Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raina
kamar iffaat amma itace take gwadamai axaba,
iffaat kuwa tana samu ya saketa ta fita da sauri
ta wuce gida tana zuwa ta fada dakinta ta kulle
tana kukan takaicin rayuwa da mutum irin Yy
farhaan ta daga kai taga hoton Yaya Suhaila da
Yy farhaan sun rungume juna suna dariya tayi
tsaki,ta tashi ta cireshi ta saka a drawer ta
dawo taci gaba da tunaninta har barawo bacci
ya dauketa, bayan ta tashi taje gun mama..
Ah ah yaushe kika dawo?
Tayi murmushi wallahi tun dazu na dawo nasan
kina bacci lokacin shi yasa banma zo natayar
dakeba, okay suka yi tadi mama tana tanbayarta
ta gyara Gidan dakyau kuwa? Dan tasan son jiki
ya mata yawa
Laaa mama kin manta nayi aikatau suka saka
dariya gaba daya, Yaya Ameen ne yazo da Yaya
Ali suka zauna akayi tadin dasu suna cikin
magana Yy Suhaila ta kira...
Sister sorry na sakaki aiki da yawa,!laa kinji dai
Yy Suhaila wane aiki kuma idan ban mikiba
mawa xan yiwa, ta fara godiya, wallahi idan
kinamin godiya zan kashe wayata, to nabari yi
haquri, kin tarar da farhaan a gida?? Wallahi
Naso nace idan yananan ki masa Dan girki,
Tseeeet tayi kamar ruwa ya cita qirjinta yake
bugawa, lokaci daya ta tuna abinda ya faru
tausayi Yy Suhaila ya kama ta Amma bazata iya
fada mataba, hello kinajina kuwa sister? Tayi
xumbur ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi..
Inaji Yy Suhaila, to ki bawa mama wayar na
miqawa mama ta tashi tsaye, Yaya Ali ya kamo
hannunta..
bayan sun qare yace wani abokinane yakeson ta
kinma sanshi Nurane mama tace nikam ko
sunansa banaso bare shi na tsani wannan yaron
akwai shegen rawar kai, iffaat tace wallahi nima
mama na tsani Nura kamar me nima dai jabo ba
abarni a bayaba gun tsanar sunan Nura mugu.
Duk aka saka dariya kowa ya tsani Nura Allah
sarki har ya bani tausayi......
**
Goben ranar tinda safe Suhaila tayi waya da iffat
ta gaya mata sun kamo hanya
Guraren qarfe 11 iffat na zaune da mama dasu
yaya da yake yau Saturday, wayar iffat tayi qara
laaaa yy Suhaila hatman sun iso, hello Yy
Suhaila kuna ina? Kun kawo hala?
Taji namiji yace ke sister din Suhailar ce ??
Tace Eh kai waye?
Sorry Dr ne daga Chika, yayar Ki sun sami
accident Allah ya mata cikawa driver kuwa
gashinan kwance ya kakkarye?
Iffaat wata irin qara ta saka ta fadi
sumammiyaaa....
[12:18PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 59
Na Hauwa M. Jabo
Mama tayo kanta tana tambayar lafiya amma
ina iffaat ta riqa ta suma,
Yy Ali ne ya dauki wayan ya kira number Yy
Suhaila, Dr. Ya masa bayanin da ya yiwa iffaat
yace babbar motace ta shiga gabansu suka
yanka daji anan motar ta wuntsila rai yayi
halinsa Yaya Ali ma dashi da qarfin halinsa sai
da yayi kuka, ya yiwa mama bayani tuni gida ya
rude da koke koke Yy Ali yayiwa baban Suhaila
waya ya fada Masu abinda yake faruwa kamin
kace kwabo labarin rasuwar Suhaila ya baje
family namu kowa yaji mutuwar Suhaila cox
Suhaila mutunce mai mutunci ga haquri da
kawaici, bata shiga harkar da ba nataba kai
mutuwa tana dauke nagari. farhaan kam da ya
samu labari mutuwar tsaye yayi bai samu damar
maganaba saida yaga gawar Suhaila, sannan ya
fara kuka kamar qaramin yaro kamar wani
zararre, lallai ta tafi tana binsa basussuka cox
bayajin tayi wata biyu yana kyautata mata
kullum cikin muzguna mata yake, su farahnax
kam haka ta dawo kamar mahaukaciya, mutuwar
ta ratsa kowa a gidannan musamman iffaat da
farhaan da maman Suhaila.!!!
Iffat koda ta farfado har an kai Yy Suhaila
makwancinta wayyo Allah, mutuwa mai raba da
da mahaifi miji da mata Yaya fa qanwa aboki da
aboki. Mutuwa tayi yankan qauna a wannan
family...
cikinta ma anciroshi da ranshi amma da yake
wata7 ne kwana biyu yayi yabi uwar shi, cikin
da farhaan yayi burin ta zubar tun tana amarya
zan iya cewa ma bayason cikin.
Sauda yawa Suhaila tana kiran iffaat qanwarta
ta fada mata abinda farhaan yake mata amma
tace kada ta fadawa kowa, kuma bata taba
fadaba
Mutuwar Suhaila yasa iffaat ta qara tsanar
farhaan gani take kamar shiya kashemata Yar
uwa! amma fa still sonsa yana cikin zuciyarta,
hmmm soyayya manya..!
*****
Arba'en din Suhaila yayi daidai da fara jarabawar
su iffaat mutuwar Suhaila tadan natsar da ita
kadan dama iffaat ta iya matsuwaa idan Abu ya
faru da ita! sunyi neco da waec lfy sai jiran saka
mako, xubi xubi iffaat tana zuwa gidansu
farahnax ta gaida mamarshi da farahnax din da
kuma qawarta Yar baqa zainb khalifa,
Ranar tana zaune dakinta taji sallamar farhaan,
da yake Gidan idan aka shigo dakinsu yana daga
gefe ne sai dakin mama, tanaji ta gane tayi
banxa dashi.
Sunyi hira da mama, tanaji yana tambayar ina
iffaat tace tana daki,
Har ta manta da wani farhaan yazo gidan. Chan
taji sallamar sa a dakina, Dan amsa sallama
wajibine da nasan iffat ba zata amsa maiba, taci
gaba da aikinta, ya zauna ya fara sun batunsa,
yaga ba nasara, yace iffaat.......
[12:21PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA.?? 60
Na Hauwa M.Jabo
Iffaat miyasa kike min hakane? Koba komai ni
Dan uwankine tun kamin mu hadu da margayiya,
kuma naxo na auri yayarki, kina tunanin kodan
wannan ai bai dace ki riqa min wani gani ganiba,
ki tuna kin min laifinda ya dace na hukuntaki
amma na gyaleke na yafee miki..!
Anti masifa madam iffaat ta watsa mai kallon
banza hadi da wata uwar harara! Laifin me na
maka oga? Wato ma ni na maka laifi ko?? Ka
manta chin mutuncin da kake yiwa Yar uwata?
Kamanta wulaqancin da kake mata?? Ka manta
yaudarar da kake mata?? Sannan duk ka shuresu
kaxo kana cewa ni na maka laifi?? Ta daga kai
tayi karo da hotonta ita da Suhaila sun rungume
juna suna dariya. Hawaye ne suka wanke mata
fuska tayi missing din Yar uwarta abar sonta,
farhaan ya kamo hannun iffaat yana zaune iffaat
Dan Allah ki yafemin! Nasan ban kyautawa
Suhaila ba ko kadan, wallahi sai yanxu nake
ganin irin rashin kyautatawar Dana mata idan
kika yafemin tamkar itace ta yafemin ta kasa
kwace hannunta daya riqe batace komaiba.!
Tayi ajiyar zuciya ta karbe hannunta, ta zauna
har ya qare surutansa batace masa komaiba,
wallahi iffaat ina tsananin son Suhaila, ji tayi ya
daba mata wani gwaho a zuci har saida ya
gane. Nasan baxaki yardaba amma gaskiyane na
fada miki, ya gaji ya tashi Ya qara wuta..
*****
Iffaat yan mata result ya fito ana kiciniyar
shigarta jami'a ta sami damar shiga cikin nasara
an bata course dinda takeso kuma.
Dai dai lokacin auren farahnax ya matso sai
shirye shirye suke qawayen amarya, komai itace
gaba itada Yar baqa sai iyayi suke, anyi auren
farahnax lafiya ankai amarya Gidan mijinta da ke
abuja, iffaat dai kam kullum sai tayi sabon
saurayi amma ko kallo Basu ishetaba karatun ta
ta saka gaba.!
Ranar umma tayi rashin lfy sunje dubata itada
mama da maman suhaila, umma ke tambaya ta
yaushe zatay aure? Ko sai ta samo mini mai
saida ruwa irin na dijee, akasa dariya kunya ta
kamani na tashi na shige lanbu don demo
abincina na da na barsu su nan.....
KU BIYOMU DON JIN ABINDA IYAYEN
WAYANNAN YARAN ZASU TATTAUNA AKAI,
jiya banyi posting ba wallahi network yamin tsiya
nayi nayi fcbk dina ya bude yaqi buduwa kuyi
haquri.!!!
[10:49PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..??61
Na Hauwa M.Jabo
Suna tsaka da labarin su saiga farhaan ya shigo
ya gaida surukansa yama ummanshi ya jiki ya
shige dakin abbansa,
Bayan ya wuce ne maman Suhaila take cewa
Allah sarki yaronnan har yanxu bai nemi
mataba? Umma tace kedai bari gashinan
Bansan mi yake jiraba, niko ga shawara, mizai
hana a hada farhaan da iffaat aure. Mama tayi
dariya kai hajiya kulu ina kika taba ganin rigima
da rigima sun hadu duk sukasa dariya umma
tace lallai kam Dan farhaan da iffaat basa zama
guri daya. Mama tace koda yake shi aure daban
ne wata qila sai kiga sun zauna lfy.
Gaskiyar magana dukansu sunyi na'am da
shawarar hajiya kulu maman Suhaila sun tsaya
akan zasu shawarci mazajensu suji,
Suna zaune suna tadi saiga iffaat da ta ciki
kyale da su mangoro da gwaiba umma tace um
um mai hali baya barin halinsa..! duk suka saka
dariya, taje ta wanko ta kawo musu suka
farasha, dama ita qa'idarta idan zatasha
mangoro saita mulmulashi yayi laushi yayi ruwa
sannan tasha. Ta kuwa miqe qafafu ta saka
basket dinda ta saka kayan a ciki ta fara shan
mangoronta tana zaune saiga farhaan ya shigo
ya kalleta, xaman da tayi ya bashi dariya ya
tuna mai da lokacin da take qarama sai yaji bari
ya tsokaneta komai ta fanjama fanjam.!!
Wai umma wannan Yar taki ba university take
xuwaba? Umma tace eh chan take kaga yata an
zama yan mata ko..!! Inafa yan mata har yanxu
bata wayeba! Kalli Dan Allah yanda take shan
mangoro kamar wata Yar ruga,! ruwan
mangoromangoro suna bin hannu, ya kwashe da
dariya hadda buga qafa ya gama quleta ya kalli
umma anya kuwa zata sami miji a haka??
Umma tace ka sakawa yata ido dayawafa miji
kam sai ta xaba Dan ma bakaga yanda ake
layiba dukansu suka dara nima dai jabo na dara
kuma Masu karatu sai Ku dara.!!
Iffaat tace umma ki barshi, ta dago ta kalleshi
ido cikin ido tace mijina sai ka Ganshi wayayye
na gaske ba irin wayewarkaba, ba Wanda yagane
habaicin da ta masa sai shi damu Masu karatu.
Yadan Sosa kai yayi murmushi qarfin hali mama
bari na tafi tunda kun hanani mangoro, umma
tace sai kace wacce da debo ta sammaka, yace
waa ai wannan tafi dijee rowa.! da zai fita ya
hada da gefen chinyarta ya take saida tayi qara
ta jefeshi da qallon mangoro......
[10:57PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?? 62
Na Hauwa M. Jabo
Mama tace Waike iffaatu bakida kunya ko, miye
na jifanshi da kwallon mangoro? umma tace
rabudamin da ya, wallahi shiya tsokaneta ina
kallonsa ya taketa, Dan ya taketa sai ta jefe shi,
karki sa mata baki Dan Allah ke iffaat tashi ki
shiga ciki.
Bayan ta wuce umma tace kin ganiko,? Haka
suke kamar tom & Jerry, hajiya kulu tace ai aure
daban yake alkhairin sa zamu nema kawai,...
***
Hajiya kulu na komawa gida ta sami mijinta
mahaifin Suhaila tamai xancen ai tuni ya amince
abbah ma da umma ta masa magana ya amince
100% mama ma haka tayi shawara da su Yaya
Ameen akan wannan auren kowa ya aminta
yanxu ya rage aji ta bakin gogayen...
Abba da umma suka kira farhaan aka fara masa
maganar Dan tsananin rudu da tsoro saida ya
manta yana gaban iyayensa, atafau farhaan yace
aah miye dalilinsa yace kawai matsayin farahnax
ya dauketa, shi bazai iya auren taba tun ana
lallashi har Abba ya yanke dole ya aureta ko
bayaso, kana tunanin zamu aura maka macen da
zakayi kuka da ita? Duk cikin mu ka fimu sanin
WACE CE ITA! cox ka zauna da ita tun tana Yar
mitsiyayarta,
Farhaan dai kawai yajisune amma Sam bai amin
taba,
Itama madam iffaat an mata maganar farko
dariya ta saka musu irin ga zancen nan Mara
kan gado.
Da taga dai da gaske akeyi kawai saita saka
musu kuka! Aka buga Sama da qasa tace bazata
auri mijin yayartaba...
Abba Suhaila ne yace sun Riga sun yanke
magana ba chanji ba mijin yayartaba ko waye
shi zata aura..
Nikam jabo abin mamaki ya bani yanda iffaat
tayi jinyar son farhaan tun batada wayo amma
yanxu ga dama ta samu tace batasosa! Uhum
kuma ga dukan alamu da gaske takeyi, ta daga
ba nasara taci gaba da kuka ta wuce dakinta,
Yaya Ameen ne yabi Yar qanwarsa yana lallashi,
Haba iffaat miye aibin farhaan? Kina gani wallahi
guy ne gashinatsatse ga kamala, wallahi yanzu
dagyar ki sami namijin na kirki kamarsa baya
shaye shaye baya Neman mata. ta dago kai da
sauri ta kalleshi amma sai ta kasa fadar cewa
yana Neman mata, kowa ya shedeshi ke kanki
shedace akan haka! Sabida kinyi rayuwa dashi,
iffaat dai batace komai ba har Yy Ameen ya qare
rarrashinta ya tashi ya fito!
Ta miqe wallahi da na auri farhaan gara na shiga
duniya....
[10:58PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?? 63
Na Hauwa M.Jabo
Tun daga ranar ta kamawa su mama mutunci ta
daina musu magana tadaina chin abinci ba
ruwanta dasu ita dole fushi, anyi sati biyu da
maganar sai ranar taji su yy da mama suna
maganar, ana maganar daurin aure kuuut saidai
wata ba itaba, ta miqe tsaye ta riqe kunkumi ta
fara shawara da zuciyarta yanxu ita iffaat har
sun isa su mata auren dole? Waima...! Idan ta
saka musu ido zasu aurar da itane, su Basu
damu da damuwartaba, abinda ya fado mata
kawai ta gudu, kai guduwa ba jarumta bace, duk
macen da za'ayiwa auren dole ta gudu ba
jaruma bace,so bataso ta gudu a ganinta ba
jaruma bace duk wani tunani sai taga bai dace
da itaba, nidai jabo zaune nayi ina kallonta ina
jiran muga abinda zata aikata, amma ga dukkan
alamu ba wani Abu da ya rage gwagwalwarta
bata aiki, sai fashewa tayi da kuka..
Yanda ta tsani halin Yy farhaan ko sonsa zai
kasheta bazata aureshiba, tanada mahaukacin
kishi
Tayita tuna yan matan farhaan din da yanda
yake musu ta runtse ido da qarfi ta daki madubi
tace Nooooooooooo, ta na kuka tana dukan
madubin duk ya yayyanke mata hannu, ashe su
mama sun jiyo mama ko a jikinta, Yy amin ne
yaxo gunta da sauri ya riqe hannunta duk ya
yayyanke, ya yiqeta ya kalleta yaga yanda ta
rame tana juyowa ta fada jikinsa tana kuka, tana
cewa Yaya ka taimakeni wallahi banason sa Yy
Ku aura min wani not Yy farhaan, yace to
shikenan kiyi shiru zamuyi magana da mama,
dagyar ya samu tayi shiru ya dauko first aid
yadan gyara mata hannun ta ta ta yayyanke, ya
jata da hira har tadan saki jiki, qarshe yace tazo
su fita yawoooooo...
[10:58PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?64
Na Hauwa M. Jabo
No ka tafi Yaya ni baxanjeba ya rarrasheta har
ta amince suka shirya suka fita. Sunje wani park
ne suna shan ice cream, hakan ya faranta mata
rai matuqa suna sha suna tadi a hankali yy amin
yake nuna mata illar abinda takeson tayi, suna
tsaka da magana tana yan kalle kalle charab ta
hango wani abu wacce ta hango ba shakka itace
ba qarya budurwar farhaan ce ramcy, tayi
murmushi su ramcy ananan da yake Yy baisan
taba tana kallon ta har ta shige ba'ayi minti
goma sai kuma ta hango farhaan, wani rasss taji
ko shakka babu tare suke da farhaan amma da
yake shi mai wayone a hankali yake takunsa, wai
farhaan wane irin jarababben mutum ne?
Tayi tsaki, yy amin yace miya faru kuma? Ta
kalleshi idonta sun kada sunyi jaa ba komai! Ya
ba komai, ta dago mai idonta da har sun zama
qanana tace ba komai yy, sukaci gaba da
tadinsu amma Sam bata tare da yy amin
tanachan tana tunanin farhaan, kusan 30mnt
Basu fitoba ta kasa haquri ta miqe tsaye, ina
zaki kuma? Y tace ina zuwa yaya ya kalleta,
yanxu zan dawo Yy, ta wuce da sauri ta shiga
Ashe cikin gurin hotel ne ta fara dubawa duk ta
zagaye gurin bata gansuba, sai taje gun
reception ta tambayi farhaan mutumin yace
mata yanada baquwa wani rass taji, tace ai na
na sani shi yace nazo na karbi saqo yayanane,
ya kalleta sosai sai ya gaya mata number
dakinsa wani dumm dummm dummmm takeji,
ana mata zagaye a zuciya ta isa gofar dakin tayi
jimm ta daure ta bubbuga saida ta buga uku
sannan aka bude, ramcy ce ta bude qofar iffaat ji
tayi kamar ta shaqeta ta mutu ramcy bata gane
iffaat ba Sam.! ta watsa mata harara, tace lfy
iffaat ta daure tace yy farhaan yace naxo na
karbi saqo na kaiwa umma, tanajin haka sai ta
saki fuska, okay bari na kirashi, ta kwala mai
kira yazo yana zuwa ya ganta.........
Tofa.
[11:19PM, 5/12/2015] .: WACE CE ITA..?? 65
Na Hauwa M. Jabo
hankalinsa ne ya tashi! Ya rude yama rasa
mizaice mata, itama haka wato wani tashin
hankalin sai mutum yama rasa mi zaiyi, ta
kalleshi tayi murmushin qarfin hali tace sannu Yy
farhaan.!! Kamin ya bata amsa hawaye ne suka
zubo mata batasan dalilin zuwansuba, gaskiya
hawayennan sun kwafsa mata taso tayi chin
mutunci cikin ruwan sanyi amma ina kuka ya
kwafsa mata, bazai yiwuba chin mutunci ana
kuka baiyiba, da sauri ta bar gurin tana juya
kenan sai ga yy amin yaxo nemanta, lafiya kike
kuka? Tace
Ta hadu da wata qawartace shine take bati
labarin mutuwar mijinta .........
Eyyah Allah yajiqanshi ina take? Tace sun wuce,
farhaan yana jinsu kuma yaji abinda tace, yayi
tunanin zata tona masa asiri amma ina bata
fadaba,
Suka kama hanya idon iffaat Sam bata gani
gabanta hawayene suke rally a fuskarta.! ta kasa
jurewa sai wani Abu takeji yana taso mata,ta
rasa gane kanta, Yy amin yana gefenta yanata
bata labari amma taqi bari su hada fuska kuma
taqi cemar komai, har suka isa suka zauna!!
Waike har yanxu kukan kikeyi?
Ta dago kai ta kalleshi, wallahi Yaya ta bani
tausayine tana matuqar son mijinta amma
mutuwa ta rabasu, sai na tuna da yy Suhaila...
yace Eyyah sai haquri Allah yajiqanta ya Dan
qara lallashinta har tayi shiru amma zuciyanta
cike da tunani.! Har suka dawo gida tunani
takeyi.
Shiko farhaan yana ganin sun bulle ya kori
ramcy tana tambayar lafiya ya daka mata tsawa
akan ta bace mai da gani, ta tattara yan kayanta
ta wuce, ya fada kogin tunani,!
Baisan miyasa wannan yarinya takeda bala'en
tasiri rayuwarsaba, duk abinda yake a boye yake
yinsa, amma kuma bawai yana damuwane da
kada a Ganshi ba amma yana jin haushi idan
iffaat ta Ganshi..! Gashi tun tana qarama
tasanshi da wannan hali,amma har yanxu
baidainaba, yasan yana fama da sonta kuma tun
tana qarama yakejin haka yaqi qasqanta hakan
ne, ya yakamata fa ya daina. Kai wannan
mitsitsiyar yarinyar tama isa ta hanashi abinda
yakeso!? Amma miyasa take yawan kamashi?
Yaja tsaki ya juya ya miqe tsaye yana zagaye
dakin. Chan ya daki iska yace auren ta kawai
zan aminta dashi shine zaiyi maganinta, shima
ya huta da azabar rashinta.
haka dai ya qare yan tunane tunanensa cike da
damuwa.
Iffaat kuwa ana isa gida ta fada daki ta kulle ta
fara sana'ar tata yanda take kishin farhaan
tasan wata rana kisan kai zatayi, gara kawai ta
nemawa kanta zama lafiya ta aureshi, ba wata
hanya da takeda da ta wuce ta amince masa
kamin baqin cikin sa ya kasheta ko banxa zata
rage azabar rashin ganinsa da take fama da ita,
haka har bacci ya dauketa, Yy amin ne ya tayar
da ita daga bacci, ya kawo mata pizza tayi
murmushi Yy amin ne kawai yake rarrashinta
idan tana fushi mama kam ko kallo bata
ishetaba itama haka....
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 67
Na Hauwa M.Jabo
20/5 idan ban mantaba yayi daidai da ranar
daurin auren yy Suhaila kuma shine ranar brdy
dina ni Hauwa Jabo wannan ranar itace rana
mafi girma da daraja a idon iffaat wannan ranar
ita ta chanxa ta daga jerin yan mata zuwa matar
aure a wannan ranar ne ta taka matsayi na
Chika da kamala,
Farhaaan kuwa jinsa yake gashinan dai ya rasa
abinda yake damunsa tsorone ko kuma murna
ko baqin ciki gashinan dai kamar ba angoba..
Ba wani shagali da akayi, Dan zance muku iffaat
har ranar dauren auren ta saida ta sulale taje
makaranta wayanda sukasan da zancen auren
suna ta mamaki irin ga serious student dinnan,
basusan dawar garinba, ai kuwa tana dawowa
tasha fada gun mama haka dai aka qare taro
akan gobe za'akai amarya gashi Kuma amarya
gobe ma tanada test gashi ance sai ta fadawa
ogan zata iya fita, sai kawai haqura tayi, ankai
amarya gurin su umma suka mata nasiha, nidai
tunda nake ban taba ganin amaryarda ana mata
nasiha tana kallon mutaneba sai iffaat ba Dan
sunkuyar dakai ba komai haka umma na mata
nasiha ido cikin ido tana kallon ta har abin ya
baiwa umma dariya amma ta fuske Abba ma
yayi har ya bata kudi yace ko zata buqaci wani
Abu. Daganan aka kwashi amarya aka kaita
Gidan mijinta PURHUUN...
Abokan ango sun rako ango yan matan amaryar
da suke nan su black one ZZ da najma da meena
slow sune suka sayi baki idon amarya tar
akansu Allah ne kawai ya dinke bakinta batayi
maganaba Dan kuwa taso tayi magana, an sayi
baki kowa ya kama gabansa amarya ta tashi ta
cire kayan jikinta dama sun dameta kuma gata
da jin zafi kamar me, ta saka wasu kayan tana
danna waya saiga farhaan ya shigo ta kalleshi
shima ya kalleta ta mishi kyau itama ya mata
kyau uhuuuuum ya zauna gefen madubi.
Iffaat ya kira sunanta koni nan Jabo saida na
jiyo bugawar zuciyarta, ta dago ta kalleshi,
Ya fara yan maganan ganun da ake yiwa amarya
sannan ya qara jadda mata cewa yanxu da da
ba dayaba akwai haqqinsa akanta itama haka
yana cikin mata nasiha sai yaga ta dauki waya
hello tana dariya, shiru yayi yana kallonta tana
rai nashi yana maganaba tana waya tsaki yaja
ya kwanta abinshi ta qare wayarta itama ta
kwanta nayita jira ko za'ayi wani Abu amma har
na gaji ba wani bayani na fito abina.....
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??66
Na Hauwa M.Jabo
Taci pizzar sosai suna dan labari sama sama
chan ya sako zancen auren ta da farhaan irin dai
yana son ta amince ya nuna mata illar fushin
iyaye akan yayansu, jiki a sanyaye tace mishi ta
amince, Dan murna baisan lokacinda ya tashi
yayi rawaba ya juya itama abin ya bata dariya
nima Jabo abin ya bani dariya, yana ta saka
mata albarka, yaje jikinsa na rawa ya gayawa
mama da Yy Ali sun ji dadi ko ba komai sun
yanke shawarar idan taqi aminta za'a bar
auren..
***************
Magana ta kowane ban qare ta kan kama iyayen
sai murna suke sunata shirye shirye, amma
amaren kam ko a jikinsu, ana saura kwana biyu
daurin aure saiga goggo da dijee da rukayya
sunzo, koda sukazo iffaat tana skull Dan ita
wannan shirye shirye bai hanata zuwa
makarantaba,
Koda ta dawo bakin qofar dakinta taga wasu
takalmi Masu kama da kito amma dai na
matane, ta shiga dakin saiga su dijee anyi arshe
arshe tsakayar daki da yayanta biyu rukayya ko
yarta daya da ciki ta kallesu ta kwashe da dariya
harda durqusawa qasa Dan dariya, tayi dariya
saida ciknta yayi ciwo suko sun tsaya kallon
ikon Allah ta dago ta qara kallonsu nan ma ta
kwashe da dariya dijee tace ke bamusun iskanci
Dan kin zama Yar birni zaki ijiyemu kina mana
dariya kamar Kinga tutu...!!
ta harareta ta zauna da kyau tana dariyar tace
wallahi mamaki nakeyi wai dijee da Yara har
biyu! Ta qara saka dariya dijee ma sai ta dara,
ta kalli yayan tace amma dai dijee kina dukansu
ko? Rukayya tayi charab ta chabke tace ai
yanzu duk bala'en dije akansune Dan har danbe
tanayi da uwayen yara akansu, dijee tace ke
rukayya banason sharri da zuwa ko gaisawa
ba'ayiba zaki fara mini sharri, nan dai qawayen
suka yini suna tadi suna dariya duk da qauyanci
su bai sa ta gyamacesuba tunda itama chan aka
fito sun cire mata kewa matuqa kuma bata bari
suka gane cewa auren nata sai a hankali bane....
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 70
Na Hauwa M.Jabo
Taje ta zauna sai ta kasa chin abinchin don an
hanata fita kuma sai a hanata xuwa skull...
Wasa wasa iffaat na Neman wata daya Gidan
farhaan baya kulata itama bata kulashi amma
rashin xamansa gida na damunta ko ina yake
zuwa Allah masani kuma bata gane takunsa,
Ranar tana zaune dabara ta fado mata yanda
zata gane ina yake tafiya, bayan ya dawo
gantalinsa na dare ya kwanta bacci, dama
batayi bacciba tana jiransa ya dawo ya ijiye
wayansa tana tabbatarda yayi bacci ta dauki
wayansa ta shige bayi ta kulle ta danna power
off screen din yayi duhu ta duba da kyau sahun
hannunsa ya yake zana pattern dinsa bataci
wuyaba tana zagaya yanda taga sahun
hannunsa yabi tayi sa'ar bude wayar pattern
dinsa ba wahala ma, tana budewa ta fara aiki,
farko saida ta budamai Google account sannan
taje play store tayi downloading din latitude
tamai register dama tana dashi ta dauko
wayanta tayi sending request ta karba shikenan
ta gama da wannan duk inda yake matuqar data
dinsa a kunne take zata Ganshi baya buqatar
GPS latitude din, ta shiga SMS bata sami
komaiba taje contact ba wani number da bata
yarda dashiba harda searching na sunayen yan
matansa data sani amma babu ta duba logs nan
ma babu da qanqaro WhatsApp a kulle yake
kuma da pin number kawai zai bude bata
wahalda kanta ba taje gallery ba wasu hotuna
daga nashi sai iyayensa sai kuma na margayiya
Suhaila, gasunan sunfi 100 wani qololon baqin
ciki da kishi ya taso mata ganin hotunan da
Wanda suke tare da Wanda rake ita kadai amma
ba nata ko daya kamar ta goge amma kawai
saita fasa har zata fita sai taga wani folder ta
shiga akwai wani aciki ko wanne an rubuta
empty haka tayita dannawa saida ta wuce folder
14 sannan takai gunda aka rubuta Mrs
PURHUUN, ta shiga ciki hotunan tane aciki daga
kan wayanda ya mata lokacinda ta fara koyon
gayu gun Yar baqa Dana zuwa qauyen da yayi
wasu ma ya saka su a cikin frame mai heart
wasu kuma itada Suhaila ne amma an gutsure
Suhaila ko farahnax wasu ma batasan ya
dauketa suba irin tana zaune dinnan tana shirme
ko kuma tana surutunta tun kamin ta qare
wayewa gasunan dai kala kala, mamaki da jin
dadi suka mamaye mata zuciya ganin ya damu
da ita hatta hotunanta a wayar, sai wani video
da ta gani rawar da suka tabayine itada
farahnax a daki sukayi video ko ina ya samu
ohoooo tana tsaka da kallo taji yana qwanqwasa
bayi tsoro da tashin hankaline suka
baibayeta.....
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 69
Na Hauwa M. Jabo
Tace Idan da kana dukana ada yanxu akwai
banbanci wata qila ada ina gyalewa ko kuma ina
ramawa to ka sani yanxu akwai banbanci, ni
matar aurece inada yanci kuma nasan yancina
so ka kiyaye hannunka daga Taba matar aure.!
Ta sake mai hannu da qarfi Ta wuce abinta ya
bita da kallon Mamaki hadida zargin abinda ya
kawota yi anan ya akayi tasan yana nan ya daki
iska baima jira karuwarshiba ya fito da qarfi
koda ya fito bata ba labarinta ya shiga mota
gudu yake kamar ya ya hira sama koda ya isa
gida bata isoba yayi kusan 30mnt sannan ta iso
da ledojin abinci a hannu.! Tana zuwa ya daka
mata tsawa ina taje? Ta kalleshi dukda taji tsoro
amma bonewa tayi, ta danqaramar uwar harara,
kamar ma bada ita yakeba, tana Neman guri ta
zauna ya fincikota ke badake nake maganaba, ta
kalleshi ido cikin ido tace mai inda yaje chan
taje? Mi kikaje yi achan nanma ta bashi amsa
abinda kajeyi achan shi najeyi.? Idonsa suka
kada sukayi jaaa sun firfito waje iffaat kinsan
abinda kike fada ya qara fincikota ya mannata a
garu kinada auren nawa zakije gurinnan ? Ko kin
manta ke matar

Please Login or Register in order to submit comment