Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a samun masoyiya a
wannan
duniya.Nan take kyakkyawar ta ajiye
farantinan
abincin a gaban jarumi Darusi tayi
masa waniirin
kallo wanda dole ne ya dimauta
dukkan 'da namiji
tace lale marhaban da babban
masoyi,ban taba
zaton cewa mafarkina zai tabbata
gaskiya
ba,kullum sai an nuna mini
dawowarka garin nan a
cikin barcina,ashe kuwa kana tafe,ka
sani cewa jina
da ganina sun zama naka,tafiyata ta
zamana da
kwanciyata,duk begenka ne babu
wata kalma dake
fita daga cikin bakina face
sunanka.Shin yanzu a
wannan karon zaka ceci rayuwata ka
amsa mini
tambayar da nayi maka kayi mini
alfarmar nan
dana nema a wajenka?Kayi hakuri
idan na takura
muku daga zuwanka na dameka da
surutu ko
hutawa da cin abinci ba kuyi ba.Koda
kyakkyawar
budurwar tazo nan a zancenta sai
Jarumi Darusi
ya budi baki cikin sanyin murya yace
yake
GIMBIYA SUZAINA me kike ci ne na
baka na zuba?
Shin kin manta ne na gaya miki cewa
zakiji amsar
tambayarki amma sai bayan na
kammala aikin
daya kawo ni wannan nahiya
taku,haka ma wannan
alfarma da kika nema a wajena bazan
iya yi miki
ita ba yanzu sai bayan na dawo daga
kogon
Taskar Ajali.Koda jin haka sai fuskar
budurwar ta
juye izuwa tsananin damuwa tace
gaskiya zuciyata
da jikina ba zasu sake iyayin wannan
dogon jira
ba,ka sani tuni na roki sarki akan
cewa indai ka
dawo tare da ni zaka wuce kogon
taskar Ajali
kuma ya amince mini saboda mana
sami damar
koyon ilmin bautar ALLAH nima na
dawo na sanar
da sauran yan uwana mata.Baya ga
haka kaima ka
sani cewa zan iya taimaka maka a
cikin wannan
MUGUWAR TAFIYA mai hadarin
gaske.Yayin da
Gimbiya Suzaina tazo nan a zancenta
sai hankalin
Jarumi Darusi ya DUGUNZUMA yace
saboda me
abbanki zai yanke wannan hukunci
alhalin baiyi
shawara dani ba?Koda jin wannan
tambaya sai
Gimbiya Suzaina tayi murmushi tace
Abbana ya
yanke wannan shawara ne saboda
yasan cewa yin
bazai
cutar dakai ba ni kuma zai ceto
lafiyata da
rayuwata daga vutar dana kamu da
ita ta yawan
begenka da tunaninka a kullum da
koyaushe DARE
da RANA.Koda jin wannan batu sai
Jarumi Darusi
ya gyada kai cikin mamaki yace da
Gimbiya
Suzaina wai ke akan wane dalili zaki
kamu da SO
na alhakin ma baki taba ganin fuskata
ba?To idan
kuma ni mummuna ne fa ko kuma ina
da wata
illah a fuskata?Koda jin wannan batu
sai Gimbiya
Suzaina tayi murmushi tace ai mu a
zuci mukeyin
SOYAYYA,koda ban taba ganinka
ba,bansan yadda
kake ba muddin a ka bani labarinka
naji cewar
haka kake kamar yadda na gani da
idanuna tofa
shikenan na kamu da matukar SON
ka.Koda jin
wannan batu sai Jarumi Darusi da
Mujahid suka
dubi junansu cikin matukar mamaki
sannan Darusi
yace to ni din yaya nake?Suzaina tace
kana da
tausayi,hakuri, kunya,kawaici gaskiya
da kuma son
Al'umma.Duk macen data sami namiji
mai irin
wadannan halayen to koda yafi gaba
dayan
mazajen duniya muni da talauci tafi
dukkan mata
samun dacewa saboda zai iya zama
da ita a cikin
kowane irin yanayi take kuma zai
bata cikakkiyar
kulawa,uwa uba zai bata soyayya dari
bisa dari,shi
kuwa SO na gaskiya wanda babu
algus a cikinsa
yafi dinare da lu'u lu'u daraja saboda
su abubuwa
ne da kowa ke iya samunsu amma SO
na gaskiya
ba'a samunsa a gun kowa.Na rantse
da girman
UBANGIJIna ba MUSULUNCI koda
fuskarka ta dodo
ce zan zauna da kai a haka.Koda
Gimbiya Suzaina
tazo nan a zancenta sai jikin Jarumi
Darusi yayi
sanyi matuka kuma nan take yaji ya
kamu da
tsananin SON Suzaina fiye da koyause
duk da
cewa dama can a wancan zuwan farko
da yayiwa
birnin nasu yaji ya kamu da SON ta
amma saiya
danne shi a can karkashin
zuciyarsa.Nan take
Jarumi Darusi ya dubi Suzaina yace
shikenan ki
gayawa Abban naki kicewa na amince
zanyi
wannan tafiya tare dake,koda jin haka
sai Gimbiya
Suzaina ta kamu da tsananin farinciki
taji kamar ta
rungume Jarumi Darusi amma saita
mike tsaye
zumbur ta fice daga cikin dakin da
gudu tana tsalle
da rawa tamkar wata karamar
yarinya.Fitarta keda
wuya sai Jarumi Darusi yaga Mujahid
ya daga
kansa sama yana tunani kuma
idanunsa sun kafe
tamkar ya zaman gunki.
TASKAR AJALI
Littafi Na Shida (6)
Part D
Tamkar ya zama gunki.Al'amarin daya dan razana
Jarumi Darusi kenan ya kama kafadun Mujahid ya
girgiza.Take Mujahid ya dawo cikin
haiyacinsa,Darusi ya dubeshi yace wane irin
mugun tunani kakeyi haka wanda yasa ka zama
tamkar gawar da babu ruhi a jikinta?Koda jin
wannan tambaya sai Mujahid ya kawo gwauron
numfashi ya ajiye tamkar wanda ya farfado daga
dogion suma sannan ya dubi Darusi cikin
murmushi yace yakai abokina kayi sani cewa ba
komai ne ya jefani cikin wannan hali ba face
tsananin mamaki bisa ganin babban dace da
kayi.Duk da cewa banyi yawo a duniya sosai
ba,iyakata nahiyarmu kuma ni ba masanin labarai
bane,amma na tabbatar da cewa wannan budurwa
data fita yanzu daga cikin dakin nan wato gimbiya
Suzaina a duniya kaf a halon yanzu dai babu mace
mai kyanta,amma kuma gashi ta kamu da tsananin
sonka kuma irin son da babu dukiyar da zata iya
siyansa.A yanzu da nayi arba da ita kuma naji irin
kalamanta sai na gane cewa sauran mata sun
kasance tamkar rakota sukayi a wannan zamani
babu wani sarki ko attajiri ko matsafi ko kuma
jarumi dayake da irin wannan mace.Waishin ma
idan Yazirina da Sarila sukayi arba da Suzaina ya
zasuji?Na rantse da girman iyayena sai sun raina
kansu domin bambancin kyawunta da nasu tamkar
an ajiye hoge ne a gaban tsauni.Sa'adda Mujahid
yazo nan a zancensa sai Jarumi Darusi yayi
murmushi yace ai kuma inda kasan daya baiwar da
Allah yayi mata daka dada tabbatar da cewa
Gimbiya Suzaina daban ce a cikin mata,kai ko a
cikin mazan ma samun mai irin wannan baiwa sai
an tona hatta ni kaina dinnan kuwa.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya turnuke Mujahid yace
wannan wace irin baiwa ce take da ita?Darusi yace
baiwace ta jarumtaka da sadaukantaka,ba zan iya
baka labarin Jarumtakar Suzaina da baki ba sai ka
gani da idanunka,ni kaina da muka fafata na gane
kurena kuma saida na nemi taimakon Allah sannan
na sami nasara akanta,ga yadda na sami labarinta
ita kadai take tare ayarin fatake ta tarwatsa su
komai yawansu ta kwace dukiyarsu ta kame
matansu da samarinsu a matsayin bayi kuma tun
da takeyin gumurzu ba'a taba yi mata rauni ba
kuma ba'a taba kaita kasa ba.Nine Jarumi na farko
dana taba fitar da digon jini a hancinta kuma na
kaita kas,abinda ya fara burgeni da ita shine a duk
gwagwarmayar fashin da tayiwa fatake bata taba
kashe mutum ba saidai ta karya shi kuma bata
taba mata,yara da tsofaffi.A yanzu data musulunta
idan ma ta tuno da abubuwan da tayi baya na
zalunci kuka take yi da nadama.Gama fadin hakan
keda wuya sai sarki ya shigo,koda ganinsa sai
Jarumi Darusi da Mujahid suka mike tsaye da
sauri don girmama shi amma sai yayi sauri ya
ruke hannun Darusi ya mayar dashi zaune ya dubi
farantin abincin da Suzaina ta kawo musu sannan
ya dubi Darusi yace me yasa baku ci abincin ba
alhalin nasan cewa irin wannan abincin ka fiso a
garin nan musamman gimbiya ta shirya maka
shi.Koda jin haka sai Jarumi Darusi yayi murmushi
yace ai gimbiya ce ta jamu da hira yanzun nan
bata jima da fita ba kai kuma ka shigo.Koda jin
haka sai sarki yayi murmushi yace to ni dai ba hira
nazo muyi ba dama nazo ne na shaida muku cewa
gobe da safe akwai GASAR JARUMTAKA ta karshen
shekara wacce muka sabayi a kofar fadata.Na
sanar da abokan tafiyarku Sarila da Yazirina cewa
'yata Suzaina ce ke ruke da kambun a hannunta
shin a cikinsu akwai wanda yake sha'awar shiga
cikin wannan gasa?Koda jin wannan tambaya sai
Mujahid yayi caraf yace nidai ban kasance Jarumi
ba don haka zan tsaya ne na more kallon wannan
gasa na baiwa idanuna abinci.Koda jin haka sai
Sarki yayi murmushi yace ai kai dama bakayi
ruwan jarumai ba kafi kama da masu son samun
kudi a banza,kai fa BABBAN JARUMI?Ina fatan zaka
shiga wannan gasa saboda ina da matukar
sha'arwa sake ganin gumurzunka da 'yata saboda
gumurzu ne mai ban al'ajabi da ban sha'awa.Koda
jin haka sai Jarumi Darusi yayi murmushi yace zan
shiga wannan gasa amma bazan karbi kambun
ba,gimbiya nake so ta lashe gasar saboda ta
nunawa abokan tafiya girman jarumtakarta akan
tasu.Ya shugabana na roke ka da kada ka gayawa
gimbiya cewar zan bata dama ta lashe
gasar.Waishin Sarila da Yazirina sunga Gimbiya
kuwa?Sarki yace a'a basu ganta ba,ai wani
bangare dabam a cikin gidan nan nasa aka kaisu
nesa da inda turakar gimbiya take.Koda jin haka
sai murna ta kama jarumi Darusi yace yauwa dama
nafiso sai a filin gasar suyi arba da ita inda zasu
ga irin tsananin kyawun da Allah ya bata da kuma
baiwar jarumtakarta domin su san cewa kome
mutum yake takama dashi akwai wanda ya fishi.ME
ZAI FARU A WANNAN GASAR JARUMTAKA DA
ZA'AYI A BIRNIN ARNAN DAJI WADANDA TUNI SUN
KARBI ADDININ MUSULUNCI A WAJEN JARUMI
DARUSI?
WACE IRIN MASIFA CE TAKE ADDABAR MUTANEN
BIRNIN ZAMRAS KUMA ME ZAI FARU IDAN SU
DARUSI SUKA ISA BIRNIN?
INA LABARIN SARKI DAMNASH WANDA YA TAFI DA
YANKAKKEN HANNUNSA GUDA?
SHIN ZAIYI WANI SHIRI NE NA DAUKAR FANSA A
KAN DARUSI DA KUMA NEMAN KOGON TASKAR
AJALI?
YAYA KARSHEN KIYAYYAR SARILA AKAN JARUMI
DARUSI ZATA KASANCE?
WACE IRIN ALFARMA CE GIMBIYA SUZAINA TAKE
SON DARUSI YAYI MATA KUMA YAUSHE NE
DARUSI ZAI BUDE FUSKARSA KOWA YA GANI?
Mu Hadu A Taskar Ajali Littafi Na Bakwai domin
Jin cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen
Labari.TASKAR AJALI
Littafi na Shida 6
Littafin Abdulaziz Sani m gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]
TASKAR AJALI
Littafi na bakwai 7
Littafin Abdulaziz Sani m gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]

KASHE GARI tun da duku dukun safiya kafin
haske ya baiyana mutanen birnin daji suka rinka
tururuwa a kofar
fadar sarkinsu saboda murna da dokin
gasar jarumtakar da za agabatar wacce kambunta ke
hannun
gimbiya suzaina yar sarki
kafin rana ta bude tayi haske''
Fadar ta cika ta batse da bil'adama duk inda
ka hanga baka ganin komai face kawunan bil'adama.
Yazirina , sarila, mujahid da jarumi Darusi tuni
suma sun halacci filin gasar tun da farkon safiyar
shi ma sarki da fadawansa da dukkan jama ar
gari maza da mata sun halacci filin gasar
amma har sa 'o'i biyu suka kara
shudewa ba a fara gabatar da wannan gasa ba sarila
yazirina da darusi na tsaye a cikin filin gasa tare da
sauran dakarun da zasuyi gumurzu kimanin mutum
arba'in
nan fa kowa ya kosa da yaga an fara wannan gasa
musamman sara
da yazirina cikin alamun fishi sarila ta dubi darusi
tace wai shin wa ake jira ne har yanzu da ba za a fara
wannan gasa ba ga shi rana na dada budewa
an shanyamu a cikinta saikace tsummokara?
Koda jin wannan tambaya sai jarumi darusi yayi
murmushi
yace ba kowa ake jiraba face jarumar jarumai
mai rike da kambun wannan gasa wato gimbiya suzaina''
koda jin wannan batu sai sarila da yazirina sukayi tsaki a
lokaci
guda tamkar hadin baki sannan sarila tace kawai don ta
kasance yar sarki shine zata wulakanta mutane tayi
ta bata mana lokaci to ai kuwa yau saina wulakantata
a gaban jama ar ta nayi mata dukan kawo
wuka na ragargaza sassan jikinta da takobina in yaso naga
ta girman kai
jarumi darusi yayi murmushi sannan yace '' Tabdi jan ai
gimbia ta wuce zatonku
domin ba kanwar lasa bace ku sani ita rijiyace
gaba dubu kowa ya shigeta ba zai iya fita ba
ta kasance barkono duk wanda ya shaketa saiya zubar
da hawaye da majina amma banda Al amin Guyson ehm
bugu da kari ita hadarice duk inda ta so nan take sa
gabanta
kuma ta cika mace mai dakawa maza gumba a hannu
koda jin wannan batu sai sarila ta bushe da dariyar
mugunta
kuma ta murtuke fuskarta tace
ai idan kaji ana cewa gaki gudu to sa gudu
ne baizo ba inda ba kasa a nan ake gardamar kokawa
tunda dai ga fili kuma ga doki zamuga karshen tika tiki tik!
Kafin sarila ta gama rufe bakinta tuni an buga tambari
kuma an busa algaita
koda jin sautin tambari dana algaitar sai fadar ta rude da
shewa tafi gami
da jinjina nan fa maroka da mawaka suka shiga yiwa
gimbiya suzaina kirari tsawon kusan dakiku dari da
ashirin
ana tayin sowa amma gimbiya suzaina bata fitoba
Al amarin daya kara fusata sarila kenan ta dubi yazirina
tace ai wannan ma shirme ne da kauyanci
yaza ayi ka kuranta wacce take tsoron fitowa ta
tunkaro dodannin da suke jiranta hm guyson.
Koda jin wannan batu sai yazirina ta yi ajiyar zuciya
sannan ta dubi sarila cikin alamun karayar zuciya tace ke
yar uwa
nifa jikina ya fara yin sanyi tun daga lokacin
da naji darusi ya kuranta wannan yar sarki na fara ji
a jikina cewa lallai ta cika jaruma yanzu kuma danaji
yadda mutanen garin nan ke tsananin sonta dayi mata
jinjina saina sake samun karayar zuciya
cikin fushi sarila ta tare numfashin ta tanamai daka mata
tsawa
tace wai shin kema matsoraciyace haka ban saniba yaya
mu da muka ragargaza maza
har ya mace yar uwarmu zata baki tsoro ni na
sani cewa karya ne a sami wannan mace a doron kasa
wacce zata fini karfin damtse
iya yaki da karfin sihiri
idan ke kin karaya ba zaki iya fafatawa da ita ba to ki
janye daga cikin wannan gasa
kikoma gefe daya ki zuba ido kiga yadda zanyi da ita
gama fadin haka keda wuya sai ga gimbiya suzaina ta
shigo cikin filin gasar ta yafa wata kyakkyawar alkyabba a
jikinta
wacce akayita da shudin alhariri sai sheki da walwali yake
alkyabbar ta lullube gaba dayan jikinta
A kanta akwai hular sarauta ta zinare dogon gashin
kanta mai tsananin sheki da walwali ta daureshi ya zuba a
gadon bayanta
har izuwa kan duga dugunta takalmin dake kafarta kuwa
na fatar damisa ne wanda akayi masa ado da zaren zinare
wohoho da baiyanar gimbiya suzaina a cikin filin gasar
sai jama a suka dimauce ba wai maza ba wadanda
suka kama yin kwalla saboda sunsan wutsiyar rakumi tayi
nesa da ksa
mata ma miko hannayensu suka rinka yi domin
su sami damar taba jikin suzaina subar abin tarihi amma
ina damar hakan bata samu ba saboda
dakarun dake takewa suzaina baya sun kewayeta
sun hana kowa rabarta hatta sarila da take ta faman
cika baki tana yin arba da suzaina saita kame kamar gunki
bata san sa adda ta wangame baki ba ta kura
mata ido saboda tsananin mamakin ganin kyawun
fuskarta wanda a duk lokacin da tayi murmushi
sai kyawunta ya ninka kai fatar jikin suzaina kadai ta isa ta
dimauta mutum
domin ta fita daban da ta kowa a duk fadin garin
babu mai irin launinta kuma ko ido idan mutum ya
dubi fatar yasan cewa a fagen taushi ko auduga albarka
ehm guyson ma ya kyasa fa
Ashe sarila bata ga komai ba domin lokacinda
gimbiya suzaina ta iso tsakiyar filin gasar sa adda jama a
keta shewa da tafi ta haukan wani dogon
mumbari sai ta cire alkyabbar dake rufe a jikinta
Tayi cilli da ita sama ai kuwa sai maza yan kallo suka
daka tsalle sama suka sawa alkyabbar wawa kowannansu
na shinshina kamshin dake jikin alkyabbar
koda jama ar sukayi arba da gimbiya suzaina a cikin
shigar datayi sai suka dimauce suka fita hayyacinsu nan
take
samari da yawa suka rinka shidewa suna zubewa kasa
saidai kaga ana yayyafa musu ruwa ana dauke su daga
cikin mutane
mata kuwa yan uwanta kuka suka kama yi saboda
bakin cikin rashin samun irin surarta
wohoho wadansu bakaken tufafi fari gimbia suzaina ta
sanya
rigar ta kasance yar karama kuma mai yankakken hannu
iya cibiya wandaon jikinta kuwa gajerene iya
guiwarta shima ya matseta ainun don haka dukkanin
surorin jikinta sun bayyana
suzaina ta kasance doguwar mace mai matsakaicin
kaurin jiki dai dai misali
kwankwasonta yana da fadi sosai kuma mazaunanta suna
da tudu
kirjinta a cike yake fal kuma duk da cewa
bata sanya rigar rufe kirjinta ba a kumbure suke a tsaye
tamkar balanbalan aka hura''
cikinta a shafe tamkar bata taba ciko shan wani abuba
idanunta manya ne dara dara kuma farare kal tamkar
madarar shanu
tana da dogon siririn hanci tamkar alkalami bakinta dan
karamine
ga kyawawan labba kamar zanen wuka
kaicon maza koda namiji zai zamo shine yafi kowa
talauci a duniya indai zai rinka bude idanunsa yana ganin
suzaina a matsayin matarsa
ta aure to kuwa har abada ya daina takaici da bakin ciki
rataye a bayan suzaina wadansu gajerun adduna ne
wadanda akayi su da zallar karfen
lu'u lu'u
koda ta zaro suta gyara tsayuwarta sai kyawunta ya sake
bayyana
nanfa mazan da hankalinsu bai gusheba gaba daya suka
rinka
fashewa da kuka suna ta zubar da hawayen bakin ciki
fiye da shekaru baya samari da yawa sun rasa rayukansu
bisa
tsananin kamuwa da son ta
a cikin wannan birni domin
duk wanda ya doshe ta da batun so sau daya
ba zai kara marmarin sake son ganinta ba
ma domin kashedin ransa zata yi masa wasu
tsananin tunanin da begentane ya sanya musu
cuta ta zamo sanadin ajalinsau
lokacinda sarki yaga masoya sunata fitowa
don neman aurenta amma taki ta fitar da gwaninta sai ya
kirawo
ta ya kadaita da ita a inda babu mai jinsu
sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace yake yata menene
dalilin daya sa kikaki
fitar da gwani guda daya daga cikin masoyanki
ya zama cewa kwata kwata ma bakya yin soyayya ki dubi
yadda samari
da yawa a wannan kasa tawa suka hallaka
saboda soyayyarki ki sani cewa wannan abu yana
damuna matka tamkar
kina zubar mini da kimata ne mutuncina
lokacinda sarki yazo nan a zancensa sai idanun gimbiya
suzaina
suka ciko da kwallah ta dubeshi tace yakai
abbana kayi sani cewa duk da namijin da zaizo yace yana
sona sai dai fa yasoni saboda dalili guda uku
amma ba dai yasoni sona gaskiya ba wanda babu algus a
cikinsa
kodai yasoni saboda tsananin kyawun da allah ya bani ko
kuma ya soni don matsayina na yar sarki
mai jiran gado ko kuma yasoni saboda irin jarumtakar
da nake da ita ranar da duk na rasa daya
daga cikin wadannan abubuwa guda uku shikenan saina
fita daga ransa
ya daina sona ba zan taba son wani da namiji ba
face na sami wanda na tabbatar da cewa bai damu da
duniya ba sannan kuma dolene ya kasance ya fini
jarumtaka kayi
hakuri ya abbana na sani cewa abune mawuyaci na sami
irin wannan miji amma tabbas indai ban sameshi ba to
na hakura da yin aure har abada
( hm ga Guyson nan ai Indai jarumtane ko Sarki sahibul
hairi na sarkin sarakai bai kaini ba )
Al amin guyson ke magana
ka gafarceni idan wadannan kalamai nawa sun bata maka
rai na barka lafiya
koda gama fadin hakan sai gimbiya suzaina ta mike tsaye
ta fice daga
cikin turakar shi kuwa sarki saiya bita da kallo cikin
alamun tsananin mamaki gami da takaici
saboda tsananin son da sarki yake yiwa
gimbiya suzaina tun daga wannan rana kawo iyanzu
bai sake yi mata maganar aure ba har saida itada
kanta tazo masa da batun cewa ta zabi jarumi darusi
a matsayin abokin rayuwarta nan take sarki yakamu
da farinciki mara misaltuwa saboda murna
a ranar kasa yin bacci yayi
lokacin da yazirina ta dubi sarila taga yadda ta dimauce
bisa ganin tsananin kyawun suzaina da kyawun surar
jikinta saitasa
hannayenta biyu ta kama kafadunta ta girgizata da karfi
nan take sarila ta dawo cikin haiyacinta sarila
ta dubeta tace kada ki bamu kunya mana shin
kin manta ne cewa mu ma kyawawa ne babu kamarsu
a garin nan face wannan gimbiya?
Koda jin haka sai sarila tayi yake cikin alamun
borin kunya tace kenifa ba wani burgeni tayiba
kawai mamakine bisa ganin yadda mutane suka
rude a kanta
dajin wannan batu sai dariya ta kwacewa yazirina tace
haba yar uwata
ai komai hassadarki dolene a ce da mijin iya baba a ko
ina
cikin duniya sai an jinjinawa
wannan yar sarki ke a gaskiya ma ni ina ji a jikina cewar
babu wata ya mace mai
kyanta a wannan zamani kuma ga dukkan alamu
jarumtakarma dolene a samu a tare da ita saboda
akwai alamun hakan
shikuwa jarumi darusi koda yaga irin shigar da
gimbiya suzaina tayi sai ransa ya baci ya daka mata
harara sannan ya kauda
fuskarsa ga barin kallonta da ganin haka sai guyson yaci
gaba da kallonta shi abinsa hm.
Da ganin haka sai suzaina tayi murmushi itama ta kau
da kai ta daina kallonsa saboda tasan cewa tabbasa
tayi laifi to amma da gaiya tayi hakan domin ta nunawa
su sarila cewa ruwa ba sa an kwando bane
nan take alkalan gasa suka shigo cikin filin gasar
ya fuskanci jama a lokacin da filin yai tsit yace
yaku jama ar wannan birnin namu mai albarka ina
mai yi muku barka da zagayowar wannan rana ta
gasar jarumtaka wacce muke gabatar da ita a
karshen kowace shekara kamar yadda aka saba bisa
al ada tun da idanuwanku ga zakarar gasarmu
mai rike da kambu a tsaye a tsakiyar fili wato
gimbiya suzaina
sannan kuma ga jarumai goma daga cikin mutanen
birninmu
Akwai kuma bakin jarumai guda uku mata saikuma
jarumi darusi wanda kunsan shi ba bako bane
kuma ya karbi kambun daga hannun gimbiya
suzaina amma sai ya maida mata da abinta
to wannan karon dai ya sake shiga gasar
ina mai sanar muku cewa wannan karon gasar
ta sauya launin domin gimbiya ta bukaci ta fafata da gaba
daya jarumai goma a lokaci guda sabanin dacan da take
yi
da mutum dai dai
ragowar mutum ukun kuwa zata fafata dasu
daya bana daya ne kuma duk a yau dinnan
take son ayita ta kare ko da jama ar sukaji wannan
tsari sai suka kamu da tsananin mamaki saboda sun san
cewa
ba karamar wahala suzaina zata sha ba
a ce tayi gumurzu da manyan zaratan jarumai
su goma a lokaci guda sannan kuma tazo ta
fafata da wadannan bakin jaruman mata
wadanda suma da ganinsu sun taki wani abu kuma
ga uwa uba jarumi darusi wanda kowa ya tabbatar
da cewa yafita jarumtaka domin a wancan gumurzun
da sukayi tasha wahalar gaske a hannunsa
batare da bata wani lokaci ba aka buga gangar
fara gumurzu nan take alkalan gasar
,
sarila yazirina da jarumi darusi suka fice da sauri
daga cikin filin gasar suka bar gimbiya suzaina tare da
zaratan jaruman goma a tsaye sunyi mata
kawanya kowannansu na rike da zabgegen
makami abin kwatance
su dai wadannan jarumai guda goma ana matukar
ji dasu a wannan birni domin ko yaki za a
dasu ake fita sune a kan gaba saboda sadaukantakarsu
gami da kwarewarsu a yaki
A tarihin yake yakensu ma ba a taba yi musu
rauni ba a filin daga kuma duk yakin da suka jagoranta
sai an
sami nasara ba a taba samun akasi ba amma gaba
dayansu suna shakkar gimbiya suzaina amma a yau
da sukaji cewar suzaina ta yarda su hada
karfi su goman su yaketa sai suka yi murna
saboda lokacin ramuwarsu tazo domin suna ganin
cewa farat daya ma zasu gama da ita
dama wadannan jarumai goma suna matukar jin haushin
gimbiya suzaina saboda babu wanda bai nemi
ya aureta ba har daya daga cikinsu ta wulakanta shi kuma
ga shi
ta dakusar da kimarsu da daukakarsu a idanun jama ar
tunda duk ta kaisu
kas a yayin da suke fafatawa
nan take jaruman goma suka fara kewayeta
suna jujjuya makamansu cikin zakuwa da
mugun nufi ita kuwa suzaina ko motsawa batayi
ba daga inda take tsaye rike da addunanta guda
biyu kuma a natse take bata waigen komai
idanunta ma kasa suke kallo kawai saboda tsabar
yarda da kanta amma ta kasa kunnuwanta sosai tana
sauraren sautin motsin kafafuwan jaruman goma
kwatsam sai jaruman goma suka afka mata gaba
dayansu a lokaci guda sukayi mata rubdugu
suka rinka kai mata sara da suka tako ina
cikin bakin
zafin nama da dukkan karfinsu kaico ciwon ido sai
hakuri
hakika idan allah ya baiwa mutum baiwa tofa
babu yadda makiya zasuyi da shi wanda ya iya
ya huta nan take jama a sukaga abin al' ajabi
domin suzaina bata gusa daga inda take ba
taku guda a haka ta rinka kaucewa sara da sukansu
tana
karewa da addunanta ba tare da ta maida martani
ba sai dai
kaga tana sunkuye da kauce kauce gami da tsalle tsalle
a waje daya su kuwa jaruman goma su kayi
ta sara da sukan isa
har tsawon kusan rabin sa a ba tare da dayansu
ya sami nasarar koda lakutar jikinta ba
bisa dole sukaja da baya sukayi cirko cirko suna haki
gami da kallonta kawai cikin alamun tsananin
mamaki suna tunanin irin salon yakin da yakamata
su sauya
A wannan lokacine yan kallo suka kaure da yiwa
suzaina tafi suka rinka yi mata jinjina
a dai dai wannan lokacine yazirina ta dubi sarila tace
yaya kikaga takun hannun suzaina?
Sarila ta tabe baki cikin alamun raini tace '' eh to babu
laifi ta cika jaruma amma ai kada mage ba yanka bane
kuma sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo
kafin sarila ta gama rufe bakinta sai taga gimbiya
suzaina tayi nuni da danyatsan hannunta na dama
ga dukkan jaruman goma tace
tunda dai na baku dama ku cutar dani
amma kun salwantar da damar bari na jarraba amfani
da tawa damar
koda gama fadin hakan sai suzaina ta yafito jaruman
goma da hannunta
cikin alamun raini tana mai kiransu dasu zo a fafata
koda ganin haka sai jaruman goma suka fusata suka rugo
izuwa
kansu aka ruguntsume da azababben yaki nan take
suzaina ta sauya salon yakin ta hada da kai musu
naushi da bugu da hannu da kafa kuma ta rinka tsalle
tsalle da kwance kwance
a tsakiyarsu wani lokacin har shawagi takeyi a samansu
tamkar ta kasance tsuntsuwa
mai fuka fuki nan da nan kuwa ta fara hada musu jini da
majina
tana kulle musu ciki
Al amin Ahmed Guyson Ke magana..
Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan cikin
kankanin lokaci suzaina ta rikirkita dakarun goma
kuma ta kuntata su har ya zamana cewa basa iya kai mata
hari sai kokarin kare kai
ba zato ba tsammani sai akaga suzaina
ta daka tsalle sama tayi wata irin katantanwa
a sama tamkar an murza mazari kafin ta
diro kasa ta yanke gaba dayan dakarun
goma a kan kafadunsu da kaifin addunanta
kuma ta doki kirazansu da kafafunta su duka
suka zube kasa suna masu dafe raunikan kafadunsu
hatta sarila bata san sa adda tayiwa
suzaina tafi ba bisa ganin wannan gagarumin
jarumtaka da tayi ta ban Al ajabi
Ni kaina Guyson me baku labarin saida na kame kuma
dakyar na cigaba da rubutun..
Sai bayan tayi tafin ta lura da cewa baikamata
ta nuna ta burgete ba nan take ta murtuke
fuskarta a wannan lokaci ne filin gasar ya
rude da sowa a ka rinka yiwa suzaina tafi da jinjina
fiye da wadda akayi mata a farkon shigowarta
filin gasar,
nan take aka fitar da dakarun goma daga filin
da sauri
cikin hanzari alkalan gasar ya rugo izuwa
cikin filin gasar ya dubi suzaina cikin girmamawa
da risinawa yace ya shugabata shin kina da
bukatar hutawa ne kafin kici gaba da yin wannan gasa?
Koda jin wannan tambaya sai suzaina ta dakawa
alkalin gasar harara tace shin kaga alamar na

Please Login or Register in order to submit comment