Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a bace baya so iyayensa su zama masu son kansu. Meye laifinta? Ko basu kula da irin dukan da tasha fuskarta duk ta chanja ba. Shikenan sai duk wani jindadinta ya yanke saboda anyi mata fin karfi.

Kwanansa daya ya tattara ya koma. Inna tace ala raka taki gona, yafi ruwa gudu idan yaso. Aure ne dai baza'ayi ba duk nacinsa.

Su Baba ma dai ranar suka tafi. Daga asibiti matan zasu kwana a gidan Barira shi kuma zai nemi wani abokinsa ya kwana wurinsa da safe su hadu a tafi kotu.
****

Haj Mara ta fita hayyacinta cikin kankanin lokaci kai kace ita ce ma BB din. Shi uban gayyar hankalinsa a kwance in ka cire nacin a aura masa Mawadda. 'Yan uwa duk ta nuna musu ba abin damuwa bane saboda tana da shaidu akan sharrin da aka kulla musu. Kowa dai yaja jiki tunda ba wai wani mutumci gareta ba. Daga ita sai 'ya'yanta suke ta fama.

Sun dauko lauya wanda ya cajesu kudi ba kadan ba. Ita duk wannan bai dameta ba ma kamar Alh Sule da ya zare hannunsa a ciki kuma yace bazai katse aikinsa ya dawo ba kasar ba.

Bisa ka'ida ba'a son yiwa lauya karya domin ya sami dabarun kare wanda yake wakilta. Lauyan nasu bai ha'incesu ba yace ta daure taje su sasanta dasu kafin a shiga kotu saboda idan aka kama danta da laifi kulle shi za'ayi sannan ana iya cinsa tara mai tsoka saboda dukan da ya yi mata. Sannan BB da kansa ya nuna masa yana son yarinyar. Ganin da yake masa kamar wani dan kwaya yaji tsoron kada ya bata komai a gaban alkali shiyasa ma yace taje su sasanta.

Tariwa suka tafi suka daki gurbi babu kowa a gidan nasu. A makota ne aka sanar dasu sun tafi Kano. Haka suka kama hanya tayi ta kiran Gambo domin jin inda zata samesu ko ta sani.

Gambo tayi dariyar mugunta don bata mata karyar da tayi mata ba ta fada mata suna asibitin Malam domin kuwa ba jimawa da ta baro su suna jiran Dr Tani. Kwantar da kai Haj Mara tayi Gambo kuwa ta kwatanta mata bangaren da suke.

Ba tare da shan wahala ba ta iso. Daga inda take hangosu ta hango mata biyu da namiji daya sai Mawadda a bakin wata kofa. Da gani tasan iyayenta ne ta shafa jakarta ta jiyo envelop din da ta sako dubu dari da zata basu a kashe maganar. Sai dai ko rabin tafiya batayi ba ta hango Dr Tani ta isa garesu harda dafa kafadar Mawadda. A take hanjin cikin Haj Mara kada ta juya da sauri.

Mota ta koma a gigice ta shiga ta cewa dreban su fita da sauri. Gabadaya kanta ya dau zafi ta kasa tunani.

Su Yaya kuwa rokon Dr. Tani sukayi da ta taimaka ta amince sun bada sunanta a matsayin shaida a kotu.

Dan nazari tayi ita bata son shiga sabgar mutanen to amma tana tausayin rayuwar yarinyar nan.
"Ba komai ai aikinmu ne. Duk lokacin da shari'a ta hado da aikinmu dole mu tsaya mu fadi abinda bincike ya nuna"

Su Ade sai godiya suke mata. Ciki ta shiga ta duba Mawadda tare da hadata da wasu magungunan.

Bayan fitarsu wayar Haj Mara ta shigo mata.

Cikin nishadi da shewa yadda ta saba tace "Bokan turai gani a Kano anjima zanzo gidanki yau nayi zuwan bazata"

Dr. Tani sai murna ko akan maganar auren ne. Qareeba ta kira tace idan batayi wanka ba maza ta shiga tayi amma kafin nan a hadata da Kuku. Umarnin gyaran gida da girki ta basu sannan ta tattara kayanta ta fito.

A gidan Haj Mara tayi la'asar suka zauna hira.

"Hmmm kinga yadda Babawo ya sakani a gaba kan kanwarsa kuwa? Baban ma duk ya damu so yake yayi ya kammala abinda ya kaishi China azo asa rana"

Wani mugun dadi Dr Tani taji ta kara fadada murmushinta "nima haka Qareeba take min, motsi kadan tace BB. Gara asa ranar kurkusa don naga sun fimu doki"

Dariyar shakiyanci suka yi suka tafa. Haj Mara ta lura ba karamin matsuwa aminiyar ta tayi da ayi bikin ba. A ranta tace ta sami makamin dafawa.

"Ya kamata muyi zama na musamman akan shirye-shiryen bikin. Yanzu ma fa in fada miki wai sammaci aka kawo mana har gida gobe zamu kotu"

"Ko... me?"

Haj Mara ta tabe baki "kar fa ki damu ba wani abin arziki bane da ya wuce sharrin 'yan aiki"

Ina zata ki damuwa ana batun kotu.

"Me ya faru?" Wannan karon muryarta ta soma sanyi

"Yarinya ce take min aiki kinsan halinsu da sun sami dama su fara bibiyar maza. Shine fa tayi wani saurayi mai shago ashe irin 'yan duniyan nan ne ina gida aka zo aka ce min anga mai aikina a dakinsa can bayanmu"

Kirji Dr Tani ta dafe "kinji halin yaran nan ko, kana zaman zamanka su janyo maka masifa"

Rangwadar da kai Haj Mara tayi "nima ai ta jaza min. Tana dawowa nayi mata duka kin sanni da zuciya ga raina ya baci. Kuma nace gida zan mayar da ita. Duk yadda ta bani haushi haka naje gidan yaranki da kaina nasa suka hado min kayayyakinsu na sawa da na yara na bata da dubu ashirin nace ta shirya washegari zan mayar da ita."

"Dama zaman me zata yi miki sai taje tayi ciki ta dorawa maigida ko dansa"

"Kamar ko kin sani"

Jikin Dr Tani ya hau rawa danginta da na Daddy kusan babu wanda bata sanarwa Qareeba tayi miji ba don su huta da gori. Mijin ma dan gidan Alh Sule Chanji.

Ganin ta tsorata Haj Mara tayi murmushi "ita ba ciki tayi ba fitar da nayi ne ta lallaba ta shiga dakina zata yi min sata Babawo ya ganta. Cikin fushi ya mammareta da safe muka kaita gida. Wai kawai bayan sallah sai ga sammaci ana zarginsa da yi mata fyade"

"Me???" Kanta taji yana sarawa. Idan makiyanta suka ji zancen nan ai ta banu.

"Ban fada miki don ki tada hankali ba domin ina da shaidu da zasu kareni. Babawo ban taba jin ya yabi wata mace ba balle ince fuska ta gani sai Qareeba. Alfarma daya nake nema kada babansu yaji zancen nan ku hanamu 'ya a gaba"

"Wa? Ni? yaya ma za'ayi na fadawa kowa. Ko shi bazaiji ba" ji tayi kamar ta saki ihu. Damarsu daya ta aurar da Qareeba tana neman subuce musu.

Haj Mara ta sami yadda take so ta cigaba "ai Mawadda da iyayenta sun dauko ruwan dafa kansu. Mistake dina bai wuce na rashin kula ba tun farko kila da na gano suna wani abu da saurayin nata da wuri"

Idanu a waje Dr. Tani tace "Mawadda kika ce?"

"Eh, kinji sunan wani iri ko" ta fada tana satar kallonta

"Patient dina ce indai wadda za'a shiga kotu gobe ne Mawadda Fatihu"

"Laaahhhhhh" Haj Mara ta saki baki ita a dole mamaki take "kinji wani abu kamar a fim"

Ran Dr. Tani ya baci matuka. Tasan kawarta bazata yi mata karya ba musamman ma da bata san ta sansu ba. Yadda ta matsu Qareeba tayi aure shine tana tausayinsu zasu kullawa yaron da yake son 'yarta sharri. Lallai zata shayar dasu mamaki. Kwafa tayi ta riko hannun Haj Mara wadda ta dukar da kai harda hawaye

"Tunda suka zo asibiti da gaske an mata fyade kenan zata dorawa Babawo"

"Babawo ba naki bane ke kadai Marakisiyya. Barni dasu kawai".
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰8

*Batul Mamman*💖



Fuska na nuni da alhini Dr Tani tace "ina Babawon yake yanzu?"

"Yana tare da wani abokinsa yace zai kwana a wurinsa. Nima akwai 'yar kanwar babana gidanta zan wuce yanzu" Haj Mara ta bata amsa muryarta har tana dan rawa kamar zatayi kuka.

"Haba ke kuwa Marakisiyya maimakon kuyi zamanku a nan, kada ki manta fa alaka mai karfi ke shirin shiga tsakaninmu banda ta kawance. Kiyi zamanki a nan. Shima ki kira shi ya taho ya kwana dakin 'yan uwansa. Ai mun zama daya"

Dadi ya baibaye Haj Mara. Batayi zaton abin zai zo da sauki kamar haka ba. Cigaba suka yi da tattauna yadda zasu bullowa su Mawadda a kotu washegari.
*****

Saukarsu kenan daga tasi suka ga gaban kotun cike da jama'a. Wasu 'yan kallo ne kawai wasu kuma 'yan jarida.

Cincirindonsu kadai ya sanyayarwa da Mawadda gwiwa ta daga hannu ta kamo Ade.
"Mu koma gida" tace a hankali wani siririn hawaye yana fita daga idanunta.

"Ki karfafi zuciyarki Mawadda. Idan kika sare tun yanzu to shari'ar nan bata da wani amfani. Ni dama nasan za'a rina tun jiya a rediyo da naji ana zancen fyade da ake yiwa 'yan aiki har aka bada misali da zaman kotun da za'ayi yau akan irin case din" Inji Basira kanwar Yaya.

Suna tsaye daga gefe wasu 'yan sanda biyu suka zo za'ayi musu jagora zuwa cikin kotun. Nan da nan 'yan jarida suka rufar musu domin sai sannan suka gane su waye. Tambayoyi ne ake ta jefa musu su dai suka samu suka shige da kyar fuskar Mawadda lullube da mayafi.

Kotu tayi shiru an gama sauraren shari'ar wasu kamar daga sama suka ji ance.

"Shari'a ta gaba da za'a saurara ita ce tsakanin Mawadda Fatihu da Babawo Sule Chanji inda ake tuhumar Malam Babawo dake zaune a gida mai lamba 190 Gambara cresent Kaduna da laifin yiwa Mawadda duka tare da fyade a ranar 14 ga watan Yuni 2010."

Hantar cikinta ce ta kada sosai da taji ance idan tana kusa ta taso. Mikewa tayi tana ji a jikinta duk wani mai ido a wurin ita yake kallo. Tamkar ta shige cikin kasa ta rufe kanta haka taji a lokacin. Wurin da aka kebe domin tsayuwar wadanda shari'a ta shafa taje ta tsaya kanta a kasa. Alkali ya bukaci Babawo ya fito shima. A razane ta daga kai su ka hada ido. Zuciyarta ce ta dauki zafi saboda radadin da take ji da ta sake ganinsa ga Haj Mara itama a zaune hankalinsu duk su biyun a kwance.

Bayan shima ya tsaya lauyoyi suka gabatar da kawunansu gaban kotu.

"Sunana Barista Shafa'atu Aminu. Lauyan gwamnati mai kare mai korafi wato Mawadda Fatihu"
Cewar wata mace mai cike da nutsuwa da kamala.

Kujera ce ta danyi kara yayin da Barista Dalhatu Talba ya tashi ya gabatar da kansa a matsayin lauyan wanda ake tuhuma.

Alkali Dawud ya gyada kai sannan yace su fara tambayoyi da kawo shaidunsu.

Barista Shafa'atu ta taso ta matsu gaban zagayen inda Mawadda take tsaye

"Malama Mawadda ko zaki iya sanar da kotu abinda ya faru a ranar shahudu ga watan Yuni tsakaninki da Babawo?"

Shiru tayi gabanta na lugude, wuri yayi tsit ita kadai ake kallo da sauraro. Tunawa tayi da yadda Baba da Iya suka sakata a gaba da magiyar kada ta cuci kanta tayi shiru. Idan taji tsoro taki fadar gaskiya tamkar ta amince gobe Babawo ya sake yiwa wata yarinyar kwatankwacin abinda yayi mata ne.

Wani mugun yawu ta hadiya sannan ta soma bada labari harda yadda ya rinka bibiyarta kafin wannan rana. Da kyar ta iya kai karshen labarin saboda kukan da take yi mai taba zuciya. Mutane da dama a wurin wannan abu ya tabasu sosai. Sai da Alkali ya buga gudumarsa ya samu aka tsagaita da kananun surutan da suka soma tashi.

Barista Shafa'atu ta dan ja hanci alamun itama labari ya tabata sannan ta sake tambayarta game da Haj Mara. Shima duk yadda suka yi haka ta bada labari.

"My lord ina rokon wannan kotu mai adalci kamar yadda muka saurari bayani daga bakin Mawadda ta taimaka tayi mata adalci wurin hukunta Babawo da mahaifiyarsa daidai da laifinsu domin sunyi tarayya wurin cutar da ita" cewar Barista Shafa'atu.

Sai da yayi 'yan rubuce-rubuce sannan ya dubi Barista Dalhatu yace ko yana da tambaya da zai yiwa Mawadda ya amsa da eh.

Tun daga kallon da yake jifanta dashi tasan ba mutumin kirki bane. Wani kallo yake mata kasa-kasa irin na sai na gama dake.

"Kince Babawo ya dauki wani lokaci yana bibiyarki da son ki bashi hadin kai haka ne?"

"Eh"

"To amma me ya hana tun tsahon wannan lokacin ki sanar da mahaifiyarsa domin a yiwa tufkar hanci?"

Da sauri ta dago kai ta kalli Alkalin shi kuma yace ta amsa tambayar.

"Saboda....uhmmm dama saboda ina tsoron kada Hajiya ta dakeni ne"

"Uhmm Mawadda kenan, kina jin akwai uwar da zata daki wadda ta kawo karar danta yana neman keta mata haddi. A tunanina zata yi saurin kawo karshen matsalar ne ko don kada a wayi gari a rana irin ta yau"

Haj Mara daga inda take zaune tayi wani murmushin jindadi gamin Mawadda ta kasa bada amsa.

"Don baka santa bane na rantse duka na take yi ko yaya nayi laifi. Kuma tana sonsa shiyasa naji tsoron kada na fada tace karya nake"

"Ke kuma gaki jaruma zaki iya kwatar kanki ko ki jure duk wani hari da zai kawo miki"

Barista Shafa'atu ta mike da hanzari "objection my lord, Barista yana amfani da kalmoni domin cusa mata ra'ayin da ba nata ba"

"Objection sustained! Barista Dalhatu ka gyara kalamanka ko ka chanja tambayar" Alkali ya fada masa.

Dan sunkuyar da kai yayi "Nagode my lord. Idan kotu ta bani dama ina son yiwa wanda ake tuhuma tambayoyi"

Alkali ya bashi dama tare da umartar Mawadda ta koma ta zauna.

"Babawo Sule Chanji ko zamu iya jin takaitaccen tarihinka?" Ita ce tambayar da ya jefa masa.

Bai ko bude baki ba Barista Shafa'atu ta sake cewa objection wato bata amince da tambayar ba.

Baristar Dalhatu yayi saurin cewa "wannan tambayar tana da mahimmanci domin sanin wane ne Babawo kafin a tuhume shi da laifi irin wannan"

Alkali yace "objection over ruled, Barista ka cigaba da tambayarka"

Sai da ya bi Mawadda da kallo sannan ya fara basu labarin rayuwarsa da karatunsa da kuma dawowarsa wata hudu da suka wuce. Ya cigaba da sanar dasu cewa shi mutum ne mai mugun kyankyami ko kofi mai aiki ta wanke baya iya amfani dashi sai ya sake wankewa. Shi a ka'idarsa ma babu wani abu da yake hada shi da masu aiki koda maigadi ne kuwa.

Yana gama jawabinsa Barista Dalhatu yace "My lord daga bayanan Babawo zamu iya gane cewa abu ne mai matukar wahala ace ya yiwa mai aikin gidansu fyade. Muna da shaidu da dama da zasu tabbatar mana da halayyar Babawo. Sannan kuma ita kanta Mawadda maganarta taci karo da korafinta. Ta nuna cewa ya dade yana binta kuma tasan manufarsa amma ta kasa sanar da kowa. Da wadannan dalilai nake rokon kotu da ta wanke Babawo domin kazafi ne kawai Mawadda tayi masa don cimma wata manufa tata"

Tasowa Barista Shafa'atu tayi bayan an bata izinin yiwa Babawo tambaya.

Duk motsinsa dazu tana kula da yadda yake bin Mawadda da kallo.

"Babawo kace kai mutum ne mai kyankyami sai dai ina so ka tuna girman rantsuwar da kayi a kotu farkon tsayuwarka a nan. Ka dubi wannan yarinyar da kyau zaka iya sake rantsuwa baka taba binta ka roki ta baka hadin kai ba?"

Kallon Mawadda yayi yana kokarin yi mata murmushi yaji ance

"Objection my lord, Babawo ya riga ya tabbatarwa kotu tsakaninsa da masu aikin gidansu. Idan an bani dama zan gabatar da shaidata ta farko"

Korafin Barista Dalhatu ya karbo Alkali Dawud ya umarci Barista Shafa'atu da ta chanja tambayarta. Komawa tayi ta zauna tana jiran shaidar da zasu kawo domin tasan me ya kamata tayi.

Mal Ramadan maigadi ne ya gurfana gaban kotu. Barista Dalhatu yayi masa tambaya ya kuma tabbatar musu da cewa Babawo baya shiga sabgarsu. Kai hatta mota idan ya goge masa in zai fita sai yasa hankici yake budeta wai akwai kwayoyin cuta a hannun maigadin. Aka tambayeshi game da Mawadda ya kallota da dan murmushin tausayawa a fuskarsa.

"Yarinya ce mai nutsuwa don gidan basu taba mai aiki irinta ba. Bata da hayaniya ko kadan shiyasa Na'ibi mai kiyos yake matukar sonta"

Maganganu ne suka fara tashi da kuma kallon kallo daga Mawadda zuwa Babawo da Maigadi.

Shi kuwa Barista Dalhatu dama sun shiryo abinsu ne. Abaibai suka dunkulewa Mal Ramadan bayanin shaidar da zai kawo kotu ana neman wanda yayi mata fyade ne. Tausayinta yaji amma baiyi zaton nema ake a dorawa wanda bashi da hakki laifi ba. Duk wata dabarar boye gaskiya ita Barista yayi amfani da ita ya ha'inci maigadin.

"Ko za ka iya sanar da kotu tsahon yaushe kake aiki a gidan Alh Sule." Ya yi masa tambayar yana murmushi don abu ya fara tafiya yadda yake so.

"Shekara biyar da kusan rabi"

"A iya zamanka ka taba ganin Babawo wato BB yana kula wata mai aiki mace fiye da alakar ubangida da hadiminsa?"

"Oga BB bashi da sakin fuska kuma gashi baya boye kyamarmu da yake yi"

Hankalin su Ade ya soma tashi da jin amsoshin nan suna ganin kamar ma an gama shari'ar sun sha kasa.

"Naji kayi maganar wani mai kiyos muna bukatar karin haske game da mu'amalarsa da Mawadda"

"Ehhhh to, Na'ibi ya jima yana sonta don yana yawan bani sako haka su kayan kwadayi kamar biskit yace na mika mata....to amm..."

Bai bashi damar karasawa ba yayi wata shu'umar dariya "My lord nasan zuwa yanzu kowa ya fara fahimtar inda shari'ar nan ta dosa. Mawadda bata da alaka da Babawo amma akwai wani abu tsakaninta da Na'ibi mai kiyos. Anya babu lauje cikin nadi a zaman nan kuwa? Anya ba wani ne yasa Mawadda kama sunan dan ubangidanta ba domin su samu su tatsi wani abu a jikin mutane masu mutumci kamar su Haj Mara ba"

Ran Barista Shafa'atu ya soma baci ga shari'a tana neman komawa hannun abokan hamayya sannan ita ko kadan Mawadda bata ambaci sunan wani mai kiyos ba. Kanta ya kulle ta rasa me zatayi. Tashi tayi ta nuna bata gamsu da furucin Barista Dalhatu ba domin yana neman karkata akalar shari'ar kan wani daban bayan kuma har yanzu ba'a wanke Babawo ba.

Alkali ya karbi korafinta sannan aka bukaci Haj Mara ta taso. Hankali kwance taje ta tsaya.

Ajiyar zuciya Barista Shafa'atu tayi tana kallonta. Shigar mutumci tayi harda hijab fuskarta fayau kalar tausayi.

"Haj Mara a ranar shahudu ga watan Yuni kin koma gida kin tarar da danki ya yiwa mai aikinku fyade bayan mugun duka da yayi mata. Ke kika taimakata ma tayi wanka sannan tsoron tonon asiri duk da raunukan dake jikinta kika ki kaita asibiti. Dadin dadawa kika dauketa kika mayar gida batare da yiwa iyayenta bayani ba"

"As....as...sal...salam...as..."sai kawai kuka ya kufce mata mai sauti da tsuma zuciya. Ta kwashi wurin minti biyu tana kuka tana goge hawaye.
"Ku gafarceni, assalam alaikum. Ni dai sunana Marakisiyya kuma nice mahaifiyar Babawo. Nayi mamaki matuka ranar da sammacin kotun nan ya iso garemu har gani na rinka yi ko anyi kuskure ne."

Ta kalli Mawadda idanunta jazur "Mawadda me nayi miki a duniya zakiyi min wannan sakayyar? Tabbas nasan ni mutum ce mai zafi bazan boye ba. Amma hakan bai hanani rungumar duk wata maiaiki ba saboda nasan da na kowa ne. Me muka yi miki Mawadda har kika rasa wanda zaki kai kotu sai ni? Ni bazan tonawa kaina asirin zaman da mukayi ba balle na kwashe ladana da baki. Idan kotu ta kamamu da laifi ayi mana duk hukuncin da ya dace." Ta kare a raunane.

Mutane sai tausayinta suke ji. Mace kamar wannan wadda ko ba'a fada ba zaka san cewa arziki ya zauna mata take yiwa yarinya karama kuka.

Da kyar aka iya rarrashinta ta bada nata jawabin kamar haka.
"Banyi niyar tozartaki ba Mawadda amma kin nuna min da gaske ne da ake cewa kayiwa mutum inuwa shi kuma ya kaika rana. Ya maigirma mai shari'a yarinyar nan satar da take min bazata kirgu ba ina kawar da kai. Da zata tafi iyayenta shaida ne ba karamin tanadi nayi mata ba. Yaron da ake magana a kai wato Na'ibi, kiyos gareshi kusa damu. Daga aike a hankali na fuskanci ko ban nema ba sai tayi kwalliya tace min akwai aike? Idan nace babu sai tace zata dan fita. Ban kawo komai a rai ba nake kyaleta. Sai kawai wata rana aka kawo min zancen an ganta a dakinsa. Nayi kuka nagode Allah. Sakacina shine rashin mayar da hankali da na fuskanci ta fiye yawo amma banyi mata zaton yawon banza ba. Wannan abin shine ya daga min hankali nace gara ta koma gida kada a haifi da mara ido. Tayi kukan tayi magiya duk a banza don bazan boye muku ba ranar har dukanta nayi. Na hukuntata kamar yadda zanyiwa 'yar cikina. Ina fita ne ta shigar min daki sata Babawo ya kamata shima zuciya ta kwashe shi ya mareta. Washegari na maidata gida bamu sake jin komai ba sai kararmu da aka kawo"

Mawadda kuka iyayenta kuka. Hatta Baba hawaye yake yi sosai.

Alkali Dawud yace idan suna da shaidar da zasu kawo ana bukata. Waige waige suka soma yi ba Dr Tani ba dalilinta. Wani mai kaya irin na masinja ne ya fadi uzurinta cewa ta taho aka kirata patient din da ta yiwa aiki tana zubar da jini. Wannan dalilin ya sanya aka dage sauraron karar sai bayan kwana goma sha biyu.

A sanyaye suka tashi kafin su fita Barista Shafa'atu ta hau Mawadda da fadan me yasa bata yi mata zancen Na'ibi ba. Su Iya suka tsaya sauraronta tana fada mata cewa da gaske ne ya nuna yana sonta amma da wuri ta sanar dashi aure zata yi. Kuma duk wata kyauta da yake bawa Ramadan maigadi ko tsinke bata taba karba ba. Game da zuwa kiyos dinsa tun da ta gane yana sonta ta gwammace ta tsallaka titi idan an aiketa. Dama yawanci siyan katin waya ne yake kaita. Kafin faruwar wannan abu gareta kuwa yafi wata bata ganinsa. Kiyos din ma ya koma shagon renting din finafinan hausa shi kuma bata san inda yayi ba.

"Wato sun nemo wanda baya nan bare ya kare kansa shine za'a dora masa laifin da baiji ba bai gani ba" Barista Shafa'atu ta fada tana rubutu.

Mawadda ta kalleta "wallahi babu karya a duk abinda na fada miki"

Murmushi tayi "na sani Mawadda kuma in sha Allah sai an kulle BB an bi miki hakkinki"

"Idan ba mu muka ci shari'ar ba ni za'a kulle kenan?" Yadda tayi maganar da raunin murya yasa Baba fita hankalinsa duk a tashe yake ya rasa me zaiyi ya samarwa 'yarsa farincikin rayuwa.

Fitarsa waje ke da wuya yaji wasu suna tattaunawa suna aibata 'yan kauye a matsayin kwadayayyu wadanda basa iya rike talaucinsu.

"Tsabagen son zuciya ke dibarsu su kwaso rida-ridan 'yan mata a kawosu birni aiki."

Wani yace "sai ta kwabe musu ayi ta dauki ba dadi"

"Idan basuyi haka ba ai basu amsa sunansu na 'yan kauye ba. Da anyi magana sai ace an turo yarinya tara kudin da za'a yi mata kayan daki."

Zuciya ta kwaso Mal Fatihu, ransa ya kai makurar baci ya karasa gaban wadannan mazan cikin daga murya wanda ya janyowa kansa taruwar 'yan jarida yace

"Shi dan kauye ko talaka ba mutum bane? Meyasa idan dan birni ya nemi kudi ake jinjina masa idan dan kauye ya nema yake zama kwadayayye? Masu kudin da mutanen birnin me suke yi mana domin inganta rayuwa? Ko nan da Jigawa ban taba zuwa ba amma ina da tabbacin ko ina a fadin duniyar nan akwai masu kudi kuma akwai masu yi musu aiki talakawa kauyawa irinmu. Haka Allah Yaso kuma haka Ya tsara duniyar arzikin wani yana karkashin wani. Idan munyi bara kuce zukatanmu sun mutu idan mun nemi halak da guminmu ace mun kasa rike talauci. Wannan wane irin son kai ne da rashin adalci? Mune 'yan dako mune leburori mune masu kaskantacciyar sana'a amma duk ba'a gani. Talauci yasa yaro sa'an jikanka zai tsaya ka bude masa kofa ya shiga mota yana binka da harara. Mu maza mun nema a waje matanmu kuma su nema a cikin gidajen aure. Kuna da mata maaikata, suna bukatar masu tayasu raino, gyaran gida ko girki. Idan ba kaddara ta rabo mace da gidan mijinta ba ai dai bakwayi tsammanin matan aurenmu ne zasu baro nasu kananan yaran a kauye su fito aikatau ba. Dole yaran namu da suka kawo karfi zamu turo. Babu mai zurfafa tunani yaga cewa banda abinci muma fa muna rashin lafiya kamar 'yan birni waye zai bamu kudin asibiti, lalura da dama ta kudi tana taso mana. Kai da kake cewa muna turasu neman kudin kayan daki waye yace maka don muna kauye shikenan idan mun tashi sai mu aurar da 'ya mu kaita da tabarma? Haka al'adar bahaushe take waye yaki ya sami wani abu da zai taimaka masa yaji dadin rayuwarsa?

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

10 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment