Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da aka daure ta
murza sosai, koda batada nauyi saida ramcy ta
saki wata qara Dan azabar da taji, ya kalleta irin
kallon nan nata na wulaqanci, idan mijin naki ya
dawo kice ya kasheni, ta koma lanbu abinta.
Farhaan ya dawo ya tararda ramcy a qasa tana
kuka ya tambayeta tace ba komai gida kawai
takeson ya maidata tana tsoron ta fada yaqara
daku iffaat idan yafita ta kasheta haka ya maida
ramcy gida....
su iffaat sarkin gaba tun daga ranar bata qara
yiwa farhan maganaba ta daina aikin da takeyi,
burinta kawai a maidata gida, amma ina ba hali,
Ranar tana zaune a sabon dakinta wato lambu
cox yanxu kullum tana gun dare da rana ko tsoro
bataji, dama tsoro bashida muhalli a zuciyar
iffaat tana zaune ta hango wata qofa, koda taje
ta daga an sa sakata an kulle ta bude sakatar
tana budewa qofa ta wangale saiga ta taganta
waje,....
[10:15PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 18
Na Hauwa M. Jabo
Dama an hana mai gadi ya barta ta fita, itama
an hanata zuwa gurinsa ba gunda take zuwa
daga aiki sai aiki...
Sai yau cikin ikon Allah gata waje, Ta kalli gidan
da tafito kallon sosai, gidane na gani na fada,
kusan duk unguwar ba gidan dayakaishi tsari da
girma, tayi yan kalle kallenta, ta samu guri ta
zauna anan taga yan mata nakai da komowa ko
wacce kayan jikinta abin kallone fuska duk fenti
ta kalli yanda suke tafiya kamar basason taqa
qasa, aranta tace lallai birni birnine bata taba
ganin yan birniba saiyau. Amma ita iya sanin ta
karuwai ne basa yawo da gyale, amma taga
wayannan manya dasu amma basa saka gyale
kodai karuwanne?, haka dai aranta tayi ta saqe
saqe har guraren yamma sannan ta koma cikin
gida.!
Tana shiga taga farhaan da wata mata, aranta
tace matansa uku kenan, lallai suna qoqari,
Bata takansuba dama bayi tazo, wucesu tayi ta
fita abin ta bawanda ta ko kalla balls gaisuwa,
budurwar ta kalli farhaan waye wannan?? Yace
watace,! to WACE CE ITA?? Mai aikice, amma
batada ladabi shine kota gaida mutane, look
hafsa! ba ruwanki da masu aikiin gidan mu
please, ke kullum kikaxo sai kin kawo Qatar
masu aiki haba, Bawai komai bane illah bayason
rigimar iffaat yanxu sai ta zubar mai da
mutunci, ya qara da cewa kuma ma kurmace
bata iya magana Dan ki fita hanyarta, tace Allah
sarki,
Yaja budurwarsa ya wuce daki da ita, kwanan
hafsa biyu a gidan. ranar iffat ta dawo daga
kallon mutanen unguwa da takeyi da yake tun
lokacin ta daina mai magana tadaina yini gida
hatta aikin ta dainayi, ta fado ba sallama, sai
hafsa ta kalleta a yamutse ke Dan kina kurma
baki iya ishara da hannuba Ko uyayenki basu
koya miki gaisuwa bane? Kai Allah wadaran
halinki, ran iffaat ya baci amma guduwarta data
korota tafi mata tsayawa masifa Ta kalleta
kawai ta mata tsaki ta wuce bayi abinta, Dan
abinda takeji ya matseta!! ta qare ta fito tana
waqarta ta badi ba rai soyayyah jigon
rayuwa......., nan ma hafsa ta qara magana,
wallahi sai na sa farhaan ya koreki duk masu
aikin gidannan suna gaisheni amma bandake
Mara kunya kawai, waike kurmako?? da ganin
idonki nasan ba kurma kikeba iskancini kawai
kurmace ke waqa .dama farhaaan duk masu
aikin da yake mafi yawa yan matanshi suke sa
yana korarsu, wasu kuma baqin halinsu kesa ya
koresu, iffaat har zata tankata nan ma sai ta
mata kallon banxa tayi tsaki ta wuce abinta.
hafsa kamar an tsikareta dama idan kayi masifa
akayi banza dakai yafi haushi, ta janyo iffaat ta
wanketa da mari....
[10:22PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 19
Na Hauwa M. Jabo
Habawa!! iffaat bata dubu girmar matarba Dan
kobata kaiba zata kai 25yrs ita kuwa yanxu take
Shiga14, itama ta wanketa da wawan mari
daidai shigowar farhaan, kee iffaat lafiyanki?
hafsa ta riqe kumatu tana mamaki, yau yar aiki
take dukanta, tasan tafi qarfinta Dan ubanta
mashhurin mai kudine itama kawai tanason
farhaan ne take biyoshi har gida amma tafi
qarfinsa, yana zuwa daidai ita hasale a ya
wanketa da mari biyu masu kyau saida ta fadi,
ya nunata da yatsa, ina Dada jaddadamiki ke ba
kowa bace illa mai aikina kuma bazan maidaki
gidankuba anan zaki ci gaba da zama, kinamin
bauta, idan kikayi ba daidaiba am always ready
na babbalaki,dama sabida umma nake raga miki
so naga ba amfanin haka, qara in nuna miki ni
waye, stupid girl kawai ya, rungume hafsa yana
bata haquri, hafsa ranta yayi fari Sol Dan yayi
hukuncin da ya mata dadi, ta kuwa narke a
jikinsa farhaan mai farin jinin yan mata.
Ta miqe tsaye taja ta toge ta rasa abinda zatayi
ta rage haushi kuma ta bashi haushi ya
sallameta amma ina kwakwalwanta baya aiki ko
kadan hasalima tausayinsa takeji,
***
Tafita daga gidan taje waje kallon yan mata,
wata yarinya da take yawan gani tana wucewa
yarinyar ta shiga ranta har takeji ina mazata yi
qawance da ita, wata zuciyar tace a haka zatayi
qawance dake kina duqun duqun, ta kalli jikinta
ta tuna tafi wata daya a gidannan amma duka
wankanta uku, kamar yan makarantar su jabo
basa wanka daga frdy sai frdy..
Ta kalli kanta aranta ta fara imagine irin
gasunan tare da yarinyar suna driving a mota
Habawa ta gyalgyale da dariya hadda buga qafa
a qasa, har ta manta da an mammareta ita
kadai kamar zararriya, lallai idan har tayi
qawance da yarinyar chan Yar baqa ta qare
qawance a duniya, tana nan zaune taji kamar
maganar farhaan saida hanjin cikinta suka juya
dan kuwa shine, lallai kamin ta ruga ta shiga
gida zai iya hangota, kamar monkey dinda ya
kirata haka ta Dane bishiyar da take zaune
gurinta farhaan yazo daidai bishiyar ya zatsa
yana danna waya.....
[10:29PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 20
Na Hauwa M. Jabo
Yaci gaba da wayansa saida ya qare kamar zai
daga kai ya ganta amma hankalinsa na gun
budurwar da yake tsarawa a waya, bata gane mi
yake cewaba Dan da English yake magana, ya
wuce kamar da second 30 ta sauko ta shiga
gidan da sauri ta kulle qofar lanbu taje gurin
zamanta tana addu'a da Allah yasa bai gantaba,
idan ya ganta tunda yace bazai maidata gidaba
ya zatayi, zai kulle qofarne ya hanata fita ko ina
gashi tanason tayi qawance da yar baqar
yarinyar da take gani tana wucewa. Tana nan
zaune Tana Zane a qasa ya kwala mata kira taje
ta turbude fuska, yace taje hafsa na kiranta,
batamai musuba ta wuce shima yayi mamaki
sosai yanda ya wasketa da mari batace
komaiba, aransa yace kodai ya fara nasarar
natsar da itane, hafsa a Palo zaune, wai ta dan
qasa mata qafafuwanta da ruwan xafi, ( inaga ta
kusa fara period ne coz yan chinar skull dinmu
haka sukeyi kuma zakiga sun Dan sami sauqin
ciwon cikin) na watsa mata harara, banganeba,
tamin bayani shiko gogan yana tsaye ya
rungume hannuwansa, nikaina jabo nayi
mamakin iffaat data amince da aikin, ta zauna ta
riqa juya ruwan turinisu suna dukan qasar qafar
hafsa har suka huce ta zubar ta dauko wasu ta
mata daqowar da hafsa zataye ta hanbare iffaat
ta fadi xaune ruwan suka zube a jikinta duk ta
jiqe amma ruwan ba wani zafi sosai, farhaan ya
kallesu baice musu komai ba, yaci gaba da
kallon ball dinsa, karo na uku ta dauko ruwan
zafin da gangan iffaat ta juye matasu a qafafu,
hafsa ta tsallara ihu, iffaat ta miqe tsaye da qarfi
tayi gefe farhaan yazo da sauri yana duba qafar
ba abinda tayi a Zahiri amma tana zugi daga ciki
iffaat tayi tsaye tana jiran hukuncin da farhaan
zai yanke mata da sauri ya kira Dr. hafsa sai
aikin kukatakeyi, yana rungume da ita tanata
ihun, yace iffaahh. Ta watsomai idonta da gani
tadan tsorata ya akayi haka?? Ta fuske kamar
da gaske, naje zan juye ruwan sai kawai tasa
qafa zata shureni saita shure ruwan suka juye
mata a qafa, harga Allah ya yarda cox yaga
yanda ta shureta karo na farko, ya jinjina kai,
duk da baiji dadiba amma yasan iffaat batada
laifi,......
Dr yazo ya dubata ya bata
magunguna, tace zata koma gida kada yar
aikinsa ta kasheta, baiji dadiba cox duk cikin yan
matanshi hafsace kawai take iya jure jarabarshi,
cox ita sonshi takeyi so duk wahalan da zai bata
tana jurewa sauran kuma, kudi kawai sukeso,
Yakaita gida, ya dawo bai kula iffaat ba ya wuce
dakinsa sai yanxu ya kula dakin yayi kacha
kacha ya kwala mata kira, ke zaman me kike a
gidannan?? Kalli dakina kalli toilet dina! Miye
amfanin kine??
[10:33PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 21
Na Hauwa M. Jabo
Dole kiyi aikinda aka kawoki kiyi idan har
kinason amaidaki gida, so zabi ya rage naki, ko
kiyi aiki a maidaki gida ko kuma kiyi ta zama
anan har qarshen rayuwarki. taga gara tayi
aikin ya maidata gida.
***********************
Yau watan iffaat biyar a gidansu farhaan inda
sabo yaci ace ya saba da halinta ya kawo
budurensa daidai har 8 suna chin uban juna Ita
dasu, kuma ko wacce sai tayi nasarar daukar
fansar abinda suka mata ta hanya kala kala,
kuma farhaaah Sam baya ganewa, ita
Har yau ta kasa gane cewa ba matansa bane
matan banxa ne da taga sunfi hudu sai kawai
aranta tace auri saki yakeyi, irin na wani alhajin
qauyensu da akace auri saki yakeyi, kullum
sukaje Gidansa kallon TV sai suga sabuwar mata
a gidan akace auri saki yakeyi, anan ta gane
halinsu daya da farhaan...
*********
Yau dai iffaat an tashi ba lafiya zazzabi yake
damunta da wani gwauron ciwon ciki, har bacci
ya dauketa tsakar bacci ciwon ya tayar da ita
taji danshi danshi a qasanta dubanwa da zatayi
sai taga jini Habawa ta fashe da kuka koda ta
tashi ya mata kache kace a jiki Ashe ya Dade da
zuwa bata kulaba, tayi Sa'a farhaan yana palo
yana kallon ball ta fito a hargitse tana kuka, ta
nuna mai jininta fa na xuba, ya kalleta habo
kikeyi? aah ta gun fitsarinane, kunya ta
kamashi, shi wace irin yarinyace umma ta sashi
dole zama da ita wai mai aiki gashi ta zame mai
jaraba, yayi tsaki yana kall ball dinsa za'a
katseshi, to kije daki zan siyo miki magani
yanzu, yama Dr waya akawo mai pad da
maganin ciwon cikin na mata bada jimawa ba Dr
ya kawo mai, ya kirata amma ba amsa ya gaji
yayi banxa da ita, sai da ya qare kallon ball
dinsa ya miqe tsaye sai maganin ya fadi sannan
ya tuna da wata iffaat ba lafiya yaje dakinta da
yake yana mura baiji qarnin da dakin yakeyiba,
koda yajee ya ganta ta dunqule a qasa sai juyi
takeyi, duk jikinta ya baci, ya rasa yanda zaiyi
idan ya dauketa zata bata mai jiki ya waya da
Dr waya shiru bai daukaba, ya tsaya gabanta
ganin numfashinta na hawa da sauka kamar
zata mutu yaji tsoron tamutu a gida da zamo
mai aiki, yaqara yima Dr. dinsu waya yace mai
normal ne na farkone ya bata maganin da ya
kawo zata warke kada ya damu, ya dagata
chak ya yakaita bayinsa ya wanke mata jiki ya
rasa yanda zai chire mata tufafi tunda duk sun
jiqe yaje dakinta ba kayan da zai saka mata duk
saman gadonta suke kuma duk ta batasu da jini,
yaje dakin farahnax qanwarshi ya memo wata
jallabiya baqa yazo ya rufe idonsa Dan kada ya
ganta ya chanxa mata kayan jikinta ya....
[10:38PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 22
Na Hauwa M. Jabo
Ya bata magani dagyar tasha ta amaryar ya
qara bata wani, yace ta daure ta saka wannan
abin pad tace bata iyaba, ya kalli bayan ledar
yaga yanda ake sakawa ya hada mata ya bata
ta saka, pant ma a kayan farahnax ya daukoshi,
yace ta kwanta dakinsa dakinta ya harqitse
tunda batada lafiya, tanashan magani tuni tayi
bacci,
Bata farkaba sai bayan la'asar tafito Palo tana
dingishi zata tafi dakinsa ya kirata zonan, ya
jikin ta amsa a kasalance, naji sauqi da gani
hajiya iffaat anji jiki Dan har idonta sun fada, tayi
wani iri da ita, ya kir Dr. ya miqa mata waya Dr
ya mata bayanin yanda xatayi komai kuma kada
ta damu duk mace mai lafiya tana wannan abin
sabida haka ta godewa Allah ya fada mata zata
iyayin kwana bakwai tana xubarwa, likita jinina
bazai qareba?? No wannan ba jini bane ciwone
yake fita idan bai fitaba idan kinyi Aure bazaki
haihuba ko bakyason haihuwa?? inaso mana,
him wayaga iffaat da ciki, yadai mata bayanin
komai sukayi sallama, ta bashi wayarsa, ta wuce
daki koda taje duk an tattara kayanta gabi daya
da zanin gado duk babu, an saka wani, sai
yanzu ta tuna yanda tayi kacha kacha da ko
ina...
Iffaat saida tayi kwana biyar sannan ta
kammala, farhaan ne yasa aka kai mata kayanta
wanki.
Wannan ciwon shine mafarin fara shirin iffaat da
farhaaah..
Tunda ta fara ciwo sai yau ta fita waje kamar
yanda ta saba, tana zaune sai ga black girl
dinnan ta wuce qamshinta ya doki hanchinta
aranta tace anyi yar gayu anan gurin, ta qare
kalle kallenta ta shiga cikin gida bayan ta koma
gida tana dakinta zaune tunaninta daya ya zata
zama yar gayu irin na yar baqar yarinyar nan,
taje bayi ta kalli madubi, sosai ta bude
haqoranta taga yanda sukayi laka laka a qasa ga
wata tsatsa da sukayi tofa bata wankewa fiye da
haka ma sai tayi, batasan yanda zatayi dasuba
suyi haske irin na tsohuwar matar farhaan
ramcyba, cox ramcy akwai wushirya kuma da
fararen haqora Tass dasu, tayi tsaki ta qara
gaba...
Ranar ta fito Palo, karo na farko da ta taba
tsayawa kallon TV tunda tazo gidan nan sabida
farhaan kullum ball yake kallo itako batason ball
a rayuwarta, tafison indiya an qare ball ne Anje
talla sai kawai ga tallar signal, mouth Clean ne
mai kyau, taga yanda ake wanke baki sai ta tuna
ta tabaa ganin farhaan yana wankewa har ta
tsaya kallonsa, taje bayin dakin ta nemi mouth
clean din koda ta duba sai taga exactly irin
Wanda aka nuna a TV ne, tayi murmushi Ashe
haqoranta zasuyi fari irin na matar Tv ta Dan
barashi a brush tana wankewa yana jini duk da
ya mata xafi ta daure cox tanason ta zama yar
gayu irin na yar baqa sunanda ta sanyawa
yarinyar kenan, iffaat dai haka tajuri yi brush
kullum ko nace duk lokacin da abin ya motsa sai
tayi cox.......
[10:45PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 23
Na Hauwa M. Jabo
Cox a rana sai tayi brush Sau biyar ba'ayi
kwana sati day ba suka fara cire wannan lakar,
kuma tsatsar ta fara bacewa,
Ranar tana zaune tana charafke sai ga farhaan,
dama bata gaidashi idan yazo ya zauna yace
yau kuma TV ake kallo da charafke, ta juyo ta
kalleshi tayi dariya, tace eh so nake in zama yar
gayu irin na matan Tv ya kalleta sosai sai yau
ya kula tana da wushirya,idan ba idonsa suke
masa gixo ba yaga haqoranta sun cire wannan
laka lakar na da,.
Yace gashi kuwa su Umma zasu dawo anan
zasuyi azumi, Dan murna batasan lokacinda ta
tashi tsayeba Ashe nayi kusa tafiya gida,? Naga
su dije da rukayya da goggo, tanata dariya, lallai
gaskiya ya hango, haqoranta sunyi haske, kinga
idan kin tafi kin huta dani ko, ta kyalktale da
dariya saida kumatunta ya lotsa, ai zama da
mugu irinka sai An shirya kamaci arzikin ina
tausayinka, shi yasa duk matanka suke guduwa
duk matar daka aura sai ta gudu, kalli fa cikin
wata biyar saida kayi Aure 8 lallai yarinyar nan
batada wayo,! ita ta dauka duk matanane kena,
hahaha nine mugu iffaat?? babba ma kuwa. Ta
fada ba tareda shakkar komaiba bakya kunyar
fadamin haka a gabana? lallai kin girma, ta
kalleshi ta tabe baki, ai gaskiya na fada, nima
yanzu zan shirya suna dawowa sai in tafi
gidako? Taci gaba to yanxu kai zaka mini
dunkin sallah ko hajiya??
Yagyara zama ni xan miki ai ni kike yiwa aiki ko?
Eh Kaine maigiana, ta juyo tana fuskantarshi
kasan wani abu,?? Saikin fada, naga aminar
baba sule idan ta dawo aikibirnib sai ta dawo da
kayan gayu, tufafi sabbi qanzon shinkafa sabulai,
abubuwa dai da yawa na birni, ni ina zan
samu?? yayi murmushi dama tanada surutu
haka? Yace kema da kina min aiki da kyau da
duk zan siya miki abubuwan da kika lissafa
hadda qari ma zan miki, amma ke bayan tsiwa
da rashin kunya da zubar min da mutunci ba
abinda kika iya LA ilaha illallahu, yanzu duk
aikinda na maka haka zakace? kallifa baka taba
dukana na ramaba, au da ramawa kikeyi?
Taaaab wallahi a qauyen mu komi girman qato
idan ya dakemu sai mun rama, kai hadda
shugaban yan sandan garinmu ya dakemu
mukaje gidan sa da dare muka fasa mai mota,
ya fito da I do da gaske kikeye??
Ta qara gyalgyalewa da dariya sai tamai kyau,
wallahi da gaske nakeyi, kicemi ke yar
ta'addace...!
[11:13PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 24
Na Hauwa M. Jabo
Nan ma dariya tayi ai baka sannibane, ta fara
bashi labarin ta'addancin da takeyi a qauye, ya
jinjina mata sosai kuma ta bala'en burgeshi Dan
yanason yaga mace mai kamar maza, anan ya
gane duk abinda yan matansa suke fada akanta
gaskiya ne,
Abinda yaxo mishi gona hafsa da tayi da ruwan
zafi yace Kena da gangan kika xubawa hafsa
ruwan zafi? Ta kalleshi ta kanne mai ido ai
muguwace, kuma ita tafara xubamin ruwan kana
kallo bakace komaiba, sannan akanta kamin
mari biyu ita ma tamin daya shiyasa duk cikin
matanka nafi tsanarta, kuma da gangan na zuba
mata ruwan,? Ke yanxu data qonefa??
Aaaaaaaa miya dameni badai na rama ba!! Ya
kalleta da kyau yarinyace sosai kuma lallai
batada wayo ko kadan ga shegen surutu...
To yanxu dai ki riqa aiki da kyau zan siya miki
duk abinda kikace waccan qawar taki tana tafiya
dashi qauye idan zaki tafi gida, yatashi ya wuce
dakinsa, yabarta tanata zuba, aranshi yace lallai
da yana kula yarinyar nan da ta debe mishi
kewar qanwarshi farahnax Dan ya kula akwaita
da shegen surutu ga saurin sabo saidai sabon
baya hana tama mutum rashin kirki Dan yaji
yanda take danbe da qawarta dijeee !!!
Kamar kullum bayan fitar farhaan taje S pool tayi
wanka da yake shi yake debe mata kewar kogin
garinsu, tayi wanka abinta ta qare tabi ta lanbu
taci abinda xataci ta fita doguwar rigar da
farhaan ya bata lokacinda batada lafiya ta saka
sai ta mata kyau sosai, tana zaune tana wasa
da qasa sai ga yar baqarta tazo tayi kwalliya
baqinta sai kyalli yake tayi kyau tsab tsab da ita
da takalminta masu tsokane duniya, ba abinda
yake burgeta irin yanda take wani Dan tuntu
saman kanta ( acucu maza take nufi) yana
burgeta matuqa amma batasan yanda
zatayishiba ta qare zamanta, ta koma gida da
tunanin yanda zatayi wannan abin na saman kan
yar baqarta, tayi tunanin Idan ma gashintane
zaiyi irin na Yar baqa, tinda gashinta yanada
tsawo sosai tunda tazo gidan da kitso bata
tsefeshiba.
[11:23PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 25
Na Hauwa M. Jabo
Tashiga dakinta ta zauna ta tsefe amma saida
tayi kuka dan zafi kuma gashi ba kibiya duk ya
harhade ko gida kullum sai tayi kuka idan ana
mata tsifa, yauma saida tayi taje ta wanke da
man da taga anyi hoton qashi jiki haka datti ta
riqa zuba kamar an kwaba qasa, haka tayi ta
xubarda daddi har yayi fess dashi kamar bana
iffaat ba, matsalar daya ba tada mataji kuma ba
tasan yanda zatayi irin na yar baqaba, sai ta fito
Palo tana goge gashin farhaan ya kalli gashinta
aransa dama tanada gashi haka, ya zauna yace
dama kinada gashi shine baki kyarawa, tace
wallahi parhuun zafi yake min.! Ya kalleta tanata
kiciniya da gashi yace ya sunana? Tace Parhuun
mana haka naji kowa yana fada, ya kwashe da
dariya saida yayi kwalla wai PURHUUN yarinya
katki bata min suna sai nanatawa yake
PURHUUN lallai wato kusan shima bata iyaba
gaskiya anyi baqauya anan yace to ba haka
bane farhaan ne, ta dago kai tace Parhan, yace
aah farhaan, parha, ke kalli bakina, kice far, tace,
par, kalli ki haqoranki akan lebenki zaki Dora sai
kice far, takuwa yi tace far yayi dariya yauwa
kinyi daidai, sunana farhaan,ta fada daidai tace
Dan gayu ko sunan ka sai ka koyamin. Ta bashi
dariya wai Dan gayu, so funny, tace to yanxu
gayamin yanda ake wannan abin a saman kai
yayi sama sosai, yace ni ban iyabafa banmasan
mi kike nufina, LA ilaha illallahu, ta to saki
gashin ta toshe baki babba na qarya, wallahi ko
wasu a matanka kamin ka sakesu nagansu dashi
kace baka sanshiba, yayi dariya lallai yarinyar
nan case ce, ni nake qarya?? Waima waya gaya
miki matanane?? Ta zunburo ta kama gashinta
ita burinta a mata irin na yar baqa ta hanya,tace
to miye naka? Abokainane ko ban fada miki
inada abokai mataba, ta saki gashin kanta ta
qara rufe baki da hannu, shine kake tabasu?
Hmmm!! Ta tabe baki Mudai garinmu duk namiji
mai taba mata Dan iskane, ko wasa bamayi da
maza duk iskancine garinmu, kaga da garinmu
kake da nace maka Dan iska, keeeee, nine dan
iska,?? ta zaro ido ai ban fadaba. nace da garin
mu kake.. aranshi yace ko inane wannan
iskancine, yace to a birni wayewace ba
iskancineba, ya fuske ya miqe zai fita, baka
gayamin yanda akeyiba, sai na dawo zan gaya
miki...
A hanyarshi ta dawowa yayi karo da wata tayi
acucu maza sai ya tuna da alqawarin da yayi,ya
siyo mata ribbon manya da mataji da man kai
ya kawo mata.. Tanatajin dadi zata yi irin na Yar
baqa, ba'anan kizo ke saqarba bata iya
sakawaba ta kuwa fara hadashi da Allah, ya
koya mata shi ba iyawa yayiba, yana mamakin
yanda take mai kamar wani sa'arta yanaga ta
mance WACE CE ITA.!! Yayi tsaki ke kada ki
dameni kinji, na siyo miki kuma ni zan saka
miki? duk ma yan matanshi basuda gashi irin
nata duk qarine sukeyi, ya zauna yaci gaba da
kallon ball dinsa, dama iffaat akwai naci akan
abinda takeso. tazo tana hadashi da Allah tana
mai shagwaba abin ya burgeshi.. Yayi tsaki
aranshi yace yarinyar ta fara rainani, ta kuwa
miqamai gashi ta zauna ya rasa yanda zaiyi to
ki taje mana ta fara tajewa tana gwalla Dan duk
ya sarqe tanayi yana shafa mata mai har ya
taju yayi kyau gashin yana gyalli abinka da
gashin fulwni sai Wanda ya gani,ya karbi gashin
ya kasa tattarshi yace ta tattara da kanta ya
nuna mata yanda zatayi ta tattara, to aike basai
kin saka irin nasuba tunda gashinki yana da
tsayi sosai, Allah ko? eh mana, haka ya
taimaka mata tayi parking dinsa kuma yayi irin
yanda take so, yanxu kasan mi nakeso? Yace
Aah, akwai wasu kaya da ake sakawa sai ayi
wannan abin sai ayi kyau a zama yan gayu idan
xantafi gida zaka siyomin? nama taba ganin
abokiyarka da irin su! Ke ni ban ganesuba, kuma
ki sani duk suna cikin kayan sallanki, eh na
yaddda ta amsa tana zagwadii....
[11:30PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 26
Na Hauwa M.Jabo
Bayan ya dawo, ita duk wautarta yau zai siyo
mata kayan taga wayam hannunsa ba komai,
laaa farhaaah Yaushe zaka siyomin kayan
gayuna? irin na abokanka,? Ya harereta bakida
kunyako kina kiran sunana. Ko bangirmekiba. yi
haquri Mixance makato? ta fada irin ta matsu
dinnan taji zancen kayan gayu, look ki bari zan
siyo miki kawai kamin ki tafi gida, yayi niyar yaje
da ita a aunata gun mai dinki amma ina yana
tsoron ta kwafsa mai wannan hargitsatsaiyar
wataqilama taje ta nemo magana, to kawai tace
mai amma ranta baiyi dadiba ta wuce daki ta
zauna, ta fara tunaninta na zama gayu irin na
Yar baqa iffaat yanxu batada buri irin taga ta
zama Yar gayu, Niko inason ganin iffaat da gayu,
aranta tace gayufa dole saida wanka, taaaab
yanxu kullum sai tayi wanka kenan.?? idan ba
wanka ba gayu, ta tashi ranar farko data ji tayi
wanka Dan ra'ayin kanta, ta fada wanka tayi
wanka da ruwan zafi ta wanke dattin
wafafuwanta sabida bata yawo da takalmi ko
lanmu haka take tafiya ba takalmi tana wankewa
ta tuna da qafafun hafsa lokacinda tasata gashi,
sumul sumul qafar yan gayu ba kaushi, ta
wanke iya yanda zata iya, ta fito ta saka yan
tsumma karonta.. Tayi bacci anan tayi mafarkin
ta zama Yar gayu, tayi qawance da Yar baqarta,
ta farka ta fito Palo cin abinci bata dadeba sai
gashi ya kawo mata kaya English Wear ne, ya
nuna mata wayannan kayan kike nufi?? Sauran
nakai dinki duk na sallah ne amma, Ta kallesu a
tsorace ita a qauyensu idan mace ta saka wando
za'ace mata yar iskane so bazata sakaba, data
fada mai yayi dariya sosai wato qauye bala'ee
ne, qauyanci masifa, yace ki riqa saka wannan a
gida idan zaki fita saiki saka wayanda bana yan
iskaba. OK bari in saka ka gani, anan yaga zata
cire kayan jikinta no ki shiga daga ciki mana, ta
kwashi kayan ta shiga daki da gudu ta saka
wandon yafito da ita ainihin ita sai Wanda ya
gani mazaunan suka fito hips din ma ya fito, da
yake dukiyar fulanin yanxu take fitowa yayi dan
tudu kadan sai head dinsa ake gani ya fito
saman rigar, ta fito da gudu tana dariya na fara
xama yar gayuko? farhaaah ya kalleta tashin
hankali, Ashe babyn nan ta hadu a ransa ya
fada, dukda cewa ba daidai ta saka kayan ba
amma sun mata kyau, kalli nayi kyau, sosai kin
ganki kuwa, tace kamar ba yar aikiba ko, yace
sosai kuwa, tana ta dariya ta janyo gashinta da
yake ta cire riboon garin saka tufafi wai dole sai
yayi mata yanda akeyi dinnan, no ki bari in miki
hoton tarihi kuma na turawa umma taga
yarinyarta ta fara zama gayu, nan ya sa tayi
wannan tayi wannan idan tayi wani style sai
yakai zauna Dan dariya, qarshe yace to tazo ya
dauketa ita dashi ba tare da damuwaba ta
kwanta a qirjinsa ya daukesu photo tana dariya
duka dimple dinta sun lotsa gwanin ban sh'awa,
kawai daga kan da zasuyi sukaga hafsa kamar
daga sama, ta kalli kayan jikin iffaat ta watsa
mata harara, ta riqe kunkumi wai farhan na
tambayeka waye wannan yarinyar?? kawai fada
min gaskiya, ya kalleta kallon bangane mi kike
nufiba, sau nawa ina fata miki WACE CE ITA!
Amma kina min magana wai iri, hafsa ranta ya
gama baci iffaat kuwa dama batayi ta kantaba,
murnar kayanta takeyi batama gane hafsarba
yana juyowa tace Yaya farhaaah yaushe zaka
kawo min kayan sallah? Ya kalleta ita ba abinda
ya dameta sai su umma sun dawo,
Kamin ya juyo hafsa ta fita Yabi bayan hafsa,
itakam ta dauki kayanta ta je dakinta,
Kamin ta tada mota yasha gabanta yace mai
gadi ya kulle gate, hafsa kuwa anriga anyi fushi,
ya bude motar ya janyota jikinsa, ya rungumeta
yana shafata a hankali, miye na fushi, hafsa??
Ni kawai ka fada min WACE CE ITA please!!
[11:45PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 27
Na Hauwa M. Jabo
Wallahi na gaya miki WACE CE ITA, ba kowa
bace illa house girl dina, house girl take saka
English Wear??

Please Login or Register in order to submit comment