Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje ba haka
ma jama ar gari suna nan tsawon kwanaki shida
baci ba sha sai addu a sukeyi Sarbila ta dubi dan
uwanta tace ya zama dole in ziyarci bokanya
Alimma dake tsaunin karkif domin samun wasu
bayanai suka shirya suka futo sai sukayi arba da
mutanen kasar baki daya sun taru a kofar fada
kai tsaye zasu wuce sai sarki maridu ya mike
yace yaku kannai na tabbbas mun yi laifi amma
mun karbi laifin mu.
.
Kuma mun saduda tabbas kin nuna cewa kece
birnin nan mu kuma mun tabbata hoto to kisani
matukar kikace ba zaki kara kula mu ba to kamar
yadda mukayi kwana shida a nan haka zamu
cigaba da zama baci ba sha har mutuwa ta
riskemu koda Sarbila taji zancen dan uwanta sai
tayi murmushi
tace lallai kun sami afuwa agareni na yafe muku
tace yanzu zanje in ziyarci bokanya alimma
domin karbo wasu bayanai kamar yadda Boka
karibu bn Kalab ya nutsa a kogin nilu domin
ganin aljani makus bn kwas domin ya karbi
bayanai tabbas tsakanin ni da shi sai wani ya
mutu a hadu ta gaba WAYE ZAI RAYU
Zan Cigaba Insha Allah
SIHIRTACCIYA Part 6
Littafi Na Daya 1
Marubucin Littafin
Abdul aziz sani m/gini.
Typing... by Goni.
Lokacin da boka karibu bn kalab ya nutse acikin kogin
nilu sai da yayi tafiyar kwana biyu da wuni daya sannan
ya isa wani katon gida duk da gidan acikin ruwa yake
kwata kwata babu alamar ruwa a jikinsa boka karibu ya
tsaya a bakin kofar gidan ya rufe idanunsa ya fara
karanto wasu kalaman tsafi take kofar ta bude ya kunna
kai cikin gidan tamkar gidan shi sai da yayi tafiya mai nisa
sannan ya isa wani katon fili sai akace masa maza ka
zauna sai ya fara kokarin zama a bisa ciyawa abin
mamaki lokacin da ya kai kasa sai ya ji shi akan wata
lumtsumemiyar kujera koda yayi duba izuwa filin nan sai
kawai yaga filin ya bace ya tsinci kansa a wani
tankamemen daki wanda aka kawata shi da kayan alatu
sai wasu tsala tsalan mata suka shigo suka kawo ma boka
karibu kayan ciye ciye da lashe lashe sai da yaci ya koshi
kawai sai ya ga aljani Shamsuna a gaban shi yana
babbaka dariya boka karibu ya daure fuska yace haba
babban abokina yazan tozarta a idon duniya kuma ka
ringa min dariya kuma kasan na zo neman taimako ne a
wajen ka aljani Shamsuna ya daure fuska yace abokina
kayi kuskure ne kar ka manta na fada maka duk garin da
ka tunkara in ka ga mutum daya ne ya iya tunkarar ka shi
kadai to kafin kayi yaki da shi lallai ka tuntube ni amma
sai kaki tuntubata boka karibu yace nayi kuskure ka
taimake ni ajani yace mafita daya ne ya zama dole kaje
dajin hadiqatul maut ka samo ma ulnar wanda ake ce
mar daskararren ruwa domin da shine kawai zaka iya
galaba a kan jaruma sarbila kuma kasani shiga dajin
hadiqatul maut daidai yake da tunkarar ajalinka kwata
kwata abubuwa uku zaka fuskanta amma sai kayi da
gaske zaka tsira da rayuwarka boka karibu ya budi baki
zaiyi magana sai aljani shamsuna ya daga masa hannu
yace babu lokacin tambaya kuma babu lokacin amsata
maza ka dauki hanya kawai.
.
al amarin Sarbila kuwa ta dauki hanya zuwa bakin tsauni
domin ta gana da bokanya Alimma lokacin da ta isa bakin
tsauni sai ta ja da baya tayi taku shida sannan ta falfalo a
guje ta daka tsalle ta kama tsaunin nan tamkar kadanga
haka take hawa tsaunin nan sai da sa a bakwai tana hawa
tsaunin nan sannan takai kan tsaunin kawai sai ta taradda
bokanya Alimma atsaye sarbila ta durkusa tayi gaisuwa
alimma ta dago sarbila tace na gaisheki tauraruwar
zamani lallai akwai aiki a gabanki babu lokaci yawaita
surutu lallai ya zamar miki dole idan har kina son kiyi
nasara akan karibu to sai kije dajin ikbal domin kishiga
kogon zum ki dauko wukar tarihi da itane kadai zaki iya
kashe makiyinki Sarbila za tayi magana alimma ta daga
mata hannu tace babu lokacin tambaya ki kama hanya
take ta dauki hayar dajin ikbal tayi tafiya na tsawon sati
uku sai ta riski dajin ikbal tun da ta shiga dajin taji komai
ya canza wani masifaffen zafi gami da wari tana tafiya zafi
na karuwa warin na karuwa tabbas akwai wani abu a
gaban ta
Kwatsam sai tayi kicibis da wani katon gwaggwan biri yayi
girman katuwar bishiya yana rike da wata katuwar
guduma sai gurnani yakeyi taja tunga birin nan ya daki
kirji ya sheko da gudu ta gyara tsayuwarta sai da ya kawo
mata duka tayi sulu ta shige ta osinsa ta ta mike tayi wuf
ta cakumi kugun birin duk girmansa sai da tayi sama da
shi ta sandara da kasa birin yayi ihu ya mike ya cafi
wuyan ta ya shake ta taji azaban shaka idanunta suka
furfuto ta farajin kanshin mutuwa ta fara ganin
manzannin mutuwa tayi na maza ta bude hannayenta ta
tara iya karfinta ta daki kunnuwansa tsananin radadi da
azaba da zafi birin yayi wurgi da ita tayi wani irin juyi a
sama ta kara gabza masa naushi a makoshi birin yayi
sama sannan ya fado kasa kamar rushewar gini amma
saboda naci sai ya mike ya ja da baya ya daki kirjinsa ya
falfalo da gudu ita ma Sarbila ta sheko da masifaffen
gudu za ayi haduwar karshe
Zan Cigaba Insha Allah
Admin Goni S AbubakarSIHIRTACCIYA Part 7
Littafi Na Daya 1
Marubucin Littafin
Abdul aziz sani m/gini.
Typing... by Goni.
Lokacin suka zo daf da juna sai birin nan ya kaima Sarbila
wani wawan duka ɗan kadan ta zame kuma tayi amfani
da wata yar karamar wuka ta karta masa a
makogwaronsa take jini yayi tsartuwa birin ya durkushe
kasa bisa guiwowinsa sannan ya fadi
matacce ko kallon shi batayi ba sai ta cigaba da tafiya
burin ta kawai ta isa kogon zum inda zata dauko wukar
tarihi sai da ta kwana ta yini tana tafiya sai ta isa wani
katon dutse dutsen baki kirin kamar zunubi amma babu
tsiro daya a kansa ta zagaye dutsen hagu da dama ta
tabbatar babu hanya matukar tana so ta wuce
ya zamar mata dole tabi takan dutsen nan ta kalli saman
dutsen ta tunkare shi ta fara kokarin hawa kamar aradu
taji wani tsawa gami da rugugi sai taji ance mata ke
karamar jaruma kada ki kuskura kice zaki hau dutsen nan
lallai zaki mutu taja da baya ta kalli saman dutsen sai tayi
arba da wasu murda murdan katti.
Tunda Sarbila take a rayuwarta bata taba ganin mutane
masu girma da kauri da tsawo irin su ba tabbas sai da
tasha jinin jikinta domin tasan karo da maza ba dadi wani
kato ya daga murya yace yadai karamar jaruma kin
karaya ne a haka zaki dauko wukar kisa wukar tarihi lallai
ina mai baki shawara da ki koma gida ki jira ranar
rushewar birnin ku.
.
Wadannan kalamai sun harzuka sarbila taji kamar katon
nan ya watsa mata wuta ta takarkare ta kwarara ihu taja
da baya tayi taku shida ta zaro wani kakkaifar gatari ta
daga murya
tace kuuu la anannu tsinannu lallai kunyi kuskure da
kukayi batanci ga kasa ta abin alfahari na tabbas sai na
wuce ta gabanku in kun cika mazaje ku tareni tayi
kururuwa ta falfala a guje ta kama hawa dutsen nan kai
kace tana gudu ne a shimfidaddiyar kasa kattin nan suka
zare makamai suka tunkareta sukayi wani irin mugun
haduwa mai sa rago futa aguje kamar tana girbin amfani
haka take gididdiba kattin nan daga tasa kafa ta make
wannan sai tasa hannu ta make wancan ko tayi amfani da
gatari ta faskara kato kafin kace haka sai ga kattin nan
suna gungurewa kasa tayi faca faca da jini kisa takeyi baji
ba gani yaki yayi yaki yan maza sun ji ba
dadi dole suka ja tunga suka tsaya cikin takama da izza
Sarbila take hawowa dutsen tana gama hawa
gaba daya kattin sukayi gaisuwa tayi murmushi tace dole
kanwarnaki ta kunna kai tayi gaba ko waigensu
bata karayi ba.
.
Al amarin boka karibu kuwa nausawa yake cikin daji
tafiya yake baji ba gani sai ya isa wata korama dama yana
fama da matsanancin kishi sai kawai ya nufi koramar ya
durkusa don ya dibi ruwa yana sa hannu caraf aka cafke
hannun aka fizgoshi cikin ruwan aka kuma nutso da shi
sai yayi arba da wasu dodanni masu kama da mutane
amma basu da kunnuwa sai wasu kaho guda biyu da
wata zabgegiyar bindi gawasu gatsogatson hakora kai da
gani kasan za suci
naman mutum danye boka karibu yasa wuka ya yanke
hannun dodon da ya rike shi dodan yayi kara yan uwansa
suka tasoma boka karibu yayi kururuwa ya afka musu
nan aka kulla cinikin rayuka boka karibu ya shiga aikasu
lahira yana musu kisan wulakanci wani abin takaici shine
dodannin sai karuwa sukeyi kamar tururuwa hankalin
boka karibu ya tashi domin yasan matukar za a cigaba da
wannan yaki.tofa zai kasa
domin jiki da jini sai kawai yayi wani
yunkuri yayi sama kamar kibiya sai gashi yahudo saman
ruwa kamar yana taka tudun kasa haka yake falla gudu
suma kuma haka suke binsa
kamar jela koda karibu ya waigo ya ga tarin yawan
dodannin nan wanda sun fi karfin lissafi sai yakara
dagewa da tsala gudu a saman ruwa tsananin gudu har
numfashin shi na neman daukewa saura kiris su cimmasa
ya daka tsalle sai gashi a tudu ya futa a cikin ruwan cikin
dodanin suka tsaya suna kallonsa suna lashe baki ya dube
su ya tintsire da dariya yace
kwalelen kare da hantar kura dole suka juya shi kuma ya
nausa cikin daji domin ya isa dajin hadikatu maut inda
zai samo ma unnar ruwan mutuwa.
.
Al amarin sarbila kuwa tayi nisa cikin tafiyar ta inda tazo
wata hanya da ta kasu biyu ta rasa wanne za tabi bayan
dogon tunani da wani dan nazari sai kawai tabi hagu sai
taji an fashe da dariya wata murya na cewa wayyo
yarinya cak ta tsaya har zata juya zata koma baya sai ta
sauya tunani bisa nazari da tunanin yaudara irin na
aljanu sai kawai.ta cigaba da tafiya kawai sai taji an kama
kuka ana cewa hatsabibiyar tayi nasara ta iso wani
dan yanki mai dauke da itatuwa gaba daya sai taji gurin
bata yadda da shi ba sai tasa nutsuwa gami da taka
tsantsan tabbas tana da gaskiya domin malafar wani
gawurtaccen
zaki ne da ya hana duk wata hallita a yankin kwanciyar
hankakli kamar daga sama sai ya diro a gaban jaruma
Sarbila ta kalli zakin nan taji tsigar
jikinta ya tashi sabo da tsananin muninsa sukayi ido biyu
da zakin nan
.
kamar an bashi umurni sai ya tunkaro ta a guje ya daka
tsalle da nufin danne ta tayi wuf ta kauce ya kara kai mata
bara nan ma ta kara zillewa ya kara yanko ta shi akaro na
uku ranta ya baci itama ta daka tsalle suka hadu a sama
tun a saman suka shiga kafsa fada.' sukayi dungure a kasa
zakin nan kamar mutum haka ya rika jera ma sarbila
naushi ta shaki wuyan zakin ta matse gam zakin yaji
azabar shaka yayi wani gunji gami da girgiza take yayi
watsi da Sarbila gefe a fusace yayi kanta baki bude take ta
kama surkulle tana karanta dalasumai na tsafi ta nuna
zakin da yatsa cak ya tsaya sannan ya karaso gurinta a
hankali ta shafi kansa sai kawai ta dare gadan bayan zakin
kamar doki sai ya nausa da ita cikin daji
.
Al amarin boka karibu bn kalab kuwa yana cikin tafiya sai
yaji an zabga mar duka a take ya fadi sumamme bai tashi
farfadowa ba sai ya tsinci kansa a daure tamau ga arnan
daji nan suna ta kaiwa da komowa da alama biki sukeyi
ba shi kadai ne aka kamoba sun kai su bakwai kuma a
gabansa daya bayan daya ake daddatsa mutum a jefa
namansa a wata katuwar tukunya da aketa faman dirka
mata wuta gadan gadan malamin yanka da
mukarrabansa suka tunkaro Boka karibu domin su yanka
shi a jefa a tukunya asha shagali lallai da bakar fitina a
nan hhhhhhh
.
Zan Cigaba Insha Allah
Admin Goni S AbubakarSIHIRTACCIYA
.
Littafi Na Daya 1
.
part 9
.
Lokacin da Sarbila taji kalaman da ake fada sai ta
harzuka take ta murza mabudin kofar tayi wani irin
kara sarbila taja da baya ta shirya shirin kota kwana
kawai sai kofar ta bude take sarbila ta kunna kai
cikin kogon ba tare da tsoro ba ko fargaba ba ta
iske kogon wani wawakene ya tafi har bata ganin
iya karsa ga wasu gumaka
masu suffar mayaka maza da mata kowane kamar
yayi magana tana tafe tana dube dube cikin natsuwa
sai taga wani kyakkyawan gunki kamar kirar jarumai
sai ya bata sha'awa sai tasa hannu ta shafi kan
gunkin kaico da sarbila tasan masifar da zata
tsokano ma kanta tabbas da bata taba gunkin nan
ba.
Taba gunki keda wuya sai ya motsa take ya dawo
mutum haka suma daukacin gumakan dake wurin
sai da suka tashi gaba daya sukayo kan Sarbila
makaman su azare tofa duniya makwanta rikici dole
sarbila ta zare takobi tayi fito na fito suka kacame
da yaki suka shiga kai mata sara da suka tana
karewa kuma tana mai da musu da martani abin
takaici shine idan
ta sare ma daya kai take zai durkusa ya dauki kansa
ya mayar da ita inda take ya cigaba da yaki lallai
wannan ba karamar masifa bace domin duk abin da
ta sara ta sari banza domin zasu dauka su mayar
suci gaba da yaki.
Sarbila ta fara gajiya inda tayi iya kokarinta taga tayi
nasara akan daya daga cikinsu amma ta kasa nan fa
gajiya ya riske ta inda mayakan nan suka shiga
tamola da ita sukayi mata
kaca kaca lallai sarbila ta san ta shigo kogon Zuum
kogon bala i can tayi karaji gamida kururuwa ta
daka tsalle ta tashi sama kamar tsuntsuwa sai
gashi tana taka kawunan mayakan nan cikin sa a
sai ta taka kan gunkin da ta fara shafa mar kai.
Cak ya tsaya sannan ya koma gunkinsa take sauran
ma suka kame kam suka koma siffofinsu na
gumaka a wurin ta zube saboda tsananin gajiya
tana maida numfashi daya bayan daya sarbila ta
kama wani mimimi da baki tana wani karanto
karatun surkulle take wani dan karamin gora ya
bayyana a gabanta take ta damki goran ta
kwankwadi ruwan cikin goran tana sha sai ta
wartsake ko kwarzane babu ajikinta sai ta mike ta
tunkari kofa na gaba ta isa jikin kofar sai ta tarar da
wata siririyar kofa wanda koda an bude ta to dakyar
mutum daya zai iya wucewa ta karema kofar kallo
gami da nazarinta sai tayi niyyar sa dan mabudin
don ta bude sai taji an kwarara uban ihu ana ce
mata kar ki kuskura ki bude lallai zaki budo ajalin
ki zaki hallaka
Sarbila tayi nazarin maganar sannan ta fahimci wani
abu take ta gyara tsayuwarta sannan ta cusa dan
mabudin ta murza tana murzawa sai ta daka tsalle
gefe guda ai kuwa kofar na budewa sai wata
mahaukaciyar wuta ta kawo bara duk da hanzarin
Sarbila sai da wutar ta laso damararta duk da kofar
ta bude to tana rufe kanta kuma tana bude kanta da
karfin ban mamaki kuma hakan na faruwane acikin
dakika biyu kacal sarbila ta tsaya agaban kofar
sannan tayi nazarin kofar ta tabbatar indai tana son
ta shige ta wannan kofar to dole ne ta wuce acikin
dakika
biyu rak in ko ya wuce haka to ba makawa kofar ne
ajalinta ko kuma ta koma baya abinda bazai taba
yuwa ba kenan wai ta koma da baya.
Al amarin boka karibu kuwa Kamar daga sama aka
dakama Boka karibu tsawa ana cewa kai abokina
ahaka zaka dibo ma unnar ruwan guba to maza ka
mike kamar tsinke yayi zumbur ya mike aka ce
masa maza kabi wannan hasken lallai shine
jagoranka kuma kasani acikin hasken zakayi karo
da abubuwa masu hatsari lallai zasuyi kokarin
hallaka ka kuma kai ma dole ne kayi kokarin kaisu
kiyama kuma kada ka kuskura ka tsaya dole ne ya
kasance kana yaki kana tafiya acikin hasken nan
domin idan harka sake hasken ya gudu ya barka to
kai da cika burinka har abada kuma tabbas sai ka
hallaka.
Take wani haske ya bayyana kafin Boka karibu yayi
wani abu tuni hasken ya fara tafiya ya fara yin nisa
cikin hanzari da masifaffen gudu boka karibu yabi
hasken nan amma hasken sai kara guduwa yakeyi
kamar ransa zaifita haka yake gudu amma ko kusa
da hasken baiyi ba take boka karibu ya sabi wasu
kalamai masu kama da
gwalan gwalan din yara yayi wasu sarkakkun
kalmomi daga cikin kalaman tsafi ya kira wani hargi
tsatstsan suna sau uku take wani zabgegen aljani ya
bayyana suka sa tseran tare suna ahalin gudu aljani
yace lafiya mai gida ka kirani a wannan lokaci kuma
a wannan tsinan nan dajin mai hatsarin tsiyar.
Afusace Boka karibu yace masa kai sha sha sha ba
surutu nake so ba maza ka sada ni da hasken can
da yake kokarin kulewa kamar ka dauki dutse ka
ajiye atsakiyar ruwa haka aljanin nan ya dauki Boka
Karibu bn kalab ya ajiye atsakiyar hasken nan
tashin hankali wanda ba a sa masa rana lallai
wannan daji bala ine kuma masifane domin shi kan
shi boka karibu bn kalab da yayi arba da miyagun
halittun dake cikin hasken nan sai da ya tabbatar da
cewa ya tunkari ajalinsa
.
SHIN BOKA KARIBU DA SARBILA ZASU SAMU ABIN
DA SUKA FITO NEMA KUWA?
SHIN YAUSHE ZA A FAFATA GASAR KARSHE
TSAKANIN BOKA KARIBU DA SARBILA?
SHIN WAYE ZAI CI NASARA A WANNAN GASAR?
SHIN SAMAR ZAI YADDA YA AURAR DA SARAUNIYA
YAZRINA GA SARKI JUNDARU NA BIRNIN BANGUS
KUWA?
Gaba daya wannan amsar mu hadu a SIHIRTACCIYA
littafi na biyu don jin yanda zata kaya daga mai
nishadantar da ku wato real rayyanu ke cewa
mu hadu a littafi na 2

SIHIRTACCIYA
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz Sani m Gini
Ebook created by Shuraih 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng

SIHIRTACCIYA
.
Littafi Na Biyu 2 part A
.
Lokacin da Boka karibu bn kala yayi arba da
masifun dake cikin hasken nan sai ya zazzaro ido
wasu mahaukatan damusai ne mace da namiji
suka tunkaro shi gadan gadan sai boka karibu
yayi wani surkulle take wani dogon mashi ya
bayyana a hannunsa suka fara dauki badadi da
damusan nan yayi iya kokarinsa dakyar ya kashe
daya amma sai dayan ta zamar.mishi alakakai
tana neman ta tsayar da shi alhali an masa
kashedin
kada ya kuskura ya tsaya ran boka karibu ya baci
sai yayi wurgi da mashin hannunsa aiko sai
damisar nan ta dako tsalle caraf ya shaki
wuyanta ya matse gam kuma yaci gaba da gudu
ba tare da ya tsaya ba a haka tayi ta shure shure
ahannunsa
har ta mutu boka karibu yayi jifa da gawar
damisar kuma ya cigaba da tsala gudu acikin
hasken nan kamar kibiya haka wasu garza garza
mayaka sanye da bakaken damarar yaki suka
bayyana acikin hasken nan.
Take suka tunkari Boka karibu aguje kamar masu
gudun tsira boka karibu ya kara yin surkulle take
bakin mashi ya bayyana ahannunsa ya jijjiga
mashin ya daga sama ya auna wasu mayaka
dake kan gaba wajan tunkararsa ya cillo mashin
nan mashin yayi wani futar borgu kai kace an
harbo shine daga cikin baka mashin ya tafi a
aune ya caki wani barde ya hudashi ya fita ya
caki na bayansa kai sai da ya hallaka mayaka
goma ya cigaba da tsala gudu acikin haske haka
shima hasken ke tsala gudu kokarinsa ya guduma
boka
karibu shi kuma boka karibu yaki amincewa gudu
yake ba kaukautawa mayakan nan suka farmar
da sara shi kuma ya shiga tsiresu da mashi ba
kakkautawa kai maza gumbar dutse boka karibu
yana gudu amma yana daukar rayukan mazaje
yana shallake wasu yana kwalloda wasu yana
bangaje wasu wani aiki dai sai mai shi.
kwatsam wani jarumi ya daka tsalle ya cakumi
Boka karibu kafin kace haka jarumai sama da dari
sun rungume shi da karfin tsiya yayi iyayinsa
domin
ya kwace amma ina ya kasa domin yawa suke
karawa suka taru akansa hasken nan sai tafiya
yakeyi har ya gudu ya bar boka karibu koda Boka
karibu ya ga hasken nan yana neman yayi masa
nisa gashi kuma mayakan nan sun yanyame shi
burin su hasken ya bace koda boka karibu ya
fahimci nufin su ya kuma tuna gargadin da aka
masa na cewa indai ya saki hasken nan ya bace
masa lallai dukkan burinsa ya ruguje sai ya
takura yayi wani wawan kara gami da gunji hadi
da wani nagartacen yunkuri take yayi watsi dasu
sai ga mayakan nan suna shawagi asama kamar
tsuntsaye suna kuma fadowa kasa kamar buhuna
tim tim boka karibu ya fita da wani matsanancin
gudu saboda tsananin gudun har bacewa yakeyi
kamar mai kokarin hayewa doki.
Haka yake kokarin kamo hasken wuf
ya fada cikin hasken fadawarsa keda wuya sai
yatsinci kansa agaban wasu furda furdan aljanu
sama da dubu dari uku wasu sun kewaye wani
bakin ruwa wasu sunyi sahu sahu wasu sai zirga
zirga sukeyi makamai azare fuskar su ba imani
bare tausayi kai da ganinsu kasan babuma suwa
ciyeta
Boka karibu ya tsaya cak hasken nan ya bace
sukayi ido biyu da aljanun nan shi baice da su
haka ba suma basuce da shi komai ba sai
zazzare idanu kawai sukeyi suna wani hucin wuta
Al amarin Sarbila kuwa sai tayi nazarin kofar nan
mai bude kanta kuma ta rufe kanta acikin dakika
biyu kacal ta fahimci cewa lallai wucewa ta kofar
nan kamar tsallake mayen damisace mai yaya
gashi kuma babu wata hanya sai ita Sarbila tayi
duk wani surkulle wai don ta tsaida kofar nan
amma Abin ya gagareta A karshe sai taji muryar
bokanya alimma na cewa lallai in kika ci gaba da
tsayuwa a wanna guri kuma a gaban wannan
kofa to dakiku kadan ya rage ki hallaka take ta
jada baya tayi taku shida ta falfalo ague tana
zuwa daidai kofar nan sai tayi sufa kamar walkiya
ta wuce tana wucewa kofar ta rufe da
matsanancin karfi tafada ciki ai kuwa sarbila tana
mikewa sai tayi tozali da tarin dandazon tashin
hankali lallai bala in da Sarbila ta gani ya ninka
wucewa ta kofar sau biyu tashin hankali.
Wasu irin hallitu ne masu kama da zakuna amma
sun ninka girman zaki
sau bakwai yawansu zai kai dari bakwai suna da
wani katon kaho mai tsawo da kauri da tsini
kamar tsinin mashi gawasu mahaukatan hakora
kamar takubba sai wani turza sukeyi sai dalalarda
yawu sukeyi kai da ganinsu kaga mayu kamar an
hura musu usur sukayi turza suka fakai a kasa da
kahonsu kawai sai suka tunkaro Sarbila da
mugun nufi sarbila ta gyara tsayuwarta ta girgixa
mashin ta tayi murmushin da ba mai iya fassara
shi ta kwarara ihu tayi turza kura ya tashi ta
tunkari halittun nan da bakar zuciya don agwabza
yakin mutuwa.
.
Lokacin da akayi arangama tsakanin halittun nan
da Jaruma sarbila sai abin yayi muni domin wani
bakin gumurzune aka fara
kaftawa tirkashi lallai mai karfi sai Allah ya isa
sarbila ta shiga sukan halittun nan tana gabza
musu naushi duk in ta naushi halittan nan sai ta
baje a kasa amma abin takaici sai ta tashi da
matsanancin fushi ta tunkari sarbila haka kuma
koda sarbila ta soki halittun nan da mashi to
mashin baya iya huda fatar su gashi dai Sarbila
ta zamar ma halittun alakakai.
Amma ta kasa kashe koda guda dayane hankalin
sarbila ya tashi tayi iya dabaranta da nuna
hikima da kwarewa na yaki amma abin yaki gashi
ta fara gajiya har dabbobin nan sun fara cin
galabarta domin sun karceta da kahonsu har guri
hudu matsanancin jinine ke zuba can wani dabba
yayi kukan kura ya surfafu da gudu sarbila takai
masa
sara dabban ya kauce wuf ya sunkuceta da kansa
yayi wurgi da ita tayi sama ta dawo kafin takai
kasa wani ya kara sa kai ya gabza mata duka ta
fado atsakiya dabbobin nan.
Nan fa suka far mata sukayi ta kwallo da ita suna
tattaka ta sukayi budu budu da ita saura kiris su
hallaka ta domin numfashinta ya fara nisa su
kansu halittun sun dauka ta mutune saboda haka
suka jada baya suka tsaya suna mata kallon
gawa suna wani turza da kafa can wani iska ya
hura sanyi ya ratsa kunnuwan sarbila da hancinta
nan ta fara motsawa take ta fara yunkurawa ta
mike ta zauna dabbobin suka zura mata ido cikin
mamaki domin sunyi zaton ta mutu
ta yunkura ta tashi ta mike tsaye ta kwarara ihu
gamida girgiza wani kura ya tashi ta daga kafar
ta na dama ta daki kasa ta kara kwarara ihu
Sarbila ta karewa dabbobin nan wani irin kallo ta
tuna irin fafatawan da sukayi a farko ta tuna duk
wani wuri data sara ajikin dabbobin nan da inda
ta soka amma batayi wa ko daya rauni ba ta
karewa halittun kallo sai tayi murmushi sannan
tayi wani surkulle gami da wani sambatu ta
karanta wasu sarkakkun kalmomi da kalaman
surkulle ta daga hannunta sama take sai wani
kakkaifar gatari ya bayyana a hannunta baki.kirin
ta girgiza shi take gatarin ya kara girma da
tsawo harda kaifi tayi kururuwa ta nufi halittun
nan afusace halittun nan sukai wani irin gurnani
suma suka tunkarota wai wai rikicin duniya.
Nanfa sarbila ta fitowa halittun nan ta bayan gida
sai tasa hannu daya ta damki kahon dabba sai
tasa gatari ta sare kahon take sai dabba ta sheka
barzahu nanfa Sarbila ta fara musu kisan gilla kai
masifa tayi masifa Sarbila ta fitowa dabbobin nan
a shaidaniya kashe su kawai takeyi kamar kisan
kiyashi halittun nan suka jada baya domin sun
tsorata sarbila tayi murmushi kawai sai takara
afka musu nan fa suka tarwatse ta shiga binsu
tana daukan rayukansu haka suka sa tsere suna
gudu tana binsu duk wanda ta samu sai ta kama
ta daga sama sannan ta sare kahon a haka kaf
sai da ta gama da halittun nan saura daya tak
nan fa suka fara tsere saura kiris ta kama dabbar
nan sai suka isa kofa na uku take dabbar nan tayi
tsalle ta wuce Sarbila ta daka tsalle sai kum ta
hadu da murfin kofa domin tun kafin ta rufe. Take
Sarbila ta fado
kasa asume
Al amarin Boka karibu kuwa sai yayi duba izuwa
ga aljanun nan masu gadin bakin ruwan nan ya
tabbatar wannan bakin ruwan shine ma unnar
domin ruwan har wani turiri yakeyi wani zubin
har wuta ke kamawa a saman ruwan
sannan yayi duba ga aljanun wadanda sukayi
sahu sahu suna tsaye kikam sai muzurai sukeyi
kamar zasu ci babu sannan yayi duba ga masu
zirga zirga da miyagun makamai sai ya tabbatar
ma kansa cewa lallai in har yana so ya debi
wannan ruwa to dole ne
sai ya gwabza da duk wadannan dakarun aljanu
aransa yace karo da maza badadi amma ni zan
kara da su.
Kai tsaye sai ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment