Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafina daya 1
Marubuci Shuraih Usman 99%
Ebook created by Shuraih Usman
Sold @ www.hausaebooks.com.ng


SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@hausaebooks.cf
Part A
.
.
Kimanin shekaru dubu daya da suka gabata a nahiyar sudan anyi wata birnin mai suna yemen birnin yemen babban birni ne don duk nahiyar babu wata birni data kaita girma, tattalin arziki da yawan dakarun yaki,
.
Birnin yemen na karkashin mulkin wani adalin sarkine ma'abocin addinin musulunci, sannan daukkan jama'an wannan birni Addini daya suke bi, itace kuwa Addinin Islama
.
Sarki ayyub ya kasance yana da matan aure hudu sannan kuma yana da ilmin Addini daidai gwargwardo kuma ya kasance yana kamanta adalci a tsakanin matayensa bil haqqi
.
Wayannan matayen nasa kyawawane na gaban kwatance dukkansu sun fito ne daga manyan gida in ka dauke amaryarsa mai suna Taufidatu, itace kawai ta kasance ya ga wani talakan masinci
.
Mahaifinta sunansa Imran kuma talaka ne don kuwa tun yana karami ya ke bin mahaifinsa a rafi, kuma da wannan sana'ar suke ci sannan susha har takai ga ma sun biya wasu bukatunsu
.
Ahaka imran ya taso har mahaifinsa ya rasu shi kuma ya riqi wannan sana'a da kima ya kuma jajirce ba'a dade ba ya auri wata kyakkywar mace wacce saboda saban kyawunta sai da akayi gasa kafin ya samu aureta
.
Al'adar wannan garine a duk lokacin da aka samu wasu suna son mace daya toh gasa akeyi don a fidda gwani, wannan gasar bata komi bane face gasar jarumta, shi dai imran da farko ba jarumi bane amma saboda tsananin kaunarsa ga Halimatu hakan yasa ya dage lallai sai ya shiga wannan gasa
.
Da ranar gasa tayi, mutane da yawa sun taru don kashe kwarkwatar idanuwansu, yayin da aka zagaye filin da wani yanki na jan kyalle, a dokar wannan gasa duk wanda ya fita daga cikin filin ko ya kama jan kyallen nan, ko kuma ya bari ta taba jikinsa toh ya fadi take zai fito daga cikin filin
.
Yadda akeyin gasar dai shine dukkanku za'ataru ku a cikin wannan fili duk wanda ya samu nasarar fitar da dan uwansa daga filin har ya rage babu kowa a filin sai shi kadai toh shine zakara
.
Zaratan Jarumai ne da sadaukai masu kirar sadaukan taka sannan sai kirba kirban katti sun kai su hamsin sai kuma masunci Imran wanda duk cikinsu shine san karami kuma baya da kirar jarumtaka a jikinsa,
.
Hakanne yasa mutane sukai tai masa dariya , koda aka buga gangar fara gasa sai filin ya haustine karajin mazaje ya yawaita kura ta turnuke, don kuwa sai dai kaga kato ya daka kato sama ya yi jifa dashi wajen filin , take wannan da'akayi jifa dashin zai karkade jikinsa yaje gefe don kuwa ya riga daya fadi
.
Shi kuwa imran cikin ikon Allah sai ba'a samu wani wanda ya dumfare shi ba, har dai jaruman da suke filin suka rage basufi su goma ba, can sai wani jarumi ya dumfari imran, take sai imran ya fara addu'a tun kafin jarumin kariso
.
Ai koda jarumin ya kariso sai ya kaiwa imran sura nan kuwa yayi nasarar kama mai wuya ya daga shi sama ya rungi tafiya da shi har yazo daidai wajen jan kyallen nan, shi kuwa imran sai wutsil wutsil yake da nufin ya kwace kansa amma katon yafi karfinsa , abisa dole yayi lamo tamkar ya suma
.
Koda katon yaga ya sumar da imran sai ya sake shi ya fadi a kasa sannan ya daga kafa da nufin ya taka shi ya fice daga filin , cikin shammata sai imran ya farka sannan ya matsa wa kafar wannan jarumi ai koda kafar wannan jarumi tabi iska sai yayi tangal tangal saakamakon rinjayi yarshi da kafartayi, shi kuwa imran koda yaga haka sai yazo ya bangeje wannan jarumi da kafarsa take jarumin yafadi ajikin wannan jan kyalle daya zagaye filin ai nan take jama'a suka dau shewa
Cikin jin kunya wannan jarumin ya fice daga filin
.
Haka aka cigaba da wannan gasa har ya rage saura imran da wani narkeken kato kadai a cikin filin, shi dai wannan kato ana kiransa da suna Narkul kuma duk cikin birnin yemen babu wanda yakaishi girman jiki, asalinsa ma zuwa yayi daga wata kasar,
.
Narkul ya dubi imran ya kece da dariyar farinciki don kuwa shi yariga da ya aiyana akan ya gama cinye wannan gasa don har ya fara hango amaryarsa a cikin dakin shi,
.
Narkul ya dumfari imran gadan gadan shi kuwa imran sai zulliya da gociya ya runga yiwa narkul take mutane suka ringa kiran sunan narkul, koda narkul yaga imran na neman ya bata mai lokaci sai yayi kukan kura ya falfalo da gudu don yayiwa imran kwab daya ya fiddashi daga filin ,
.
Alokacinda imran yaga narkul ya falfalo da wannan azababben gudun sai dai hankalinsa yayi matukar tashi, dai dai ya rage baifi saura taku goma b ba narkul ya riski imran sai imran shima falfalo da gudu yana dumfarar narkul, ai nan jama'a suka zuba idanu don suga waye zaa kayar
.
Koda ya rage baifi saura zira'I daya ba su hadu sai imran ya tsuguna akan guiwowinsa cikin wani irin salo na ban mamaki ya bi ta tsakanin kafafuwan narkul ya wuce, shi kuwa narkul saboda karfin gudunsa yama kasa tsaida kanshi don kuwa yayi turjiyar amma sai da ya karisa wajen jen kyallen nan har ya ballata
.
Ai koda da ganin hakan sai jama'a suka dauki shewa kowa yana ma imran jinjina
Toh kunji yadda imran yayi gwagwarmaya akan mahaifiyar Taufidatu,
.
Basufi shekara biyu ba Allah ya arzucesu da kyakkyawar yarinya inda suka saka mata suna taufidatu, tun taufidati tana karama take da matukar kyawu don kuwa saboda kyawunta ne ma masunci imran ya hanata fitowa koda bakin kofar gidanne ahaka har ta girma
.
Wata rana ta tafi icce a jeji ta saba takan rufe fuskarta da mayani ta tafi yin iccenta kuma izan ta tafi tunda safe bata dawowa sai dare hakan yasa take daukar abincinta da abinshata ta tafi dasu wannan jeji,
.
Wata rana ta fita icce kawai sai taga wata barewa tana gudu dakyar a kafar barewan na dama akwai wani kifiya take tausayin wannan barewa ya darsu a zuciyanta
Barewar ta zube kasa sakamakon raunin dake kafarta,
.
Taufidatu ta karisa wajen barewar sannan ta zare wannan kibiya daya ke kafar barewar, har hawaye na zuba a fuskarta ta cire mayanin data rufe fuskarta ta daure daidai wajenda yake zubar dai jinin, motsi taji abayanta ta cikin surkukin daji
.
Hakan yasa ta waiga don taga wanene nan tayi arba da sarki Ayyub koda sarki Ayyub yaganta sai ya dimauce nan danan ya ce " tsarki ya tabbata ga Allah daya halicci wannan kyakkyawa"
.
Sarki ayyub yaji ya kamu da tsananin son taufidatu ya tambayeta gidan da suke da zama ta bashi amsa , ko takan barewar daya biyo bai bi ba yana komawa fada ya shirya yanufi gidan don neman auren taufidatu, babu wata gardama masicni imran yaba shi aurenta
.
Ranar auren anyi shagali kala kala, don kuwa duk cikin matan sarki ayuub babu wacce yake matukar kauna tamkar Taufidatu
.
Wannan ce ta sanya hassada hade da kishi suka darsu a zuciyoyin wayannan kishiyoyin nata
.
Sarki ayyub baya da wata matsala sannan talakawa najin dadin mulkinsa ayayin da attajirai da masu hannu da shuni ke matukar bakin ciki
.
Kunsan ance kowane dan adam adunua bazai rasa wata matsala ba toh hakan take ga sarki ayyub, don dhi matsalar saya ce
Matsalar saiki ayyub itace rashin samun haihuwa
Yakan tara manyan malaman kasar yasanya su roka masa Allaj yabashi haihuwa a bangarensa kuwa baya samun isasshen barci sakamakon raba dare dayake yana rokon Allah akan yasa mu magaji
.
Izan kuwa ya zauna a waje guda kuwa babu abinda yake face tunanin irin duk arzikinan daya mallaka da kuma shuhurar dayayi a fadin nahiyar nan yasan cewa yana mutuwa shi kenan za'a dibi arzikinsa wanda shi bai masan yawansu ba , a raba wa matansa saura kuma asaka a baitulmali, daga nan shikenan an manta da shi kenan
.
Wata rana a fada ana ta fadanci sarki ayyun ya kacire bisa wata kujera ta alfarma wacce aka sana'antata da zallar jauhari sannan aka mata cinbaki da duwatsun yakutu a gefensa kuwa waziri ne sannan sai galadima a gefen hauninsa
.
A sannan ne wata mummunan kara mai kama da sautin jaki ta bayyana koda jin wannan kara sai hadimmai da dakaru suka fara zarya a cikin wannan suna neman daga inda karar yake fitowa,
............99%
........
....
..
.
Toj anan zan tsaya kar dai ku manta nidinne Shuraih Usman inkiya shuraih 99%
A littafina na SADAUKI UBAN SADAUKAI
Daga hausaebooks.cf
.
SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@hausaebooks.cf
Part B
.
.
Koda wannan kara yayi kamar dakiku ashirin sai ya dauke dif tamkar bai taba wanzuwa ba
Wazirine ya dubi sarki ayyub sai yaga ko gezau ba yayi ba, sannan fuskarsa yana duban gaban fada kai daga ni kasan yayi nisa acikin tunani
.
"Ranka shi dade " waziri yace
Firgigit sarki yayi sannan ya mike tsaye a matukar razane koda ganin hakan sai kowa dake wannan fadar ya mike tsaye
.
Sarki ya dubi jama'ansa a matukar tsorace yace da su
"Yaku Al'ummar birnin yemen shin idanuwanku basu gane muku abin dana gani bane, "
Koda jin haka sai dakaru ,hadimai da yan majalisa duk suka hada baki suka ce
"Ba muga komai ba ranka shi dade"
Nan take sarki ayyub ya dubesu yace da su
"Yaku mutanina kuyi sani cewa dazu da wannan kara mai amo mara dadin sauraro ta bayyana a wannan fada, to kusani a sa'ilin ne wani haske ya bayyana a gabana take wannan hasken ya rikide ya koma izuwa wani kyakkyawan saurayi wanda ko atarihi ban taba jin labarin sa ba
.
Saurayin ya dubeni yace dani "yakai wannan sarki mai tarin iko ina mai yi maka albishir da abubuwa guda biyu, na farko ina mai sanar dakai nan da kwana bakwai daya daga cikin matayenka zata sami cikinka,
Koda naji ya ambata cewa zan sami haihuwa sai na kamu da tsananin farincik, ai bansan lokacin dana tari numfashin wannan kyakkyawan saurayi nace da shi
"Ya kai wannan kyakkyawan saurayi gaggauta sanar dani shin waye kai?" Nan take wannan saurayi yayi murmushi sannan yace " sanin ko waye ni ba shine mai muhimmanci ba, n manzo ne kuma zan isar da sakon da aka aikoni da shi,
Abu na biyu dazan sanar dakai shine
.
Yaron da zaka haifaa zaizo da ababen mamaki da al'ajabi, sannan kuma zai shuhura agaba dayan wannan duniya har sai takai cewa kowa dake fadin wannan duniya ya sansa, kuma ya san sunansa, ammafa zai shiga cikin muggun yanayi don kuwa zaiga masifu da bala'u kala daban daban, akarshe sai ya yada addinin musulunci a gaba dayan wannan duniya"
.$
Koda kyakyawan saurayinnan yazo nan a zancensa sai yayi mani murmushi wanda sai da hakoransa suka fito take wani siririn haske ya daga cikin tsakiyan hakwaransa tun wannan hasken na fitowa kadan kadan har wannan hasken ya cika mani idanuwa har takai bana iyaganin wannan saurayi,
Lokaci guda sai wannan hasken ya bace bat , na nemi saurayin kasa ko sama ban ganshi ba, hakan ya tabbatar mani da cewa ba mutum bane
.
Sarki ayyub ya tada gwauron numfashi sannan ya dubi dukkan yan majalisarsa wayanda suke a matukar tsorace game da jin wannan labari da sarki ayyub ya basu, yace dasu
"Kunji al'amarin daya kasance dani a yayin da wannan karar mai amo da sauti ya bayyana"
.
Koda yan majalisa da sauran fadawa suka saurari wannan zance mai kama da al'mara daga bakin sarkinsu sai wasu daga cikinsu suka kamu da matukar farincikin jin cewa burin adalin sarkinsu zai cika, a sannan ne wasu kuma suka kamu da tsananin bakin ciki
.
****
Babban turaka ne wanda aka kawata shi ainun da ababen kawa
Zaune bisa kujeru na alfarma yan mata ne kyawawa su uku, dukkansu sunci ado ainun
Wayannan yan mata ba wasu bane face matayen sarki ayyub kishiyoyin Taufidatu
Dukkansu suna zzazaune a bisa kujeru na alfarma a yayin da suka yi zagaye da junansu yadda zasu fuskanci juna
.
Babbarsu mai suna zulaikha ta mike tsaye tace "yaku yan uwana, hakika kunsan cewa an sanar da mai martaba cewa daya daga cikin matansa nan da kwanaki bakwai zata samu ciki, shin idan cikin ya kasance ya bayyana ga abokiyar hamayyarmu fa, mene ne mafita
.
Ta biyun wacce ta kasance sunanta shamlika , ta mike tsaye ta fara bayani "hakika zulaikha kinzo da magana mai muhimmanci, ni kuma nan take zan warware wannan matsalar"
Zulaikha ta dubeta tace " tayaya kenan "
Murmushin mugunta shamlika tayi sannan tace "ta hanyar hana sarki ayyub kusantar taufidatu, ta hanyar kissa da kisisina "
.
Ta ukunsu wacce tunda aka fara wannan tadin bata ce uffan ba , sunan ta zarishatu ta dubesu sannan ta kyalkyale da dariya sai da tayi mai isarta sannan tace
" Yanzu akan wannan dan abin ne muke ta wani damun kawunanmu, sannan tayi shiru na dan lokaci kankani
.
Ita dai zarishatu bakaramar hatsabibiya bace don kuwa mahaifinta wani babban Attajirine wanda duk kasar yemen babu mai arzikinsa, ko sarki ayyub bazai nuna masa arziki ba sunansa Sirrinaddalib
.
Alokacin da sirrinaddalib ya cika shekaru ashirin da biyu a duniya sai ya kasance wata rana da daddare yana barci yayi mafarki acikin mafarkin nasa yaga wata kyakkyawar budurwa sai gudu take a cikin dokar daji kafafunta babu takalmi sai sossokewa take da kayoyi koda yai duba izuwa bayan wannan budurwa sai yaga wani murtukeken naman jejine yake biye da ita, koda wannan dabbar ya kusan cimma kyakkyawar budurwan sai sirrinaddalib yasha gabansa take wannan dabbar yayi tsalle da zummar ya fadawa sirrinaddalib
.
Firgigit ya farka daga wannan mafarki washe gari kuwa da sirrinaddalib yayi shiri ya fita farauta don kuwa halaiyarsa ce duk wata ranar alhamis toh wajibine agareshi sai yaje farauta shida hadimansa da dakarunsa kimanin su dari,
Ayayin da suka tsinci kansu acikin dokar daji sun
.
Sai ya kasance cewa sun zagaye wannnan jeji kaf amma ko bera basu kama ba, nan take sirrinaddalib ya harzuka yaba wa hadimansa umarni cewa acigaba da tafiya koda kuwa za'a kwana ne ana wannan farauta ba zamu koma da baya zuwa gari batare da mun kama wani dabba ba,
.
Suna cikin wannan zance ne sukaji alamun motsi a cikin ciyawa take kowannensu yayi shirin fada dakarunsa suka zare takubbansu masu kibbau suka dameta,
Wata kyakkyawar budurwace mai matsakaicin tsayi da matsakaicin jiki ta fito daga cikin wannan ciyayin tana mai falfala masifaffen gudu,
A bayanta kuwa wata murgujejiyar zakanya ce ke biye da ita ,
Koda sirrinaddalib yaga haka sai ya tuna da mafarkinsa nan take yabada umarnin a sakar ma wannan zakin ruwan kibbau
Dakiku kadan sai ga wannan zakanyar ta fadi rikica aa kasa gaba dayan jikinta kibiyoyine
.
Bayan kuran ta lafane attajiri sirranaddalib ya iso gaban kyakkyawan budurwannan sannan yayi mata nuni data hau kan dokinsa , batare da gardama ba kuwa ta hau,
Koda Sirrinaddalib da tawargarsa suka cikin gari sai ya nufi gidansa wacce aka kawata ainun har tafi gidan sarauta kawatuwa,
.
Yana isa gidansa ya sa kuyangi suka shiga da kyakkyawar budurwannan wacce har yanzu bai san sunanta ba, wani shashe na wannan gida
.
Sannan ya umarcesu da su gyarata suka wo mai ita falonsa,
Sirrinaddalib ne zaune bisa luntsuma luntsuman kujerun dake makare a wannan falo, sallama yaji sannan wata kuyangarsa tazo ta russuna akusa da shi tace ranka shi dade ga wannan bakuwar nan isowa
.
Murmushi kawai yayi sirrinaddalib ba karamin kyau yake da ba, don ba kowacce budurwace zata hada idanu dashi bata kamu da sonsa ba, shidai attajiri sirrinaddalib tunda ya hada idanu da fuskar kyakkyawan budurwar yaji taake ya kamu da matsanancin kaunarta
.
Takun sahu yaji alamun wani yana shigowa , juyawar da zaiyine yayi arba da abunda ya zauta mai kwakkwalwa, tunaninsa ya dushe, suciyarsa bugawa take da karfi tamkar zata faso kirjinsa,
.
Tana sanyene da kayan sarauta ayayin da wannan kaya ya kasance na zallar alharini ce, a kasan doguwar rigar wasu duwatsu ne masu maatukar daukar idanu, sa'adda wannan budurwa ta iso gaban sirrinaddalib sai ta zauna bisa kilishin da daben wajen rufi,
.
Attajiri sirrinaddalib yayi murmushi sannan yai mata inkiya da hannu kan cewa ta tashi ta zauna bisa luntsumemen kujeran dake gefenta, ba musu ta mike ta zauna bisa kan wannan kujera, zamanta keda wuya sai Attajiri sirrinadalib ya dubeta ido cikin ido sannan yace da ita"yake wannan kyakkyawar budurwa shin wacece ke , sannan daga ina kike mekike a cikin wannan daji mai hatsarin gaske,"
.
Koda budurwannan taji wannan batu sai ta fashe da kukan bakin ciki mai tsuma zuciyan dukkan mai sauraro, sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru ta bude baki tace "yakai wannan attajiri mai jin kai da tausayi lallai kayi sani cewa suna na Akisa mahaifina falkene, yakan yawata manyan kasashe fatauci, tun ina yar shekara biyar mahaifina ke futa yawon fatauci dani,
.
Wata rana mun fito fatauci ni da mahaifina da kuma sauran hadimansa su goma muka durfafi wannan birni naku don munji jama'a suna labarinsa ,
Asalin tafiyarma nice na takura wa mahaifina nace sai munzo sabida irin labarin birnin da nake ji daga bakin jama'a
.
Akan hanyarmu ta zuwa wannan birni naku ne a cikin wani jeji mai yawan dogayen bishiyu muka hadu da yan fashi,
Nan take wayannan yan fashin suka kashe gaba dayan mutaninmu ya rage daga ni sai mahaifina,
.
Shugaban yan fashin ya fashe da dariya sannan yace "yaku wayannan fatake lallai kuyi sani kunyi babban kuskure da har kuka biyo wannan hanya, "ya nuna mahaifna da yatsa yace "kayi sani yakai wannan tsoho lallai yanzu a take zan yi maka kisan gilla, sannan na maida wannan kyakkyawar budurwa dake gefenka ta zamto karuwata ,
.
Yana gama fadin hakan sai ya daga Addansa sama ya lumata a ruwan cikin mahaifina n
Mahaifina ya sulale daga kan dokinsa ya fadi kasa nan na kwala ihu sannan na na sauko daga kan dokina na durkusa na tallafo wuyan mahaifina, a sannan ne ya dubeni yace "yake yata hakika banso wannan abu ya faru garemu ba, nan ya saka hannu cikin aljihunsa ya dauko wata zobe ya bani sannan ya umarceni dana sanyata na mika hannu na karbi zoben na ciri zoben zan sanya a hannuna sai naga kan mahaifina ya langwabe,koda naga haka sai rungume gawan mahaifina ina mai rusa kuka shugaban yan fashin ya iso inda nake rungume da gawan mahaifina,
.
Kawai sai ya saka hannunsa ya tallafo wuyana sannan yace yake wannan kyakkyawa shin ba gani ba meye na kuka don wannan lalataccen tsohon ya mutu....."
Yana gama fadin haka shida yaransa suka fashe da dariya, inata fisge fisge don na kwaci kaina daga hannunsa amma na kasa
Nan idanuwana su ka kai kugunsa naga wata yar karamar wuka ,
Banyi wata wata ba na zaro wukar daga kubenta sannan na soka ma wannan dan fashin a cikin tumbinsa, take ya kwallara waata irrin kara sannan ya fadi matacce, koda sauran yan fashin sukaga abunda naiwa shugabansu, sai suka yun kuro kaina take na falfala da gudu na nausa cikin daji
.
Aduk lokacin dana waiga bayana sai naga sun kusa cimmini, hakance tasa na zage na dunga wannan gudu iya karfina, ba zato babu tsammani na jini na lume cikin kasa anan na suma
.
Dana farfado na tsinci kaina cikin wani wawakeken rami nafara kiciniyar fitowa daga wannan kwari dakyar na fito
.
Ina fitowane mukayi arangama da wannan zakin da kuka ceci rayuwata daga gareshi "
Koda akisa tazo nan a labarinta sai ta kara fashewa da kuka
.
Attajiri sirrinaddalib ya jinjina kai sannan ya dubi akisa yace "lallai na tausaya maki abisa rashin mahaifinki da kikayi, Allah ya jikansa,'
Ya sauke gwauron numfashi yace ........
Me kuma zaice
......
Yo anan zan tsaya sai wani jikon
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Hakkin mallak (m) keffians News Teller (K N T)
Tare da hadin guiwan hausaebooks page
SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@hausaebooks.cf
Part C
.
.
Attajiri sirrinaddalib ya jinjina kai sannan ya dubi akisa yace "lallai na tausaya maki abisa rashin mahaifinki da kikayi, Allah ya jikansa,'
Ya sauke gwauron numfashi yace "yake akisa kiyi sani a farkon lokacin dana ganki take naji ina matukar kaunarki kuma naji bazan iya jure boye sonki a cikin zuciyata ba hakance tasa na sanar dake kudirina da fatan zaki karbeni hannu bibbiyu,
.
****
Bayan andaura auren akisa da attajiri sirrinaddalib da watanni uku sai akisa ta samu juna biyu bayan wasu watanni ta haifi yarta kyakkyawa ,son kowa kin wanda ya rasa, a sannan ne wata rana da daare tana gyara kayanta acikin wani jakan fata, ba zato ba tsammani sai taga wani abu na walkiya koda ta lura da kyau sai taga she zoben nan ne da mahaifinta ya baTa lokacin dayake gargarin mutuwa
.
Murmushi tayi sannan ta dauki zoben ta sanya a hannunta tadan shafi zoben da gefen hannunta
Kwatsam sai wani murgujejen Aljani ya bayyana ya durkusa yace " Umarce ni yake shugabata koda akisa taga wannan aljani saita kadu ainun sannan ta juya da gudu da nufin ta fice daga dakin
.
Wannan aljanin yace da ita "bazan cutar dake ba ya shugabata hakika ni bawan kine akisa najin haka sai ta juyo ta dubi aljanin a tsorace tace "yakai wannan aljani shin ya akayi ka zama bawana"
$
Koda aljanin yaji wannan batu sai ya dago kai yace ni bawan wannan zoben dake sanye a hannunki ne, hakika duk wanda ya sanyashi kuwa toh zan kasance bawanshi"
Koda jin wannan batu sai akisa ta cika da matukar mamaki, tayi shiru sannan tace "toh nidai bana da bukatanka don haka kar ka sake bayyana mani"
.
Aljanin yayi murmushi yace "ya shugabata ai kece ki kayi kirana "
Ta yaya na kiraka akisa ta bukata,
Aljanin yace ai duk lokacin da kika shafa zoben
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment