Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cibi.

"Fadawa mijinki ba hurumi na bane Tani nazo dubaku ne duk da kin yanke alaka damu saboda sawa ranki da ki ka yi bama kaunarki bama kaunar zuri'arki. Duk wani abu da muke yi miki muna yi ne don gyara son 'ya'ya ya rufe miki ido kin kasa fahimta"

Kujera ta samu ta zauna tana kuka Alh Munzali ya kalli Qareeba yace "Allah Ya baki lafiya Ya saka miki. Fyade ba karshen rayuwa bane zaki cigaba da harkokinki kamar kowa"

Dr Tani ta katse shi "Yaya Munzali baiyi raping dinta ba"

Irin dariyar kin ma raina min hankali yayi kafin yace mata "ko duk jikina kunne ne bazan yarda. Nasan dama dole kiyi kokarin boyewa amma ki sani rufewar ba gata bane. Zan wuce amma zamu dawo anjima tunda na tabbatar da labarin ba jita jita bane"

Bin bayansa ta yi tana ta cewa ba'a yiwa Qareeba fyade ba yayi tafiyarsa ya kyaleta. Da ta koma tsareta Dr Auwal yayi tana kuka take bashi labarin komai tun daga zuwan Mawadda asibitin har yadda suka yi da Haj Mara da shigarsu kotu.
Qareeba tana ji tayi ta kuka saboda ita mahaifiyarta ta bada shaidar zur ta batawa wata rayuwa. Batun Alh Munzali kuma alkalin da ya yi shari'ar Justice Dawud ashe kanin abokinsa ne bata sani ba. Ta manta wani lokaci da rashin haihuwa ya damesu Alh Munzali ne yayi sanadiyar hadata da matarsa har aka dace. Ranar da taje kotun bada shaida bata gane shi ba. Shine ya tuna ta har yake fadawa dan uwansa ya ga likitan nan yau a kotunsu wanda Alh Munzalin yaji labarin a wurinsa. Baiyi kasa a gwiwa ba har gida yaje ya sameta saboda ya bincika ya gane shine wanda aka ce zai auri Qareeba a lokacin. Dr Tani ta shafawa idonta toka tace karya ne kuma ta kula dukkansu 'yan uwan nata basa son yaranta su cigaba. Yayi bakinciki sosai a lokacin yace mata taje da sannu duniya zata bayyana mata halin yaron domin yayi bincike a kansa ya kuma tabbatar bashi da tarbiyya. Gashi kuwa ta gani zahiri.

Dr Auwal ransa yayi matukar baci "shine kika boye min abu mai girma irin wannan saboda kina son 'yarki tayi aure? To gashi nan kin bada shaida an sake shi yazo ya lalata miki taki 'yar. Auren da ki ka so tayi kuma bai yiwu ba."

Hakuri ta shiga bashi yana rike da hannun Qareeba yaki kallonta " Kuma bai sami nasarar yi mata fyaden ba mu ka je dakin"

"Da gaskiyar Alh Munzali tunda asibitinki ne nan nayi imanin zaki yi duk yadda zaki iya ki rufe maganar "

"Daddy zan gyara al'amarin nan wallahi ko zan rasa aikina sai na kulle Marakisiyya da danta. Amma ku yarda Allah bai bashi dama akanta ba"

Tana ta magana bai sake ce mata komai ba har 'yan uwansu 'yan ganin kwaf su ka fara taruwa zance ya bazu kamar gobara an yiwa Qareeba fyade.
*****

BB da ya bar gidansu Qareeba wani abokin shashancinsa ya nema yazo ya dauke shi saboda ya kasa tuki. Hanci jini baki jini jikinsa ya bugu sosai Dahiru ya tara masa gajiya.

Kashe wayarsa yayi don yasan Haj Mara zata kira. Shi kuwa burinsa ya cika wannan wawiyar Qareeban yanzu ko giya iyayenta ke sha dole su sarara masa. Takaicinsa daya da bai samu ya karasa ba sai kuma tunanin waye wannan mutumin da yazo har ya dake shi haka. Ko bacci ya kasa yi saboda rashin sanin mutumin da sunansa. Ya sawa ransa don sun fado masa a bazata ne amma ranar da zai sake haduwa dashi sai ya nuna masa shi BB ba'a ja dashi.
******

'Yan uwan Mawadda su Rafia duk suna gidan yau ana ta tsare tsaren biki. Jinsu take yi wai ita ce zata yi aure abin kamar almara. Gani tayi har azahar ta wuce yau Dahiru bai kirata ba ta tashi ta barsu a tsakar gida taje ta kira shi.

Yana zaune a falon Baba Prof ana masa gyaran targade. Hannunsa na dama garin dukan BB ya sami targade bai sani ba sai cikin dare wurin babban yatsansa ya kumbura ya soma damunsa da ciwo. Abu harda su zazzabi karfe takwas ya kira Attahir shine ya taho dashi gidan. A hanya kafin su zo yake bashi labarin abinda ya faru.

"Ina ma tare muke wallahi bayan munyi masa duka mu dandake matsiyaci. Irinsu fa kamata yayi a mayar dasu huhulahu ta yadda ko sun ga mace nan gaba iyakar su da ita ido"

"Gara da baka gani ba Bro, da abin na kwana a raina ya dameni matuka. Da shi da wanda ya yiwa Mawadda jiya na tsine musu yafi a kirga."

Ana gyara hannun yana gumin wahala ta kira har sau biyu. Attahir ne ya dauki wayar a kira na uku yace mata ana masa gyara zai kira idan an gama.

Tunda taji haka hankalinta ya kasa kwanciya ko hirar ta kasa da yayyenta. Bayan minti goma ta sake kira Attahir ya kuma dauka.

" 'Yar uwarmu an gama amma kinsan mutumin nawa rago ne kuka yake yi shiyasa na karbe wayar"

Dahiru ya tashi yana cewa ya bashi ya hana. Yadda yaji ta damu sosai yace ta kwantar da hankalinta zai kawo mata shi yanzu.

"Baka tausayina zaka ce na fita yanzu" Dahiru yace yana karbe wayarsa.

"Naji kamar tana kuka ne" ya zolaye shi.

"Waye ma yace ka daukar min waya?"

Sai da ya huta yaci abinci sannan suka tafi da Attahir din. Da ya kirata yace suna waje cewa tayi su shigo ciki.

Shi kadai ta samu a zaune ta tambaye shi ina Attahir tana kallon hannun.

"Na kora shi waje"

"Yaya hannun?" Tace da damuwa.

"Ni fushi nake tun safe baki neme ni ba"

"Yayanmu kaine fa jiyan nan..."

Yayi murmushi "me nayi jiyan?"

"Babu komai"

"Ashe dai kina sona Attahir yace kinyi kuka da ya fada miki"

"Ba wani nan kaine yace kayi kukan. Naso in gani sai na tara bokiti"

"Kinci bashi yarinya. Bari na tashi zazzabi nake ji. Hankali ya kwanta kin ganni ko" yace da dariya.

Ita ma tace "Kai naka bai kwanta ba da ka ganni?"

"Sosai kuwa Mawaddatan wa Rahma. Saura kwana 8 kina tayani kirge kuwa?"

Dariya tayi suka mike tare tana masa Allah Ya kara sauki.

Ya karkace kai yana kallonta "kina jindadinki"

"Me kuma nayi?"

"Nine mara lafiya, ni na kawo miki kaina ki dubani sannan ko rakiya babu."

Murmushi tayi masa "Allah Ya baka hakuri muje"

Tare suka fito waje suna yiwa juna murmushi Attahir yana hira da tasa masoyiyar Nawal ya hango su sun burge shi.

Daga bayan motar babban yaron Garwashi ne Danmani ya saitasu ya dauke su hoto a kofar gidan. Dariyar mugunta yayi shi kadai. Garwashi kwatancen karya ya yiwa BB duk da sun gano ainihin gidan harda batun aurenta da za'ayi. Batare da bata lokaci ba BB ya turo musu kudin wanda suka raba su bakwai. Shine Danmani ya zagaye shi kadai ya dauko hoton duk da baisan waye Dahiru a gareta ba. Burinsa ya dauketa a kofar gidansu dama. Wayarsa ya tura a aljihu ya nufi titi yana fito zai je ya saidawa BB a farashi mai tsada.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰16

*Batul Mamman*💖



Baba ya kalli Attahir da tausayin Dahiru ya tsinka masa zuciya "samari yaya sunanka?"

Amsa masa yayi jiki a sanyaye. Baba yace ya tafi da Dahiru gida don ya sami nutsuwa shima ciki zai koma ya duba Mawadda.

Sai da ya fita Attahir ya kwashe wayoyinsu ya dago Dahiru. Ko kofa basu kai ba aka soma kiran sallar Magrib. Marwanu ne ya fito cikin sauri yace Baba yace su jira shi zai fito suje masallaci kafin su tafi.

A ciki dakin su Inna aka kwantar da Mawadda. Kuka take yi sosai mai cin rai su Yaya suna rarrashinta amma ta kasa shiru. Rabonta da irin wannan firgicin anfi shekara. Tun wata rana da tana cikin adaidaita sahu suka tsaya a danja. Gefe da gefe maza ne akan babura sun matsi adaidaitan. Abinka da 'yan tasha suka fara yi mata zantukan banza bata san lokacin da ta fara ihu ba. Abu ya kaita da suma ranar ne ta fara haduwa da Dr Imran.

Yau kuwa kukan bakincikin nakasa ta da BB yayi take yi. Wannan abu ya kara tabbatar mata aure bai kamaceta ba domin da wahala matuka ta iya rayuwa da miji. Bata jin akwai wata soyayya da zata sa namiji ya iya hakuri da matar da bazata iya kebewa dashi ba batare da tsoro da fargabar kada ya tabata ba.

Ade tun tana rarrashinta itama har ta soma fada karshe ta fashe da kuka. Tashi tayi ta fita daga dakin ta barsu da Yaya. Zuciyarta bata iya jurewa kukan Mawadda don tasan yarinyar ta ga rayuwa.
Kuma a haka ma don tana da dauriya ne.

Bayan sun dawo hakuri Baba ya sake basu Dahiru ko uffan bai iya cewa har suka tafi. Gani yayi Attahir ya dauke hanya alamun gidan Baba Prof zasu koma yace ya kaishi gida baya jindadi.

Idonsa akan titi yace "nasan baka jindadin shiyasa bazan bari ka kwana kai kadai ba yau."

"Attahir please" yace da kyar.

"Sai dai kayi hakuri idan ba haka ba zan sanar da Baba halin da ake ciki.Kuma ka manta motarka na can?"

Taga ya koma kallo bai kara magana ba sai tunane-tunane. Suna zuwa dakin Attahir din ya wuce ya kwanta. Shima sai ya rabu dashi don yasan yana cikin damuwa.

Sai bayan isha ya matsa masa suci abinci yace ya koshi.

"Sannu baban soyayya abin kuma harda hora kai da yunwa? Dadin abin gidansu Anti Qareeba babu nisa..."

Saurin kallonsa Dahiru yayi shi kuma yayi dariya sannan yace "na rantse ko kaci ta dadin rai ko kuma naje gidansu na kirawota. Nasan zata zo kaga sai a nunawa su Haj Mama"

Tsaki Dahiru yaja sannan ya dauki cokali kamar shine ya bata masa rai ya rinka tura abincin da kyar.

Can dare bacci ya gaza daukarsa. Tunaninsa bai wuce wane hali Mawadda take ciki ba. Da abin ya isheshi alwala ya dauro ya soma nafila da addu'o'i a nan kan abin sallah bacci ya dauke shi.

*****

Wayarsa ce take kara alamun kira ya bude idanu da kyar. Karfe goma da rabi ya gani ya tashi yana dafe kansa dake matsanancin ciwo. Da kyar yayi sallar asuba ma saboda ciwon kan. Bilya ne ya kira shi Baffa da Inna sun zo suna gidansa. Amma Baffa yace bazai kwana a Kano ba saboda haka yayi sauri ya zo ya kaisu gidan Mal Fatihu.

Da sauri ya mike yayi sa'a ba ranar aiki bace. Attahir ne ya shigo ya ganshi yana saka kaya cikin sauri.

"Sai ina koma Baban soyayya? Yaya kan naka"

Dube dube yake da sauri sauri "Attahir ina mukullin mota ta? Jiya sai da nace ka kaini gida gashi su Baffa sunzo ina nan"

Kafadunsa Attahir din ya rike "dakata mana, ni bansan ka da wannan garajen ba. Me yake faruwa?"

Daurewa yayi duk da yana ganin lokaci na kara tafiya ya fada masa wayar Bilya. Murna sosai ya tayashi don ya kula ba karamin so yake yiwa Mawadda ba. Abu ne kuma na gida shiyasa da Dahirun ya nemi ya raka shi yace ba yau ba. Har ya fita ya dawo ya mika masa hannu suka yi musabaha.

Rike da hannun nasa Dahiru yace "nagode kuma kayi hakuri ina ta masifa"

"Its called love babu damuwa. Abu daya ne dai idan ka kwaso mana Anti Qareeba ..."

Fita yayi yana dariya ya tafi gidansa domin ya shirya. Fatansa dai iyayen nasu su taimaka su amince wannan karon kada wani abu ya sake rabasu.
******

Garwashi da yaransa sunyi nasarar zuwa garin Tariwa inda da naira dari biyu suka sami wani mai bakin reza ya kwashe komai da ya sani game dasu Mawadda ya fada musu. Gidan ne kawai bai sani ba a Kano amma yasan na Maigari ne.

******

Mawadda tana kwance a daki Ade ta shiga ta sameta. Tashi tayi da sauri don tasan Ade ta hanata wannan kwanciyar da tunani. Kamar ta sani kuwa Ade tace

"Me na fada miki dazu da na shigo?"

"Kiyi hakuri na tashi yanzu" ta amsa tana gyara katifar da ta kasance tasu ita da Rafi'a a da.

"Dazu me yasa da aka turo tambayar gyaran jiki ki ka sallami yaron wai baki da lafiya? Zaki fara wasa da sana'arki ne saboda damuwa ko me."

Yadda tayi maganar da fushi yasa Mawadda yin kasa da kanta. Bata da wani kuzarin aikin kanta cushe yake da tunanin rayuwarta.

Sakaya kofar Ade tayi kada ace tasa 'yar fari a daki ta sassauta murya
"Ki kara hakuri yadda ki ka saba kinji ko? Ni kaina abin nan ba karamin damuna yake ba amma yaya muka iya da abinda ya gagaremu." Hawaye ne ya taho mata tayi saurin sa gefen dankwalinta sai dai Mawadda ta riga ta gani. Hankalinta yayi matukar tashi kuwa.

"Ade wallahi na dena. Me zan dafa idan kin tafi?" Tace tana bude kofar dakin.

Yau ake kai lefen 'yar Barira kanwar Yaya shiyasa ta fita da wuri. Itama Ade yanzu zata karasa shiryawa su tafi dasu Iya. Mawadda kadai zata rage saboda Baba.

Fara'ar dole ta kirkiro domin kwantarwa mahaifiyarta hankali ta tafi kitchen. Tana fita Ade ta zauna taci kukanta don tasan babu wani abu da zasu iya yi domin kawowa 'yarsu farincikin da kaddara ta shiga tsakaninta dashi.
******

Shabiyu Dahiru ya isa gidan Bilya. Baffa ya gama fadan ya bata musu lokaci yayi ta aikin bada hakuri.

Inna ta kalle shi a ranta ta yaba da yadda 'ya'yanta suka koma. Burinta yanzu akansa ya kare shima ya ajiye iyali kamar 'yan uwansa.

Hansa'u ana ta firirita Dahiru yazo. Abinci ta kawo masa dayake yunwa yake ji yau bai gwaleta ba yaci.

Furaira tace "kana yawo da yunwa har tsakar rana haka ance kayi aure ka zauna shiririta."

"Kai Yaya Furaira kin matsawa Yayanmu Dahiru" cewar Hansa'u tana satar kallonsa.

Inna ta gane ina zancen ya dosa don Furaira ta jima tana maganar a hada Hansa'u da Dahiru aure. Sauya hirar tayi saboda kada su fara rigimar da suka saba.

"Ince ko ka sanar da su Mal Fatihu zamu zo?"

Dafe kai yayi tace ya hanzarta kiran Mawadda ta fada kafin Baffa ya fito daga dakin da suke tattaunawa da Bilya.

Jin an ambaci Mawadda yasa Furaira hade rai "Inna gidansu Mawadda zaku je kuma? Yanzu biye masa zaku yi ya auri yarinyar da ta gama lalata rayuwartaa titi? Idan ma Hansa'u ce bakwa so ba dole amma bai kamata ku barshi ya dauko wadda zata gurbata mana dangi ba"

"Tashi ki bar wurin nan kafin na saba miki" Bilya ya daka mata tsawa yana shiga falon. Ranta a bace ta mike Hansa'u na mara mata baya suka fita.

Inna tace ya rinka hakuri tunda yasan halinta. Dahiru kuma ya fita waje ya kira Mawadda. Wayar tana ringing gabansa yana faduwa kada taki dauka.

Su Ade sun gama shiryawa suna jiran Adaidaita sahu da Marwanu yaje samowa a bakin titi ita kuma tana gyaran salad taji wayar.

Ganin sunan mai kiran ya sanya zuciyarta tsananta bugu. Muryarta ma gabadaya chanjawa tayi kamar wadda tayi gudu tayi masa sallama.

Lumshe idanu yayi yana jin daddadar muryarta tana gaishe shi.

"Yayanmu ko baka ji ne?" Ta fada tana jijjaga wayar.

Ajiyar zuciyarsa taji sannan yace "ina jinki, kin tashi lafiya?"

"Lafiya kalau" tace duk ta kidime da jin muryarsa.

"Zamu zo dasu Inna nan da...ina ganin bazai kai awa ba. Baba yana nan ko?"

"Eh zan sanar dashi"

Kashe wayar tayi ta tashi. Yanzu me zata fadawa Baban. Tana tsoron kada ace ita tace ya kawosu tunda bata san yadda suka kare jiya ba. Ade taje ta fadawa ta hau salati

"Mu da zamu fita? Tsaya na sanar da babanku"

Basu jima ba suka fito tare da kansa ya fadawa su Inna. Mawadda kitchen ta koma Ade tace ta kara abincin. Tana aiki tana ji suna tattaunawa akan amsar da Baba zai bayar idan Mal Isiyaku ya tado da zancen Dahiru. Iya kadai ce tabi mai adaidaita sahun aka bar Ade da Inna.

Biyu saura suka karaso. Mawadda ta sake gyara gida ko'ina yaji turaren wuta. Falonsu na soro a gyare sai kuma dakin Ade inda Inna zata zauna shima da tsakar gidan fes. Hatta abinci, kunun aya da ruwan sanyi duka ta ajiye musu.

Marwanu ne ya yiwa Inna jagora zuwa cikin gidan yayin da Baffa, Bilya da Dahiru suka tsaya a falon tare da Baba.

Tamkar wani abu bai taba hadasu ba Baba ya taso ya tarbe su cikin mutumci da karamci. Haka Innar Fatihu da Ade suka yiwa Inna suma a ciki.

Da Mawadda ta fito gaisheta janyota tayi jikinta kwalla na taruwa a idanunta.

"Allah Sarki 'yata, na rasa me zan ce dake. Kiyi hakuri kinji 'yannan"

Innar Fatihu tace "Haba Indo do Allah banda dawo da hannun agogo baya. Yadda lokaci ya shude haka komai ya wuce. Ziyarar da kuka kawo mana tafi komai a wurinmu"

Ade ta tursasawa Inna cin abinci tace ciwon suga ke damunta bata dade da samun sauki ba shiyasa take tsoron shinkafa.

Wata karamar jaka Ade ta dauko ta ciro kudi ta bawa Mawadda.
"Yi maza ki bawa Marwanu ya siyo cous-cous a bakin titi. Idan baya nan ki hanzarta kije"

"Kai Sa'ade kamar baki ki barshi ba yunwa nake ji ba"

Mawadda tuni ta saka hijabinta mai hannu wanda ya sauko zuwa gwiwarta tayi waje. Tana jin Inna na cewa ai fa dole ne taci.

Kiran Marwanu tayi a waya yace ya tafi gidan Anti Barira. Takalmi ta dauko wasu masu tudu kadan ta saka ta fita. Dahiru yana cikin falon soron kuma inda yake zauna yana fuskantar kofa ya ganta ta wuce da sauri kada su hangota. Tashi yayi yace yana zuwa ya biyo bayanta.

Tana fita daga gidan ya fito shima.

"Ina zaki je?"

Cak ta tsaya har ya iso gefenta ya tsaya.

"Uhmm, uhmm cous-cous zan siyo"

Ya dan bata fuska "da kanki?"

"Marwanu baya nan"

"Tsaya a nan na siyo miki"

"Ka koma ciki zanyi sauri ba nisa sosai"

Yadda ya kalleta yasa ta mika masa kudin. Ko kallonsu baiyi ba ya wuceta ya shige mota ya ja. Tafiyar da tasan da ita ce a kafa zata kai har yanzu bata isa titin ba shi da yaje a mota sai gashi ya dawo cikin 'yan mintuna.

Mamaki ya bata ganin ya dauko katan guda ta bude baki tana kallonsa har ya iso bakin kofar gidan inda take tsaye.

Murmushi yayi ganin tana ta kallon ikon Allah ita da zata siyo kwali daya shi ya dauko katan

"Rufe bakin mana Kanwarmu"

Kamar tayi masa kuka tace "Yayanmu me zance idan na shiga da wannan?"

"Aikena ki ka yi shiyasa baki dade ba mana"

Turo baki tayi "kasan ba haka nake nufi ba"

Jingina bayansa yayi da bango a gefenta sannan ya juya kansa bangaren da take. Shashantar da zancen yayi don ba hirar katan din cous-cous yake so suyi ba.

"Wane irin so nake yi miki ne? Komai naki ina so harda wannan tura bakin"

Daburcewa tayi ta shiga tura katan iya karfinta saboda kunyar da taji. A nan waje ta barshi yana mata dariya ta tura shi kitchen ta dafa rabin kwali daya ta kaiwa Inna.

A falo su Baba suna hirar yaushe gamo inda Baffa ya roke shi da ya yafe masa abinda ya faru a Tariwa.

"Fitar maganar nan daga gidana ne sai na kasa zama aboki nagari nima na biyewa sauran jama'a"

"Kada muyi haka da kai mana Mal.Isiyaku. Kaddara ai ba'a guje mata. Ni dai don Allah mu bar zancen nan. Zumunci yafi komai gashi kazo har gidana me zance banda godiya?"

Bilya taya Baffa bada hakuri yayi Baba yace shi dai a bar tada tsohon zance baya so.

Baffa yace da Bilya "ina kaninka ne?"

Shima dayake yaga fitar Mawadda dazu sai yayi murmushi kawai "ina jin iska ya fita sha"

Sun cigaba da hirarsu Mawadda kuma ta koma daki. Zamanta ke da wuya Dahiru ya kira. Kai ta girgiza kafin ta dauka.

"Ki fito muyi hira"

Kamar yana gabanta ta zaro idanu "Da wa? Rufa min asiri"

"So nake naji yaya kika kwana jiya?"

Zancen jiyan take ta gudu don bata son tunawa ma.

"Lafiya kalau"

"Kizo na ganki na tabbatar"

"Ba yanzu ka ganni ba?"

"Aikena fa kika yi daga fitowata"

Yana ji tana dariya kasa-kasa.

"Ina mota ni kadai bana son hirar manya. Ke da nake son taki hirar kuma kina ja min aji. Bari kawai na kira Anti Qareeba" yace a kalar tausayi.

Dariya yaji ta sake yi ya shiga bata labarin haduwarsu ta gidan mai jiya. Mawadda sai da ta koma rufe bakinta kada a jiyo ta. Yayin da shi kuma yaji ransa ya sake gabadaya babu sauran damuwa tunda ya sakata farinciki.
*****

Sai da suka yi la'asar suka fara haramar tafiya saboda a ranar zasu koma Tariwa. Bilya ne ya fara fita Baffa ya danyi gyaran murya Baba ya kalle shi.

"Mal Fatihu game da yaran nan..."

Baba yace "munyi magana da Dahiru jiya nace ya hakura mu cigaba da zumuncinmu"

Fuskar Baffa ta nuna rashin jindadi "nasan bamu kyauta ba kuma bazan gaji da baka hakuri ba. Amma rashin amincewarka yanzu tamkar baka mayar da komai ya wuce din bane kamar yadda ka fada min"

Dariya yayi
"Kada ka daureni Mal Isiyaku. Ai shi ya gani da idanunsa yarinyar nan har yanzu fa bata gama dawowa daidai ba. Abu kadan yake zaburar da ita ta firgita. Karin nauyi kawai zamu bashi idan aka aura masa ita"

"Sauki na Allah ne. Ni dai zuwan yau na zumunci ne amma zamu dawo ayi magana ta gemu da gemu" yace yana dariya.

Baba ya rasa amsar da zai bashi yace bari ya kirawota ta gaishe shi sai ta yiwa Inna magana ta fito.

Cike da ladabi tazo ta gaishe shi sannan su Ade suka rako Inna yayin da ta koma ciki.
*****

Kwanakin da suka gabata Dahiru ya yisu cikin neman amincewar Mawadda a bangaren su Baffa shima sau biyu yana kiran Baba akan zancen. Iyayensa biyu da zaiyi shawara dasu duka suna gidan ya tara matansa a gabansu yace ga yadda suka yi da Mal Isiyaku.

"Anya baka ganin wannan wata dama ce Allah Ya bamu domin samarwa Mawadda farinciki?" Cewar Innarsa.

Iya tace "kuma ina tsammanin mun daukaki abin nan da girma sosai muma mun bada gudunmawa wurin dakushe mata tunanin aure. Mace take gama yawon bariki ma tayi aure balle wadda aka yiwa fin karfi? Mutanen nan ba mune muke binsu ba kazalika babu abinda basu sani ba su da dansu suka kawo kansu saboda haka ni dai tawa shawarar shine a basu dama"

Har kasan zuciyar Ade godiya take ga Allah da Iyanta ta kawo wannan shawara. Tana son Mawadda tayi aure kuma bata ga wanda ya dace da ita ba sama da Dahiru.

Yaya ma dari bisa dari ta goyi bayan shawarar Iya
"mu gwada Malam kada nan gaba muzo muna dana sani. Yarinyar nan tayi kokari kuma tana kan yi wurin nuna maka komai ya wuce kuma ta amince da hukuncinka gareta. Sai dai wallahi tana da rauni sosai. Sai dare yayi kaji tana kuka ita kadai gari ya waye ta shiga aiki kamar babu komai a ranta."

Ade Baba ya kalla yana jiran jin ta bakinta sai tayi murmushi kawai sannan tace duk shawarar da aka tsayar tayi mata.
*****

Mal Isiyaku ya nemi 'yan uwansa akan maganar tunda dole dasu za'a nemi aure babu wanda ya goyi bayansa. Daga me cewa tun farkon karuwanci tayi sai masu cewa yanzu ma da jikinta take ciyar da iyayenta. Rigingimu dai daban daban Inna har ta soma tunanin ko su fada masa ya hakura kawai. Don abin yafi zafi daga bangaren 'yan uwan da suka so ya auri 'ya'yansu bayan sun fara masa kallon Alhaji.

*****

"Alhaji kasa baki mana" Haj Mara tace cikin bacin rai. Gani take ita kadai ce ta damu da rayuwar danta. Yanzu ma maganar zuwa Kano tayi masa yace ba inda zashi.

Kallon BB yayi wanda yake tsaye a gefen dinning table yaki ma yazo gabansu.

"Babawo wannan karon na goyi bayan mamanka. Ka shirya ranar Juma'a kaje ku gaisa mu kuma zamuyi abinda ya dace game da sa rana da sauran shirye shirye"

Kankance idanu yayi "Alhaji zanyi aure fa ku dena damuwa. Akwai information da nake jira akan yarinyar ku zan fara sanarwa idan magana ta kankama"

"Babawo wallahi zanci mutumcinka akan maganar Qareeba. Kai wane irin yaro ne mara jin magana? Dole ne sai yadda kake so za'ayi?" Ta taso tayi kansa kamar ta mare shi sai ta kasa. Yanzu fa makotansu ma kowa zancen BB yake ana cewa yaje turai ya zama dan iska. Kitson kansa yafi komai kona mata rai.

"Wai da marina zakiyi. Hahahahhh abin dariya"

Hanyar dakinsa yayi ta dafe kirjinta da hannu daya ta rike kujera.

Alh Sule ya taso yazo gabanta "Marakisiyya duk wanda yace gyara kayanka ba yana nufin sauke mu raba bane. Ni da dana

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

10 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment