Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bata mata rai
a skull sai ta sauke akaina, maman Suhaila tayi
dariya tace kice iffatun dai har yanxu hukumace
kenan suka dara gabaki dayansu...
*****
Ranar iffaat tana zaune gindin bishiya a
makaranta tana shan malt da snack sai taji
wasu yan mata suna tadi akan soyayya ta kuwa
kashe kunne, dayar take bada labarin cewa
tanason yaron qanin baban ta amma batasan
yanda zata bullowa abinba tana bayanin duk
abinda takeji a ranta game dashi dayar ma tana
fadar nata keni Zumar abinda yafi bani haushi
baimasan inayi, Zibraheeem tace kar kuwa
kisake ya sani Dan raini ne zai shiga tsakaninku.
Iffat sai taji d same da abin da takeji suma shi
sukeji, ta juyo ta kallesu sun girmeta duka ta
musu sallama, please tambaya ce dani, naji kuna
wata magana, yanxu kuna nufin duk maijin
wayannan abubawan da kuka fada shine me,??
dayar tace its mean ya fada tarkon soyayya!! ta
kallesu, kuna nufin nima na fadane? Toni wa
nakeso?? Suka kalli juna suka kwashe da dariya,
mu muka San Wanda kikeso, dayar tace Wanda
kikejin haka
akanshi shi kikeso!!
Ta zare Ido kuna nufin YAYA FARHAAAH
NAKESO??
suka kalleta sukayi tsaki ke baquwace yarinya
dayar tayi dariya tace kinji suna mai dadi daji
gayen zai hadu, daji akwai zafi a gunsa har naji
inasonsa !! Iffaat ta juyo a fusace keeee ta
wanketa da mari.....
[11:28PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??47
Na Hauwa M. Jabo
Yan matan gaba daya suka miqe tsaye, dayar ta
gefe ta kwasheta da mari itama dayar taci
kwalarta suka mata lilis,duk sun buge mata
fuska, suna tsaka da dukanta saiga baba sajeen
yana kora kamin yazo sun gudu bai tsaya duba
halinda iffaat take cikiba kawai yaganta kamar
tsugune yahau zuba mata bulala tun tana kuka
har tayi shiru. Ke wace irin mai taurin kaice?
Maza ki tashi ki wuce class bai tsaya kulataba
ya hango wasu yara biyu ya bisu a guje suka
tsere, iffaat dai an mata lilis baki sai jini yake
yaji duka gun yan mata gashi baba sajeen ya
qara mata wani, tana nan gurin taji ana cewa
still tanananfa, kixo mu dubata, nidai baxanjeba
ke kije , habadai sabida kefa na daketa kuma
kice bazakijeba, please kixo muje, sukazo gurin
iffaat sai kuka ganta tana xubar da jinin baki da
hanci duk hijabinta ya lalace, nidai jabo abin har
mamaki ya bani wai iffaat ce take daukar xilla
yau!! Rayuwa juyi juyi....!!!
Suka dagota suka tallabota hannu biyu dayar ta
ruga ta siyo pure water Leda daya sukaxo iffaat
bata iya koda magana, suka wanke mata jikinta
suka qaro ruwa suka wanke mata hijabinta da
duk gun da jini ya bata, dayar take gulma a
hankali tace kalli gashinta! Dayar tace ummm
nagani, suka kalli iffaat wacce ta bige mata
bakince ta fara bata haquri, sai dayar ma tac ci
gaba da bata haquri batace dasu komai ba,
hasali ita batajin zafin dukanda aka mata illa
xafin Cewar da akayi Yy farhaaan takeso.!
Sunata bata haquri ita kuwa tanata tunaninta.!
Wai yaza'ayi taso saurayin yayaryta?
Yaza'ayi taso Wanda nake kallo a matsayin
yayantaa?
Lokaci daya ta tuna da rashin kamun kansa
shegen Neman mata, ta tuna duk wani iskanci
nata yasanshi, shine yafi kowa sanin WACE CE
ITA, har abada baxai karbi soyayyar taba, idan
ma zai karba yazatayi da yayarta Suhaila, anya
ma gaskiya suka gaya mata da sukace sonshi
takeyi,???
[11:32PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 48
Na Hauwa M. Jabo
Tayi ajiyar xuciya Ta juyo ta kallesu sunyi cirko
cirko dasu, da kunburarren bakinta take musu
magana, kiyi haquri Dan Allah wallahi bansan
lokacinda na daki qawarkiba, sukace ba komai
kema kiyi haquri, nan dai suka yafi juna suka
qulla qawance da ita da alqawarin zasu
taimakamata da duk abinda sukasan zasu iya.
Haka suka zauna Kowa shiru har aka tashi
makaranta..
***
iffaat na zuwa gida mama ta fara tambayar ta
lafiya kike kunbura haka kamar jabo tayi kuka??
Wallahi mama anyo korane, zasu shiga class tayi
karo da wata frnd dinta sai kuma ta fadi qasa
shine bakinta ya kunbura, Subhanallahi. Kinga
yanda kika kunbura kuwa? Allah ya tsare gaba
ta amsa da amin ta wuce dakinta.
Bayan ta shiga daki ta cire uniform, ta zauna ta
fara tunanin abinda yan matannan suka fada
tabbas kuwa idan har abinda suka fada shine
kaji kanason mutum to wallahi tanason Yaya
farhaaan, aiki jaa wanda zai zama mijin yayarta
takeso??
Dole ta dauki mataki wa zuciyarta.! Tayi
murmushi Kai amma so shegene shine ya hanata
sukuni shekara da shekaru! Amma so ya
wanketa! Waima miyasa bata ganeba? Tayi tsaki
ni ko zan mutu zan auri Yy farhaan ne gashi da
shegen son mata! Duk maganar da takeyi aranta
takeyinta amma Sam zuciyarta bata aminta da
ko kalma daya tataba, kawai tana fadane amma
tasan yanda takeji da gudu idan yace yana so
zata amince,...
Hmmmm dole zuciya taso Yy farhaan ta saba
dashi, yy farhaan duk inda namiji mai lfy zai
shiga yana shiga haka tayita karanto siffarsa da
maganar sa da tafiyarsa da murmushinsa tana
murmushi, lallai ta yarda tanasonsa but miye
mafita???
Dole ne ta ijiye sonsa taci gaba da danneshi har
Allah ya bata mijinta tayi aure??
Anya zata iya kuwa??
Zaki iya mana dayar zuciyarta ta bata amsa aiki
ja gabanta..
Suhaila ce ta shigo tana waya ta gane da
farhaan take wayar kuma taji yanayinda ta saba
ji amma ta basar.....
[11:37PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 49
Na Hauwa M. Jabo
Ta juyo suka hada ido Subhanallahi sister miya
sameki? Tambayawa kawai tayi batayi tunanin
samun amsa ba, Dan tasan halin mutuniyarta,
cox jiyama da dare ma kamin su kwanta bacci
sun sayar da hali..
Ta miqe zaune Ki bari kawai Yy Suhaila..... ta
bata labarin abinda yanda ta baiwa mama labari,
Eyyah kinji yy farhaan yaba miki sannu Allah ya
kiyaye gaba, sai kuma taji sanyi aranta, nagode
bani mu gaisa, ta karba tana karba ya fara mata
tsiya anya faduwa kikayi ba tsokana kikayiba aka
miki duka?
Tasa dariya. Laaa wallahi aah faduwa nayi, koda
naga yanzu kin natsu kamar bakeba,amma kinfi
kyau da qiriniyafa, tayi dariya sai mu samo miki
miji mu aurar dake kowa ya huta, kar kuma mu
samo ki kashe Dan mutane da rigima, da yake
Suhaila tanajinta itama tayi dariya, Yy Suhaila
karbi wayar ki kinji tsiyar da yy farhaan yake min
ko !?
Ta bata waya chike da nishadi,
Ta shiga bayi ta kalli kanta a madubi taga yanda
ta kunbura kamar rukayyah qawarta ta qauye
Dan haka fuskanta take kamar fulawa ta kwana
ta tashi, tayi wanka ta fito, tanata Jan Suhaila
da hira itadai Suhaila abin mamaki yake bata,
cox tun dawowarta ba ranar da basa saida hali
har ta saba, idan basuyi da safeba tasan kamin
a kwanta sai anyi, dama ita bamai kulawa bace,
haka bata baiwa Abu muhimmanci...!
*********
Tun daga wannan ranar iffaat ta daina fada da
Suhaila idan taga tana wayarta sai ta tashi ta
fice gun mama ko ta danna eir ps dinta tana
sauraro waqoqinta. Ataqaice dai sun daina fada
da juna, bata kula da ita idan tana abinda tasan
zai bata mata rai,
Iffaat itada qawayenta. skull mate dinta zainb
Ibrahim da zainb Umar da ita iffaat Habeeb, da
yake sunan baban farhaan take amfani dashi tun
lokacinda ya sakata makaranta har yanxu.
Zan iya ce muku ZZ sun ninka su dijee iskanci
da rashin kunya kowa yasansu a makarantar
kuma anqi korarsu sai suka hadu da iffaat
Habawa sai abin ya qaru dama iffaat ba bayaba
soyayya ce ta dangwasheta amma yanxu kam ta
gano bakin zaren so bonewa takeyi bata baiwa
abin muhimmanci Sam duk da tana jin zafi cikin
ranta...
[11:43PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 50
Na Hauwa M. Jabo
Suna zaune gindin bishiya sun fito break aka
fara kora ko ajikinsu tadinsu suke yi suna baiwa
iffaat shawara kada ta yarda ta nuna tanason
farhaan harma yanda suke gida daya da wacce
zai aura, daga sama suka ji bulala akansu
Malam tunde ne zibraheem ta tashi ta riqe
bulalarshi, haba sir miyasa kullum sai ka riqa
dukanmu Dan muna kunyar Kane kawai muka
sharewa but gaskiya ya isa haka.!
Ta fuske, ki sakarmin bulala Mara kunya, sai
nayi maganinku a skull dinnan, duk da English
suke zancen nan.
Da hausa zumar tace saidai muyi maganin juna
bayajin hausa so baiji mi sukace ba, yadai
qyalesu ya wuce gaba abinsa, iffaat tace
malamin nan Dan rainin wayo ne, suka kama
hanya ko wacce ta kama hanyar clss dinsu da
yake duk yara sun shiga clss sai su gagararru.
Koda iffaat taje clss malami ya shiga kuma
Malam jocob ne baya wasa ko kadan,economic
master, ta fuske yace from ware? Tace daga
gidanku da hausa ta fada duk clss suka saka
dariya, Habawa yaji haushi ya gane zagin sa
tayi ya fara zuba mata bulala taji zafi tuni tayi
cikin sa tana duka ta kamashi da kokowa clss
ya dau ihu ana buga table, saida sukaci uban
juna kawai ta saki jiki ta fadi wai ita mai aljannu
so aljanun sun tashi, dama su ZZ sun gaya mata
cewa tayi iskancinta idan ta qare ta fadi kawai
ita batasan tayiba,
Kaji iskanci...
Haka dai akasha oga jocob a banxa gashi ta
wawwaskamai mari ta karyamai glass..
Tofa iffaat hatsabibanci ya dawo.
Akaje gun principal tace ita sam batasan tayiba
sharri ake mata, haka a ka rufe case akasha oga
jecon a banxa.
Wata rana suna zaune suna tadinsu kowa ya tafi
class saisu kawai saiga principal ta biyo hanyar
duk yara suna clss amma su suna nan zaune
kamin ta qaraso iffatu tuni ta haye bishiya,
principal taga hawanta amma bata San
kowayeba, iffaat kuwa tayi tsanda a hankali ta
hau rufin classes din kamar mage taje qarshen
rufin ta diro qasa, koda taje class ta tarar
malimi ya shiga yana note ta lallaba ta shiga ba
tare da ya gantaba tayi sauri ta dauko note book
ta fara rubutu.
Tana fara rubutu saiga principal tare da ZZ
akaxo nemanta, malamin mu yace lallai koda ya
shigo ina clss din, students dinda suka ganni
sukace yanxu Na shigo malamin yaji haushi kuna
nufin kunfini ganine ko qarya nakeyi? ya za'ayi
mutum ya shigo clss banganshiba.....
[11:50PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??51
Na Hauwa M.Jabo
Duk sukayi tseet principal taja su ZZ aka Basu
punishment mai tsanani dama ansha kawo
qararsu gaskiya sunji jiki ba kadan ba ga duka
ga uban aikinda aka sakasu, duk sun kamawa
iffaat mutunci sunqi mata magana, aka tashi
suka kama hanyarsu itama tayi banxa dasu.
Gobe sukazo nan ma gaba sukeyi sun shirya
mata sharri da zataci duka amma bata saniba
tazo ta musu magana sukayi banza da ita har ta
juya sai Zumar tace ke banza ce wallahi, jiya
shine kika gudu kika barmu, mufa duk wani
hanyar dojewa mun koya miki amma ke baki
koya mana komaiba kalli Dan Allah jiya yanda
aka lallasamu, ta nuna mata hannunta dayasha
bulaloli.
iffaat tayi dariya son ranta sannan ta Basu
haquri suka fara tambayar ta ya akayi daga
saman bishiya ta wuce clss? Harda baba sajeen
aka saka yahau bishiya amma baki ba labarin ki
tayi dariya sosai lallai bakusan iffaatu Yar
mamaba nan ta Basu details yanda tayi sunata
mamaki lallai wannan yarinyar mayyace, kuma
hartashiga class malamin bai gantaba......
Sun shirya mata sharri ZZ kenan sun hada mata
gadar zare sukace sujee baya, sunje baya kuma
an hana xuwa wajen da yake iffat bata taba
zuwa gurin ba, kuma batasan an hana zuwa
gurinba suka turata sukace suna zuwa, har ta
shiga sai kawai ta hango bishiyar mangoro ya
nuna tayi murmushi haba Ashe dadi suka turota
tasha tuni ta haye bishiya ta fara tsinko mango
tana saman bishiya kawai sai taji maganar su
da wani malami wallahi tananan kullum nan
take zuwa mun gaya mata an hana zuwa tace
ba ruwanta. yanxu ma mungaya mata zamu
fada muku tace sai dai a kasheta, kaji mugayen
qawaye....
Iffaat tanajin haka tayi tsanda daga saman
bishiyar tahau garu ta dira a toilet, ta barsu a
gurin, taje da gudu ta kira principal tace tana
bayi taji maganar mata da maxa a bayan skull
principal taje da sajeen koda akaje aka gansu
duk sun cire hijabi suna Neman ta wai ko ta hau
bishiya coz ta gaya musu ta iya hawa bishiya ko
wace irikuwa.
jikinsu ya fara rawa ganin principal tana zuwa ta
fara yiwa Malaminda yake tare dasu fada mi
yaxo yi da yayan mutane anan bayan an hana
zuwa anan tasa aka tafi da su ZZ office.. iffaat
tayi wata dariya ta musu gwalo aranta tace
wallahi saidai Ku wahala duk case dn dana shiga
a duniya zan iya fitardakaina yanxu ya rage naku
ta kakkabe hunnu ta qara gaba.....
Muje zuwa.
[11:13AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 52
Na Hauwa M.Jabo
Anje dasu office ana tuhumarsu da aikata lalata,
Dan yan iska kawai suke zuwa gurin kuma duk
Wanda aka kama gurin qa'idace korarsa za'ayi
da sukaga lallai korarsu za'ayi suka fara kuka
suka fadi gaskiya principal abin ya bata dariya
tace a kira iffaat aka kirata akace ta fadi gaskiya
ko a hadasu a koresu ta fuske tace gaskiyar
kenan yanda ZZ suke kuka sai suka bata
tausayi, sai kuma ta tuna da ita aka kama
korarta za'ayi imani dai ya shigeta ta fadi
gaskiya...
abin ya ba kowa dariya wato ko junansu basu
bariba sharri suka mata tafisu zama yar duniya
ta rama, nan dai aka shirya su aka musu fada
akace suje class tun a hanya iffaat take musu
dariya tana maimaita abinda ya faru tun suna
daurewa har suka fara dariya lallai iffaat taci
jinjina duk abinda takeyi Allah yana
taimakonta......
Akwai lokacin da iffaat tayi zazabi aka bata
maganin mura da maganin bacci to maganin
yana Jakarta ne, sai kawai ranar tayi lettin shiga
clss to malamin akwai shegen gayu da jiji da kai
kawai ta karbi permission tace xataje bayi da
gyar ya barta ta fita taje ta siyo drink ta bude ta
saka maganin baccin har guda shida a ciki ta
girgiza ta kulle ta baiwa wata students tace ta
kaiwa malaminsu tace inji anti funke.
Aka kawo masa yana mamakin funke zata kawo
mai drink yace bari yayi sauri ya shanye kar azo
ace ba nashi bane, ya zuge banxa ko minti biyu
ba'ayi ya buge da bacci iffaat sukayi iskanci a
clss sir na bacci
sannan ta daukeshi hoto a wayarta ta bayan
kowa ya qare aka tayar dashi bacci ya fara na
yan giya tamai video, yanata sunbatu yana fadin
ya akayine baby??wallahi saida aka kwasheshi
ranar cox ya kasa ko bude idonsa..
Goben ranar aka saka bincike amma ba Wanda
ya gano anti iffaat...
Kai iffaat manyan duniya.
Kuma haka tayita tura video da hoton nasa gashi
malamin Dan gayu da jiji dakai tuni ta zubar mai
da clss a gurin yan matansa da sauran students,
yanxu sunansa ya koma ya akayine?? Cox
lokacin da aka tayar dashi bacci sai ya fara
fadar ya akayine baby yana layi....
Wasa wasa iffaat Iffaat an kai Ss2 su ZZ kuwa
ana final year sun yi hatsabibanci bana wasa ba
har andaina kulasa kuma iffaat ce leader
dinsu.......
[11:21AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 53
Na Hauwa M. Jabo
*******
An saka ranar auren Yy farhaan da Yy Suhaila
20/5 daidai da ranar brdy din Hauwa jabo.
Tunda aka saka ranar auren iffaat sukuni ya
qara kubce mata saidai ta fuske takeyi tayi
harka amma tana azabtuwa matuqa, ta fadawa
ZZ suka bata shawara taci gaba da haquri
kawai..
Lokaci sai matsowa yakeyi ita dai mama ta rasa
gane sirrin zuciyar iffaat farko ta gano cewa
tanason farhaan ne musamman lokacin da ta
suma, nan zatoƱta ya zama gaskiya, sai kuma
yanxu komai ya tsaya mata yanda iffaat ta
chanxa gaba daya duk wani Abu da take da wa
suhaila batayinsa yanxu, hakan yana basu
mamaki sai kawai suce ta qara girmane....
An fara shirye shiryen biki su iffaat da farahnax
sune qirjin biki dama farahnax ta hada auren, shi
farhaan irin ya nuna yanason suhaila irin
soyayyar shan minti sai kawai farahnax taje ta
fadawa su umma, kuma Suhaila ce keson
farhaan sosai shi ba wani sonta yakeba, amma
ganin iyayensa sunshige gaba yasa ya sallama
ko banxa Suhaila kyakyawace kuma tana daga
cikin matan da yake so dalilin da yasa ya
amince da ita kenan. amma bai taba sontaba
daidai da rana daya..
hasalima mafi yawar da sukeyi ita take kiran shi
kuma ita Suhailar tasan ba wani sonta yakeyiba
haka take son kayanta. Allah sarki Suhaila tana
bala'en burgeni cox ba ruwanta abinda na
fahimta farhaan ya sace zuciyar Suhaila da iffaat
ne amma iffaat ta barwa Allah tasan ba yanda
za'ayi ya aureta bayan ma ya rainta gata
qanwar matarshi...
haka dai akayi komai cikin jin dadi auren ya
qayatar anyi komai cikin jin dadi da arxiki naira
taci ubanta...
An kai amarya dakin mijinta,
Hmmm Daren dai iffaat ba'ayi bacci ba gaskiya
na jinjinawa iffaat matuqa cox tayi jarrumta ba
kadan ba nidai jabo idan nice wallahi sai nayi
ciwo, Ashe Banida labari hadda iffaat anyi
zazzabin daurewa kawai takeyi, ta bani tausayi
matuqa kowa sai yace gajiya ce da kuma kewar
Yar uwarta har mama Dan yanxu mama ta gane
ba komai zatonta ba gaskiya bane,.....
[11:27AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..??54
Na Hauwa M. Jabo
Suhaila anachan ana barsar amarci da
angonta...
Iffaat kuwa ananan ana fama da axaba gwanin
ban tausayi....
ko wata Biyu ba'ayi farhaan ya fara chanza wa
ya gama da ita kenan, ya koma Neman
matanshi duk qoqarin Suhaila na kyautata mishi
ta ko wace hanya duk abinda tasan zaiji dadi
tana masashi iya qarfinta kuma qaryane yace
bata gamsar dashi cox a dare daya sai yayi
round biyu haka take haqura duk da tana jin jikii
burinta ta faranta masa, amma abanza takeyi su
farhaan kam ba hali.. dama mai hali baya barin
halinsa abin dai ba dadin ji sau tari takan
qyanqyasawa iffaat amma tace kada ta fadawa
mama.....
Ranar Suhaila ta kama farhaan yana waya da
wata akan zasu hadu wani guri, ranta ya baci ta
mai magana kuma tace sai ya fada mata ina
zaije sannan ta barshi ya fita...
Habawa kamar jiranta yake ya wani taso mata
kamar ya cinyeta hadda su gori wai albarkar
qanwarsa takeci ita tasa ya aureta, ba itace
choice dinsaba inda yake shiga banan yake
fitaba, maganganun farhaan sun qona Suhaila
matuqa ta shige daki tana kuka...!
Allah sarki Suhaila.!!
Kamar daga sama saiga iffaat yan mata dama
iffaat bata cika xuwa Gidan ba cox abinda take
gani ranta yana quna, idan dai kaga tazo Gidan
to aikota akayi, yanxuma wani tsimine aka kawo
mata daga sokoto shine akace ta kawo mata
aka aiko iffaat...
tin tsakar gida take kiran yy Suhaila har tashigo
palo bata nan, tashiga daki taganta tana kuka
hankalinta ya tashi tayi ta tambaya amma taqi
fada mata dagyar ta fada mata Ashe yana bakin
qofa yana jinta tana qare fada ya shigo a
fusace.. Kin gayawa uwata sai ta kasheni ko ta
hanani yin abunda naga dama wawuya kawai.!
Ashe bazaki iya rufawa mijinki asiriba..?? yayi
tsaki ya koma Palo tofa masu sayen fada da
kudin su bare an sami dalili,ta miqe tsaye ta
tsallake Suhaila ta fito Palo...
Taxo gaban sa ta riqe kunkumi amma wallahi
Yaya farhaan ka bani mamaki, ashe har yanxu
kana wannan mugun halin naka?? Koda ba abin
mamaki bane hali zanen dutse. Ta nunashi da
hannu abin kunya namiji kamilalle a fuska amma
xuciya ta shedan tirr da hali irin naka, koda ba
komai bane wayewace!!! Amma Allah wadaran
wayewa irin taka wacce akeyinta da Neman
mata ni wall...... Kamin ta qare farhaan ya miqe
ya kwashe ta da mari kuuut.....
[11:32AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 55
Na Hauwa M. Jabo
kaiiii..! Ya na sauke hannu itama ta wanke shi
da nata Marin, kamar daga sama saiga Suhaila
taga an mari mijinta tuni ta wanke iffaat da mari
tofa iffaat ansha mari ta daga kai ta kalli yayarta
taga yanda tayi wani iri haushi ya qara kamata,
dama ita iffaat duk bala'en da takewa farhann
da biyune ga kishin abin da ya aikata ga baqin
cikin rashin samunsa. Yayar ta fara mata masifa,
bata cewa yayar komaiba taci gaba da yimai
masifa da fitsara yayar tanata cewa ta bari tana
rufe mata baki Amma inaaa saida takai aya ta
zazzagemasa kwandon rashin mutunci Suhaila
abin ya qara kwabe mata baqin ciki kamar ta
hade rai ta mutu, ta qare tamai tsaki ta murguda
baki ta juyo gun yayar ke kuma ki zauna yana
qunsa miki baqin ciki kina shiga daki kina kuka
kamar wata doluwa.!
ta kama hanyar fita Suhaila ta bita tanason tace
kada ta fadawa mama farhaan ya daka mata
tsawa akan ta dawo, ta rasa yanda zatayi, taxo
gabansa ta tsuguna tana bashi haquri abin
mamaki yace ba komai ya wuce laifin sane
shima dama baiji dadin abinda ya fada mataba
nan dai suka shirya hmmm mata da miji sai
Allah hardai suka aikata aikin lada nan take,
farhaaan yasan bala'en iffaat yafi nashi nesa ba
kusaba cox shi yasan WACE CE ITA baisan
miyasa yake shakkartaba.!!
Ta isa gida a fusace amma kuma saita tsinci
kanta da kasa fadar abinda ya faru, ta rufa masa
asiri chaiiii soyayya bala'ece nan ma qarya ta
xubawa mama tace wasu samarine suka bata
haushi. mama tace nidai zanso naga mijinki
kullum cikin korar samari waike yarinya, tayi
murmushi ta wuce dakinta,. Tana shiga ta kulle
qofa ta fara kuka tayi nadamar dukan farhaan
koba komai ya girmeta kuma gashi mijin yayarta
haka kuma masoyinta ta tsinewa kanta yafi sau
dubu amma ita kanta batasan lokacinda ta
aikata hakan ba.!!
Farhaan kuwa duk ya damu yayi nadamar
abinda ya aikata qarshe yasa Suhaila ta kira
iffaat tana bata haquri itama ta bata haquri tana
ce mata ga yy farhaan zaiyi magana da ita ta
kashe wayar farhaan yace ta kyaleta amma ya
damu matuqa...
[11:38AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 56
Na Hauwa M. Jabo
Su ZZ an qare skull an bar su Iffaat yan mata
anata gwagwatawa Da students, dama ko ita
kadai tana abinda taga dama....
Cikin ikon Allah iffaat ana shirye shirye kammala
secndry skull any qara hankali amma fa har
yanxu tana jinyar soyayyar farhaan a zuciyarta,
ba Wanda yasani sai qawayenta ZZ....
******
Wata Ranar Suhaila taje sokoto bikin dangin
mamarta kusan sati biyu tayi bata gari, ana
gobe zata dawo tace wa iffaat taje ta gyara
mata gidanta tasan yayi qura ba kowa aciki
tunda tasan farhaan aikin banxa ne ba abinda
yake iya tabukawa kuma idan ta dawo ma ba
wani abin kirki zata iyaba gata da tsohon ciki
kwata 7 , dagyar iffaat ta aminta shima saida
aka hada da mama sannan ta aminta. mama
batasan sirrin ba iffaat tun lokacin da abin nan
ya faru bata qara zuwa Gidan Suhaila ba sai
wani zuwa da sukayi duba Suhaila itada mama,
sai kuma yau...
Waike Dan Allah idan bakiyimata wa zaki yiwa??
yarinyar tana qaunarki ta damu dake amma ke
kina Neman ki yanke zumunci mama dai haka
tayi fadanta dole tasa iffaat ta tafi Gidan..
Hmmmm Su farhaan ba'asan da zuwan iffaat
gidanba, kuma yasan sai gobe matar shi zata
dawo hankalinsa kwance shida karuwarsa...
iffaat tazo ta gyara ko ina na Gidan har ta
kammala Basu saniba suna chan ciki. haka
kawai taji tanason shiga dakin farhaan ta gyara
kuma batasan yana gidanba.
Takama hanyar dakinsa Ta buda qofar tajita
abude sai ta tsaya ta qara budewa Sanyin Ac da
qamshin turarensa ya daki hancinta ta lumshe
Ido ta dauke numfashi hadi da wani ajiyar zuciya
ta tura kai dakin tana bude ido sai taga mace
kwance tana sharar bacci daga ita sai wasu
tsinannun kayan bacci, numfashin tane ya tsaya
chak..!! tama rasa mi zata mata ta gane ta tsab
hafsa ce tsohuwar budurwar farhaan, ta tsaya
waige waige ta hango Yar yawo gefen fridge ta
Ciro ta zo zata fara zabga mata sai ta tuna duka
ana bacci bashida xafi sosai, ta bude fridge ta
samo ruwa ta juyesu a jug taje ta yaye bargon
da ta rufa ciki da qarfi, hafsa ta juya cikin
shagwaba tace dear kabarni zuwa anjima
mana.!! tace kinci ubanki keda dear. ta watsa
mata ruwan da qarfi a fuska, hafsa ta wani
zabura da qarfi tana miqewa zaune iffaat ta
kwashe banxa da mari saida ta koma kwance
tuni hafsa ta gigice, iffat kuwa batayi qasa a
guiwa ba tafara zuba mata bulala hafsa tana ihu,
ta mata lilis chan farhaan ya fito bayi da gudu
yayi turus da ganin madam iffaat.....
[11:41AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 57
Na Hauwa M. Jabo
Bata tsaya ba taci gaba da chin uban hafsa
farhaan ya kasa aikata komai kunya ta isheshe
dagyar hafsa ta samu ta miqe tayi bayan
farhaan da gudu tana kuka, tabbas hafsa ta
gane iffaat Dan kuwa itace ta qona mata qafa
shekara wajen Shida da suka wuce, iffaat ji take
kamar ta hada da farhaan din ta musu lilis
amma bazata iya dukan farhaan ba, tsanar sa ta
rufe mata ido ta tausayawa yayarta da take
tareda fasiqi irin sa tagodewa Allah da bata
aureshiba, da saidai suyi kashin kai a gidan Dan
bazata dauki wannan iskancinba ta dakawa
hafsa tsawa tabar gidannan hafsa ta kasa fitowa
bayan farhaan ta qara mata tsawa wallahi idan
naxo sai na kakkaryaki, inbanda hafsa batada
gaskiya ai ko qanwar hafsa iffaat bazata iya
fada da itaba bare hafsa mai Shekara wajen 30,
zata kakkarya iffaat. amma tunda batada
gaskiya dole ta boye farhaan kuwa ya rungume
hannuwa yana kallon ikon Allah kunya ta isheshi
da nadamar abinda ya aikata, tayi cikin hafsa
da qarfi hafsa ta riqe farhaan da qarfi wani baqin
cikine ya qara tasomata yanda taga tana
rungume farhaan ta baya uhum su kishi manya
tayi cikinta da qarfi ta janyo gashin da tayi qara
da qarfi ta wurgata a kan fridge farhaan ya
dakawa iffaat tsawa akan miye haka ta juyo
tamai kallo keep quiet ina zuwa gunka kaima..!!!
tama hafsa gargadi kamin ta lissafa biyar tabar
gidannan hafsa dagyar ta miqe ta kwashi
kayanta a hannu taji jiki tana gudu tana tunanin
wai wannan WACE CE ITA?? House girl ce haka
kyakyawa kuma ta mata haka gaban farhaan.
Anya kuwa?? Bayan ta kori hafsa ta juyo ta kalli
farhaan ido cikin ido tana tunanin balbala masa
masifa ji take kamar zuciyarta ta fito Dan baqin
ciki aranta tace wai ita kenan inaga matarsa da
sukasan juna idan taga haka sai hade rai ta
mutu.! Ya dago ido ya mata wani kallo ta
mayataccun sexy eyes dinsa tuni ta manta
abinda takeson ta masa sai ya bata tausayi tayi
tsaki.....
Har zata fita dakin sai kuma ta daure ta dawo ta
gyara ko ina ta tattara sauran kayan hafsa data
bari ta miqa masa tace ga kanan tsohuwar
karuwarka nan idan ka bita ka kai mata.. ta juyo
kenan ya janyo mata gashi da qarfin bala'ee
saida tayi wata qara....
[12:12PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 58
Na Hauwa M.Jabo
Ta sa hannu tana qoqarin kwacewa amma ta
kasa ya qara janyota da qarfi saigata saman
qirjinsa, ta daga kai tuni idonta sun cika da
kwalla Dan tsabar azabar da takeji, da qarfin
hali, tace, so bansan kacika wayayyeba sai ka
aikata abinda kake da niyyar aikata wa aikana.!!
yanxu ya gane manufarta tuni ya saketa yayi
tsaki ya fada bayi ya kulle kansa cike da baqin
ciki da nadama, a duniya ba wacce ya

Please Login or Register in order to submit comment