Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 1: Kana tunkarar filin babu abin da zai fara maka maraba face karajin fusatar hatsabiban mutane da aljannu kai hada ma dodanni kururuwar mayakan asali ta yawaita, kasa ta rinka girgiza da raurawa kamar zata tsage duwatsu suka rinka farfashewa, itatuwa suka rinka kamawa da wuta, guguwar annoba ta tashi sama ta tokare hasken rana wananne ya ba filin yakin damar yin duhu, hatsabiban mutane da aljannu da dodanni suka rinka shawagi a sama suna fauce rayukan junansu tabbas wanan bakin gumurxun ya cika sunansa turnuku fadan ibilisai, daidai lokacin ne wata bakar gobara ta taso daga tekun bahar sufiyya inda makaman mazanjiya suke, saidai abin da zai baka mamaki idan aka ce maka duk wanan masifa da balain dake aukuwa bai sa bakaken rundunoniba suka dakata da yakar junansu ba saima kara himmatuwa da sukayi wajan yakar junansu da kaiwa juna sara da suka mutuwar yawa ta kara yawaita mayaka da dama sun afka tarkon mutuwa batare da sun ankara ba saidai lokaci daya wanan bakin gumurxu da ake ya tsaya shaidanun mutane da aljannu da dodanni da suke shawagi a sama suka silmiyo kasa domin tsira daga halaka duk wanan abu ya faru ne sanadiyyar bayyanar wani haske mai daukar ido yana saukowa daga sama a hankali hasken ya sauko kasa lokacin da ya gama saukowa sai hasken ya fara raguwa sai suka bayyana, bayyanarsu ce tasa kowani hatsabibi dake filin yakin ya shiga taitayinsa ga duk wanda ya karanta littafin mazan jiya farat daya zai shaida wadanan mutanen da suka bayyana"lallai kam to bari mubar wajanan tunda har manyan shaidanu sun fara bayyan me ya kawo su SARKI MAHRAZ DA SARKI DUJALU nan gurin bari kagani in bar gurin tun kafi ta ritsa dani'' cewar wani bakin katon mummunan aljani tsawar da yaji ce ta dakatar dashi daga tashi sama ba kowane ya kwantsama wanan tsawar ba face sarki dujalu sanan ya fara magana cikin murya mai amo yana cewa yaku mayakan birnin matsafa, jaruman birnin sadaukai duk dacewa kunsha tsimin dodo kiryanu, an saka ku a cikin ragayar tsafi tun kuna yara hakan ba zaisa ku taka matsayin murucin kan dutse ba mu mune muruccin kan dutse tsawar da sukaji itace ta tsaida sarki dujalu daga maganar da yake cikin zafin nama suka juya domin suga wani mai tsautsayine wanan juyawar su ita tayii dadai da karasowar wasu kibiyoyin tsafi wanda ake musu take da kibiya ratsa maza badan sarki mahraz yayi saurin dafa kafadar sarki dujalu sun bace ba da tuni kibiyoyin sun cake jikinsu sana suka bayyana a gefe cikin fushi suka daga kawunansu....
BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 2:
Yayinda su sarki mahraz da sarki dujalu suka daga kawunansu sama domin suga wani mai karar kwanane yayi musu wanan danyen aikin sai sukaga wani tsohon aljani mai kwarjini da cikar kamala zaune kan wata bakar kujerar tsafi tsaye kan iska hannun sa na rike da wani katon littafi a jikin littafin an rubuta da babban baki KUNDIN TSATSUBA da saukarsa kasa yayi daidai da sakin fitsarin wani katon bakin aljani saboda tsananin tsoro idan kayi duba zuwa ga tarin hatsabiban mutanen da aljannu da dodanni duk zakaga zabar tsorone da fargaba tab cike da fuskokinsu ” shin mi ya kawo SHAMHARU SHAHARARRE wajan gasar kwarzon kwaraza shida ya tsufa ko tafiya ma bashiyi" cewar sarki mahraz sarki dujalu yayi murmushi ya mayar masa da amsa ya kai aarki mahraz duk yanda kake tunanin wanan gasa ta wuce nan domin kaf sarakunan duniyar mutane da aljannu, dodanni zasu taru anan duk wani tsohon hatsabi zai nuna kansa don haka kada kayi mamaki dariyar shamharu ce ta katse musu firar tasu kafin bisani ya fara magana karyarku tasha karya duk da nasan ku ba kananun hatsabibaine ba kowani babba da babban sa don haka ni shamharu shahararre nine mamallakin kundin tsatsuba nine muruccin kandutse nine gagara badau kuma ni zan ci wanan gasar ta gwarzon kwaraza kamar walkiya ya bayyana cikin shiga ta tsaffin matsafa wanda suka amsa sunansu tsawarce da ya dakawa shamharu itace ta jawo hankalin manya-manyan hatsabiban saidai kafin a ankara dayawa daga cikin mayakan sun duke bisa gwiwoyinsu " lallai yau tamu ta kare tunda abin har ya kai ga bayyanar MARGANU" cewar wani tsohon mayaki wanda kana ganinsa kasan yaga jiya yaga yau anjima ana damawa dashi marganu ya fara magana da cewa ni MARGANU dan jaddadu jikan gundugurki magallabin maza nine zan cinye garsar gwarzo gwaraza... Zan cigaba

BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 3:
MARGANU ya cigaba da magana dalilina kuwa na cewa ni zan cinye wanan gasa ta gwarzon gwaraza ku saboda ni na ziyarci yakin makashin maza da gallabar maza kuma ni naziyarci kogon zakun kogon da ya gagari mutum da aljan shiga nine mutuman da ake zaton ya mutu bayan shekaru aru-aru na dawo dan haka ni yafi can-canta in zama gwarzon gwaraza guguwar da ta karade filin ita ta tsaida marganu daga maganar sa nan take kowa ya daga kansa sama ba komai ne ya haddasa wanan guguwa ba face kadawar fukafukan wani kato aljani ba ajima ba aljanin ya sauko kasa wani kyakyawan dogon dattijo ya duro daga kan aljanin durowarsa ce ta haifar da wata kura yayin da kurar ta yaye sai gashi ya bayyana cikin shiga mwadda ta nuna murdadden jikinsa irinna manyan sadaukan da suka amsa sunansu duk da cewa ya fara tsufa amma hakan baisa ba kuzarinsa ya ragu yana nan yadda yake ga wanda suka sanshi cikin murya mai amo ya fara magana cikin takama da tsantsar nuna isa yana mai nuna shamharu da marganu yatsa kai tsaffin banza kusani ku baku isa ku kira kanku da gwarazan-gwaraza ba kai shamharu idan baka san ko ni wanene ba ka tambayi yayarka tsohu mundiga da danta kulkulu zasu baka labari na nin e SADAUKI makashin dodo kusumu da sarki jata nine mamallakin zoben sihiri dan haka nine yafi cancanta da in zama gwarzon gwaraza, karan takun dawakan azabar da sukajine yasa kowa juyowa wohoho nan take kallo ya koma sama abida suka gani shi yasa kowa shiga taitayin ba komaine suka gani ba face jarumi shaddadu hannunsa na rike da mashin galilul haraz bayansa kuwa ziya'ul hak ce ke take masa baya gefen damarsa kuwa sadauki hantarune hannunsa na rike da takobinsa saiful lujara hagunsa kuwa sadauki hulkas ne mai hular lamsara a gefensa kiwa yar uwarsa ce jaruma siyama suna zuwa tsakiyar filin suka ja birki kura ta tashi sama lallai idan har kayi karfin halin duban fuskokin taron hatsabiban dake wanan filin zakaga du kowa ya kara shiga taitayinsa domin miyagun makaman dake hannnun mazanjiya bayan shiru na dan wani lokaci sai aka karajin takun sawayen wasu dawakan azabar kallo ya kara komawa sama gani wasu kyawawan mutane mace da namiji sun tunkaro filin sunyi shiga irin ta mazajen fama duk dacewa macen tayi shiga irin ta kamala domin ta rufe duk jikinta idan ka dauke kyakyawar fuskarta suma sukazo suka ja turjiya bayan shiru na dan wani lokaci sai namijin ya fara magana cikin murya mai amoyana cewa ....

BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 4;
Kyakyawan saurayin ya fara magana cikin izza da takama nasan dayawa daga cikinku sun sanni musamman ma wadan da suka halarci wajan gasar GAGARA BADAU nine jarumi HASANUL BASARI makashin maza nine jarumin da ya zamewa sarki hamadu alakakai nine zakaran gwajin dafin da ya lashe gasar gagara badau wanan kuwa da kuka gani matatace jaruma safila uwar maza duk wanda ya halarci gasar gagara badau to yasan rawar da ta taka a tare da ita akwai rantsatsiyar takobin ta wanda ta gada daga wajan mahaifinta dirar wasu fararen dawakaine ya katse masa maganar sa hakika kowa na filin yayi mamakin ta yadda wadanan dawakai suka tsallake mutane da aljanun kai hadama dodanni suka dira a tsakiyar wanan filin nan da nan kowa ya zuba ido domin yaga wasu hatsabibanne wanan kuma da me suka zo yayinda matashiyar kurar da ta tashi sakamakon dirar dawakan ta yaye sai gasu sun bayyana cikin fararen tufafi dukkan jikinsu a rufe yake ba'a ganin komai sai idanuwansu dukkansu suna rataye da zabga-zabgan miyagun takubba duk ba wanan ya ja hankalin mutanen da ke filinba abinda aka rubuta a jikin takubban nasu shine yasa kowa dake filin ya kara shiga cikin taitayinsa idan ka cire jarumi basaru da matarsa safila wanda su maimakon firgici saima murmushi da sukayi na ganin "yan uwansu musulmai abinda aka rubuta a tkobin shine cikin manyan baki SAIFUL ISLAM nan take daya daga cikin jaruman ya yaye fuskarsa ga wanda ya karanta littafin saiful islam nan take zai shaidashi nan take ya fuskanci mazanjiya kafin ya fara magana cikin murya mai amo da yadda dakai yaku mazajen jiya ina mai baku shawara da ku bace mani da gani tun kafin a fara wanan gasar domin duk jarumin da ya sake mukayi arba dashi a wanan gasar har ya yadda makaminsa ya hadu da takobina ta saiful islam to hakika makaminsa zai narke domin kunfi kowa sanin takobina tana tarwatsa duk wani sihirin tsafi komin karfinsa saboda haka ina tausaya muku domin duk duniya babu wanda bai san irin bakar wahalar da kuka sha ba wajan mallakar wanan makamai ba na mazan jiya da irin rayukan da suka salwanta na masoyanku dama abokan gabarku dan haka ina mai shawartarku da kucire rai daga lashe gasar gwarzon gwaraza ....zan ci gaba.
JARUMAN GASA SUN GAMA HADUWA SAURA SARAKUNA

BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 5:
Wanan maganar da jarumi HUZAIFA mai takobin saiful islam ba karamin batawa mazanjiya rai tayiba wanan ne dalilin da yasa ma sadauki HANTARU ya zare takobinsa dalilinda yasa haske mai daukar ido ya cika filin hade da wani yanayi na tsohon babban sihiri kafin ya afkawa sadauki huzaifa sai yaji an ruko rigarsa ta baya cikin fushi ya jiyo abinda ya gani shi yasa jikinsa yayi sanyi jarumi shaddadu ne ya rike masa riga yayi masa murmushi kafin ya fara magana me kake ci na baka na zuba ai inda ba kasa nan ake gardamar kokowa ka kyaleshi lokaci shine zai banbance, jarumi hantar yayi kwafa kafin yayi ajiyar zuciya sana ya meda takobinsa cikin kube dalilin da yasa yanayin wajan ya komo dai-dai hayaniyace ta mamaye wajan.
Abin zai baka mamaki idan nace maka duk wanan cakwakiya da take aukuwa tana faruwane a wani shimfidedan katon fili wanda duba daya zaka masa kasan cewa an tanadeshi ne kawai saboda rana irinta yanzu wato saboda gasar gwarzon gwaraza filin zagaye yake da kananu kujeru mararsa adadi iya ganin mutum sana bangaren sama kuma wani dansamaline wansa akayi shi da zinare samarsa shake take da manya -manyan kujeru na sarauta wanda akayisu da zallan zinare cikin katuwar shema wanda akayita da zare na alharini aka mata cin zanzana da ruwan zinare hakika wajan ya kawatu kallo daya zaka yiwa wajan kasan an tanadesane saboda hamshakan fitattun sarakuna wanda sunansu ya shahara wanan fili na musamman an ginashi ne a bayan birnin ruma shine babban birni a daular rumawa inda babban sarki nawwar ke mulki bairnin da duk duniya anyi ittifakin babu birnin da ya kaishi kyawu da tsari hade ma da kwanviyar hankali abinka da birni da yake gefen teku duk wani tattalin kasuwancinsu ya ta'alaka da wanan teku wanan ne dalilin da yasa idan har kayi duba zuwa ga gabar teku a yau zaka ganta cike take da manya-manyan jirage kowani jirgi da dakwai tambarin kasarsa a manne jikinsa sanan akwai hatsabiban dakaru da matsafa dake tsaronsa karan bude kofar birnin da ita kanta abin kalloce shi yasa dukkan hatsabiban mutane da aljannu da dodannin juyowa suna jiran suga wanene zai fito karan tambura,algaita da kakin sune suka fara wa mutane sallama sana suka hango wata tawaga tana fitowa daga birnin nan take kowa kallo ya koma sama idan kayi duba ga fuskokin mutanen dake wanan fili zaka ga tsantsar mamaki a tattare dasu ba komaine yasa su mamaki face wasu aljannu masu siffar batoyi da suka gani sun masa rumfa tabbas wanan inuwa ita akeyiwa kirari....


)
BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 6:
Tabbas wanan inuwar ita akewa kirari da inuwar mutuwa domin duk wanda ya tunkari wanan rumfa da nufin kawo wargi ga wanan hashakiyar tawagar sunan sa gawa yayin da suka iso filin nan take mafiyawa daga cikin aljannu da dodannin da hatsabiban mutanen dake filin vikinsu ya duri ruwa saboda duk wanda ya kwana ya yini a duniyar hatsabibanci to yasan wanan sarkin "kai sarki hamad mai turnuku fadan ibilisai, gagarabadau hamshakin sarki" cewar jarumi basari hakika bakaramar wahala da azaba ba muka sha a hannunsa yayin gasar gagara badau badan mun nemi taimakon ubangijin musulunci ba da tuni ya shafemu daga doron kasa jaruma safila ce tayi wanan maganar taku yake dai-dai cikin takama da nuna isa ta hamshakan sarakuna yana tafe ana shimfida masa wani tattausan kilishi wanda akayisa da jan alharini ya tunkari wata jibgegiyar katuwar kijera wadda akayita da zallan zinare ya zauna ya harde kafin ya ida gyara zamansa ne aka karajin wasu tamburan da algaitu, kakaki kowa ya kara juyowa domin ganin wanene zai kara bayyana wata tawagarce ta kara tunkaro filin kowa ya zuba ido domin ganin ko wani sarkine wanan domin tawagar ta nunka ta sarki hamard yawa da tsaro yayinda tawagar ta matso kusa abinda suka gani shi ya kusan girgiza kowa dake wanan filin sarakuna ne guda biyu tafe suke suna fira cikin annashuwa sunyi shiga irinta sarki harmad sak ga wanda ya karanta littafin mutum da aljan da littaffin mazanjiya farat daya zai gane wanan sarakun SARKI LAFFARU ne da SARKI ALKASIM tafe suke cikin tafiya ta hamshakan sarakuna wanda suka amsa sunansu a wajan jarumta, tsafi, girman kai, kai da ka gansu kasan basa shakkar duk wani mutum da aljan kai hadama dodanni suma suka samu kujeru irinna sarki harmad sak suka zauna suka kame.
Abinda ya ba kowa dake wanan filinamaki shine ganin har yanzu dakwao sauran kujeru har guda biyu wanda suka rage babu kowa a kansu nan take mutane suka zuba ido domin gani wasu issassun sarakuna ne zasu kara bayyan....

BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 8.
Bayyanar labulayen da suka tokare da sama ce ta sa kowani hatsabibi dake cikin wanan fili kara shiga hankalinsa sanan kowanne daga cikinsu ya ware idanunsa yana mai kallon wanan abin mamaki labulen bakine sidik idan ka daga kanka sama zaka iya cewa ya tokare da sama domin iya ganinka shine zaka gani zukatan kowanne daga cikinsu na saƙa masa abubuwa da dama shin dama can wanan labule yana nan idan yana nan me yasa bamu ganshiba tun zuwanan mu lalle wanan aikine na tsafi kafin kowa ya dawo da nutsuwarsa ne sarki nawwar ya kara tafa hannunsa karo na biyu nan take wanan bakin labule ya fara nannade kansa yana yin sama abin da "yan kallo suka gani shine ya kara rudasu kuma tsabar mamaki ya kara gauraye fuskokinsu tabbas sarki nawwar ya cika hatsabibi ba komaine ya bayyana ba face yan kallo manya da yara kai hadama tsaffi suna ta hayaniya da iface-iface inda hayaniyarsu ta cika filin kowa ya kara ware idanunsa domin gani wanan abun mamaki ganin wadanan "yan kallo, jinsi ukku ne yammacin filin jinsin mutanene wanda suka hada manya da yara da tsaffi kabilu iri-iri, yare kala-kala, sanan ga banbancin launin fata wasu bakake, farare, jajaye, kai hadama ruwan tarwada, kowa na fadin albarkacin bakinsa kowa na ziga gwaninsa kallo daya zakayiwa wanan mutane kasan sun fitone daga nahiyoyi daban na duniya tabbas wanan gasa babu in da labarinta bai kaiba, ɓangaren kudu kuwa cincirodon jama'ar aljannu ne wanda suma kar mutane da ganisu kasan sun futone daga mabanbantan kabili, addinai, da yare, dakuma nahiyoyi, wasu bakake wasu farare wasu jajaye wasu munana, wasu ma fukafuki garesu wasu ƙahonnine a kawunansu haia zaka rinka ganinsu manya da yara da tsaffi, bangaren arewa kuwa dodannine suma kamar aljannu kabilu ne iri suma sun fito ne daga mabanbanta nahiyoyi kowa na koɗa gwaninsa saidai su dodanni ba kamar mutane da aljannu bane su kowanne daga cikinsu kan yana daure da wani jan kyalle wanda akyi masa wani hatimi na tsafi wanan jan kyallen yana nufin yarjejeniyar dake tsakaninsu da sarki nawwar na cewa bazasu taba cutar da wani ba imma bako ko dan gari duk kuwa wanda yayi yunkurin cutar da wani to nan take wanan hatimin na jikin wanan kyalle zaiyi haske yanyin haske kuwa nan take wanan dodo zai kubura ya fashe ga duk dodon da aka kamashi ya cire wanan kyalle to sunansa gawa domin akwai hatsabiban matsafa da mayaka da sarki nawwar ya tanada wanda zasu daka masa wawa su halaka shi.
INA YIWA KOWA MURNAN ZAGAYOWAR WANAN RANA MAI ALBARKA.


Umar Abdulhadi Mati ▶ DANDALIN LITTATTAFAN YAKI AND HAUSA NOVEL BY (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 9.
A gabashin filin kuwa katuwar rumface wadda sarakuna suke zaune a cikin ta a gefen damar wanan rumfa kuwa wata karamar rumfa ce wadda take shake da manya-manyan kujeru zaune akansu wazirai ne da hamshakan attajirai, da manya-manyan hatsabiban bokaye wanda suka shahara, hagundin wanan rumfa kuwa wani dogon membari ne wanda shima cike yake da wasu kananu kujeru a gaban kujerun kuwa wani karamin teburi ne da yake dauke da manya-manyan takardu zaune a kan kujerun kuma alkalan gasa ne sanye suke da wasu fararen kaya masu shige da babbar riga sanye akansu wasu huluna ne na saki wanda akayi su da gashin ragon dawa kallo daya zakayi musu kasan lallai mutanen kirkine domin dukkansu dattijaine masu kamala da kwar jini sanye a idanuwan kowanne daga cikinsu wani sihirtaccen gilashin wanda yake zuko duk wani abu na nesa ya dawo kusa kaganshi yadda kasan ka taba hakan zai basu damar ganin duk wani abin dake faruwa a wanan fili ba iyakar nan amfanin wanan gilashi ya tsayaba yana taimaka musu wajan ganin duk wani algus da jarumin gasa yayi domin su samu samar yin hukunci bisa adalci alkalan gasar sun fito ne daga bangare biyu akwai manya-manyan likitoci wanda aka yadda dasu a wanan kasa ta ruma sanan akwai hatsabiban bokaye wanda suka san duk wani tuggu na sihiri da makircinsa.
Zagaye da filin kuwa wasu hatsabiban kasurguman mazajen fama ne tunjim cikin sulke kallo daya zakayi musu kasan sun cika jarumai kuma hatsabiban matsafa domin bayan sulken dake jikinsu kuma damatsansu cike suke da guru da laya wanda hakan zai nuna maka a shirye suke tsaf dasu tunkari duk wani hatsabibi hakika tsarin wanan katon fili na gasa yayi ga duk wanda ya kalli wanan fili zai haka zai bada wanan sheda.
Tashin sarki nawwar ne tasa hayaniyar dake wanzuwa a wanan fili ta lafa sana daga baya ya daga hannunsa sama lamarin da yasa filin ya ida yin shiru kenan kama mutuwa ta gitta sana ya fara magana cikin nuna isa da izza abin da zai baka mamaki shine ....

BAKANDAMIYAR GUMURZU
Littafin Umar Abdulhadi Mari
Ebook created by Shuraih Usman
Published at www.hausaebooks.com.ng


(IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter11.
Yayin da sarki nawwar yazo nan jawabinsa sai ya tsaya sana ya koma kan kujerarsa ya harde yana mai fuskantar filin gasar lokacinne shugaban alkalan gasa ya tashi hannunsa na rike da wani katon karfen da aka kwakware tsakiyarsa sana karshensa aka fadadashi kamar kaho ya kafa wanan katon kafen a bakinsa ya fara magana nan take muryarsa ta karade daukacin filin ya fara magana kamar haka yanxu batare bata lokaciba zamu fara wanan gasa ta gwarzon gwaraza don haka muna umartar jaruman gasa da su bar wanan fili su tafi wajan da aka tanadar musu nan take jaruman gasa suka rabu kashi ukku kowani kashi ya tunkari wani babban daki da aka tanada na musamman domin jaruman gasa mutane suka shiga nasu aljannuma haka dodannima haka kowani rukuni daga cikin rukunannan ukku sai da sukayi mamaki mutuka yayin da suka shiga wanan dakin gani bangon dakin cike yake da makaman yaki kala-kala da wanda suka sani da wandama basu taba ganiba kafin daga bisani suka zauna suna mai saurare nan take wanan alkalin gasar ya dauko wata takarda da akayi ta da jemammar fata wadda take dauke da sunayen jaruman gasa ya fara magana kamar haka wanda zasu fara fafatawa a yau sune SADAUKI DALƘUS da JARUMI SALJAM wanda dukansu sun fito ne daga jinsin mutane nan take "yan kallo suka zuba ido domin ganin wanan sadaukai ba'ajima ba sai gasu sun bayyana suna mai fitowa daga wanan katon daki na jaruman gasa tabbas kowa na filin saida ya girgiza dagani sadauki dalƙus domin shine ya fara fitowa daga wanan dakin sadauki dalƙus bakar fata ne kuma duk inda ake neman kato to sadauki dalƙus yakai gashi dukkan illahirin jikinsa a murde yake yadda kasan an jera masa duwatsu gashi da tsawo kallo daya zaka masa kasan cewa jarumin gaskene kuma fasa taro yana bayyana filin ya dau shewa da ihu yana zuwa tsakiyar wanan fili ya ja tunga yana mai dagawa masoyansa hannu nan take filin ya kara kaurewa da shewa, bayyanar saljam ce ta kara sawa filin ya kara kaurewa da ihu inda mabiyansa suka fara kiran sunansa saljam, saljam,.. Tabbas shima jarumi saljam ba bayaneba wajan girman jiki da murdewa hakama kwarjinisu da dalƙus zai iya zuwa daya banbancinsu da dalkus kawai tsawo ne domin shi saljam yanda kasan ragowar samudawa haka yake kafin ka samu mai tsawonsa a mutane sai ka jima, da bayyanar jarumi saljam aka buga kugen fara gasa nan take suka fukanci juna sai a lokacinne suka ƙarewa junansu kallo tabbas ko ba'a gwadaba sun san za'a sha fama kafin daya daga cikinsu ya illata

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment