Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka sai ya ga jini bai

daina

tsatstsafowa ba kuma har a sannan

Sarila bata

farfadowa ba.Al'amarin dayayi

matukar dugunzuma

hankalin Jarumi Darusi kenan ya kasa

zaune ko

tsaye ya rinka kai kawo yana tunanin

abinda ya

kamata yayi.Koda ganin haka sai

Mujahid ya dubi

Darusi a fusace yace saboda me mu

ba zaka zo ka

taimake mu ba alhalin kana ganin

cewa duk mu

biyun mun sami karaya a jikinmu

kuma jikinmu ya

bugu sosai ba zamu iya yiwa kanmu

komai

ba.Koda dai ka kamu da son Sarila ne

shi yasa ka

dimauce haka?Koda jin wannan batu

sai jarumi

Darusi ya fusata ainun ya dakawa

Mujahid tsawa

yana mai cewa baka da hankali ne ko

kuwa baka

ganin halin da take ciki ne?Duk ku

biyun kuna

cikin haiyacinku ita kuwa bamu san

ma halin da

take ciki ba,shin ka manta ne cewa

nayi alkawarin

zan ceci rayuwarku a duk sa'adda

kuka kasa ceton

kanku.Koda gama fadin haka sai

jarumi Darusi ya

koma kan Sarila ya tofa mata wata

addua'a akan

raunin,faruwar hakan keda wuya sai

jini ya daina

tsatstsafowa daga cikin raunin amma

kuma da

Darusi ya dubi yadda take sai

hankalinsa ya

dugunzuma ainun saboda ya fahimci

cewar jini mai

yawa ya zuba a jikinta.Mafi akasarin

mutanen da

suka rasa jini mai yawa haka a jikinsu

mutuwa

sukeyi kuma koda sun rayu sai an

basu kyakyawar

kulawa kuma sai sunyi jinya ta dan

lokaci sannan

zasu sami cikakkiyar lafiya gami da

kwarin

jiki.Jim!Kadan da tofawa Sarila

wannan addu'a

saita farfado daga dogon suman da

tayi tana mai

jan dogon numfashi gami da bude

idanu a hankali

da farko cikin dishi dishi taga jarumi

Darusi

tsugune a gabanta kuma fuskarsa a

rufe idanunsa

kadai ne a waje,sannu a hankai

idanun nata suka

washe amma sai taji kanta da sauran

gangar jikin

nata sunyi mata nauyi ainu ko motsin

kirki ba zata

iyayi ba.Da kyar ta juya da kan nata

ta dubi inda

Yazirina da Mujahid suke,kawai sai

taga kafar

Yazirina a karye har ta dan fara

kumbura shi kuma

Mujahid hannunsa ne a karye kuma

dukkaninsu

akwai alamun tsananin jigata a tare

dasu.Sarila ta

dago hannunta da kyar ta shafi raunin

nata koda ta

jishi a dinke har an shafa masa

magani sai ta dubi

Darusi tayi masa dan guntun

murmushi a karon

farko tunda suka hadu tace ina godiya

a gareka

bisa ceto rayuwata da kayi.Koda jin

haka sai

Darusi yace ki gafarceni lalura tasa na

taba jikinki

domin yi miki maganin.Sarila ta sake

yin

murmushi tace nayi farinciki daya

kasance

addininka bai hanaka taimako ba a

irin wannan

domin da tuni yanzu na dade da

zama

gawa.Darusi yayi murmushi yace ai

addinina yana

da adalci kuma baya son zalunci,na

sani cewa ba

zaki iyayin komai ba yanzu da kanki

don haka in

Allah ya yarda zan cigaba da

taimakonki har izuwa

lokacin da zaki sami lafiya.Yanzu

zanje na taimaki

sauran yan uwan naki.

HALEEFAH A ABUBAKAR

Yanzu zanje na taimaki sauran yan uwan

naki.Koda gama fadin haka sai Jarumi Darusi ya mike tsaye ya tafi inda Yazirina ke kwance ya shiga gyara mata karayar dake kwaurin kafarta.Nan da nan cikin kankanin lokaci ya daure kafar da karare ya shafa mata wani magani na musamman sannan ita ma ya tofa mata addu'a daga nan sai kuma ya mike tsaye ya koma kan Mujahid yayi

masa duk irin taimakon da yayiwa Sarila da

Yazirina.Bayan ya gama yi masa komai tsaf sai ya dubeshi yace dazu kace naki na taimake ku na taimaki Sarila har kana cewa ko na kamu da sonta ne ko?To yanzu kuma me zaka ce tunda gashi

nayi muku duk irin taimakon da nayi mata kuma ka gane cewa na fara taimakonta ne saboda halin data shiga yafi naku hadari.Koda Darusi yazo nan a zancensa sai kunya ta kama Mujahid ya dan

sunkui da kansa kas yana sosa keya yace ka gafarceni yakai JARUMIN JARUMAI hakika zargina kawai yasa na fadi haka.Dajin haka sai Darusi ya mike tsaye daga gaban Mujahid ya juya masa baya sannan yace a addinina zargi haramunne koda ya zamana gaskiya don haka sai ka kiyaye.Darusi ya dubi Sarila,Yazirina sannan ya juya ya sake duban Mujahid yace duk ku ukun ba zaku iya cigaba da tafiya ba a cikin halon da kuke ciki yanzu.A kallah sai kunyi jinya ta kwanaki ashirin kunga kenan kwanakin tafiyarmu sun karu.Koda jin wannan batu sai hankalinsu Sarila,Yazirina da Muhajid ya dugunzuma ainun,Sarila ta dubi Darusi ta budi baki cikin matakuar karfin hali tace yakai wannan GWARZON JARUMI yanzu babu yadda za'ayi mu

cigaba da tafiyar nan a haka in yaso mu cigaba da jinyar jikinmu akan hanya.Ka sani cewa zamanmu a waje daya yana da matukar hadari saboda duk sa'adda ka gusa daga kusa damu masu farautarmu zasu iya baiyana su kashe mu domin su rabamu da taswirar zuwa kogon Taskar Ajali.Koda Sarila tazo nan a jawabinta sai Jarumi Darusi yayi

murmushi yace da izinin Allah babu abinda zai sameku a tsawon zaman da zamuyi,inaso ku tuna cewa a halin yanzu fa doki daya ne jal daya rage mana tunda Aljana Marwisa ta kashe naku

dawakan.Ta yaya zamu cigaba da tafiyar da doki daya kuma a cikin yanayin da kuke musamman ma Sarila wacce ko zama akan dokin ba zata iya ba,ko zata iya fara zama sai nan da cikar kwana bakwai kuma ko ta fara zama ba zata juri dadewar zaman ba a kan doki.Koda jin wannan batu sai duk su ukun suka jinjina kai alamar cewa sun gamsu da abinda ya fada amma sai Sarila ta kuma budar baki tace na amince muyi kwanaki bakwai muna jinya a nan.A ranar kwana na bakwai ni da Yazirina sai mu hau dokinka,Mujahid a matsayinsa na wanda ya karye a hannu zai iya taka kafarsa yayi tafiya kaima haka,idan kun gaji da tafiyar kafa zamu iya tsayawa ku huta sannan mu cigaba da tafiya

hankalinmu zaifi kwanciya idan ka amince da

wannan tsari dana zo maka dashi.Koda jin wannan batu sai Jarumi Darusi ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yace hakika wannan shawara da kika zo da ita zata yiwu to amma kuma akwai yan matsalolin da zamu iya fuskanta wadanda zasu zamo tamkar munyi gudun gara ne mun tarar da zago.Caraf sai Yazirina ta tari numfashinsa tace babu matsala zamu iya jurar duk irin matsalar da muke fuskanta.Dajin haka sai Darusi ya gyada kai yace shikenan tunda kun aminta da hakan,yanzu abu na farko da zamuyi shine mu dauke gawar

wannan Aljana mu kaita can nesa mu kone ta yadda warinta ba zai dame mu ba koya dami

sauran halittun dake cikin dajin nan.Bayan nan kuma sai mu shiga cikin wannan kogon dutse na wannan Aljana mu caje shi mu tabbatar da cewar babu wani mugun abu a cikinsa domin mu zauna acikinsa.Koda jin wannan batu sai Sarila tace to yanzu in banda abinka ta yaya mu da muke a

nakasce zamu iya tayaka wannan aiki?Darusi yayi murmushi yace ai dama ba cewa nayi sai kunsa hannu ba a cikin wannan aiki,kawai dai ina sanar daku ne yadda ya kamata ayi.Gama fadin hakan keda wuya sai Darusi yaje ya dauko wata doguwar igiya a cikin jakar guzurinsa wacce matafiya ke amfani da ita wajen hawa duwatsu da tsaunika masu tsawo ya hada gawarwakin dawakan a waje guda gami da gawar Aljana Marwisa ya daure su tamau kawai sai ya kama igiyar da hannu daya yaja gawarwakin duka a kas ya nufi wani bangaren daban na dajin.Yana cikin tafiya ne ya tsaya cak kawai sai ya dawo da baya ya baro mushen

gawarwakin acan gaba yazo gaban su Sarila ya tofa wata addu'a sannan ya dube su yace kada dayanku ya kuskura ya ketare nan inda kuke.Koda gama fadin hakan saiya juya yaje ya cigaba dajan mushen su kuwa su Mujahid sai suka bishi da

kallo kawai cikin tsananin mamaki har saida ya kauce,ba komai ne ya basu mamaki ba face ganin irin tsananin KARFIN DAMTSEn sa sun sami cewa inda zasu taru duk su ukun ma ba zasu iya jan gawarwakin ba uku a kasa saidai da karfin sihirin tsafi amma gashi Darusi ya hada har dama gawar Aljana Marwisa wacce nauyinta ita kadai ya ninka na doki guda sau uku.Nanfa sukayi ta Al'ajabi suna tattaunawa akan al'amarin inda Yazirina ta dubi Mujahid tace kai waishin anya kuwa Darusi mutum be kamar mu dinnan?Koda jin wannan tambaya sai Mujahid ya bushe da dariya yace tabbas Darusi mutum ne kamar mu yana ci yana sha kuma

yanayi duk irin bukatar da mukeyi,idan yaji ciwo jini na fita a jikinsa,idan ciwo ya kama shi sai yayi jinya,to menene bambancinmu dashi?Bambanci

shine yana da baiwa ta matukar karfin

damtse,Addininsa ba irin namu bane,yana da

matukar hakuri gami da jurewa wahala komai

tsananinta domin cika burinsa,ban taba haduwa da mutumin daya burgeni ba kamarsa.Koda Mujahid yazo nan a zancensa sai Sarila da Yazirina suka kamu da tsananin mamakinsa.

5 hours ago

Abubakar Haleefah Physicist

Yazirina ta dubeshi tace idan har Darusi yana

burgeka hakan na nufin cewa zaka iya yin imani da addininsa haka ne?Mujahid yayi murmushi yace wannan tambaya ba akaina ni kadai take ba,tana kanmu duk mu ukun nan nina tabbatar da cewa

kuma Darusi yana burgeku.Koda kuwa kun tsane shi a cikin zukatanku amma na sani cewa da

sannu za kuji kuna sonsa kafin mu kare wannan tafiya.Akwai abu guda dazai faru yasa dukkaninmu muyi amanna dashi.Koda jin wannan batu sai

Sarila da Yazirina suka dubi Mujahid,cikin mamaki Sarila ta budi baki da kyar tace menene wannan abu dazai faru wanda zai sa na kaunaci wannan shashashan jarumi?Ka sani cewa na tsaneshi

kamar yadda na tsani mutuwa ta duk da cewa ya cece rayuwata ni kawai inayin wannan tafiya ne tare dashi bisa larura saboda yana da matukar amfani a garemu.Sa'adda Mujahid yaji wannan

batu na Sarila sai ya gyada kai yace ba zan gaya miki abinda zakiyi ki kaunaci Jarumi Darusi

ba,anan gaba kuma ina mai shawartarki daki boye kiyayyarki a gareshi kuma kiyi kokari ki saisaita zuciyarki a kan kinsa saboda tsananta KIYAYYA ko SOYAYYA abu ne mai hadari a rayuwa saboda

makiyi kan iya zama masoyi kuma masoui kan iya zama makiyi.Koda Gama fadin hakan sai Mujahid ya mike tsaye yaje inda dokin Darusi yake ya dauko battar ruwa ya bude ya kurba sau biyu

sannan ya juya ya dubi Yazirina cikin murmushi yace kina da bukatar ruwan ne?Yazirina tayi

murmushi tace ina bukata mana.Mujahid ya nufi inda Yazirina ke zauna domin ya bata ruwa tasha amma sai Sarila ta kira sunansa tace ni laifin me nayi maka da bzakayi mini tayin ruwan ba?Ka sani cewa ko don doguwar tafiyar da muka sha kafin muzo nan da kuma bakin gumurzun da muka sha

da Aljana Marwisa dole ne kowannenmu yaji

kishirwa,idan kuma son da kake yiwa Yazirina yafi wanda kakeyi yi min ne saika fara bata ruwan tasha na gani.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Mujahid ya kasa gane abinda take

nufi,shidai ya sani cewa tsakanin ita da Yazirina babu wacce ya furtawa KALMAR SO a fili amma

kuma ya fuskanci cewar kowaccensu tana sonsa amma a badini cikin zuciyarsa hankalinsa yafi karkata izuwa kan YAZIRINA saboda yana

matukartsoron Sarila bisa ganin irin tsantsar rashin imaninta da yadda ta mauar da rayukan bil'adama tamkar na kiyashi.Mujahid ya tsaya yana duru duru ya rasa wacce zai kaiwa battar ruwan yayin da yake ruke da battar da lafiyayyen hannunsa,daya hannun nasa kuwa Sa'adda Darusi ya gyara masa karayar ya rataye shi bisa wuyansa da wani farin

kyalle mai kwari.Mujahid na cikin wannan hali ne suka jiyo sukuwar dawakai da yawa an durfafo bakin wannan kogon dutse daga can nesa.Nan

take duk su ukun suka dimauce hankalinsu ya

DUGUNZUMA ainu Mujahid ya rasa abinda ya

kamata yayi har ya yunkura zai ruga izuwa gaba ya barsu Yazirina a wajen sai Yazirina ta daka masa tsawa ta dubeshi da idanunta da suka ciko da kwallah tace Kai!Mujahid ashe dama zaka iya guduwa ka barni yayin da kaga masifa?Ni a tunani na kana sona kamar yadda na kamu da tsananin sonka na zaci cewa zaka iya sallama rayuwarka domin ceto tawa tamkar yadda zan iya sallama tawa don taka.To ka sani cewa tsayuwarka anan ne kadai zaisa ka tsira da rayuwarka amma idan kayi taku daya gaba mutuwa zakayi tunda Jarumi Darusi ya gargademu akan hakan,idan ka manta ne yanzu na tuna maka kaga kenan na ceci

rayuwarka.Yanzu nike binka bashi a rayuwa ba zan sake yarda da kai ba har abada face ka biyani wannan bashi da nake ninka wato ka ceci

rayuwata.Koda jin wannan batu sai Sarila taji wani irin mugun KISHI ya turnuketa har ta bude baki zata ce wani abu saiga rundunar mayaka ta iso daf da bakin kogon dutsen.A kalla mayakan sun kai su Dubu Dari Hudu kuma dukkaninsu a cikin

gagarumar shigar yaki suke dauke da muggan

MAKAMAN YAKI a gabansu mutum hudu ne mafiya

kwarjini.KALLO DAYA zakayi musu ka gane cewa SARAKAI ne saboda yanayin shigarsu da kuma

kayan yakin nasu irin na sarakai.Uku daga cikin sarakan fitattu ne a nahiyar,daya kuwa bakon sarki ne daga wata nahiyar daban kuma duk ya fiso

girman kwarjini gami da kira irin ta manyan

SADAUKAI.Da kira irin ta Manyan Sadaukai.Da

isowar wannan

runduna sai suka ja linzamin

dawakansu sukayi

cirko cirko suka kurawa su Yazirina

idanu yayin da

kurar dawakan su ta fara lafawa,bayan

kurar ta lafa

sai bakon sarkin ya dubi Sarila da

Yazirina ya

bushe da mahaukaciyar dariyar

mugunta sannan

ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko

masa da

sakon mutuwa yace yanzu gashi a

karon banza

mun sami tsuntsu daga sama

gasasshe,kun gama

yakar junanku kunyi hadin kan dole domin kuje ku

malli dukiyar dake can taskar Ajali

amma ga iya

inda gudunku ya kare ba tare da mun

sha wahalar

komai ba zamu kashe ku mu dauke

taswirorin

dake tare daku tunda abin dogaron

naku Jarumi

Darusi baya nan bare ya baku

kariya.Ku sani cewa

nine Sarki Damshan na birnin

Damashkar a halin

nine shugaban sarakuna uku na

nahiyarku dake

tare dani domin sunyi muba'aya a

gareni,ina mai

tabbatar muku da cewa duk duniya

babu wani

matsafi daya kaini karfin sihirin

tsafi,nasan komai

akan dukiyar taskar ajali kuma duk

abinda ya faru

tsakaninku da wannan bakon jarumi

na gani a

cikin madubin tsafina,yanzu kuna da

zabi biyu ko

dai kuyi mubaya'a a gareni ku bani

wadannan

taswirori guda uku cikin ruwan sanyi

ko kuma na

kashe ku na kwace taswirorin da

karfin tsiya.Koda

Sarki Damshan yazo nan a zancensa

sai kawai yaji

Sarila ta bushe da dariya cikin

tsananin karfin hali

duk da cewa a kwance take tana jin

matsanancin

zafi da zugi a jikinta.Dafa can sai ta

karkato da

kanta da kyar ta dubi sarki Damshan

ya budi baki

tace yakai wannan sarki kayi sani

cewa kamar

yadda wannan duniya take da fadi

haka ma abin

cikinta yake da yawan gaske.Komai

sammakonka

wani a tafe ya kwana,komai nisan gari

akwai wani

a gabansa,idan ka gane abinda nake nufi kome

kake takama dashi sai an sami wanda

ya fika bisa

ganin yadda aka raine ni a cikin

tsumin tsafi kuma

aka bani gagarumin horon yaki dazai

iya fafatawa

dani ba ya kaini kas,amma dana hadu

da wannan

bakon jarumi sai na raina kaina

alhalin da ina

ganin kamar zan iya aza gammo a

kaina nayi

dakon duniyar gaba daya.Kamar

yadda ka bamu

zafi guda biyu nima yanzu na baka

zabi biyun

kodai ku gudu kaida mukarrabanka

domin ku ceci

rayuwarku kafin jarumi Darusi ya

dawo nan ko

kuma ku jarraba karbar wadannan

taswiroro guda

uku daga hannunmu wanda hakan

bazai taba

yiyuwa ba.Koda jin wannan batu sai

Sarki

Damnashi ya fusata ainun take

zuciyarsa ta kama

tafarfasa kamar zata kone kawai sai

ya dubi

dakarun dake bayansa yace kuyi musu

ruwan

kibiyoyi.Nan take dakarun suka

zazzaro kibiyoyi

suka dana akan baka kowa ya tabe

bakan nasa ya

saki harbi.Wohoho!Ha kika abin

al'ajabi baya

karewa a cikin wannan dubiya,koda

dubunnan

dakarun suka harbo kibiyoyin su sai

kibiyoyin suka

tsaya cak a gaban su Yazirina a sama

su basu

cake su ba kuma basu fadi kasa

ba.Koda ganin

haka sai Sarki Damnash ya fara

amfani da karfin

sihirinsa da hannayensa ya rinka

motsa kibiyoyin

domin suje su cake su Sarila amma sai kibiyoyin

suka jiyo da baya da gudu tamkar

sannan aka

harbo su daga cikin bakan suka je

suka cake gaba

dayan dakarun da suka harbo su da

farko.Nan take

gaba dayan dakarun suka fado kasa

matattu daga

kan dawakansu.Sai sarakunan uku

suka firgita

ainun suka dimauce nan take suka

kada linzamin

dawakansu suka juya da baya da

gudu suka

runtuma izuwa cikin daji suna yiwa

dawakansu

kaimi domin su tsira da rayuwarsu

suka bar sarki

Damnash shi kadai a tsaye zuciyarsa a

kekashe ko

alamar tsoro babu akan fuskarsa duk

da ganin

abinda ya faru,fuskarsa ce kawai ta

cigaba da

yatsinewa zuciyarsa na cigaba da

tafarfasa kamar

zata kone.Adaidai wannan lokaci ne

suka hango

Jarumi Darusi ya durfafo su a guje

yana ruke da

takobinsa tsirara,ba komai ne yasa

Darusi ya zare

takobinsa ba ya rugo da gudu face

hango dubban

daruruwan dawakai daga can nesa

amma koda ya

matsa kusa sai yaga ashe gaba daya

mahayan

dawakan sun zube kasa matattu saura

mutum daya

jal a tsaye a wajen sai ya daina gudu

kuma ya

mayar da takobinsa cikin

kufenta.Koda ganin haka

sai Sarki Damnash ya saulo daga kan

dokinsa ya

rike kugu yana mai fuskantar jarumi

Darusi yana

jiran isowarsa.Da isowar Jarumi Darusi

ya zamana

cewa tazarar dake tsakaninsu da sarki Damnash

bata wuce taku biyar ba sai ya tsaya

cak suka

kurawa junansu idanu.Kawai sai sarki

Damnash ya

bushe da dariya bayan yayiwa Darusi

kallon raini

da wulakanci,lokac i guda kuma saiya

murtuke

fuskarsa yace yakai wannan wawan

jarumi kayi

sani cewa bakin rijiya ba wajen wasan

yaro bane.A

halin yanzu duk fadin duniya babu

wani jarumi

daya fini KARFIN DAMTSE,iya yaki da

kuma karfin

sihirin tsafi,idan ka isa kazo mu fafata

da zallan

karfin damtsenmu da iya yakinmu.Na

rantse da

girman iyayena bazanyi amfani da

karfin sihirin

tsafi na ba kai ma ka rantse da

girman iyayenka

cewa ba zaka yi amfani da karfin

sihirinka ba

yanzun nan cikin dakiku kadan zan

kashe ka.Na

rushe burinka na son yada addininka

a wannan

nahiya gaba daya sannan na kashe

wadancan

matan na dauke taswirorin dake

hannunsu guda

uku naje na mallaki taskar ajaki na

zamo SARKITa gaban kwatance.Tunda Darusi yake karo da mazaje bai taba haduwa da zarton jarumi mai zafin nama,karfin sara da nauyi ba tamkar sarki

Damnash domin suna fara yin wannan gumurzu ne ya gane cewa lallai yaufa ya gamu da

gamonsa,amma saboda karfin imaninsa da dogaro da Allah ko kadan zuciyarsa bata karaya

ba.Sarila,Yazirina da Mujahid kuwa ko da sukaga irin salon yakin sarki Damnash kuma sukaga

yadda yake neman kuntatawa jarumi Darusi sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka fara tunanin cewa lallai wannan takadirin sarki zai iya samun nasara akan jarumi Darusi kuma da zarar ya gama dashi suma tasu ta kare.Nanfa zuciyoyinsu suka karaya suka kamu da tsananin bakin ciki gami da

karayar zuciya suka fara tunanin cewa dukkan burinsu na duniya ya rushe.Babban abinda ya

daga musu hankali shine koda aka sami kusan

rabin sa'a anayin wannan bakin gumurzun sai ya zamana cewa da kyar jarumi Darusi ke iya kare hare haren sarki Damnash kuma ko kadan baya iya mayar masa da martani saboda ya fara gajiya,shi kuwa sarki Damnash kamar ma a sannan ya fara gumurzun.Anan cikin haka ne sarki Damnash ya shammaci Jarumi Darusi ya daka tsalle sama ya kawo masa wani wawan sara a kafada.Darusi yayi amfani da hannayensa biyu ruke da takobi ya kare saran amma saboda karfin saran da nauyinsa saida kaifin takobin ya dira akan kafadar tasa ya yanke shi.Take jini yayi tsartuwa,Darusi bai san sa'adda ya kwala kabbara ba sakamakon tsananin zafin zogin da yaji amma sai shima ya yunkura cikin shammace ya daka tsalle sama ta gabzawa

Damnash duka da kafarsa a fuska.Saboda karfin dukan saida Damnash yayi katantanwa a tsaye sau biyu amma saiya tsaya cak ba tare daya fadi ba saboda tsananin jarumtaka.Koda Damnashi yaji danshi a kan lebensa ya shafa yafa ashe jini ya fito sakamakon bugun da Darusi yayi masa sai ya

kamu da tsananin takaici ya kurma uban ihu a karo na biyu sannan ya dubi Jarumi Darusi yace kaine Jarumi na farko daya taba samun nasarar fitar da jini a jikina,tabbas daga yau ba zaka sake samin irin wannan damar ba kuma yanzu take zan

maishe dakai tarihin da ko a labari ba za'a sake tunowa dakai ba.Darusi yace ni kuma yanzun nan da izinin ubangijina zan bar maka shaidar da saidai a binneka da ita a kabarinka kamar yadda za'a binne tarihin daukakarka da

jarumtakarka.Kafin Darusi ya gama fadin abin dake bakinsa tuni Sarki Damnash ya fara ja da

baya.Koda ganin haka sai shima Jarumi Darusi ya fara ja da bayan yana kirga takun da Damnash keyi har saida kowannensu ya kurawa abokin gwamin idanu suna tunani da nazari akan abinda zasuyi su sami nasarar hallaka juna.Duk wannan abu dake faruwa Mujahid,Sarila da Yazirina sun zuba idanu suna kallo cikin tsananin tsoro da fargaba.Kamar hadin baki sai Jarumi Darusi da sarki Damnash suka daga takubbansu sama a lokaci guda kuma suka rugo da gudu izuwa kan juna.Koda ya rage saura taku uku kacal su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama ya kaiwa dan uwansa mugun

hari.A tare suka diro kasa suna masu juyawa juna baya amma sai su Muhajid sukaga Darusi da Sarki Damnash sun kame cak kamar gumaka

kowannensu akwai jini a jikin takobinsa amma

kuma a sasssan jikinsu ba'a ga digon jini ba.Tsawon yan dakiku kimanin goma suna tsaye a kame kawai kuma sai akaga hannun sarki

Damnash na hagu ya tsinke ya fadi kasa jini ya kama zuba daga cikin dungulmin hannu amma

saboda tsananin juriya da jarumtaka sai sarki Damnash ya sunkuya ya dauki yankakken hannun nasa ya kura masa idanu yana mai tsananin

mamaki da takaicin yadda akayi jarumi Darusi ya sami nasarar sare masa hannu.Shi kuwa Jarumi Darusi sai gani akayi ya dafe gefan cikinsa

bangaren dama jini na zuba kuma ya durkushe

kasa bisa guiwoyinsa amma saiya yunkura cikin jarumta ya mike tsaye yaje inda dokinsa yake yana layi kamar zai sake faduwa,a haka ya bude jakar guzurinsa ya dauko zare da allura ya kama dinke raunin dake gefen cikin nasa da kansa.Har ya kammala dinke raunin Sarki Damnash na tsaye

ruke da yankakken hannunsa yana kallon hannun yana dukan kansa tamkar mahaukaci sabon

kamuwa.Kuma yana cizon lebensa saboda

tsananin takaici da bakin ciki.Daga can kuma saiya takarkare ya kwarara uban ihu,ihun nasa ya cika dajin gaba daya da amsa kuwwa ya firgita duk wani abu mai rai dake cikinsa.

Mu Hadu A ''Taskar Ajali' Littafi Na Shida(6) domin jin cigaban wannan kasaitaccen kayataccen labari.

TASKAR AJALI 5

Littafi na biyar 5

Na Abdulaziz Sani m gini

Ebook creat by Shuraih Usman

Ebook publish by www.hausaebooks.cf

Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai

Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]





TASKAR AJALI
Littafi na Shida 6
Littafin Abdulaziz Sani m gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]


Sannu a hankali kuma sai ihun nasa ya rikide ya
koma kuka,idanunsa na zubar da hawaye shabe
shabe,adaidai wannan lokaci ne Jarumi Darusi ya
karanta wata addu'a ya tofa akan raunin da sarki
Damnash yayi masa sannan ya mike tsaye daga
durkusan da yayi bisa guiwoyinsa ya goge jini
Damnashi dake jikin takobinsa a kasa cikin yashi
sannan ya mayar da takobin cikin kufenta ya daga
kai ya dubi sarki Damnash yace,tabbas ka cika
Gwarzon Mayaki kuma gawurtaccen jarumi da
bazan taba mantawa da biwarka ta jarumta
ba,amma ka tafi da yankakken hannunka izuwa
birninka idan tsafinka zai iya dinke maka hannun
ya koma daidai kamar yadda yake da to sai yayi
idan kuma bazai iya ba to lallai da dungulmin
hannu guda za'a binneka cikin kabarinka kamar
yadda nayi alkawari,kaga kenan na dakusar da
dukkan daukakar ka da kuma shahararka ta
jarumtaka a yanzu cikin kankanin lokaci bisa
taimakon ubangijina.Koda gama fadin hakan sai
Jarumi Darusi ya karasa inda Sarila ke kwance a
kas ya sunkuya ya dauketa ya goyata a bayansa
sannan ya dubi Yazirina da Mujahid yace ku tashi
mu shiga cikin kogon dutsen nan mu kwanta
domin dukkaninmu muna bukatar muyi jinya amma
wancan sarkin mai yankakken hannu a yanzu ya
fimu bukatar agajin gaggawa indai yana son ya
rayu dole ne ya gaggauta tsayar da jinin dake
zuba a dungulminsa.Koda gama fadin hakan sai
Darusi ya juya ya kunna kai izuwa cikin kogon
dutsen goye da Sarila ba tare da tsoron komai ba
duk da cewa kuwa basu caje kogon dutsen ba sun
tabbatar da lafiyarsa.Cikin hanzari Yazirina da
Mujahid suka yunkura cikin matukar karfin hali
suka mike tsaye suka ruke kafadun junansu suka
taka Yazirina na dingisa kafa suka bi Darusi a baya
izuwa cikin kogon dutsen suka kule.Sai bayan
kulewar tasu ne sarki Damnash yaji ya fara jin jiri
kuma ya kama yin layi daga tsaye saboda jininsa
dake zuba nan take ya sake kurma ihu wanda yafi
na farko kara da tsoratarwa sannan yayi sauri ya
yagi kasan rigarsa ya daure dungulmin hannun
nasa ya nannadeshi don tsaida jini,kawai sai ya
ruga izuwa kan dokinsa yai tsalle daya ya haye
kan dokin ya zunguri cikin dokin da
kafafunsa,dokin ya zabureshi da gudu da
baya,lafiyayyen hannunsa na ruke da yankakken
kuma ya cigaba da kwarar ihu tamkar wanda ake
sara a sannan.Kamar yadda Jarumi Darusi ya fada
haka al'amarin ya kasance wato saida suka shafe
kwanaki bakwai a cikin wannan kogon dutse suna
jinyar jikinsu amma a cikin kwanaki biyu rak raunin
Jarumi Darusi ya warke sumul tamkar ma bai taba
yi saidai tabo wajen kawai.A tsawon kwanakin
bakwai Darusi ne ke ta fama yin hidima ga Sarila
domin shi ke bata abinci da baki har ta koshi
sannan ya goge mata maikon bakin,idan zata
kawar da wata bukata sai ya bata wuri ta kawar da
bukatar idan ta gama zata kwala masa kira ya
dawo ya dauketa ya sake goyata ya mayar da ita
cikin kogon dutsen.Abinda baya yi mata kawai
shine sauyin tufafin jikinta wannan Yazirina ce keyi
mata duk da cewa ita ma tana da karaya a
kafarta.Mujahid da Yazirina sunyi matukar mamaki
bisa ganin yadda Jarumi Darusi ya rinka dawainiya
da Sarila tamkar yar uwarsa ta jini,alhalin ita ko
kadan bata sonsa a cikin zuciyarta.Duk tsawon
wannan lokaci babu wanda yaga fuskar Jarumi
Darusi a cikinsu bare yaga irin kamanninsa ko

Please Login or Register in order to submit comment