Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

mayakan baki daya saura boka Balbuna da
Dan uwansa sune suka zamarwa Maridan nan
alakakai can sai akaji wani kara gamida hargagi
yaki ya tsaya cak sai wani sintimemen katon
Maridi ya bayyana girmansa yayi icen rimi
kaurinsa tamkar rumbu idanunsa manya manya
kamar tulu wagegen bakinsa kamar kofar gari
gaba daya maridan nan suka durkusa suka
gaidashi ko kallonsu bayyi ba sai ya dubi balbuna
da dan uwansa yace kun kasance kuna neman
Yarima Samar domin kusace takobinsa dan wata
bukata taku to kusani Yarima Samar yana
hannun mu kuma kun shigo hannun mu .
.
Boka Balduna da dan uwansa sukayi kukan kura
sukayi kan kafcecen mutumin nan yayi murmushi
yasa hannu ya makesu tamkar ya make beraye
haka suka baje akasa sumammu ya kece da
dariya yace saini Gurdo babba dan babba inci
mutum insha kwanyarsa kawai sai yayi gaba take
yaransa suka kwashi balbuna da balduna sukayi
awon gaba dasu sai da sukayi tafiya mai nisa
acikin duwatsun nan sai suka isa birninsu wani
dan karamin garine mai cike da tarin maridai
akalla maza da mata zasu kai dubu goma koda
aka hangosu sai gaba daya maridan suka kaure
da ihu da tsalle an samu karin nama take aka
bude wani katon keji aka wurgasu aciki sai suka
fado agaban Yarima Samar kuma tsananin zafi
da radadin buguwa da sukayi da murda murdan
itacen kejin nan tasa suka farka daga suman da
sukayi sai sukayi ido biyu daYarima Samar ya
kamayi musu murmushin mugunta sai suka ji
hayaniya abayansu atare suka waiga nan ma sai
sukayi arba da tarin cincirindon maridai maza da
mata sunata kallonsu suna lashe baki tamkar
zasu ci danye.
.
A tsorace suka dawo da kallonsu ga Yarima
Samar Sai ya kyalkyale musu da dariya yace kai
ya dai tagwaye kun kasance kuna bin bayana dan
ku rabani da takobina to kuma Gashi ni daku
muna hannu mayu masu cin naman mutum
danye lallai kusani sun kama mu ne domin gobe
zasuyi bikin haihuwar matar sarkinsu kuma mune
abin yanka awannan biki lallai gobe za ayi ta ko
dai mu mutu ko mu rayu cikin biyu tabbas sai
anyi daya ko mu ko su suka zazzaro ido Yarima
Samar yace kuma kusani idan har mun rayu to
zumu gwabza yaki tsakanin NI DAKU IN KUN
kasheni ku dauki takobina ni kuma tabbas inna
samu dama to ba makawa sai na kasheku.
.
Gari ya waye haske ya gauraye ko ina sai
maridan nan suka fara fitowa daga gidajensu
nanfa suka fara shirye shiryen biki tirkashi mata
da maza sai kaiwa da komowa sukeyi kafin wani
lokaci sun taru sun cika guri sai kade kade da
wake wake sukeyi wani abin tashin hankali shine
kafin sarki ya fito an yanka mutane sunkai
bakwai an jefasu cikin tukunya wanda aka a'sana
an tata da kasa duk wannan shagali da akeyi
agaban yarima Samar akeyi da su Boka Balbuna
boka balbuna ya dubi dan uwansa yace dan
uwana lallai yau sai buzun mu dubi mahaukatan
mutan nan yadda suke dafa naman mutum kalli
yanda suke gasa hanjin dan adam lallai tamu
tazo karshe Balduna yace tabbas dan uwa neman
duniya ya kawo mu ga halaka.
.
Koda yarima Samar yaji wannan hira sai ya fashe
da dariya yace kai lallai da sauranku a
gwagwarmayan duniyar yanzu kuna nufin har kun
sare ne kun yarda ayau zaku mutu balduna yayi
wa Samar kallon mahaukaci yace yanzu kana
nufin kana saran kubuta daga hannun mayun
nanne Yarima Samar yayi murmushi yace kwarai
kuwa tabbas sai dai insha wuya amma ina da
yakinin cewa bazan mutu ahannun maridan nan
ba Boka Balbuna ya tintsire da dariya yace haba
dan samari ka daina yaudarar kanka amma ina
tabbatar maka yaune ranar karshe na rayuwarka
Yarima Samar yayi murmushi irin na mazajen
fama ya dafa kafadar Boka balbuna yace kaidai
ina baka shawara duk lokacin da ka samu dama
to kayi kokarin guduwa.
.
A dai dai wannan lokacin ne sarki ya fito gabaki
daya maridan nan suka fadi kasa mata da maza
suna gaida Sarki bayan ya wuce ya zauna awata
katuwar kujera wanda aka sana'antata da dutse
sai kowa ya mike sarki ya fara jawabi jama'a
muna muku barka da zuwa wajen wannan
kayataccen biki domin taya 'yata murnar bikin
karin shekara saboda haka afito da mutanen da
aka tanada don a yanka mata take aka zaro
Yarima Samar Su balduna aka tsaidasu agaban
sarki malamin yanka ya fito babban kuskuren da
maridan nan sukayi shine da suka zabi makamin
yarima Samar ya zama abin yankansu wasu katti
biyu suka gabato da takobin an ajiye ta a wani
katon baka sannan aka ajiye bakan agaban su.
.
Yarima Samar gadan gadan malamin yanka ya
taho domin ya dauki wukar ai sai da ya durkusa
zai dauka sai yarima Samar ya jijjiga kafarsa ya
tabkatawa malamin yanka sai da yayi sama
kamar kibiyar da aka harba sannan yayi wani
kara na azaba tsananin mamaki Maridan nan
suka tsaya kallon inda duk girman malamin
yanka ke cilla gudu asama kawai saboda yarima
samar ya masa kafa lokacin da hankalinsu ya
dawo jikinsu sai sukayi arba da Samar rike da
takobinsa sai muzurai yakeyi nanfa aka fara
kallon kallo Sarki ya daka wa Yarima Samar
tsawa yace kai yaro kada kuruciya ya dibeka
lallai bazaka iya yaki damu ba tabbas kwananka
ya kare dama kadan gana ka mutu a saukake da
yafi maka
.
Samar yace karyane maza dangin gujjiyane lallai
sai anfasa ake sanin mai kwaya lallai zan gwabza
yaki daku ko ni ko ku za agane wanene jarumi
afusace sarki yayi umurni da ai kaca kaca da
Yarima Samar take maridai sukayi kanshi shima
yayo kansu yana karaji yayi kururuwa ya afka
musu da sara ai sai mayun nan suka sha mamaki
domin zarya biyu yayi acikinsu sai ga mattatu
sama da dari ransu ya baci suka rufe shi da sara
da suka amma sai ya zamar musu alakakai yaja
tunga ya bude daga yayi runfa ya shiga turasu
kiyama guri ya yamutse ya hargitse bakajin ihun
komai sai ihun mazaje Yarima Samar ya zama
kamar wani aljani har wani tsalle yakeyi sama
yana dawowa kasa idan maridan nan ya rufe
Burinsu kawai suga sun illata SAMAR
.
Sun mance da Balduna da balbuna su kuma tun
da suka ga ba a ta ta su sai sukayi wa kansu
kiyamallaili suka bace bat afilin sannan suka
yanki daji tuni sukayi nisan ban mamaki afilin
daga kuwa maridawa sunji badadi Yarima samar
sai shiga da fuce yakeyi atsakan kaninsu kuma
duk inda ya gilma sai dai kaga maridan nan na
faduwa kamar bishiya dole sukaja da baya koda
ganin haka sai sarkinsu ya kwarara ihu ya mike
yana wani huci yana wani kumburi ya takarkare
ya kwarara wani uban ihu sannan ya nuna Samar
yace kai karamin halitta lallai ka cika shaidani
yau kimanin shekaru dari ba a taba samun
mutum ko aljan ko wata muguwar halitta da tazo
ta iya kashe mana mutum biyu ba amma kai yau
ka kashe mana mutane sama da fin kirge lallai
dole sai ka mutu kuma tabbas sai munci naman
ka danye Yarima Samar yayi dariya yace to karka
soma gwada yaki dani domin bazaka iyaba
tabbas in ka gwada mutuwa zakayi.
.
Sarki ya kwarara ihu yayi kan Samar sukayi wani
irin mummunan haduwa yasa kafa ya banke
Samar take ya baje akasa sarki ya daga takobi
da niyyar raba shi gida biyu af ai ya makara tuni
Yarima samar ya rarumi takobinsa yayi wani
yunkuri jikake cas ya farwa sarkin maridan
tsananin zafi ya kwarara ihu ya kama tsalle yana
birede Yarima Samar ya daka tsalle kamar
tsuntsu ya tashi sama ya sare kan sarki ai sai ga
kai daban gangar jiki daban wayyo ai sai maridan
nan kowa yayi ta kansa Yarima Samar ya baje
akasa tamkar ya mutu saboda tsananin gajiya
yana nan kwance yana numfashi sama sama sai
ya farajin wani iska asamansa dakyar ya iya bude
idonsa Dan kari ai sai yayi arba da wasu maka
makan angulaye girmansu yayi girman saniya
suna shawagi asamansa lallai tsigu ne bata
kareba domin suna shirin afko masa ne wai suma
sunga nama
Lokacin da Yarima Samar ya daga kansa yaga
wasu ma yunwatan angulaye suna neman daka
masa wawa sai yaji gaba daya gajiyan dake
jikinsa yakau yayi zumbur ya mike yafara jada
baya da niyar zai gudu amma sai yaga sun
kewaye shi sama da kasa wasu asamansa wasu
kuma sun dira a kasa sai ya dage ya zare
takobinsa yaja tunga kamar suna jiransa ya
shirya kawai sai suka falfalo aguje suna wani irin
kara mara dadin ji.
.
kwaram kwatsam aka fara tafka yaki angulayen
nan suka haukace suna kawo masa wafta suna
kokarin hallakashi shi kuma ya himmatu wajen
kaucewa da zillewa sai da aka dauki tsawon sa'a
biyu suna tabka gumurzu koda YARIMA samar
yaga wankin hula zai kaishi dare sai ya fusata ya
kumbura yayi dam ya cika ya batse tamkar zai
fashe sai ya wage baki ya saki wani wawan ihu
kai ihun maza in suka fusata dole kananan
jarumai suja baya ba shiri Angulayen nan suka
tashi sama suka yiwa Samar runfa su basu gudu
ba kuma basu afka masa ba ya fita aguje
angulayen nan suka rufa masa baya da masifan
gudu ta sama da ta kasa.SIHIRTACCIYA
.
PART END
.
Kaico da angulayen nan sunsa bala i da masifar da Yarima
Samar zai kunno musu to da baza subi bayansa ba suna
cikin gudu sai ya tsaya cak sannan ya juyo yana wani
sambatu yana damdam yana hamm ham yayi tsawa
gamida nuna Angulayen nan na sama da yatsa take wata
curarriya wuta tayi sama sannan ta watse asama take ta
kone angulayen nan ya dunkule hannu ya daki kasa take
kasa ta rufta da angulayen dake binsa ta kasa ya kwarma
ihu wuf wata katuwar Angulu ta sunkuci takobin yarima
Samar ta fita da gudu tana gare gare akasa
.
Samar ya bita aguje suka kifa tsere ya kure mata gudu
saura kiris ya cimmata sai tayi wuf ta tashi sama Yarima
Samar yayi girgiza take ya zama wani jibgegen tsuntsu
sukasa tsere asararin samaniya da matsananci gudu irin
na fanfalaki ya kure mata gudu ya cimmata suka fara
dauki badadi asararin samaniya gumurzu yayi gumurzu
ba shiri sukayo kasa tun kafin su karaso kasa gaba daya
suka rikide suka koma suffarsu Samar ya koma Samar ita
kuma angulun ta rikide ta zama wata santaleliyar
budurwa tana rike da takobinsa ahannunta cikin tsananin
mamaki ya kalleta yace ke wacece ke idan har mazaje na
bukatar takobina dan su auri Sarauniyar kyau na duniya
Gimbiya lubiya to ke me zakiyi da takobina tace kayi
hakuri domin ni bukatata yasha banban da bukatar
sauran mazajen domin ni ina neman sane don tseratar
da masarautata da jama'ata Yarima Samar yace a ina
Masarautanki yake kuma menene ke muku barazana tace
zanfada maka amma ka kasani lallai idan har kaji labarina
cikin biyu dole ne ai abu daya Samar yace na amince
Al amarin Boka balbuna da dan uwansa Balduna kuwa
tun sa'ar da suka samu damar tserewa agurin maridan
nan sai suka samu kansu awani daji mai yalwa itayuwa da
ganyayyaki bayan sun samu natsuwa sai Balduna ya fashe
da kuka ya dubi boka Balduna yace kaico dan uwana
hakika ina matukar son Gimbiya Lubiya to amma ya
zama dole in hakura tunda na tabbatar takobin Gimbiya
Sarbila bazai kwatu ahannun Yarima Samar ba Zumbur
Boka Balduna ya mike ya kwarara ihu yace karyane ace
dan uwan haihuwata ya nemi abu awannan duniya ya
rasa alhali ni ina raye tabbas sai ka samu gimbiya Lubiya
koda ko zan rasa raina Balduna ya mike yace kaico dan
uwana karmu yaudari kan mu na hakura.
Boka Balbuna ya kwashe dan uwansa da mari sannan ya
fashe da kuka ya rungume shi sai da suka dau lokaci mai
tsawo sannan suka rabu da juna Boka Balbuna ya dafa
kafadar dan uwansa yace tabbas zamuyi nasara kawai ka
saurareni Boka balbuna ya share kasa ya rubuta wasu
murdaddun rubutu ya share sai ya kece da dariya ya
mike ya kama hannun dan uwansa yace tashi muje
Balduna yace ina zamu yadan uwana Ya tintsire da dariya
yace gurin hatsabibi dan hatsabai kaji mutum da rabinsa
mutum rabinsa shaidan dan shaidanu kaji haihuwar
mutum da aljan iblisu uban shaidanu garnakaki garkami
wandon karfe koya saka ya kwana atsaye tinjim yasha
kundum mijin masifa da bala ii.
.
Koda Balduna yaji irin wannan kirari da zuzutawa da dan
uwansa kewa wani mahaluki sai yace yakai dan uwana
shin wani Hamshakin Bokane wannan da kake
kururutawa haka Boka Balbuna ya kece da dariya yace
babban malami nane abokanci lallai ya shahara kuma ya
tumbatsa aharkar tsubbu da bokanci ahalin yanzu yana
can gidansa dake karkashin kasa adajin Sauban lallai in
har muka riskeshi tabbas zai mana maganin matsalarmu
amma akwai matsala guda daya Balduna yace menene
matsalar yakai dan uwana boka Balbuna yace tabbas
kafin mu isa gidan Boka Ruman sai mun dandani azaba
da masifu kala dari lallai daji ne da akewa lakabi da
kurman adajin akwai miyagun mutane da shaidanu
aljanu adajin Sauban amma idan muka jajirce kuma
mukasa aranmu sai munyi nasara to kuwa lallai sai munyi
nasara Balduna yace ai matukar zuciya zata samu abinda
takeso to gangar jiki zai daure wuya tunda ba haushe
yace wuya bata kisa sai suka rungume juna
.
Al amarin yarima Samar da budurwar nan kuwa sai ta
miko masa takobinta sannan tace ni sunana Kaulatu
bintu Kaluta sunan kasar mu kahunam ya kasance
babban birni dake cike da mutane maza da mata muna
zaune cikin soyayyar juna da kaunar juna domin
mahaifina shine Sarkin kahunam kuma ya kasance adali
mai tausayi ga talakawansa ya tsani zalunci kuma baya
son azzalumi gashi sam baya bambance tsakanin talaka
da mai kudi matukar wani zai zalinci wani tofa bazai
kyaleba wannan dalilin ne ya haifar mana da kwanciyar
hankali da soyayyar juna tabbas mutanen kasar
Kahunam sun kasance jarumai kuma zakakurai afilin
daga sam bamu san tsoro ba kuma muna da tsananin
hadin kai domin idan masifa ta samu dayan mu to duk
tsananin wuya baza kaga yan uwansa sun gujeshi ba
tabbas sai sun taimake shi koda ko za ayi asarar rayuka.
Da mutanen Kahunam su ga mutuwar dan uwansu
agabansu to ina tabbatar maka gara su rasa rayuwarsu
gaba daya koda kuwa sun kai su dubu da wannan hadin
kanne muka gagari makiyan mu domin bamu da
munafiki kuma bamu da rago kwatsam muna zaune
lafiya sai wata annoba ta fado birnin mu wata muguwar
cutane ta bayyana akasar haka kurum sai mutum ya
kama kuraje ajikinsa ta ko ina da zarar an kwana biyu sai
fatar mutum ta fara rubewa haka kuma da an kara kwana
biyu sai fatar ta fara
zagwanyewa haka za kaga mutum ya koma ba komai
ajikinsa sai kashi kuma abin mamaki sam mutum bazai
mutuba tun ana ganin abu kamar wasa sai abu ya cika
gari ko ina cuta tayi yawa ta buwayi jama'a munyi duk
yanda zamuyi mu samu maganin cutar nan amma abin
ya gagara.
.
kwatsam rannan ana fadanci sai wata aljana yar gajeruya
ta bayyana atsakiyar fada dakaru suka zare takobi sukayi
kanta sai ta sabi kalaman surkulle gami da kalaman
tsatsuba ta nuna dakarun da su nufota take wuta ta
konesu wasu suka taso mata tayi hura da bakinta wata
kakkarfar iska ta sunkucesu tayi waje dasu har yanzun
nan da nake maka bayani ba a sake ganin su ba kuma ba
a san inda suke ba koda sarki kaulata yaga haka sai ya
hana Dakaru fuskantar Aljanar nan take kowa ya tsaya da
fada tayi shiru bakajin motsin komai sai wurwurga idanu
jama'a sukeyi suna kallon aljanar nan atsorace can Sarki
ya mike yace yake wannan bakuwar aljana menene
dalilin ki na zuwa wannan guri aljana ta kece da dariya
tace da tun farko kun tambaye ni ai da mutanen ku basu
mutu a banza ba
.
taci gaba da cewa ni sunana gurdil kuma nice sarauniyar
gajerun aljanu tabbas mun kasance muna bukatar
Takobin Jaruma Sarbila wanda ahalin yanzu takobin tana
hannun wani jarumi wanda ya kasance jinin tane na asali
mai suna Yarima Samar to wannan takobin muke so kuje
ku raba Yarima Samar da ita Sarki Kaluta yace mu
mutane ne ku kuma aljanu ne me zaisa bazaku karbo da
kanku ba alhali kun fimu karfi kuma kun fimu karfin sihiri
aljana ta daure fuska tace kasani yakai wannan sarki
Ahalin yanzu Samar yana hannun Maridan nan masu
tsananin tsawo da karfi lallai inda wadannan maridan
suna raye to da bamu da damar kusantar dajin nan
domin sun fi mu hatsabibanci amma ku zaku tsince shine
abagas bayan ya gabza yaki da muridan nan yasha wuya
ya galabaita to sai ku shammace shi ku wafce takobinsa
Sarki kaluta yace to idan har muka dauko takobin nan
menene ladar mu agareku Aljana Gurdil ta kece da dariya
tace zamu muku maganin cutar dake damun ku Sarki
yace tayaya zamu amince da cewa zaku iya yi mana
maganin cutar dake damum mu aljana tace akawo
kwarya aka kawo ta karba takama surkulle tana sambatu
take kwaryar tacika da ruwa tamika kwayar tace abawo
masu fama da cutar nanfa aka fara bawo wasu na farko
yana sha tuni sai yakoma kalau tamkar bai taba wani
cutaba nanfa aka shiga rububi ana shan ruwan nan duk
bakin wanda yasha ruwan nan sai da ya warke koda ganin
haka shine muka tari aradu daka muka shirya muka fito
farautarka

Kawai sai yarima Samar ya mikawa Kaulatu takobin ta
kalleshi yace jeki maza ki ceci Jama'arki ta karba takama
hanya ta nufi birninta saura kiris ta isa kofar garin Kawai
sai taji kasa na girgiza tana tangal tangal kamar zata kife
kwatsam sai ga jerin gwanon tawagar wasu Shirga
shirgan mutane suna bisa wasu maka makan giwaye sun
tun karota ta juya da baya sai tayi arba da wata tawaga ta
murza murzan mayaka su kuma sukan nagartattun
dawakai bakake sidik Gabas da yamma kudu da arewa
mazaje ne sun kewaye KAULATU
Tab bari na pece kafin abu yazo ya dugunzume hehehhhe
MUHADU A LITTAFI NA UKU DON JIN YANDA ZATA
KASANCE nàku real rayyañu

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment