Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunkari hanyar ma unnaru wani
wawan tsawa aka daka masa boka karibu yayi
duba ga mai yi masa tsawan sai yaga wani
basamuden aljanine aljanin yace kai bil adama ka
tsaya a matsayin ka lallai bamu da niyyar kashe
ka amma in ka kara taku daya kai gaba ba baya
ba lallai yau zaka mutu boka karibu ya dubi
aljanin ya kece da dariya yace kai maigadi lallai
kasani yaro ake wa umurni yabi amma uban gida
sai dai ya baza iko.
Ya nuna aljanin da dan yatsa yace to kasani koda
kakan ku ifritu minal jinni zaizo nan to bai isa
yasa in juya da baya ba lallai tunda nazo nan
babu wani mahalukin da ya isa mutum ko aljan
ya hanani diban ruwan nan lallai in kukace zaku
dakatar dani to mutuwa ce zata yanke hukunci
tsakanin nidaku aljani ya kwarara ihu yayi umurni
da a afkawa Boka karibu
.
Lokacin da wani yanki na aljanu sukayi kan Boka
Karibu sai yayi girgiza take ya rikide ya zama
wani basamuden dodo ya mika hannu
sama sai wani mahaukaciyar guduma ta bayyana
a hannunsa yayi kansu a fusace har wani aman
wuta yakeyi take ya zamar wa aljanun nan
alakakai ya shiga shirga musu guduma duk
wanda ya daka ya tashi daga aiki kenan domin
tarwatsewa yakeyi aljanun nan hankalinsu ya
tashi suka kara zage dantse suka zagaye shi
suna kokarin su masa kofar rago koda
boka karibu ya fahimci haka sai yayi wani gurnani
sannan ya bude bakinsa take wata wuta zazzafar
wuta ta futo a bakin sa tayi wa aljanun nan
kurmus.
Turkashi gaba da gaban ta aljani ya taka wuta
nanfa aljanu suka sha jinin jikinsu katon aljanin
nan da ya masa tsawa a farko ya dubi boka
karibu ya kece da dariya yace lallai ka cika
shu'umi amma zaka san kazo gidan iyayen ka
kafin Boka karibu yace wani abu tuni komai da
komai na wurin ya bace ya dawo
tantagarya sahara boka karibu ya dawo siffarsa
na asali ya fara dube dube yana waige waige
kawai sai yaji an kwashe da dariya ba
kakkautawa tsit akayi shiru kawai yaji An tabka
masa sara jini yayi
tsartuwa ya waiga a fusace sai yaga wani aljani
ya nutse acikin yashi boka karibu yaje gurin
amma
baiga ko wani alama ba kamar fitar kibiya wasu
bakaken aljanu kimanin su arba in suka fito daga
cikin karkashin kasa.
Suka kewaye shi suka afka masa da sara da suka
yaki mai tsanani ya kullu atsakaninsu tabbas
aljanu ne masu taurin rai domin sun dauki tsawon
sa a uku suna kafsa yaki amma ya kasayi wa ko
daya kwarzane haka suma sun kasayi masa
komai saboda tsananin naci sai da suka gajiyar
da shi lilis sannan suka daka tsalle suna dira sai
sunutse acikin kasa Boka karibu ya kama waige
waige yana
haki kamar kibiya haka wasu aljanun suka kara
futowa daga karkashin kasa suka farwa Boka
karibu da azababben yaki wannan karon sai da
aljanun nan sukayi wa boka karibu yanka har uku
ganin
haka ransa ya baci ya takarkare ya kwarara ihu
ya far musu da sara da suka.
Kafin kace haka ya kashe aljanu uku koda aljanun
nan suka ga haka sai suka nutse acikin a yashi
ran yan maza ya baci yayi wani muni ya kumbura
ya kara tsawo ya koma kamar wani dodo sai ya
kama kirari saini boka karibu bn kalab in sha jini
in barwa yaro fata tsafi gado nane mugunta ajini
nane saini azzalumi dan azzalumai wane yaro
kuma wane uban yaro sai ya kurma ihu ya daka
tsalle yayi alkafira sai ya nutse acikin kasa waiyo
bala i ya auku ai sai karafkiya da karar mazaje
kakeji haka kawuna da kafafuwan aljanu suka yo
waje gunduwa gunduwa daga karkashin kasa
tabbas yau aljani ya taka wuta sai tsalle acikin
kankanin lokaci boka karibu yayi kaca kaca da
aljanun dake karkashin kasa sai gashi ya bayyana
a saman sahara kai in ka kalle shi sau daya
bazaka sake son kallon sabaSIHIRTACCIYA
.
Littafi Na Biyu 2 part B
.
Lokacin da Boka karibu bn kalab ya bayyana a
sararin sahara sai ya takarkare ya kwarara ihu
yayi girgiza wani kura ya tashi yayi wani surkulle
wani gora cike da da ruwa ya bayyana ahannunsa
yak kwarara ruwan akansa ya girgiza kansa yana
samun natsuwa sai yayi arba da wani makeke
gida ginin dutse da dutse sai yaji wata kakkausar
murya tana cewa dakyau abokina lallai kayi kokari
amma kasani wannan gida shine wahalarka ta
karshe domin wannnan ruwan ma unnar yana
cikin wannan gidan saboda haka ka shige shi
kasani tsagwaron karfi da tsafi bazai fitar da kai
awannan tsinannen gidan ba dole sai kayi amfani
da ilimi da basira da kuma lura kai tsaye Boka
karibu ya tunkari gidan dutse babu fargaba ba
tsoro tafiyane na a mutu ko ayi rai.
Al amarin Sarbila kuwa lokacin data farfado sai ta
mike tasa mabudin kofar karshe ta bude kofa
tana budewa sai tayi arba da bakar damisa a
tsaye a bakin kofar tabbas babu wata hanya da
zata iya wucewa face ta gwabza fada da bakar
damisar kawai sai ta jada baya taku uku sannan
ta sheko aguje ta afkawa damisar nan suka
kacame da fada damisar tayi wa Sarbila mugayen
rauni har guda Uku ita kuma tayi nasarar karye
wa damisar wuya tilas tazube akasa tanaji tana
gani Sarbila ta wuce Sabila na shiga sai ta tsinci
kanta awani wawakeke kogo ga fadi ga zurfi sai
taji muryar bokanya alimma tana cewa tabbas
aikin ki yazo karshe domin awannan kogon ne
zaki samu takobin tarihi wanda da itane zaki iya
kashe babban makiyinki Boka karibu bn kalab
amma kisani zaki sha azabar da baki shaba
abaya lallai kishirya shirin tunkarar mutuwa ko
rayuwa
.
Lokacin da Sarbila ta tsinci kanta awannan
wawakeken kogo sai taci gaba da tafya tana
tafiyane anatse tare da shiri ko ta kwana sai ta
riski wasu hanyoyi guda uku kowacce hanya anyi
rubutu akan allo ankafe ahanya ta farko an
rubuta ya mai tafiya wannan hanyar in ka bita
lallai zaka sadu da arziki mai tarin yawa hanya ta
biyu an rubuta ya kai mai tafiya idan kabi
wannan hanyar to zaka riski ajalinka hanya ta
uku an rubuta ya kai mai tafiya shin kana bukatar
samun sarauniyar kyau ko sarkin kyawawa na
samari kabi wannan hanya.
Sarbila tayi nazarin wadannan rubutun tace nidai
banzo nan da niyyar samun dukiya ba sai tace
haka kuma kwata kwata ban shirya yin aure ba
sannan bana bukatar mutuwa ayanzu har sai na
cika burina ta rasa hanyar da ya kamata tabi can
sai tayi dogon tunani tace ance hanya ta biyu zan
riski ajalina to idan na gagari mutuwar akarshe
dole akwai wani abu da zan samo kai tsaye ta
danna kai hanya ta biyu sai taji wata murya tana
cewa tashirya mutuwa masheka kushirya shirin
aikata kiyama.
Kawai sai taji wani shuuu abayanta tana waigawa
sai taga wasu kibiyoyi sama da guda dubu sun
nufota bata da zabi dole tasa gudu suka kasa
tsere da kibyoyin nan abin mamaki ko tayi kwana
sai kibiyoyin suma sunyi kwana sai da ta shafe
sa a uku tana tika gudu amma kibiyoyin nan na
biye da ita atsiyace ta tabbatar in zata shekara
tana gudu baza su daina binta ba gashi kuma
haki na neman yaci karfinta take taja ta tsaya ta
fuskanci kibiyoyin nan ta zaro wani dogon mashi
tana jiran zuwan kibiyoyin nan suna karasowa sai
ta shiga karkade su suna faduwa kasa abin
mamaki indai bata daki kibiyar ba toko kibiyar
bazata fadi kasaba tana nan tana kokarin neman
Sarbila.
Sai da ta dauki lokaci mai tsawo sannan tayi
nasarar karkade kibyoyin nan duk da haka sai da
wasu suka soketa sun kuma yi mata munanan
raunika sarbila ta durkusa ta zare kibiyoyi uku
ajikinta jini ya tsartuwa dakyar tayiwa kanta
magani sai ta baje akasa ai tana kwance sai taji
ana shawagi akanta ta kyalla ido sama sai taga
wasu maka makan angulaye ne ke shawagi
asamanta tayi zumbur ta mike ai kamar suna
jiran mikewarta sai suka afka mata wai zasu
cinyeta da ranta dakyar ta samu damar ciro
makami suka shiga bata kashi sai da angulayen
nan sukayi mata fata fata amma tayi nasarar
kashesu gaba daya ta durkushe tasa guiwarta
akasa.
Ana wata ga wata sai ta hangi wata ruduna na
mzaje sun tunkarota da muggan makamai ta
rintse idanunta ta bude ta girgiza kanta tace ance
in aski in yazo gaban goshi zafi gareshi tabbas
gaskiyane sai ta ware baki tayi kururuwa gami da
karajin fusata tazaro wasu takubba ta mike ta
shiga aguje ta afkawa mazanjen nan dayakin
mutuwa.
Ko sau daya bata ba wo wani damar ya sare ta
ba duk lokacin da ta kai sara to bata kuskurewa
rayuka kawai take dauka cikin dakika kadan
takarar da mazajen nan ta kwarara ihu ta zama
kamar mahakaciya tayi cikin kogon agoje ba
mutum ba ko aljan ya sha mata gaba sai ta
rabashi gida biyu ahaka tazo gaban wani katon
tebur sai taga wata jar takobi wanda har wani
mele mele takeyi tabbas itace takobin tarihi ta
tunkareta sai nau'in aljanu da miyagun dabbobi
da shu uman mutane da tsuntsaye kai har da
iska da ruwa suka shiga fuskantar ta amma
sarbila take kashesu tamkar dutse take jinta ita
kanta sarbila ta mance kanta sam bata tsoron
mutuwa yaki take ba tare da tasan me take yaka
ba ita abinda take hange kuma take iya gani itace
takobin tarihi saboda haka duk abinda yasha
gabanta to kwanansane ya kare.
Lokacin da Sarbila tayi nasarar sa hannunta ta
dauki Wukar tarihi bata san wukar tana tsakiyar
narkakkakiya ruwan dalma bane sai da ta jefa
hannunta sannan taji wani bala in masifaffen zafi
kamar na fitar rai amma saboda tsananin kafewa
da jarumta sai da ta dauko takobin tana daukowa
gaba daya halittun suka bace ita ko sai tayi
maza ta daure wukar a damarrarta sannan tafal
falo aguje ta nufi kofar fita kamar ana jiranta
kawai sai kogon ya shiga rushewa duk inda
sarbila tasa kafa ta cire take gurin zai burma
gudu takeyi kamar ranta zai fita sai taji an
tattarata an watsota waje tayi koli koli ta fado
cikin dajin ikbal tana kallon kogon yana narkewa
ta shafa wukar taji ta tana nan take sarbila ta
suma saboda tsananin wahala
.
Al amarin boka karibu kuwa gadan gadan ya
tunkari gidan nan ya tadda kofar arufe ya takura
ya tara jini ya kumbura yasa kafa ya banke kofar
take kofar ta babbake ta sama ta fadi wani yanki
na gidan ya kama rugujewa kai tsaye ya fada
cikin gidan yana shiga sai ya tarar gidane lungu
lungu sako sako ya fuskanci wani lungu yayi
tafiya mai nisa sai yaga wani matattakala yayi
sama ya tunkari matattakalar nan yana zuwa ya
fara hawa ya taka matattakalan farko yawuce ya
taka na biyu ya wuce a na biyun sai matattakalar
ya kauce aiko sai Boka karibu yayi cikin wani
wawakeken rami sai tafiya yake ba alamar zai kai
karshen ramin tun yana ganin haske har ya daina
ganin haske tun yana numfashi har ya fara jin
iskar tana masa kadan.
Daga kasa kuma wani masifaffen zafine keyowa
sama Boka karibu yayi duba zuwa kasan ramin
sai ya hango wuta gagga gagga tayo sama
tabbas yana gab da halaka tuni ya kama kalaman
tsafi gami da surkulle yayi tsatsuba gami da
kalaman surkulle take wata kakkarfar igiya ta
zuraro ramin daga sama caraf ya kama igiyar ya
fara yowa sama da masiffen sauri haka itama
wutar tayo kansa sukasa tsere tirkashi lallai
wuya badadi da masifaffen gudu ya karaso bakin
ramin yayi tsalle ya fito yana fita wata
dunkulalliyar wuta tayi waje.
Boka karibu ya kece da dariya yace lallai na shigo
shu umin gida sannan ya koma yayi nazarin
matattakalar nan sai yayi murmushi kawai sai ya
kama hawa in ya taka na farko to bazai taka na
biyu ba in ya taka na uku to sai ya tsallake na
hudu da na biyar ahaka yawuce ya isa wani fili
wanda aka kawatashi da kayan alatu ga kujeru
luntsuma luntsuma an ajiye abinci kala kala
Boka karibu yayi murmushi kawai sai ya wuce
kayan dadin nan kaaaaaiii yaji an daka masa
tsawa yayi duba ga mai yi masa tsawar nan sai
yaga wani narkeken kato rike da takobi yace wa
Boka karibu idan kanaso kawuce lafiya to dole sai
kaci wani abu daga abubuwan dake cikin wannan
falo Boka karibu yace to bana bukata katon nan
yace to lallai kuwa zaka mutu boka karibu ya
zare takobi yace wa katon nan taho mu gwabza
suka runtumo aguje akayi haduwar gwanaye
Yaki ya sarke atsakaninsu mai tsanani tamkar
zasu kashe kansu tabbas karfi yazo daya saida
suka shafe sama da sa a bakwai babu wanda
yayi nasarar yankar wani kai koda Boka karibu
yaga wankin hula zai kai shi dare sai ya canza
salon yaki ya shiga yin tsalle gamida alkafura
yana kai yanka ta sama ta kasa ai nan take
lissafi ya canza tuni yayi wa katon nan fata fata
kankace haka ya sare masa hannaye guda biyu
ya baje akasa kawai sai boka karibu yayi gaba ya
barshi akwance yana tafe sai ya tarar hanya ta
kare sai ya juya zai koma da baya kikam nan ma
sai yaga kofa tarufe nanfa hankalinsa ya tashi
yafara surkulle gamida tsatsube tsatsube yayi
gumi yayi sharkaf amma bai samu kofa ba sai ya
koma ya kalli gaba yayi nazarin gunkin dake
gabansa ya tabbatar dole akwai kofa ajikin katon
gunkin daya toshe masa hanya kuma lallai zayui
ya zama daya daga cikin sassan gunkin nan ne
zai zama mabudin kofar take ya kama hannun
gunkin.
Caraf gunkin ya rike hannunsa ya matse shi gam
tsananin zafi da zugi boka karibu ya fasa ihu sai
dakyar aka sakeshi ya kara kurawa gunkin ido
nanfa yashi ga rudani ya rasa inda zai taba ajikin
gunkin nan yayi kumaji ya cafki nonon gunkin nan
haba ai sai yaji an rufeshi da duka ko ta ina
bakakkautawa sai da akayi masa lilis aka hada
masa jini da majina sannan aka rabu dashi.
Wata kakkausar murya tana cewa kayi kuskure na
karshe muddin ka sake lallai zaka halaka Boka
karibu bn kalab ya natsu yayi nazarin gunki sosai
kawai sai yayi kundun bala ya damki cibiyar
gunkin take yaji wani kara sai kofa tabude ya
kunna kai ciki nan yayi arba da rijiyar ma unnar
take ya nufeta gadan gadan nanfa kwankwamai
suka taso masa da mugun nufi inda shi kuma ya
haukace sai girbesu yake yi anyi bakin artabu
kuma anyi mummunan arangama domin sai da
aljanu suka karya boka karibu amma saboda naci
da juriya bai tsaya ba sai da ya dangana da bakin
rijiyar ya dauki gugan karfe ya zura arijiyar aljanu
suka yanyame shi amma sai da ya jawo ruwan
suna dukansa suna yankansa sai da ya dura
ruwan a wani gora ai yana durawa sai gaba daya
aljanun nan suka kama da wuta gidan ya kama
girgiza zai rushe duk da karayar kafansa in kaga
gudun da yakeyi sai ka dauka aljanine yana fita
gidan ya rufta kasa ya nutse take boka karibu ya
suma.
Acan kasar Manohar kuwa tun saura wata guda
jama'a suke bulbulowa daga sassan duniya guri
ya cika ya batse take kasuwan duni ta wanzu
agurin mutane harda aljanu sunata halarta kasar
Manohar dandazon taron mutane afilin gasar sun
cika ko ina ba masaka tsinke kowa yana ta
harkansa sai akaji wani tsawa gamida rugugi
jama'a suka samu natsuwa aka mai da hankali
inda tsawar ke fitowa kura tayi sama ba a iya
ganin komai sannu ahankali kurar ta yaye sai ya
bayyana Boka karibu bn kalab yana bisa wani
toron giwa yana sanye da rigar fatar damisa yana
rataye da wata zabgegiyar takobi sannan ya
makale wani kuttu akugunsa
Take fili ya fashe da ihu da shewa da tafi Boka
karibu yana cika yana batsewa sai kumbura yake
yana fashewa tirkashi har tsakiyar filin gasar
giwan nan ya kawoshi yayi tsalle gami da
katantanwa sannan ya dire atsakiyar fili yan kallo
suka dau ihu da tafi suko mutanen kasar
manohar sai suka shiga cikin damuwa ganin Boka
karibu ya dawo babu duriyar Sarbila hankalin dan
uwanta Sarbilu yafi na kowa tashi inda ya kama
zirga zirga yana kaiwa yana komowa shi ko
Sarkin kasar manohar wato yayun Sarbilu da
Sarbila tuni ya fara kukan zuci yana tunanin in
har Sarbila bata dawo ba to lallai zasu fuskanci
wulakanci na karshe awurin Boka Karibu bn kalab
Kawai sai boka karibu ya takarkare ya kwarara
ihu mai firgitarwa wanda sai da mutane suka fara
guje guje yakara tsaga ihu take jama'a suka
shiga taitayinsu yakama kirari sai ni boka karibu
Dan mai dole in sha jini inbarwa yaro fata wane
mutun wane aljan ni bakar fura dakar iblisai yaro
ya shani ya kwana kiyama ni tuwon tulu mai
wuyar kwasa ya kara tsandara ihu sannan ya
nuna inda jama'ar kasar Manuhar ke zaune yace
ku gayyar matsiyata lallai kusani baku da
tabbacin cewa yar uwanku zata dawo to koma ta
dawo lallai zan kasheta in kifar da kasar ku lallai
sai an rubuta tarihin rushewar kasar ku tabbas
duk wani mai rai akasar Manuhar ba mutum ba
aljan koda kwaro ko dabba to sai ya dandani
azabata lallai sai na muku azaba kala dari
sannan kowannenku sai na kasheshi sau dari da
sannu zaku san yar uwanku ta jawo muku bala'i
da masifa mara adadi.
Kaiiiiiii Sarbilu ya dakawa boka Karibu tsawa yace
kai mahaukaci ka saurara dakyau shin bakaji
karan takun tahowar mutuwar kaba to idan baka
jiba ka saurara lallai ajalinka na tunkarar ka
amma kai wawane baka gane ba kawai sai akaji
kasa na girgiza jama'a suka kalli inda takun ke
fitowa sai kawai aka hango Jaruma sarbila bisa
wani kasurgumin namijin zaki tab di ai sai kallo
yakoma sama ihu ya barke shewa shi kansa sarki
Maridu sai da ya mike yarika tafawa yar uwansa
inda jama'ar kasar manuhar sukasa wata waka
mai tsananin dadi inda gaba daya filin baki daya
na garin suka dauki wakar nan wohoho nanfa fili
ya rikice Sarbilu sa yaruga aguje yaje ya
rungumeta suka fashe da kukan murna jama'a
suka ci gaba da raira waka ran boka karibu ya
fara tafarfasa yana kuna ya cika ya batse wani
dunkulin abu yazo ya tokare masa kirji kishi ya
mamaye ruhinsa ya takarkare ya kwarara ihu mai
razanarwa take guri yayi tsi masu waka suka
daina masu kida suka jefar da ganguna masu
rawa suka shiga taitayinsu na zaune ya mike na
tsaye ya zauna sam babu natsuwa a zukatan al
umma hatta manya manyan sarakuna dake
wannan fili sai da suka firgita guri yayi tsit.
Sarbila ta saki dan uwanta ta haye kan zakinta
cikin takama da nuna isa da izza Zakin nan ya
nufi filin gasa kai abin ya bada sha awa ta yadda
jama'a sai suka sawa Zakin nan tafi tana isa tayi
tsalle tayi katantanwa sau uku sannan ya dira
agaban Boka karibu bn kala ta kalleshi sai ta
fashe da dariya tace yaya har kishi ya kama kane
ganin jama'a na rera min wakokin yabo to ai
tsakanin nida kai akwai bambaci kai azzalumi ne
ni kuma adalace kaga dole in kasance ni na
jama'a ne Boka karibu ya daka mata tsawa yace
ke yarinya ki fadi iya abin da zaki iya fada amma
kisani a karshe mutuwa zakiyi ta daga murya tace
kai bakin azzalumi kasani ni murucin kan dutse
ne ban fito ba sai dana shirya lallai yau ce ranar
ka ta karshe a duniya kamar sun hada baki suka
jada baya taku bakwai sannan suka kwarara wani
kururuwa mai figitarwa da suka zare makamai
suka falfalo aguje za ai haduwar karshe wanda
zai mutu ya mutu mai rabon ganin badi ya gani
Zan Cigaba Insha Allah
>SIHIRTACCIYA
Littafi Na Biyu 2 part 3
.
Lokacin da suka jada baya taku bakwai kamar an
dakatar dasu sai suka tsaya cak sannan suka zare
makamai kamar an busa musu usur sai suka falfalo
da ma tsanancin gudu sai da suka kusa haduwa
sannan suka daka tsalle suka hadu asama suka
sarke da bala en en fada tabbas fadan ba kyan gani
kuma yayi muni ga yan kallo sai da sukayi dakika
dari biyu asama suna kafsa fada sannan suka diro
kasa dole jama'a suka sa tafi domin kowannensu ya
nuna bajintarsa Boka karibu bn kalab ya shiga
jerawa Sarbila miyagun hare hare ita kuma tana
karewa cikin zafin nama ahaka ya yanketa akafada
da kuibin cikinta ta jada da baya tayi kamar zata
fadi tayi ta maza ta jawo wani kyalle ta daure kuibin
cikinta sannan ta kalli boka karibu tayi masa nuni
da yazo ta shirya ya sheko aguje ya kawo mata
wani wawan sara ta damki hannunsa ta shiga auna
masa wasu mudikam naushi sai da yayi sama
sannan ya fado kasa yayi kokarin yunkurawa amma
ya makara tuni tayi kwallo da shi yaje ya bugi wani
katon dirka yayi kara sannan a fusace ya mike ya
kwarara ihu gamida kururuwa yayi kanta ahaukace
Wani masfaffen sabon yaki ya fara tashin hankalin
gaba daya yan kallo sun rude sun kidime tsoro ya
kamasu tuni wasu sun kama kuka wasu sunyi hijira
kai bala i lallai wannan yaki ya amsa sunansa fadan
karshe domin gaba daya Sarbila da boka karibu sun
yiwa junansu kaca kaca a dai dai wannan lokacin ne
Boka karibu ya shammaci Sarbila ya watsa mata
MA UNNAR ruwan wuta take sarbila taji jikinta yana
wani sassandarewa tabbas akwai abinda ke shirin
faruwa agareta shi ko boka karibu sai ya fara sheka
dariya duk da jikin Sarbila ya fara canza kala zuwa
kamannin gunki sai da tayi kukan kura tasa takobi
ta sare hannun boka karibu wanda ke rike da kuttun
MA UNNAR ruwan take hannun ya tsinke ya saki
kuttun Sarbila ta cafe ta watsa masa ruwan boka
karibu yayi kururuwa take shi da sarbila suka zama
gumaka kowanne a kamannisa amma a matsayin
gunki
Gaba daya filin ya rude da ihu wasu suna kuka wasu
na murna an rabasu da alakakai domin dama boka
karibu ya gallabi duniya awannan taron aka nemi
gunkin Boka karibu aka rasa bayan kowa ya watse
sai aka daukin gunkin sarbila aka shigar dashi Garin
manohar daga ranar aka canza abin bauta suka
kama bautawa Gunkin sarbila shi kuma Sarbilu har
ya mutu yana yiwa gunkin hidima har mutuwa ta
rikeshi Samar ya karasa labarinsa da cewa wannan
shine labarin SIHIRTACCIYA WATO MAKARBIYA
KUMA JARUMA SARBILA.
Majalisa tayi tsit can wani dattijo yace ya kai yarima
samar yanzu yaya za ayi a tashi sihirtacciya samar
yayi gyaran murya yace lallai hanya daya ce dole sai
anje Darul sabah domin dibo wani ruwa a wata rijiya
mai suna Baroki tabbas wannan ruwa babu sihirin
da baya karyawa amma kusani masifa da bala in
da suke hanyar zuwa Darul Sabah dai dai yake da
ka tunkarar karanta littafin kudin tsatsuba kuma
kusani idan mutum yayi nasarar zuwa darul Sabah
to mutanen kasar zasu sa masa sharadi guda daya
matukar mutum bai amince ba to komai jarumtar
mutum da hatsabibanbcinsa sai dai ya hakura.
Kuma kusani da zarar munyi nasarar tada
Sihrtacciya to duk inda gunkin Boka karibu bn kalab
yake to shima zai tashi gaba daya yan majalisa
suka mike suka kurawa Yarima Samar kallon
mahaukaci ganin zai taso masifar da bayan shekara
dari bakwai da ya shude Yarima Samar yace yaku
shuwagabannina ya zama dole agaremu mu tashi
Sihirtacciya domin kwanaki casa in Sarki shaddadu
ya bamu zai zo ya dauki sarauniyar mu Yazrina
tabbas yafi karfinmu kuma kuna sane da matukar ya
dauketa har ya kusance ta to masifa da bala'i zasu
rufto mana saboda haka gobe zan dauki hanyar
Darul Sabah lallai sai na tashi Sihirtacciya in cece
mu
.
Gari na waye wa sai garin manohar yayi tajin jita jita
ko ina ka shiga akasar sai kaji ana cece kuce wasu
na cewa basu ga laifin Yarima Samar ba in yace zai
shiga Jandaki wasu kuwa cewa sukeyi akan me zai
bude dakin da yakai shekara dari bakwai arufe
dakaru sun hau layi waziri ya dube su yace yaku
dakarun kasar Manohar lallai ku tsaya tsayin daka
ku hana Yarima Samar shiga wannan daki lallai
masifa zata iya rufto mana sai wani barde mai suna
Zaidu ya ware sannan yace ina tabbatar muku ni
bazan yaki Yarima Samar ba kuma idan kakuce
zaku yakeshi to ni zan goya masa baya take
rundunar mayaka suka rabu biyu wasu suna bayan
waziri wasu suna bayan Samar nanfa aka fara jan
ido ana neman afar wa juna kai kai aka daka musu
tsawa sukayi duba ga inda tsawar ta fito sai sukayi
arba da Yarima Samar yana rike da wata
sharbebiyar takobi sun jero da yar uwansa gimbiya
Yaxrina suna tafe cikin takama da izza da nuna isa
suka isa gurin dakarun nan yace akan me kuke
neman ku yaki junanku bai dace ba.
Magoya bayana na gode muku masu kokarin
takamin birki mu zuba ya dubi sarauniya Yazrina
yace muje ki bude min kofar inga mai burin mutuwa
yasha gaban ki take ta wuce ta nufi jandaki wani da
kare yasha gabanta samar yayi fatali da shi ya mai
da wukansa cikin kufe ya murza hannunsa yace
tabbas bazan kashe dan kasata ba amma in
takama zan kakkarye shi nanfa suka shiga kokarin
tsai da ita shi kuma yasa kafa ya banke wancan ya
make wannan ya sunkuci mutum yayi watsi dashi
da dakaru fulu fulu Akasa Yarima Samar ya kakkarye
su dole kanwar naki suna ji suna gani Yazrina ta
sanya mabudi tabude jandaki Yarima Samar yadubi
jarumai yace duk wanda ya isa ya kuma cika
namijin duniya to ya biyo mu ciki
Ya kama hannun yar uwansa suka shige Jandaki
suna shiga kofar tarufe tsananin duhu dake cikin
jandaki sai da Yarima Samar da Yazrina suka firgita
suka rungume juna sai sukaji kamar ana tahowa da
sauri suka saki juna Samar yace yake yar uwata
mene sirrin duhun nan tace tabbas haske zai
bayyana amma bayan ka zayyano nasa barka ga
dangin uba guda goma ba kuskure lallai idan ka
fadi daya ba daidai ba to zamu halaka dakika biyu
kawai ya rage mana ahalin yanzu muhalaka. Take
samar ya kama fadar nasabarsa Nine SAMAR DAN
SAFAR DAN BAHAR DAN BADAR DAN MARIDU DAN
SAFFA'U DAN ZAFFAR DAN SAKIB DAN SAMRU
DAN ZAMRA'U SAFARA'U.
take haske ya gauraye dakin tirkashi ai sai sukayi
arba da kayayyakin yaki kala kala iri daban daban
Samar yabude baki yana kallo cikin mamaki da ajibi
kuma wani abin mamaki kowane kayan yaki dake
cikin dakin to akwai wani katon gunki a tsaye akan
kayan yakin Sarauniya Yazrina tace ya kai dan
uwana kasani duk kayan yakin daka gani a jandaki
to kayane na tsofaffin dakarun mayakan kasar nan
tsawon shekara dubu biyu duk wani jarumi da
yayiwa kasar Manohar wani abin tarihi to bayan
mutuwarsa a jandaki ake ajiye kayan yakinsa bayan
mutuwarsa yace to yaya idan ina so in dauki kayan
yakin.
Sarauniya Yazrina ta zazzaro ido tace ya kai dan
uwana kasani daukan kayan yakin wani jarumi
acikin jandaki to dai dai yake da yaki da mai kayan
lallai zaka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment