Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya dauka amma bayan ka sare gabobi
masu mahimmanci guda bakwai ajikin gunkin dake
gadin kayan jarumin sannan kasani koda kai nasarar
sare gabobi bakwan dake jikin gunkin to kafin ka
fita da kayan yakin to sai ka fuskanci turjiya lallai
wannan aikine da zaka iya rasa rayuwarka takama
hannunsa tace yakai dan uwana ina baka shawara
da ka hakura kazo mu fita awannan dakin domin
zamu iya halaka akoda yaushe awannan dakin ya
fizge hannunsa ya jada baya yace haba yayata kisani
bokana ya tabbatar min da cewa matukar na samu
nasarar dauko kayan yakin jaruma sarbila guda biyar
da damarar ta da takobinta da Garkuwar ta da
mashinta da kuma takalman yakinta lallai ba
makawa sai naje Darul sabah na samo ruwan
waraka kuma ya tabbatar min da cewa lallai indai
nayi nasarar wannan tafiya zakiyi aure kuma zaki
hayayyafa kuma babu abinda zai taba mutuncin
kasar mu lallai ina bukata kamar yadda muka rasa
zurriyar mu dalilin kare kasar mu to mu sake
yaduwa ta dalilin kare kasar mu.
Yazrina ta fashe da kuka ta rungume dan uwanta sai
da suka dauki lokaci mai tsawo ta sakeshi tace ya
dan uwana lallai na tabbatar duk duniya babu mai
gatana kai kadaine dan uwana aduniya amma
kanaso ka saida rayuwarka saboda ni hakika ina
son aure amma an haramtamin dole na hakura
saboda kasata kaje dan uwana darajar soyayyar yan
uwantaka babu abinda zai same ka tabbas zakayi
nasara Samar yai murmushi ya sumbaci yazrina
sannan ya fuskanci bangaren inda aka ajiye kayan
yakin Gimbiya Sarbila tun kafin ya karasa Gunkin
dake gadin kayan yakin Jaruma Sarbila ya fara
motsi jajayen idanunsa suka fara jujjuyawa wata
kafceciyar takobi ta fado hannun gunkin wani
zabgegen mashi ya fado hannun gunki wani
hayaniya ya fara tashi adakin.
.
YARIMA Samar yana tunkarar kayan yakin Jaruma
Sarbila sai gunkin shima ya tunkari Samar takobinsa
ahannu suna haduwa sai suka kacame da
masifaffen yaki suka shiga dauki badadi suka dinga
kaiwa juna miyagun hare hare yarima Samar yayi iya
kokarinsa ganin ya kare duk wani hari da gunkin nan
ke kawo masa abin takaici shi kuma in yayi nasarar
saran gunkin sai yaji kamar ya sari dutse yayi iya
dabaransa ya samu makama ajikin gunkin nan
amma abin ya gagara samar ya shiga tashin hankali
Gimbiya Yazrina tace dan uwana yi kokari ka sari
kafadarsa.
Cikin sa a ya zabgawa gunkin sara akafada sai da
gunkin yayi kara kafadar ya tsinke duk da haka sai
gunki yakara azama wajan yakar samar har ya
yankeshi acinya Samar ya fusata ya afkawa gunkin
da fada yasa tsinin takobi ya tsire idon gunki yayi
kara cikin zafin nama Samar yayi kwance kwance ya
sare kafar gunki ya koma mai kafa daya hannu daya
ido daya amma har yanzu bai saurara wajen yakar
Samar ba saima azama da himma sukaci gaba da
yaki mai tsanani da tashin hankali Samar ya
shammaci gunkin yakara soke idon yasa takobi
yakara sare daya kafar take gunkin yakoma yahade
sannan ya kame kamar ba shiba SAMAR ya mika
hannu zai dauki kayan yaki sai yaji an daka masa
tsawa ko saurarawa bai yiba sai ya dauki kayan
kawai sai kota ina aka saki guda har da tafi take ya
sanya kayan yakin ya dubi Yazrina yace muje yar
uwata muje ta kama hannunsa suka tunkari kofar ita
kanta kofar tasan shirin yanzu yafi na dazu da kanta
kofar tabude sai gasu sun fito dole kanwar naki.
Gaba daya dakaru da masoya da makiya sai da
suka sarawa Yarima Samar da Gimbiya yazrina inda
mutanen gari musamman yan mata suka shiga rera
wakokin yabo ga yarima Samar suna tafe jama'a na
bin su har tsakiyar fada sannan yakama yar uwansa
ya daurata akan karagar mulki sannan ya dubi
jama'ar dake fada ya daga murya yace yaku jama'ar
kasata kusani Yau saura kwanaki hamsin Sarki
Shaddadu yazo kasar nan da niyyar daukan yar
uwata Gimbiya Yazrina kuma kun sani matukar ya
dauketa amatsayin mata to kuna sane da bala ine
zai rufto mana mara adadi har sai mun tarwatse
mun watse baki daya tarihin mu zai rushe sai an
nemi mutum daya daga ahalin wannan gari an rasa
kuma bamu da karfin da zamu iya hana Sarki
Shaddadu hana daukar Gimbiya yazrina domin ya
fimu karfi ya fimu tsafi rundunansa taninka namu
sau dubu goma lallai hanya daya ne mafita shine
mu tashi Sihirtacciya daga daskarewar da tayi na
shekaru dari bakwai ya dubi al umma yace toni
bance kowa ya taimake niba kuma babu mai hanani
zuwa gaba daya jama'a aka dauka muna mafatan
alheri mun yarda mun amince daga nan Samar yace
babu lokaci gobe zan dau hanyar zuwa Darul Sabah
domin samo Ruwan waraka arijiyar Baroki.
Tsai tsaye suke kamar gumaka sun kai kimanin su
dubu dari yau kwanansu bakwai atsaye kuma da
rayukansu basu mutuba sun tsayane suna jiran Boka
Balbuna ya fito daga haular tsafinsa daya shiga yau
kwana bakwai can sai gashi ya fito fuskarsa baki
kirin babu annuri babu wani alamun tausayi yayi
sharkaf da zufa har diga yakeyi ya dubi jama'ar da
ke tsaye yace yaku dakaruna kusani shigan halwar
tsafina na samo bayanai kusani na gano wani
saurayi mai burin tada sihirtacciya lallai jarumine na
gaske da alamu zai iya zuwa darul sabah sai dai
zuwan sa ba alheri bane ga matsafa da kafuran
duniya domin da yuwwar ya dawo da sabon addini
kuma tabbas addinin mai rinjaye ne akan kafurci
Wani sadauki yace yakai Boka Balbuna yanzu meye
mafita Balbuna yace mafita shine muma mutashi
sihirtacce Gaba daya dakarun suka tsorata suka
zazzaro idanu suka dan jada baya suka fara yiwa
boka Balbuna kallon mahaukaci wai zai tashi Boka
Karibu bn kalab Daga daskarewar shekaru dari
bakwai.
.
Afirgice wani dakare yace yakai babban Boka kasani
tada Sihirtacce kamar tsokano masifa ne tana
kwance Boka Balbuna ya kece da dariya yace kasani
ko mu tashi sihirtacce ko kar mu tashe shi tunda
yarima Samar yayi kudirin tashin Sihirtacciya to
masifa zata fado mana matukar yayi nasara lallai
sai kafurai da mushirikai da matsafa sun koka sai
mu nemi gurin buya barden nan yace ya shugaban
bokayen duniya yanzu menene abinyi Boka Balbuna
yace Zamuyi tafiya ta kwanaki talatin zuwa dawowa
zamu tafi tsibirin kumana don mu samo bakin ruwa
wanda zamu tada boka karibu bn Kalab
Acan Birnin Manohar kuwa Yarima samar yayi
bankwana da jama'arsa ya durfafi daji yayi gabashin
duniya da niyyar zuwa Darul Sabah domin debo
ruwan waraka a rijiyar baroki sai da ya shafe
kwanaki bakwai yana keta dazuzzuka da
kwazazzabai wata rana daga ranakun tafiyarsa sai ya
hango wani ayarin fatake sun taru kimani su dubu
yana karasowa sai ya tarar yan fashine suka taresu
suna karbe musu dukiya Samar na isa sai wani ya
daka masa tsawa yace yakai kyakkyawan saurayi
maza ka sauka akan dokin ka ka ajiye damararka
da takobin ka da guzurin ka kakoma gefe kamar
yadda sauran jama'a sukeyi Samar yayi murmushi
yace to aini ba rago bane bakuma sakarai bane
sannan ni ba mace bane da har wani zai min
muzurai ya karbi kayana wani barkeken bakin kato
mummuna dake zaune a tushen wata katuwar
bishiya ya mike yana gurnani ya cika yana batsewa
ya takarkare ya daddage yakwarara ihu ya nuna
Samar da yatsa yace kai yaro wanene kai me ka
taka shin duniya tayi maka kunci ne kake son ka
mutu Samar yayi dariya yace sam babu daya aciki
kawai kayana ne bazai karbuba idan ko ana son a
karba to sai dai mu gwaza yaki tsakanin ni dakai
duk wanda yayi galaba akan dan uwansa to sai yaci
ribar fadan.
Katon mutumin nan ya kece da dariya ya dubi
yaransa yace kunji wani mahaukaci wai da Kodago
zaiyi yaki suka fashe da dariya sukace maigida ai
sai ku jarraba lallai yau zamu sha kallo Kodago
yace wo yaransa lallai zamu gwabza fada tsakani na
da wannan wawan kuma ina gargadinku da kada
kowa ya tayani wannan fadar koda kuwa yaga za a
hallakani ransa abace ya dubi Samar yace fiye da
shekara talatin ina fashi awannan dajin amma ban
taba ganin mahaukaci kamarka ba domin babu
wanda ya taba gangancin tarata da fada koya yi min
kallon banza balle ya tareni da yaki Samar yace
kana haduwa da yan matane yau kuma ka hadu da
namijin gaske lallai yaune karshen fashinka awannan
dajin Kodago ya kwarara ihu ya shata layi da takobi
ya daga murya yace yaku mutanen ayarin da mukayi
wa fashi kusani daya daga cikin ku ya takale ni da
yaki kuma zamu gwabza lallai kusani in yayi nasara
to kun tsira daga kaifin takobina amma matukar
nayi nasara akansa lallai sai na yanka ku daya
bayan daya cikin matafiyar ya duri ruwa Kodago ya
nuna Samar da takobi yace yaro lokacin mutuwarka
yayi taho.
Samar yayi wa dokinsa kaimi ya nufi kodago
afusace sukayi wani irin haduwa mai tattare da
mugun nufi yaki ya kullu atsakaninsu suka shiga
neman ran juna hankalin yan kallo ya tashi domin
kowa zai iya nasara awannan yaki kaiwa juna sara
sukeyi ba kakkautawa ran Kodago ya baci kamar
shine wani karamin yaro ke jayayya dashi ya canza
salon fada ya shiga kaiwa Samar farmaki ta sama
da ta kasa take ya rikita Samar kuma har ya
yankeshi a kafada jini yayi tsartuwa Kodago ya kece
da dariya yace yaro lokacin mutuwarka yayi taho in
karasa ka afusace Yarima Samar ya afka wa kodago
da wani azabebben yaki ya shiga auna masa wasu
mahaukatan hare hare dakyar kodago ke iya karewa
can Samar ya kawo wani nagartaccen sara dakyar
kodago ya kauce amma duk da haka sai da saran
ya sauka awuyan dokin take ya guntule kan dokin
Kodago ya baje akasa kafin ya tashi Samar ya diro
ya damke shi yayi sama da shi ya maka da kasa.
kodago yayi kara
Kafin ya rufe baki tuni Samar ya tsinke masa kai da
takobinsa ai tuni sauran yan fashin suka cikawa
wandon su iska suka shiga daji don neman tsira
matafiya sukayi murna kowa aka bashi dukiyansa
sannan kowa yakama hanyansa Samar yakara gaba
sai da yayi tafiya mai nisa sannan ya isa wani katon
birni ya kunna kai cikin garin babu wanda ya damu
dashi yana tafe sai ya taradda wata dattijuwa ta
hada kai da guiwa tanata kuka ga kuma wasu yan
mata biyu suna gefenta suma kukan sukeyi yarima
Samar ya sauka yaje gurinsu yace musu yanaso su
taimake shi da ruwan sha duk da suna halin bakin
ciki sai matan nan ta umurci daya daga cikin yan
matan nan data kawo masa ruwa bayan yasha sai
ya tsaya yana kallonsu cikin tausayi matar nan tace
masa kai ka nemi taimako mun maka to me kake
jira
Samar yace kuyi hakuri amma ina son inji dalilin
kukan ku matan nan ta mike tace koda mun fada
maka lallai ba abinda zaka iyayi don haka karu fama
kanka asiri ka kara gaba samar yace ki fada min ba
mamaki in muku maganin matsalarku ta kyalkyale
da dariya sannan ta daure fuska tace wane kai yaro
abun ya wuce sanin mutum sai dai Aljan Samar
yace karki damu kiban labari da yuwan in zame
muku garkuwa ta daure fuska ta haderai kamar
wanda aka yanke wa hukuncin kisa ta nuna shi da
yatsa tace kasani ka nemi taimakon mu mun
taimaka idan har kaji damuwar mu kaji labarin mu
to ya zama dole ka fuskanci bala i da masifa dake
cikin labarin mu Samar yace na amince tace to ka
biyo mu cikin gida
.
tabdijan aradu bazan bisu gida ba ko akwai Wanda ze
rakani>SIHIRTACCIYA
Littafi Na Biyu 2 part D
.
Lokacin da suka shiga cikin gidan sai matar nan
ta Samar tace yakai wannan bako namu kasani
sunan wannan garin JAMHU mun kasance muna
bautawa wata tsohuwar rijiya ne kuma akwai
wata aljana acikin rijiyar mai suna TSAMURA ita
wannan aljana duk shekara sai an kai mata
mutum biyu saurayi da budurwa tasha jinin su to
shine zamu samu albarkar shekara in ko muka ki
bata to masifu da bala o i ne zasu dinga kunno
mana na rashi ruwa ciwuwwuka mace mace
tabbas munyi imani da aljana Tsamura dari bisa
dari domin duk wata bukata to a wurin ta muke
nema boka LAMAMU shine shugaban bautan
wannan rijiyar kuma shine mai karbo sako daga
gurin aljana Tsamura yazo ya gaya mana kuma
duk shekara shine zai ce aljana tsamura tace akai
mata wane da wance bawai ina karyata aljana
tsamura bane Aa ni ina shakkane akan cewa boka
lamamu duk shekara yana zaben son ransa ne
kawai ya mikawa aljana ta shanye jininsa.
Yarima samar yace me yasa kike zargin Boka
lamamu da son zuciya matar nan tace boka
lamamu ya dade yana so yayi lalata dani amma
naki bashi hadin kai wannan ne yasa wata
shekara ya bada sunan kannena mace da namiji
amatsayin wanda za atsotse wa jininsu sai da
akayi shekara uku yana bada yan uwana yau
kuma gashi ya bada suna yayana guda biyu ta
fashe da kuka tace tabbas wannan ba tsarin abin
bauta bane kawai Boka lamamu ne kemin
ramukon gayya duk shekara Samar yayi
murmushi yace to yanzu wani taimako zanyi
muku tace nidai so nake rayuwar yarana su tsira
samar yace to idan ko hakane ya zama dole in
kashe aljana Tsamura matar nan ta kwarara ihu
tace karyane kai bazaka iya ba kuma ma duk
duniya babu wanda zai iya yaki da ita.
Domin wata shekara an taba ambaton yar sarkin
garin nan amatsayin wanda za aba aljana tasha
jini sarki yayi tsalle ya dire ya hana runduna ta
jarumai da mayaka ya aika dan aje a yaki aljanar
nan amma an kasa domin fitowa tayi arijiyar
gaba daya tayi kaca kaca da kowa ta kuma koma
rijiyarta kuma a shekarar nan mun dandana
azaba da masifu kala kala lallai ko yaki aka zo
mana ya kasance anfi karfin mu to komai yawan
tarin runduna to ita kadai take watsar dasu
tabbas ta gundire mune kawai dalilin kashe mana
yara da takeyi ta hanyar shanye jinin su Samar
yace yau shene za a kaisu ga wannan aljana
azzaluma tace gobe Samar yace ina tabbatar miki
yayanki sam baza su mutuba ta buda baki zatayi
magana yace kar kice min komai lallai ki saurari
gobe lissafi zaicanza daga gobe kawai kibani
wurin kwana ta nuna masa gurin kwanciya
Washe gari gaba daya gari ya tashi da kide kide
da wake wake akayi wa yara wanka aka caba
musu ado sannan aka nufi bakin rijiya dasu aka
tsaida su agabanta sannan aka cigaba da kide
kide yara sai rusa kuka sukeyi ita mahaifiyarsu
tana can gefe tana sharba kuka kwatsam sai
wani hannu ya fito daga rijiyar ya kama wuyan
macen zai murde Samar yayi fitar burgu ya zare
takobi ya zabgawa hannun sara take hannu ya
guntule akayi wani mummunan kara daga cikin
rijiyar jama'a suka rude suka kama guje guje
aljana tayi yo sama ta fito afusace daga cikin
rijiyar wata doguwar aljanace mai matukar tsawo
ga wani karamin kai kamar gwan gwani tana da
hannaye shida kuma akwai kaho atsakiyar kanta
ta kalli hannunta da Samar ya sare take hannu
ya koma dungulmi sannan ta kama kumbura tayi
wani fadi tana cika tana batsewa sai ta takarkare
ta kwarara wani uban ihu ta dubi Yarima Samar
tace lallai yaro ka debo ruwan dafa kanka tabbas
sai nayi gunduwa gunduwa dakai.
Samar ya kece da dariya yace tabbas kin dade
kina karo da maza suna shan kashi ahannunki
amma yanzu lissafi ya canza domin yau kece zaki
kwashi kashinki ahannu tayi kururuwa ta bude
bakinta harshenta ya fito yayi dogo kamar maciji
yaje ya shakewa Samar wuya idanun Samar suka
zazzaro numfashinsa na kokarin tsayawa yasa
takobi ya sare harshen kafira sai yaji kamar ya
sari dutse yayar da takobinsa ya dauko wata
karamar wuka adamararsa baki kirin ya yanke
harshen kafura zafi da radadi ya shige ta tayi
kara afusace ta zare takobi tayi kan Samar shima
yayi kururuwa ya dau takobinsa ya karci kasa
yayi kanta za ai ragab mugun gamo haduwa mafi
hadari da firgitarwa.
.
Lokacin da akayi taho mugama tsakanin Samar
da aljana sukayi wani mummunan gamo sukayi
karan batta wani miyataccen kara ya tashi suka
sarke da masifaffen yaki mai tsanani suka shiga
musayar takubba guri yayi guri kura tayi sama
tabbas karo da aljani badadi amma tabbas Samar
yakara kwazo domin sai da ya rikitata ta rude
Samar ya shiga sauke mata luguden sara da suka
take ya yanke mata hannu daya tayi kururuwa
tasa kafa ta makeshi tayi wuf ta cafki wuyan
Samar tayi wuji wuji dashi ta maka da kasa yayi
yunkurin tashi tasa kafa tayi kwallo dashi yaje
yabigi wata katuwar bishiya take bishiyar ta karye
kansa ya fashe bayansa ya makale ya kasa
mikewa ya daki kasa ya ciji lebe hawaye ya zubo
a idanunsa aljana tayi girgiza hannun da Samar
ya sare ta kece da dariya ta nuna Yarima Samar
tace wane mutum wane aljan aljanu ma sun buga
dani sun barni yau shekarata Dari uku ina
matsayin abin bauta na wannan kasa amma rana
daya kace zaka yakeni wanene kai baka isa ba.
Ta sheko aguje da niyyar tayi masa kwaf daya
Samar yakama sumbatu yana surkulle yana
karanta kalaman siddabaru take wani masifaffen
karfi yazo masa yaji kamar zai iya yakar duniya
tana zuwa daf dashi yayi wuf ya shaki wuyanta
ya matseta gam tayi ruri saboda tsananin zafi ya
tattara karfinsa ya murda kan kafura ya tsige kan
yasa kafa ya banke gangar jikin ya fada rijiya
yasa kafa ya take kan take kan ya tarwatse yayi
wani surkulle take rijiyar takama da wuta takone
kurmus da gudu matar nan ta rugo da gudu ita
da yayanta suka rungume Samar suna masa
godiya daukacin jama'ar garin sun taru suna yiwa
Samar godiya dama wannan kazamar bauta ya
damesu suka nemi da ya zauna dasu Samar yace
akwai abinda ya raboshi da gida yayi musu
bankwana ya kara gaba.
Al amarin Boka Balbuna da rundunarsa kuwa
suna keta dazuzzuka da kwazazzabo sai suka ji
an daka musu tsawa take suka tsaya sai wani
Mutum ya bayyana kamarsa daya da Boka
Balbuna koda sukayi ido biyu sai suka ruga da
gudu suka rungume juna sai da suka dau lokaci
mai tsawo sannan suka rabu da juna Boka
Balbuna ya dubi bakon yace yakai dan uwana
Balduna ina kashiga tsawon shekara biyu ba
labarinka Balduna yace tabbas nayi nisan kiwo
domin na tafi Birnin Alkarmar binnin mafiya
yawan jama'ar duniya kuma acan ne sarauniyar
kyau na duniya take tabbas na kamu da sonta
amma tasa gasa cewa duk mutumin da ya raba
Yarima Samar da takobinsa yakai mata to shine
zai zamo mijin Sarauniya Lubiya mai sarautar
kyawawan duniya Boka Balbuna yace gaskiya dan
uwana ka dauko aiki kuma kana bukatar
taimakona wajen ganin mu hada karfi da karfe
don raba Yarima Samar da takobinsa gashi ni
kuma nay niyyar nemo bakin ruwa dan tayar da
Sihirtacce wato Boka karibu bni kalab.
Koda Balbuna yaji burin dan uwansa sai ya kece
da dariya yace to ai wahalar banza kakeyi domin
da zarar Yarima Samar ya samo Ruwan waraka
daga rijiyar baroki dake Darul sabah ya yayya
fawa Sihirtacciya to da zarar ta tashi ba makawa
shima Boka karibu bn Kalab zai tashi kaga kai
baka da bukatar samo bakin ruwa koda boka
balbuna yaji wannan zance sai ya kece da dariya
sannan yakara rungume dan uwansa sannan yayi
rantsuwa cewa ko zai rasa rayuwarsa to sai ya
taimaki dan uwansa wajen ganin ya sami gimbiya
Lubiya Boka Balduna yace na gode dan uwa
amma kasani akwai manya manyan jaruman
duniya da manyan matsafa da suke burin auren
gimbiya Lubiya saboda haka sun watsu aduniya
suna neman Yarima samar don su rabashi da
takobinsa Boka Balbuna yace tabbas raba Yarima
Samar da takobinsa tamkar raba Zakanya ne da
danta
Al amarin yarima Samar kuwa nagajiSIHIRTACCIYA
Littafi Na Biyu 2 part e
Al amarin yarima Samar kuwa yana tafe cikin
sassarfa akan dokinsa kwatsam sai yaji an
nannadeshi acikin ragar karfe kuma aka rataye
asaman wata katuwar bishiya kawai sai wasu
murda murdan katti suka bayyana akalla sunkai
su dari suka kewaye bishiyar suna kyakyata
dariya tsit sukayi sakamakon bayyanar
shugabansu ya dubesu yace dakyau yarana kunga
mun samu takobin Jaruma Sarbila a saukake
yasa hannu ya dauki takobin da dama ya fadi
akasa yayin da tarko ya kamashi kawai sai yace
da yaransa tunda mun samu abin harin mu kawai
muyi gaba koda Samar yaga sun juya zasu tafi
sai ya takarkare ya kwarara ihu ya kumbura yayi
gunji take ragar karfen ya kekkece yarima Samar
yadiro kamar wani zaki yana wani gurnani tamkar
damisa mai yaya idanunsa suka kada sukayi jajur
yana kumbura yana sacewa tamkar aljani ya
takarkare ya daka musu tsawa tabbas duk da
suma jarumaine sai da suka razana amma sai
suka dake sannan suka gyara tsayuwarsu yarima
samar ya irgasu yace tabbas ku dari da dayane
amma ko daya daga cikin ku babu wanda zai
rayu shugaban dakarun nan ya kece da dariya
yace tomu gwabza mugani waye zai mutu kuma
waye zai rayu sukayi kansa afusace suna wani
ihu mai ban tsoro ko motsi YARIMA SAMAR
BAIYIBA yana tsaye kikam kamar ice sai da ya
gyara tsayuwarsa ya dunkule hannayensa ya fara
wani huci kamar wani kumurci.
.
Lokacin da Samar ya tunzura ya gama fusata
yakai makura afushi sai yazaro wata yar karamar
wuka ya tunkari kattin nan suma afusace suka
nufo shi suna haduwa akayi karan batar uwar
bare ya suke mutum biyu yasa kafa ya make
shida lokaci guda baki daya ba wanda ya motsa
ya shiga cikinsu afusace yayi zarya atsakaninsu
da wasu miyagun soke soke tuni sai ga fiye da
rabinsu akasa kwance ba wani mai amfani saura
ba sufi arba inba suka tsorata suka jada baya
Samar ya kallesu yayi dariya yace kai ya kuke
jada bayane kodai ku matayene ransu ya baci jin
an kirasu da mata sukayi kansa da wata irin
zuciya kakkarfa nanfa aka yamutse ai banban
goro sai magofin karfe tuni yarima samar ya
sadasu da makomarsu saura babbansu Samar ya
dubeshi yace To yaro gashi yanzu ka rasa
jama'arka zaka bani Takobina ne ko sai mun
gwabza yaki katon nan ya kafe takobin akasa
yace yallabai ga takobin ka.
Sai da yarima samar ya saki jiki zai dauka sai
yaji wani shararren naushi afuskar shi sai da ya
tashi sama sannan ya baje akasa bakinsa ya
fashe katon nan ya fashe da dariya ya nuna
yarima Samar da yatsa yace kai wawa me
kadaukeni in samu takobin Gimbiya Sarbila
sihirtacciya shine zamu kama ta cikin sauki lallai
kayi kuskure ai dole ne sai mun goga sai munyi
yar kashi dakai yarima Samar ya tashi yayi wani
Girgiza Afusace ya sheko da gudu shima katon ya
fallo afusace suka daka tsalle suka hadu asama
ai tun asama labari yasha banban domin tuni
Samar ya sossoki katon nan sau sama da arba in
aduk sassan jikin katon nan suna dirowa Yarima
samar ya dire shiko katon ya baje akasa yana
kakarin mutuwa ko kallonsa yarima Samar
baiyiba ya dauki takobinsa zai wuce sai katon
mutumin nan yakira Sunansa Samar ya juya ya
kalleshi mutumin yayi murmushin karfin hali
alokacin yana gargaran mutuwa dakyar yabude
baki yace da Yarima Samar sam bazaka zauna
lafiya ba matukar kana rike da wannan takobi to
ka zama abin farautar Sarakunan duniya da
Jarumai da bokaye sai ya mutu Yarima Samar
yana mamaki ya cigaba da tafiya yana keta daji
sai ya isa wasu manya manyan duwatsu guda
biyu makotan juna ya ratsa ta tsakiyar dutsan
nan yawuce sai da ya kusa fita atsakanin
duwatsun nan sai yaji saukan wani guduma
akansa take kansa yayi girim duniya ta fara juya
masa tun yana gani dishi dishi har ganinsa ya
dauke numfashinsa ya tsaya cak ya kame kamar
gunki ya fadi kasa tamkar gawa.
Boka balbuna da dan uwansa Balduna sun iso
gunda Yarima Samar ya fafata yaki da kattin nan
sukaga kattin nan akwarkwance matattu sai
Balbuna yace yakai dan uwana kasani lallai
Yarima samar yana kusa tabbas bayyi nisaba
Shine ya kashe duk mutanen nan kuma bai dade
da kashe suba Balduna ya durkusa ya debi kasa
ya watsa ya kura mata ido iska ta debi wani
yanki na kasar tayi kudu da ita Balduna yace
tabbas kudu yayi taho mubi bayansa lallai burin
mu nadaf da cika suka sa gabansu kudu suna
tafiya cikin sauri domin su riski yarima Samar
suna tafe sai suka iso manyan duwatsun nan
guda biyu sai Boka balbuna yace mu dakata anan
domin nayi binkice gameda wadannan duwatsu
lallai ban yarda da suba ta yuwu akwai wani
hadari aciki take ya sabi wasu zantuttuka yana
wasu sambatu ya sassarka sarkakkun kalmomin
tsafi can sai wani bakin hayaki ya tashi yayi
sama Boka balbuna yazazzaro idanu yayi dogon
numfashi ya girgiza kai Balduna yace yakai dan
uwana me kagani acikin wannan tagwayen
duwatsu Boka Balbuna yace da matsala tabbas
da matsala lallai Yarima Samar yana cikin
wadannan duwatsun kuma shima yana cikin
hadari domin akwai wani mugun abu atsakanin
duwatsun nan kuma yana da matukar hadari
domin na kasa gane iya girman lamarinsa
Balduna yace to menene abinyi Boka balbuna
yace ya zama dole mu fuskanci duwatsun amma
fa zamu kasance ne atsakanin
SIHRTACCIYA
Littafi Na Biyu 2 part F
.
Lokacin da Boka balduna da dan uwansa suka
tunkari tagwayen duwatsun sai suka kasance
cikin shiri kuma suka kasance da dari dari sai da
sukazo tsakiyar duwatsun sai sukayi kicibis
mugun gamo wasu sharba sharban maridai ne
masu cin naman mutane suke fitowa daga
lungunan duwatsun nan da daya da daya sai da
maridan nan sukayi fiye da dubu daya sukasa
Boka balbuna da dan uwansa atsakiya sai
muzurai sukeyi tabbas mutanen nan ba su da
kyan gani ga tsawo ga girma ga fadi Boka
balbuna ya daka musu tsawa yace kai lalatattu
masu cin naman yan uwansu kusani bagurinku
muzoba saboda haka karfa ku jamu da fada lallai
zakuyi dana sani
Shugaban mariddan nan ya kyal kyale da dariya
sai da ta isheshi sannan ya daure fuska alokaci
guda ya turbune fuska ya nuna balbuna da yatsa
yace kai karamin halitta kasani kashigo tarkon
mu kai da dan uwanka kuma sam bazaku tsiraba
ran boka Balduna yabaci ya kwara ihu ya sabi
wasu kalaman surkulle ya kama jujjuya hannunsa
take wata wuta takama guri guda ya daki wutar
tayi kan maridan nan take shima shugaban
mariddan yayi kolo kolo yayi sambatu irin na
matsafa ya nuna wutar take wutar ta mutu nanfa
suka shiga musayar tsafi sukayi wa juna kaca
kaca suka koma bakake sidik saboda tsananin
bala i kai tsafi gaskiyar mai shi sai wannan ya
turo kura wancan sai ya turo zaki ya gama da ita
kai koda suka ga karfin tsafinsu yazo daya sai
suka jada baya sukayi kururuwa suka falfalo
aguje kowanne takobinsa azare suka kacame da
yaki tofa ai sai sauran maridan nan suma suka
zare makamai suka afkawa rundunar boka
Balbuna tashin hankali wanda ba asa masa rana
yaki yarin cabe masifa tayi masifa.
.
Babban tashin hakali awannan yaki shine kaifi da
tsini sam baya tasiri ajikin Maridan nan amma
kuma su sai kashe mazaje sukeyi take sukayi wa
jaruman Boka Balbuna kan kace ahaka sun karar
da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment