda ta hau hirar gyaran jiki tana bawa su Yaya labari abinda ba halinta ba. Kowa yana mata dariya ko a jikinta.

Bayan kwana biyu Iya tace waken soyan da Innar Dahiru ta basu suyi awara dashi mana suci. Ai kuwa anyi awara Mawadda da Rafi'a suka tsiri jajjagen attaruhu da albasa suka soya yana ta kamshi suka ci dashi. Abu yayi musu dadi suka fara tunanin ko zasu fara awarar siyarwa. Kamar da wasa suka yi ta mai kyau da dadi maimakon yaji sai wannan jajjagen na attaruhu da albasa. Makota suka shiga suna sanarwar sun fara awara amma har dare ko kaza bata shigo saya ba. Allah Yasa ba yawa suka yi suka cinye abinsu.

Bayan wasu kwanaki Marwanu da Saifullahi suka ce sun gano masu kayan sayarwa a gefen titi a sake suyar awara zasu kai can. Batare da gajiyawa ba sukayi ta rabin kwano kada ta sake kwantai.

'Yar roba suka samu Mawadda ta yanka kabeji, tattasai da albasa kananu tace idan sun zubawa mutum sai su dan diba a watsa a kai.

'Yan samarin ba girman kai suka tafi shiru babu wanda ya tsaya siyan tasu. Haka sukayi ta yi har sau hudu. A karo na biyar Saifullahi zaman ya ishe shi sai ya soma waka yana cewa

"tamu ba irin tasu bace...awarmu ba irin tasu bace" haka nan ya kirkiri kayarsa yana yi Marwana ya hau buga cokali akan kwanon da ake zuba mahadin awarar. Mutane suna ta kallonsu wani mutum yace bari dai a bashi yaji irin tasu.

Da rawar jiki Marwanu ya zuba masa Saifullahi yana cewa "kasan shi yaji iska na kadawa sai ido mutum yazo ya kasa gane hanyar gida. Mu kuwa namu a soye yake ga gishiri ga mai tauraro, wani abin sai kaci dai"

Mutane suna ta dariya mutumin nan yaci ya hau santi. Kan kace kwabo an siyeta tas kowa yana cewa an ga sabon salo.

Awarsu uku da fita Yaya taji sallama.

"Oh ni Haule sai mu hakura da awarar nan kuma a nemi wata sana'ar. Kitson ma shiru babu wadda ta leko"

Baba yace tayi hakuri komai lokaci ne sai ga su Marwanu da kwanuka kwalam. Dadi ya kama mutan gidan kar ma Baba yaji labari. Yana zaune bashi da wani abu da zai iya domin tallafin gidansa.

A ranar suka fara tsarin yadda kasuwar awara zata cigaba. Cikin dan kankanin lokaci ta sami karbuwa har a cikin unguwa. Da rana tsaka sai mace taki girki a tura gidan awara a siyo. Kitson Jamila shima lokacin aka gane masa ya zamana gidan basa rasa abin batarwa.

Ana haka Zahra mai gyaran jiki tazo. Bayan 'yar hira dayake tana da mutumci take cewa Mawadda idan bata komai ta rinka zuwa tayata aiki don lokacin bukukuwa ya gabato saboda karshen shekara ne. Abu kamar wasa Mawadda ta fara don yanzu ta saki ranta ba kamar da ba. Matsalarta kuma ta ragu sosai yanzu sai idan tayi tari, zabura, ko wani aikin da zaisa jikinta motsawa ba shiri shine fitsarin yakan digo. Duk da haka kuma Ade tana dan tarin kudadenta idan anyi albashi ta kaiwa masu kemis ta siyo mata magani da kuma na Baba na hawan jini.
******

Karshen zangon farko na karatu yayi inda Dahiru yayu matukar dagewa ya sami G.P.A 2.34, ranar harda hawaye yayi saboda Prof yace masa so yake yayi kokari sosai sai gashi duk da babu darasin da zai sake maimaitawa amma bai sami yadda yaso ba. Rashin turancin nan da kuma rashin wadatar lokacin karatu yasa abubuwan nasa sai a hankali.

Yanzu sunyi sabo sosai da Baba Prof yana zuwa gidansa lokaci lokaci. Ranar da ya sanar dashi sakamakonsa duk kuwa da Prof Abdulhadi ya ma riga shi sani ya nuna masa farincikinsa sosai. Babu abinda ya bashi mamaki sai dauke masa nauyin kudin makaranta da yayi kamar yadda yayi masa alkawarin yi masa wani abun mamaki tun baya. Baffa da Bilya har gida suka je yi masa godiya yace da na kowa ne. Burinsa kawai Dahiru yayi karatu idan Allah Ya bashi iko shima ya zama inuwar da wani zai raba a gaba.

Har suka koma gida suna yabon kyaun hali irin na wannan bawan Allah. Ya hada Dahiru da dansa Attahir wanda shi yanzu yake shirin shiga jami'ar abota shiyasa zumuncinsu ya karu sosai.

******

"Kin sake magana da kawarki kuwa akan zancen yaran nan? Shirun yayi yawa" cewar Daddyn su Qareeba yana kallon Dr Tani fuska ba fara'a.

Tasan za'a rina yanzu kusan kullum sai ya tado zancen. Sun gama bazawa 'yan uwansu cewa biki ya matso komai lokaci guda za'ayi amma har yanzu wata kusan biyar ba amo ba labari. Sai ta jera sati tana kiran Haj Mara bata daukar wayar. Idan ta dauka a dakila take amsawa tana mata karyar aiki ne yake rike Babawo ita kuma tun zaman kotun nan lafiya tayi mata karanci.

Dr Tani dai ta shiga muguwar damuwa yayin da Qareeba soyayyar Babawo ta hanata sukuni.

A can Kaduna kuma Haj Mara ta rasa yadda zatayi don Alh Sule tun wannan tafiyar tasa China har yanzu bata sake saka shi a ido ba. Kamar kullum bashi da zancen da ya wuce zama ne baya yi sosai shiyasa taji shiru.

Tana zaune ta rafka tagumi bayan sun gama waya BB ya shigo yana tangadi. Tashi tayi hankali a tashe ta soma masa fada. Shima ya daga hannu yana nunata da yatsa yana fada cikin muryar maye.

"Hajjaju wal Makkatu ina matata Mawadda?

Tsaki taja "Babawo ka shiga taitayinka fa. An baka aiki kaki tafiya har sun cike gurbin da wani. Baka da abin yi sai kokarin lalata rayuwarka ko"

Ya zauna kamar kayan wanki a kujera "to kiyi min aure mana ki gani idan ban shiryu ba"

"Za ka auri Qareeba din ne? Dazu ma nayi ta ganin wayar Dr din ai"

"Dangin dolayen??? Gaskiya kin ma cuceni Hajjaju. Ai ni duniya babu wata mace a idona sai Mawadda. Duk sauran mata sunansu majajjawa"

Duka ta kai masa "dan ubanka harda ni?"

Ya dago yatsansa yana dariya "kece lamba one....hahahahhh"

'Yan uwansa mata tayi niyar kira to amma dukkansu ta kula wani zukewa suke daga gareta. Ga miji baya nan ji tayi komai ya soma kwance mata. Hanyar hawa sama ta nufa kakarin aman BB ya tsayar da ita. A nan kan tsadadden kafet dinta ya kwara abinsa ya damalmale ciki. Kamar tayi kuka amma babu wanda zata ce yazo ya gyara ko da dattijuwar dake mata aiki ce kada a sami na bada labari haka ta dawo tana gyarawa yana ta zage zage.

"Hajjaju ni dake nace kada ki sola ni akan maganar Mawadda ki ka ki. Ki nemo min ita miyi aure a ragargaji soyayya ko kuma wallahi na ragargazo miki ta'asa a gidan nan"

Dena abinda takeyi tayi tana kallonsa shima ya kafeta da ido. Shi fa banda tsoron shiga kurkuku da tuni a kotun nan ya fadi gaskiya.

Duk wani tunaninta ya kulle mafita daya ta hango idan ba haka ba yaron nan a gaba sai ya hanata shiga taro.
*****

*SHEKARA KWANA: 2018*


Wata macece mai cike da kamala da haiba ta shiga ofishin likita bayan an kira sunanta. Sanye take da doguwar rigar atampa ta daura dankwalinta ta yane kanta da mayafi mai kyau wanda ya dace da kayan. Ko kadan shigarta babu bayyana tsiraici don indai zata sa mayafi to fa sai wanda ta tabbatar ba shara-shara bane. Duk da ba kwalliya tayi ba da ta wuce kwalli, hoda da man lebe amma kallo daya zaka yi mata kasan cewa mace ce da tasan me take yi.

Da sallama ta shiga ofishin ta sami likitan zaune akan kujerar marasa lafiya yayin da yake nuna mata tasa da hannu nufinsa ta zauna.

Cogewa tayi a tsaye "Ni dai zan roki a canja min likita gaskiya idan haka zaka rinka yi min"

Mikewa yayi yana dariya ya koma mazauninsa "abin bai kai haka ba zo ki zauna ranki ya dade"

Zama tayi suka gaisa tayi masa bayanin yadda take ji yanzu kusan ta gama warkewa daga lalurarta ta rashin rikon fitsari. Ya ji dadi sosai yace zata yi wata batare da wani magani ba domin su tabbatar da samun lafiyarta.

"Alhamdulillah Mawadda wannan sauki daga Allah ne da kuma dagewarki wurin shan magunguna da yin kegel exercise yadda ya kamata. To sauki ya samu sai maganar aurenmu ko?" Ya daga mata gira.

Kai ta girgiza tana murmushi "kayi ka gama. Tare muke da Baba yana wurin karbar magani na barka lafiya"

"Mawadda meyasa kike min haka ne?" Ya fada a sanyaye.

Dan hade fuska tayi "saboda kasan komai game da ni Dr Imran. Babu wani dalili da zaisa kai ko wani yayi sha'awar aurena. Sannan....kasan burina na rayuwa har yau bai cika ba"

Cewa yayi zai kirata kawai don idan suka fara wannan muhawarar zancen baya taba karewa. Kafiya ce da ita sai kace irin mutanen farkon nan. Akwai ranar da ya zolaye ta ma yace da a wancan zamanin tazo irinsu ne suke yin riko da manyan gumaka a kasa chanja musu ra'ayi. Baya mantawa ranar ne ta fara sakin jiki dashi saboda dariyar da ya sakata sai dai gashi har sun bawa shekara baya babu wani cigaba.

Wurin Baba taje ya gama karbar magani da Saifullahi suka fito suka tafi.

Mawadda Fatihu kenan matashiya yar kimanin shekaru ashirin da biyar. Taga rayuwa ita da gabadaya ahalin gidansu a dalilin fyade da akayi mata a gidan da take aiki.

Bayan dawowarsu Kano sunyi ta fadi tashi har Allah Ya buda musu da taimakon Anti Zahra mai gyaran jiki. Matar nan ta riketa da zuciya daya ta koya mata sana'ar gyaran jiki sosai. Da ita take biyanta idan sunyi aiki daga baya cikin ikon Allah ta kware Anti Zahra tace lokaci yayi taci gashin kanta. Sannan ita sun dade da barin unguwar ta koma tudun yola da zama. Suna zumunci sosai har yanzu. A lalace a wata Mawadda bata sami kudi ba ta rike dubu talatin. Budi suka samu na ban mamaki da tasbihi ga Allah. Matan manya da 'yan uwa bata taba rainawa har kasuwarta ta bude haka.

Idan an zo gyaran jiki tana yi Rafi'a na lalle Jamila na kitso. Mal Fatihu sai son barka don kuwa 'ya'ya matan da bai taba rainawa ba sun zame masa babban arziki. Hatta 'yan uwansu na kauye su Nana suna cin arzikinsu.

Shekaru biyar baya Malam kakansu ya rasu amma bai bar duniya ba sai da ya mayarda auren Ade da Baba. Itama ta dena aikatau yanzu sun hada kai da Yaya awara suke yi fin kwano biyar a rana. Marwanu da Saifullahi sun koma makaranta almajirai ke jigilar fita da awara mai sauce da ta sami karbuwa sosai.

Kanen Mawadda na wurin Ade suma bata barsu ba tana tura musu kudin makaranta. Gabadaya ta sauya ta koma Mawadda cikakkiyar mace mara tsoro wadda burinta daya yanzu a duniya shine tayi ido hudu da Haj Mara da rabin ranta BB.

Innar Fatihu da Iya sun kara tsufa amma duka gida daya suke. Gidan Mal Fatihu na kauye sunyi kakara da Maigari ya karba suka yi masa ciko suna biyansa a hankali yanzu gidan Tunga ya zama nasu.

******

Tun kafin ya fito daga motar yara sun yanyameta suna ta shafawa ana kiran sunansa. Wata leda ya dauko a gefensa cike da kayan kwalama na yara ya bude motar ya fito. Kamshin turarensa da sanyin ne suka biyo bayansa. Rufe motar yayi ya shiga rarraba musu suna karba ana murna.

Daga cikin gida Innarsa tana jinsu ta soma fara'a tasan ya iso. Shima sauri yayi ya shiga gidan wasu matasa biyu suka biyo shi da akwatinsa da wata katuwar jaka.

Inna ta tashi tana tafi farincikinta baya buya "marhabin lale lale da mutanen ya ma sunan kasar...?"

Dahiru yayi 'yar dariya yana durkusawa a gabanta "Inna na sameku lafiya?"

"Lafiya lau Dahiru....oh ni Indo tafiyar wata biyu shine ka sake cika haka duk ka zama wani basamuden kato."

Ai kuwa ta saka shi dariya sosai. Muryarsa ma ta kara zama ta manya baka ce Dahiru saurayin Mawadda bane mai aikin kubewa a gona.

Baffa ne ya shigo suna tsaye Inna tana ta yiwa Dahiru tsiya yace ta barshi ya huta mana.

Bayan Isha suna hira da iyayensa Inna ta soma mitar rashin aurensa.

"Sai dai kaci banza kaci wofi aje iyali ya gagara" cewar Baffa

Bangaren da aka gyara masa da sunan zama da Mawadda ya kurawa ido yana tunani. Inna ma wurin ta kalla wanda Danlami ne daga baya ya ajiye matarsa kafin su koma cikin gari suma.

"To....to an tabo inda yake masa kaikayi ya lula duniyar tunani" Inna tace tana nunawa Baffa yanayinsa.

Tashi yayi bai kara magana ba ya shige dakin da ya sauka zuciyarsa duk babu dadi. Ina Mawadda take? Ina zai kara ganinta? Kuma a wane yanayi.

Bayan tashinsa Baffa yayi ajiyar zuciya. Tsahon shekarun nan basu taba sanar dashi Maigari ne ya basu gida ba saboda haka za'a iya gano inda suka koma. Hana karya lokacin rasuwar Malam ance masa Mal Fatihu yazo jana'izar mahaifinsa amma ko kwana baiyi a kauyen ba. Shi kuma lokacin baya gari sunje Kano daurin auren 'yar Baba Prof ne.

Rayuwar Dahiru ta dade da sauyawa tun bayar hduwarsa da Prof Abdulhadi. Mutumin ya amsa sunansa mutum ta kowace sigar kwatancen halin kwarai. Bayan ya daukarwa kansa biyan kudin makarantar Dahiru yakan taimaka masa da ihsani. Shi kuma Dahirun sai ya mayar da hankali sosai kada ya bashi kunya. Anyi sa'a kuwa sakamakonsa ya rinka kyau yana gama aji biyar ko bautar kasa bai tafi ba Prof ya samar masa tallafi wato scholarship aka tura shi Turkey karo ilimi. Yaje yayi masters dinsa ya gama cikin shekara daya da rabi. Wannan kudi da ya samu dasu ne ya rinka taimakon iyayensa. Gidansu yanzu idan ka dade baka garin sai yayi maka wuyar gamewa. Yayi masa gyara dan gaske don ma Baffa ya dage bazasu bar garin ba.

Bilya shima likkafa taci gaba yana da nasa garejin har 'yar mota ya saya. Danlami kuma sana'ar busasshen kifi yake wanda yake zuwa kudu ya saro kala kala ya kawo. Yana nan da teburinsa har wuri biyu a kasuwar sabon gari. Ummiyo tayi aure harda yara uku. 'Yan uwanta maza sune gatanta don bata rasa komai.

Dawowar Dahiru kasar ke da wuya ya sami aiki a kamfanin Etisalat. Abu ne da ba zato ba tsammani wani abokin karatunsa ya takura masa suka cike form online. Ashe kawunsa wani babba ne a kamfanin sai gasu suna isowa ba jimawa aka basu offer shi yana Kano abokin nasa yana Lagos.

Haka Allah Yake abinSa Ya baka a lokacin da baka zato bare tsammani. Yanzu haka wani aiki aka tura shi Qatar na wata biyu shine ya dawo jiya ya wuto Kano yau.

Da tunani kala kala ya kwana washegari lahadi da yamma yace zai koma saboda baije ofishinsu ya yi reporting ba. Inna dai tunin aure tayi masa da barazanar idan baiyi wasa ba watarana zai dawo ya tarar da mace an auro masa.

Jikinsa duk ba kwari tun jiya ya kasa samun sukuni da tunanin ko zai kuma ganin Mawadda. Shatara ta arziki yayi musu kamar yadda ya saba

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

10 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment